Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
5 / 9
akan halayen fatima" ka tuna fa tun muna yara ni da ita muke xuwa gidan nan" tun muna firamare" idan har akwai wadanda xasu fi kowa sanin halayenta" ai mu ne" mujahida ya sake yin shiru yana tunani" Umma ta tambayeshi" "yaya kodai wani abune ya paru a tsakaninku kai da ita kake boye mun?" . . Mujahid ya girgixa kansa" "babu abinda ya paru" kawai dai gani nayi ya dace muyi magana akan hakan! Umma ta dubeshi sosae ta ce-: "yaya mujahid" idan ma kana wani haufi ne a game da fatima ka daina" Domin kuwa nixan fada maka ko wacece fatima" idan har tana da wani hali" watakila a wajena ya kamata ka fara ji ba a wajen wani ba" Ka tsayar da hankalinka waje guda" fatima macece ta gari" na taba fada maka haka kwanakin baya" yanxu kuma gashi na sake fada maka kenan" fatima macece ta gari" wacce a matsayinka na dan uwana" xanyi farin ciki idan ta xama matarka" . . Mujahid yayi ajiyar xuciya" "Na gode Umma" dama abinda nake so kawai mu tattauna kenan" shikenan" tashi ki tafi" xanso cikin gidan anjuma" Umma ta tashi cikin mamakin dalilin da yasa yaya mujahid yayi mata wannan maganar" ta san cewar akwai wani abu da yasa yayi mata maganar" amma yadai boye mata ne kawai" amma akwai abinda yake faruwa tsakaninsu" A haka ta tashi ta shiga cikin gida tana xullumin kome yasa mujahid yake wasi-wasi a game da fatima" A ranar ita ma Umma wuni tayi cikin damuwa saboda fatima ta xamo kamar wani bangare na jikinta" kome ya same ta tare ya same su" kona dadi kona bakin ciki" . . FATIMA tayi mamakin yadda mujahid yayi kwana biyu bai kirata a waya ba" kuma baixo gidansu ba kamar yadda yayi mata alkawarin xaixo" don haka ita sai ta kira shi domin taji ko lafiya" Da ya dauki wayar ne sai taji kamar yana cikin damuwa" kamar yana fushi da ita" ta tambayeshi cike da farin ciki a muryarta" mujahid yace-: "Lafiya lau fatima" yasu Hajiya" "lafia lau" Data ji shiru baice komai ba sai ta tambayesh-; "Maji kwana biyu shiru ka kamce dani" shiyasa na gaya ya dace ni in tuna da kai" . . Tayi tsammanin xaiyi dariya amma sabanin sauran lokutan da sukayi tare" sai taji kawai yace da ita" "Ba haka bane fatima" ina cikin wani aiki ne da aka bani a ofis" shine ya tsare mani lokaci banxo ba" amma kada ki damu" fatima ta tambayeshi-: "yanxu har akwai wani aiki da xai sa ka kasa kirana koda na minti daya ne mujahid?" "i'am sorry idan komai ya kammalu xanxo fatima" kiyi hankuri" bata iya cewa komai ba ta rike wayar cikin mamakin yadda mujahid ya canxa mata haka kawai ba laifin komai" . . Ya kashe wayar basuyi bankwana ba" basu yi wani wasa ba wanda suka saba yi a waya idan suna cikin farin ciki" da yake lokacin fatima tana daki ne tare da xabba'u sai tayi tagumi" xabba'u wacce ke karatu a kwance akan gado ta juyo ta dubeta" "ke da waye" kuma naga kin gama waya kinyi tagumi?" fatima tace-: "Ni da mujahid ne" xabba'u ta tambayeta-: "Ba shine wannan masoyin naki da muka gaisa kwanaki ba?" "shine mana" xabba'u ta sake tambayarta" "to ya kuma naga kun gama waya kinyi tagumi lafiya?" . . Fatima tace-: "Ni ban sani ba" kawai dai naga ya canxa mun kamar yana fushi dani" xabba'u ta yatsine fuska tayi tsaki" "Ni kina bani mamaki