Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
8 / 9
su ba?" nima xanyi alpahari ace wacce naje da ita tayi ankon an ganta" indai baxata sa kayan ba" sai tayi xamanta insan xuwanne bataxa yi ba" tafi karfina" mama rakiya tace-: "jepa mata su" taje tasa ku tafi" mujahid ya cilla mata kayan suka fadi a gabanta a cikin leda" Umma ta duka ta dauki ledar ta tafi dakinta a hankali" kamar kwai ya fashe mata a ciki" ta kai kusan minti goma sha biyar tana nuku'nuku bata fito ba" mujahid yace da ita" "kepa nake jira Umma" me kike yi ne dakin?" . . Umma ta daure dai a karshe ta fito sanye da kayan" kamar xata fashe da kuka" da kyar take iya tafiya" siket din ya dabaibaye ta" rigar kuwa kamar an bude lema" sai fifita takeyi da iska" mujaid yace da ita cikin gatse" "kai ankon kuwa yayi maki Umma" kamar dama kinsan ke xaki sa" kika dandansa wannan dan uban dinki hadadde" xoki nunawa mama ta gani" Umma ta rufe puskarta da hannu cikin kunya da pushi" ta taho a hankali" koda taxo bakin kopar mama Rakiya tana ganinta sai ta bude idanu ta daga hannuwa" "ke menene wannan kuwa?" me xan gani haka" mujahid ya dubi umma wacce ta kasa cewa komae" mama ta tambayi mujahid" "kai a ina kakai aka bata wannan leshin mai tsada haka mujahid" . . Mujahid yace da mama rakiya-: "ita ta dinka shi" jiya na bata dinkin leshin baki nan" ita ta mayar dashi haka" shiyasa don munafunci kikaji tace baxata sa ankon ba" tasan wulakancin da tayi mani" saboda taji nace xabba'u xan kaiwa kayan" da gangan tayi haka" tana sane" . . Mama rakiya ta rasa abinda xata ce" ta kalli umma cikin burgumin rigar" saita fashe da dariya" "wai ne ya kuke so kuyi dashi a................¤TUN A DUNIYA¤ . . . ραgє 20 ωιтн Aßßαη ßαѕмαян Dαη мυтαη уσßє ωнтѕαρρ ριη +2348082035050 . . Ta dade bata tashi ba bayab yaron ya tafi" a karshe ne saita tashi tasa hijabinta ta fita" ta tsaya a bakin kofar gidansu taki fita waje" da danladi yaga itace ta leko saiya karasa inda take" yayi mata sallama" Fatima ta amsa" Danladi yace da ita-: "ßaiwar Allah" nasan baxaki gane ni ba" Naxo ne in roke ki afuwa" ki yape mun a bisa laifin da nayi maki" nina san na xalunce ki kuma na cuci rayuwata" to amma nima sani akayi" A lokacin ne fatima ta gane ko wanene" shine saurayin da yaxo yayi mata kaxapi a lokacin da take hira da mujahid" wanda a dalilin haka ne soyayyarsu da mujahid yaxo karshe" ya komawa xabba'u" . . Fatima tace dashi-: "kaje ka nemi gaparar ubangiji" ni tuni dama na mance da abinda ya paru" da ace abinda ka fadi a kaina ya faru dani da gaske" shi xaisa in damu" to amma babu dalilin da xaisa in tashi hankalina" tunda nasan sharri kayi mun" shi kansa wanda ka fadi maganar dominsa da yana da tunani xai gane sharri kayi mun" tunda nake ban taba kusantar wani da namiji ba a rayuwata" Ita kanta soyayyar ma a kansa na fara yinta" Amma kaxo kayi mun kaxapi akan abunda banji ba" ban gani ba" Danladi yayi nadama kan maganar da ta fada masa" yace-; "kiyi yape mani fatima" wallahi sani akayi inxo inyi maki haka" wata yarinya ta sani mai suna Asma'u kawar xabba'u" su suka sani inxo inyi maki sharri" don ku samu sabani ke da saurayinki" Fatima tayi murmushi tace-; "to sunyi nasara" mun samu sabani" kuma mun rabu" Amma da akayi haka meya ragu a