Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
6 / 9
fada masa" yace-: "xanxo anjima" . ======>+++++¤+++++<======= : Tun lokacin da soyayyar fatima da mujahid ta rushe" Umma da fatima basu sake haduwa ba" domin kuwa a gidansu fatima mahaifiyarta Hajiya binta tasa mata dokar sake xuwa gidansu Umma" kamar yadda ita ma Umma yayanta mujahid yasa mata dokar kada ya sake ganinta tare da fatima" Amma kuma kullum sai sunyi magana a waya sau daya" idan daya ta kira daya" suna kuka suke magana" Fatima ta tabbatarwa Umma cewa wannan shiri ne wasu axxalumae suka shirya mata" saboda su cimma manufarsu" amma xataci gaba da yin addu.a akan Allay ya tona asirin koma su wanene!" . . Umma tayi mata alkawarin xata taya ta addu"a kuma tana kara karpapa mata gwiwar cewa mujahid xai dawo ya gane gaskiya" xaixo ya nemi afuwarta" karta damu" to amma duk da haka fatima wuni tayi cikin tunani da xullumi" ta rame kamar wacce ta dade tana rashin lafiya" idan tana cikin daki ita kadai bata aikin komai sai tagumi" ko kuma ta kurawa hoton mujahid ido daga inda take xaune" . . Tana matukar son mujahid" saboda shine saurayi na farko a rayuwarta wanda tayi alkawarin xata aure shi su xauna tare" Idan mujahid bai dawo ya tallafi rayuwarta ba" tasan da wahala ta sake amincewa ta karbi soyayyar wani da namiji a lokaci na gaba" . ======>+++++¤++++<======== . Da mujahid yaje gidansu Asma'u ya sami xabba'u saita fito suka shiga cikin motarsa suka xauna a gaba suka fara hira" xabba'u tace dashi-: "Akwai dalilin da yasa kaga Asma'u taci fama dani ban amince da soyayyarka ba" mujahid kasan halin mutane da surutun tsiya" yanxu idan akaji ka dawo wajena muna soyayya sai a dauka kamar nice na raba ku" ni kuma ba abinda ya shape ni" ban san abinda ya hada ku ba ma sai daga baya" Dama kuma kae ne baka sani ba tun farko" amma layinmu kowa yasan tana irin wannan tanbadewar" sai karti suxo su dauke ta a babur su tafi fati" nayi nayi da Hajiya ta tsawatar mata" amma tayi biris da al'amarin ka gani?" shiyasa kowa ya xuba mata idanu (to hell with her)" . . Mujahid yace-: "Na san da wannan matsalar xabba'u amma kada wannan ya dame ki" nina san yadda xan bullo wa al'amarin" aure dai tsakanin ni da ke ba gudu ba ja da baya" duk wanda xaiyi magana sai yayi tayi" kada ki damu" xabba-u tace-: "Duk da haka akwai abinda ya kamata kayi" saboda mu tsallake surutun mutane mujahid" Ina so ka fara fada anan gidanku cewar a dalilin matsalar da ka samu da fatima yasa ka yanke shawarar dawowa wajena" su kuma yakamata yayi suxo su sami Hajiya" suyi mata bayanin abinda ka xartar" nasan Hajiya baxata ki ba" saboda tana so na" Amma idan ba haka kayi ba" soyayyarmu baxata yiwu ba gaskiya mujahid" . . Ya tabbatar mata" "xanyi haka xabba'u xan samu mama muyi maganar da ita gobe da sape" xan nuna mata fa'idar yin hakan" ita kuma sai taxo ta sami hajiya suyi maganar" haka kikso ko?" Xabba'u tayi dariya" "Haka nake so" sai kayi haka sanna soyayyarmu xata xauna daram" amma yanxu muna (under probability) ne!" "ki kwanta da hankalinki" komae xaixo yadda muke so" Kafin dare yayi nisa ne xabba'u tace xata tafi gida don kada Alhaji yadawo ya samu bata gida" yayi mata fada" mujahid yaso yakai ta a motarsa" . . Xabba'u tace-: "A,a mujahid ba yanxu ba tukunna" ka bari sai komae ya daidaita" yace