Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
wanda ya shiga cikin kogin kankara Koda wuya tayi wuya baisan sa'adda ya kwallara karaba saboda bala'in da yaji ajikinsa kuma bisa dole ya rufe bakinsa ya daina karanto wadannan dalasiman tsafin Shima ya tsaya domin ganin me zai faru garesu in yaso sai suyi tunanin mafita A daidai wannan lokacin ne kuma sukaga wata irin iska mai karfi ta fito daga cikin katon ramin ta zukesu gabaki dayansu suka fada cikinsa Babu irin kokarin da basuyiba domin sauka daga bayan aljani zarikul laham Amma suka kasa saboda suma jin jikinsu sukayi kamar an daddauresu da murtuka murtukan sarkoki Suna kara nisa acikin ramin suna karajin tururin zafin na kara ninkuwa fiye da farko Koda sukayi nisa acikin sai sukaga wani irin katon dutse yana narkewa yanaci da wuta Kamar tafasashshiyar dalma Ita kanta wannan wutar abar tsoroce Domin launinta ma kalar makuba makuba ne sai ci take tana fallatsi a sama kamar tafasasshen mai Tun daga nesa kafin su riski inda wutar take sukaga wani katon dutse ya fada cikin wutar Koda saukar dutsen a cikinta sai wata iriyar kara ta tashi ji kake cuuuuuu!!!!!!!!! Kamar an zuba ruwa a cikin tafasasshen mai take shima wannan katon dutsen ya narke ya zama kamar ruwa Koda ganin wannan al'amari sai sukaji wani irin tsoro a karon farko ya darsu acikin zukatansu suka tabbatarwa da kansu cewa mutuwa zasuyi don haka duk sai suka rufe idanuwansu ME ZAI FARU DASU IDAN SUKA FADA CIKIN WANNAN MASIFAFFIYAR WUTAR SIHIRIN? SHIN YARIMA WALISU NA GASKIYA YANA FARAWA DAGA CIKIN BARCIN DA YAKE? ME ZAI FARU IDAN YAGA SABON WALISU YA KASHE SU GIMBIYA WALISA TUN KAFIN SU ISO DAJI NA FARKO? DAN JIN AMSOSHIN WADANNAN TAMBAYOYI SAI MU HADU A KASHI NA GABA NA WANNAN KAYATACCEN LABARIN MAI SUNA HATSABIBAN SADAUKAI DAGA NAKU HABIBULLAH KBR LIKE, COMMENTS AND SHARE*****---******** HATSABIBAN SADAUKAI CI GABAN ZUBAR DA JINI ***************6 PART B LBR ********---*********HABIBULAH KBR Lokacin da su gimbiya walisa suka runtse idanunsu. Saboda sun gama saddakar da cewa babu makawa sai sun fada cikin wannan wutar sun kone gabaki dayansu Sai daya rage baifi saura taku ashirin tsakaninsu da wutar ba Har ma sannan ta fara laso jikinsu tana konasu ba zato ba tsammani sai sukaji sun tsaya cak a saman iska ba tareda sun fada cikin wutar ba Cikin sauri suka bude idanunsu domin suga abin daya rukesu ya hanasu fadawa cikin wutar Kawai sai sukaga babu komai face iskar da take kadawa agurin daga can kuma sai sukaga wannan iskar ta sake zukosu zuwa sama ba tareda sun fada cikin wutar ba Daga can kuma sai sukaji an bushe da wata mahaukaciyar dariya Wacce saboda karfinta sai da sukaji kamar kunnuwansu zasu fashe Daga can kuma sai sautin dariyar ya dauke kawai sai sukaga wani irin abu yazo ya tsaya agabansu kamar madubi Acikinsa kuma sai sukaga fuskar yarima walisu yayinda yake kyalkyala musu dariya acikin madubin Sai da yayi dariyar ta isheshi sannan ya tsuke bakinsa ga barin dariyar Ya dubi su walisa yana mai nuna yu da tafin hannunsa Yana mai cewa Lallai sai yanzu na yarda cewa dukkanku taron kanananun kwari ne Yanzu ku da wannnan dan kankanin karfin sihirin naku kuke tunanin zaku iya yaki dani ?To ina mai tabbatar muku da cewa kun tabka babban kuskure Inda ace yanzu nayi niyar kashe ku da ko guda daya daga cikin ku bazai