jikina?" Na daina rayuwa ne ko kuwa meya same ni?" su da suka yimun wannan sharrin na tabbata basu fini kwanciyar hankali ba yanxu" kuma ko baka fada mun ba" dama nasan sune suka turoka kayimun sharri" sun samu abunda suke so" wacce aka yi sharri saboda ita" tana can tana soyayya da mujahid" ni kuma ina nan ina rayuwata" sai me kuma?" . . Danladi ya tambayi fatima cike da mamaki" kina nufin xabba'u tana tare da mujahid" yanxu haka suna soyayya?" "mexai hana" dama ai don haka suka sa kaxo kayi mani kaxapin" Danladi ya ciji yatsa yace da fatima-: "Nasan abinda nayi maki ba abu ne mai kyau ba" kuma In Allah ya yarda daga kanki babu wani mutum da xan sake yiwa sharri a duniya" saboda ba abu bane mai kyau" Amma duk da haka nayi alkawarin sai naje na samu wannan mujahid din dana rabaki dashi" saina fada masa komai" kai harma da abunda bai sani ba a game da xabba'u da Asma'u" saina fada masa saina yi musu tonon silili fiye da yadda suka sani nayi maki" kuma saina raba soyayyarsu" . . Fatima ta roki danladi" "Ina so kayi musu afuwa" kuma kada kaje ka samu mujahid ka fada masa wannan maganar" bana so ka raba su" kamar yadda suka rabani da shi" nasan xabba'u tana son mujahid sosae" shiyasa har idanunta suka rufe tayi mani sharri ta rabani dashi" kuma abinda baka sani baxan sanar dakai yanxu shine-: xabba'u kanwar babat ce" uwa daya uba daya suke da mahaifiyata" kamar yadda batayi la'akari da alakar dake tsakanina da ita ba" ni xan duba xumuncin dake tsakaninmu" baxan taba barin wani abu dana san xai cuceta" ya cuceta ba" Don Allah kada ka daga wannan maganar" kayi hankuri" nima na yape mata" kaima ka yape mata" na yapewa kowa" mubar wannan maganar anan ta wuce" . . Danladi ya girgixa kai cikin nadama" bai san lokacin da hawaye suka xubo masa ba" Da ace tun farko yasan haka fatima take da tawakkali" da babu dalilin da xaisa yabi umarnin su Asma'u yaxo yayi mata sharri a game da saurayinta" Fatima ta koma cikin gida yabar danladi a tsaye yana nadamar abinda yayi mata" to amma duk da tace ita ta yape" komai ya wuce" Danladi yayi alkawarin saiya tonawa xabba'u da Asma'u asiri a wajen mujahid" . . =====>+++++ß+++++<======== . Danladi bai hankura ba saida ya gano inda mujahid yake aiki a banki" yaje ya same shi da yamma yana shirye-shiryen tashi" mujahid yayi tsammanin Danladi kwastoma ne yaxo xai amshi kudi" to amma sai yaji yace dashi" "yallabai wajenka fa naxo" "to lafiya ko?" Danladi yace-: "maganar bata sauri bace" idan baxaka damu ba" mu fita waje" mujahid yace-: "kaga yanxu muna shirye-shirye ne xamu tashi" idan baxaka damu ba" kayi jirana a waje" ka tsaya a bakin kopa" idan na fito sai inko ko menene ke tafe dakai" Danladi yace-: "xan jiraka a wajen sai ka fito" ya fita waje ya tsaya jiran mujahid" baiyi mamakin rashin ganeshi da mujahid yayi ba" don kuwa lokacin da yaje ya same shi tare da fatima suna hira" da daddare ne" baxai iya ganeshi ba yanxu" . . Danladi yakai kusan minti talatin yana jira kafin mujahid su gama aikin da suke yi a cikin bankin" bayan sun kammala ne ya fito da jakarsa a hannu ta xuba takardu" sai yaga danladi a xaune akan wani dutse yana jiranshi" yace dashi" . . "yauwa malam" to xo inji mana" DANLADI ya matsa wajen mujahid suka koma gepe suka juyawa titin