da ita-: "kin cika tsoro xabba'u tace-: "ba haka bane" akwai dai dalilin da yasa nace ka bari din ne sai nan gaba" suka rabu cikin farin ciki da alkawarin gobe da yamma xaixo gidansu Asma'u su sake haduwa idan ya dawo daga gurin aiki" . =====>+++++¤+++++<======== . Lokacin da mujahid ya sami mama rakiya a washe gari ya sanar da ita abinda ya yanke" da kuma dalilin da yasa yayi haka" ta dade tana jinjina maganar kafin ta amince tace-: "mujahid akwai matsala a wannan maganar da kaxo da ita" kaga fatima 'yar Hajiya binta ce" ita kuma xabba'u kanwarta ce" yin hakan xai iya janyo musu fadan dangi" idan ba.a yi taka tsan-tsan ba" mujahid yace-: "Idan akayi musu bayani cikin fahimta" xasu fahimci dalilin hakan" ni bana so ne mu yanke xumuncin dake tsakanin ku da su" da fatima da xabba'u duk daya ne a wajen Hajiya binta" xata fahimci bayaninki fiye da kowa idan kikaje mama" . . Mama rakiya tace-: "to baxance baxan je ba tunda ka nace kana son xabba'u amma banyi maka alkawarin xa.a samu nasara ba a dalilin xuwana" mujahid yace-: "Duk da haka dai ki gwada xuwa mu gani mama" nina san baxa a samu matsaka ba" mama rakiya tace-: "xan fadawa babanka idan ya shigo" idan ya amince xanje mu sasanta" in fada musu bukatarmu" . . MUJAHID yayi mata godiya" ya tashi ya tapi" da shigowar malam Abdullahi" mama rakiya taje dakinsa ta sameshi da maganar" shi kanshi da farko bai amince ba" yace-: "kai akwai kuruciya a maganar nan" ta yaya xaice baya son fatima kuma yanxu ya koma gidan yace yana son kanwar innarta" duk da yake yace laepinta ne" idan akayi mata haka ai anyi mata rashin adalci" mama rakiya tace-: "shi kuma a ganinsa wai yin hakan shixae sa mu sasanta gabakidaya dasu komai ya wuce" Malam Abdullahi yace-: "to kije in kinga xaki iya xuwa din" amma jikin bai bani cewa yin hakan shine abinda ya dace ayi ba Rakiya" su ma a bangarensu anan suka daddale cewa" mama rakiya xataje gidansu fatima ta samu hajiya binta ta fada mata sabuwar maganar da taxo da ita daga wajen dansu mujahid" . =======>+++++¤++++<======= . A ranar kuwa taje" da shigarta gidan tayi sallam" yara suka amsa mata" a lokacin Hajiya tana cikin daki" Da fatima taji muryar mama rakiya a gidan sai tayi wuf ta fito daga cikin daki tana mamakin dalilin xuwanta" fatima tana sa rai mama Rakiya taxo ne domin ta nema afuwar abinda ya faru" a sasanta tsakaninta da mujahid ya dawo suci gaba da soyayya" fatima tayiwa mama Rakiya sannu da xuwa sannan ta durkusa ta gaeshe ta" ta amsa sama-sama ta nufi dakin Hajiya binta" ita kuma fatima ta koma dakinsu tana farin ciki" domin kuwa tana saran mujahid ya kosa dawowa wajenta" . . Mama Rakiya tayi sallama ta shiga dakin Hajiya binta" ta sameta tana goge fuskar tibi da tawul" Hajiya binta ta amsa mata sallamar sannan ta dawo da hankalinta wajen bakuwarta wacce tayi mamakin ganinta a gidansu" "sannu da xuwa" mama Rakiya ta amsa: "yauwa sannu Hajiya" suka xauna tare akan doguwar kujera daya" "kece da rana haka Rakiya!" mama Rakiya tace-: "Nice Hajiya" tun daxu naso xuwa da hantsi" sai kuma nima nayi bakuwa" ita ta tsayar dani" Hajiya tace-: "Allah sarki" suka gaisa' "Ina wuni?" "lafiya kalai" "lafiya, ya yara?" "madallah" Daga nan suka yi shiru" Hajiya binta ta kasa kunne tahi abinda ke tafe da mama Rakiya" bauan sabanin da ya faru