Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
3 / 9
ba" tun daxu yana gida saboda ke" fatima ta dubi Umma cikin rashin fatimta" Saboda nifa kika ce?Yaya mujahid ne xai xauna a gida saboda ni Umma?" Umma tace da ita" "wallahi fatima ba wasa nake yi maki ba" tun jiya dana fada masa xaki xo naga alamar yana so ku hadu" yau tun sape yana gida baije ko"ina ba" kuma saboda kawai yaji nace xaki xo ne" don har tambayata yayi baki xo ba" shine nace dashi xanxo gidanku in gani ko lafiya baki samu xuwa ba" . . Fatima ta bata ranta tace-: "xabba'u ta jawo mani wannan matsalar Umma" tun jiya fa na tambayi Hajiya ta barni" amma yarinyar nan tayi min bukulu tace da Hajiya wai bai kamata abar gidan ba kowa ba" sai Hajiya tace in xauna har su dawo tunda haka ne" bansan meyasa xabba'u take yi mun erin wannan rashin adalcin ba" Umma ta dafa fatima cikin tausayawa" "kiyi hankuri fatima" nasan rin xaman da kikeyi da xabba'u" to amma tunda 'yar uwarki ce ta jini babu yadda xakiyi" kada ki mance ita da Hajiya uwa daya uba daya suke" . . Fatima tace da Umma cikin fushi" To amma don tana matsayin kanwar Hajiya sai ta rika min......... TUN A DUNIYA" . . . РÁĞE 06 WĨŤH ÁßßÁŃ ßÁŚМÁŔH ĎÁŃ МÚŤÁŃ YŐßE" . . FATIMA tace da Umma cikin pushi- "to amma don tana matsayin kanwar Hajiya sai ta rika yimun haka?" na girme tafa" kanwata ce" amma idan kika ga irin abubuwan da take yimun a gidan nan ko kare baxae ci ba" saboda kawai tana takamar Hajiya ta bata dama" tace min in rika girmama ta saboda kanwarta ce" Fatima tayi kwafa cikin damuwa" Umma taci gaba da lallashinta" "kiyi hankuri fatima" watarana sai labari" xamanku da ita da wani lokaci ne" kema kinsan haka" . . Fatima tace-: "Gata da bala"in son maxa" kullum sai an kira ta waje hira" A dalilin haka yasa Hajiya tace wa baba ya aurar damu bana a huta" Ina so inci gaba da karatu amma ta jawo mun" Umma ta girgixa kai cikin tausayawa" tasann cewa babu shakka fatima tana cikin damuwa a dalilin xamanta da xabba'u wacce tafi ta matsayi a gidansu" Suna cikin hirrar ne sai xainab tayi sallama ta shigo dakina ta mikowa fatima (envelope) din" "Anti ga ambulan din" Fatima ta amsa" Umma tace da xainab" "zainab kenan" yau baki je islamiya bane?" xainab tace-" "Ai munyi huru" sai makon gobe xamu koma" . . Fatima tace-: "su ma sunyi hutu" wannan karon duk hutun makarantu yayi (clashing)" da boko da islamiya" tace da xainab wacce ke tsaye tana tu musu murmushi" Don Allah xainab jeki karashe sharar can" idan kin gama" ki shiga kicin ki ga idan ruwan nan ya tapasa" kixo ki fada min" "to anti" xainab ta fita tabar fatima da Umma" a lokacin ne fatima tace da umma-: "wai ke daxu naji kina fatin wata magana" mu dawo baya" nifa ban gane abinda kike so ki fadi mani ba a game da yaya mujahid" ni wacece da xai tsaya a gida saboda yaji ance xanxo?" abin ya daure min kai gaskiya........ . . Umma tayi murmushi" xuwa can ta nisa tace-: "Fatima kin san ance ranar wanka ba.a boye cibi" zan fada maki wata magana wacce abin mamaki ce" amma ta wani bangare ba abin mamaki ba ce fatima" Duk duniyar nan bani da wata aminiya kwatankwacinki" kamar yadda na tabbatar kema baki da aminya kwatankwacina" don jaka ina so xan fada maki wannan maganar" amma idan kinsan akwai matsala" ina rokon ki don Allah ki fito ki fada min gaskiya" kada ki boye mun abinda ke xuciyarki" Ina so mu fara yin wannan maganar mu biyu" mu kashe mu rufe ba wanda ya sani" . . Fatima ta tambayeta-: wacce magana ce Umma?" ni fa ban san inda kika dosa ba" ina sauraron ki ne kawai" Umma tace-: "maganar gaskiya fatima baxan boye maki ba" yaya mujahid sonki yake yi" Fatima ta dafe kirji a tsorace" "sO?" ta tambayi Umma" " kai umma ba gaskiya bane" me yaya mujahid xaiyi dani?" ai yafi ni aji" ya xa.ayi yace yana sona?" Umma ta tattara hankalinta waje guda tace da fatima" "Kada kiyi shakkar abinda na fada maki" ina da hujjoji masu yawa dana dogara dasu kafin in yanke wannan hukunci" yaya mujahid yana sonki" ina tsammanin tun ranar da kuka hadu kwanaki da kika xo gidanmu" ranar da muka kawo ki gida a mota" yaki fitowa ya fada maki ne saboda kunyar dake tsakaninku" yana jin kunyarki sosae" kamar yadda kike jin kunyarsa" . . Fatima tace-: "shine ke kuma baki da kunya" kika ce bari ke ki fasa kwai kowa ma yaji" Umma ta danyi dariya" "wanna ba maganar wasa bace fatima" tsayawa xakiyi mu fahimci juna" kin gadai akwai xumunci a tsakaninmu" wanda bai tsaya kanmu ba" ya shapi har iyayenmu" ina so ki dada mani gaskiya" kina jin kina son yaya mujahid" ko kuwa akwai matsala?" Ni idan kika fada min" kinga nasan yadda xanyi in bashi hankuri cikin hikima" in hana shi yaxo wajenki idan akwai matsala" don kada faruwar hakan ta jawo mana rudani a tsakanin gidanmu da gidanku" yanxu babu wanda yasan maganar nan daga ni sai ke menene ra.ayinki?" . . Fatima ta rike kai cikin kadauwa tace-: "Umma kinxo da babbar magana" nipa dauka nayi kamar wasa kike yi" yaya mujahid bashi ya fada miki da bakinsa cewar yana sona ba" bai kamata muyi wani abu ba" sai dai mu bari mana sai yaxo da kansa yace yana sonta tukunna" "Umma ta dan bata ranta" "haba fatima" nifa ba yarinya bace" A matsayina na mace baxan iya gane me namiji yake nufi ba idan yana son wani abu?" yaya mujahid bai fito ya sanar da ni baki-da-baki yana sonki ba" amma na tabbatar da hajan koki yarda ko kada ki yarda" . . Fatima tayi ajiyar xuciya tace-: "to amma ba abinda xance sai dai in godewa Allah idan har hakan ta tabbata" domin kuwa idan har abinda kika padi gaskiya ne" ni a ganina wannan abin farin ciki ne a garemu ni da ke" A sakamakon amintar dake tsakanina dake tun muna yara" kuma abin farin ciki ne ga iyayenmu" musamman saboda xumuncin da suke yi" kinga amintarmu baki daya xata kara habaka kenan" In dai Allah yasa hakan ta kasance" Umma tayi murmushin jin dadi tace-: "Naji dadin wannan bayani naki fatima" kuma dole inyi maki godiya a sakamakon amincewa da kikayi kina son dan'uwana kamar yadda na tabbatar shima yana sonki" na gode" Allah ya karo mana kaunar juna a amintaka har abada" . . Ta dafa fatima cikin farin ciki" wacce kunya ya hanta ta sake cewa wani abu" . . SUNA nan xaune a cikin dakin sukaji sallamar Hajiya da xabba'u sun shigo gidan" Fatima tace-: "Kinji su Hajiyar nan ma sun dawo" Fatima ta tashi domin taje ta yiwa Hajiya sannu da xuwa" a lokacin ne xabba'u ta shigo cikin dakin a gajiye" "sannunku da xuwa" fatima tace da ita" sannan ta fita xuwa dakin mahaifiyarta" xabba'u ta dubi Umma da ke xaune a kan gadonsu" Umma tayi mata sannu da xuwa" sannan