fatima" wai ku sai yaushe xaku waye ne a duniya ku daina bada mata?" tayaya don namiji ya canxa maki a waya xaki wani tsaya kina yin tagumi?" menene don ya canxa maki?" Aini bana iya gane wai na miji yana farin ciki ko yana cikin damuwa (i'am indifferent about men) to jeki ya canxa maki" ke baki iya canxa masa ne a tafi a haka?" fatima ta girgixa kai cikin wasi-wasi" "kin san irin soyayyar dake tsakanina da mujahid ba irin soyayyar da kika magana akai ba ce" mujahid masoyina ne na musamman" shi kadai ne namijin da xaiyi fushi na damu sosae a xuciyata" . . Xabba'u ta tashi xaune cikin sauri" "ke bari in fada maki ki share shi ki rika ja masa aji" idan yaxo kice ya dawo (next week) baki da lokacin hira yanxu" sai ki ga yana ganin kimarki" Amma ke kenan gwanar xumudi akan saurayi" kullum baki da wani xance sai mujahid" mujahid daya xo kunui hira baki da wata magana sai (ßegging) dinsa ya dawo gobe ko jibi" ba dole ya rika yi maka wulakanci ba" . . Fatima tace-: "Ba haka bane xabba'u" mujahid ba haka yake ba" (He is very kind) bashi da wulakanci" nidai nasan akwai wani abu ne da ya bata masa rai" Xabba'u ta harareta" "Can maki! Sai kije kici gaba da fushi kina bata ranki akan namiji" yana can yana hidimarsa wajen wata budurwa ke ya barki anan kina yin tagumi saboda shi" . . Ta sake yin tsaki sannan ta dauki littafinta taci gaba da karantawa" taji kamar ta tashi ta hau fatima da duka saboda tsabar takaici" taga alamar fatima tayi nisa a son mujahid" xata basu wahala fiye da komai a wannan makircin nasu da suke kullawa domin su rabata da shi" fatima taci gaba da tagumi tana mamakin yadda mujahid ya canxa mata" laifin me tayi masa?" ta tambayi kansa ta jinjina da kujera ta daga kanta sama tana tunani" . . A dalilin mujahid ta hankura da cigaba da karatu" A dalilin mujahid ta fara son aura a rayuwarta" amma gashi suna tare yai ba xato ba tsammani ya fara xanxa mata" ya fara wulakantata" tun basu dade tare ba" . . Fatima taji hawaye ya xubo mata cikin sauri" wannan shine karo na farko a rayuwarta data fara yin kuka saboda wani d'a namiji" . . . Sai da aka kwana uku mujahid............¤TUN A DUNIYA" . . . РÁĞE 12 WĨŤH ÁßßÁŃ ßÁŚМÁŔH ĎÁŃ МÚŤÁŃ YŐßE" . . Yawan comment naku" shixae bani karpin gwiwar ci gaba da labarin" . . Sai da aka kwana uku mujahid baixo ba" kum bai kira ta ba" mujahid yana da wani hali wanda komae son da yake yiwa mace" indai xa.axo a fada masa wani abu mara kyau a game da ita" xai dade yana tunani a kanta kafin ya sake xuwa wajenta" Da yaga ya dauki lokaci mai tsawo yana tunani yana komarin gano abinda Asma'u take nufi" Amma baiyi nasara wajen gano komai ba" saiya yanke shawarar yaci gaba da wajen fatima" . . A ranar ya kira ta da yamma yace da ita" "fatima xanxo anjuma" tace dashi" "sai kaxo" ßa wanda ya sake magana" saboda akwai xargi a tsakaninsu" fatima tana xargin mujahid ya gaji da eta ne" ya fara yi mata wulakanci" shi kuma yana xargin tana yin wani abu wanda bai dace ba" shi kuma bai sani ba sai yanxu da suka fara soyayya" Da yake xabba'u taji lokacin da fatima keyin wayar" sa'ar da ta fito daga (kitchen) sai ta tambayeta" . . "yanxu haka keda mutumin naki ne?" fatima tace-: "shi ne" "yau kuma yaga dama xai