Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
fassara shi Tsawon wadannan kwanakin babu abinda sukeyi face karance karance dare da rana domin hatta bacci ma dan kadan suke yinsa Acikon sati na biyun ne da kwana uku suka yi bankwana dattijo kusaid suka kama hanyar fita daga birnin gaba daya Tsawon wadannan kwanaki sun shaku dashi ainun har suka ji kamar ma ba zasu iya tafiya su barshi ba amma a haka bisa dole dukkansu suka hakura suka tafi suka barshi idanunsu cike da kwalla Bayan sun fito daga gidan ne kawai sai walisa ta dubi kusail Tace amma dai yanzu ba zaka sake komawa cikin halayyar sata ba ko? Dajin wannan tambaya sai kusail yayi murmushi fuskarsa cike da alamun kunya yace Ai da dinma duhun jahilci ne ya sakani haka amma yanzu ai na gane gaskiya Kodajin haka sai dukkansu suka bushe da dariya Sannan suka koma cikin kasuwar garin suka sayi ingarmun dawakai kosassu guda uku sannan suka sayi abincin da zasuyi guzuri dashi A wannan lokaci gimbiya walisa tana dauke da sandar sadauki hassanul basari Suna gama sayen dawakan sai suka yi bankwana kusail Sannan suka kama hanya suka fice daga cikin birnin gaba daya suka kutsa kansu cikin daji domin fita farautar yarima walisu Duk inda suka gifta da dawakan su saidai kaga kura tana tashi Kuma suna gudun ne cikin nishadi kamar masu yin gasar tseren gudu WANNAN SHINE ABINDAYA FARU GASU GIMBIYA WALISA BAYAN SUN KARBI ADDININ MUSULUNCI KUMA SUN SAKE FITA NEMAN YARIMA WALISU ****** ******** ******** Al'amarin aljani dargatul amnar kuwa lokacin dayaci birnin amnatul kais da yaki kuma ya kama hanya ba tareda yasan gurin da zai kara zuwa agaba ba Sai yayi ta tsala gudu acikin sararin samaniya kamar zai fita daga cikin duniya Domin cika burin mai gidansa yarima walisu Sai yayi ta kyalkyala dariya dariya wacce ta dinga amsa kuwwa agaba daya ilahirin samani wacce sautinta yake fita kamar saukar aradu A wannan yini gudan sai da yaci birane ashirin da yaki kuma ya bazar dasu daga doron kasa Kuma kisa iri daban daban ya dinga yi aduk inda ya sauka Awannan ranar saida manyan koramu suka dinga cika da jinin bil'adama Kasa kuwa ta dinga cudanya da jini abin babu kyan gani Bayan ya gama da wadannan birane ashirin din ne ya doshi na ashirin da daya Kawai sai ya tuna da maganar su gimbiya walisa kuma sune akafi bukatar ya fara gamawa dasu da wuri Koda yin wannan tunani sai take ya juyar da akalar tafiyarsa Cikin sauri ya nufi can kogon dutsen da su gimbiya walisa suke yana mai tsala azababben gudu Awannan lokaci sai ya kure dukkan balagar dayake ji da ita cikin wannan tafiyar fiye da wanda yake yi a baya Tafiya rabin yini kacal yayi ya isa bakin wannan tsaunin Koda zuwansa sai yaga kofar kogon akulle kamar ba'a taba bude ta ba Kuma gurin gabaki dayansa babu alamar sawun bil"dama ko kuma na dabba Koda ganin haka sai yaji wani irin farinciki acikin zuciyarsa Domin yana da tabbacin cewa su gimbiya walisa basu fito daga cikin kogon ba Don haka sai ya kwantar da hankalinsa kuma yaji ya samu nutsuwa acikin zuciyarsa Sai ya yanke hukuncin kawai ya zauna anan gurin ya jira har zuwa lokacin dasu gimbiya walisa zasu dawo Abinda bai sani ba shine tun tuni su gimbiya walisa sun fita daga cikin kogon dutsen Amfani sukayi da karfin sihirinsu suka suka boye sawun kafafunsu Yadda koda an