Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
1 / 13
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels MAGAJIN WILBAFOS Fita na biyu 2 Marubucin littafin Dr Abdullahi Muhammad Ibrahim Ebook creat by Shuraih Usman Ebook publish by www.hausaebooks.cf Ebook din nan yazo maku ne daga shafin www.hausaebooks.cf Kuna ziyartar shafinmu don samun sababbin littatafai Ga duk wanda ke bukatar ebooks nashi ya samu shiga cikin wepsite namu sai ya turo mana da littafin ta Email namu hausaebooks@gmail.com MAGAJIN WILBAFOS Marubuci: Dr Abdullahi Muhammad Ibrahim Babi na 51: Umarnin Ururu Post by: Shuraih Usman @shuraih 99% www.facebook.com/hausaebooks . Daga:- Taskar Magajin Wilbafos ___ SHEKARU DA SUKA GABATA (ALAƘA TSAKANIN HIDAYA DA ALJANI JIDAIME) ___ Hidaya ta ɓata rai tana duban aljani Jidaime wanda ke tsaye yana lilo akan iska, "Kasan mai yasa Ururu suka fi kowacce ƙabila ƙarfi a wannan zamani, ba komai bane saboda su basu dogara da aljanu ba. Saboda haka babu wata farar-laya da zata iya aiki a kansu. Sun dogare ne kachokam da ƙarfin Izzar dake cikin baƙaƙen idanuwansu. Haka nake so Armad shima ya dogara da ƙarfin jininsa na Wilbafos. Bana son ya dogare dakai a matsayinka na aljaninsa, domin hakan bazai kaishi ko'ina ba." Aljanin najin haka ya murtuke fuska, "Kina nufin kin raina ƙarfina ne. Kuma kema ai kina amfani da aljaninki, danme yasa kike so ki hana shi amfani da nasa." Hidaya ta ɗanyi murmushi sannan ta amsa da cewa ,"Bawai ina cewa ban yadda da ƙarfin ka bane, Jidaime. Kawai dai nasan akwai ƙarfin Izza irin wadda ni kaina ban san iyakacin ta ba acikin ruhin ƙani na, saboda haka ina so yayi amfani da ita maimakon ya dogara da ƙarfin aljaninsa. Saboda haka kayi haƙuri zan ɗaure ka ta yadda babu yadda Armad zai iya amfani da haƙiƙanin ƙarfinka. Kuma ina mai yi maka gargaɗi na ƙarsge da kada wani tsautsayi yasa ka ƙara haɗa kanka da aljani na domin yin hakan zai jawo maka hukunci. Aljani na bai taɓa biyayya ga Ururu ba kuma Ururu basu isa su baahi umarni ba. Kai kasan mai nake nufi." Tana rufe baki Aljani Jidaime ya fara jada baya yana neman guduwa, amma ina tuni Hidaya ta saukarda al'amudan Farar-laya akansa. Tun daga wannan rana yake a ɗaure, kuma basu samu wata damar ganawa da Armad ba sai a wannan lokaci. Hasalima Armad baisan cewa aljaninsa a matsayi ɗaya suke dana Ikenga ba. Kuma bawai kaɗai Walƙiya aljanin nasa yake sarrafawa ba. Kai a taƙaice ma wannan walƙiya ba daga aljanin nasa take fitowa ba. Tana fitowa ne daga ainahin cikin ƙarfin ruhin Armad wanda aka haifeshi dashi. Irin ƙarfin da yayarsa Hidaya take so yayi amfani dashi. _____ Acikin filin Jinzidal kuwa, har wannan sadauki mai muƙamin kyaftin ya ɗauki Armad a sume da niyyar tafiya dashi sai Uznu Ururu ya dakatar dashi. Uznu na tafiya taku ɗai-ɗai ya iso ga jikin Armad ya kuma saka hannunsa akan zuciyar Armad. Haka na faruwa wani haske ya fara fita daga jikin hannunsa yana shiga jikin Armad. ____ Acikin duniyar aljanun nan kuwa Armad yana tsaye yana tunani wacce shawara ya kamata ya yanke kawai sai yaga duniyar ta fara cika da wani baƙin haske. Lamarinda yasa shi ajiyar zuciya. Amma tun kafin ya gama gane maike faruwa yaga fuskar aljaninsa Jidaime ta canja. "Armad ko ka kwance ni yanzu ko kuma baza ka iya ƙara amfani da fasahar