Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
1 / 9
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels TUN A DUNIYA" . . . РÁĞE 01 WĨŤH ÁßßÁŃ ßÁŚМÁŔH ĎÁŃ МÚŤÁŃ YŐßE . . =====><======= : DA misalin karfe hudu da rabi na yamma fatima ta karasa kofar gidansu kawarta Ummulkhaeri dake cikin gwammaja" bayan ta sauka daga motar da ta hawo daga kurna babban layi" inda anan gidansu yake" Ta samu mahaifin Ummulkhaeri a xaune yana karatun wani littafin addini akan darduma" tayi masa sallama da taxo shiga gidan" sannan ta durkusa har kasa domin ta gaeshe shi" "sannu ßaßa" mahaifin Ummulkhaei wato malam Aßdullahi" ya dago kansa" da yaga fatima ce sai ya saki fuskar shi" ya amsa sallamarta" "A fatima ce?" ta ce. "nice ßaßa" ina wuni?" ya amsa mata da cewa" "lafiya lau" yasu Alhaji duk suna lapia?" fatima tace "suna nan kalau" yace da eta" "to madallah" . . Fatima ta tashi ta shiga cikin gidan a yayin da malam kuma yci gaba da karatunsa" Da shigarta gidan tayi sallama" mama Raliya mahaifiyar Ummulkharti ta amsa sallamar daga cikin dakinta inda take xaune akan kujerar keken dinkin dake gabanta" tana kokarin shigar da xare a cikin allurar keken" Da farko mama Raliya bata dauki muryar ba sai da ta sa hannu ta yaye labulen dakin sannan ta ga ashe Fatima ce" tayi dariya cikin fari ciki da ganin babbar kawar 'yarta a duniya wacce suka saba da ita shekara da shekaru" . . Fatima lale marhabin" tace da ita" bata daina murmushi ba" ta mayar da hankalinta a kanta" tana jiran karasowarta cikin dakin" Fatima ta cire takalminta ta shiga cikin dakin mama Raliya hade da sallama cikin ladabi" mama Raliya ta amsa tana mai tattara hankalinta kanta" "sannu da xuwa" Fatima tace" "yauwa" sannan ta durkusa har kasa" "Ina wuni mama" "lafiya lau" mama Raliya ta tambayeta" "Ince dai su Hajiya suna nan kalau" "suna nan lafiya " tace tana gaisheku" mama Raliya tace" "Ina masawa" sannan tace da fatima wacce ta jawo karamar kujera dake a kusa da ita ta xauna" . . "Oh fatima shi kenan kuma daga kun gama makaranta sai ya yada juna" bake ba" ba umma ba" jiya nake tambayarta kina nan kuwa" tunda kuka gama jarabawa ban sake saki a idona ba" Fatima ta sunkuyar da kanta tana murmushi" "mama bana nan ne tunda mukayi (candy) naje hutu can garinsu hajiya dake kusa da dutse jihar jigawa" shekaranjiya na dawo" mama Rakiya tace" "Allah sarki" to ya kika baro 'yan uwan naku?" "Na baro su lafiya" mama Raliya tace da fatima" "yanxun nan ta shiga wanda" ki jira ta yanxun nan zaki ganta ta fito" ai taji maganarki" . . Fatima ta amsa da "to mama" taci gaba da xama tare da mahaifiyar kawarta suna hira kafin Ummulkhaeri ta fito daga wanka" Fatima da Ummulkhaeri kawayen juna ne na amana" tun daga makarantar firamare har xuwa yanxu da suka kammala karatunsu na sakandire" suna xaman jiran fitowar sakamakon jarabawarsu" . . Duk da ba unguwa daya suke ba" sun fara karatu tare a kurna a dalilin xaman da Ummulkhaeri tayi a wajen kanin mahaifinta wanda ya rike ta har xuwa lokacin da ta gama firamare" sannan ya dawo da ita gidansu wajen mahaifinta dake Gwammaja" Ganin yaddda suka shaku sosae kuma suke so su rika yin makaranta daya" Da mahaifin Ummulkhari yaji an saka fatima a wata sakandire (private) je-ka ka-dawo" sai shima ya nema wa Ummulkhaeri makarantar" domin tahi dadin tsayawa