tsira daga wannan azabtacciyar wutar ba Dajin haka sai sarki fadarul munnar ya daka masa tsawa da cewa Kai yaro karyarka tasha karya baka isa ko mutum daya daga cikin mu ya hallaka a hannunka ba Dole mune muke da nasara akanka kuma koda ace ka jefa mu acikin wannan wutar taka bata isa ta iya cutar damu ba A zahirin gaskiya shi kansa sarki fadarul munnar ya firgita da lamarin walisu Kuma yana da tabbacin cewa idan suka shiga cikin wannan wutar ko tokar su ba zata tsira ba Kawai dai dakewa yayi kuma ya nuna tsantsar rashin tsoronsa Dajin haka sai walisu yayi masa wani dan guntun murmushi mai kama da murmushin mugunta yace Ammafa wannan taurin kan da kuma jiji da kan naka ya burge ni Tabbas walisa kai ta gado a gurin wannan dakewar zuciyar Dama ance barewa batayi gudu danta yayi rarrafe ba Amma ai shi kenan yanzu za'a banbance tsakanin aya da tsakuwa tunda har kuna ganin kuma wuyanku ya isa yanka kuna da abin dogaron da zaku kwaci kanku daga tarkona To ai sai ku gaggauta tahowa nan fadata idan har kun iso a raye ni zan farin ciki da hakan Yana gama fadin haka sai take hoton fuskar tasa ta dauke dif suka daina ganinsa gaba daya Sannan kuma gurin daya zaizaye wuta take ci acikinta Take gurin ya hade komai na gurin ya koma daidai kamar yadda yake a da Mai makon Aljani zarikul laham ya kada fuka fukansa yaci gaba da tafiya saiya tsaya cak a saman iska yana duru duru ya kasa yin gaba ko baya saboda razanar da yayi Da ganin haka sai sarki fadarul munnar ya daka masa tsawa yace Tsayuwar me kakeyi ne maza ka kara gaba don muga abubuwan daya zuba acikin tarkunan nasa kuma mu fasa su da karfin tsiya muje har fadar tasa Da jin haka sai zarikul laham ya kara kada fuka fukansa da karfin tsiya ya kara gaba cikin azababben gudu ya nufi daji na farko Wani irin gudu ya dingayi da karfin gaske sai da ta shafe rabin sa'a yana wannna gudun sannan suka tsinci kansu Acikin wani kasurgumin mai matukar muni da kuma abubuwa masu firgitarwa Tun afarkon dajin suka lura da yanayin sa yasha banban da irin dajijjikan da suka saba gani a rayuwarsu Domin ita kanta kasar cikin dajin motsi takeyi sai kace tsutsa Kallo daya zaka yiwa dajin ka san cewa dole akwai mugayen halittu Koda isowarsu wannan dajin sai aryan, marfuza da gimbiya walisa sarki fadarul munnar suka kalli junansu domin sun san cewa dole akwai wani mugun abin acikin sa Shi kuwa aljani zarikul laham saiya rage karfin gudun nasa ya dinga tafiya kamar baya son yi Da ganin haka sai jaruma marfuza tace dashi kai kuma menene yasa ka rage gudu? Dajin wannan tambayar sai ya juyo ya dubeta yace ya shugabata ai wannan gurin da gani kinsan babu tambaya domin dolene a sami abubuwa masu hatsari acikinsa don haka dolene mu sawa kanmu nutsuwa idan har munaso mu fita daga wannan daji lafiya Kafin ya gama fadin abinda yake bakinsa tuni yaji an kawo masa wata iriyar mahaukaciyar wafta Cikin bakin zafin nama ya kucewa harin da aka kawo masa In badon yayi saurin kaucewa ba da tuni an tsarga wuyansa kan nasa daga jikin gangar jikinsa Ba komai ne ya kawo masa wannan harin ba face wani Irin gajeren dodo amma kuma hannunsa yana da mahaukacin tsawo domin ya ninka gangar jikin sau goma a tsawo Koda su sarki fadarul munnar suka sunkuyo da kawunansu kasa Sai suka wangame bakinsu suna kallon abin mamaki domin wadannan dodannin