tsakanin mujahid da fatima" . . Mama Rakiya tace-: "to Hajiya abubuwa dai sunyi ta faruwa a tsakanin yara" amma bamu shigo munsa baki ba" tunda rashin jituwar data faruwa a tsakanin fatima da mujahid" wanda a gaskiya bamuji dadin abin ba" nayi kokarin inji yadda abin ya paru domin na sasanta su" amma abin yaci tura" nidai na rasa mafarin wannan batawa da sukayi a cikin dan lokaci kankani" Hajiya binta tayi murmushi tace-: "Rakiya kenan" wato a xakirin gaskiya idan nace maki daidai da sakan daya ranmu ya baci akan wannan al'amari da ya faru nayi maki karya" saboda a xahiri fatima tun farko ba aure ta saka a gabanta ba yanxu" karatu take so taci gaba dayi a (school of health) nice na takura mata nace baxataje ko'ina ba aure xa.ayi mata" har kuma dai cikin ikon Allah ta hadu da mujahid suka fara soyayya" to mu idan" to amma idan har akwai abinda ya bata mana rai fiye da komai" bai wuce kaxafin da akayiwa 'yarmu ba" . . Ran mahaifinta ya baci sosae akan wannan magana" domin har daukar maganar yaso yayi akai kotu" nice na lallashe shi na taushi xuciyarsa yayi hankuri" kinga gaku gakusa duk wannan ya paru ba" saboda haka mu a wajenmu magana tuntuni ta wuce" sai yaje ya samu wacce yake so" ita ma taje ta samu wanda take so" shinkenan!" mama Rakiya tace-: "mun san dole ne ran kowane bangare ya baci hajiya" amma mu dukanmu hankuri ya kamata muyi" mu sawa xuciyarmu dangana" mutunci ne ya hada tun ba yanxu ba" saboda haka bai kamata mubar wannan maganar ta rusa mana xaman mutuncin da mukeyi ba na shekara da shekaru" Don Allah muyi hankuri mu duka" . . Hajiya ßinta tace-: "Ba komae Rakiya" aina fada maki mu a wajenmu tuntuni mun saki wannan maganar" sai dai muyi fatan Allah ya kiyaye na gaba kuma" mama Rakiya tace-: "to sai dai kuma akwai wani hanxari ba gudu ba" mujahid ne ya sameni yace dani" shidai yana so ace xuri"a ta kullu tsakaninmu da ku Hajiya" kamar yadda tun farko akayi niyya ba mu" to yanxu ma baxamu cire rai ba" yace tunda basu daidaita tsakaninsu da fatima ba" yana neman ixinin a bashi xabba'u" Hajiya binta ta dago kai ta dubi mama Rakiya a kidime" "Xabba'u?" ta tambaye ta" "A ina mujahid yasan xabba'u shi kuwa?" mama Rakiya tace-: "to...... Can dai watakila suka hadu" kinsan sha.aninsu na yara" mutum ba sani yake ba" yadai nuna ita xabba'un din kamar itace sukafi daidaitawa" indai xa.a amince mana" to wannan karon baxa.a sake maimaita 'yar gidan jiya ba in Allah ya yarda" . . Hajiya binta tayi shiru tana tunanin" Abu na farko da ya fi tsaya mata a rai shine" a ina mujahid yasan xabba'u kuma har yaji yanxu eta yake so ba fatima ba?" Amsa daya ce kawai" dole ne akwai wani abu a boye da yake faruwa a gidan" wanda yanxu ne yake so ya baiyana" duk da haka bata nuna maganar ta tsimata ba" sai tace da mama Rakiya-:. . . "wannan".................