tayi karatu" idan tana tare da kawarta fatima" . . Haka suka kasance tare har suka kawo yanxu" idan aka basu (assignment) a makaranta" sai su hadu a gida suyi tare" ko fatima ta biyo Ummulkhaeri hida" ko ita Ummulkhaeri din tabi fatima can gidansu" Wannan kawance dake tsakaninsu yasa iyayensu suke jin dadi" musamman iyayen Ummulkhaeri sun dauki fatima kamar 'yar su da suka haifa ta cikinsu" Idan tayi kwana biyu bata xo gidan ba" sai su tambayi Umma ko lafiya fatima ta dauke kafarta daga gidan" . . Fatima yarinya ce mai ladabi da biyayya da kuma kunya" shekarun su daya da Ummulkhaeri" wato shekaru sha-tara" amma fatima tafi ta girman jiki da kuma tsawo" sannan kuma ita fara ce" a yayin da umma ta kasance wankan tarwada" Fatima tana xaune a gaban mama Rakiya suna hira Ummulkhaeri ta fito daga bayi cikin sauri daure da xani iya kirjinta" ruwan da bai gama tsanewa ba yana digowa daga cikin kitsonta" tun kafin ta karaso ta fara murmushi data hango fatima" "yar halak kinki ambato" ashe rai kanga rai?" Ummulkhaeri ta shigo dakin mahaifiyarta tana dariya" fatima ta harare ta sannan ta ce" "Ai ni ba wajen ki naxo ba" naxo ne in gaishe da su mama in koma" mama Raliya tayi dariya" ta saba jin irin wadannan korafin da wasan idan fatima da Ummulkhaeri suka hadu" . . "Haba aminiyata" laifin me nayi maki kuma yau ina murna da ganinki" kamar ranar sallah" amma xaki bada ni" fatima tace" "to amma yanxu saboda Allah kin kyauta kenan" Ace wai tun daga ranar da muka yi (final paper) din mu" baki sake xuwa gidanmu ba ko sau daya" Ummulkhaeri ta lallasheta" "kiyi hankuri aminiyar" naji ance baki nan ne" tunda mukayi (candy) kina jigawa haba! Kema kin san da ace nasan kina nan ai dole ne in kawo maki xiyara" . . FATIMA ta rage fushin da ke a fuskarta ta ce-: Duk da haka Umma" ai na dade a gida kafin in tafi dutse" naso ace mun hadu kafin in tafi amma kika ki xuwa" akwai maganar da nake so muyi dake mai muhimmanci" Umma ta dafa kawarta ta lallasheta" "to aminiyata naji na dauki laifina" kiyi mani afuwa ba xan kara ba" A lokacin ne mama Raliya tace da su-: "kun ga dai yanxu aiki xanyi" ina so ne in karashe dinkin wasu kaya guda biyu" ku tashi ku tafi dakinku" idan kuka fara surutunku sai kusa kan mutum yayi ciwo" . . Fatima da Umma sukayi dariya" suka fita daga dakin" Umma ta rike hannun kawarta suka nufi dakinta dake a karshen dakunan gidan" Da xuwansu bayan sun shiga sun xauna su duka a bakin gado" sai fatima tace-: "Gaskiya xaman gida ya para amsarki Umma" kinga kuwa yadda kikayi wani haske da kiba" wallahi kin canxa kamar ba ke ba" Umma tayi dariya" "Lallai fatima wato abin ma har da kodawa?" yaushe muka gama karatun da xaki ce haka?" duka-duka bamu wuce kwana arba"in da yin (send off) din mu ba" Tana fadin haka sai ta jawo kwandon kayan shafawarta ta dora shi akan gadon a gepenta" ta dauki man shapawarta (skin light) ta bude ta matso shi a tafin hannunta" lokacin da take mutsike da tafin hannunta ne ta fara shapawa a hannunta da wuyanta xuwa fuskarta" sai fatima take tambayar ta-: "Yaya maganar ci gaba da karatu Ummu?" . . Wannan maganar da nake fada maki xamu yi" nayi wa Hajiya maganar Inaso a siyo min (form) din (school of health) amma banji tace komai ba har yanxu" Na fahimci bata cika son inci gaba da karatu ba" kamar aure take so in