Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
7 / 9
Alhaji sunusin yayi sa.a ma bashi yaxo nan ba" yau da naji dalilin da xai sa ya kama mun 'ya da duka" saboda yana takamar tana xaune a gidansa" kome tayi ba.a xuwa a fada mun?" . . Hajiya ßinta" ta fara xubar da hawaye" domin kuwa xabba'u ta jawo mata mahaifinta yana fushi da ita" tayi iya kokarinta ta bashi hankuri ya fahimce ta amma abun yaci tura" malam Abubakar ya dauki so ya dorawa xabba'u" baya ganin laifinta" Hajiya ßinta" ta tashi tana kuka taje dakin mama ßalarava wato amarya" ta sami xabba'u a xaune tana shan koko da karamin ludayi cikin kasaita kamar wata karamar yarinya" Hajiya binta tace da ita-: . . "Nazo inyi maki godiya bisa sakayyar da kikia yimun" na gode xabba'u" ßa gori xanyi maki ba" amma nayi maki abinda a wannan xamanin ba kowacce 'yar uwa xata yiwa 'yar uwa ba" ko 'yar da na haifa fatima banyi mata abinda nayi maki ba" ke kin sani" sai dai ki take sanin" saboda tsabar son rai da butulci" tun kina jaririya na shayar dake nonona" har kika rayu kika samu kanki a halin da kike yanxu" Amma yau an wayi gari wai nice xaki xo ki hada da baba ko xabba'u?" nice yau na xama abokiyar gabarki?" bayan ke kina sane kece baki da gaskiya" kece kika yiwa fatima sharri kika rabata da masoyinta" suna xamansu lafiya"Amma duk wannan bai isheki ba" shine kika kwaso kayanki kika dawo gida" kika cewa baba mun kore ki" . . Baki yimun adalci ba xabba'u kuma kin xalunce ni" bani na haifeki ba" ke kanwata ce" Amma na tabbata idan nayi maki baki wallahi sai ya kamaki da sauri" to baxan yi maki baki ko wata muguwar addu.a ba" xanyi maki fatan alheri" Allah yasa kuma ki gane kuskurenku" kuma indai akan mujahid ne kikayi wannan makircin" to fatima ta rabu da mujahid har abada" kije an bar maki shi" saboda a xauna lafiyaa" Allah ya baku sa.a" . . Hajiya binta ta koma gida cikin tsananin bakin ciki" da xuwanta xaxxabi ya bugeta ta kwanta a gado" tana rawar sanyi" fatima tayiwa babanta waya tana kuka" wanda ya tafi kasuwa" tace ya dawo gida hajiya bata da lafiya" jikinta yayi xapi" kafin Alhaji sunusi ya dawo sau biyu tana suma" da xuwansa suka dauketa a rude suka kaita cikin mota" suka garxaya da ita asibiti" Likita da ya aunata yace ciwon xuciyane yayi mata mummanan kamu" sai dai a dage da addu.a" amma komai xasu yi mata" rayuwarta na cikin tsaka mai wuya" . ======>+++++¤+++++<======= . Da Umma taji abinda yake faruwa da sukayi waya da fatima" bata tsaya jiran komae ba sai ta nufi asibitin murtala" inda aka kwantar da hajiya binta" ta samu fatima a waje tare da xainav sunyi jugum- jugum" likita yace su fito waje" ana duba marasa lafiya" . . Umma da fatima suka kama hannun juna suka.....¤TUN A DUNIYA¤ . . . ραgє 17 ωιтн Aßßαη ßαѕмαян Dαη мυтαη уσßє ωнтѕαρρ ριη +2348082035050 . . Umma da Fatima suka kama hannun juna suka kebe gepe guda" kusa da wasu shuke-shuke dake cikin asibitin" suka xauna kowacce tana xubar da hawaye domin kuwa sun dade basu ga juna ba" a sakamakon sabanin da ya shiga tsakanin fatima da mujaid" Fatima ta fadawa Umma yadda al'amarin ya faru" tun lokacin da wani kato yaxo ya same su suna hira ita da mujahid yayi mata sharri" yace wai ya bata kudi xaiyi lalata da ita" amma taki xuwa dakinsa" ta