ne suka dinga bubbukowa daga cikin kasar gurin Fitar burgu daga cikin rami dukkan wadannan dodannin jikinsu gaba daya an halicceshi ne da duwatsu masu matukar karfi Kai da ganinsu kasan cewa dolene sh kasance sihirtattu kuma masu matukar juriya Kuma wani abin da zai baka tsoro da kamar yadda wadannan dodannin suke da matukar karfin tsalle domin tsalle daya kawai suke Sai ka gansu sun tashi sunyi kololuwa a sama ta yadda komai nisan da tsuntsu ko kuma aljani yayi bai isa ya iya ketarewa ta saman dajin ba face sun gama dashi Tun daga nesa wadannan dodannin suka ankara da zuwansu sarki fadarul munnar Don haka sai sukayi kwanton bauna suka zauna zaman jiran isowarsu sarki fadarul munnar domin suyi musu kwaf daya Koda wadannan dodannin suka gama bayyana akan doron kasa Sai suka daka tsalle alokaci guda suka tashi sama suka yanyame aljani zarikul laham Dasu gimbiya walisa da nufin suyi gunduwa gunduwa da sassan jikinsu Suna masu kai masa mahaucin sara da suka da wasu dogayen adduna da suke hannunsu Koda suka kawo musu mugayen hare hare, cikin zafin nama sai su gimbiya walisa suka zare nasu makaman yakin da suke jikinsu Suka kare harin da dodannin suka kawo musu koda makamansu suka hadu da juna take wata iriyar kara mara dadin ji tare da tartsatsin wuta kamar ana dukan karfe a makera suka tashi Take cikin karfin tsiya suka tarwatsa dodannin suka tarwatse suka basu hanya Amma saboda naci irin na dodannin sai sukayi kukan kura lokaci guda Suka daka tsalle suka kewaye aljani zarikul laham a sama suka hanashi samun damar da zai kara koda tafiyar taku guda Saboda tsananin karfin da suke dashi bisa dole aljani zarikul laham ya saki fuka fukansa ya sauko kasa domin a hadu guri guda ayi dauki ba dadin da zasuyi Koda dirarsa akan kasa sai suka far masa gaba daya akachame da azababben yaki Nanfa guri ya rincabe in banda sautin karar karafiiyar karafa babu abinda kunne keji Duk inda su walisa suka ratsa saidai kaga suna banke dodannin da karfin tsiya Amma da zarar sun fadi sai kaga sun kara mikewa zumbur Nanfa kura ta turnuke guri ya yamutse kura ta tokare sararin samaniya yadda koda tafin hannunka ba zaka iya gani ba saboda azababben yakin da suke yi Sautin gurnanin dodannin ya cika dodon kunne gami da wani irin sautin gurnani da dodannin suke yi Wanda shi kadai kan iya razana mutum idan mace mai tsohon ciki ta ji wannan gurnaninda sukeyi take zata haife abindake cikinta Idan kuwa karamin jarumi ne zai iya haukacewa ta dalilin wannan fafatawar da sukeyi Saboda irin bakin gumurzun da sukeyi kasa ta dinga girgiza kamar ana yakin duniya Da zarar makamansu sun sauka ajikin dodannin saidai kaga tartsatsin wuta ya tashi Gumurzu yakai gumurzu duk inda su sarki fadarul munnar suka ratsa sai dai kaga suna banke dodannin Amma duk wannan abin sai ya zama na banza domin ko kadan makamansu baya tasiri ajikin dodannin Su kuwa su walisa badon suna da zafin nama ba da basu isa su yi koda dakika guda ba agaban wadannan dodannin Saboda duk da kasancewarsu gajeru suna da matukar karfin damtse, naci da kuma taurin kai A wannan lokaci aljani zarikul laham yaga ta kansa saboda duk da kasance sa aljani sai daya rai na kansa agurin wadannan dodannin Sai da takai ga cewa su gimbiya walisa ne suke hada karfi da kafe wajen taimaka masa suna kareshi daga sharrin wadannan