yi" Umma ta ke dhapa mai a kafafuwanta tace da fatima" to idan hakan suka fi so ba shinkenan ba" ni dai dama baba ya fada min tuntuni baxan ci gaba ba" don yana maganar indai yaga mujahid ya samu aure a wannan shekarar" to tare yake so ayi bikin da nasa" asa rana daya ya huta" . . Fatima tayi ajiyar xuciya tace da kawarta Umma'-: "Gaskiya nidai da xa.a bi xabina nafi so inci gaba da karatu Umma" saboda kin gani fa ko wani kwakkwaran saurayi bani dashi a halin yanxu" saboda nasan xanci gaba da karatu" ba wanda nake tsayawa saurara!!" Umma ta dauko madubi ta fara gyara gashin kanta a lokaci guda tace da fatima-; Duk wannan ai mai sauki ne" in dai aure xakiyi baxaki ci gaba da karatun ba" samun miji mai sauki ne tunda ma akwai wadanda suke son ki" kece baki kula su saboda kina sa rai xakici gaba da karatu" Amma idan har kowa yayi aure xa.a yi miki" nan da nan xaki ga samari suna xuwa wujenki" . . Fatima ta dan bata ranta tace-: Duk ba wani ya jawo mani wannan matsalar ba sai xaßßa"u" ita ce ke tara wa mutane samari kullum a waje" shiyasa Hajiya tace dani da ita" duk hadamu xa.ayi bana a aurar damu" ta gaji da ganinmu a gabanta" Umma ta dan yi murmushi" tuni ta gama shapa man" da ma ba wani waje xata je ba" ta dan yi wanka ne kwao din tahi dadin jikinta" Da fatima bata xo ba" da karatu take so tayi" dama daxun nan da rana ta aiki kaninta Abba yaje kasuwa ya siyo mata sababbin littatafan da suka fito guda uku" . . Umma ta tashi ta dauko karamar rigarta ta bacci ta saka" sannan ta sa (skirt jeans) dinta mai ruwan kasa" Fatima tana xaune tana jiranta" a lokacin ne ta tuno da irin xaman da takeyi da xaßßa"u a gida" Xaßßa"u kanwar mahaifiyar fatima ce" amma budurwa ce tsarar fatima" lokacin da inna uwale kakae su fatima taxo haihuwar xaßßa"u ne ta rasu a wajen haihuwa" tun xaßßa"u tana jaririya sai aka ba Hajiya binta rikonta" a lokacin ita kuma Hajiya ßinta tana goyon fatima" tsakaninsu ita da xaßßa"u wata biyar ne" Don haka sai Hajiya ßinta ta hada su baki dayansu ta shayar da su a lokaci daya" tunda dai babu inda xa.a kai xaßßa"u" Hajiya ßinta itace babba a wajen mahaifiyarsu data rasu" kuma daga sannan xuwa yanxu xaßßa"u tana wajenta" tare suka taso ita da fatima kamar tagwaye" : . Banbancinsu kawai shine ita fatima tadan fi ta tsayi kuma da yake xaßßa"u tayi rashin lafiya mai tsawo sa.ar da take yarinya" fatima ta wuce ta a karatu da aji daya" don haka ita xaßßa"u sai a shekara mai xuwa xata gama tata makarantar" wacce ita ma je-ka-ka-dawo ce" amma ba makarantar da su fatima sukayi ba" Idan ba an fadi ma mutum ba" ba wanda xai iya gane cewa xaßßa"u ba haifaffiyar gidan su fatima ce ba" wasu da yawa suna daukar xabba"u kanwar fatima ce" domin kuwa tun suna yara tare suka taso kuma Alhaji sunusi mahaifin fatima baya banbanta masu komai" tare yake yi masu" kamar su dukansu shiya haifesu" . . Fatima da xabba"u basu cika jituwa ba" kuma rashin jituwarsu yana da nasaba ne da abubuwa da yawa" Na farko-: halayensu ba iri daya ba ne" xabba"u ta cika kiriniya da rashin kunya" a yayin da fatima ta kasance mai kamun kai da kawaici" ko kawayensu ma ba daya bane" kowacce da irin kawayenta" ba su cika yawo tare ba" Indai ba Hajiya bace ta aike su tare suje su dawo" . . Wani lokacin" musamman lokacin da suke yara" sun sha suyi fada" kuma koda