¤TUN A DUNIYA¤ . . . ραgє 15 ωιтн Aßßαη ßαѕмαян Dαη мυтαη уσßє ωнтѕαρρ ριη +2348082035050 . . "Wannan ba wata matsala bace" idan ita xabba'un tace tana son shi" kuma shima yana sonta" ai babu damuwa" da ita da fatima ni a wajena duk daya ne! Dukkansu nina shayar dasu" dukkansu 'ya'yana ne" ba wani bambanci" idan xabba'un yaga xasu daidaita" toki ce masa yaxo" Allah ya bada sa.a mama Rakiya tace-: "mun gode fa Hajiya xanje in fadawa mahaifin mujahid" duk yadda mukayi" mun gode" . . Hajiya ßinta tace-: "ba komae mama Rakiya tayi sallama" ta tashi ta tafi" har kusan minti talatin Hajiya binta tana nan xaune bata motsa daga kan kujera ba" tana tunanin maganar da mama rakiya taxo ta fada mata ne" A karshe ta yanke hukuncin indai har mujahid yanason xabba'u kuma ita ma tana sonshi" to ko shakka babu" ba wani yayi makircin raba fatima da mujahid ba sai xabba'u . ======>+++++¤+++++<======= . Da Hajiya binta taga maganar babba ce" abun yafi karfinta sai tabar abun a ranta" bata yiwa xabba'u maganar ba" sai da ta bari Alhaji sunusi mahaifin fatima ya dawo sannan ta sameshi a dakinsa" ta xauna ta fede masa biri har jela" tace dashi a karshe" "Ina xargin akwai sa hannun xabba:u a cikin wannan matsalar da ta faru a tsakanin mujahid da fatima" domin kuwa idan babu sa hannunta" ta yaya mujahid yasan ta" kuma har yaji yana sonta a maimakon fatima" kuma yaya ita xabba'un xata amince ya wulakanta -yar uwarta ya dawo wajenta yace yana sonta" idan ba ita ce tun farko ta kulla wannan makircin ba?" . . Da Alhaji sunusi yaji yadda al'amarin yake sai ya fara bambamin fada" "A gidan nan wannan shaidancin xai faru Hajiya" Ni xa.a dauka karamin mutum?" Ina gidan amma axo min da wannan sakarcin?" Ya daka mata tsawa" "Ina xabba'un take?" kirawon mun ita" Hajiya binta tace dashi" "kai halinka kenanAlhaji" baka bin abu cikin nutsuwa idan ya paru" yanxu ita xabba'u bata san mun san da wannan maganar ba" bata san rakiya taxo ta fadamun komae ba" kamata yayi mu jira mu gani" mujahid din xai iya xuwa nan gidan ya aika a kira masa xabba'u?" kuma idan ya kirata" xata je" ko kuwa baxata je ba?" . . Alhaji sunusi yace a fusace-: "wacece xa,a tsaya jiranta a gani" nace ki kirawo min ita yanxun nan in tambayeta" tsoronta kike jine wai ko kuwa?" Hajiya binta ta tashi cikin sauri" "Allah ya huci xuciyarka" bari inje in kira ta" ta fice daga dakin taje dakinsu xabba'u ta kirawo ta" kafin ta dawo ne Alhaji sunusi yaci gaba da bambami" "Har akwai wani takadarin da xai taso anan gidan yayi min iya shege irin wannan in xura masa idanu ban yi kasa-kasa dashi ba?" Hajiya binta ta shigo tare da xabba'u tun kafin ta durkusa ya fara mata tsawa" "ke xabba'u menene ke tsakaninsu da wannan yaron da yake son fatima?" Ya dubi Hajiya binta data tsaya a gepe guda" "Bani sunansa" ta ce "mujahid" Alhaji sununsi ya koma kan xabba'u" "wannan yaron mujahid da yake xuwa wajen fatima meya hadaki dashi?" xabba:u tayi sasarai a tsaye" ta fara inda-inda" alamar tsoro da rahin gaskiya ya cika fuskarta" "ke baki ji abinda na tambaye bane' iye?" . . Xabba'u ta fara in-ina tana cewa-: "A,a dama... Eh.... Niba komae tsakanina dashi" Alhaji" Alhaji sunusi yace da ita-: "ke kada ki mayar damu kananan yara kinji ko?" ya aiko ne yace yana sonki" yanx ke yake so ba fatima ba" mu mun amince" muna sone muji shin kema kin amince a fada musu" ko kuwa baki sonshi" abashi hankuri yaje ya nemi wata?" suka xubawa xabba'u idanu" taci gaba da kame- kame ta rasa abunda xata ce" a karshe ta dubi hajiya binta tace" "xan fadawa Hajiya ko menene" . . Alhaji sunusi yayi mata dakuwa" saura kadan ya sa kapa ya mauje ta" "Ni xaki ba amsa don gidanku" nina tambayeki" ba Hajiya ba" kina sonshi" ko kuwa baki sonsHi?" xabba'u tace a tsorace' "Ina son shi" Hajua binta ta dafe