biyo bayansu ba za'a riskesu ba wannan shine dalilin dayasa aljani dargatul amnar ya kasa sanin fitowarsu Kuma kuskurensa guda daya shine kin yin amfani da sihirin tsafinsa wajen binciken halinda suke ciki don ya san gaskiyar lamarin Don haka sai. Ya sami guri ya zauna domin jiran fitowarsu Aikuwa zamansa keda wuya sai take barci mai nauyi ya sace shi ba taredaya sani ba WANNAN SHINE BABBAN KUSKUREN DAYA AIKATA ****** ******* ******** A can cikin kogon tsafin yarima walisu kuwa lokacin daya shiga cikin Halwar tsafi domin ya gano wanne irin bala'ine yake neman tunkaro shi Saiya manta da maganar su gimbiya walisa domin yasan cewa abune mawuyaci su tsira da rayuwarsu daga cikin kogon dutsen sa suka fada Idan ma har sun samu dama sun kubuta to ya tabbatar da cewa aljani dargatul amnar shine zai taresu akan hanya ya kashesu Don haka sai ya bata tunaninsa domin ya gama tabbatar wa da kansa cewa Abinda ke shirin tunkaroshi babban abune mai hatsarin gaske Acikin wannan sabuwar rayuwar da ya kafawa kansa Amma kuma ya tabbatar da cewa wannan abin dole yana da nasaba da hassanul basari wanda ya kasance bashi da abokin gaba a rayuwarsa kamarsa Babban burinsa shine yasan halinda hassanul basari yake ciki Sai daya shafe kwanaki masu yawa yana wannan binciken Atsawon wadannan kwanakin baiyi barci ba ko sau daya Haka zalika koda ruwa makurwa daya bai sha ba Arana ta karshe ne da kyar da makyarkyata domin sai daya sha bakar wahala sannan ya gano cewa hassanul basari ya mutu Koda ganin wannan al'amari baisan sa'addaya bushe da mahaukaciyar dariyar farinciki ba wanda sautin dariyar saidaya ratsa ko ina acikin fadar tareda amsa kuwwa Saida yayi dariyar ta isheshi sannan kuma ya hade ransa Sakamakon tunawa da maganar su gimbiya walisa kawai sai ya shafi madubin tsafin da tafin hannunsa Take saiga hoton aljani dargatul amnar ya bayyana acikin madubin tsafin acikin daji yanata faman sharara barci abinsa Daya barin kuma na madubin tsafin nasa ga hoton su gimbiya walisa can suna shirin fitowa daga cikin birnin labtarul halkam bisa ingarmun dawakai Koda ganin wannan al'amari sai take duk fara'ar da take kan fuskar sa ta disashe zuwa bakin ciki Cikin matukar fushi ya daga hannunsa daga inda yake ya zabgawa hoton aljani dargatul amnar duka yana daga inda yake Awannan lokaci dargatul amnar yana kwance abakin kogon dutsen Kawai sai ya ji sautin dukan da yarima walisu yayi masa Saboda zafin dukan baisan sanda ya daka tsalle ba ya tashi firgigit kamar an tsulawa yaro bulala Yana tashi sai yayiwa yarima walisu sujjada Jikinsa na karkarwa kamar kace kyat ya ruga a guje saboda matukar firgitar da yayi Yarima walisu ya dubeshi yace kai kuma aikin dana saka kenan? Dajin wannan tambayar sai aljani dargatul amnar yace kayi mini afuwa ina nan ina zaman jiransu ne barci ya sace ni ban sani ba Amma kayi hakuri bazan kara yin wannan kuskerenba Dajin wannan batu sai yarima walisu ya daka masa tsawa yace Kai shashashan banza maza ka tashi yanzu kabisu domin basa cikin kogon dutsen nan Yanzu haka sun fito daga birnin labtarul halkam ka tare su hanya ka gaggauta kashemini su Idan kuwa kayi wani kuskure ni da kaina zan kasheka Dajin haka sai jikinsa ya fara kyarma yace kayi hakuri ya shugabana yanzu zan cika umarnin ka kar ka sami damuwa Yana gama fadin