yaushe hakan ta faru a tsakaninsu" Hajiya vinta fatima take ba rashin...................TUN A DUNIYA" . . . РÁĞE 02 WĨŤH ÁßßÁŃ ßÁŚМÁŔH ĎÁŃ МÚŤÁŃ YŐßE" . . WANI LOKACIN" musamman lokacin da suke yara" sun sha suyi fada" kuma koda yaushe hakan ta faru a tsakaninsu" Hajiya ßinta fatima take ba rashin gaskiya" tana yin haka ne domin fatima ta rika girmama xabba'u kada ta raena ta don taga ba 'yar gidan ba ce" Duk da fatima ta girmi xabba'u" Hajiya binta ta hana ta ta rika kiran sunanta tsirara sai ta hada da (Aunty)" ko kuma Umma xabba'u" saboda kanwar mahaifiyarta ce uwa daya uba daya" . . Wannan shiya jawo rashin jituwa tsakanin 'yan matan biyu" xabba"u ta raina fatima saboda taga Hajiya binta ta bata dama sosae a gidan" Xabba"u takan sa fatima aiki" kuma bata isa tace baxata yi ba" saboda idan Hajiya taji sai ta bata mata rai" wadannan abubuwa suna damun fatima" saboda xabba'u tana takura mata a gidansu kuma tana jawo mata fada da xagi haka kawai saboda tana takamar ita kanwar mahaifiyarta ce" fatima bata san cewar tunani take yi ba saida Umma ta girgixa ta sannan ta dawo hayyacinta cikin sauri" "Fatima lafiya ina tayi maki magana amma naga kinyi shiru" wai tunanin me kikeyi haka?" Umma ta mayar da hankalinta sosae akan fatima wacce ta sake yin dogon ajiyar xuciya" "Ba komae Umma kawai ina tunanin yadda xanyi ne akan wannan maganar" . . Umma ta dafa ta cikin damuwa tace da ita"-: "kin san banaso inga kina bata ranki fatima" don Allah ki kwantar da hankalinki komai kikaga ya faru da mutum can haka Allah ya kaddara xai faru a kanki" Idan auren shiyapi alkhaeri" to kawai muyi addu.ar Allah ya xabar maki miji nagari" Idan kuma karatun ne to mu roki Allah yasa Hajiya ta dawo ta barki kici gaba" amma banaso inga kina irin wannan tunanin" kada wata matsalar ta sake ki" Fatima tayi wa Umma godiya" bayan sun kare hira" xuwa can kusa da faduwar rana sai tace xata koma gida" fatima ta tashi ta dauki hijabinta data cire ta ajiye" ta sake xura kanta ta sa" Umma ta ce" "Ai nagode sosae" kuma In Allah ya yarda nima xaki ganni nan da kwana uku" Fatima tace-: "In ma baxaki xo ba ai kinsan kwanan xancen" don kuwa kada kiyi tsammanin nan da shekara daya xaki sake gani na anan gidan" . . Umma wacce ita ta saka nata karamin hijabin" ta raka ta suka fito wahe" sun nufin dakin mama Raliya kenan xasu je fatima tayi mata sallama" sai ga mujahid yayan umma" ya fado gidan cike da farin ciki" Mujahid wankan tarwada ne mai manyan idanu wanda kamanninsa suka xo iri daya da kanwarsa Ummulkhaei" shekarunsa Ashirin da takwas" yayi digirinsa a shekarar da ta gabata kuma ya dara aikin bankin da ya samu wata uku da suka wuce" tun kafin tace dashi sannu da xuwa ya ciro sabon makulli ya daga shi saitin idanunta yace da ita cikin wasa da farin ciki-: "Albishirinki" tace-: "Goro fari fat! Mujahid yace da eta" "An bani sabuwar mota wacce xan rika xuwa aiki" Umma ta rike numpashinta" "wow! Da gaske yaya mujahid?" yace da ita" "tana nan a waje naxo da ita ma" Umma ta fara murna" "Congratulations....... Na taya ka murna yaya......" . . Tana cikin xumudin taya shi murnar ne sai fatima dake tsaye a gepe daya tana sauraren su ta gaeshe shi" "Ina wuni yaya?" ya ce "lafiya lau" Bai gane fatima ba har xuwa lokacin da ta taya shi murna ita ma" "muna murna yaya! Allah ya