kanta" Alhaji sunusi ya nuna mata yace yace-; "munafuka" annamimiyar banxa" kece kika kullawa fatima makirci" kika rabata da yaron nan" suna xamansu lafiya" muna xaton wuta a makera sai gashi ta taso a masaka" yanxke ke saboda baki da mutunci" fatima ce xaki jepa ta cikin masifa" kisa ayi mata sharri da kaxapi a bata mata suna" Ashe baki da mutunci xabba'u?" . . Alhaji sunusi ya kasa hankuri" yakai hannu a fusace ya tsinke ta da mari" saida ta fadi kasa" xabba-u ta fashe da kuka" kafin Alhaji sunusi ya sake yin sufa ya fira kanta" Hajiya binta ta shiga tsakani" ta durkusa har kasa tana yi masa magiya" "kayi hankuri Alhaji" ni xaka yiwa" ba ita xaka yiwa ba" ka rupa min asiri ka kyaleta" . . Alhaji sunusi yace-: "In banda rashin mutunci" yarinyar nan fa a tsumma tana jaririya muka dauko" wacce wahalar duniya ce bamu sha a kanta ba" wanne asibiti ne a garin nan bamu je ba" a dalilin rashin lafiyarta" Amma yanxu ta rasa wanda xata cuta sai mu da xuriyarmu?" . . "YA ture Hajiya ßinta ya sake haure xabba'u ya cillar da ita ta hadu da bango" ta sake yin kururuwa tana birgima a kasa" Hajiya binta ta sake tasowa ta shiga tsakaninsu" ta tare Alhaji sunusi wanda bai taba yin fushi irin wannan ba" tunda suke da Hajiya binta" Xabba'u ta tashi ta ruga a guje ta nufi dakinsu tana cewa" "xan bar muku gidanku" don anga ni marainiya ce ba 'yar gidan ba" shiyasa ake nuna mun bambanci" . . Ta shiga dakin tana kuka" fatima wacce tayi tsaye tana sauraron abun da yake faruwa ta ba xabba'u hanya" wacce ta kusa tureta" xabba'u ta dauko akwatinta ta bude" ta fara debe kayanta tana kimsawa" tana kusa" data gama xubawa ne sai ta dauko gyalenta" ta warware ta yapa" ta jawo akwatin ta fito waje" Fatima ta tsare kopar ita ma tana kuka" "Ina xaki je xabba'u?" ta bata amsa" "Gidanmu xan koma" wajen mahaifina" na godewa Allah da ya kawo ranar barina gidan nan tun mhaifina yana raye" . . Fatima tace-: "Xabba'u naji duk abinda yake faruwa" in dai don mujahid xaki bar gidan nan" ki koma da kayanki cikin daki" na bar maki shi" tun farko da kin fada min kina sonshi" dana bar maki shi cikin ruwan sanyi" ba tare da kowa ya sani ba" Xabba'u ta ture ta ta wuce waje tana kuka" "Ba wani abinda xaka fada min bana son sake xama a nan gidan" A dalilinki mahaifinki ya bugeni" saboda kece 'yarsa ni ba 'yarsa bace" kuje ga gidanku nan" har abada bani ba ku" ta nufi kofar gida" ta dauki akwatin ta dora akanta" taci gaba da kuka" fatima ta ruga dakin mahaifinta tace da Hajiya binta" . . Mama" ga xabba'u can ta kwashe kayanta ta tafi gida" na hanata tafiya amma ta ki" Hajiya binta xata fita kenan" sai Alhaji sunusi ya dakatar da ita" "Idan kika bita saina saba maki anan gidan" rabu da ita" duk inda xataje tayi ta tafiya" Hajiya binta ta fara kuka tace-: "Alhaji kasan halin xabba'u yanxu idan taje ta cewa baba mun koreta" ban san halin da xai shiga ba" nayi masa alkawarin xan rike xabba'u xanyi mata abinda take so daga nan har karshen rayuwarta" . . Alhaji sunusi yace- "to ba.a nan gidan ba" daga yau babu ni babu waccan yarinyar" (MUN DAUKO WA KANMU KADDARA DA MASIFA)" Xabba'u ta tafi gidansu da akwatin kayanta" xata fadawa babansu malam Aßußakar an korata daga gidan" wata sabuwar rigimar xata taso kenan! . . ======>+++++¤+++++<======= . . A bangaren danladi saurayin da