Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

inda take xaune akan
gadonsu"
"Anti xabba'u" lafiya naganki a haka?" ko wani abu
yake damun ki?"
xabba'u ta dago kanta ta dubi fatima" ta koma ta
kwanta tace da ita"
"bana jin dadi ne..... Kasala ce ke damuna" amma
xan tashi yanxun nan"
Fatima tae da ita-:
"ko in tambayi Hajiya idan ta rage magani ta bani
in kawo maki ne?"
xabba'u ta girgixa kanta"
"A.a barshi kawai" bana son maganin" xan tashi
yanxun nan!
:
.
Fatima ta rabu da xabba'u ta mayar da hankalinta
akan hoton mujahid" tace da kanta"
"Oh! Har na mance da hoton nan" kusa ya kamata
in samo a dakin Hajiya in kife shi a jikin bango"
ta dauki hoton da hannu daya" xabba'u ta sake
daga kanta ta kalli fatima tana rike da hoton
mujahid"
A karo na farko xabba'u tayi mata magana akan
masoyin nata"
Qdama wannan shine mujahid din"
"shine Ashe dama baki taba ganin sa ba"
xabba'u ta yatsine fuska cikin kishi"
"A ina xan taba ganinshi?" ko a hanya na ganshi
da wahala in ganeshi"
.
.
Fatima wacce bata san abinda yake a xuciyar
xabba'u ba" ta mika mata hoton ta ce-:
"dube shi da kyau ki gani Anti xabba'u" ance yana
kama da Umma" ni banga wata kama da suke yi
ba"
Xabba'u tayi karpin hali ta amshi hoton mujahid
tana kwance bata tashi ta xauna ba" Akan gadon ta
rike hoton da hannu biyu ta sake xuba masa
idanu" taji ya kara son mujahid a ranta"
tace da fatima-:
"sunyi kama mana" ba kanwarsa ba ce?"
fatima tayi dariya"
"Gaskiya basa yin wata kama" ai Umma tafi shi
kyau" ko kuwa ke ya kika gani?"
xabba'u tayi ajiyar xuciya cikin rashin kuxari tace
da fatima-:
"xata fishi kyau mana" ita ba mace bace!" Amma
shi ma yana da nasa kyan daidai shi"
.
.
Fatima ta xauna kusa da xabba'u akan gadon ta
tambayeta"
"Na ga kamar baiyi miki ba xabba'u bai hadu ba
koh?"
xabba'u ta sake bata fuska ta juyi ta dubi fatima
tace-:
"ya xaki ce haka?" yayi mana" kuma koma baiyi
ba" xance ne ki rabu dashi?" ba masoyinki bane?"
ke kika ce kinji kin gani shi kike so"
ta mika mata hoton" fatima ta karba" xabba'u taci
gaba da ce mata-:
ki dai yi a hankali da samarin nan na xamani
wadansu 'yan karya ne" sai suxo su tsaraki suce
xasu aureki" amma a xuciyarsu abin ba haka yake
ba"
.
.
Fatima ta dubi hoton mujahid tayi murmushi tace
da xabba'u
"Gaskiya ne anti xabba'u" amma mujahid baxai
taba yimun haka ba saboda yana sona kuma yana
kulawa da duk wani abu da yasan xai faranta mun
rai" na yarda da mujahid (hundred percent) baxae
taba yimun karya ba"
Xabba'u taji wani bakin ciki ya soki xuciyarta" ta
tabbatar fatima tayi nisa akan son mujahid" baxata
iya rabuwa dashi ba"
ta sake cewa da ita"
"ke baki san irin wadannan samarin bane dake
aikin banki?" kullum sai sunyi budurwa a wajen
aiki" ko aurenki yayi mata xai rika jawo maki har
cikin gida kullum"
xabba'u ta fakaici idanun fatima ta harareta" fatima
tace da ita tana kallon hoton mujahid dake
hannunta"
.
.
"Anti xabba'u don dai baki san mujahid bane" shi
da kunya ne dashi" baya yiwa mata magana kwata
kwata" Ni kaina ya dade yana sona" amma ya kasa
fada mani" dole sai da Umma ta fahimci halin da
yake ciki" ita taxo ta fadamin" mujahid yana da
kunya" baxai rika jawo mata suna biyoshi har gida
ba"
Xabba'u ta cije lebenta cikin fushi" ta sake cewa
fatima-:
"Amma yana shaye-shaye" don naga idanunsa
kamar irin na 'yan daba ne" kinyi binciken hakan
kuwa?"
fatima ta dubi idanun mujahid a cikin hoton da ke
hannunta" tace da xabba'u"
.