xone?" naji kina cewa saiya xo" fatima ta gyada kai" "wai xaixo" ta tafi daki tabar xabba'u a kusa da dakin ajiya" a lokacin ne xabba'u ta tashi ta shiga dakin yara inda babu kowa duk suna dakin hajiya suna wasa" ta dauki wayarta ta kira Asma'u" Da daukarta tace da ita-: "Yau mujahid xaixo" ya gama fushin maganar da kika fada masa a banki" ya ya tuna da ita xai xo wajenta" . . Asma'u tace da xabba'u-: "Anjima xaiyi wani sabon fushin na gaske" suka yi dariya tare a waya" Asma:u dake can gidansu ta kira danladi suna gama waya da xabba'u tace dashi'-: "yau xaka yi mana aikin nan dalladi" in anjuma da misalain karpe takwas" Dalladi yace-: "xanxo ki hada ni da wani ya kaeni gidan" ya nuna mun inda suke tsayawa suyi hirar" Asma'u tace dashi-: "Bana son kowa yasan meke faruwa" kaxo gidanmu inyi maka kwatancen inda gidansu yake" xaka gane gidan ba nisa daga gidansu" Dalladi yace "sai na xo" . =====>+++++¤+++++<======= . Koda mujahid yaxo ya kira fatima a waya sai ta fito ta same shi a waje" gaisuwa kawai sukayi sai kowa yayi shiru" fatima ta rasa abinda xata ce dashi" sai shine a karshe yace da ita" "kinji ni shiru kwana biyu koh?" fatima ta gyada kai" "mhm" ta sake yin shiru" mujahid yace-: "Ai na fada maki wani aiki ne ya tsare ni ko?" tace a sanya ye" "Eh ka fada mani" . . Mujahid ya sake saurarawa yace"-: "yan kwanakin nan muna fama da aiki a ofis" sai mutum ya dawo a gajiye" wani lokaci bana sanin sanda barci yake kwashe ni da daddare" sai dai in bude ido inga safiya tayi" fatima tace-: "matsalar aiki kenan?" dama haka abin yake!" mujahid ya tambayeta "ya hajiya dasu xabba'u?" "tace-: "suna nan lafiya" "madallah" ya sake yin shiru kafin yace-: "Da ba wani abu da kikeyi da yamma ai da a lokacin xan rinka xuwa fatima" tace dashi-: "A,a daren dai yafi gaskiya" bani iya fitowa waje da yamma saidai idan cikin gida xaka rika shigowa" . . Mujahid yace-: "Ni kuma ai xanji kunyar shigowa cikin gidan" suka ci gaba da hira sama-sama ba yadda suka saba yi ba" tun kafin mujahid yaxo dama tuntuni dalladi yaxo" Dalladi yaxo kusa da kofar gidan ya xauna" dalladi mutum ne kato wanda xai kai shekaru ashirin da shida" baya rabuwa da tabarau a fuskarsa" badon komae ba sai don ya dinga sakaya jajayen idanunsa wadanda shi kansa yasan indai yana barin su a bude baxai rika yin kasuwa wajen 'yan mata ba" kuma idan ma har yayi kasuwa yasan to duk wacce babanta yaganshi" toda wahala yabar ta ta sake tsayawa dashi" . . A da can dan acaba ne" sanya yake da ragowar hankali" amma yanxu ya sake sana.o'i da dama" sana.a ta farko da yafi yi ita ce kamasho" a wata karamar tashar mota dake titin gidansu take" kullum sai an raba shi fada da direbobin mota sau kusan goma saboda kudin sallama" sana.arsa kuma ta biyu wacce yafi yinta in gari yayi xafi itace yakan dauki gurasa ya xagaya kasuwa inda baki suka fi shigowa" . . Danladi" yana son atine kawar Asma'u da gaske bada wasa ba" yana xuwa har gidansu atine" amma bata fitowa sai dai ya gahi da tsayuwa ya kara gaba" Ansha fada masa cewa Asma'u itace kanwa uwar gami" indai yayi kamun kapa a gurinta xata iya karkato da ra'ayin atine" ta rika saurarenshi" saboda haka danladi ya nemi lambar wayar Asma'u ya rinka kiranta yana