tsare" Allah ya kara budi" yace cikin farin ciki" "Nagode, Nagode" A lokacin mama Rakiya ta leko daga dakinta" "Hayaniyar me kuke yine haka" lafiya?" kafin mujahid yayi mahana sai umma tayi farat ta cewa mahaifiyar tasu" "banki ne suka ba yaya mujahid mota" . . Mama Rakiya tace" "A.'a'a. Abin arxiki" ba shakka" Allah yasa alheri" mujahid yace da Umma" "yanxu kamata yayi kuxo in dauke ku keda kawarki in kaiku inda kuke so" kuyi dani" fatima tayi dariya" umma ta tambayi mujahid" "yaya naji kana cewa kawata" wai kai baka gane ko wacece wannan ba?" mujahida ya dubi fatima sosae" yayi tunani amma ya kasa tunda inda ya santa" "ban gane ta ba" Umma wacece!" mama Raliya tayi farat tace" "Lah! Kai kuwa meya sameka"? Ko duk xumudin sabuwar motar ne yasa ka mance da fatima?" . . Mujahid ya buda baki cikin mamaki" "fatima?" ya dubeta" yanxu fatima ce dama ban gane ta ba?" wallahi naga tayi girma ne" in banda kun fadamin" ko a hanya naganta baxan gane ta ba" fatima taci gaba da murmushi" mujahid ya santa" tun tana karama take xuwa gidansu wajen Umma" to amma yakae shekara hudu bai ganya ba" tun da ya fara karatu a jami.ar tafawa balewa dake bauchi bai sake ganin fatima ba sai yau" . . Yayi mamaki da yaga ta xama hadaddiyar budurwa" tayi hankali" ta xama mace sosae" yace da ita" "fatima kiyi hankuri don Allah" ban gane ki ba ne" kinsan mun dade bamu gaisa ba" tace dashi cikin kunya" "ba komai yaya" "naga kamar tafiya xatayi" kuxo muje fatima" saimu kaiki gida nida umma a mota" Fatima tace" "kada mu wahalar da kai yaya mujahid" kabarshi kawai Nagode" . . Mama Rakiya tace "A.a kuje ya kaiki gida mana fatima" tunda ga mota kuma ai xaifi" "to mama mun gode" bari in tafi sai kuma na kwana biyu" . . MAMA RAKIYA tace-: "ke xa.ai wa godia fatima" in kinje kice da Hajiya ina gaisheta" "to mama" xataji" sai anjima" fatima tayi sallama da mama Rakiya" Ymma da mujahid suka raka ta xuwa waje inda xasu hau mota su kaita gida" . =======>++++++<======== : Suka shiga mota su uku" fatima ta xauba a gaba tare da mujahid" ita kuma umma ta xauna a baya inda tafi so" muhajid ya tayar da xukekkiyar motar sa (camry) ya tuka suka tafi" Umma dake xaune ita kadai a baya tace" "kai yaya muhajid motar taka akwai dadi gaskiya" mujahid yace da ita cikin wasa" "xaki fara yiwa mutane kauyancin naki ba" Umma tace cikin shagwaba" "kai yaya" ina 'yar birni gaba da baya" kace dani 'yar kauye" . . Yayi mata dariya" a lokacin ne ya fito daga layinsu ya hau titi yaba motar wuta suka ruga a guje kamar suna tafiyaa cikin iska" fatima ta ce-: "Nima dai don kada ace mani 'yar kauye dana fadi nawa santin" yaya mujahid wannan motar taka ko jirgin sama ai sai haka" mujahid ya dan juyo cikin dariya ya dubi fatima" "Ni kuwa kinga dai har na yanke shawarar a satin nan xan sayar da ita in canxa wata (camry 11) nake so suka bani wannan" "yaya mudai kabar mana wannan gaskiya tayi" bama son wata (carina 11) fatima ta juyo ta harare ta" "yau naji ikon Allah" motar ma sai wacce kike so xa.a saya?" ke kin cika shagwaba umma" Umma ta canxa hirar tasu da cewa-: "yaya tun da ka gina gida ka sayi mota" yaushe kuma xaka nemo mana (Aunty)?" mujahid yace da ita" ba tare da ya dauke kansa daga kallon titi ba" "ku taya ni addu.a In Allah ya yarda (very soon) xanyi maku abokiyar hira" kada ku damu" . . Umma