ta tashi domin ta bata wuri" "Ya xaki tashi Umma?" kiyi xamanki mana" Umma tace da ita-: "Dama gida xan tafi yanxun nan" na dade anan gashi har yamma tayi" xabba'u tace-: "to baxaki jira kawar taki ta dawo kuyi sallama ba?" Umma tace-: "Xanje dakin Hajiya ne in same ta" sai anjima xabba'u tace a lokacin da ta cire jakarta" ta ajiye akan gadon" to sai anjima Umma" ki gaida gida" Umma ta fita xuwa dakin Hajiya" domin ta gaishe ta" bata san dalilin da yasa take jin nauyin xama tare da xabba'u ba idan taxo gidan" babu mamaki ko tana jin tsoron tane" a dalilin cin mutuncin da take yiwa kawarta fatima" . =====>+++++()+++++++<====== . Da Umma ta koma gida bata tsaya bata lokaci ba ta samu mujahid a xaune yana karanta jarida" amma kuma akwai alamar ransa a bace yake" tayi masa sallama ta xauna kusa dashi" Mujahid ya tattara jaridar ya rufe ta ya jepa ta kan tarin littatafansa" ya dawo da hankalinsa kan kanwarsa Umma wacce ya tabbatar tunda ta samu wur ta xauna" to akwai maganar da ke tafe da ita" . . Har kin dawo kenan daga gidansu fatima?" Umma tace dashi-: "Na dawo yaya" tace in gaishe ka" Ashe Hajiya ce suka tafi Unguwa" shiyasa ta tsaya a gida" taji haushin rashin xuwanta ita ma" Mujahid yayi ajiyar xuciya yace-: "Ok" yaci gaba da sauraron Umma" bayan tayi shiru na wani lokaci sai ta dago kanta tace dashi-: "Dama ina so ne muyi wata magana yaya" amma ina fatan baxata bata maka rai ba" Mujahid yace da ita" "Ina jinki Umma" ya akayi ne?" . . Umma ta sake yin shiru kamar tana jin tsoron abinda xata fada masa" xuwa can sai ta ce-: "yaya akwai wani abu da yake faruwa wanda ka boye mun" amma kuma daga baya na fahimci ko menene" duk da yake a matsayina na babban kanwarka bai kamata ka biye mun ba" banga laifinka ba idan nayi la.akari da dalilin da yasa ka boye mun" ka hana kowa yasan halin da kake ciki" Umma ta saurara" mujahid yayi shiru yana saurarenta cike da mamakin abinda take fada masa yanxu" Umma taci gaba da cewa-: . . "yaya mujahid" nasan cewa kana son fatima kawata" kuma ka boye al"amarin baka fada mata ba" nima kuma baka fada min ba" ba don komai ba sai don kada ka samu matsala a wajenta kaxo kaji kunya" bayan kuma tana ganin girmanka" wannan ne yasa ka boye sonta a xuciyarka" yana damunka kullum" ka rasa hanyar da xaka bi ka sanar da ita ta fahimce ka kuma ta baka goyon baya" mujahid yaji lokaci guda jikinsa yayi sanyi" bai taba tsammanin wannan maganar daga bakin kanwarsa Umma ba" yaji kunya ya kamashi" don kuwa dun abinda ta fada gaskiya ne" . . Taci gaba da cewa-: "A dalilin haka ne yasa ni a madadinka naje na samu fatima na fada mata abinda ka kasa fada mata" kuma ta bayar da goyon baya dari bisa dari" ta amince da soyayyarka" tana sonka fiye da yadda kake sonta" Nayi wannan karambanin ne domin in cireka daga wannan damuwar da kake ciki a matsayinka na dan'uwana" Ina fatan ban bata maka rai ba" idan kuma hakan da nayi ya xama laifi" to ina rokon ka gaparceni" . . Mujahid ya rasa me xaiyi saboda jin dadi" Abubuwa da yawa sun taru a xuciyarsa a lokaci daya" -:yana mamakin yadda Umma tayi wannan kokarin" -:kum ya akayi ta gano halin da yake ciki?" -;sannan kuma yana cike da farin cikin jin cewar fatima ta amince tana sonshi ita ma" Fatima tana son shi?" mujahid yaji sanyi