yi mata magiya ta taimaka tasa masa hannu" bata taba yi masa alkawarin xata taimake shi ba a wurin atine sai da wannan aiki wanda ta sashi ya taso yanxu" . . Tun kwanaki da ta kirashi yaxo gidansu" ta fada masa cewar indai yana son ta allashi Atine ta soshi" sai yayi mata wannan aikin" wanda dama tun a ranar ta gama yi masa bayani" kuma tun a ranar yayi alkawarin xaiyi mata wannan aikin" shiyasa yau da Asma'u ta kira shi yaxo tace dashi saurayin fatima xaixo" bai tsaya bata lokaci ba" tana kwatanta masa gidan su fatima yaxo ya tambayi wasu yara suka ce masa nan ne gidan" ya samu wuri ya xauna yana jiran saurayin nata da akace xaixo ya kirata suyi xance-: . "Ya dade yana xaman jira" saida karpe takwas saura minti goma tayi sannan yaga wani yaxo a mota ya tsaya a kopar gidansu fatima" Da danladi yaga saurayin ya fito ya kira fatima a waya sai ya tabbatar shine saurayin nata da yake xaman jira" Yana kallon fatima ta fito suka fara hira dashi a kusa da bayan motarsa a jikin gidan" da ya ga sunyi kamar minti biyar sai ya tashi tsam ya je inda suke" ba wata fargaba ya same su" . . Ya tsaya a gaban fatima ya nunata da yatsa yace da ita cikin pushi" "ke mara mutunci wajenki naxo" haka mukayi dake?" kin san baxaki xo ba" meyasa kika amsar min kudina?" ni xaki bari a daki ina xaman jiranki fatima?" fatima ta dubi katon a rude" ta fara kokarin bude baki tayi magana tace-: "wa kake son gani malam?" dawa kake?" Danladi yace da ita-: "Oh! Kina nufin baki ma sanni ba" saboda kina tare da wannan bakon naki koh?" nine xaki ce wa nake son gani fatima?" . . Mujahid da yake kallon abinda yake faruwa yaji gabansa ya fadi" tsoro da raxana suka sa ya kasa cewa komae! Bai taba tsammanin da gaske fatima tana mu.amala da irin wadannan 'yan iskan samarin ba" fatima ta dora hannu aka cikin rudani" ta daga murya tace wa Danladi-: "A ina kasan ni?" wacece ka ba kudi?" a ina ka taba ganina?" wanene kai ma tukunna...." Danladi ya harareta" "Ok, xaki ce wanene ni yanxu" saboda wani yaxo xaki cuceshi kamar yadda kika cuceni koh?" to bari kiji in fada maki" koki bani dubu biyu na dana baki" ko kuma inyi maki dukan tsiya anan" in bugi kudina" tunda ba kudin banxa bane" kinji na fada maki" . . Fatima ta fashe da kuka" ta rasa me xatace tasan wannan katon sharri kawai yaxo yayi mata" mujahid yaji kamar ya nutse kasa saboda tsananin kunya da takaici" da kyar ya samu ya iya bude baki ya tambayi katon-: "malam (in fact) meya hadaka da ita?" kuma kudin me xata biya ka?" Danladi ya juyo bangaren mujahid yace dashi" "ka gane ko Alhaji" wannan yarinyar munafuka ce" na dade ina tare da ita" ßabina ce" duk lokacin da taxo dakina ina biyanta kudinta" kawai a wannan satin sai tace wai baxata xo ba sai na bata kudi a hannu" duk irin abubuwan da nake yi mata ta mance" shekaranjiya na canke mata kudinta dubu biyu (cash down) dama abinda nake bata kenan idan taxo kowanne lokaci" shine mukayi xataxo a ranar" tace inyi hankuri sai jiya xata xo" taki xiwa" tace in bari yau xataxo da yamma" sai wasa take mani da hankali" taki xuwa" shine naxo ta biyani kudina tunda abun nata rainin hankali ne" ina fada" bebis dinda nake casu dasu" ba ita kadai bace....." . . Da mujahid yaga katon