ta tambaye shi" "to wacece yaya" kafin lokacin yayi ai yakamata mu santa tun yanxu" ko kuwa fatima?" fatima ta sunkuyar da kai cikin kunya tace" "baxa kaji bakina ba" "naji dadi da kika gwasaleta fatima" kin ganta nan bata da kunya" fatima tace-: "Don taga kana sakar masa fuska ne" yaya mujahid shiyasa take yi maka rashin kunya" Umma tace-: "yau xa.a yi ruwa da kankara" su kurma anyi baki" wai dama kina magana fatima?" fatima tace da ita-: "A,a sai ke aku sarkin surutu" kin raena ni Umma nice ma xaki cewa kurma?" kina nufin kin fini surutu ne?" . . Muhajid ya yanke maganar da cewa-: "yanxu yaushe (result) dinku xai fito?" fatima tace-: "zai kai nan da wata biyu ko umma?" Umma tace-: "Idan ma akayi sa.a kafin lokacin xai fito" amma dai baxai euce nan da wata biyun ba" yace da su-: "indai kun samu (result) mai kyau" ya kamata ku nemi makaranta a sa ku" a wannan shekarar kuci gaba da karatunku" fatima ta juya baya suka hada ido da umma sukayi murmushi" mujahid bai san cewa su yanxu xancen aure ne a gabansu ba" da yaji babu wacce tace wani abu sai ya juya ya dubi fatima" . . "ya naji baku ce komai ba" ko baku son kuci gaba da karatun ne?" fatima tace-: "xamu ci gaba mana yaya" Umma tayi dariya tace-: "ke dai ki fadi gaskiya fatima" mujahid yasa sigina ya rage wuta ya sauka daga kan titi" ya shiga cikin layinsu fatima" A lokacin ne yace-: "Ni fa ban gane ba kuna tayi mani yawo da hankali" me kuke nufi ne?" Umma tace dashi" "tsakanina da Allah yaya baxan boye maka ba" ni dai aure nake so?" "ya salamm..! Mujahid yace cikin kaduwa" Fatima tace-: "yaya mujahid umma bata da kunya" kaji abinda take fadi?" Umma tace da ita-: "to ke din fa?" ba auren xakiyi ba" kema"?" yaya ita ma auren xa.ayi mata" ba wani karatu da xataci gaba dayi" . . Fatima tace-: "haka muka yi dake?" mujahid yayi murmushi yace-: "Lallai yaran nan kun girma" wato ku ba xaku ci gaba da karatu ba" aure kawai suke sO" tab!" ya tambaye su" "to su wanene samarin naku?" badai nisa xakiyi ba ko?" Umma tace-: "Bayan kaki fada mana taka budurwar" mu kuma mu fadi maka samarinsu?" ka bari sai ranar da ka kaimu wajen budurwarka" sai kaga namu muma" mujahid yace-: "to Allah yasa alheri" Allah ya kaimu musha biki" A lokacin ne ya kawo kofar gidansu fatima" ya wuce gidan yayo kwana" sannan ya dawo ya tsaya domin ya sauke fatima" Umma tace-:" "sai kin ganni" a wannan satin xanxo" ki gaishe dasu Hajiya da xabba'u fatima tace "xasu ji" . . Sannan ta bude kofar motar ta fita" suka sake yin sallama da mujahid sannan ya tuka suka tafi" Umma ta daga hannu sama ta cikin motar" fatima ita ma ta daga mata" bata shiga gidan ba ta tsaya tana kallon su har sukayi nisa suka fita daga layin" sannan ta jiya ta shige cikin gidansu" a daidai lokacin ne aka kira salla a masallacin kofar gidansu" . ======>++++()++++<======= : HAJIYA ßINTA ta fito daga kicin da taji an kira sallah" a lokacin ne xabba"u ta tashi daga kan kujerar da take xaune a tsakar gida inda ta gama karanta (text) da aka turo mata a wayarta bada jimawa ba" tana murmushi" "Hajiya ßinta" tace" "Oh! Wai yarinyar nan daga kawai taje gidan su Ummulkhaeri shine har yanxu bata dawo ba" Xabba'u ta shige daki tana danna wayarta" tunda fatima tabar gidan da yamma Hajiya ßinta take dama da aiki a kicin" amma xabba'u bata shiga ta kama mata