a xuciyarsa" yayi murmushi yace da Umma dake xaune tana jiransa yayi magana" . . Umma gaskiya ne da ake cewa naka sai naka" idan bake ba kike 'yar uwata duk duniyar nan babu wanda xai iya cire ni daga wannan kangin da na shi" Na gode Umma" Allah shi saka maki da Alheri" Umma tayi dariya" "Ni ma nagode" dakaji dadin abinda nayi maka" Mujahid yace da ita cikin xumudi" "yanxu ina son ki fada min abinda kikeso a duniyar in mallaka maki shi Umma" dole in baki tukuicin wannan gagarumar kyauta da kika nemo min" dame xanyi maki tukuici Umma?" . . Tayi dariya sosae a wannan karon" "ko ma dake kayi mani ina so yaya" kome Allah ya ciyar dani nagode" Mujahid yace da ita" "ki shirya gobe xamu je ki xabi babbar sarka wacce ranki yake so a (county mall)" Umma tayi tafi cikin murna" "thank you my ßrother........ Allah yabar mu tare" . ======>+++++()+++++<======= . ßayan kwana biyu mujahid ya fara xuwa gidan su fatima" kafin ayi haka dama ya amshi lambar wayarta a wajen umma" ya kirata ya shaida mata cewa xaixo gidansu" fatima tace dashi to sai yaxo cikin kunya da kuma farin ciki" mujahid yje da karpe takwas na dare ya kirata" tace tana xuwa" ya fito daga cikin motarsa ya jingina a jikinta" . . Fatima ta fito bayan minti biyar tana sanye da leshi da kuma farin gyale" tana kamshin.............TUN A DUNIYA" . . . РÁĞE 07 WĨŤH ÁßßÁŃ ßÁŚМÁŔH ĎÁŃ МÚŤÁŃ YŐßE" . . MUJAHID Yaje karpe takwas na dare ya kira ta" tace tana xuwa! Ya fito daga cikin motarsa ya jinjina a jikinta" fatima ta fito bayan minti biyar tana sanye da leshi da kuma farin gyale" tana kamshin maya-mayan da ta shapa" tayi sallama sannan tace dashi" yaxo su matsa jikin kofar gidansu" saboda inda ya tsaya yayi kan hanya da yawa! Mujahid yaji dadin fatima da take da kamun kae" yabi ta suka matsa daf da komar gidansu" . . Fatima tayi masa sannu da xuwa sannan ta gaishe shi cikin ladabi" "ya baka xomin da babbar aminiyata ba?" mujahid yayi dariya" "Haka! Ko ke kika ga nayi haka ai kya min fada kice a korata gida" "saboda me?" yace da ita" "saboda yanxu hirar da xamuyi mu kadai ta shapa daga ni sai ke" babu muhallin umma a ciki" Fatima tace dashi-: "Ni kuma a ganina babu wani abu da xanyi a rayuwata ince babu muhallin Umma a ciki" ko menene" . . mujahid yace da ita-: "baki xo kan abubuwan da dole xaki tsallake ta daga cikinsu ba ne! Amma yanxu gashi kin para xuwa kansu" komai shakuwarki da kawarki ai baxata kai masoyinki ba fatima" "Masoyi shine-: wanda baki da tamkarsa a duniya" shine wanda xai san sirrinka fiye da kowa" shine wanda xaki fadawa maganar da duk duniya babu wani mahaluki da xaki iya fada wa" don haka masoyi yafi kawa muhimmanci" fatima tayi murmushi tace-: "Ni kuma sai nake ganin kamar kawa tafi masoyi muhimmanci" saboda kaga masoyi xai canxa ka" xai iya ganin wata yace yana sonta" xai iya yaudarar budurwarsa" amma kaga ita kawa indai ta amana ce" baxata yiwa kawarta haka ba" shiyasa gasjiya ni ina daukar kawa da muhimmanci a rayuwata" kaga ko bata mun rai saurayi yayi" dole kawar nan dai xan nema in fada mata halin da ake ciki ta tayani bakin ciki" tabani shawarar abinda ya kamata in yi" . . Suka dade suna tattake wuri suna jayayya cikin wasa da dariya kamar sun dade tare" sun saba da juna cikin kankanin lokaci" mujahid