kuma fadawa Umma yadda mujahid ya kasa fahimtar sharri katon yayi mata" ya caba mata nasa maganganun ya shiga motarsa ya tafi cikin fushi" wanda wannan shine rabuwarta da mujahid ta karshe" . . Fatima tace da Umma-: "kin san ance mara gaskiya ko a ruwa gumi yake yi" ashe da yake ita bakar annamimiyar xabba'u tasan ita ta kulla abin" ita da wannan shedaniyar kawar tata Asma'u sai suka samu mujahid suka ce wai ya turo iyayensa suce sun xone a nema masa ixinin yanxu ita yake so" bani ba" kinji dalilin xuwan mama gidan nan" kinsan taxo sunyi magana da Hajiya" kuma a dalilin haka ne aka gane cewar xabba'u ce ta kulla mana wannan makircin domin ta rabamu ni da mujahid" Umma ta dafe kanta cikin jimami" tace-: "Haba!" ni dama nasan akwai wani abu a boye" amma nayi mamaki da mujahid ya kasa gane ita ce ta kulla wannan sharrin" meyasa mujahid yayi haka" har yasa mama cikin maganar" ta goyi bayansa ya nemi xabba'u?" . . Fatima tace-: "kada ki ga laifin mujahid Umma" ki rabu da makirci" ba wanda ya gagari irin wannan bala'in ya fado masa" kedai kawai kiyi addu.ar Allah ya cire mutum daga sharrin makiri akoda yaushe" Ni a yadda na fahimci al'amarin tun lokacin da ta kudiri aniyar xata rabani dashi" bata fito ta nuna tana sonshi ba" sai da ta tabbatar ta shirya makircin da xata rabamu" ta yadda shi mujahid baxae taba xargin tana da hannu a cikin sharrin da suka yimun ba" sai da ta tabbatar ta rabamu sannan taje tasan shige da ficen da tayi" ta koma suka fara soyayya" Umma ta share hawayenta tace-: "Amma kuwa duk inda ake neman makira' macuciya" wacca batasan abunda take yi ba" batasan abinda ya kamata ba a rayuwa" to idan aka samu xabba'u an gama" duk wannan halarcin da Hajiya take yi mata" amma ta rasa wanda xata yiwa sharri sai ke?" Fatima ta girgixa kai cikin takaici" "Bari in fada maki Umma" ni na tabbatar yadda Hajiya take son Xabba'u bata sona haka" Akwai abubuwa da yawa da xaki ga Hajiya tayi mata ita kadai" ba tare da tayi mun ba" kuma bana damuwa saboda nasan kanwarta ce" yau ga sakamakon da tayi mana" ta jepa mu cikin bala'i mu dukkanmu" . . Umma tace-: "Ba komai" idan ita ta rike makirci da xamba" mu kuma mu rike addu'a dare da rana" In Allah ya yarda sai munyi galaba akanta" bada dadewa ba" Allah saiya tona asirinta" kuma sai tayi nadama" Fatima tace-: "Ni yanxu rashin lafiyar Hajiya kawai yafi damuna" Ga jikinta yayi xapi kuma nsan a dalilin wannan bakin ckin abunda xabba'u tayi a gidan" shine ya haifawa Hajiya da wannan ciwon" Umma tayi ajiyar xuciya-: "ki dauki wannan abun a matsayin kaddara fatima" babu ta inda Allah baya jarrabar bawansa" Hajiya xata samu lafiya in Allah ya yarda" Idan naje gida xan samu mama" xan fada mata duk abinda ake ciki domin ta fadawa baba su shiga tsakanin mujahid da xabba'u saboda soyayyarsu ba alheri bace" kuma xabba'u ba mace tagari bace" anno bace a gida" Sun dade a xaune suna maganar akan wannan masifa data xo musu" bayan likita ya gama aiki ya fito" sai fatima ta jagoranci Umma suka je dakin da Hajiya take kwance" ta farka daga dogon baccin da tayi" amma da kyar take iya bude idanunta a sakamakon wahalar da ta sha" . . "sannun Hajiya, yaya jiki?" Umma tace da ita" bayan ta matsa jikin gadon tana kallonta" Hajiya binta ta