.
"kodai kallon tsoro kika yi masa Anti xabba'u"
amma mujahid baya shan komai wallahi" nasan
shi tuntuni" tun muna firamare ni da Umma" yana
da kamun kai sosae" yana da ilmun addini"
babansu ma babban malami ne a layinsu" a
wajensa xaki ga ana xuwa ana daukan karatu" Idan
kika je da yamma" yaya mujahid yayi shaye-
shaye?" Ai baxai yiwu ba" gaskiya baya yin haka"
Xabba'u ta lumshe idanunta kamar xatayi kuka
saboda takaici" ya xatayi ta raba mujahid da
fatima?" komai ta fadi a kansa sai fatima ta
kareshi" tana sonshi kamar ta hadiye shi"
xabba'u tace-:
"to Allah ya baki sa.a" Amma dai ki tabbatar anyi
mashi (H.I.V test) kafin kuci gaba da soyayya"
saboda kinga yanxu cutar nan ta kanjamau tayi
yawa ako ina" mutanen da bakiyi xato ba saiki ga
sune suke da wannan cutar" kice kina so kuje a
gwada shi a asibiti ki gani"
.
.
Fatima tayi ajiyar xuciya-:
"Gaskiya babu xargi a tsakanina da mujahid" ya
yarda dani" bai taba dada man wata magana ba
wacce ke nuna yana xargi na" kinga bai kamata ba
ni in fara fitowa in numa ina xarginsa"
Idan nayi haka sai in ga kanar xan rage kima da
martaba a wajensa"
.
.
Na fauwala Al'amarina a wajen Allah" domin kuwa
shine masanin sirrin abinda yake boye" kuma ina
rokon Allah kullum ya kare ni daga kowacce iriyar
masifa" da wacce na sani da wacce ban sani ba"
.
.
Xabba'u tayi shiru har xuwa wani lokaci tana
mayar da numpashi domin kuwa ranta ya baci
sosae"
ta bude idanunta ta.........TUN A DUNIYA"
.
.
.
РÁĞE
09
WĨŤH
ÁßßÁŃ ßÁŚМÁŔH
ĎÁŃ
МÚŤÁŃ YŐßE"
.
.
Xaßßa'u tayi shiru har xuwa wani lokaci tana
mayar da numpashi domin kuwa ranta ya baci
sosae" ta bude idanunta ta kalli fatima wacce ke
xaune tana kallon 4ton masoyinta mujahid tana
murmushi" tace da ita a fusace-:
"Ai sai ki bani wuri haka insha iska" hirar ta ishe
ni"
FATIMA tayi sauri ta tashi ta bata wuri domin da
alama 'yar tsiyar sun fara xuwa" ta ajiye foton a
inda ta dauke shi" har xata fita sai xabba'u ta sake
daga murya tace da fatima"
"wai ke me kike nufi fatima?" baxaki nemo (duster)
ki goge mana ledar tsakar dakin nan ba" kina gani
tayi datti" ko kuwa ni kikeso in tashi in goge maki
daki?"
.
.
Fatima tace da xabba'u
"Bari inje in dauko a dakin Hajiya" daga nan sai in
debo ruwa a roba inxo in goge"
xabba'u tayi tsaki a lokacin da fatima ta fita daga
dakin cikin ladabi" taje ta dauko robar da (duster)
goge leda"
Xabba'u ta sauko daga kan gadon cikin fushi ta
tsaya tana kallon hoton mujahid tayi murmushi
tace da kanta"
"Nice matarka" ni nafi cancanta da kai" ba wannan
sokuwar ba wacce ko soyayya bata iya ba"
.
.
Xabba'u tana da muguwar kawa wacce suka fi
shakuwa" sunanta Asama'u ko a makaranta
halinsu daya" idan suka xauna basu da wata
magana sai ta samun kudi a wajen samari" su
duka biyun da wahala wani namiki yaxo don su
saurarashi" indai ba ganinsa sukayi da kumbar
susa ba"
Asma'u da xabba'u sun yarda da kwacen saurayi"
basa jin kunyar su kwance kawarsu saurayi komai
shakuwar da tayi dashi" shiyasa yawancin
kawayensu wadanda basu da hali irin nasu suka
taka tsan-tsan da su" basa so su rika nuna masu
ko lambar wayar samarinsu bama hoto ba" domin
kuwa sun san mugun halinsu"
.
.