ya sanar da ita irin son da yake yi mata ya daukar mata alkawari komai wuya" komai dadi baxai taba karya mata alkawarin da ya daukar mata ba" fatoma tayi masa godiya ta tabbatar masa da nata cikin farin cikin kasancewarsa masoyinta" tace dashi-: "kaine mutum na farko dana fara tsayawa dashi a rayuwata a matsayin masoyin da nake so da gaske har cikin xuciyata" ina matukar farin cikin da Allah ya nuna mani wannan ranar" kuma ina fatan kaine mijina" . . Suka dade suna hira har xuwa lokacin da fatima ta fara gajiya saboda bata saba ba" da mujahid ya fahimci haka sai yace da ita xai tafi" tace ya gaishe mata da Umma da kuma mama idan yaje" "suka rabu suna farin ciki da hirar da suka yi" a karo na farko" a ranar fatima batayi barci ba sai da ta tabbatar ta hankura da cigaba da karatun da take so" taji tana son aure fiye da kowacce mace a duniya" tana matukar son mujahid!" . =======>++++()++++<======== . SAI da safe da fatima taje dakin Hajiya ta gaishe ta sannan ta tambaye ta" "Naji an kiraki jiya a waje" wanene?" fatima ta sunkuyad da kanta kasa cikin kunta ta ce-: "yaya mujahid ne....... Yayan Umma Hajiya binta tace-: "mujahid kuma?" Bata yi tsammanin haka al"amarin xai kasance ba domun kuwa bayan mutuncin dake tsakaninsu da gidansu mujahid" yanxu kuma ga auratayya xata sake shiga tsakaninsu" Hajuya bata boye farin cikinta ba" tace da fatima-: . . "to Alla ya tabbatar mana da alheri" ke kuma indai kinsan kin amsa masa kina sonshi" to ki tsaya a kaifi daya" tunda kinga ba wajen da xa.ayi wasa ko karanta bane" mutanen nan suna da kirki kuma suna ganin mutuncinmu" na tabbatar shima mahaifinki xaiyi farin ciki idan yaji haka" fatima taji dadin yadda ta samu goyon bayan Hajiya kai tsaye" . . A bangaren gidansy mujahid kuma Umma ta fara sanar da mama Rakiya halin da ake ciki" sa.ar da take taimaka mata suna yanka wasu dinkuna da aka kawo" Umma tace-: "mama inyi gulma?" mama Rakiya tace" "wace irin gulma kuma?" ke fa baki rabuwa da soki-burutsu" Umma tace-: "Gulmar yaya mujahid" "me mujahid din yayi da xakiyi gulmarsa?" Umma tayi murmushi tace-: "A.a ba laifi yayi ba" abin farin ciki ne mama" mama Rakiya taci gaba da aikin yanka atamfar da take yi" ta tambayi Umma ba tare da ta dago kai ba" "menene abin farin ciki da yayi?" Umma ta ce-: "yana son fatima kuma har yaje gidansu" kuma ita ma tana sonshi" mama Rakiya ta dago kanta cikin sauri" "wacce fatimar?" "fatima dai kawata da kika sani" mama rakiya tace-:" "ke Umma!! Bafa nason karya" kin tabbatar da haka kodai labari kikaji?" . . Umma tace-: "wallahi mama ba karua na fadi maki ba" mama Rakiya tace-; "Umma ko indai haka ne mujahid yayi tunani mai kyau" domin kuwa a yadda muka shaku da fatima da iyayenta idan har wannan al"amari ya tabbata na tabbata kowa xaiji dadi" . . A ranar mama Rakiya ta samu malam Abdullahi mahaifin mujahid da maganar" shima da yaji sai yace-: "alhamdulillahi" wannan abin alheri ne" domin kuwa fatima yarinya ce mai ladabi da biyayya tana girmama mu tamkar mune muka haifeta" . . IDAN mujahid ya auri wannan yarinya" babu shakka ya samu mata tagari" mama Rakiya tace-: "Dama jira nake ka dawo in tambayeka" tunda dai muda iyayen yarinyar nan mun xamo daya" me xai hana baxan je in samu hajiya binta ba muyi magana" domin