haka sai ya sake bude fuka fukansa ya nufi hanyar da zata kaishi birnin labtarul halkam domin ya riski su walisa ahanya ya kashe su don cika umarnin mai gidansa SHIN YANA RISKARSU WALISA AHANYA ? YAUSHENE ZASUYI GABA DA GABA DA YARIMA WALISU? SHIN RUHIN BOKA SAHIBUL UKUB YANA FITA DAGA JIKIN YARIMA WALISU ? DON JIN AMSAR WADANNAN TAMBAYOYI SAI MU HADU AKASHI NA GABA DAGA NAKU HABIBULLAH KBR LIKE, COMMENTS AND SHARE************----HATSABIBAN SADAUKAI ******************CI GABAN ZUBAR DA JINI ********************5 PART A LBR *************************HABIBULLAH KBR Lokacin da aljani dargatul amnar ya bude fuka fukansa ya tashi sama Sai gashi fuka fukan sun lullube gurin gaba daya sannan ya fara kadasu da karfi Domin ya gaggauta riskarsu gimbiya walisa tunda yasan cewa idan har yayi kuskure akan aikin da aka saka shi hukuncin kisa yarima walisu zai yanke masa kuma ko kadan bazai tausaya masa ba Saboda haka sai yayita tsala azababben gudu kamar kiftawar ido haka ya dinga giftawa ta saman manyan birane Duk inda ya gifta sai fuka fukansa sun yiwa birnin gaba daya inuwa saboda girman su Cikin kankanin lokaci ya riski su gimbiya walisa alokacin suma suna tsaka da tafiya Kuma rana ta kwalle sosai suna cikin tafiya sai sukaga Tun daga nesa suka hango wata jibgegiyar inuwa tana doso inda cikin azababben gudu Koda ganin wannan inuwar sai duk sukaji jikinsu yayi sanyi domin sun san tabbas wannan abin gurinsu ya doso kai tsaye don haka duk sai suka tsayar da linzaman dawakansu Domin suga abinda yake shirin faruwa sannu a hankali sai suka fara hango manyan fuka fukan aljani dargatul amnar wanda suka tokare sararin samaniya Da ganin haka sai dawakan dasu walisa suke kai suka firgita suka fara turjiya suna daga kafafuwansu na gaba sama domin su daga su walisa sama su zubar dasu domin su kara tsira da rayukansu Amma sun rasa yadda zasuyi domin su walisa sun ruke linzaman dawakan sosai kuma sun tokare ko'ina da kafafunsu yadda dawakan ba zasu iya kwacewa daga hannayensu ba Daga can sukaji an kece da wata mahaukaciyar dariya mai kama da saukar aradu Tareda wata irin tartsatsjn wuta daya zubo daga sararin sama Koda wutar ta sauka akan kasa sai take ta haifar da wani wawakeken rami Wanda za'a iya binne mutum goma aciki Cikin sauri su walisa suka sauka daga kan dawakan nasu suka sakesu Domin suma su samu su tsira da rayuwarsu tunda sun san indai akan dawakan za'ayi wannan fafatawar zasu sha wahala sosai Take dawakan suka ruga da gudu zuwa can cikin daji domin su ceci rayuwarsu Cikin kankanin lokaci saiga aljani dargatul amnar ya keto cikin hazo Ya zuro da fuskar kasa yana kyalkyala wata mahaukaciyar dariya wacce tasa dajin gaba daya ya dinga amsa kuwwa Tunda su walisa suka zo duniya basu taba ganin aljani mai girma da kuma muni irin aljani labtarul halkam ba Domin su kansu saida sukaji kamar suja da baya su gudu domin tsira da rayukansu Amma sai suka danne tsoron daya darsu azuciyarsu Kuma suka tsaya cak ba tareda sun janye kafarsu baya koda da taku daya ba Daga can kuma sai ya tsuke bakinsa ga barin yin dariyar da yakeyi ya kurawa su walisa mummunan idonsa mai kama da gasasshen dan buda yace Ku kananun halittu masu ganganci da rayukansu wanne irin ganganci ne Ya shigar daku cikin tarkon mai girma walisu? Gaskiya kun tabka babban