baya" danladi yace da mujahid-: "Nasan baxaka ganeni ba yanxu Alhaji" Amma ina tunanin ai xaka iya tuno wani wanda yaxo ya same ka tare da fatima kuna hira" wanya ya tsare ta ta biya mashi kudinshi" da ya ce ya bata xata xo dakinsa" mujahid ya rage fara.ar da yakeyi da ya gane ko dawa yake tsaye" ya gane danladi shine katon da yaxo ya tsare fatima" wanda yace itace abokiyar holewarsa" danladi yaci gaba da fadawa mujahid-: . . "Lokaicn da naxo na sameka kana hira da fatima" na fada mata maganganun marasa dadi" wadanda na tabbatar sune suka bata maka rae har ka tsaneta" kuka samu sabani" har yanxu ina tabbatar maka shine" kaga wannan xuwan da nayi na samu fatima" wallahi ban taba ganinta ba sai wannan ranar" Mujahid ya kalli danladi cikin rikicewa da yaji ya fadi haka" "ban fahimci abunda kake so ka fada mun ba" malam me kake nufi da a ranar ka taba ganinta?" . . Danladi yace dashi" "Gaskiyar magana ba wani boye-boye sharri naxo nayi mata" kuma duk wannan maganar da kaji na fada da wannan kurarin da nakeyi mata" wallahi kaxapi ne" babu abinda ya taba hadani da fatima, ban santa ba" kai in takaice maka ko sunanta ma ban sani ba" a ranar aka fada mani sunanta" babu wani abu a tsakanina da ita"" mujahid yaji jikinsa yayi sanyi" kamar an cire masa rai" ya durkusa kasa ya ajiye karamar jakarsa ya dape kansa" Danladi ya sake ce masa-: . . "kuma ina so kasan ko su wanene suka sani naje nayiwa fatima wannan sharrin" to ba wasu bane" illa Asma'u da xabba'u" su suka kirani suka ce akwai wata yarinya sunanta fatima" suna so ne su rabata da masoyinta wanda xai aureta" suka fada mun abinda xance idan naxo" kaji dalilin xuwan da nayi na same ku na fadi wadannan maganganun" mujahid ya fara xubar da hawaye" domin kuwa maganganun da danladi ya fada masa kamar bulala ce mai hade da xapin wuta" Ashe dama fatima batayi laepin komae ba"?" mace ce kamila kamar yadda ya santa tun farko" mujahid ya tuno lokacin da xabba'u taxo tare da Asma'u suka gaishe shi dayaxo wajen fatima" suka ce suna so ya taimakesu" Asma'u xata bude akawut a bankin da yake aiki" da kuma maganar da Asma'u taxo ta fada masa a game da fatima" Abunda yasa ya amince" yayi la.akari ne da irin kusancin dake tsakaninsu da fatima" baxasu iya yi mata sharri ba" mujahid ya tuno irin maganganun cin mutuncin da ya fadawa fatima" Ashe bata da laifi" kaxapi su xabba'u sukayi mata" . . Danladi yace dashi-: "kuma a game da xabba'u inaso in fada maka" idan har kana tsammanin mutuniyar kirki ce" toka daina daga yanxu" da ita da Asma'u sun dade suna huldar banxa da maxa" idan ma wadanda suke bin samari daki ake nema" to sune" Fatima macece ta gari" amma xabba'u da Asma'u sune manyan bata-gari" kai ba wani boye-boye Alhaji" sau uku ana xubarwa da Asma'u ciki" idan ma baka sani ba" kuma duk abinda Asma'u takeyi to xabba'u ma tanayi" kawarta ce kut'da-kut halinsu daya" kuma ka tambaya kaji" xa.a fada maka" mujahid yaji ya tsani xabba'u fiye da kowacce mace a duniya" yaji tsohuwar soyayyar da yake yiwa fatima ta dawo sabuwa" ya share hawayen dake fuskarsa" yace da danladi-: . . "ka cuceni malam" ko kuma ince kun cuceni kai da su xabba'u" to amma tunda yanxu ka gane gaskiya" kaxo ka fada mani naka laifin nagode kuma na yafe maka" xanje in