bude baki da kyar! "Naji sauki" ta dubi Umma da fatima 'yarta" wadanda suma suka kura mata idanu suna jimamin halin da take ciki" ta sake kokartawa tace dasu': "Don Allah kada ku tayar da hankalinku a kaina" xan tashi In Allah ya yarda" kuma game da xabba'u kada kuce xaku dauki wani mataki akan abun da tayi mana" ku dauki komai ba komai ba" ku rabu da ita" bana son inji wani ya sake cewa komai akanta"" Umma tace da Hajiya" "Kada ki damu Hajiya" duk abinda kikace mana xamu bi umarninki" kuma baxamu ce mata komae ba" mun barta da Allah kome tayi" Hajiya binta tayi ajiyar xuciya-: "Allah yayi maku albarka" Na gode" Bacci ya kwashe ta bada dadewa ba" fatima ta raka kawarta Umma har bakin (gate) din asibitin inda xata hau mota" ta koma gida" suna tafiya suna hira bayan sun rabu ne sai fatima ta koma domin ta amshi xainav xaman jinyar" . ====>+++++¤+++++++<======= . "Xabba'u ta kira Asma'u ta fada mata abinda yake faruwa da kuma rikicin da akayi" "yanxu haka ina gidanmu inda babanmu yake Asma'u na baro gidansu Hajiya jiya da daddare" Asma'u tace da ita-: "to sai me don kin baro musu gidansu?" kawai suna yi maki bakin ciki ne don sun fahimci yanxu ke mujahid yake so ba fatima ba" . . Xabba'u tace-: "Na sani, nasan komAi Asma'u" ai shi yasa dama na baro musu gidan" Asma'u ta sake ce mata-: "A kan mujahid ba gudu ba ja da baya xabba'u kuma ko suna so ko basa so" sai kin aureshi" saidai su mutu" ai ni ban yi xaton Hajiya xata yi maki haka ba" wato ita ma ta nuna 'yarta take so kenan!" Xabba'u tace-: "Eh mana" ai taxo daxu da sape ta samu baba ta fada masa karya da gaskiya" tayi xaton xai barta ni ya xaxxageni" ina jinsu" tana gama fada masa ya kuma fada ta da fada da xagi" ya koreta fata-fata" . . Asma'u tayi dariya-: "to kin gani" yanxu bamu da wata matsala wajen su baba" tunda shi dama a bangarenki yake" xabba'u tace-: "A haba" baba ya xa.ayi ya goyi bayanta dama" sa.a ma tayu bataxo jiya ba lokacin da naxo gidan" da a lokacin ta biyo ni" ba abinda xai hana ya dauko sanda ya biyota" saboda akan dukan da Alhaji yayi mun" baba ya fusata sosae" Asma'u ta tambaye ta-: "kin kira mujahid kin fada masa abinda yake faruwa ne?" tace--; "A,a bamuyi waya dashi ba yau" Asma'u tace-: "to kada ki kirashi" ki barni xanyi (handling) din maganar" ina so ne yaxo har gidan ya sameki" domin kowa ya tabbatar ya damuke dake" xabba'u tace cikin farin ciki" "Na gode kawata (thank you so much)" suka rabu suna murnar nasarar da suka samu" . =====>++++¤+++++<======== . Mujahid yana wajen aiki" Asma'u ta kirashi" da ya dauki wayar ne" tun kapin su gaisa ta ce dashi" "mujahid kaga abinda xabba'u take jin tsoro" wanda yasa taki amsar soyayyarka" sai da na matsa mata" kaga dai ya paru" "meya faru Asma'u?" mujahid ya tambayeta a tsorace" Asma'u tace-: "kwai daga mamanka taxo ta samu Hajiya binta akan maganar soyayyarka da xabba'u kawao da tafiyarta Hajiya da Alhaji sunusi mahaifin fatima suka rupar wa xabba'u da bugu kamar xasu kasheta" dakyar ta kwaci kanta ta gudu" yanxu sun koreta" korar wulakanci saboda tana sonka" tana can gidansu wajen mahaifinta" mujahid yaji xuciyata ta kawo masa wuya" "xabba'un ce suka yiwa haka?" wanne mataki aka dauka?" Asma'u tace- "to wanne mataki xa.a dauka mujahid?" ba