walƙiya ba." Aljanin ya faɗa cikin sauri da alamun tsoro. Idanun Armad suka cika da mamaki a lokacin da yaga canjin yanayin da aljanin ya samu kansa aciki. Nan take ya buɗe baki ya tambayi aljanin, "Mai yake faruwa?" "Uznu Ururu ne yake neman ƙara ƙarfin ankwar dake ɗaure dani. Ban san tayaya ba, amma da ƙarfin baƙaƙen idanun sa yana iya gani har cikin ruhinka. Wato dai a taƙaice yana ganinmu a halin yanzu. Kana da ƙasa da daƙiƙa biyar ka yanke shawara akan abinda zakai." Aljanin na rufe baki ya fara karkarwa lamarinda ya ƙara ruɗa Armad, domin har a wannan lokaci ya kasa yanke shawara. Abu ɗaya dai da Armad ya sani shi ne ba dukkan maganganun da aljanin ya faɗa zai yadda dasu ba, yasan cewa lallai ba'a raba aljanu da ƴan ƙarairayi nan da can. Amma a halin da yake ciki bashi da wani zaɓi face ya bawa wannan aljani dama yaga kozai iya kuɓutar dashi daga halin da yake ciki. Saboda haka Armad yayi tsalle izuwa wannan aljani, ya kuma ja ankwar da ƙarfin tsiya. Abun mamaki bai taɓa tsammani ba, amma kawai sai yaga ankwar tana murmushewa tana sakar wannan aljani. Wanda a iya lissafinsa cire ankwar zai ɗau lokaci kuma yana buƙatar makami kafin ya faru. Amma koda Armad ya tuna cewa ai ankwar ta tsafi ce, sai kuma ya gane yadda abin yake. Aljani Jidaime yai ƙaraji tare da miƙe hannayensa sama bayanda yaji shi a sake. Ranar daya daɗe yana jira tazo. Amma kafin ya fara komai yana buƙata ya kashe Uznu Ururu dake waje, wanda idan baiyi saurin yin hakan ba wannan baƙin hayaƙi zai iya ƙara ɗaure shi ya maida shi gidan jiya. Nan take ya finciko ruhin Armad daga wannan duniya ya dawo dashi izuwa jikinsa a wannan fili. Shi kuma ya bayyana a gaban Uznu Ururu yana mai riƙe da farin al'amudin aljanu a hannunsa na dama. Koda bayyanarsa sai dukkanin kyaftin guda biyar ɗinnan dake biye da Uznu sukai tsalle suka dira a gabansa domin su kare shi. Amma suna dira aljani Jidaime ya kawo wata muguwar wafta da al'amudinsa inda ya share su baki ɗayansu a lokaci guda. Sannan kuma yayi kan Uznu gadan-gadan. Lallai ƙarfin aljanu da bil-adama da banbanci. Nan da nan fuskar Uznu ta canja, yanayin firgici ya bayyana akanta. Amma a wannan lokaci ne ya ciji ɗanyatsansa na dama, inda jini ya fara ɗisa. Uznu baiyi wata-wata ba wajen saka wannan jini acikin idanunsa baƙaƙe guda biyu. Ai kuwa haka na faruwa wani baƙin haske ya fara ɓulɓula daga ciki, sannan Uznu ya fara magana, "Ina mai umartarka da ƙarfin Ururu dake jini na, da ƙarfin Ururu dake bisa ƙasa ta farko daka tsaya a inda kake." Abin mamaki yana rufe baki wani irin ƙarfin izza marar misaltuwa mai cike da buwayar Ururu ya fara ambaliya acikin filin. Kan kace meye wannan aljani Jidaime ya tsaya a inda yake cak ya kasa motsi. Sannan kuma Izzar Uznu ta fara hawa tana ambaliyar har saida takai Shekaru dubu huɗu da ɗari tara da casa'in da tara. Uznu ya cafi takobinsa yayi kan aljani Jidaime. Tun kafin ya ƙarasa akaji muryar aljanin na cewa, "Idan ka kashe ni kasan ƙabila ta baza suyi shiru ba. Kuma babban sarki Ururu Kuyurussa'ayi yayi mana katanga daku..." Yana magana yana karkarwa, kuma ganin cewa Uznu baya saurarensa kawai sauri yake ƙarawa yasa tsaya ya kasa ƙarasa abinda yake faɗa tare da fara karkarwa. Uznu na ƙarasowa yasa takobinsa ruwan toka ya tsarge aljani Jidaime gida biyu. Aljanin yai