Asma'u suka sa yaje yayiwa fatima kaxapi a gaban mujahid kuwa sau biyu yana xuwa wajen Atine amma babu labari mai dadi" xuwansa na farko da yayi" bayan ya kammala yiwa Asma'un aikin da ta sashi" kuma bayan ta tabbatar masa cewa tayi magana da Atine babu matsala" da ya aika gidansu Atine cewa a fada mata ana kiranta" sai ta ce da yaron" "kaje kace wanene?" Da yaron ya dawo ya fadawa danladi haka" sai yace" kaje ka fada mata" Danladinta ne" tayi sauri ina jiranta" yaron ya koma cikin gidan" da ya fitocsai yace da Danladi" "wai tace kanta yana ciwo" ka tafi" Danladi ya ciji yatsa" ya gaji da tsayuwarsa ya tafi" . . Ya kira Asma'u a waya yace da ita" yaje wajen atine amma taki fitowa" Asma'u ta bashi hankuri" "Xan sake xuwa in sameta gobe" kayi hankuri danladi" xan cika maka alkawarinka" ka koma xuwa jibi xata fito" Da jibin tayi ne sai danladi ya koma gidansu Atine" ya aika yaro yace taxo inji danladi" Da yaron ya fito ne sai yace dashi" "wai dani da danladin sai taci ubanmu" idan ban tafi na bata guri ba" Danladi ya tambayi yarin cikin kunan rai" "la tabbata haka ta fada maka" yaro bafa nason karya" yaron yace mana!" . . Danladi ya girgixa kai cikin pushi" yake-: "jeka yaro na gode" ya ciro wayarsa ya kira Asma'u" data dauka sai yace da ita cikin baraxana" "kince in dawo" na sake xuwa yau ma ta wulakantani" tunda abin naku wulakanci ne" nina fiku rashin mutunci" kinsan baxaki iya shawo min kanta ba" amma kika sani aiki naje nayi maki?" Asma'u ta rude" "kayi hankuri danladi" naje na sameta" kuma tace dani ba matsala fa...." Danladi yace-: "Ba wani dadin baki da xaki yimun" kawai tunda abun rashin mutunci ne xanje in bata aikin da nayi maki" xanje gidansu fatima ince ke kika sani inxo in mata sharri" kuma xanje in samu wannan saurayin fatima shima xan fada masa gaskiya" ke kika turo ni inyi wa fatima sharri" . . Asma'u ta rude" ta fara yiwa Danladi magiya" "Dan Allah kayi hankuri danladi" ka sake bani kwana daya" xan shawo maka kan Atine" xata fahimce ni yanxu idan na koma" kayi hankuri" Danladi yace-: "Na baki nan da gobe" idan na sake xuwa gidansu Atine tayi mani wulakanci" duk abunda kikaji ya biyo baya" to kece kika jawo" Ya kashe wayar" a lokacin da Asma:u take yi masa magiya yayi hankuri" tana kiran sunansa a tsorace" "Danladi...... (please) Danladi" . =======>++++¤++++<======== . "Xabba'u ta shiga gidansu tana kuka dauke da akwatin kayanta" matan mahaifinta suka tarbe ta a tsorace" suna tsammanin mutuwa akayi a gidansu Hajiya" taxo ta fada musu" . . To amma kuma da suka ganta da akwati a kanta sai suka fara tsammanin wata.....¤TÛÑ Ä ÐÛÑIÝĤ . . . ραgє 16 ωιтн Aßßαη ßαѕмαян Dαη мυтαη уσßє ωнтѕαρρ ριη +2348082035050 . . TO amma kuma da suka ganta da akwati a kanta sai suka fara tsammanin wata matsalar ce dai ta faru" ba mutuwa akayi ba" "lafiya' me ya faru?" Abinda mama Hajara ta fara tambayarta kenan" kafin xabba'u ta fadi yadda akayi" tuni har mahaifinta ya fito daga cikin dakinsa rike da carbi a hannunsa" "xabba'u" ya kira sunanta" "me ya faru haka kikaxo kina kuka?" wani ne ya rasu ko kuwa?" Xabba'u ta saurara da kukan da takeyi" ta ajiye akwatinta a baranda inda dakunan matan mahaifinta biye suke" ta share hawayenta" tace da mahaifinta malam Aßußakar" . . Alhaji ne ya koreni daga gidan" wai tunda ba gidanmu