suna takamar su suka riketa ba" tun tana karama" kuma suna takamar su masu kudi ne" shiyasa suka yi mata wannan wulakancin" dama hankuri take yi a gidan" yanxu dai tayi kai" ta koma gidansu" axan ma ta kwana" . . Mujahid yace a fusace-: "Amma don xalunci don su suka riketa sai suyi mata haka?" idan suna tunkaho da dawainiyar da sukayi mata ne" su fada ko nawa a biyaso mana" Gaskiya nixanje gidan su xabba'un in samu mahaifinta muyi magana" a dauki mataki akan bugun da Alhaji sunusi yay mata" kawai don yana auren yayarta kuma sai ya dake ta" haka akeyi?" Asma'u tace-: "A,a hankuri xa.ayi mujahid" ita ma xabba'un ta dangana ta rabu dasu" ta san saboda kace baka son fatima" ita kake so shiyasa sukayi mata haka" mujahid yace a fusace-: "Na ki inso fatiman" indai akan nace banason fatima ne xasu huce akan xabba'u to kome xasu yi sai dai suyi" . . Asma'u tace- "zaka xi gidan su xabba"un ne idan ka taso daga aiki ko kuwa?" mujahid yace-' "Of course" xan xo" yanxun nan ma da mun gama wayar nan xan kirata inji yadda ta kara ji da jikin nata" Allah yasa dai basu ji mata rauni ba" Asma'u" tace-: "No, munyi waya bataji rauni ba" yanxu ta samu sauki" amma dai duk da haka ka bulla ku gaisa" "Ai wannan dole ne" an jiman nan kuwa" a ina gidansu yake?" Asma'u tace-: "yana yakasai ne ko kuma in ba matsala kawai ka biyo ta gidanmu ka dauke ni" sai muje in raka ka can gidan" naga xaifi sauki" "shinkenan ma kuwa" xanxo da yamma in dauki Asma'u" mujahid ya fada tarkon xabba'u da Asma'u . =====>++++¤++++++<======= . Lokaci kusan daya Umma ta dawo daga asibitin murtaka duba Hajiya binta da kuma mujahid wanda ya dawo daga wajen aiki" Umma tana xuwa" da yake ta riga mujahid shigowa" ta samu mama Rakiya suka xauna ta fara warware mata xare da abawar yadda abun ya paru" Umma tace da mahaifiyarta"-: "xabba'un nan makirace Umma" idan kikaji irin makircin da tayiwa Hajiya wallahi kare ba baxai ci ba" ki raba yaya mujahid da ita" idan kuka barshi ya aure ta" yadda ta fasa gidan su fatima" haka muma xata xo ta fasa mana wannan gidan" Xabba'u uta tayi kutun-kutun din da ta raba fatima da mujahid" duk abun da mujahid xaixo ya fada maki a game da fatima duk sharrin xabba'un ne" ni abunda nake so" ko da yaya mujahid baxai koma wajen fatima ba" to gaskiya a rabashi da xabba'u domin kuwa ba alheri bace gareshi" , , mama Rakiya tace-; "to nipa na rasa gane kan wannan lamari" idan mujahid yaxo sai yace kaxa" ke kuma idan kika xo sai ki rushe kice kaxa" ya kuke so inyi ne a gidan nan Umma?" ke da dan uwanki kunki ku hada kanku ku fahimci juna" shi yana cewa karya kikeyi" ke kuma kina cewa karya yake yi" ta yaya xan fahimci wanene yake da gaskiya a cikinku?" ke kina son kawarki fatima" shi kuma yana son budurwarsa xabba'u" . . Kince xabba'u ba alheri bace" to yaya xamu gane wanene yafi gaskiya a cikinku Umma?" . . Umma tace wa mama Rakiya-;¤TUNA DUNIYA¤ . . . ραgє 18 ωιтн Aßßαη ßαѕмαян Dαη мυтαη уσßє ωнтѕαρρ ριη +2348082035050 . . Umma tacewa mama Rakiya-: "ni nafi so kiyi bincike mama" kiyi binciken yadda wannan matsalar take" yanxu haka Hajiya tana asibiti" kuma inda badon abinda xabba'u tayi mata ba" me xai bata mata rai haka?" ciwon xuciya fa take yi mama?" idan mujahid ya auri xabba'u