kuskure arayuwarku da har kuke ikirarin karawa dashi Ku uku kacal baku da karfin da zaku iya jayayya dashi Kai bama ku kadai ba duk duniya babu wand iya galaba akansa Domin shi kadai yaci dubu sai ceto kuma tsautsayima yana shakkar tunkararsa saboda bala'insa Bayan haka inaso ku sani yanzu kun gama fusata shi da kansa ya turoni nan domin na kai masa kawunan kanku Kodajin wannan batu sai sarki aryan shima ya maidawa dargatul amnar da martanin murmushin raini yace Hakika bamu ne mukayi kuskure ba kaine ka tabka babban kuskure Daka har ka kuskura ya aikoka gurinmu domin ina tabbatar maka da cewa Baka isa ka tsira ba daga hannunmu duk da cewa azahiri kafimu karfin damtse Da kuma girman jiki amma ka sani hakan bazai hanamu samun nasara akanka ba Don haka kaine ka aikata kuskuren zuwa garemu idan har ka isa cikakken namiji sai ka taho mu gwada gaba da gaba Amma ina rantsuwa da ubangijin musulunci baka isa ka tsira daga kaifin takobin mu ba Dajin sun ambaci ubangijin musulunci sai dargatul amnar Ya tuntsure da dariya da katon bakinsa Daga can kuma sai ya murtuke fuskarsa kamar an aiko masa da sakon mutuwa yace lallai kun bani kunya tunda har kuka ajiye addinin da kuka gada tun iyayenku da kakanninku Kuka karbi wani sabon addini agurinku wanda bashi da asali agurinku kuma sabone shi Kuma wannan itace babbar hujjar da zata tabbatar mini da cewa zan sami nasara akanku Yana gama fadin haka sai ya bude wangamemen bakinsa da nufin ya zuko su gimbiya walisa gabaki dayansu ya cinyesu Cikin bakin zafin nama dukkansu suka daka tsalle daga inda suke suka kaucewa harin nasa Da ganin haka sai ya kara kawo musu sara da kaifin faratan yatsunsa Nanma suka kara daka tsalle suka kauce wa farmakin daya kawo Sai gashi gurin da faratan nasa suka sara sun haddasa wawakeken rami agurin Kawai sai su walisa suka falfala da gudu zuwa inda yake suka. Kacame da azababben yaki wohoho ai kuwa koda fara wannan bakin gumurzun sadaukan sai Gurin gaba daya ya sauya yanayi Wata iriyar kura ta tashi sama tayi tsiri kamar zata tokare sararin samaniya Kasa kuwa ta dinga girgiza tana jijjiga Bishiyoyin da suke cikin dajin kuwa suka dinga jijjigowa daga cikin karkashin kasa har jijiyoyinsu suna faduwa kasa Duwatsun da suke cikin dajin ma suka dinga farfashewa Suna fadowa kasa kamar an saka musu nakiya ,tekunanda suka ratso ta cikin dajin ma suka dinga tambal tambal saboda masifar da take afkuwa acikin dajin Ba komai ne ya haddasa hakanba face Duk sanda dargatul amnar ya kawowa su walisa duka idan suka kauce ya sami kasa take yake haddasa wawakeken rami Tabbas in badon su walisa suna da zafin nama ba da tuni dargatul amnar ya gama kashesu Kuma dukkansu sunki yarda su fuskanceshi ta bangare daya domin kasa kansu sukayi gida uku kuma suna fadan suna canja matsaya Ma'ana Idan gimbiya walisa ta fusanceshi ta gabansa to ita kuma jaruma marfuza Zata kasance abayansa ne Haka shima sarki aryan zai tsaya agefensa Kuma sunayi suna zazzagaya shi kamar shaidanu tako'ina Amma da zarar sun sareshi saidai kaji wata irin kara ta tashi kamar haduwar karfe da karfe Ana cikin wannan hali ne kawai dargatul amnar yasa mafarsa guda yayi bal da gimbiya walisa Nantake tayi sama kamar an janyeta da majaujawa Sannan ya shammaci sarki aryan da jaruma marfuza ya sunkuya Ya shuri