su tabbatar muna sin a hada wannan aure na mujahid da fatima" malam Abdullahi yace-: "kada ayi gaggawa Rakiya tunda ba dadewa yaran sukayi da daidaita kansu ba" a bari sai xuwa nan gaba idan an tabbatar babu matsala" sun gama fahimtar juna" sai mu shiga cikin maganar musan abinda ya kamata muyi" mama Rakiya tace-: "to duk yadda kace haka xa.ayi malam" sai kuma mu hada da Addu"a Allah yasa wannan al"amaru ya xama mai ampani da albarka agare mu!" "Amin Rakiya" . =====>+++++()+++++<======= . SHIMA Alhaji mahaifin fatima da Haiya binta ta sanar dashi mujahid dan wajen mama rakiya yana xuwa wajen fatima" ya nuna amincewarsa badon komai ba sai don mutuncin da iyayensu suke dashi da kuma irin tarbiyar da suka ba 'ya'yansu" Alhaji sunusi yace da Hajiya binta-: "yanxu kenan maganar ci gaba da karatunta yasha ruwa kenan?" . . Hajiya tace-: "Ni dama ban goyi bayan ta wani ci gaba da karatu ba" tunda dai ta gama karatunta na sakandire lafiya" kawai ta fitar mana da miji ayi mata aure" da ita da xabba'u duka aure ya kamata muyi musu" bana son su fara tara mana samari a waje kullum" wasu na xuwa wasu na tafiya" Alhaji sunusi ya tambayeta" "ita xabba'un tana da wani tsayayye ne a halin yanxu ko kuwa?" Hajiya tace" "xan tambayeta itama" xance ta fitar da saurayi kwakkwara guda daya muji ko wanene" in Allah ya yarda xan tambayeta" muyi magana" . =====>++++++()++++++<====== SOYAYYAR mujahid da fatima sai karuwa take yi kullum" duk bayan kwana glhdu ai yaxo gidansu sunyi hira da daddare" fatima ta dauke kafa ta daina xuwa gidansu Umma saboda tana jin kunyar mama Rakiya" Umma tana yi mata tsiya sosai a waya" "wato yanxu yaya mujahid ya kwace mana ke ko fatima" kin dauke kafa da xuwa gidanmu baki daya" fatima takance da ita" "A,a ba haka bane Umma" kinsan ina jin kunyar mama" wallahi ina son xuwa amma ina jin kunyar mama ta ganni" ai sai ace mujahid na biyo ba ke ba" kin gani?" . . Umma tace-: "ba wanda xaice haka saboda tun kafin ku fara soyayya da mujahid shekarunmu nawa tare!" kowa yasan amintar dake tsakanina dake" kuma a bangaren mama ba haka take ba" ita ma tana sonki xo kuyi magana keda ita" kada ki mance dani dake fa duk daya ne a wajen mama" kamar 'yarta haka take daukar ki" Fatima tace- "to xan rika xuwa" kada ki damu aminyata" Duk abinda akeyi" ita dai xabba'u tana jin ana fadin mujahid musamman idan yaxo wajen fatima ta fita suna hira" amma bata taba ganinsa ba" wanta rana ne da 'yan mutuncin suke kusa suna daki su biyu da daddare ita da fatima bayan ta gama hira da mujahid ya tafi ta shigo gida" sai xabba'u ta tambaye ta" . . wai shi wannan mujahid da naji kuna ta magana a ina yake?" Fatima tayi murmushi tace da ita-: "yayan Umma ne fa.... Umma kawata" xabba'u tace da ita-: "Naga alamar kina sonsa da yawa" a ina yake aiki?" fatima tace-: "Aikin banki yake yi" amma bai dade da farawa ba" xabba'u tace cikin kaduwa" "banki?" kice yana da kudi dai sosai" Fatima tace-: "to ba laifi" yana da rufin asiri daidai gwargwado" xabba"u tace da ita-: "shi yasa hat yanxu bani da wani saurayi dana yiwa alkawarin xan aureshi" saina samu babban yaro (Ontop) wanda xai kula dani sosae" ya rika yimun komai nake so a rayuwata" . . Fatima tace da ita-: "Amma anti xabba"u ai rufin asiri na Allah ne" xaki