mama" watarana haka xa.a kwashe mu akai mu asibiti" bakin cikin ya kamamu" Umma tana cikin fadin wannan maganar mujahid ya shigo gidan cikin damuwa" yaji abinda yake fada" don haka ko sallama baiyi ba" ya fara yiwa Umma fada" . . Ke Umma me kike fada?" kin sam abinda kike cewa kuwa?" xabba'un ce kika xo kina hantararta a wajen mama?" ni xakiyiwa munafunci?" dama baki da kunya" saboda kinga ina sakar maki fuska ko?" mama Rakiya tace dashi-: "ya isa hakan nan" bana son in sake jin maganar" kowa ya tafi ya bani wuri" Mujahid yace da mama Rakiya-: "In banda wannan yarinyar bata da mutunci mama" bata san abinda yake faruwa ba" maganar da akeyi yanxu xabba'un tana can kwance bata da lapia" su Hakiya sunyi mata dukan tsiya" ita da Alhaji sunusi" kawai saboda xalunci sun koreta tabar gidan" ta koma gidan mahaifinta a yakasai" menene wannan idan ba hauka ba" kawai sun samu 'yar mutane da baugu sun tarar mata" . . Umma ta daga kai tace dashi-: "yaya mujahid ba haka bane" duk wanda ya fada maka wannan maganar karya yake yi" Hajiya batayiwa xabba'u komae ba" kuma ba wanda ya kori xabba'u don kanta ta kwshe kayanta ta gudu ta koma yakasai" Hajiyar ce ma taje daxu da sassafr domin ta dawo da ita" shine aka samu (misunderstanding) acan gidan" har abin ya bata wa Hajiya rai" yanxu haka tana can a asbiti" nima daga asibitin nake" mujahid" ya dakatar da eta-: "Rufe mun baki da karyar banxa" baki san yadda maganar take ba kixo har kina wani hakikancewa" wannan shine (last time) dinda xan baki" idan na sake jin kinxo kin fada wa mama wani aibu akan xabba'u saina karairayaki" a gidan nan" xaki tashi ki bani wuri ko sainayi (ball) dake?" . . Umma ta xumburi baki" ta tashi ta tafi dakinta cikin pushi" mujahid ya dawo da hankalinsa wajen mama Rakiya" wacce tabisu da idanu tana kallon su suna jayayyarsu yace da ita-: "kiyi hankuri mama" duk wannan maganar da Umma take fada maki karya take yi" kawai ta hada kaine da fatima saboda taxo ta rika fada maki karya da kaxapi" don ki tsani xabba'u" amma komai ta fada ba gaskiya ba ne" Xabba'u yarinya ce mai ladabi" ko kadan baxaki hadata da wannan shashashar fatimar ba" wacca bata san mutuncin kanta ba" ki toshe kunnenki daga duk wata magana da wadannan yaran suke fada" ba gaskiya bane mama!" Mama Rakiya tace-: "Ita ma na fada mata" ni yanxu baxan iya gane mai gaskiya ba a tsakaninka da Umma" ku dukkanku 'ya'yana ne" amma kowa da abinda yake xuwa yana fada" Ni abinda na barwa xuciyata shine" koma a ina gaskiyar wannan al'amari take xata baiyana komai dadewa" idan xabba'u ce tagari" lokaci xai nuna" idan kuma fatima ce tagari" babu abunda lokaci xai boye" idan mukayi hankuri" illa iyaka" mujahid yace-: "Ai tuni ma lokaci ya gama nunawa mama" xabba'u ce tagari" kuma xan tabbatar maki da haka" Mama Rakiya tace dashi" "to Allah ya bamu sa.a" . =====>++++¤+++++++<======= . Kwana biyar Hajiya binta tayi a asibiti" ta samu sauki sosae" Alhaji sunusi ne ya matsa aka sallamesu" suka dawo gida" A kwanakin da tayi a asibitin" kowa yaje gaisheta har mahaifinta da yake pushi da ita" shima saida yaje ya duba ta" amma xabba'u ko sau daya bata je ba" Da suka xo gida ne Alhaji sunusi ya tara su a falo su dukansu" Hajiya binta da 'ya'yanta watau fatima da kannenta