kafafunsu yayi jifa dasu a sama kamar yadda yayi da walisa Sai gasu duk su biyun suna yawo. Asama kamar iska ta debi tari ledoji Amma saboda matukar naci sai sukaki yarda su fadi duk suka dinga dunkule jikinsu asama suna dira bisa kafafunsu kuma ba'a cure suka fado kasa ba aguri daban daban suka dirga Amma fa dukkansu babu wanda baiyi aman jini ba saboda dukan da yayi musu Kawai sai dargatul amnar ya juya inda walisa take domin itace akafi bukatar ya hallakata gadan gadan da nufin yayi mata kisan wulakanci Ai kuwa tun kafin ya isa inda take tuni ta daka tsalle ta mike tsaye sannan ta daki kasa da hannayenta tare dayin alkafira ta tashi sama kamar tsuntsuwa mai fuka fuki Kawai sai gata ta dira ajikinsa ta makalkale kamar kadangaruwa tana faman gudu ajikinsa kuma tana saran jikinsa da takobinta Aikuwa kodasu marfuza sukaga haka sai suma sukayi taho da gudu suma sukayi koyi da abinda walisa tayi Tun suna saran jikinsa da makamansu harsai da takai cewa makaman nasu duk sun dakushe basu da wani amfani Suna cikin wannan haline kawai sai dargatul amnar ya karanta wasu sirrikan tsafinsa Faruwar hakan keda wuya sai su walisa sukaji gaba daya jikinsu ya makale ajikin dargatul amnar yadda koda yatsan hannunsu ba zasu iya dagawa ba Kawai sai ya bude fuka fukansa ya tashi sama dasu a doron bayan nasa Sai gashi yana tsala gudu dauke dasu yana ta faman wujijjigasu asama Tareda kyalkyala musu dariya yana cewa Ai na tabbatar muku kuskuren ku dayane shine ajiye addinin gado ku karbi sabon addini Yanzu babu ta yadda zaku tsira da rayuwarku daga sharrina Yana cikin wannan zance ne kawai sai gimbiya walisa ta tuna wata addu'a da kusaid ya koyar dasu Aikuwa nan take ya fara karanta wannan addu'ar ba zato ba tsammani sai taji wani irin sabon azababben karfi ya shiga jikinta Nantake ta banbare jikinta daga nasa Sannan tayi kabbara da karfi Karfin kabbarar ne ya rikita dargatul amnar yaji kamar kansa zai fashe Bisa dole ya saki fuka fukansa ya dawo kan kasa Haka suma su jaruma marfuza cikin sauri suka fara karanta addu'ar da walisa ta karanta Nantake suma sukaji duk irin yanayin da walisa ta shiga Cikin zafin nama kafin dargatul amnar ya sauka kasa tuni Jaruma marfuza ta daka tsalle ta haye kan gadon bayansa Ta kwanto doguwar sarkarta ta zura ta acikin hancinsa Sannan ta ruke da hannuwanta guda biyu Wohoho ai kuwa sai gashi nan danan ta fara sarrafa dargatul amnar ta dole kamar doki domin sukuwa suka dingayi akansa kamar doki Haka suka dinga sarrafashi shi kuma a lokacin ya gama gigicewa saboda yadda suka dinga yi masa rugugin bala'i tako ina Duk da karfin damtsen da yake takama dashi sai gashi ya zama na banza domin bil'adama ne guda uku kacal suke sarrafashi Koda yaji bala'i sai ya dinga bude bakinsa yana faman yin aman wuta kamar batoyi tana zubowa kasa tana kona bishiyoyi da ciyayin da suke cikin dajin Suna cikin wannan haline sai itama gimbiya walisa ta kwanto sandar hassanul basari da caka tsininta agadon bayan dargatul amnar Aikuwa sai take dargatul amnar yayi wani irin gurnani alokacin da jini yayi feshi daga gadon bayansa Kawai saiya sulale ya fado kasa acikin wani katon daji wanda yake kusa da wata katuwar teku Sannan ya kama da wuta kamar an zubawa karmami kalanzir Cikin sauri su gimbiya walisa suka sauka daga gadon