Asma'u ta taba kwace wa kanwarta saurayi wacce
suke uwa daya uba daya da ita"
Abinda Asma'u da xabba'u suka yarda dashi shine
in dai suna son saurayi" to ko da wacce budurwa
suke soyayya" xasu iya yin makirci da ita domin
su cimma burinsu"
Ganin yadda fatima ta kekashe akan son mujahid
sai xabba'u ta yanke shawarar xuwa ta shaida wa
Asma'u kawarta halinda ake ciki domin su nemo
mafita tun da wuri"
.
.
Xabba'u ta shirya ta fita xuwa gidansu Asma'u
wacce gidansu ke kan layin dake gaba da nasu"
layin tsakaninsu babu nisa" ta samu Asma'u tana
gyara gashin kanta a waje kanwarta tana taimaka
mata"
Da ganin xabba'u sau ta mayar da hankalinta
kanta"
"Manya-manya maganin kanana-kanana" tace
sannan taba ta hannu suka tafa"
tace da kanwarta ta tafi" Asma'u ta jagoranci
xabba'u suka shiga daki"
Asma'u gajeriya ce mai kaurin jiki" xata girmi
xabba'u amma ajinsu daya a makaranta"
Da ganin xabba'u tasan akwai wani abu da yake
damun ta" don haka sai tayi saurin fara tambayar
ta"
.
.
Meye labarin farar kawar?" naga kamar yau kinxo
ranki a bace"
Xabba'u tayi tsaki"
"Bari ke dai Asma'u ina cikin matsala babba"
"wacce iriyar matsala kike shiga?" meya faru?"
xabba'u taji ajiyar xuciya tace da Asma'u
"Na kamu da ciwon son wani saurayi ne da
samunsa xaiyi mun wahala" ina son shi fiye da
yadda xan fada maki" kuma baxan taba daina son
shi ba" to amma matsalar baxai yiwu in mallakeshi
ba domin kuwa ya samu wata har sun fara
maganar aure"
Asma'u ta dan bata ranta" ta tambaye ta-:
"Wanne saurayi?" kuma wacce yarinya yake so xai
aura?"
xabba'u tace-:
"Akwai matsala Asma'u saurayin fatima ne wacce
muke gida daya" fatima 'yar yayata Hajiya binta"
hotonsa kawai na gani a wajenta" amma tun
lokacin xuwa yanxu ji nake kamar bani da lafiya"
son shi yayi reshe a ko'ina a cikin jikina"
.
.
Asma'u ta dan yi murmushi tace-:
"wannan ai mai sauki ne" nina yi tsammanin ma
wani saurayi ne dake can wata uwa duniya" a
nesa" Amma wannan kwace shi kamar wasa ne"
kada ki tayar da hankalinki"
xabba'u ta daga kan ta dubi Asama'u sosai"
"Na fada maki saurayin fatima ne" saurayi ne na
cikin gida" ya xa.ayi in kwace shi ya dawo wajena"
ya rabu da ita?"
Asma'u ta ce-:
"to me don yana saurayin fatima?" Ai irin
wadannan samarin na gida sunfi dadin (snatching)
indai kina son shi ki kwantar da hankalinki" ni da
kaina xan taimakeki mu rabata dashi" ya dawo
wajenki cikin sauki"
.
.
Xabba'u ta fara sakin ranta-:
"kina jin xamuyi nasara, Asma'u?"
tace da ita-:
"to nawa mukayi" ko kin mance ne" Ai mu yanxu
munci dubu sai ceto" kada ki mance da kanwata
Aziza sai da nayiwa (snatching)" na kwace gayen
da xata aura" dana ga ya fara lafawa" 'yan canjinsa
suna ka baya" nayi (dropping) dinsa na kama
wani"
Xabba'u ta bata hannu suka tafa tana dariya" bata
baro gidansu Asma'u ba sai da suka gama
tattauna duk yadda xasu yi wajen kwace wa fatima
masoyinta mujahid"
.
=======>++++()++++<=======
Da komawar xabba'u gida ta tambayi fatima"
"yaushe masoyin naki xaixo" a gaisa dashi
fatima?"
Fatima wacce ke cin abinci akan doguwar
kujerarsu daya dake dakin" tace wa xabba'u-:
"Gobe ma xaixo da yamma" haka muka yi da shi"
in dai ba wani abu ya tsare shi ba"
Xabba'u ta ce-:
"Allah ya kaimu goben lafiya" Idan ina gida lokacin
xamu gaisa dashi"
.
.
