Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
a kowanne fanni karfin damtse da kuma karfin sihiri Amma yanzu tambayar da nakeson yi miki itace a ina kika samu sihirin tsafi mai karfi? Dajin wannan tambaya sai itama walisa ta sami guri ta zauna sannan ta dubeshi Tace Kada fa ka manta ni 'yace ga sarki fadarul munnar ka sani cewa tun muna jarirai ake shayar damu tsumin tsafi tun kafin mu fara shan nonon mahaifiyar mu Haka aka ci gaba da yi mana har zuwa girman mu ba'adaina tsuma mu acikin tsumin tsafi ba ni da yarima walisu Hakika nima nayi mamakin yadda ruhin boka sahibul ukub Ya iya shiga jikinsa har yake sarrafa shi, Yanzu dai zaifi kyau mu ajiye batun hira a tsakaninmu mu samu muyi barci domin rama barcin da yake cikin idanun mu Ku sani cewa idan har muna cikin wannan daki babu mahalukin da zai iya shigowa cikinsa komai karfin sihirinsa Saidak yarima walisu kadai shi dinma kafin ya shigo sai mun san da zuwansa ta hanyar wannan dutsen Nantake ta sanya hannu acikin aljihunta ta dauko bakin dutsen da boka makassar ya bata tun kafin ta baro gida Kunga wannan dutsen shine zai yi mana ishara da zuwansa idan har ya bayyana Tana gama fadin haka sai ta sami guri ta kwanta ba tareda ta kara cewa komai ba Koda sukaji wannan bayani nata sai duk suka cika da al'ajabi Suka tabbatar da cewa tabbas walisa da walisu sun sami horo sosai da kuma kariya daga iyayensu Don haka dole ta fita daban dasu Take suma duk suka sami guri suka kwanta Abinka da gajiyayyu Aikuwa suna kwanciya sai barci mai nauyi ya dauke su Basu farka ba saida safiya tayi lokacin rana ta gama budewa ta haska ko'ina Acikin dakin sannan suka farka daga barcin aikuwa suna farkawa kuwa atake duk suka hada kayayyakinsu suka nufi birnin labtarul halkam tun daga nesa suka fara hango dakaru atsaitsaye abakin kofar birnin ruke da makaman yaki a hannunsu sai muzurai sukeyi Da ganin haka sai jaruma marfuza ta dubesu tace Zaifi kyau dukkan mu mu boye siffofinmu don kada wadannan dakarun su san gaskiyar su waye mu Domin idan har suka sani ba zasu bari mu gama aikin da mukazo yi da wuri kuma acikin sirri ba Zai fi kyau duk mu sauya kamanninmu tunda ba zama mukazo yi cikin birnin nan ba Har yanzu akwai aiki mai yawa agaban mu, kodajin wannan shawara sai dukkaninsu suka aminta da shawararta Don haka take dukkansu sai suka rikide suka koma siffar tsuntsu hankaka Sannan suka tashi sama suka shiga cikin birnin Duk wannan abu dayake faruwa dakarun dake tsaye abakin kofar basu kula ba Saida tsuntsayen suka zo giftawa ta saman kofar inda masu gadi suke Sai kawai sarkin kofa ya daga kai ya karewa hankakin kallo Nantake yaji zuciyarsa bata sami nutsuwa dasu ba don haka dole akwai alamar bakin haure ne su ba tsuntsaye ba don haka sai kawai ya girgiza kansa sannan ya koma kan aikin da yakeyi Lokacin da wadannan hankakun suka gifta ta saman dakarun da suke tsaron kofa basu wuce ko'ina ba Sai cikin babbar kasuwar birnin don haka sai hankakun suka sauka abayan wata rumfa acikin kasuwar Sannan suka rikide suka koma ainihin siffarsu suka fito daga cikin kasuwar Kai tsaye suka zarce cikin wata rumfa inda suka tarar ana sayar d abinci Nantake suka karasa cikin rumfar suka zauna mai sai da abincin tazo ta tambayesu mai suke bukata Kowa ya fada mata kalar abincin