wata ƙara mai firgitarwa, inda daga bisa ya fara narkewa izuwa toka yana murmushewa. "Da kasan da tsakanin da akai mana da baka tunkare ni ba. Ko ba komai ina da hujja idan aka je gaban babban sarki Ururu Kuyurussa'ayi." Uznu na magana yana goge takobinsa. Sannan nan take ya ɗau Armad ya ɓace daga wannan filin gasa. ___ A can gefe guda kuwa sarki Deniz Iluru da dakarunsa suna tsaye suna kare duk wani hari da yayo kan ƴan kallo a lokacin da ake wannan fafatwa tsakanin Uznu da su Armad. Duk da kuwa cewa tunda Uznu ya buɗe idonsa dukkan ƴan kallon suka sume, amma bayan da aka gama komai hankali ya dawo jikinsu saida hukumar yaƙin garin tayi amfani da rahoton ƙarya na cewa girgizar ƙasa ce tasa aka tsayar da gasar wannan shekara. Amma ta ƙarƙashin ƙasa sarki Deniz Iluru ya rubuta ƙara izuwa fadar Ururu dake ƙasa ta biyu mai kula harkokin Jinzidal akan su hukunta Uznu Ururu saboda cikas ɗin daya kawo a gasar Jinzidal ɗin. Cewa kuma suna fata ai musu adalci. To haka dai aka kawo ƙarshen wannan gasa ta Jinzidal ta wannan shekara. ____ To ALLAH ya kawo mu ƙarshen Jinzidal. Yanzu zamu shiga wani sabon sashi na wannan littafi. Duk mai tambaya ko kuma wani abu da bai gane ba a babika 50 da suka wuce ya rubuto a comment. Nidinne dai Shuraih Usman inkiya 99% Daga taskar magajin wilbafos MAGAJIN WILBAFOS Marubuci: Dr Abdullahi Muhammad Ibrahim Babi na 52: Dordor mai waka Post by: Shuraih Usman @shuraih 99% www.facebook.com/hausaebooks . Daga:- Taskar Magajin Wilbafos Doron ƙasa na huɗu Shalkwatar Mayaƙan Ururu ____ Sahu-sahu ne na mutane ɗai-ɗai har sahu ɗari, kowanne ɗaya daga cikin wannan sahu yana ɗauke da mutane guda ɗari. A taƙaice dai mutanen dake cikin wannan sahu su dubu goma ne. Dukkaninsu na sanye da baƙaƙen kaya. Babu mai ko magana acikinsu. Kai ko tari babu maiyi. Dukkanin wannan mutane ba kowa suke jira ba illa kwamanda Uznu Ururu. Uznu Ururu dai yaje ƙaro ilmi a jami'a mafi girma a duniya dake bisa doron ƙasa ta farko. Jami'ar da ake kira da Namibiya da yaren Aldurish na Ururu. Saboda daɗewar da yayi nema baya nan suka shirya masa wannan gagarumar tarya. Amma bisa mamaki Uznu yana bayyana kawai tsayawa yayi kimanin daƙiƙa ɗaya, inda ya kyaɗa musu kai alamun jinjina sannan yai ɓangaren inda ofishinsa yake. Koda yake baza a iya kiran wajen na Iznu Ururu da ofishi ba kaɗai, tunda iya girman wajen kaɗai yakai wani ɗan ƙaramin gari. Sannan kuma ga shirye-shirye na musamman na al'amura da suka shafi Izza da ake gudanarwa a wajen. Kusan zaka iya cewa duk wani sinadari da za'a iya samu a ƙasa bakwai akwai a wannan ɓangare na Uznu Ururu, kasancewar shi ɗin yawanci kayansa daga doron ƙasa ta farko yake tahowa dasu. Amma dukkanin wannan abubuwa basu suka dami Uznu ba, a yayin da cikin sauri ya shige wani ƙaton ɗaki na bincike-bincike inda yana shiga ya turo ƙofa ya rufe, tunda dama babu kowa acikin ɗakin. Sannan ya zaro wani ɗan irin Ayrid na musamman daga aljihunsa ya karanta wasu ɗalasimai, wanda nan take wannan Ayrid ya fara ƙara girma yana girma har saida ya kai girman ƴar ƙaramar ƙofa, inda nan take wannan irin Ayrid yai aman Armad ta cikin wannan ƙofa. Uznu ya fizgi Armad ya kwantar dashi akan wani ƙaton taburi na aiki. Sannan kuma ya fara karanta wasu ɗalasimai wanda suka saka wani farin haske ya fara cika