"DA komawar xabba'u gida ta tambayi fatima-:
"yaushe masoyin naki xaixo" a gaisa dashi
fatima?"
fatima wacce take cin abinci akan doguwar
kujerarsu daya dake dakin" tace wa xabba'u
"Gobe ma xaixo da yamma" haka mukayi dashi
indai ba wani abu ya tsare shi ba"
xabba'u tace-
"Allah ya kaimu goben lafiya" idan ina gida lokacin
xamu gaisa dashi"
Fatima tace-:
"Na gode"
saboda a yadda xabba'u take fushi da ita" suna
fada tana ganin alheri ne da kuma alamun
sasantawa idan har ta cire girman kai taje ta samu
mujahid suka gaisa"
fatima bata san makircin da suka shirya mata ba
akan soyayyarsu da mujahid"
.
=====>++++()+++++<=========
.
WASHE GARI ana gama sallar isha'u mujahid ya
kira fatima a waya yace da ita yaxo yana kopar
gidansu" yana jiranta ta fito"
fatima wacce ke daki tare da xabba'u sai ta dubeta
tace da ita"
"Ga mujahid din yaxo" Anti xabba'u yana waje"
shiya kira ni a waya yanxu"
Xabba'u wacce kamar abin bai dame ta ba tace-:
to idan yaxo sai menene? Wajena yaxo ko kuwa?"
fatima tace da ita-:
A'a dama naji jiya ne kina cewa idan yaxo xaki je
ku gaisa"
Xanna'u tace cikin ixgilanci"-:
"Na mance ne (any way) kije xanxo kafin ku gama"
.
Fatima ta tashi ta fita xuwa kofar gida wajen
mujahid"
fitarta xabba'u ta dauko wayarta ta kira kawarta
Asama'u tace da ita cikin sauri"
Yaxo yanxun nan Asma'u suna nan a waje shi da
fatima suna hira"
Asma'u tace-:
"Ok" gani nan xuwa yanxun nan" sannan ta kashe
wayar
.
======>+++++()+++++<=======
:
LOKACIN da Asma'u taxo gidansu fatima ne tagan
ta tare da mujahid" sun xauna suna fuskantar juna
a karamin dakalin xaman dake jikin gidan" har ta
wuce ta shiga cikin gidan basu ganta ba"
Data shita ne ta wuce dakin su xabba'u kai tsaye"
ta sameta tana rike da waya" tana kokarin sake
kiranta"
Asma'u tace da ita"
"Gani naxo ajiye wayar"
xabba'u ta rage muryarta don kada Hajiya taji
maganar da suke yi"
"shine wanda nake baki labari Asama'u ina son
sa" ( I very much luv him)
.
.
Asma'u tace da ita-:
"ya xa.ayi muje wajensa ba tare da fatuma tana
tare da shi ba" don kada ta xargi wani abu?"
xabba'u tace-:
xata xo ta kirani idan xai tafi" baxan yarda tabi mu
ba" kamata yayi mu saba dashi amma ba.a nan
ba" ina so ne ya kasance wani abu ya hada mu"
wanda xai sa mu rika haduwa dashi a wani wuri"
ba.a nan ba"
Xabba ta dube ta cikin xullumi"
"Idan haka ne to yaya xamu yi kenan?" a ina xamu
rika xuwa muna ganinsa?"
.
.
Asama'u tace-:
"Na gama shirya duk wannan hikimar" ke dai
karkade kunnenki kisha labari"
xabba'u ta karkade kunnenta tana dariya"
"na karkade"
minti arba'in bayan haka saiga fatima ta shigo cikin
dakin" tayiwa Asma:u sannu da xuwa sannan tace
da xabba'u.
"Ya ce xai tafi" xaki xone ku gaisa Aunti xabba'u?"
"ke dai kin matsa sai anyi gaisawar nan fatima"
bari mu fita wajen" dama xan raka Asma'u xata tafi
gida" daga nan sai mu gaisa dashi"
Asma'u ta tashi ta dauki gyalenta" xabba'u ta saka
karamin hijabinta suka dunguma xasu fita har
fatima xata bisu" sai xabba'u ta juyo tace da ita'
fatima sai kinbi mu kin tsare mu don xamu gaisa
da shi?" irin haka ai muxaki dorawa kunya a
gabansa" nida ba kawarki bace fatima" kanwar
babarki ce"
fatima ta tsaya a cikin daki" ta barsu suka fita su
biyu"
.
.