samu fatima in roketa ta yape mun" xan fada mata duk abinda ya paru" Danladi ya tambaye shi-: "to ita kuma xabba'un wanne hukunci ka yanke a kanta" mujahid yace-: "wannan kabarni da ita" xanyi maganinta ita da shaidaniyar kawar tata" Allah ya isa tsakanina da xabba'u da Asma'u" . . Mujahid ya sallami danladi yace ya yape masa kudin da ya bashi lokacin da ya biya wa fatima kudin da yayi mata kaxapi a kansu" yaje ya lallaba ya shiga motarsa da kyar ya iya tukawa yakai kansa gida" Da xuwansa ya fito ya shiga cikin gida ya kira Umma" ta fito daga daki" tunda ta hangi idanunsa sunyi ja kamar yayi kuka" ta fahimci wani abu ya faru" tayi sauri ta bishi suka nufi dakinsa dake a xaure" da xuwansa bayan ya xauna" Umma ta shigo dakin" ita ma ta xauna akan stool din karatunsa" sai yace da ita" . . "Ranar wanka ba.a boye cibi Umma" yau dai gaskiya ta bayyana" Ashe su xabba'u sharri sukayiwa fatima" ita da wata kawarta Asma'u Ashe sune suka kulla makircin da suka raba mu" daxu wannan mutumin da yaxo ya tsare fatima muna hira yaxo wajen aiki ya sameni" ya warware mun xare da abawa" su xabba'u sune suka sashi yaxo yayi mata wannan sharro a gabana don su raba mu" Umma ta daga hannu sama tace-: "Allah na gode maka daka nuna mun wannan ranar" ta kalli yayanta mujahid-: "yau Allah ya nufa ka gane gaskiya" yaya mujahid" dama kullum abinda nake addu'a kenan" . . Allah ya tonawa Axxalumae asiri don ka gane gaskiya" ni dama tuntuni nasan da sa hannun xabba'u a wannan makircin da aka yiwa fatima" domin a raba soyayyarku" . . Yaya mujahid sau nawa nake fada maka cewa xaiyi wuya fatima ta aikata abin da ake............. ¤TUN A DUNIYA¤ . . . ραgє 21 ωιтн Aßßαη ßαѕмαян Dαη мυтαη уσßє ωнтѕαρρ ριη +2348082035050 . . YAYA MUJAHID sau nawa nake fada maka cewa xaiyi wuya fatima ta aikata abinda kake xarginta dashi" sai dai idan sharri wasu sukayi mata" nasan fatima kamar yadda nasan kaina" amma kaki ka yarda da abinda nake fada maka yaya mujahid" "Xabba'u da kake ganinta" wannan yarinyar tafi annoba sharri" Hajiya ita ta dauke ta tun tana jaririya a tsumma" ta shayar da ita nono" ta riketa tana yi mata komai na rayuwa" Amma a karshe ka duba abinda ta saka mata dashi" yanxu maganar da mukeyi da kai" ta bata Hajiya da mahaifinsu" tayi mata sharri" ta bata Hajiya a wajen danginsu" tayaya xaka so irin wannan macen yaya mujahid?" menene xai baka sha.awa a wajen xabba'u wanda baxaka samu a wajen fatima ba?" . . Mujahid ya dukar da kansa yayi ajiyar xuciya" ya dade a haka bai dago kansa ba" xuwa can sai yace-: "Abin da ya faru ya riga ya faru" Umma kinsan ina son fatima" dama a sakamakon wannan matsalar da aka fada yasa muka samu sabani" to amma tunda yanxu na gane gaskiya" ina so in sameta in bata hankuri" in nemi afuwarta domin mu dawo kamar da" muci gaba da soyayya" kuma xanyi mata alkawarin (as long as we are 2gether) baxan sake maimaita irin kuskuren da ya paru a baya ba" Umma tace-: "(any way) fatima tayi fushi" amma duk da haka yana da kyau ka sameta din" kuma nima xanyi maka kokari wajen ganin na lallashe ta domin ku dawo kuyi (setting) din matsalolin da suka faru" . . Mujahid yace-: "Anjuma xanje gidansu da daddare" ina jin kunyar in sake hada ido da ita" amma ba yadda xanyi" xanje na roketa afuwa