bayansa suka fada cikin wannan tekun sukayi nustso aciki Shi kuma suka barshi a sama yana mai ci da wuta Su kuma sai sukayita iyo suna ninkaya acikin tekun har saida sukayi nisa da inda yake sannan suka dago da kansu sama suka dawo gefen tekun Suka fita daga cikinsa, koda fitowarsu sai suka sami guri daya dukkansu suka zauna suna masu jan dogon numfashi Tsawon lokaci suna zaune suna faman kallon juna ba tareda daya yace uffan ba Daga can sai sarki aryan ya dubi su walisa yace Tabbas yanzu na mara imani da cewa babu abin bautawa da gaskiya face ubangijin musulunci Domin wannan karfin da muka samu karfine wanda sihirin tsafi ba zai iya baka shi ba Dukkanku kunga abubuwan da suka faru da idanunku Dajin haka sai marfuza tace kwarai kuwa maganar ka gaskiyace Tabbas ba don taimakonsa ba da tuni mun rasa rayuwar mu Suna cikin wannan zancen ne sai walisa tace yanzu babu abindaya dace muyi face godiya ga ubangiji Sannan ina tunasar daku cewa hanr yanzu zama bai samemu ba Dolene mu tashi mu ci gaba da tafiya domin da alama bukatar mu tana daf da cika Don haka ina so na tunasar daku cewa aduk sanda muka tsinci kanmu cikin mawuyacin hali mu dinga tunawa da ambaton ubangiji Da kuma neman taimako daga gareshi Idan har munason mu sami nasara da gaggawa Yanzu abinda ga kamata muyi shine mu tashi mu kama hanya don zaman cikin dajin nan bai dace damu ba Tana cikin wannan maganane sai sarki aryan ya dubeta yace Akwai abu guda daya wanda nakeson na tunatar daku Da sauri marfuza tace menene wannan abu Kawai sai sarki aryan yace yanzu shine lokacin da zamuyi sallar azahar Yana gama fadin haka sai ya mike ya nufi bakin wannan tekun Kawai ya tsugunna ya fara alwala cikin sauri su walisa suna suka tashi sukayi koyi dashi Sannan ya shige gaba ya tada sallah su kuma suka biyoshi suka bishi jam'i Suna idar da sallar sai suka tattara kayansu suka fara shirye shiryen ci gaba da tafiya A sannan ne suka fara tunanin hanyar da zasu sami jirgin da zasu hau su ketare ta saman wannan tekun dashi Abinda basu sani ba shine wannan takun duk duniya babu tekun da takaita hatsari bisa wannan dalilin ne yasa Matafiya da kuma masunta suka daina alaka da wannan tekun don ceton rayukansu Saida su walisa suka jima a wannan guri suna jiran jirgin dazaizo ya dauke su amma suka rasa domin ko alamar jirgi guda daya basu gani ba Koda ganin haka sai marfuza ta basu shawarar kan su tsaya a wannan dajin su kera basu jirgin wanda zai daukesu duk su ukun Nantake kuwa duk suka gamsu da shawararta suka bazama cikin daji suka dinga saro manyan bishiyoyi suna janyo su Suna tarasu aguri guda har saida suka tara masu yawa A sannan suka tuna cewa makaman yakinsu sun lalace Don haka sai suka kunna wuta sosai sannan suka zura. Makaman nasu acikin wutar saida sukayi jajur sannan suka zarosu Suka dinga sa guduma suna dukansu saida makaman sukayi tsini Sannan suka dauko dutsen wuta suka dinga wasa makaman dashi har saida makaman sukayi kaifi irin wanda ake cewa gayawa jini Na wuce Saboda sufi jin dadin sassake bishiya dasu Suna gama wasa makaman sai suka koma inda wadannan bishiyoyi suke suka fara aikin sassake su da dai dai da dai dai Suna tarawa da kullewa har sai da suka tashi jirgin ruwa mai kwarin gaske wanda dukkansu zasu shiga cikin sa ba tareda sun matsuba Kai hardama