Da fitarsu suka samu mujahid a tsaye a jikin motar
sa yana sanye da farar shadda da hula ruwan
toka" yana duba agogo" akwai alamar yana sauri
ne xai tafi gida" Da xuwansu sukayi masa sallama
ya amsa musu"
xabba'u tace dashi"
"Alhaji mukahid koh?"
"wacece antin nawa a cikinku?"
xabba'u ta harare shi cikin kissa"
menene Anti kuwa?" fatima ta fada maka haka
koh?"
yace-:
Naji tana cewa Anti xabba'u shiyasa nake yi mata
kara" ina fata hakan ba laifi bane"
xabba'u tace-:
"Gaskiya laifi ne domin kuwa fatima yaya ta ce" ta
gimeni nisa ba kusa ba" na san kaima kasan da
haka"
mujahid yace-:
"Na taba jin haka amma ba.a wajen fatima ba" sai
dai kuma banyi mamaki ba don tana ce maki anti"
saboda kema kinfi kowa sabin daalilin da yasa take
cewa hakan"
A lokacin ne Asma'u tasa baki tace-:
"Bari inyi maku karambani in shiga cikin jayayyar
taku" ni a ganina mujahid kawata tafika gaskiya
domin kuwa akwai wata adon magana dana ji ana
yiwa karamar kanwar uwa abokiyar wasa ce" ko
baka taba ji ba?"
.
.
Mujahid yayi dariya-:
"Ban taba ji ba sai yau a wajenki" kenan kina so
ku fada min fatima kawar xabba'u ce" ba antin ta
bace"
Asma'u tace dashi cikin kissa"
"Ko dai daka fadi haka yanxun" na san hakan yafi
maka dadin fada" amma yaya mutum yana cikin
kuruciyarsa bai wce shekara sha-tara ba" a rika ce
masa anti?" ai wannan abin dariya ne"
mujahid yayi murmushi yace dasu':
"Yanxu dai na fahimce ku" kunfi so in rika cewa
xabba'u" amma kada in fada da anti"
"Haka ne"
xabba"u tace cikin shagwaba"
"(that is my real name) amma anti sai a bari saina
tsufa tukunna (not now)"
sukayi dariya su dukansu"
.
.
Xabba'u tayi saurin tambayar mujahid"
"Naji kamar ana cewa a (bank) kake aiki ko?"
mujahid yace
"I, a banki nake aiki"
tace dashi-:
"wannan.........TUN A DUNIYA"
.
.
.
РÁĞE
10
WĨŤH
ÁßßÁŃ ßÁŚМÁŔH
ĎÁŃ
МÚŤÁŃ YŐßE"
.
.
XAßßA'U tayi saurin tambayar mujahid"
"Naji kamar ana cewa a (ßank) kake aiki ko?"
mujahid yace-:
"I, a banki nake aiki"
tace dashi"
"wannan kawar tawa ce dama take so ta bude
(accnt) ko xaka iya taimaka mata"
mujahid yace cikin farin ciki"
"Of course" aimu kullum dama muna neman
mutane ne" idan ma akwai wadansu da suke so su
bude accnt ki hada ni da su xabba'u
"To gashi bamu san bankin da kake aiki ba
mujahid"
A ina yake" kuma yashe xamu xo?"
.
.
Mujahid yace-:
"A (destiny ßank) nake" yana nan akan titin
ibrahim taiwo road" kafin kixo (U-turn) na farko"
xabba'u tace dashi"
"xan rakota muxo tare gobe" idan kuma na samu
wasu xan karo maka mujahid"
ya dubeta cikin godiya"
"thankx you so much xabba'u.....
Xan fadawa fatima ke 'yar uwa ce tagari"
suka yi masa bankwana suka tafi" sai da sukayi
nisa da xabba'u take raka kawarta xuwa gida ne"
suka tafa hannayensu cikin farin ciki"
.
.
Asma'u tace-:
"ki kwantar da hankalinki" wannan fa yaxo hannu"
xabba'u tace-:
"Na gode Asma.u goben da karpe nawa xamu je
mu same shi?"
Asma'u tace-:
"muje da sape erin karfe sha-daya haka" xan biyo
maki mu tafi"
sukayi sallama suka rabu"
kafin xabba'u ta dawo gida tuni fatima ta sake
fitowa ta samu mujahid a tsaye yana jiranta"
"wai har ka gama gaesawa da Anti xabba'un?"
mujahid yace da ita"
"ki daina ce mata anti' bata so"
fatima ta tambaye shi tana murmushi"
"ita ta fada maka haka koh?"
"I ita ce mana"
tayi dariya sannan tace"
.
.