dodannin A wannan lokaci ne sarki fadarul munnar ya nunawa su gimbiya walisa banbancin tsohon kashi da kuma sabo Domin duk wanda ta daka daga cikin dodannin saidai kaga ya tashi sama kamar an doka kwallo sama ya fadi a can nesa Su kuwa su walisa kawai kuzari suka fishi saboda sunfishi ji da samartaka Duk da cewa suna samun nasarar dukan dodannin sai hakan ya zama na banza Saboda sun kasa samun nasarar koda kashe daya daga cikin dodannin domin kaifi da tsini basa tasiri ajikinsu Amma saboda taurin zuciya sunki yarda su sallama kansu ga wadannan dodannin Kuma babu abinda yake dada tayar musu da hankali ba Face tsananin yawan da dodannin suke dasu kuma basu isa su iya ratsawa su wuce wannan dajin ba face sun kashe dodannin gabaki dayansu To abin tambayar anan shine tayaya zasu iyatarwatsa su? Tambayar da sarki aryan yayiwa kansa kenan kuma bai da amsar wannan tambayar Haka dai suka shafe sa'o'i uku suna wannan fafatawar har tsawon wannan lokaci basu sami damar koda kashe daya daga cikin dodannin ba Kuma a wannan lokaci dukkansu sun fara gajiya kai hatta shi kansa sarki fadarul munnar da aljani zarikul laham saida sukaji sun fara gajiya a wannan lokaci Har saida yayi mamakin wannan gajiyar da yayi alhalin yasan cewa yana iya shafe mako guda yana. Yaki ba tareda ya gaji ba Abinda bai sani ba shine wadannan ba irin halittun daya saba gamuwa dasu bane Koda yaga lokaci na neman kure musu sai ya fara karanta dalasiman tsafi yana watsawa dodannin Amma da zarar sihirin nasa ya sauka ajikinsu sai kaga yaki yayi tasiri ajikin nasu Ana cikin wannan halin ne kawai sai wani dodo mai tsananin naci ya dankarawa sarki aryan sara agadon bayansa Nantake ya kwallara ihu saboda zafi da zugin da yaji Bai san sanda ya takarkare ya kwarara wata kabbara da karfi ba Saboda karfin kabbarar saida gaba daya dajin yayi tsit hatta shima sarki fadarul munnar saida yaji gabaki daya tsigar jikinsa ta tashi kuma jikinsa yayi sanyi sakamakon jin sautin kabbarar da yayi Cikin bakin zafin nama sarki aryan ya daka tsalle sama ya kaiwa dodannin wani mahaukacin sara sai gashi lokaci guda takobin nasa ta tsarge guda goma a alokaci guda Take duk kawunansu suka rabu da gangar jikinsu suka tashi sama kamar anyi watsi dasu Koda ganin abindaya faru sai sai suma su walisa suka fara karanta addu'o'i acikin zukatansu domin neman taimakon ubangiji Ai kuwa faruwar hakan keda wuya sai fadan yasha banban domin wata irin ragargaza suka dinga yiwa dodannin Duk inda suka ratsa saidai kaga kawuna suna zubewa kasa kamar ana sassabe a gona Jini ya dinga fallatsi. Asama yana zuba sai mace ana ruwan sama Kasa ta dinga dudufniya a wannan lokaci koda wahala tayi wahala Sai dodannin suka daina gurnani suka koma ihun fitar rai Sai gashi sun zamewa dodannin alakakai ko kuma once wasan sarki ya hana dawa tsaiwa suka dingayi da dodannin Shi kuwa sarki fadarul munnar duk da kasacewar shima yana saran dodannin amma ko kadan makaminsa baya yin. Ko kwarzane ajikinsu don haka da sukaga shi da aljani zarikul laham ne kadai basa iya cutar dasu Duk sai suka harzuka sukayi gunji suka falfala da gudu zuwa kansu Suka lullubesu kamar taron kudan zuma suna kai musu sara da suka tako'ina domin su sami abincin kalaci Koda suka ga abjnsa yake shirin faruwa sai sarki fadarul munnar da zarikul laham sukayi kukan kura