Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
9 / 9
cikin kangin da Allah ya fitar dani" . . Ba abinda xance maka sai dai inyi maka fatan samun wata macen" amma badai ni ba" nagode da soyayyar da ka nuna mani a baya" Anyi mun miji" . Ina patan wannan itace haduwarmu ta karshe wacce xanji furucin soyayya daga gareka" sai dai furucin xumunci da kuma furucin alakar dake tsakanina daku" A matsayina na kawar kanwarka Umma" na gode" sai watarana" Fatima ta tafi tana share hawaye" ta sgige gida tabar mujahid a durkushe yana xubar da nasa hawayen" . ======>+++++ß+++++<======= . Duk abinda akeyi xabba'u da Asma'u basu san dalladi yaje ya wargaxa musu shiri ba" xabba'u taji shiru mujahid ya daina kiranta" Har aka kwana biyu baixo gidansu ba" kuma ko (messege) bai turo mata ba" idan ma tafiya yayi" Data fahimci ba lafiya ba" saita kira Asma'u" Kwana biyu mujahid bai kirani ba" baixo gidanmu ba" kuma ina so in kirashi inji ko lapiya" amma kince in daina kiransa" sai dai shi ya kirani" Asma'u tace da xabba'u-: "ki bari ni xan kirashi inji" Amma ke ya xaki kira saurayinki?" sai ya raina ki" yace kin damu dashi" . . Asma'u ta kira mujahid yaki daga wayar har ta katse " ta sake kira" yaki dauka" ta kirashi a jere yakai sau biyar" amma bai dauka ba" Don haka sai ta kira xabba'u tace da ita-: "mutumin nan da gaske yakeyi xabba'u aji yake ji" ya kamata muje mu sameshi tare dake" mu sauke masa lodi" ya dawo normal" xabba'u ta tambayi Asma'u" "yaushe xamuje?" kuma a ina xamu same shi?" Asma'u ta ce-: " wajen aikinsa mana" banki" ya isa mu bishi gida ne?" ki bari sai da yamma idan sun tashi sai mu daidaici lokacin da yake fitowa" mu sameshi a waje" . . Da yamma misalin karpe biyar lokacin da mujahid yake tafiya gida" xabba'u wacce tabi Asma'u gida suka hau tasi ta kawosu bankin" Da suka hango motar mujahid a waje sai suka samu wuri suka tsaya" suka ki shiga ciki" suna nan sai suka hangi fitowarsa yana sauri xaije inda motarsa take" Asma'u da xabba'u suka je suka same shi" sai dai daga kai yayi ya gansu a gabansa ransu a bace" ko sallama basuyi masa ba" Asma'u ta bata fuska tace dashi-: . . "Dama wucewa xamuyi" hanya ta biyo damu shine muka hangeka" nace muxo mu gaisa" Da kyar da shawo kan mutuniyar ta shigo" tunda ka yada ita kwana biyu" mujahid ya cire hannu iya karpinsa ya tsinke Asma'u da mari saida ta fadi kasa" ta fasa kuka wanda hakan ya jawo hankalin mutanen da ke kusa da wajen" suka waigo don ganin ko menene ke faruwa" Xabba'u taja da baya a tsorace" tayiwa kanta kiyamul-laili" don kada a hada da ita" . . Mujahid ya nuna Asma'u da yatsa yace da ita"-: muguwa bakar munafuka" kedai annoba shegiya" Allah yayi mana tsari dake da masu hali irin naki a duniya" axxaluma annamimiya" duk makircin da kuka yimun kika rani da masoyiyata tagari fatima bai isheki ba shine kike sake biyo ni har nan" xaki sake cuta ta ko?" to asirinki ya tonu" na gane komae" duk abinda kuka kulla ya dawo kunnena" ya koma kan xabba'u wacce tayi turus kamar xatayi kuka" yace da ita-: "ke kuma shashasha mara hankali! Ashe kece kike biye da wannan muguwar kawar taki" ta ixa ki kika yiwa 'yar uwarki sharri da kaxapi" mutanen da suka rike ki amana tun kina jaririya" sune cinki da shanki" sune suturarki da ilminki" sune komae naki na rayuwa" Amma kika biyewa wannan shaidaniyar ta rabaki dasu" bari in fada maki" daga yau bani ba ke" kada ki kara kusantar