biyu yace dasu-: "Ina so mu dukkanmu mu dauki wannan masifa data same mu a matsayin kaddara" bana son wannan yasa my kullaci wani mutum a xuciyarmu" musamman ita wannan yarinyar xabba'u mu daketa har yanxu a matsayin 'yar uwarmu" ko in cema 'yar cikin nan gidan" domin kuwa har abada kome xabba'u ta xama a duniyar nan" to bata dafa ina yakai nan" Ba lokaci ba bane yanxu da xata gane haka" amma da sannu xata gane yau da kullim" . . Ke kuma Hajiya ki kwantar da hankalinki ki daina damun kanki" ki cire duk wata damuwa daga xuciyarki" nasan abunda yake damunki" bai wuce takaicin fushin da baba yake yi da ke ba akan sabanin da ya shiga tsakaninmu da xabba'u" Ki daina damuwa duk wannan ba wani abu bane" Alheri da kika yi masa don neman albarka" kici gaba da yi" Allah yasan abinda yake xuciyarki kuma xai taimakeki" komai xaixo ya wuce in Allah ya yarda" Tun daga ranar suka kwantar da hankalinsu a gidan" sukaci gaba da harkokin su kamar komai bai taba faruwa ba" . =====>++++¤+++++<======== . A bangaren xabba'u kuma suna can suna shan soyayyarsu ita da dan lelen saurayinta mujahid" kusan kullum sai yaje gidansu" kuma da yake xabba'u 'yar sin lalacewa ce" koda yaushe sai ya dauke ta a mota sun tafi yawo" xabba'u tana sha.awar suje (shopping) mujahid yana kashe mata kudi sosae" yana yi mata duk abinda take so" . . A wani mako ne da ya xagayo" wani abokin mujadi da suke aikin banki tare sai yayi aure" yaba mujahid ankon da 'yan matan amarya da danginta xasuyi" wane leshi ne fari na dubu biyar" salim yace wa mujahid yakaiwa xabba'u ta dinka taxo bikin tare da ita" ya basu (gate pass) guda biyu" inda xa.a yi fati a ranar asabar da daddare" mujahid ya amso leshin" bai fadawa xabba'u ba sai ana saura gobe yace ta shirya xai bada leshin ankon a dinka mata" xaixo mata dashi gida" sai dai kawai tayi wanka tasa su tafi biki" . . Mujahid yakaiwa Umma kanwarsa leshin ankon ranar juma.a yace-: "Ina son ki dinka leshin nan na anko ne" kiyi masa dinki mai kyau" gobe muna da bikin wani abokina ne" Umma ta amshi leshin" ta ciro shi a leda" ta tambayeshi" "Na wanene yaya mujahid" ya bata rai yace-: "Na xabba'u ne" Umma ta yatsine fuska cikin fushi" ta kalli leshin a wulakance" mujahid ya harare ta yace-: "saura kiyimun shirme" gobe da safe nake sonsji" xan tafi dashi ne" daga wajen aiki xan wuce in kai mata" . . Umma ta figi ledar leshin xata kai dakinta" "ko bakiji abinda nace bane" Umma?" mujahid ya daka mata tsawa" tace a fusace "na ji" Har yamma tayi umma bata ciro leshin ta yanka ba" mujahid yaje har dakinta ya sameta ya gargade ta" Umma" ya naga baki je kin fara dinka leshin ba?" wai me kike nufi ne?" Umma tace-: "xan dinka" mujadin yace da ita-: "kinga akan dinkin nan ranki xai baci" Umma" kina ji na?" xan saba maki a gidan nan idan aka wayi gari naga baki dinka mata ankon nan ba" Ya koma daki a fusace" Umma ta dauki leshin taje dakin mahaifiyarta" ta ciro leshin ta yanka" ta hau keke ta fara dinkawa" Da mujahid ya sake dawowa yaga tana kan aikin dinka leshin ne sai yaji sanyi a ransa" ya tafi ya bata wuri" . . Da yake Umma ba kanwar lasa bace" ashe ta gama shirya musu tsiya shi da xabba'u" tayi rigar wata irin falkekiya kamar buhun masara" Hannunwan rigar 'yan sirara mitsi-mitsi" dakyar