"Anti xabba'u kenan" a waje ne bata so ina ce
mata anti" amma a cikin gida nina isa in kira
sunata ban hada da anti ba!"
"sabo me fatima?"
saboda ko ita bata ce komai ba Hajiya xata yimun
magana" kasan Hajiya tana bala'in sonta saboda
ita ce 'yar autarsu"
Mujahid yace-:
"tana da mutunci sosae gaskiya" wannan da suke
tare da ita kawarta ce ko?"
fatima tace-:
"oh Asma'u kake nufi?" kawarta ta kut da kut"
kamar yadda nake da Umma" suma haka suke"
su dukansu suna da mutunci" naji dadin yadda
suka sakar mun fuska" wannan ya nuna suna
goyon bayan soyayyarmu"
.
.
Fatima tayi murmushin jin dadi tana xallumin
abinda xabba'u tayi wa masoyinta tsiya idan ta
fito" ga abin mamki gashi mujahid yana yabonta"
tayi masa mutunci" wannan abin mamaki ne idan
tayi la.akari da yadda xabba'u bata da hankuri"
mujahid yayi sallama da fatima ya tafi"
ta shiga cikin gida tana jiran xabba'u ta dawo tayi
mata godiya" ta fada mata yadda mujahid ya yabe
ta"
fatima bata san abinda yake shirin faruwa da ita
ba"
.
=====>*****+******<========
.
Washegari da misalin karpe sha-daya" xabba'u da
Asma'u suka je bankin da mujahid yake aiki" a
sashin amsar kudi" suka gaisa dashi cikin raha" ya
basu kujera suka xauna ya kawo masu takardar da
xasu cike ta ajiya a bankin" sannan ya nunawa
Asma.a yadda xata cike takardar"
tayi dariya tace dashi-:
"mujahid ba wasu kudi fa masu yawa xan aiye ba"
da dubi biyar xan fara"
mujahid yace da ita"
"Ba komai ai dama da haka ake farawa" watarana
nasan xasu kai miliyan biyar"
"yan matan suke rike numpashinsu cikin kaduwa"
suka dubi juna"
"milyan biyar?" xabba'u ta tambaye shi"
"kada ka bani tsoro mana mujahid" nima ina so
xanso in bude nawa" (accnt ) din A ina xamu samu
kudi mu rika (saving) har sukai haka?"
mujahid yace dasu-:
"kin san kudi suna da wata halayya" saiki fara ajiye
su sannan xasu xama abinda bakiyi tsammani ba"
shiyasa dama ajiya a banki take da ampani"
bayan ya taimake su sun cike form din Asma'u
tasa hotonta sai ta bashi kudin ya shigar da su"
.
.
Sai yace da su-:
"kuna iya tafiya" yanxu ma.aikatamun suna cikin
aiki sosae" xanxo maki da (accnt number) dinki
gobe" xan bawa xabba.u ta ajiye maki idan naxo"
Asma'u ta ce-:
"No, xan xo da kaina ma in amsa" sai dai ka bani
(number) dinka idan akwai wani abu sai in sanar
da kai" ko kuwa ka kirani"
mujahid yace-:
"Na problem" bani wayarki in sa maki (number) din
kiyi (saving)
ta mika masa wayarta ya shigar mata da lambar"
kana ya dawo mata da ita tasa sunan shi"
"mun gode mujahid"
xabba'u tace dashi"
yayi murmushi"
"nice da godiya"
.
.
Tace-:
"Bari mu xo mu tafi" kada mu tsare ka kana aiki"
suka tashi a lokaci guda" mujahid yadan tako
masu har xuwa bakin kopar ficewa daga bankin ya
sake yi musu godiya ya koma" su kuma suka fita"
Daga bakin su harabar bankin xabba'u ta kama
hannun Asma'u cikin jin dadi"
Asma'u taki da dama" ya xakiyi da (accnt) dinki da
kike ajiya?" gashi kuma kin sake bude wani a
dalilin wannan makircin da xamu shiryawa fatima?"
.
.
Asma'u tace da ita-:
"wannan mai sauki ne" da mun gama" komae ya
xama (normal)" Idan mujahid ya dawo hannunmu"
xan cire kudina" kada ki damu" yanxu saura
matsala daya ce nake so in magance ta" bari in
kira wani gaye idan har na sameshi to ina jinnan
da sati daya mujahid xai dawo wajenki ba fatima
ba"
xabba'u ta tambayeta cikin mamaki"
"wanene xaki kira" kuma me xai mana?"
.
.