da yakeso Cikin kankanin lokaci kuwa matar ta kawo musu abincin Sukaci suka bata kudinta sannan suka tashi suka kara gaba Koda suka nausa cikin wannan kasuwar sai suka cika da mamaki Domin gani sukayi kasuwar ta fita daban da kalar kasuwannin da suka sani Babu abinda ake kwance hajarsa acikin wannan kasuwa face tarin litattafai marasa adadi maimakon makaman yaki, fatun dabbobi ko kuma kayan abinci Wannan ne ya nuna musu cewa su wannan birnin babu gasar da sukeyi face gasar ilimi Domin sai ka sami mutum guda wanda ya iya magana da harshe guda ashirin Kuma duk kalar littattafan da mutum yazo dasu da wuri ake siyesu Wannan al'amari ba karamin basu mamaki yayi ba Don haka sai suka ci gaba da tafiya acikin kasuwar suna kallon yadda mutane suke gudanar da rayuwarsu Suna cikin tafiyar ne suka hango wani guri ya cika makil da jama'a suna kallon wani abu a tsakiya Cikin sauri walisa tace dasu aryan Mai zai hana muje can gurin muga wacce irin gasar jarumtakar ake gudanar wa Cikin sauri kuwa dukkansu suka dunguma suka nufi wannan guri Suna zuwa duk sai sukaga abin mamaki domin ba komai ake yi ba face gasar ilimi Tsakanin wasu yara wadanda shekarunsu ba zasu gaza goma sha biyar ba su hudu Kowannensu a zaune akan mumbari suna ta musayar yare Kowanne daga cikin wadanan yara yanajin yarurruka sama da guda ashirin Su kuma mutanen gari sun kewayesu suna alkalanci domin suga wanda zai kada wani Da ganin wannan al'amari sai gimbiya walisa tayi murmushi ta dubi sarki aryan tace Hakika kowa da kiwon daya karbeshi, kamar yadda abirnin ka ake hada gasar jarumtaka su kuma wannan birnin gasar ilimi ce burinsu, duk wanda baiyi yawon duniya ba bai more kallo ba Dajin wannan batu sai sarki aryan yace kwarai kuwa maganarki gaskiyace Adaidai wannan lokacin ne sukaji filin ya cika da shewar mutane Duk da cewa basu san maganganun da ake tattaunawa akansu ba Amma sun fahimci cewa daya daga cikin yaran wanda akewa lakabi da himsad shine ya cinye gasar Ga mutane nan sai cin cirindo akeyi wajen daga shi yayin da aka tafi kaishi can gidansu anata faman yi masa kirari Da ganin haka sai jaruma marfuza tace dasu walisa ai zama bai kamamu ba dolene muma mu bi wannan yaron domin muga inda zasu kaishi in yaso sai mu nemi alfarma agurinsa ya sanar damu abinda mukazo nema Kodajin wannan batu sai dukkansu suka amince da shawarar data bayar ma'ana suka bi yaron a baya Har suka isa gidansu Bayan kowa ya watse sai suka karasa kofar gidan suka kwankwasa ta da hannunsu Basu dade ba saiga yaron ya fito koda himsad yayi arba dasu gimbiya walisa saiya firgita Har yaja da baya da nufin ya gudu sai walisa tayi caraf tace Kada ka firgita yakai himsad mu baki ne kuma bukatace damu agareka Muna fatan zaka taimaka mana Dajin wannan batun sai himsad ya kara dubansu cikin rashin fahimta yace Wacce irin bukatace daku agareni? Take walisa ta dauko masa wannan karamin littafin ta mika masa shi a hannunsa tace Shin kasan yaren da aka rubuta littafin nan? Himsad ya mika hannu ya karbi littafin daga hannunta ya kare masa kallo sosai yana nazarinsa Daga can sai ya dago da kansa ya dubesu yace Yaku wadannan baki gaskiya na tausaya muku domin ban taba jin labarin irin wannan yaren da kukazo dashi ba Kuma kaf cikin birnin nan bana tunanin akwai wanda yasan wannan