ɗakin. Nan take wasu Rauhanan aljanu guda biyu, ɗaya mai ƙaho ɗaya mara ƙaho, suka bayyana, suna bayyana suka zube a gaban Uznu, kana gani kasan alaƙar dake tsakaninsu bata wuce ta bawa da ubangidansa ba. Uznu ya amsa sannan ya fito da wasu fararen takardu daga aljihunsa guda biyu ya miƙa musu. Sannan ya fara jawabi da cewa, "Kunga wannan shi ne karo na biyu da muka shigo da Littafin takobi wannan ɗaki acikin shekaru ɗari da suka wuce, saboda haka haka ina fata zamu kiyaye duk abubuwanda suka sa a wancan lokaci bamuyi nasara ba." Ya kalli aljanin mai ƙaho daga cikin guda biyun yace, "Kalkutu kasan mai zakai." Sannan ya juya izuwa mara ƙahon, "Kaima Netti kasan meye aikinka." Uznu ya ci gaba da bayani a yayinda wannan aljanu biyu suka nutsu suna saurare, "A bisa bincike na na gano cewa Littafin-takobi yana da rai yana kuma da hankali nasa na kansa. Kawai dai ba irin yadda mutane da aljanu suke ba. Kuma ta hakan nema na gano cewa indai akwai ma'aboci Ururu a waje to Littafin-takobi bazai taɓa baƴyana kansa ba. Kuma hakan ba abin mamaki bane tunda shi wanda ya samarda Littafin takobin ɗan adawar gidan mune na Ururu. "Saboda haka a lokacin da za'ai wannan aiki dole ne ya zamanto bana kusa da wannan yaro, in ba haka ba wannan Littafi bazai taɓa bayyana kansa ba. "Sannan kuma a wani binciken da muka gudanar a jami'ar Nimibiya mun gano cewa wannan Littafin ya zaɓi ƴan zuri'ar Wilbafos har a karo biyar daga cikin karo bakwai da ya taɓa zaɓar wani. Kuma shima wannan yaron daya zaba ɗan zuri'ar wilbafos ɗinne. Amma babban abinda zaku riƙe ku kiyaye shi ne, Littafin-takobi yana bayyana ya taimaki waɗanda ya zaɓa. Saboda haka hanya ɗaya da zamu tabbatar ya bayyana shi ne mu tabbatar da cewa mun azabtar da wannan yaro ta kowacce hanya ƙololuwar azabatarwa tayadda Littafin zai fito da kansa ya taimakeshi. Da zarar ya fito kunsan abinda zaku yi na gaba, saboda haka ku fara aiki. "Zan shiga shalkwata na fara shirye-shiryen sarrafa wannan Littafi tayadda kuna zaƙulo shi kawai aiki zamu fara akansa. A tafiya ta zuwa doron ƙasa ta farko na samu dama na tattautana da Babban ɗan sarki Kuyurussa'ayi, yarima mai jiran gado Níwajítu Dúmaƙísu Kuyurussa'ayi. Kuma ya bada koyon bayansa ɗari bisa ɗari akan abinda muke niyyar yi da wannan Littafi. Saboda haka lallai sai mun tabbata munyi nasara a wannan karan." Bayan Uznu ya tabbatar da cewa aljani kalkutu da Netti sun fuskanci halinda ake ciki sai ya fita ya barsu domin su fara aiki akan Armad. ________ A can wani sashin duniya dake ɓangaren Ikwatora na doron ƙasa ta shida kuwa wata mace ce kwatsam ta bayyana cikin jini kuma a sume. Lallai kana ganinta zaka san gab take da mutuwa, kuma lallai idan ba'ai wani abu akanta ba, to babu makawa mutuwa zatai. A tsakiyar inda wannan mace ta bayyana kamar wata daula ce ta Dordor launi-launi. Domin kuwa duk inda ka duba su zaka gani. Babu gida gaba babu gida baya a wannan daji da take, babu kuma abinda kake ji sai kukan tsuntsaye da maganganun jinsin halittar nan da ake kira da Dordor. To kamar masifar da wannan mata take ciki bata isa ba, sai kurum wasu daga cikin Dordor dake wajen suka hange ta. Ai kuwa nan take manyansu suka fara isa wajen. Amma bisa mamaki kowanne Dordor idan yazo ya shanshana wannan mace sai kawai yai tsaki ya juya kai ya