"wanene xaki kira?" kuma me xaiyi mana?"
Asma'u tace da ita-:
"wata kawata yake so" kuma ni nasa take share shi
saboda gayen bai hadu ba" yana kira na yana
kamun kafa a wajena domin in shawo masa kanta
ta daina wulakanta shi" xamuyu yarjejeniya ne"
idan xaiyi mana wani aiki" xance ni kuma xan
shawo masa kan Atine ta soshi"
:
Asma'u ta ciro wayarta ta nemo lambar saurayin
mai suna dalladi" ta kira shi" tasa wayar a kunne
suna tafiya" xabba'u tabi ta da kallo tace da ita ba
komae" lokacin da wayar ta shiga ne Asma'u tace"
"yauwa na sameshi" tana (ringing)
Dalladi ya dauki wayar" yayi saurin cewa"
"hello ranki ya dade" barka da safiya"
Akwai alamar murna a muryarsa don kuwa tunda
Asma'u take bata taba kiransa ba"
tace dashi cikin kasaita"
"saurara kaji dalladi" ka gane ko ina sone xaka yi
mana wani dan karamin aiki" amma a madadin shi
idan kayi mana yadda muke so" xan hadaka da
atine" baxata sake yi maka wulakanci ba"
.
.
Danlladi yace cikin xumudi"
"fada mani Asma'u wallahi xanyi ko menene !
Tace a sanyaye-;
""ka xo ka same ni a gida anjima da yamma" xanyi
maka bayanin yadda abin yake" wata yarinya ce
muke so ka wulakanta" sunanta fatima kana jin
xaka iya?"
Dalladi yace-:
"Ba matsala xan iya" xanxo anjiman"
"sai kaxo!
Asma'u ta kashe wayarta a lokacin da saurayin
yake kokarin sake cewa sai anjima" ta dubi xabba'u
dake sauraron tace da ita"
"An gama" Anjima xaixo ya sameni" ki kirani da
daddare xaki ji abinda mukayi dashi"
Xabba'u ta sake kankame hannun kawarta Asma'u
a bakin titin" sukayi dariya tare! Motoci da babura
suna wuce su" amma babu wanda yasan abinda
suke yiwa dariya"
.
======>*****¤*****<========
.
ßayan kwana biyu Asma'u ta koma bankin ita
kadai" ta samu mujahid yana aiki" amma da yake
da saoe taje babu mutane sosae a lokacin" suka
gaisa cikin raha" ya tambayeta" baki xo tare da
xabba'u ba yau kuma?"
tace dashi-:
ßan biyo ta wajenta ba ne saboda ina sauri ne"
daga nan ma ina so ne xanje wani wuri kuma acan
xan wuni sai da yamma xan dawo"
.
.
Mujahid yace-:
"Ai jiya naje gidan nasu wajen fatima" mancewa
nayi dana bata (accnt number) dinki ta baki"
Asma'u tace-:
"Ba wani abu" dama nace maka ka bari koda kaina
xanxo in amsa""
mujahid ya bude jakarsa ya ciro mata karamar
takarda dake dauke da lambobi ya bata" yace-:
"Ga lambar akawun dinki" sai dai ba.a yi maki
(cheque book) din ba" sai nan da kwana uku" sai
kixo ki amsa idan anyi (printing) kiyi hankuri"
Asma'u tace-:
"Ba komai mujahid" na gode sosae" sai xuwa
lokacin idan naxo"
Har xata tafi sai ta dan rage muryarta yadda
ragowar abokan aikinsa dake cikin bankin baxa su
ji ba tace dashi"
.
.
"Akwai wani abi da ya faru jiya da yamma wanda
gaskiya banji dadinsa ba mujahid" amma ba ina
so ne in gaya maka don ranka ya baci ba" ina so
ne kawai ka dauki (action) akan abun don kada
yaci gaba da faruwa"
mujahid ya dubeta cikin rashin sani-:
"kamar wane abu ne yake faruwa Asma'u!" ban
fahimci abinda kike fadi man ba"
Asma'u tace-;
"wasu samari ne suka xo wajen fatima" mun fito ni
da xabba'u xamu je gidanmu" to shine muka ji
tana hayaniya dasy kan wata magana"
Gaskiya banji dadi ba domin a yadda kake da
mutunci bai kamata ace tana tsayawa da irin
wadannan samarin a wajen budurwa daya ba" ya
kamata kayi bincike kasan me yake faruwa"
.
.
Mujahid yaji gabanshi ya fadi" ya dubi Asma'u
cikin xullumi"
"meya faru asma:u?" meya kawo su wajen fatima
kuma?"