dakin kwanciya guda sukayi acikinsa Suna gama kera wannan jirgin sai suka daureshi da jijiyoyin bishiyoyi suka dinga jansa Tun yana kan kasa har saida suka janyeshi ya koma cikin tekun ya zauna daram babu alamar tambal tambal atare dashi Kawai sai suka dinga kama wadannan jijiyoyin suka hau kan jirgin suka zauna daram Shidai wannan jirgi ajikinsa akwai gurin matuka guda biyu daya abangaren hagu daya kuma a bangaren dama Can gaban jirgin kuwa daki ne wanda mutum zai kwanta aciki Asaman dakin kuma mazauni ne wanda aka ajiye kujerar itace a samansa wacce mutum zai zauna ya dinga kalle musu abinda yake gabansu Koda suka gama shiga cikin wannan jirgi kawai sai gimbiya walisa da sarki aryan suka kama matukan jirgin guda biyu Ita kuma jaruma marfuza saita karbi jakunkunan kayan guzurinsu ta shige dasu cikin wannan karamin dakin ta ajiye Sannan ta fito ta hau saman jirgin ta tsaya domin ta fara aikin gane musu abubuwan dake gaban jirgin Su kuma su sarki aryan sai suka kama aikin tuka jirgin Sannu a hankali jirgin ya fara motsawa yana tafiya acikin tekun cikin gudu Tun suna tafiya a gurinda bai da zurfi har jirgin ya nutse ya zauna daram Yaci gaba da tafiya a saman ruwan, Suna tafiyar suna hira abinsu ita kuwa marfuza ta zauna daram dam Ta harde kafafunta asaman jirgin hannunta guda yana kan takobinta tana ta zare idanu da muzurai tare da kallon ko ina na cikin tekun gabas da yamma kudu da arewa tana nazarin tekun don tabbatar da tsaro Tabbas jaruma marfuza ta cika jaruma domin ko kadan batasan tsoro ba awannan lokaci ji take kamar idan gaba daya duniya ne zasu taru akanta Ita kadaice zata iya gamawa dasu ba tareda ta nemi taimakon su gimbiya walisa ba TAFIYAR KWANA NAWA ZASUYI KAFIN SU KETARE WANNAN TEKU? SHIN WACCE IRIN MATSALA ZASU FUSKANTA ACIKINSA? ME ZAI FARU IDAN YARIMA WALISU YASAN CEWA SUN KASHE ALJANI DARGATUL AMNAR? DON JIN AMSOSHIN WADANNAN TAMBAYOYI SAI MU HADU A KASHI NA GABA NA WANNAN KAYATACCEN LABARI MAI SUNA HATSABIBAN SADAUKAI DAGA NAKU HABIBULLAH KBR LIKE, COMMENTS AND SHARE**************HATSABIBAN SADAUKAI CI GABAN ZUBAR DA JIN ***********5 PART B LBR ****************HABIBULLAH KBR Lokacin da jaruma marfuza tabar su gimbiya walisa suna tukin jirgi ita kuma ta hau samansa ta zauna zaman dirshan Tana ta kalle kalle da zare idanu kai kace neman wani abu takeyi Kasancewar su sarki aryan suna da matukar zafin nama, juriya gami da karfin damtse Sai gashi suna tuka jirgin cikin karfi da kuma karfin gudun gaske yana tafiya yana ratsawa ta cikin teku Kai kace mutane masu yawa suke aikin tukinsa Cikin kankanin lokaci jirgin nasu yayi nisa a cikin tekun yadda idan kana tsaye agefen tekun ba zaka iya hango jirgin ba Saida sukayi tafiya mai nisan gaske sannan rana ta fadi duhun dare ya soma haskawa Don haka sai suka hakura da tukin jirgin suka tsaya domin su huta kuma su ci abinci Nan da nan kuwa sarki aryan da gimbiya walisa suka saki sandunan da suke sarrafa jirgin dashi koda marfuza taga jirgin da suke ciki ya tsaya cak a saman ruwa baya gaba baya Sai ta juyo baya don ganin abinda yake faruwa Koda taga su sarki aryan sun saki matukan jirgin sai tayi dariya tace Sannunku mazanen kwarai kunyi kokari fa yanzu abindaya kamata kawai shine ku zauna kuci abinci abinku ni zan zauna naci gaba da

Chapter 8 of 13