tafi. Kuma dukkanin waɗannan dordor da suke zuwa kanta suna da kai sama da biyar. Kuma kowannensu fatar jikinsa nada launi na daban. Babu kuma wanda keda Izza ƙasa da ɗari biyar acikinsu. Lallai koda wannan mace na cikin hayyacinta bata ishe su kallo ba. To abu ne dai sananne a duniya cewa Dordor mai kai biyar zuwa sama shi ake cewa Babban Dordor, sannan kuma babban Dordor baya cin naman halittar da Izzarta bata kai ɗari biyar ba. Saboda haka dai ga dukkan alamu wannan mace ta taki sa'a. Sai dai kuma ana haka bayan waɗannan manyan Dordor masu kayika da yawa sun bar kanta sai ga wani Dordor nan mai kai biyu ya gabato, yana tafiya a hankali kana ganinsa kasan a yunwace yake. Tun daga nesa ya hangi wannan mace ya kuma fara murmushi da kansa na dama, sannan kuma yana dariya da waƙa da kansa na ɓangaren hagu. *Abinci ya samu Yau yau abinci ya samu Abinci har da kalace Abinci ya samu Abinci ya samu* Haka dai wannan aljani ya wanzu yana gudu-gudu sauri- sauri yana waƙa har ya isa inda wannan mace ke kwance. Abune sananne ansan cewa jinsin fararen Dordor sha'irai ne ma'abota waƙa, kuma sukan rera waƙa musamman a lokacin da suka samu abinci. Hakan nema yasa waƙa taƙi ƙarewa a bakin wannan Farin Dordor wanda kaf komai a jikinsa fari ne fat tun daga gashin kansa har zuwa fatar tafin ƙafarsa. Dordon ya miƙa farin hannunsa wanda yafi farar-ƙasa fari ya juyo da fuskar wannan mace. Sannan ya zaro wata ƴar ƙaramar wuƙa daga aljihunsa da niyyar ya fara yankar naman wannan mace yana kaiwa bakinsa-na- waƙa. Amma kafin ya fara komai ya ɗaga hannu ya fara da addu'a, "Godiya ga ubangijin daya jefowa da farin Dordor naman bil-adama. Muna fata gobe ma a bamu! Ameen!" Wannan Dordor ya shafa wannan addu'a sannan yai azama wajen fara yankan naman jikin wannan mace. Idan ka kalli fuskar wannan mace zaka ga ba wata bace illa Nusi ƙawar Armad wilbafos, wadda kwamanda Uznu Ururu yai cilli da ita aka nemeta aka rasa tsahon lokaci. Nidinne dai Shuraih Usman inkiya 99% Daga taskar magajin wilbafos MAGAJIN WILBAFOS Marubuci: Dr Abdullahi Muhammad Ibrahim Babi na 53: Bakar guguwa Post by: Shuraih Usman @shuraih 99% www.facebook.com/hausaebooks . Daga:- Taskar Magajin Wilbafos ___ A kowanne yanki na Ikwatora dake kowacce ɗaya daga cikin ƙasashe bakwai na duniya, akwai wani tsibiri wanda shi ne waje da ma'abota wannan yankin suke gani a matsayin tsarkakakken waje. Wannan tsibiri shi ake cewa Tsibirin-guguwa. A duk bayan kowacce shekara sittin wata guguwa mai ƙarfin gaske na tasowa daga Tsibiri. Wannan guguwa ita ake kira da Baƙar guguwa. Duk lokacin da aka fara ta akanyi watanni kamar biyar ana yinta, kuma anyi ittafaƙi wannan iska tana da ƙarfin da zata iya tarwatsa duwatsu da ƙarafa da al'amudai komai girmansu. Amma acikin wannan guguwa ake fitarda shugaban da zaiyi mulki a kowanne shashi na ikwatora a shekaru sittin masu zuwa. Hanyar kuwa mai sauƙi ce, duk wanda yake so ya tsaya takarar wannan kujera saiya fito ya kuma tsaya a tsakiyar wannan guguwa har tsahon wannan watanni biyar, indai aka kammala iskar duk wanda yai ragowa shi ne zai zama shugaba a wannan sashi na Ikwatora har tsahon wasu shekaru sittin masu zuwa. To amma mulki dai bashi kaɗai ne abinda ake muradi ba a shiga cikin wannan guguwa ba. Babban abinda ake muradi shi ne sadakar baiwa