Asma'u tace-;
"Baxai yiwu in fada maka abinda ya faru ba"
saboda akwai nauyi" Amma na san idan kana tare
da ita yau da kullum" kaima xaka ganewa
idanunka"
mujahid yaji jikinsa yayi sanyi sosai" bai san cewar
fatima tana da wani hali mara kyau ba" tunda ya
fara sonta" kuma babu wanda ya taba xuwa ya fada
mata irin wannan maganar game da ita sai a
wannan karon"
.
.
A karo na farko ya sake tambayar Asma'u-;
"me yake faruwa Asma'u!
Don Allah ki fada mani ke ba wacce xaki boye mun
wani abu bane"
Asma'u tace-;
"kayi hankuri mujahid" idan na fada maka wani abu
game da fatima" banyiwa kawata xabba'u adalci
ba"
kada ka mance xabba'u kawata ce kuma fatima
'yar uwarta ce ta jini" ita kanta baxata ji dadi ba"
idan ta san nina fada maka wannan maganar"
saboda baxata iya fada maka komai ba" Amma ina
so kayi bincike xaka san me yake faruwa""
mujahid yayi tagumi yayi shiru yana tunani"
Asma'u tace-:
Na gode xan tafi" sai naxo amsar (cheque book)
din".
.
.
Ta tafi tabar mujahid ya kasa motsawa" baima san
ta tafi ba" maganar ta bugi xuciyarsa nesa ba kusa
ba"
fatima itace yarinyar da yake so ya aura" amma
kuma yanxu Asma'u taxo masa da wata magana
mai ban tsoro" wacce ya kasa sanin kome yake
faruwa"
.
Da abokan aikinsa suka ga halin damuwar da ya
shiga cki cikin dan kankanin sai suka tambaye shi
ko lapia"" mujahid yace baya jin dadi ne"
A ranar ba.a tashi da shi ba" ya nemi ixni ya tashi
ya koma gida" xuciyarsa cike da xullumi da kuma
wasi-wasi"
.
.
Mujahid yana nan a kwance a daki" tunda ya dawo
da rana" yayi sallar axahar bai sake...........

¤TUN A DUNIYA¤
.
.
.
РÁĞE
11
WĨŤH
ÁßßÁŃ ßÁŚМÁŔH
ĎÁŃ
МÚŤÁŃ YŐßE"
.
.
MUJAHID yana kwance a daki" tunda ya dawo da
rana yayi sallar axahar bai sake fitowa daga cikin
dakinsa dake gidansu ba"
Da yake kanwarsa Umma tasan wannan ba
halayyarsa bace" idan ba rashin lafiya ba dole ne
ya shigo cikin gida dakin mahaifiyarsu su xauna
suyi hira" duk lokacin da ya dawo daga wajen aiki"
Don haka sai ta shiga dakinsa take kusa da xaure
ta sameshi a kwance yana tunani" tayi masa sannu
da dawowa sannan ta tambaye shi"
.
.
"yaya mujahid me yake damunka ne ka kwanta
yanxu da rana haka" ko baka da lafiya ne?"
mujahid ya daga kansa yace-:
"lafiya lau" wani aiki mukayi ne yau wanda ya caxa
mun kai" shine nake hutawa"
Umma tace-:
"Na ga baka shigo cikin gida bane" shiyasa dama
nace bari inxo in gani ko lafiya"
"Ba komai Umma" xan shigo idan na gama
hutawa"
Umma xata fita kenan daga dakin sai mujahid ya
tsayar da ita"
.
.
Umma xo mana-;
Umma ta dawo ta xauna akan kujerar da yake
karatu a kwanta wacce ke gaban teburin
littatafansa" mujahid ya tashi xaune ya tattara
hankalinsa wuri guda yace da eta-:
tuntuni nake so muyi wata magana dake ban samu
lokaci bane!
Umma tayi shiru tana sauraren yayanta" yaci gaba
da cewa-:
"Kinsan tunda Allah ya hadani da wannan kawa
taki fatima bamu taba xama ni dake mukayi
magana akan halayenta ko dabi'unta ba" shin kina
da cikakken sanin halayenta ko kuwa dai kuna
kawance ne amma baki san halayenta ko wasu
daga cikin dabi'unta ba?"
.
.
Umma tayi mamakin tambayar da mujahid yayi
mata" tace dashi-:
"yaya mujahid" bani ba aiko kai xaka iya bayar da
shaida

Please Login or Register in order to submit comment