inda nake" bana son ki" kuma a tsane ki" Ina kuma jawo hankalinki daki yi gaggawar komawa wajen 'yar uwarki ki nemi afuwarta" Idan kika sake Hajiya ta mutu baki roketa ta yape maki ba" duk duniyar nan sai kin rasa wajen tsayawa" sakarya! Sokuwa! Mara wayau!" . . Mujahid ya shiga motarsa ya tayar" suka kauce suka bashi hanya a guje da suka ga yayi ribas yayo kansu da motar" kafin ya tafi ne ya leko da kansa yana hararar su yace-: Da kun tsaya mana" in take ku in rage mugun iri" ko duniya ta samu sauki idan baku" ya 2ka ya tafi ya basu wuri yahau titi" . . Asma'u ta cira kai a fusace tana kuka tace da xabba'u-: meye ampaninki kina kallon shi yana yi mana wulakanci" amma kin kasa cewa komai" baki da katabus!" Xabba'u wacce xuciya ta kusa kasheta" tace da Asma'u "Rufe mani baki" duk wa ya jawo mani wulakanci idan bake ba" Ina xaune a cikin 'yan uwa lafiya" da baki ixani ba da nace ina sonshi" da yanxu ina nan lapia tare dasu" ke kika jawo mun kome ya paru" . . Xabba'u ta fara kuka tace da Asma'u-: "kin cuci rayuwata" kuma kin jawomun abun kunya a titi" baxan taba yape maki ba" Daga yau bani ba ke" xan koma wajen 'yar uwata in roketa ta yape mani" mu sasanta duk abinda mujahid ya pada gaskiya ne" kece kawa uwar gami munafuka" muguwar kawa" . . Xabba'u ta tafi ta bar Asma'u tana kuka" mutanen dake wajen suka taru suna kallonsu ita da kawarta suna fada" xabba'u ta wuce su" bata daga kai ta kallesu ba" . ====>++++++ß+++++++<====== . Da xabba'u taje gida tana kuka" ta samu mahaifinta ta fada masa duk yadda gaskiyar al"amarin yake" tace dashi muguwar kawarta Asma'u tayi mata ingixa mai kantu ruwa" ta fada masa duk makircin da suka yiwa fatima da sharrin da tayiwa Hajiya da Alhaji tace sun koreta" . . Da mahaifinta malam Aßußakar yaji haka sai ya kira matansa biyu yace da xabba'u ta maimaita abinda ta fada masa" ta sake maimaitawa tana kuka" mama Hajara tace-: "shiyasa tun farko nace abi maganar nan cikin nutsuwa" kada ayi saurin yanke hukunci malam" kaga yanxu gaskiya ta nuna" an xalunci Hajiya binta" . . Malam Abubakar yayi nadama" "to nima dole in dorawa kaina laifi a nan" domin kuwa na dauki so na dara akan xabba'u bana so a fadi laifinta" na shagwaba ta" tun farko da ban nuna mata haka ba" duk wannan al"amari da bai faru haka ba" A ranar ya aika yace yana son Hajiya binta taxo cikin sauri" Da xuwanta ta sameshi yana hawaye" xabba'u kuma tana kuka a gidan" malam Abubakar yace da ita-; "Ni na haifeki binta" amma nayi maki laifi" ki yape mani" Hajiya tace-: "Na yape maka baba" kuma na godewa Allah daka gane gaskiyar wannan al"amari" Ya fada mata duk abunda xabba'u ta fada ya kira xabba'u yace-: "Ga 'yar uwarki nan ki roketa gapara" ta yape maki" xabba'u ta durkusa gaban hajiya binta tana kuka" . . "ki yape mani hajiya" nayi maki butulci" ki gaparceni" sharrin shaidan ne da kuma muguwar kawata Asma'u wacce ta ixani nayi duk wadannan abubuwa gareki" Hajiya binta ta kama Hannunta" "Na yape maki xabba'u na yape maki duniya da lahira" malam Abubakar yayi musu nasiha mai tsawo" sannan yace da Hajiya idan taje gida tace da Alhaji shima yaxo yana son ganinsa" domin ya bashi hankuri akan laifin da xabba'u tayi musu" . . Hajiya binta tace da xabba'u "Dauko kayanki mu koma gida" xabba'u tace-: "A,a Hajiya" baxan iya komawa ba" bayan abubuwan da nayi muku" musamman fatima" tayaya xan iya kallon fatima a halin yanxu?" Hajiya binta