tayi hankuri" Umma ta karawa yaya mujahid karpin gwuiwar yin hakan" taje ta samu mama rakiya ta fada mata" duk abinda ya faru" mama rakiyat ta rike baki cikin kunya da nadamar abinda taji" musamman akan fatima" A ranar da xabba'u xatasha xagi a wajen mama rakiya" . =====>++++++ß+++++<======= . Kaddara dai ta riga fata" A ranar da wannan abu ya faru ne mujahid ya gane gaskiya" ita kuma fatima acan makarantarsu taron dalibai akayi" a sakamakon wata lakca da wasu kwararrun malaman lafiya sukaxo suka gabatar" da yake an ba dalibai damar mikewa suyi tambaya ko kuma fadar albarkacin bakinsu" fatima itama ta mike tayi tambaya a gaban malamansu da dalibai 'yan uwanta" A cikin manyan bakin da suka halarci taron" akwai wani farin mutum sanye da farin tabarau dan kimanin shekaru talatin da bakwai mai suna Dakta Usman"....... "tun lokacin da fatima ta mike ya ganta a lokacin da tayi tambaya yaji yana sonta" ya kosa ya samu dama yayi magana da daya daga cikin malamansu domin yaji ko wacece wannan yarinyar mai suna fatima" Da malamai suka fara ficewa ne bayan an kusa tashi daga taron" sai dakta Usman ya samu wani malami wanda kuma anyi sa.a shine (H.O.D) din sashen da fatima take karatu" kuma ya santa" . . Dakta Usman yace da malamin-: "yarinyar nan data mike tayi tambaya akan (Enviromental sanitation) wacece malam?" malam yace-: "Ok, fatima sunusi kake nufi?" a (department) dina take" "Dakta Usman yace-: "to malam ni banda dai kuma ace munyi girman kwabo ai da anyi mun magana da ita" domin gaskiya a yadda naga yarinyar sai naji ina sonta" Sukayi dariya" malam yace-; "Don wannan ba matsala" amma kasan da yake muna da sharrin mu.amala mai kyau a tsakanin malamai da dalibai" xansa a kirata sai inyi mata bayanin abin cikin mutunci" . . Amma idan bata amince ba ko anyi mata miji a gida" to dole ne fa sai kayi hankuri malam" tunda kasan sha.anin yaran" "A,a ai ba komai don wannan" aini ma ba xanso nayi abinda bai dace ba" ina sonta ne tsakani da Allah""" Malamin yasa wani dalibi ya kira fatima bayan an tashi daga taron" taxo cike da mamaki ko a wane dalili malamin yasa a kirata" data xo ne ta sameshi a xaune a ofis dinsa tare da dakta Usman" daya daga cikin manyan bakin da suka xo wajen taron a ranar" Fatima ta gashe su cikin ladabi suka amsa" malamin ya bata damar xaunawa a daya daga cikin kujeru biyu dake fuskantar teburinsa" bayan ta xauna ta tattara hankalinta kan dalilin kiran nata" yace da ita-: "fatima munsan xakiyi mamaki a dalilin kiranki da nasa akayi" to amma ba abin mamaki bane" idan kika auna yadda yaruwa take kasancewa" Ya nuna mata Dakta Usman da yake xaune a kusa dashi" wannan babban bakon namu da nake tare dashi a halin yanxu wato Dakta Usman" shine ya ganki kuma Allah cikin ikonsa sai yaji yana son kuyi wata magana " Don haka gaki gashi-: Dakta Usman ya gyara xama yace da fatima-: "to gaskiya fatima" duk da yake ni bako ne a wannan makaranta taku" naxo ne kawai domin wannan taro da aka gaiyace ni" to kuma sai naganki daxu a cikin dalibai" kuma naji kin kwanta mun arai sosae" shine na samu malam mukayi magana tace xaisa a kiraki" amma ina so ki fada mun gaskiya" karki takura kanta" idan kinsan anyi maki miji ko akwai alkawarin wani a kanki" to kiyiwa Allah ki fadamun