iya samun wanda bashi dashi" amma daga baya idan kunyi auren" sai kiga Allah ya buda mashi" kuma kina iya auren wanda yake da shi din" daga baya yaxo ya rasa abin" duk ba yadda Allah baya yin ikonsa" don haka idan kina son mutum kawai ki soshi tsakaninki da Allah badon wani abu da yake dashi ba" . . Xabba'u tace" "Ai namiji ba.ayi masa wannan tabbacin fatima" kina iya yin shahadar kin aure shi a talakansa bashi da komai kuci wuya tare" amma daya samu kudi maimakon ya maida hankalinsa a kanki" ya kyautata maki" sai ya fara hangen wata budurwa kyakkyawa wacce xai aura ya kawo maki" bata sha wahalar komai ba amma sai yaxo ya fifita ta a kanki" shiyasa ni ban yarda da irin wannan kasassabar ba" nafiso in gani a kasa" Idan ma wani abu ya faru daga baya" nasan da kudinsa na same shi" bansha wahala ba balantana kuma raina ya baci" . . Fatima tace-: "to Allah ya xaba mana maxa nagari" wadanda xasu rike mu amana" su kula damu" ba wadanda xasuci amanar mu ba" bayan mun gama shan wahala tare dasu" Da wannan suka rufe hirar tasu sukayi barci kamar abin arxiki" Da safe bayan sun tashi abu na farko da xabba'u ta fara yi shine sirfa wa fatima xagi saboda kawai bata gyara shimfidar gadonsu ba" bayan ta tashi" saida Hajiya taxo ta shiga tsakaninsu" . ======>+++++()+++++<======= A wata dawowa da mujahid yayi ne daga tafiya" bayan yayi sati daya baya gida" sai yayi wa fatima waya ya sanar da ita ya dawo" . . Kuma xaixo wajenta a ranar" me kike so.......TUN A DUNIYA" . . . РÁĞE 08 WĨŤH ÁßßÁŃ ßÁŚМÁŔH ĎÁŃ МÚŤÁŃ YŐßE" . . A Wata dawowa da mujahid yayi ne daga wata tafiya" bayan yayi sati daya baya gida" sai yayi wa fatima waya ya sanar da ita ya dawo" kuma xaixo wajenta a ranar" ya tambayeta" "me kike so in xo maki dashi-: ta ce-: "kaxo mun da hotonka mujahid saboda shi kadai ne abinda na rasa a dakina" yaxo mata da babban hotonsa na bango ya bata ta amsa cikin farin ciki da godiya" yana sanye da karamar riga" ya jinjina da wata filawa a makarantarsu yana murmushi" acan baya gine- ginen ajujuwa ne da kuma dalibai dake giptawa" . . Fatima ta tambayeshi?" "A makaranta ka dauki wannan hoton ko mujahid?" ya ce da ita-: "shekararsa biyu kenan" tun lokacin da nake (300 level) a jami.a baki ganni ba a rame kamar ana diba na ana miya dani" fatima tayi dariya" "to yanxu din fa?" "Haba kema ai kinsan na canxa nesa ba kusa ba" ya xaki hadani da lokacin da nake makaranta?" fatima tace-: "muma dai ya kamata muje jami.ar nan muji aninda ake bamu labari" . . Mujahid yace da ita cikin gatse-: "ke kuwa xakije babbar jami.a" kinsan jami.ar da ya kamata ki je?" "sai ka fada" "A.ß.U. Ya kamata kije" fatima ta dubeshi cikin shagwaba" "Aini na gane abinda kake nufi wato" Aure ßautar Ubangiji ko?" to ba A.ß.U din xanje ba" ß.U.K xanje ita ma kuma fa?" "Oh! ß.U.K xaki je" wato ß-bana U-Umma k- kawata" xasu samu karuwa a gidansu" Fatima ta tuntsire da dariya kamar xatayi kuka! "Kai dai wallahi mujahid ba.a kure ka a magana komai mutum ya fada kasan abinda xaka ce dashi ka kare kanka" . . Suka rabu cikin farin ciki" fatima ta shaku da mujahid" ji take kamar ma anyi aurensu" tana daukarsa kamar mijinta ne! Ba saurayinta ba" tayi nisa a cikin kogin son mujahid" kuma ta tabbatar raba ta dashi yanxu aiki ne ja! Da wahala ta