yare ko kuma zai iya koyar daku Kodajin wannan batu sai hankalinsu ya dugunzuma suka dubeshi sukace Muna rokonka da darajar abin bautarka ka taimaka mana idan har bukatar mu ta biya zamu biyaka ladan kudade masu yawa Dajin haka sai himsad yace Kuyi hakuri babu abinda na sani game da wannan yaren Yana gama fadin haka saiya juya ya shige cikin gidansu Yabar su gimbiya walisa a tsaye sunata faman zare idanu Daga can sai sarki aryan yace ai shikenan sai mu ci gaba da tafiya ni na Tabbata mai nema yana tare da samu ba zamu bar wannan garin ba face bukatar ta biya Yana gama fadin haka sai ya wuce gaba suma su gimbiya walisa sai suka bishi abaya Suna tafiya suna tsayawa suna tambayar mutane kai a wannan ranar saida suka yini suna tafiya ba tareda sun sami nasarar abinda suke nema ba Yamma tanayi sai suka sami gidan haya wanda zasu kwana aciki Duk wannan sunturi da sukeyi ashe akwai wani kasurgumin barawo Yana biye dasu duk inda zasu shiga domin ya kware sosai wajen iya sata da kuma sanin manyan mutane Don haka tun daga sanda su gimbiya walisa suka shigo cikin birnin labtarul halkam Yasan cewa dolene su kasance jinin sarauta don haka sai ya kudurce aransa cewa Duk inda zasu shiga sai ya bisu kuma ya sace duk dukiyar da take hannunsu Ana kiransa da suna kusail, mutane da dama sun sha dana masa tarko akan su kamashi saboda yadda ya addabesu da sata amma sun kasa saboda irin karfin sihirinsa Lokacin da kusail yaga su marfuza sun kama gidan haya Sai ya salallabo ya biyosu har cikin gidan ba tareda sun sani ba Dare na rabawa lokacin daya tabbatar da cewa mutane sun kwanta barci Sai ya fito daga cikin maboyarsa ya nufi dakin dasu gimbiya walisa suke ciki Yana mai karanta wasu dalasiman tsafi wadanda indai yayi su babu mahalukin daya isa yaji sautin sahun kafarsa, ko kuma ya iya ganinsa da ido ba Sannu a hankali ya isa bakin kofar dakin yana isa yasaka hannunsa ya murda mabudin kofar dakin ya kutsa kansa ciki kai tsaye HAKIKA MASU IYA MAGANA SUNYI GASKIYA DA SUKACE KOMAI SAMMAKONKA WANI A TAFE YA KWANA KUMA RANA DUBU TA BARAWO CE RANA DAYA TAK KUMA TA MAI KAYA INDA ACE WANNAN BARAWON YASAN ABINDA ZAI FARU DA BAIYI GANGANCIN AIKATA SATA ACIKIN WANNAN GIDANBA DOMIN WADANDA SUKE CIKINSA BA KANWAR LASA BANE Lokacin da kusail ya shiga cikin wannan daki sai ya tarar da cewa duk su gimbiya walisa sun sun kwanta barci Abinsu har da minshari saboda jin dadin barcin Kai tsaye ya wuce inda yaga sun ajiye kayayyakinsu Ya saka hannunsa ya fara dubawa cikinsu acikin jakar farko daya fara dubawa bai sami kudade masu yawa ba Domin jakar jaruma marfuza ce amma koda ya bude ragowar jakunkunan sai ya kamu da farinciki mara misaltuwa Domin gani yayi gaba daya jakunkunan cike da tarin dukiya wandada suka hada da darhami ,zinare da kuma lu'u lu"u Saboda farinciki baisan sanda ya tuntsure da dariya ba Wannan shine babban kukuren daya aikata Domin abinda bai sani ba shine sihirin tsafinsa ba zaiyi aiki akansu gimbiya walisa ba Lokacin da kyalkyala wannan dariyar dukkansu saida sukaji sautinta amma basu farka ba Domin a zaton su Acan waje akeyinta, sannan suka cigaba da barcinsu Cikin farinciki kusail ya juyo da baya da shirin fita daga cikin dakin Har ya gifta inda su walisa da sarki aryan suke kwance yazo daidai jaruma marfuza