gaskiya" ni xanyi hankuri nayi maki fatan alheri" . . FATIMA ta sunkuyar da kai cikin kunya tayi murmushi tace da mutumin" "Gaskiya babu alkawarin kowa a kaina a halin yanxu" sai dai kawai karatun da nake yi" kuma a wannan sharkarar na fara da sauran lokaci" baxanyi aure yanxu ba sai dai idan na gama karatuna xuwa nan gaba" Dakta Usman yace da ita-; "Duk wannan ba matsala bace fatima" xan amince kici gaba da karatunki bayan anyi aurenmu" kuma idan ma haka kike ji ba a nan kasar xamu xauna ba" ni ina aiki ne a kasar malaysia" na dawo gida ne hutun shekara" idan Har Allah ya tabbatar da wannan al"amari a tsakaninmu to can xamu koma kici gaba da karatun naki" . . Fatima tayi shiru tana tunani" malaminsu yace-: "Kiyi magana fatima" tun farko mun fada maki karki boye abinda ke ranki" me kika ce?" ki bashi amsa" kina jin kina sonshi ko kuwa akwai matsala?" ba wani boye boye a irin wannan maganar" fatima ta sake sunkuyar da kai tana jin kunya" "Allah ya tabbatar mana da alheri a cikin wannan al'amari" tace a sanyaye" malamin ya dubi dakta Usman sukayi murmushi da sukaji fatima ta amince" mutumin yace-: "to Alhamdulillahi" naji dadi da kika amince da wannan bukata tawa" koda yake na mance ban gabatar maki da kaina ba" Sunana Usman Aßduljalal" Ni haifaffen kaduna ne" amma kamar yadda na fada maki" yanxu ina kasar malaysia ne" acan nayi digirina harna samu aiki" kuma gaskiya na taba yin aure a shekaru shida da suka wuce" Allah yayiwa matata salima rasuwa a wajen haihuwa" to tun lokacin ban yi wani auren ba" sai yanxu da Allah yasa na hadu da wacce xata maye gurbinta" . . Fatima ta sake yin murmushi tace a karshe" "Allah ya jikanta" "Amin, na gode fatima" malamin su fatima yace-: "yanxu tunda kun daidaita kanku" kamata yayi mu samu mahaifinki yau" shima mu nemi ixininsa don muji ra'ayinsa akan maganar" tunda ba abu bane na wasa da xa.a xo a xauna ayi hira kawai a tashi" kina ji ba matsala muna iya xuwa anjima da daddare" mu same shi ko fatima?" tace-: eh ba matsala" kuna iya xuwa din ku same shi" suka yi mata godiya" suka tambayeta inda gidansu yake" ta kwatanta musu" Dakta Usman da fatima sukaji kamar sun dade tare cikin dan lokaci kankani" suka saba da juna" suka rabu da alkawarin xasu xo gidansu anjuma da daddare tare da malaminsu daga nan su gana da mahaifinta" . =====>++++++ß+++++<======= . Da fatima ta dawo gida ne da yamma bayan sun tashi daga makaranta" tana xuwa ta fadawa mahaifiyarta halin da ake ciki a tsakaninta da Dakta Usman" Hajiya binta tasan fatima tana da kunya da kawaici" indai taxo da xancen saurayi gida to ba shakka tana son shi" Hajiya tace da ita-: "to fatima idan shine mafi alheri a gareki" ba abinda xamuce sai dai muyi patan Allah ya tabbatar mana da al'amarin" kawai ni abinda nakeji naga baku dade tare ba" anya xaki san mutum rana daya ki yarda dashi fatima?" fatima tace da Hajiya-: "Nayi wannan tunanin mama" to amma da nayi la.akari da malaminmu shiya jagoranci maganar nan kuma kuma nasan shi mutumin kirki ne" idan akwai matsala baxai yarda ya shiga cikin maganar ba" baxai yarda ma a kirani ba" kawai da ganin haka sai nake ganin kamar mutumin shima bashi da matsala" tunda ba karamin mutum bane" . . Hajiya binta tace-: "Allah yasa Alheri ne" in babanki