gami da karaji Sukayi katantanwa atsakiyarsu Take suka tarwatsa su gabaki dayansu sai gasu suna yawo a saman iska suna fadowa kasa Amma saboda tsananin bakin nacin da suke dashi sunki hakura kawai dada tasowa sukeyi suna kara lullubesu domin da zarar sun gaji anan gurin zasu gididdiba namansu su cinye don haka sai suka bar inda su walisa suke Koda jaruma taga abindake faruwa gasu sarki fadarul munnar Saita kwarara uban ihu wanda yake firgita maza acikin filin daga Sannan ta falfala da gudu zuwa inda su sarki fadarul munnar suke tana maj karanta wasu addu'o'i acikin zuciyarta domin neman taimakon ubangiji ai kuwa sai take taji wani irin sabon kuzari ya shiga jikinta Yana isa inda ake suke wannan bakin artabu sai ta daka tsalle sama Ta dira a tsakiyar dodannin tana mai kai musu sara da suka Cikin bakin zafin nama, juriya da bajinta adaidai wannan lokaci suma su sarki aryan suka lura da halinda su sarki fadarul munnar ke ciki Don haka suma sai suka tarwatsa ragowar dodannin da suke kewaye dasu suka taho inda marfuza take domin tayata yakar wadannan dodannin Ai kuwa koda suka hadu guri guda sai sukayita shayar da dodannin gidauniyar mutuwa saboda karfin addu'o'in da suke karantawa A wannan karon basu kara shafe wasu sa'a biyu ba suka gama karar da dodannin gabaki dayansu Ya zamana dajin in banda karnin jinin dodannin babu abinda hanci yake shaka Ita kanta kasar dajin sai data rine da jini gabaki dayanta Koda suka gama da wannan rukunin na farko basu taya wani bata lokaci ba domin su huta Kawai sai suka mike dukkansu suka goge jinin dake jikin makaman yakinsu Sannan suka tashi suka haye bayan aljani zarikul laham Ya daukesu suka nufi daji na gaba saida sukayi tafiyar sa'a hutu Sannan suka isa rukunin daji na biyu wanda babu komai acikinsa Face wasu manyan duwatsu masu kama da tsaunika amma kuma abin mamakin shine gabaki daya wadannan duwatsu ba a zaune suke akan kasa ba Suna yawone a saman iska kuma kowacce kusurwa daga jikinsu zakaga dutsen yana aman wuta ta gurin Duk abin kuwa da wutar ta sauka akansa take kuwa zakaga ya kone kurmus hatta tokarsa ma ba zaka gani ba Koda kuwa karfene MAI SAI FARU A WANNAN DAJI? WADANNE IRIN HALITTUNE SUKE RAYUWA ACIKINSA KUMA SUWAYE ZASU IYA KETARE WANNAN DAJIN A RAYE? DON JIN AMSOSHIN WADANNAN TAMBAYOYI SAI MU HADU A KASHI NA GABA DAGA NAKU HABIBULLAH KBR (YARON MARUBUTA) LIKE, COMMENT AND SHARE*********HATSABIBAN SADAUKAI CIGABAN ZUBAR DA JINI ******************************6 PART C LBR ******************HABIBULLAH KBR Gabaki daya dajin haka yake wani irin hucin zafi yana dukan fatarsu Koda isowarsu wannan daji sai aljani zarikul laham ya tsaida fuka fukansa Sakamakon ganin wasu manya manyan tsuntsaye daya gani masu girman gaske Kowanne daya daga cikinsu girmansa yakai girman rikakkiyar mikiya Kuma suma jikinsu gaba daya ci yake da wuta kamar yadda duwatsun dajin suke Da zarar daya daga cikinsu ya bude bakinsa yayi ruri saidai kaga Tartsatsin wuta yana tashi kamar ana kira a makera Idanunsu ma jajur suke kamar garwashin wuta duk inda ka hanga acikin wannan dajin babu abinda zaka gani face wadannan tsuntsaye da kuma duwatsu Domin duk tsuntsayen daga cikin duwatsun wutar suke fitowa Kuma ba tareda yayi musu komai ba saboda suma jikinsu na wutar ne Kasan dajin ma babu komai face wannan wutar tsububu Duk