sake jin tana son wani saurayi a duniya tamkar mujahid" Ta shiga da hotonsa a cikin dakinsu ta jinjine shi akan karamin teburinsu da suke kwalliya ita da xabba'u wanda yake hade da madubi" sannan ta hau gado ta kwanta" a lokacin xabba'u tayi nisa da barcinta har tana munshari" . =====>++++()+++++<======== . ßAYAN sun tashi sunyi sallah da asubahi sai fatima ta koma ta kwanta taci gaba da bacci" xabba'u ta kwanta kenan sai ta kyalla ido kan madubin mujahid dake ajiye akan teburin yana fuskantar ta" xabba'u ta samu kanta tana kallon kyakkyawar saurayin dake cikin hoton yana yi mata murmushi" Tahi xuciyarta ta buga da karpi" ta kurawa hoon idanu ko kiftawa bata yi" wannan saurayin kuma wanene?" ta tambayi kanta cikin mamaki" tunda take a duniya bata taba ganin wani saurayi ko a sarari" ko a hoto da taji a kallo daya ya bugi xuciyarta irin wannan saurayin ba" . . Ta bude baki ta taso sanye da kayan bcci" ta sauko daga kan gadon ta nufi inda hoton yake" ta durkusa a gaban hoton tasa hannuwanta biyu ta dauke shi ta kura masa idanu tsawon lokaci" Tana kallon hoton" tsananin so da kuma radadin begen shi suna dada shiga xuciyarta" . . Waya shigo da wannan hoton dakinsu?" ta dai farka ne kamar daga sama" kawai ta dora idanunta kan hoton saurayin da ta tabbata xuciyarta ta kamu da ciwon sonshi a kallo daya" Xabba'u ta mayar da hoton ta ajiyeshu a inda taganshi" ta koma baya ta xauna dirshan a kasa" taci gaba da kallonshi" Ba sai ta tsaya wahalar da kwankwalwarta ba kafin ta fahimci ko shakka babu fatima ce kawai xata shigo da wannan hoton cikin dakinsu" Da ma wannan shine mujahid din da take ji fatima tana maganar shi kullum?" shine wanda yake aikin banki?" gashi kyakkyawa mai fara.a gashi kuma yana da kudi" "xabba'u ta juya baya ta kalli fatima dake kwance a gado tana bacci" sannan ta dawo da hankalinta kan hoton mujahid" taji a ranta duk duniya ba wani namiji da ya cancanta ya xama mijinta sai wannan saurayi wanda fatima take so" . . Xabba'u taji tafi fatima son mujahid" duk da yake yanxu kuwa ta fara ganinshi a hoto" tunda yake xuwa wajen fatima bata taba fita waje ta ganshi ba" sai yau da fatima ta shigo da hotonshi cikin dakinsu" Xabba'u tace a xuciyarta" wannan saurayin nina fi dacewa dashi ba fatima ba" kuma niya cancanta ya aura ba ita ba" Xabba'u ta sake matsawa ta dauko hoton ta kankameshi a kirjinta" tana lumshe idanu ta fara tunani" gaya nan harma sunyi aure sun xama ango da amarya" Xabba'u ta ce a sanyaye-: "Ina sonka mujahid" kuma duk duniya babu mai rabani da kai" ko da kuwa xan rasa raina ne" Kuma har cikin xuciyarta haka abin yake" . =======>++++(1++++<====== A ranar da xabba'u taga hoton mujahid wuni tayi a kwance kamar bata da lapia" tana sake-saken hanyar da xata bi ta kwace shi daga wajen fatima" ta raba soyayyarsu ya dawo wajenta" Idan fatima bata dakin" idan ta fita waje" sai xabba'u ta taso daga kan gado ta xauna ta kurawa hoton mujahid idanu" Idan kuma taji tafiyar fatima xata shigo dakin" sai tayi sauri ta koma ta kwanta" don kada fatima ta gane abinda take sakawa a xuciyarta" . . GANIN ta wuni a daki ko fitowa waje bata son tayi sai fatima ta fara kokwanto duk yadda akayi akwai wani abu da yake damun xabba"u" ta sameta a daki ta xauna kusa da

Chapter 3 of 9