Sai kawai yasa kafarsa ya taka kafarta da karfi saboda mugunta kuma yana zaton bata iya ganinsa Sannan ya wuce gaba yana mai murmushin farinciki Zafin wannan takun ne yasa marfuza ta watstsake daga barcin da take Ahankali ta bude idonta cikin shammace, tana bude idanun nata sai tayi arba da wani matashin saurayi dauke da jakunkunan guzurinsu ahannunsa Ya kama hanya da nufin ficewa daga cikin dakin har ya daga kafarsa zai sakata awajen kofar dakin sai tayi sauri ta kwanto wata doguwar sarka daga jikin kugunta ta jefa masa Take sarkar ta tafi da gudun tsiya ta hardo wuyansa Sannan jaruma marfuza ta finciko sarkar da hannunta guda Sai gashi ta finciko kusail kamar ta finciko sillen kara Ta gwarashi ajikin bango sannan ya dawo kan kasa kawunansa a durkushe agaban kafafunta Sautin gwaruwar tasa ce ta farkar dasu gimbiya walisa daga barcin da sukeyi tareda zare makaman yakinsu don suga abinda ya kawo musu farmakin bazato Cikin mamaki duk suka mike tsaye yayinda sukaga marfuza ta dora wuka akan wuyansa Tana tambayar sa abindaya kawoshi Cikin firgice da razana kusail yace kiyi mini rai yake wannan jaruma na rantse da abin bautarki barawo ne ni sata nazo yi muku Dajin wannan magana sai ranta ya baci harta motsa hannunta da nufin yanka wuyansa Sai gimbiya walisa ta dakatar da ita, take marfuza ta dauke wukarta daga kan wuyansa Har saida jini ma ya digo kasa daga jikin wukar saboda saura kiris ta yanka makogaronsa don tsabar kaifinta Sannan gimbiya walisa ta karewa barawon kallo alokacin dataga gabaki daya jikinsa kyarma yakeyi saboda tsabar razanar da yayi kamar kace kyat ya saki futsari a wando Ta dora hannunta na dama akan kafadarsa tace yakai kusail yanzu haka kana da zabi guda biyu Koda yaji ta kama sunansa sai ya cika da mamakin yadda akayi ta san sunansa amma daya tuna aikine na sihiri sai yayi shiru da bakinsa Walisa ta ci gaba da cewa Acikin zabin nan guda biyu dolene kayi daya Kodai ka taimaka mana akan bukatar data kawomu garinku ko kuma yanzun nan wukar da take hannun jaruma marfuza ta zabtare makogaronka Cikin rawar dari kusail ya dubeta yace Yake wannan 'yar sarki wacce bukatace daku agareni ki gaggauta sanar dani ita Ni kuma zanyi kokari duk wahalarta sai na biya muku ita muddin zaku barni da raina Kodajin haka sai walisa tayiwa sarki aryan inkiya Nantake shi kuma yaje ya daga wata shimfida wacce duk kallon kurillanka baknisa kace an ajiye wani abin akarkashinta ba Kawai sai ya fito da sandar sadauki hassanul basari da kuma wannan karamin littafin Ya nunawa kusail yace Abin da muke bukata kayi mana shine ka kaimu gurin mutumin da kasan zai iya koya mana wannan yaren Idan har kayi haka to ka tsira daga mutuwa kodajin haka Sai ya karbi littafin ya ruke shi a Hannunsa ya kura masa ido yana tunani Daga can kuma sai yayi murmushi yace indai wannance bukatar ku to na tsira Ku sani cewa kaf birnin nan babu wanda zai iya koyar daku wannan yare face mutum daya Wato dattijo kusaid shine kadai mutumin da kaf birnin nan wanda zai iya koyar dakai wannan yare Nima nasan wannan sirribne sakamakon wani lokaci na taba zuwa giftawa ta gurin da yake zaune alokacin yana bitar wani littafi wanda rubutunsa anyi shine da irin yaren da akayi wannan rubutu Tabbas idan mukaje wajensa bukatar ku zata biya SHIN