wanda ya kuskura ya fada cikinta take anan zai kone Koda ganin wadannan abubuwa sai su kansu su walisa Suka saki bakinsu suka tabbatar da cewa tabbas yau sun shiga tsaka mai wuya Gurin da babu wanda zai iya cetonsu face ubangijin musulunci Domin suna da tabbacin cewa a wannan guri tsafi ba zaiyi tasiri ba tunda gidansa sukazo Shi kuwa sarki fadarul munnar sai ya fara karanta wasu dalasiman tsafinsa Domin su sami kariya daga sharrin wadannan tsuntsaye A daidai wannan lokacin ne tsuntsayen suka kura dasu sarki fadarul munnar Don haka sai nantake suka falfalo da gudun tsiya zuwa kansu Suna wani irin kuka mara dadin saurare wanda shi kadai ma zai iya kashewa mutum dodon kunne Ai kuwa sai suma suka falfala kan tsuntsayen da gudun gaske Lokaci guda suka hadu a tsakiyar dajin suka kaure da mahaukacin fada Guri ya rincabe in banda sautin kukan tsuntsayen babu abinda kunne keji Tsuntsayen suka saka aljani zarikul laham atsakiya suka hanashi yin gaba ko baya ta ko"ina kawo masa hari sukeyi Da zarar su walisa sun kaiwa tsuntsayen sara saidai kaga makamin nasu ya ratsa jikin tsuntsun da suka sara ta wuce sannan jikinsa ya sake komawa ya hade kamar babu abindaya taba samunsa Idan kuwa suka saka hannu suka daki jikinsu dashi take hannunsu yake konewa Bisa dole suka daina dukan tsuntsayen da hannuwansu domin sune suke jin zafin dukan Haka dai suka daure sunata faman yaki da wadannan sihirtattun tsuntsaye tun da hasken rana a gari har dare yazo ya raba basu daina wannan yakinba Kuma suma su gimbiya walisa basu iya kashe ko guda daya ba daga cikin tsuntsayen Ana cikin wannan haline adaidai lokacin da gumurzu yakai gumurzu Kuma hasken gari ya dauke ya zamana ko tafin hannunka ba zaka iya gani ba Saboda duhun gari kawai sai daya daga cikin duwatsun da suke aman wuta acikin dajin yayi bindiga Take sai dutsen ya tarwatse kawai sai wutar dake cikinsa Ta zubo akan fuskar aljani zarikul laham nantake sai fuskarsa ta babbake gabaki dayanta Ta zama toka shi kuma ya saki fuka fukansa domin fadowa kasa Don tuni ya dade da shekawa barzahu koda sarki fadarul munnar yaga abinda ya faru Ga aljani zarikul laham sai hankalinsa yayi mummunan tashi ya dinga Karanto wasu sirrikan tsafi a zuciyarsa, Su kuwa su gimbiya walisa basu san sanda suka fara yiwa allah kirari ba Suna mai neman taimakon sa domin sun san cewa ba zasu iya kwatar kansu daga wannan bala'in da suka shiga ba Kafin su gama addu'ar tuni zarikul laham ya gama narkewa ya fado cikin wutar Gimbiya walisa ce ta fara dira akan kasa ba zato ba tsammani Sai taga ta zauna daram acikin wutar ba tareda wutar ta cutar da ita ba Tana daga kanta sama sai tayi arba da mahaifinta yana fadowa Kuma ta tabbatar da cewa idan har ya fada cikin wutar nan konewa zaiyi Domin tsafinsa ba zai taimakeshi ba ,kodayin wannan tunani sai ta daka tsalle Sama kamar ta kasance tsuntsuwa ta cafo mahaifin nata ta goyashi agadon bayanta sannan ta dira akasa Suma su sarki aryan da jaruma marfuza haka suma sauka acikin wutar ba tareda tayi musu komai ba Kafin suyi wani yunkuri tuni tsuntsayen sun gama lullubesu an sake kacamewa da Masifaffen yaki fiye da wanda sukayi abaya domin a wannan lokaci su kansu tsuntsayen a matukar fusace suke Haka suma su gimbiya walisa shi kuwa sarki fadarul munnar Kwallar takaicice ta zubo masa domin ganin cewa