ya dawo anjima" sai na fada masa" idan sunxo kinga yasan da xuwansu kenan" Da Alhaji sunusi ya dawo ne bayan anyi sallar magriba" sai Hajiya binta ta sameshi a daki tayi masa bayanin maganar da fatima taxo da ita" sannan ta sanar dashi xuwan mutanen anjuma" Alhaji sunusi yace-: "In dai tana son shi kuma munyi bincike mun gane cewar mutum ne nagari" ai babu matsala" Idan Allah ya nupa shine mijin nata" ko'ina xai kaita su xauna ai aure ne yakai ta" don sun tafi kasar waje sun xauna" ai bata rabu da mu ba kenan" duk sanda dama ta samu suxo gida su koma" . . Anyi sallar Isha'i kenan" Dakta Usman da malaminsu fatima suka shigo layin da dankareriyar bakar (prado jeep) dinsa" wacce yake barinta a kaduna" baya hawa sai ya dawo gida hutu" suka yada motar a kopar gidan" suka fito suka sa akayi musu sallama da Alhaji sunusi" Ya fito ya tarbe su cikin mutunci" da suka gabatar da kansu yaji kosu wanene" sai yayi musu barka da xuwa" yace su jirashi ya bude falo" da shigarsu bayan sun xauna a kasa sai ya basu hannu ska gaisa" ya saurara don yaji maganar da ke tafe dasu" duk da yake dai dama an fada masa a cikin gida" . . Malamin su fatima shine ya gabatar da kansa da kuma Dakta Usman" sannan ya fada masa dalilin xuwansu" watau neman ixni da amincewa akan neman auren fatima da Dakta Usman yake yi" Bayan Alhaji sunusi ya gama sauraren su ne sai yace-: "to wannan maganace mai matukar muhimmanci" kuma da yake kun biyo hanyar da ta dace ku biyo" naji dadi" nidai abinda xance shine" nidai a bangarena na amince na kuma baku dama" yanxu ya rage tsakaninku da yarinyar" ku sake daidaita tsakaninku" sai muga kuma abinda Allah xaiyi" . . Sukayi masa godiya cikin girmamawa" ya tashi ya shiga cikin gid.........¤TUN A DUNIYA¤ . . . ραgє 22 ωιтн Aßßαη ßαѕмαян Dαη мυтαη уσßє ωнтѕαρρ ριη +2348082035050 . . •KAMMALAWA∆°°°°√™ (THE END) . Sukayi masa godiya cikin girmamawa ya tashi ya shiga cikin gida" yasa Hajiya ta tura fatima domin su sake xantawa" fatima ta shigo ta samesu ta gashesu" sannan ta xauna a gepe guda" suka sanar da ita amincewar da mahaifinta yayi" fatima ta nuna musu jin dadinta" Suna cikin maganar ne mujahid yaxo da motarsa" ya samu katuwar jeep din a kopar gidansu" yayi tsammanin mahaifintane yayi manyan baki" ya matsa da tasa motar gaba kadan sannan ya fior" yaga falo a bude don haka sai ya saurara tukunna ya tsaya a kopar gidan" . . Ba.a jima ba yaga fatima ta fito tare da mutanen sunsha suturu na alparma" ta raka su wajen jeep din tayi musu sallama" cikin parin ciki" mujahid yaji tsoro ya kamashi domin kuwa a yadda yaga fatima tare da wadannan hamshakan mutanen ya fahimci wajenta suka xo" kuma saboda matsayinsu ma har falo aka basu" a ciki sukayi xance da ita" ya jira suka shiga motar" Dakta Usman ya tuka sukayi ribas" sukayi kwana suka tafi" duk sannan fatima tana tsaye a kopar gidan tana kallon su" bata shiga gida ba" mujahid ya matsa inda take ya kira sunanta" "Fatima" ta juyo ta dubeshi" tayi mamaki da taga mujahid ne yau a kopar gidansu" tace dashi ba tare da wata damuwa ba" . . "Ah, yaya mujahid" yaushe kaxo?" yace da ita cikin kunya" "na dan jima anan" naga kinyi baki ne shine na jira suka tafi" ta gaeshe shi cikin ladabi" "ya umma dasu mama?" yace-: "suna nan lafiya" Umma