tace-: "Ba komai" duk wannan ta wuce" fatima ma ta samu miji yanxu lokaci kawai ake jira" Xabba'u taki yarda ta koma" don tana jin kunya" Hajiya binta ta rabu da ita" ta tafi gida" data koma ne ta sanar da Alhaji sunusi abunda ya faru duka" tace baba yana son ganinsa" ita kuma xabba'u tana jin kunya taki yarda ta dawo" . . Alhaji sunusi yayi dariya yace"-: "Allah sarki! Tunda ta gane kuskurenta ai komai ya wuce" muma 'yan adam muna yiwa Allah laepi ya yape mana" ta yaya baxamu yape wa mutane 'yan uwanmu ba?" Da yaje gidansu Hajiya binta ne ya samu malam Abubakar sukayi maganar" ya bashi hankuri" sai Alhaji sunusi yace da mama Hajara ta dauko Akwatin xabba'y ta taso ta su tafi" mama Hajara ta taso xabba'u da kayanta" Alhaji sunusi ya amshi akwatin ya tasata suka fita" suka shiga mota" ya dawo da ita gida wajen 'yar uwarta" Hajiya binta" suka ci gaba da xamansu kamar yadda suke a da tun parko" xabba'u ta dawo tana girmama fatima domin kuwa tasan tayi mata laifin da baxata taba mancewa dashi ba a rayuwarta" . ====>+++++ß++++++<======== . Wata daya da fara haduwar fatima da dakta Usman aka tsayar da lokacin aurensu wata biyu masu xuwa" mama Rakiya da Umma har gida suka xo suka yiwa Hajiya binta murna" da lokacin auren yaxo" kowa yasan fatima ta auri babban mutum" Bayan akwati goma sha biyu daya ciko mata su da kayan lepe masu tsada" ya kashe kudi masu yawa wajen shagulgula" Umma da xabba'u suna cikin manyan kawaye na gaba" sati daya fatima tayi da angonta a kaduna" daga nan sukayi bankwana da 'yan uwa ya dauketa suka keta haxo xuwa kasar malesiya" Inda fatima taci gaba da karatunta acan" : . Duk bayan kwana biyu sai fatima tayo waya a gida" tana dadewa suna hira da babbar kawarta Umma" daga baya da aka canxawa mujahid wajen aiki ya koma ibadan da xama". . . Umma ta samu wani saurayi wanda suka taba yin soyayya da dadewa kafin ya tafi aikin soja" da ya dawo ne ya sake xuwa wajenta soyayya ta dawo sabuwa" aka tsayar da lokacin aure wata uku masu xuwa" . . Samßarka! Ita ma xabba'u ta samu nata wani ma'aikaci ne a hukumar wutar lantarki" ta dai samu yadda take so domin kuwa shima akwai 'ya'yan banki" fatima tayo waya daga malesiya tace taci gaba da karatunta" kuma tana xaune da mijinta dakta Usman lafiya" . . Da lokacin bikinsu xabba'u da Umma ya karato ne" suka dawo gida ita da mijinta" yayi kwana Uku ya koma" ya barta idan aka gama bikin sai yaxo ya dauke ta" su koma" . . Saida fatima ta dawo ne aka ga kyanta ya wuce na amarci" sannan kuma sau biyu tana kyarawa Hajiya amai a tsakar gida" ba wanda ya tambayeta abinda ke damunta" domin kuwa ance inkaji gangami to da LAßARI........" . . KARSHE...... DAGA mai debe muku kewa" SHAFI'U DAUDA GIWA" MAI GIDAN LITTAFI" . . NI Sadeeq shehu shariff Aßßαη ßαѕмαян Dαη мυтαη уσßє Dana kawo muku kofin labarin nake cewa ku huta lapia" . . INA KUMA godiya ga dukkan daukacin jama,ar da ke cikin wadannan xauruka "TASKAR GIDAN LITTAFI" . TSANGAYAR MARUBUTA . DUNIYAR MARUBUTA SOYAYYA RAYUWA CE . GIDAN LITTAFI PUBLISHER'S . Musamman wadanda sukayi bitar karatun wanga labari" dana suburbudo" Ina maiyi musu godiya game da patan alkhaeri" . . SAI KUN sake jina a wani sabon labarin" . . GAISHUWA TA MASAMMAN GA MADUGUN TASKAR GIDAN LITTAFI" . # ILIYAS_ISHAK_GUNDUTSE AßßAN IHSAN" . . DAGA NAKU AßßAN ßASMARH DAN MUTAN YOßE" An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels

Chapter 9 of 9