da ake acikin wannan iska. Babu wata irin baiwa a duniya ko kuma wani sihiri ko kuma wata fasaha wadda baza a iya tsinta ba acikin wannan iska ba. Sabida haka nema wasu sukan siyar da ransu su shiga duk da kuwa sunsan cewa ƙarfin Izzarsu bai kaiba, amma saboda kwaɗayin wannan baiwa da ake samu. To wannan dai shi ne kaɗan daga cikin Tarihin wannan sashi na Ikwatora inda a dai-dai wannan lokaci Nusi take kwance rai a hannun ALLAH tana jira Dordor mai kai biyu yayi layya da namanta. Sai dai kuma kash, lallai naman Nusi yafi ƙarfin wannan Dordor, domin kuwa a dai-dai wannan lokaci ne aka fara busa wata sarewa wadda duk wanda ya rayu a sashin Ikwatora yasanta. Sarewar da take nuni da cewa lokaci yayi. Wato shekaru sittin sun kewayo kenan. Ai kuwa wannan busa tana isa kunnen wannan Dordor yai tsalle gami da cilli da wuƙar dake hannunsa, sannan ya taka a guje. Bawai shi kaɗai bama, duk wani Dordor dake wajen babu abinda yake face gudu izuwa maɓoya. Tunda dama a wannan lokaci tuni lissafi ya cika, kuma a kowanne lokaci ana jira ne kawai aga baiyanar wannan guguwa. Hakan nema yasa a lokacinda Nusi ta bayyana ta iske manyan Dordor suna tsaye cirko-cirko a wannan waje. Ba jimawa da fara wannan busa sarkin dake mulki a wannan lokaci wanda ya kasance Dordor ne mai kai tara ya bayyana sanye cikin kayan yaƙi. Kowanne ɗaya daga cikin kayikansa tara yasha kwalliya ta kayan yaƙi. Lallai kana ganinsa kasan ya shirya saiya koma kan wannan mulki. Izzaraa kaɗai shekaru dubu bakwai da tamanin ce. Sannan kuma fatar jikinsa da komai na jikinsa Ja ne. Sai dai kuma amma bawai shi kaɗai bane, akwai sauran zaratan tsofaffin Dordor da mutane ma'abota Izza wanda suma suke neman wannan muƙami da kuma baiwa da za'a raba a cikin wannan baƙar guguwa. Babu wanda yake cikin filin nan wanda Izzarsa bata kai dubu biyar ba acikinsu, sannan kuma babu wanda baiyi shekaru samada da hamsin yana shirin wannan rana ba sai mutun ɗaya. Wato Nusi kenan. Ba jimawa gari yai duhu, ko tafin hannu ba'a gani, sannan kuma daga bisani Baƙar guguwa ta fara sauka. Sadaukai suka fara fitowa da shirye-shiryensu da suka tanada. _______ Babu wanda yasan taƙamaimai maike faruwa acikin wannan baƙar guguwa, domin a duk bayan shekaru sittin mutun ɗaya ne kaɗai yake samun nasara, shi kuma tarihi yazo cewa indai ya bayyana abubuwan da suka faru aciki to duk wata baiwa daya samu zai nemeta ya rasa. Hakan yasa sai dai kawai ka samu shaɗi faɗi, amma taƙamaimai babu wanda yasan maike faruwa. To haka dai wannan iska taci gaba da wanzuwa tsahon lokaci, wata ɗai-ɗai har wata biyar. Sannan daga bisani ta fara lafawa. Inda alƙalan kowanne yanki suka fara fitowa domin suga wane ne sabon sarkinsu. Saida aka ɗauki wasu kwananki ukun cir, sannan komai ya lafa gari yai haske. Alƙalai suka gabato cikin filin da aka gudanar da wannan gasa. Amma bisa mamaki maimakon su tararda sarki sai suka tararda da sarauniya. Wata mace ce mai kyawun sura baƙar fata. Tsaye take riƙe da kambun nasara wanda duk wanda yaci nasara yake samu. Babu alamun ciwo ko rauni a tattare da ita. Kana ganinta kasan ta cika jaruma irin ta mutanen farko. Idanunta suna fitarda farin hasken mai ɗauke da Izza abar girmamawa. Abin aljabi wata ƴar ƙaramar tukunyar dinare ce a hannunta na dama, sannan kuma a hannunta na hagu