tace in gaesheki" "Ina amsawa" bamuyi waya ba tun shekaranjiya" fatima ta tambayeshi" "lafiya naganka anan kopar gidanmu mujahid" baka san xabba'u ta koma gidansu ba ne?" mujahid yayi ajiyar xuciya" yace da fatima" "Don Allah ki daina yimun xancen wannan manafukar" Idan naji an fadi sunanta a gabana" sai inji kamar ana dukana" wannan yarinyar makira ce... Axxxaluma....." "Haba yaya mujahid" wannan wanne irin cin mutunci ne?" ya xaka xo har gida ka rika xagin 'yar uwata?" baka san yadda nake da ita bane?" kanwar mahaifiyata ce fa?" mujahid tace-: "Na sani" to amma abinda baki sani ba fatima" itace tayi makirci ta rabamu ni dake" Ashe wannan mutumin da yaxo yayi maki sharri" ita ta sashi" tare da wannan muguwar kawar tata" sune suka shirya wannan makircin" . . Fatima tace-: "Na dade da sanin haka" ai kaine baka sani ba sai yanxu" yaya mujahid" mujahid ya fara yi mata magiya" "kiyi hankuri fatima" nasan ranki ya baci a sakamakon irin maganganun da na fada maki" Don Allah ki yape mun" Naxone domin in nemi afuwarki" yanxu na gane duk duniyar nan babu wata mace wacce ta cancanta dani irinki" kinsan ina sonki fatima in banda wannan makircin da xabbba'u ta shirya a tsakanina dake" da har yanxun muna tare" kiyi hankuri ki yape mani" mu daidaita kamar da" Ina sonki fatima" . . Fatima tayi murmushi-: "yaya mujahid kenan" tace sannan tayi ajiyar xuciya" "to da parko dai kamar yadda ka roki inyi maka afuwa" nayi maka dama tuntuni" ban kullace ka a raena ba" kuma banyi fushi kamar yadda kake xato ba" babu dalilin da xai sa in damu akan abinda na tabbatar ba halina bane" kaine mutum na farko dana fara tsayawa dashi da sunan soyayya" duk wanda xaiyi mun adalci idan ka tambayeshi" nasan xai pada maka haka" Lokacin da wannan mutumin yaxo yayi mun kaxapi a gabanka" kai kanka ya cancanta ka gane sharri yayi mani" to amma nasan komai dadewa gaskiya taxa bayyana" gata kuma yau ta bayyana" tunda gashi kaxo da bakinka ka fada mun" ka gane sharri akayi mani" ba halina bane abinda kake xargina dashi" . . Mujahid yace da ita a karaye-: "to fatima yanxu yaya soyayyarmu...? Kinsan ina sonki" kuma ina burin ki xamo matata a duniya" fatima tace dashi kai tsaye" "Bakin alkalami ya riga ya bushe mujahid" domin kuwa ka ganewa idanunka da kaxo wannan mutumin da yaxo tare da malaminmu shixan aura" don kuwa sun riga sun nemi ixni a wajen mahaifina" kuma ya basu dama" ya amsa maganarsu" mujahid yaji kamar an kwada masa dutse akai" yaji kamar ya juwa xata kayar dashi kasa" bai san lokacin da ya durkusa a gabanta yanayi mata magiya ba" fatima ki ceci rayuwata" ki duba halin da xan shiga idan na rasaki a halin yanxu" kiyi hankuri ki amshi soyayyata" nayi maki alkawarin baxan sake maimaita abunda nayi maki ba" Idan baki amsheni ba yanxu" rayuwata xata shiga cikin garari fatima" ki tausaya mani" fatima taji hawaye ya xubo mata tace dashi-: . . "tun ran gini tun ran xane mujahid" na baka dama a lokacin da ban taba ba wani namiji ba" nasoka irin sonda ban taba yiwa wani namiji irinsa ba" nayi kuka a dalilin sonka" a lokacin da ban taba yin kuka saboda wani namiji ba" Na kasa bacci a dalilinka nayi wahala akan soyayyarka" a lokacin daka juyamun baya" don haka babu yadda xanyi in sake dafawa

Chapter 8 of 9