KUSAIL YANA KAISU GURIN WANNAN MALAMIN ? TSAWON KWANA NAWA ZASU DAUKA SUNA NEMAN WANDA ZAI KOYAR DASU WANNAN ILIMIN? SHIN KUSAIL YAUDARARSU YAKE SHIRIN YI KO KUWA GASKIYA YAKE FADA MUSU? DON JIN AMSOSHIN TAMBAYOYIN NAN SAI MU HADU A KASHI NA GABA DAGA NAKU HABIBULLAH KBR ASHA KARATU LAFIYA LIKE, COMMENTS AND SHARE******************HATSABIBAN SADAUKAI CI GABAN ZUBAR DA JINI ********************4 PART C LBR *****************HABIBULLAH KBR Kaf cikin birnin nan kusaid ne kadai ya iya wannan yare saboda haka ina da yakinin cewa idan har kuka mika masa Kudade masu yawa to tabbas zai koyar daku duk abubuwan da kuke bukata Kodajin haka sai walisa ta kalleshi cikin wani irin kallo mai kama da rashin yarda tace Idan har gari ya waye muka fuskanci cewa karya kayi mana To ka sani bama kai kadai zamu kashe ba hatta danginka gaba daya Ko mutum daya bazai tsira da rayuwarsa ba domin duk sai na yanka wuyansu da kaifin takobi na Cikin yarda da kai kusail yace na yarda da wannan sharadin naki Adaidai wannan guri suka tsaida hirar da sukeyi suka daure kusail yadda bazai iya guduwa ba Sannan suka koma suka ci gaba da barcinsu Kashe gari da sassafe Dukkansu suka shirya suka debi kayansu suka fito a wannan lokaci basu daure kusail ba Domin sun san bazai taba iya guduwa daga garesu ba Suna fitowa daga gidan sai suka janyo kofa suka rufe Sannan suka tusa keyar kusail agaba domin ya kaisu gidan dattijo kusaid Kusail ne a kan gaba su kuma suna biye dashi abaya Sannu a hankali suka dinga kutsawa ta cikin gari lungu da sako Haka kusail ya dinga bi dasu, duk inda suka gifta idan mutane sukaga kusail da mutane uku abayansa Sai kaga kowa ya kame kyam tareda ruke baki domin Sun san cewa yau rana ce ta kare masa don a wannan lokacin kallo daya kawai zakayi masa kasan cewa acikin daren jiya ya wahala kuma baiyi barci ba Don ganin yadda yake tafiya yana tangadi, tun suna yawo acikin kasuwar garin sai da suka fita daga cikinta Suka shiga cikin gari suna bi lungu lungu wani lungun ma idan suka shiga sai ka zata ba mai bullewa bane Wani abin mamakin ma shine gaba daya mutanen wannan gari ba sa kiwon kowacce irin dabba Sai aladu domin su kadai zaka gani suna yawo ko'ina na cikin garin Tun su walisa suna tafiyar da kuzarinsu har sai da suka sare suka dauka cewa yaudarar su yake shirin yi Don haka sai sarki aryan ya fusata ya zare takobinsa ya dora akan wuyan kusail Tareda cewa Kai mufa bama son raini idan har ka bata mana lokaci Idan karya kake gwanda ka fadamana, cikin razana yace kayi hakuri ai mun kusan zuwa gurin da muka nufa Kodajin haka sai shima ya mayar da takobinsa cikin kufenta sannan suka cigaba da bin kusail abaya Daga wannan guri da suke sai da suka sakeyin wata tafiyar mai nisa Suka isa wata 'yar karamar unguwa wacce mafi yawan mutanen cikinta talakawa ne A tsakiyar unguwarne suka iske wani dan madaidaicin gida Wanda kallo daya zakayi masa kasan cewa gidane na talakawa Koda isowarsu kofar wannan gida sai sai kusail yaja tunga ya tsaya yace dasu Nan gidan ne kadai zaku sami mutumin da kuke nema idan har baku yarda dani ba to na yarda ku kashe ni Koda yazo daidai nan a zancensa sai gimbiya walisa ta girgiza kanta Sannan ta karasa kofar wannan gidan bisa kafafunta tana isa sai tasa hannunta ta kwankwasa kofar Jim kadan