xai fara tara musu mutane sai yace dashi-: "yanxu ni idan na baka dubu biyun" sai me kuma?" Danladi ya kawar da kai gepe a fusace" "kawai shinkenan" sai in ware kawai Alhaji" mujahid yasa hannu a cikin aljihun ya ciro kudi ya kirga dubu biyu ya mika wa danladi" ya amsa a fusace" ya dubi faima dake rusa kuka" ta dora hannu a kanta" yace da ita-: "xaki xo har dakina ki sameni" xamu hadu" banxa karamar mara kunya" nine baki sanni ba ko,?" xamu hadu" . . Ya cusa kudin a cikinaljihin kodadden wandonsa (jeans) ya tafi yana budawa" mujahid wanda tuni ya kusa fita daga hayyacinsa" ya dubi fatima yace da ita" "Dama an fada mani" asirinki ne ya tonu" kin bani kunya fatima" kuma kin cuci rayuwarki" ban taba tsammanin xan same ki a cikin irin wannan rayuwar ba" ina so ki bude kunnenki da kyau kiji" abinda xan fada maki" Daga yau bani ba ke" kuma na rabaki da kanwata Umma" bake ba ita har abada" . . Fatima tace dashi cikin kuka-: "mujahid" wallahi sharri yake yi mani" tunda nake ban taba ganin wannan mutumin ba" mujahid ya daga mata hannu" "kada ki dauke ni karamin yaro fatima" babu yadda xa.ayi wani yaxo yayi maki haka ba tare da yasan ki ba" ke kikaji kunya" kuma ke kika cuci kanki" kika wulakanta rayuwarki" ke kika xubar da mutuncinki" yayi sauri ya bude motarsa ya shiga" ya tayar ya tuka a fusace yayi tafiyarsa" fatima ta ruga cikin gida a guje tana kuka" da xuwanta ta fada dakin mahaifiyarta tana kuka" . . Hajiya dake cikin uwar daki ta fito a tsorace" "mene ne.... Ke da wane ne?" fatima tace da ita" "mujahid yace bani bashi" wai kada ya sake ganina tare da Umma" daga kawai muna hira wani wanda ban sanshi ba yaxo yayi mun sharri" yace waini budurwarsa ce" mujahid ya amince ba tare da yayi bincike ba" . . Hajiya ßinta tace da ita"-: "to sai me don yake bake ba shi?" kuma sai me don yace bake ba umma?" An dada masa neman kai akeyi da ke!" in banda muna la.akari da mutuncin da muke yi da iyayensa" shi har ya isa yaxo nan gidan yace yana sonki?" wanene shi?" kuma me yake dashi?" ki share hawayenki" ki daina kuka" in baso kike raena ya baci ba" fatima ta share hawayenta" ta saurara da kukan ta dake yi" . . Hajiya ßinta tace-: "Ai yanxu babanki xai dawo" yana hanya xaixo muyi maganar" kamar yadda yace bamu ba su" to mun yarda a tafi a hakan" kuma idan na sake ganin wani a cikinsu" ko shi ko kanwarsa wani yasa kafa yaxo gidannan" saina ci mutuncinsu" tunda basu san...............¤TUN A DUNIYA¤ . . . ραgє 13 ωιтн Aßßαη ßαѕмαян Dαη мυтαη уσßє ωнтѕαρρ ριη +2348082035050 . . "Ai yanxu babanki xai dawo" yana hanya xaixo muyi magana" kamar yadda yace bamu basu" to mun yarda a tafi a hakan" kuma idan na sake ganin wani a cikinsu" koshi ko kanwarsa wani ya sa kapa yaxo gidan nan" sai naci mutuncinsu" tunda basu san abun arxiki ba" Xabba'u wacce take rakube a dakinta tana sauraron abinda yake faruwa" tayi dariya sannan ta dauko wayarta ta kira Asma'u tace da ita" "Al'amari yayi daidai" sun bata baram-baram" Asma'u tace-: "Da sauran aiki fa" gobe xan koma banki in same shi" akwai magana " idan na dawo kixo gida ki same ni" mujahid ya kusa xama naki kawata" A daren xabba'u ta kwana batayi bacci ba saboda parin ciki" kamar yadda fatima ta kwana ita ma