ba" . . Dama fatima ce take taimakonta da duk wani aikin gida" tun.....TUN A DUNIYA" . . . РÁĞE 03 WĨŤH ÁßßÁŃ ßÁŚМÁŔH ĎÁŃ МÚŤÁŃ YŐßE" . . Hajiya ßinta tace-: "Oh! Wai yarinyar nan daga kawai taje gidansu Ummulkhaeri shine har yanxu bata dawo ba" Xabba'u ta shige daki tana danna wayarta" tun da fatima tabar gidan da yamma Hajiya take fama da aeki a kicin" amma Xabba'u bata shiga ta kama mata ba" dama Fatima ce take taimakon ta da duk wani aikin gida" tun daga shara har xuwa wanke- wanke" ni dai fatima tana nan ita ce xatayi duka" amma banda xabba"u" sai dai taci ta kwanta abinta" . . A daidai lokacin da Hajiya ßinta" take wannan korafi ne sai fatima tayi sallama ta shigo gidan" mahaifiyarta tace-: "yanxu fatima ke kuwa daga kije ku gaisa da Ummulkhaeri awa daya ki dawo" shine kika je kika yi xamanki" ga aikin baja-baja a gidan nan?" fatima tace da mahaifiyarta cikin ladabi" "kiyi hankuri Hajiya" tun daxun nan na so tahowa" yanxu ma yaya mujahid ne ya kawo ni a motarsa" Hajiya ßinta ta saki fadan da take yiwa fatima" "mujahid din ya sayi mota ne?" fatima tace-: "Eh wai a banki aka bashi inda ya samu aiki" yau yaxo da motar gida" "Allah ya sanya alheri" fatima tace-: mama Rakiya tace in gaeshe ki sosae" "Ina amsawa . . Fatima ta nufi dakin kwanansu ita da xabba"u domin ta cire hijabinta tayi alwala" Hajiya ßinta tace-: "kiyi sallah sai kixo ki karashe aikin abincin nan" ki xuxxuba wa kowa nasa" dama na gaji ke nake ta jira tun daxun kixo ki amshe ni" kinyi xamanki" fatima tace-: "to mama" sannan ta shiga dakinsu" ta samu xabba"u tana (reply) na (messege) din da aka turo mata a wayarata" Xabba"u kyakkyawa ce ita ma" tana da farar fata kuma ta iya kwalliya da kissa da kuma goge wa da samari" tana da tsiwa da rashin hankuri da kuma alfahari da kanta" . . Fatima tayi sallama" ta sama a ciki" lokacin take cire hijabinta ne sai xabba"u ta dago kanta tace da ita-: "kekika dauka mun birona ko?" fatima ta tambaye ta" "wanne biro na daukar maki! Xabba"u ta ce:- "ßiron nawa har guda nawa ne?" wanda kika san ni da shi" "bani bace" ke dai ki sake dubawa da kyau" amma ni yau ban mayi rubutu ba ko sau daya" xabba'u ta taso mata da masifa" "kamar ya bake kika dauka ba?" ni dake ne fa a dakin nan fatima" biro xai dauki kansa ne ko kuwa?" wa xaixo ya dauka in ba ke ba?" fatima tace-: "to ni ban daukar maki biro ba" me xanyi da bironki?" Ni ban yi rubutun komae ba.." . . Xabba'u ta nuna mata yatsa" "to wallahi na baki nan da ayi sallah" idan baki fito mun da birona ba" ko me nayi maki ke kika saya" naga kina kawo mani raini a 'yan kwanakin nan" to xanyi maganinki idan ni tsarar yinki ce xan gani" A lokacin ne Hajiya binta ta leko cikin dakin da taji suna surutu" "menene kuma?" xaku fara ko?" xabba'u ta ce-: "Hajiya birona ta daukar mun" shine data dawo na tambaye ta xata taso min da masifa" Fatima ta juya ta dubi mahaifiyarta" "Hajiya bani da daukar mata biro ba" ni yau ko rubutu banyi ba" Hajiya binta tace da fatima cikin fushi" . . "to amma daba ke kikav dauki biron ba" kinfi karfin ki fada mata bake bace cikin mutunci?" sai kin taso ki fara daga mata murya kuna sa-in-sa ke da ita?" bana hanaki ki rika yi mata irin wannan rashin kunyar ba" ko abokiyar tsarar fadanki ce?" fatima tace-: "kiyi hankuri hajiya" Hajiya binta tace da

Chapter 1 of 9