da bugawarta sai akazo aka bude kofar ta ciki Sai ga wani kyakkyawan dattijo ya fito daga cikin gidan Wanda shekarunsa ba zasu gaza saba'in sa biyar ba Kallo daya zakayiwa wannan dattijon kasan cewa dolene ya kasance mutumin kirki Fuskarsa cike take da furfura sannan ya daura wani farin rawani akansa Koda dattijo kusaid yayi arba dasu gimbiya walisa tsaye a kofar gidansa sai fuskarsa ta fadada da murmushi kamar yaga 'yan uwansa na jini Yace sannunku da zuwa yaku wadannan manyan baki ai sai ku shigo daga cikin gidan Yana gama fadin haka sai ya juya da baya ya shige ciki Su kuma su walisa suna biye dashi abaya ahaka har suka isa wani dan karamin daki Wanda atsakiyarsa aka shimfida wani buzu na fata Da zuwansu wannan daki sai kusaid ya umarcesu dasu zauna su jira shi Nanfa dukkaninsu suka daga kai suka bishi da kallo cike da alamun mamaki akan fuskokinsu Jim kadan da tafiyar kusaid sai gashi ya dawo hannunsa ruke da wani katon faranti Wanda asamansa akwai kwanuka guda biyu da kuma kofuna hudu Ya ajiye agabansu sannan ya basu umarnin da suci wannan abincin Cikin mamaki dukkansu suka kalli junansu domin basu taba ganin mutum mai karamci irinsa ba Koda kusaid ya ajiye musu wannan farantin abincin sai ya juya ya basu guri Tafiyarsa keda wuya sai su gimbiya walisa suka sa hannu suka bude Kwanukan abincin Ba komaine acikin kwano na farko ba face gurasa da zuma Na biyun kuwa gasashshiyar kazace acikinsa Ba tareda bata lokaci da kuma tsoro ba Suka ci wannan abincin harda kusail sannan suka sha ruwa Basu dade sa gama cin abincin ba sai ga dattijo kusaid ya dawo Har a wannan lokacin fara'ar dake kan fuskarsa bata gudu ba Kawai sai shima ya zauna a can gefe daya da inda suke suna kallon juna atsakaninsu Sannan yace Yaku wadannan manyan baki ina yi muku barka da zuwa Sannan in ba zaku daku ba inaso insan suwaye ku kuma daga ina kuke bayan haka wacce bukatace ta kawo ku guri Dajin wadannan tambayoyi sai gimbiya walisa tace Yakai wannan dattijo muna godiya da irin karramawar da kayi mana Ka sani nice gimbiya walisa 'ya agurin sarki fadarul munnar, sannan ta nuna sarki aryan Wannan kuma shine sarki aryan, waccen macen dake kusa dashi itace jaruma marfuza 'yar uwa a gurin sarauniya suzaila Ya kai wannan dattijo ka sani cewa Ba komai ne ya kawo mu gurinka ba face muna so ka sanar damu ilimi akan wadannan abubuwa Take ta kwanto sandar hassanul basari daga gadon bayanta Ta mikawa kusaid ita tare da ciro wannan karamin littafin daga cikin aljihunta Taci gaba da cewa yanzu abin da muke bukata shine ka koya mana yadda ake karatu da rubutu na wadannan abubuwa harda ma yadda zamu fassarasu Idan har kayi mana wannan to zamu baka dukiya mai tarin yawa Koda ganin wadannan abubuwa guda biyu sai kusaid ya cika da mamaki Ya dago da kansa alokacin da idanunsa suka cika da kwalla yace Yaku wadannan baki masu daraja ku sani cewa wannan kwallar da nake bata komai bace face kwallar farinciki bisa ganinku Ku sani cewa tun cikin shekaru talatin baya an sanar dani cewa zakuzo gurina Kuma kune wadanda zasu karshen takadirin boka wato sahibul ukub Amma kafin ku sami nasarar aiwatar da hakan dole sai kun fuskanci jarraba kala daban daban Nima nasan hakan ne alokacin ina tashen samartaka Alokacin na shiga cikin daji da zummar yin farauta