batayi bacci ba" saboda tsananin bakin ciki" . =====>++++¤+++++<======= . MUJAHID yana komawa gida yayi fakin din motrsa a inda yake ajiye ta a waye" ya fito cikin tsananin sauri kamar xai tashi sama" ya shiga cikin gidansu" tun kafin yakai ciki ya fara kwadawa Umma kira" "Umma! Umma!!" Umma ta fito daga dakinta" sanye da kayan shan iska" tun kafin ta tambayi mujahid me yake faruwa yace da ita" "Daga yau bake ba fatima" kina jina ko?" ßake babu fatima har abada" kuma idan na sake jin ko labari ne kuna kawance da fatima" saina ci mutuncinki anan gidan" sai nayi maki mahaukacin duka" . . Umma ta bude baki a tsorace tana kallon yayanta mujahid" a lokacin ne mama rakiya ta fito daga cikin dakinta" "me yake faruwa ne! Naji kana kwaratsi" laifi tayi maka ko?" mujahid yace da mama Rakiya" "Ina gargadin tane mama" daga yau ba ita babu fatima" na raba su" wannan yarinyar munafuka ce mama" bata da kyawawan halaye" na gani da ido na" na rabu da ita" mun yanke soyayyar daga yau" kuma na rabata da Umma" kada na sake ganinsu tare" mama Rakiya ta rike baki cikin mamaki" "Amma kuwa wannan abin al"ajabi ne" yanxu dama haka fatima take?" ka tabbatar abinda ka gani gaskiya ne?" . . Ya ce-: "mama kinsan baxan taba xuwa na fadi irin wannan maganar a matsayin karya ba" Abinda ya faru ne a gabana" kuma mama kada kiyi fatan jin ko menene" kawai dai mun yake duk wata alaka da ita daga yau" Umma ta fara kuka" tace da mujahid" "yaya baxan karyata ka ba" amma ina so ka sake yin bincike a bisa abinda ka gani" ni nasan fatima" koma menene ka gani" ka sake bincike kafin ka yanke wannan hukuncin" mujahid ya taso wa Umma kamar xai haure ta da kafa" . . "zan bata maki rai" idan kika sake yi mun magana" ko kin fini hankali ne" baxan sake yin binciken ba" kuma in kara ganinku tare ke da ita a anan gidan" xaki ga abinda xanyi maki"" mujahid ya juya a fusace ya fice yabar gidan" Umma taci gaba da kuka" domin kuwa duk duniya bata da wata aminiya sama da fatima" yanxu idan aka rabata da fatima" ina xata sa ranta a duniya?" ta tashi ta koma dakinta" ita ma a daren ko rintsawa bata yi ba" kwana tayi tana kuka" tana addu,ar Allah ya baiyanar da gaskiyar wannan al"amari" kuma Allah ya tona asirin munafukin da yake so yayi wa fatima sharri" ya bata mata suna" . ======>+++++¤+++++<====== . Washegari ne Asma'u taje banki ta samu mujahid tace dashi ta kawo wasu kudi ne xata yi (saving) taga mujahid ya rame" kamar wanda yayi rashin lafiya" a cikin dan kankanin lokaci ya xurma" kafin suyi wata magana ne sai mujahid ya ce da ita" "kinga dai abinda kika fada mun a game da fatima ya tabbata" ya faru a gabana jiya" nima na gani da idona" Asma'u ta dafe kirji a tsorace" "kai mujahid" kaima sunxo sun sameta a gabanka?" . . Mujahid yace-: "Abun ya daure mun kai sosae" ya kuma bani mamaki" lokacin da kika fara kyankyasa mun wannan maganar banyi xaton haka xai kasance ba" gashi nima na gani da idona" Asma'u tace dashi-: "mujahid ai ba tun yanxu fatima take yin irin wannan yawon bin samarin ba" duk wani wajen fati ko wani kulob dake garin nan tasan su" kuma tana xuwa" kawai dai an sakaya maka ne" ba.a fada maka ba" mujahid ya tambaye ta-: "to amma kina jin babansu yasan tana yin irin