wata ƴar ƙaramar bishiya ce mai yawan koren ganye. Amma da dama zasu fi yadda dani idan nace babban abin mamakin shi ne wannan sarauniya ba wata bace illa Nusi. Wannan alƙalai suna ganinta suka zube a ƙasa cikin gaisuwa da biyayya. To wannan dai shi ne abinda ya kasance da Nusi bayan rabuwarsu da abokinta Armad wilbafos. ____ A can cikin fadar Ururu kuwa yau ankai wata biyar kenan aljani Kalkuta da aljani Netti suna azabtar da Armad duk domin Littafin takobi, amma babu labari. Tuni hankalin Arnad ya gushe yafi sau ɗari yana dawowa. Amma a kowanne lokaci sai dai aljanun su ƙara ƙarfin azabar da suke yi masa. Tuni Armad yaci alwashin kashe wannan aljanu guda biyu da danginsu da kuma Uznu Ururu. Yayi kuma alƙawarin lallai bazai mutu ba saiya ɗau fansar abinda sukai masa. Idan kuwa a sakamakon tsare shi da sukai anan babarsa ta mutu, to lallai saiya kashe duk wani ma'aboci Ururu sannan zai huce. Ana cikin haka ne Armad yaga watarana wannan aljanu guda biyu sun shigo wannan ɗaki. Suna zuwa suka ɗaure shi, sannan suka rufe masa fuska suka fice dashi daga cikin wannan ɗaki sannan suka ɓace sukai yamma. ___ To ko ina suka tafi da Armad? Nidinne dai Shuraih Usman inkiya 99% Daga taskar magajin wilbafos MAGAJIN WILBAFOS Marubuci: Dr Abdullahi Muhammad Ibrahim Babi na 54: Cinikin Bayi Post by: Shuraih Usman @shuraih 99% www.facebook.com/hausaebooks . Daga:- Taskar Magajin Wilbafos Aljani Kalkútu da aljani Netti na keta hazo suna tattauna al'amuran da suka shafi wannan yaro mai suna Armad da suke azabtarwa. Aljani Netti dai shi yake magana a wannan lokaci, "Babu abinda ba muyiwa wannan yaro ba amma littafin takobi yaƙi fitowa. Yau wata biyar kenan, indai abu sunansa azaba a duniya to munyi masa shi, amma babu labari. Ni ina ganin shawarar da shugaba Uznu ya bayar tayi dai-dai amma kai naga hankalinka bai kwanta ba." Kalkutu yai kyaran murya gami da kallon Armad wanda ke ɗaure a bayansa ya ce, "Eh.... Haka ne, amma kana ganin siyar dashi a matsayin bawa shi ne zaisa Littafin- takobi ya fito. Kada ka manta da irin azabar da muka gana masa. Ai ina ganin azabar da mukai masa tafi azabar siyarwa a matsayin bawa." Netti ya gurgiza kai tare da cewa, "Eh da wannan dan wannan, amma koma dai mene ne yadda aka umarce mu haka zamu yi. Zamu je mu siyar dashi a matsayin bawa ga ɗaya daga cikin sarakunan Jinzidal ɗinnan. Sannan kuma zamu ci gaba saka ido a kansa har illa mashaALLAH, har sai sanda Littafin ya fito. Wataƙila idan yaji azabar bauta Littafin ya bayyana." Haka dai suka ci gaba da tattauna yadda suke shirin siyarda Armad a matsayin bawa. ____ Ranar sha tara ga watan goma na kowacce shekara, ita ce ranar da aka tana da domin yin gagarumin taron da za'a gabatar da dukkan bayin da aka samo ta hanyar gasar Jinzidal. Duk wani mai iko yazo ya siyi abinda yake so. To kamar dai yadda aka sani sarakunan Jinzidal guda biyar sune suke gudanar da wannan ciniki, kuma sukan rarraba wajen gudanarda wannan gasa a kowacce shekara a tsakaninsu. Idan wannan shekara a ƙasar wannan sarkin akai, wata shekarar sai aje ƙasar wani sarkin. To a wannan shekara a ƙasar sarki Rafiya ake wannan taro. Sarki Rafiya ɗaya ne daga cikin sarakuna biyar na Jinzidal, kuma yana da iko akan miliyoyin mutane da kuma ɗaruruwan ƙasashe. Wajen da aka

Chapter 1 of 13