kawai sai ba fada tarkon wasu shu'uman matsafan aljanu Suka dana mini tarko domin su kasheni Amma sai wani kyakkyawan matashin aljani mai matukar kwarjini da cikar kamala Ana kiransa da suna khadimul islam yazo shi kadai ya fasa rundunar su da karfin tsiya ya kwace ni daga hannunsu Tun daga wannan ranar muka kulla abota tsakanina dashi Kuma tsawon wannan lokaci nima ina cikin addinin bautar gumaka Shi kuma ya kasance ma'abocin addin musulunci Saida muka shafe lokaci mai tsawo muna abota atsakaninmu Ba tareda yana tilasta mini kan dole saj na karbi addininsa ba Daga bayane ni da kaina na gamsu addininsa ne addinin gaskiya Kuma na nemi daya shigar dani cikin wannan addinin Agurinsa na karbi addinin musulunci kuma shine ya koyar dani yaren da aka rubuta wannan littafi dashi Kuma ya umarceni da in boye addinina har zuwa sanda wasu matasa guda uku zasu zo wajena domin na koyar dasu wannan yaren Yaku wadannan jarumai ku sani cewa akwai gagarumin aiki agabanku Kuma ubangijin musulunci ne kadai zai taimakeku ya baku nasara akansa Kuma tabbas zan koyar Daku duk abubuwan da kuke bukata amma fa ku sani hakan bazai taba amfanar daku komai ba Har sai kun ajiye addinin tsafi kun yi imani da ubangijin musulunci Domin shi musulunci haskene kafirci kuma duhu kuma dole kunsan haske da duhu basa haduwa guri daya face hasken ya kashe duhun Kunga kuwa dolene ku ajiye tsafe tsafenku kuyi imani da ubangijin musulunci akowanne lokaci sannan in zaku nemi taimako ku nema daga gareshi Kodajin wadannan kalamai sai duk su ukun sukayi tsit kuma jikinsu yayi sanyi hardashi kansa barawo kusail Daga can sai sarki aryan da jaruma marfuza suka dubeshi suka ce Duk munji batunka don haka idan ba zaka damu ba zamuso ka bamu dama domin mu danyi shawara tsakaninmu Dajin haka sai kusaid yayi murmushi yace ba matsala kuna da damar hakan domin a addinin musulunci babu takurawa Take su sarki aryan suka koma gefe marfuza ta duni aryan tace Yakai abokin tafiya shin kana ganin cewa mu ajiye addinin mu mu karbi wannan sabon addini Kada ka manta da cewa dukkanmu muna kan tafarki dayane na samar da zaman lafiya acikin duniya Kuma ina ganin wannan addinin shine babban makamin da zamu tunkari yarima walisu dashi Kodajin haka sai shima yace kwarai kuwa bamu da wani zabi face karbar wannan addini Domin ina da tabbacin gaskiyane komai na cikinsa Take duk su biyun suka koma inda suke zaune Suka dubi juna su da gimbiya walisa tareda gyada kansu Kawai sai suka dubi kusaid sukace mun amince da wannan addini naka dari bisa dari Don haka ka gaggauta shigar damu cikin wannan addini naka Dajin haka sai farinciki ya lullube kusaid nantake ya biya musu kalmar shahada tareda kusail Nantake duk su hudun suka maimaita Tun a wannan aranar kusaid ya fara koyar dasu tsarki da kuma ilimin addinin musulunci Tareda koya musu yadda zasu karanta rubutun dake cikin littafin Da ike dukkansu allah ya basu kaifin kwakwalwa sai gashi suna haddace duk wasu abubuwa da yake koya musu cikin kankanin lokaci Kamar rubutashi ake acikin kwakwalwarsu shi kansa kusaid yayi matukar mamaki yadda suke saurin haddace abinda yake kowa musu Saida suka shafe mako biyu acikin wannan gida sannan suka iya wannan yare sosai Kuma har suke iya karanta wannan littafi tareda

Chapter 7 of 13