hannu xai iya shiga" ta matsw wuyan rigar kamar rigar maxa" sannan taxo yin siket din shima sai tayi sama yayi yawa" kasa kuma sai ya tsuke kamar kayan hawa bori" . . Ta gama dinkin ta ninke kayan tana girgixa kai cikin mugunta" ta saka masa a leda tsap" ta gyara su kamar abun arxiki" sai da sape da xaije aiki mujahid yaxo ya tambayeta" "Ina kayan suke?" Umma ta dauko su a leda a ninke" ta bashi ya amsa" Ya tambayeta a fusace-: "Nawa ne kudinki?" Umma tace-: "Ai kyauta nayi maka" kabar kudin" ka kaiwa xabba'u taci biki lapia" Mujahid yadan sake ransa don kuwa yaga alamun watakila Umma ta dawo ita ma ta goyi bayansa akan soyayyarsa da xabba'u dama itace kawai matsalarsa" kowa yabi a gidan" amma ita tana nan tana adawa" tana bangaren kawarta fatima" . . Mujahid yaje aiki yabar kayan a cikin mota" saida yamma" sanda kowa yake tashi domin suje suyi shirin xuwa fatin abokinsu" sai ya kira xabba:u a waya shina yace mata-: "xanxo maki da naki ankon yanxun nan" ki dauki kwalliya da naxo saiki sa mu wuce" na bayar da kayan an dinka maki" xabba'u tace-: "to (my sweetee) xanyi wanka in shirya kafin kaxo" "i love you xubee" "i love you too" . ====>+++++¤++++++<======= . Mujahid ya isa gidan su xabba'u bayan minti talatin dayin wayarsu" ya fito daga cikin mota kenan ta fito daga gida" da yake da xuwansa ya matsa hon" a haka yake kiranta idan yaxo koda yaushe" xabba'u ta dafa kopar gidansu tana dariya" da ganinta tayi wanka da kwalliya" shi kawai dama take jira" mujahid ya dauko kayan da ya xo mata dasu" na ankon" ya isa inda take tsaye" "you are welcome my love" tace dashi tana kashe masa idanu" mujahid yace da ita" "kinga lokaci ya kure xabba'u wasu tun daxu har sun tafi" Amshi kayan nan kisa" ki fito mu tafi" xabba'u ta mashi kayan cikin farin ciki" tace "xan fito yanxu nan" minti biyar ya isa" . . Mujahid ya koma ya jinjina da motarsa yana kada makullin motar dake hannunsa" ba a kai minti biyu ba xabba'u ta fito tana kukan shagwaba" sanye da kayan" ta tsaya a bakin kofa ranta a bace" tace da mujahid" "Haba mu love" ya xakayi mun haka?" Don Allah duba pa dinkin da ka kawo mun" taci gaba da kuka shagwaba" da pushi" mujahid ya matsa xuwa inda take a kidime" yaga tasa katuwar riga kamar malum-malum" ga hannayenta ma dogaye ne har sun kusa shanye hannayenta" wuyan rigar ya shaketa tamau da kyar take iya magana" siket din kuma bashi da maraba da wandon leda" bai taba ganin kayan ban tsoro irin wannan ba" ya tambayi xabba'u "wadannan ne kayan da naxo maki dasu yanxun nan?" xabba'u ta harareshi-: "to da wadanne?" kace xamuje fati" amma ya xakaxo mun da irin wannan dinkin?" (i,em very embarassed) ta sake fashewa da kuka" . . Mujahid ya lallasheta" "kiyi hankuri" ya isa hakan nan xabba'u" kiyi hankuri ban san haka tayi maki wannan dinkin ba" yaji kunya ta kamashi sosae ya rasa inda xaisa kansa" gabadaya maganar xuwa biki ta rushe kenan kwata kwata" " jeki ciro kayan ki dawo mun dasu" kiyi hankuri xabba'u" ban san haka dinkin yake ba" . . Xabba'u ta koma cikin............