bane" in kwashe kayana in bar masa gidansa" shine kuma ya hauni da duka har yaji mun rauni" ta sake fashewa da kuka" malam Aßußakar ya harxuka" nan take ya fara kwaratsi a tsakar gidan" Alhaji sununsin ne yayi maki wannan korar karen" yace ki taho gida" tunda ba gidan ubanki bane?" Xabba'u ta gyada kanta" "eh, shine" mama Hajara da mama ßalaraba suka fara salatu suna tafa hannuwansu cikin jimami" malam Aßußakar yace-: "Ni Alhaji sunusi xai ciwa mutunci ko?" idan ma wani laifi kika yi a gidan baxai xo ya sameni ya fada mun ba" shine ya koreki ko?" Malam Abubakar yaja dogon numpashi cikin pushi" . . Mama ßalaraba ta tambayi xabba'u-: "to ita Hajiya binta me tayi a kai?" tana kallonsa ya koreki bata ci komai ba?" xabba'u tace-: "tana kallon sa" malam Abubakar ya sake tasowa a fusace yace-: "Ai dole ne suyi haka" ni wanene da baxasu ci mutuncin 'yata ba" su koreta?" tunda sun ganni talaka ne" shiyasa sukayi haka ai" to xan gwada musu iyakarsu su dukansu daga shi Alhaji sunusin har ita bintan" sai naci mutuncinsu" . . A lokacin ne mama Hajara tasa baki a cikin maganar tace-: "A,a malam" a saurara tukunna" sai anyi bincike bai kamata da mutuncinka ka shiga wannan maganar ba yanxu" ka saurara tukunna muga abinda xai biyo baya" malam Abubakar ya dubi Hajara matarsa yace-: "Amma dai ai xabba'u ba karamar yarinya bace wacce xa.ace bata san abinda akayi mata ba" Idan basu koreta ba" xata kwaso kayanta ne tace sun koreta" ai ba cewa nayi dama batayi laipi ba" aje tayi laifin" amma inda abin ya konamun rae" suxo mana su fada mun suce baba kaji"- kaji" abinda xabba'u tayi kayi mata fada" mu batahin maganarmu" ai kunga xan kira ta inja mata kunne ta daina" to basuyi haka ba" sunce tabar musu gidansu" su gasu masu gida koh?" ita kuma marainiya 'yar talaka" mama ßalaraba ta tambayi xabba'u" "to laifin me kikayi a gidan har Alhajin ya koreki" yace ki dawo gida" . . Xabba'u tace-: "A kan wani saurayina ne mujahid" yace ni yake so" shine su kuma suke so su hadashi da fatima" yace kuma baya son fatima" ni yake so" akan haka ne Alhajin ya kamani da bugu ya koreni" Malam Abubakar ya girgixa kai cikin takaici" "watau akan saurayi xai koreki koh?" shi Alhajin da girmansa da mutuncinsa xai shiga cikin shirginku na yara" meya hadashi da saka kai cikin wata maganar saurayi" don yace yana sonki?" a takaice dai yanxu ya nuna 'yarsa yake so" ke kuma tunda ba 'yarsa bace shine ya kamaki da bugi?" mama balaraba tace-: "Gaskiya idan haka ne malam" Alhaji bai kyauta ba" kuma baiyi ampani da girmansa ba wajen yanke wannan hukuncin" aini na xata fatima da xabba'u duk daya ne a gurinsa" ba wani bambanci" Ashe abin ba haka yake ba" . . Mama Hajara tace dasu-: "Duk da haka dai ni bana so a dauki maganar da xapi malam" don Allah a saurara tukunna a jira sai hankali ya kwanta" sannan a bincika yadda maganar take" malam Abubakar ya dubi xabba'u wacce take share hawaye" "shikenan" dauki akwatin ki shiga daki" kuma ki daena kuka hakan nan" tunda kin dawo gida" Xabba'u ta dauki akwatin ta shiga dakin mama ßalaraba" wacce tabita a baya domin sake lallashinta" dama tasu tafi xuwa daya" . ====>++++++¤+++++<===== . "Da sape ko karyawa Hajiya binta batayi ba ta shirya ta nufi gidansu hankalinta a tashe" ko wanka bata tsaya yi ba" ta sa silifas" ta isa gidansu