wannan halayen?" . . Asma'u tace-: "Xai sani mana" (sometimes) ai bata kwana a gida" kuma ya sani" tunda xabba'u tana fada musu abinda fatima takeyi domin su dauki mataki" amma sunyi ko-in-kula da al'amarinta" mujahid yace-; "to nidai yanxu saidai inyi mata gudumowa da addu'a Allah yasa ta gane ta shiryu" ta dawo kan hanya" "Amin" inji Asma'u wacce daga baya tace dashi" "yanxu yaya kake ganin alakarka da gidansu xabba'u xata kasance?" kuna xaune lafiya da su" kuma iyayenku suna mutunci (for long) ga kuma wannan matsala taxo ta gitta" ni ina ganin bai kamata ka yanke xumunci kwata-kwata dasu ba" . . Mujahid ya tambaye ta" "to ya xanyi Asma'u?" fatima ce ta jawo koma me ya faru a tsakaninmu dasu" ba laifina bane" Asma'u tace-: "Duk da haka" ya kamata kaje kayi tunani akan wannan maganar" bai kamata ka yanke xumuncin dake tsakanin gidanku da gidansu ba" yafi kyau ka nuna wa gidansu xabba'u cewa basu sukayi maka lafiya ba" fatima ce tayi maka" . . Kuma badasu ka bata ba" da fatima ka bata" . . Wannan shi xai sa ita kanta fatima tayi nadamar abinda ta aikata" idan taga cewar kaci gaba da mu.amala da 'yan gidansu ita kadai kayi (dropping) kuma wannan shixae nunawa iyayenta kai dan halak ne" kasan mutuncinsu" ba wai baka son hada xuriya dasu ba ne" kana son xuriyarsu" fatima ce kawai ta jawo matsala a tsakaninku" . . Mujahid yayi tunani-: "wannan haka yake Asma'u ni kaena nasan fushin da nayi yasa na yanke hukuncin yanke xumunci a tsakanin gidanmu da gidansu fatima" amma bai cancanta hakan ta faru a tsakaninmu da su ba" ni kaena banso hakan ba" abin yana damu na" Asma'u tace dashi-: "Ni da ace kaine" da abu daya xanyi kawai in magance wannan matsalar yadda xaku dawo kuyi (settling) a tsakaninku" da ace xainab kanwar fatima ta girma" da kawai sai kai (divert) xuwa wajenta" kaga kenan ka nuna kana son auratayya ta shiga tsakaninka da su" kuma suma xasuji dadi" xasu fahimci lallai laifin fatima ne! Ita ce ta jawo ka gujeta" amma gashi saboda kana son xuriyarsu ka dawo kana son kanwarta" to matsalar xaenab tayi kankanta da yawa gaskiya" . . Mujahid yace-: "Gaskiya ne Asma'u kinyi tunani mai xurfi anan" kuma nima xanje inyi tunani akan haka" tace dashi-: "kayi tunani idan ka koma gida ka huta mujahid" wannan hanyar itace kawai mafita" a wannan matsalar data faru yanxu" mujahid yayi mata godiya sosae yace-: "xanje xanyi shawara" xan duba inga abinda ya dace inyi akan haka" . . Suka rabu da Asma'u ta tafi ta barshi" A ranar ne da ya koma gida sai ya kwanta ya fara tunanin shawarar da Sma'u ta bashi" bai kamata xumunci ya yanke a tsakaninsu da gidansu fatima ba" shi kuma baxai iya komawa ya sasanta da fatima ba" saboda idan har akwai macen da ya tsana fiye da kowacce a duniya" bata wuce wacce take bin maxa ba" su kuma iyayen fatima baxasu taba yape masa ba" in har ya xame sanadin yanke xumunci da mu.amalarsu da kuma auratayyar da suke so su hada a tsakaninsu" . . Menene mafita?" mujahid ya tuno shawarar da Asma'u ta bashi inda take cewa" da ace xaenab ta girma da kawae wajenta xai koma" tunda dai fatima ta bata rayuwarta" to amma tunda xainab karama ce" wajen wa xai koma a (family) dinsu?" cikin sauri tunanin xabba'u ya fado masa a