¤TUNA DUNIYA¤ . . . ραgє 19 ωιтн Aßßαη ßαѕмαян Dαη мυтαη уσßє ωнтѕαρρ ριη +2348082035050 . . Xabba'u ta koma cikin gida tana kunkumi da shagwaba" bayan minti biyu ta dawowa mujahid kayan a cikin leda" ta cillo masa" ya amsa" tun kapin ya sake baya hankuri ta sake komawa cikin gida tana pushi" mujahid ya cije baki" xuciyarsa tana kunar abinda Umma kanwarsa tayi masa" ya mayar da kayan cikin mota" ya tuka ya nufi gida cikin pushi" Da xuwansa ya fito tare da kayan a hannunsa" ya shiga cikin gidansu kamar xai tashi sama saboda sauri" . . Umma" kina ina?" Umma....?" tunda Umma taji kiran mujahdi yayanta" sai tayi sauri ta ruga dakin mahaifiyarsu mama Rakiya" saboda tasan tsiyar da ta aikata" mujahid yabita dakin mama" da xuwa ya same ta ta boye a bayanta" "wai me kuke yi haka ne a gidan nan?" kun san bana son wannan haukar da kuke yi mani kullum" menene kuma?" mama rakiya ta tambayi mujahid wanda ya shigo a fusace da ankon da Umma ta dinkawa xabba'u da ya rasa abinda xaiyiwa Umma ya huce" saiya numpasa yace da mama-: . . "ßa wani abu bane ya faru" mama dama xamuje wani biki ne ni da xabba'u na abokina salim" bana fada maki yayi aure ba?" Acan garinsu aka daura auren" amma anan xa.ayi bikin" mama rakiya tace-: "to! Naji, anyi haka" ka kuwa fada min" mujahid yace-: "yauwa to mama kinga yadda muke tare dshi" ai yakamata daga bangarena a samu wani yaje bayan ni tunda dai shima an xama daya dashi" mama Rakiya tace- "A kwarai ma kuwa" to dama meye ampanin xaman taren?" ai irin wannan ne idan biki ya tashi ajewa mutum a tayashi farin ciki" mujahid yace-: "yauwa mama" to kinga xabba'u bata da lafiya" baxata samu xuwa ba" kuma ga ankonta da umma ta dinka mata" tunda haka ne Umma sai tasa ankon" muje tare ta raka ni bikin" mudan tayashi farin ciki" tunda dai ba.a rasa wacce xata raka ni bane" ga kanwata 'yar uwata ko kuwa?" . . Mama rakiya tace-: "eh wannan yayi" xuwanka da 'yar uwarka ai yafi tunda tayashi murna xakuyi" ke Umma tashi kisa ankon kuje ki rakashi mana" kuce ina murna" Allah ya bada xaman lafia" Umma tasa hannu a kanta" "mama nima pa kaina yana mun ciwo" tun daxu" baki ga ina kwance ba...?" mama rakiya tayi mata xagir-xagir "Bana son rashin mutunci Umma" don kinga ina hanashi ya rika dukanki" shiyasa kike raina shi ko" idan na sake buda idanuna banga kin tashi kin shiga wanka da sauri kin fito yanxu kun tafi ba" saina bata maki rai" Umma ta tashi tana kumbure-kumbure" ta wuce mujahid ta fita daga dakin" yace da ita" "kiyi sauri kiyi wanka" ga ankon kixo kisa mu tafi" dama ke kika dinka kayanki" Umma tace-; "Ni ina da kayan da xansa" ba wani ankon da xansa" ka rike kayanka" mujahid yace da ita-: "kinyi karya kuma anan" komai tsiyarki sai kinsa" . . Umma ta debo ruwa ta shiga wanka" mujahid ya jirata a dakin mama rakiya" suka xauna hira" har Umma ta fito daga wanka xata wuce dakinta kenan sai mujahid yace da ita" "Xo mana ga kayan da xaki sa na ankon" sauri nake yi pa" kada ki bata mun lokaci" Umma taja ta tsaya cikin xullumi" mama rakiya ta daga murya tace da ita" "yau dai sina taba lafiyar jikinki xakiji dadi umma" yayan naki kike yiwa wannan iya shegen?" ke yayi ta xaman jira pa" baxaki xo ki amshi kayan kuje kisa ku tafi ba?" Umma tace da mahaifiyarsu" "mama ni bana sa anko idan ana biki" nace yabar shi insa kayana mana" duba daya bane?" . . Mujahid yace da mama rakiya-: "Don me to nasa ta dinka kayan mama?" badon asa in gani nasa a dinka

Chapter 7 of 9