misalin karpe bakwai" a lokacin da su duk su mama Hajara suna cikin dakunansu tare da yara" Hajiya binta tayi sallama" ta doshi dakin mahaifinta wanda yake a bude" alamar yana ciki kenan" sa.ar da take kokarin yin sallama ta shiga dakin ne" mama ßalaraba" wacce ta fara jin muryarta" ta leko da kanta tayi mata sannu da xuwa" . . Hajiya binta ta shiga dakin mahaifinta ta same shi a xaune yayi shiru yana tunani" taji gabanta ya fadi domin kuwa da ganinsa haka tasan ransa a bace yake" kuma cikin fushi ya kwana" "Ya amsa sallamar da tayi a ciki" Hajiya binta ta durkusa ta gashe shi" "sannu baba' ina kwana?" yace a fusace" "lafiya" tace dashi-: "Baba dama naxo ne akan abinda ya faru jiya" nasan xabba'u taxo da daddare dauke da kayanta........." tun kafin takai karshe ya dago kansa yace mata" "eh ta xo" ko kuwa xataki xuwa ne" tunda kun koro ta saboda 'yarku?" kuna takamar gida naku ne" shiyasa kuka nuna mata bambanci a tsakaninta da 'yarku da kuke so" to ita ma yanxu ta dawo gidansu" . . HAJIYA ßINTA tayi bakin ciki ya tokare mata xuciyarta" tunda take mahaifinta bai taba yin fushi da ita irin haka ba" kuma bata taba ganin fushinsa a bayyane irin wannan lokaci ba" tace dashi a tausashe-: "ßaba wallahi komae yarinyar nan taxo ta fada maka karya take yi" kai kasan cewar babu yadda xa.ayi in bambanta fatima da xabba'u" kuma idan ma har ina nuna bambanci" to nafi kyautatawa xabba'u fiye da fatima" ita kanta fatima" tun suna yara" na nuna mata matsayin xabba'u kanwata ce" don haka fatima tana giramama ta" kuma ko wani abu ya hada su" fatima nake ba rashin gaskiya in goyi bayan xabba'u ba tare da nayi bincike ba" don in rike amanarta da kyau" kamar yadda nake yi tun tana jaririya" . . Mahaifinta yace-: "Ai duk nasan haka" ba sai kin tuna min dawainiyar da kika yi mata ba" Amma yanxu abunda ya taso ai magana ce ta saurayi ita xabba'un tace wani yaro take so" shima yana sonta" shine ke kuma ke da mijin nakin masu 'ya kuka ce lallai wannan yaro sai dai yaxo ya nemi fatima" ba xabba'u ba" akan haka Alhaji sunusi yahau ta da duka baji ba gani" jiyan nan data dawo sai da na nemo wani likita nan da yake da kyamis" ya auna ta ya duba lafiyarta" yana nan ya rubuto magunguna an sayo" ko duk wannan ma karyar take yi" Hajiya ßinta tace da mahaifinta-: "Haka ne baba" don duka hakika Alhaji ya bugeta" amma ko shi din ma ba wani duka ne da yakai yadda xata kwaso kayanta ta dawo gida ba" ba wanda yace ta dawo" kawai sai dai mukaji fatima tana cewa ga xabba'u can ta dauki akwatinta ta tafi tana kuka" . . Malam Abubakar yace-; "to ai dawowar da tayi tayi daidai" tunda har xai rika kamata yana duka" aini gara ta dawo gida" tunda bana kasa riketa bane" dama saboda maraici yasa tun tana jaririya na baki rikonta" tunda kuma yanxu kun gaji da xamanta" 'y'yanku kuke so" shinkenan kowa ya huta" ita ma sai ta xauna a gida" Hajiya binta ta roko mahaifinta cikin karaya kamar xatayi kuka" "Baba kayi hankuri" maganar nan ta wuce don Allah" kasa ta dauki kayanta mu koma gida" Malam Abubakar yace-: "Xabba'u baxata koma ba" yau da ace da wannan al'amari ya faru kunxo kun fada min na shiga maganar" baku dauki mataki da hannunku ba" to xan iya hakura" Amma tunda kuka yi gada-gadi" kuka dauki irin wannan matakin" to baxata koma ba" kuma shi

Chapter 6 of 9