rai" Xabba'u...! Ita ma 'yar gidan ce" tunda dai kanwar mahaifiyar fatima ce" idan ya koma wa xabba'u babu shakka xai fita daga xargin kaxafi yayi wa fatima don baya sonta" xai nunawa mutane yana son hada xuriya da gidansu fatima" haka ne! . . Wannan shawara da Asma'u ta bashi" shawara ce mai kyau" kuma xaiyi ampani da ita" xabba'u xai komawa" ita ma tana da mutunci kuma ya fahimci tana da kamun kai" xabba'u ita tafi dacewa dashi tun farko" mujahid yaji hankalinsa ya kwanta a karo na farko tun lokacin da matsala ta shiga tsakaninsu da fatima" ya dauki waya ya kira Asma'u" lokacin da ta dauka ne ya fara sanar da ita cewa" "Asma'u akan shawarar da kika bani daxu ne nake so muyi wata magana" . . Tace dashi" "Ina jinka mujahid-: yaci gaba da cewa-: "Nayi dogon tunani kuma na hango fa'idar abun da kika fada" gaskiya idan na yanke xumuncin dake tsakaninmu da gidansu fatima" ban kyauta ba" kuma ni gaskiya yanxu bana jin xan iya sake komawa ince ina son fatima" na tsane ta fiye da yadda xan fada maki" Asma'u tace-: "fatima ba mace bace' ta bata kanta" mujahid yace-: "yauwa Asma'u to shine dana ga haka nace mexai hana baxan komawa kawarki xabba'u ba?" kinga yin hakan shixai sa mu dawo da xumuncin dake tsakaninmu" kada mu bata (forever)" . . Asma'u tace-: "kayi tunani mai kyau anan mujahid" to amma matsalar daya ce" bana xaton Asma'u xata amince saboda ita bata yin soyayya" karatu kawai take so" bata kula kowa" amma idan ka bani dama xan tuntubeta inji menene ra'ayinta akan hakan" mujahid yace-: "yauwa Asma'u ki taimaka ki sameta don Allah" kuyi maganar ki nuna mata muhimmancin yin hakan" da kuma dalilin da yasa na yanke wannan shawarar" . . Asma'u tace- "xan taimake ka mujahid" ko me kenan ka kirani gobe kaji yadda mukayi" yayi mata godiya sukayi sallam" abinda yake faruwa shine" A lokacin da suke wannan maganar xabba'u tana tare da Asma'u a gidansu" (hands free) ma tasa a wayarta" xabba'u tana xaune tana jin abinda mujahid yake fada a wayar" farin ciki kamar xai kashe ta" Da suka gama wayar ne sukayi sallama" sai Asma'u ta kashe wayar" ta juyo cikin farin alfahari ta dubi xabba'u wace ta kosa su gama maganar" Asma'u tace da ita-: "kinji sarauniyar mata" mujahid yace a taimake shi a roke ki" wai yana sonki!" . . Xabba'u ta cakumi Asma'u suka fara dariyar murna da farin ciki" saboda sunyi nasara akan fatima" sunyi mata MAKIRCI sun kwace mata mujahid masoyinta" sai dai kuma basu san abinda xai faru ba nan gaba" . ======>++++¤+++++<======== . An kai kwana uku mujahid yana kiran Asma'u yana tambayarta ya ake ciki" ita kuma tana cewa yadai kara hankuri" tana nan tana iya kokarinta akan hakan" . . A rana ta hudu ne ta kirashi da kanta tace dashi......................... . . Loading page 14¤TUN A DUNIYA¤ . . . ραgє 14 ωιтн Aßßαη ßαѕмαян Dαη мυтαη уσßє ωнтѕαρρ ριη +2348082035050 . . A rana ta hudu ne ta kirashi tace dashi-: "yau dai na samu na shawo maka kan mutuniyar" ta amince" mujahid yace da ita cikin murna" "na gode Asma'u yanxu tana ina xabba'un Asma'u ta ce" "mun tsara xakaxo gidanmu ne ka sameta in an jima" idan kaxo sai kuyi hira gaka gata (face to face) ba wata matsala kaxo gidanmu" mujahid ya tambaye ta adreshin gidansu" ta

Chapter 5 of 9