wannan ce rana ta farko a rayuwarsa daya kasa taimakon kansa saidai wani ya taimaka masa Domin ya tabbata tsafinsa bai isa ya kwaceshi daga sharrin wannan dajin wutar ba In badon 'yarsa gimbiya walisa ta ceceshi ba da tuni ta sheka barzahu Haka dai su walisa suka cigaba da karanta addu'o'in neman taimakon ubangiji acikin zukatansu Don haka bisa mamaki sai sukaga duk tsuntsun da suka sara da makaminsu take yake tarwatsewa ya kama da wuta kurmus ya mutu Kafin cikar dakiku sittin sun gama kashesu gabaki dayansu Suna gamawa da tsuntsayen ne kuma sukaga wadannan duwatsun wutar sun tahi kansu gadan gadan tun kafin su iso gimbiya walisa bata san sa'adda ta kwanto sandar SADAUKI HASSANUL BASARI Ba daga bayanta ta ruke ta da hannayenta biyu Koda duwatsun wutar suka iso saita dinga kai musu duka da wannan sandar Take duk wanda ta doka ya dinga bindiga yana faduwa cikin wutar sannan kuma kaga ya bace bat kamar bai taba wanzuwa ba A haka ta suka gama da wannan dajin gabaki dayansa Sannan suka tashi suka kara gaba suka ci gaba da tafiya Saida suka shafe wata guda suna tafiya busa kafafunsu Kuma suna ratsawa ta cikin manyan dajujjuka masu hatsari wadanda sukafi Wadanda suka ratsa a baya hatsari sosai, domin ko wanne daji halittun dake cikinsa Sunfi na baya hatsari, yawa da kuma karfi amma a haka da kyar da sidin goshi suka wace gabaki daya wadannan dajujjukan suka isa daji na karshe wanda anan ne sabuwar fadar YARIMA WALISU take A cikin tsakiyar wani katon teku wanda ruwan cikinsa Ya cika ya batse har wani hankoro ruwan yakeyi idan igiyar ruwa tana kadawa Ruwan kuma har wani irin tururin sanyi yakeyi domin gabaki dayansa sanyi ne dashi Tun a kan saman ruwan idan ka kura ido zaka dinga ganin wasu irin manyan dorunonin ruwa suna yawo a saman ruwan Ba tareda sanyin ruwan kuma ya cutar dasu ba domin suma duk jikinsu sanyi ne dashi Dole saika ratsa ya cikin wannan teku sannan zaka riski fadar yarima walisu domin a tsakiyar sa take Koda isowarsu wannan guri duk sai suka tsaya sukayi cirko cirko Kuma gabaki daya dajin babu bishiya ko daya wacce zasu hada kwale kwale da ita Suna kallon wannan takun da kuma fadar da yarima walisu yake ciki Suna nazarin yadda zasu iya ketareshi har su shiga cikin wannan fadar Daga can sai walisa ta dubi sarki fadarul munnar tace ya abbana shin yanzu ka gani da idanunka abindake cikin wannan teku Idan har munason ketareshi dolene mu ratsa ta cikinsa Kai kuma yanzu babu makawa idan ka shiga cikin sa zaka iya rasa rayuwarka Domin sihirin da kake takama dashi nan ne gidansa ba zai taba tasiri ba a wannan guri Domin kaimaka gani da idanunka abaya cewa sihirin ka baya tasiri tunda muka shigo daji na farko na wannan daji Inbadon taimakon ubangijin musulunci ba da dukkanmu mun dade da shekawa barzahu Kodajin wannan batu sai sarki fadarul munnar yayi wani yake Cikin jin kunya yace yake 'yata hakika duk maganarda kika fada gaskiyace Amma inaso ki sani nima bawai ina jayayya da lamarin ubangijin sabon addinin da kuka shiga bane Amma inaso na sami cikakkiyar hujjar da zanyi imani dashi Wannan ne yasanya na baro gida na biyo ku domin naga ranarda zata zamo karshen zalunci a duniya gabaki daya Wannan shine babban burina tun kafin a haifeku bayan an haife ku kuma na dinga baku horon yaki har kuka kai matakin da kuke

Chapter 11 of 13