Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
da tsananin son sarauta da kuma zalunci azuciyarsa Saboda ubangiji ya hore masa tsananin karfi damtse domin tun yana dan shekara shida Idan ya fita yin sata ko kuma kwace ba iya sa'anninsa yake tarewa hanya ba Harda wadanda suka girmeshi kamar 'yan shekara sha biyu Ganin wannan baiwar jarumtakar da yake da itace tasa shi ya fara jin girman kai da kuma yarda da kansa aduk yanayin daya tsinci kansa Kai a lokacin ma daya fara mallakar hankalin kansa sai abin yayi tsamari Domin ba iya mutanen gari kadai yakeyiwa kwace da fashi ba Harda dakarun sarkin garin wanda yake mulki a wannan zamanin ana kiransa da siddarul hussab Shi kuma sarki siddarul hussab mutumin kirki ne domin duk zalunce zaluncen da sarakuna sukeyi a wannan karnin basu dameshi ba hasali ma shi ya tsani zalunci Yana matukar kaunar talakawansa, Aduk lokacin da dakarun sarki siddarul hussab suka dawo daga karbar haraji a kasuwar garin ko kuma ya aikesu wani gurin sai jarumi yarmuna ya taresu akan hanyarsu ya kwace dukiyar da suka taho da ita yaje can wani kogon dutse ya boyesu Koda sarki siddarul hussab yaga wannan tsaurin ido na jarumi yarmuna Sai yayi tunanin dolene daga baya wannan yaron nan gaba idan aka barshi acikin birnin yayi yunkurin tayar da tarzoma acikin birnin gaba daya Saboda hak ne Yasa dakaru suka koreshi daga cikin birnin gaba daya Shi kuwa jarumi yarmuna tun daga lokacin da koreshi daga cikin birnin amnatul kais Sai ya shiga cikin daji yaci gaba da sabgar fashinsa da kwace acikin dajin Kuma ahaka ya dinga tara dakaru masu yawa yana koyar dasu dabarun yaki da salon yaki Cikin shekara guda ya hada guggun rundunar 'yan fashi wadanda saida suka addabi nahiyar gabaki dayanta kuma sunansa ya shahara a ko'ina cikin nahiyar kuma aka rasa wanda zai iya taka masa burki agabaki daya nahiyar ana cikin wannan haline wata rana cikin dare alokacin gabaki dayan mutanen birnin amnatul kais suna ta sharar barci abinsu sai 'yan tsiraru daga cikin dakarun birnin ne basuyi barci ba idonsu biyu sun tsaya suna gadin birnin kamar yadda suka saba Kwatsam sai sukaji dakarun jarumi yarmuna sunyi musu dirar burgu sunata sakar musu harbi da kibiyoyi ta sama da kasa Nanfa dakaru suka dinga zubewa kasa matattu kamar ana ruwansu Ba shiri suma dakarun suka shiga debo makamansu na yaki suna fitowa domin kare rayukansu Suka hadu a bakin kofa akayita kafsa gagarumin yaki acikin wannan daren Amma saidai kash aikin gama ya gama domin tuni dakarun harin sumamen sun gama kewaye birnin tako ina kuma sun fasa kofofin shigarsa da karfin tsiya sun shiga cikinsa Sukayita ragargazar dakarun babu ji babu gani ta ko"ina Kafin lokacin ketowar alfijir tuni sun gama karar da dakarun birnin gaba daya Ya zamana cewa mutum dayane kadai a raye kuma ya kasance dattijo domin a akalla shekarunsa ba zasu gaza saba'in da uku ba A zaune akan doki rike da wata sharbebiyar takobi yana ratsawa ta cikin dakarun sumamen ta ko'ina yana kai sara da takobinsa Duk inda yakai hannunsa kuwa saidai kaga dakaru suna zubewa kasa kamar ana sassabe agona Kayan da suke Jikinsa da kuma takobinsa kuwa tuni duk sun rine da jini kamar wanda yayi wanka acikin kogin jini Shi kadai ne kadai yake ratsawa ta cikin dakarun kamar shaidani Duk inda ya ratsa acikinsu saidai kaga dakaru suna ihu da karaji saboda tsananin jin radadin zafin fitar rai Kawunan dakaru kuwa sai suka dinga shawagi kamar ana zubar da ganyayen bishiya Jini kuwa ya dinga fallatsi daga jikin gangar jikinsu yana fallatsi a sama kamar an bude magudanar ruwa Ba kowa bane wannan dattijon ba face sarki siddarul hussab shine yaketa wannan gagarumar barnar domin yaga ya kare martabar kasarsa daga harin wadannan dakarun sumame Tabbas sarki siddarul hussab ya cika gagarumin gwarzon mayaki wanda ya cancanci a yaba masa domin har yanzu birnin amnatul kais suna tunkaho da irin jarumtakarsa da kuma jajurcewarsa Ana cikin hakane wani badakare mai tsananin naci ya shammaci dokin da sarki siddarul hussab yake kai kawai ya caka masa mashi adaidai kahon zuciyarsa Take dokin yayi turjiya adaidai inda yake tareda daga kafafuwansa sama yayi haniniya sannan ya fadi kasa ya danne sarki siddarul hussab akasa da ganin haka sai nantake dakarun sumamen suka yi cincirindo suka lullube shi da nufin suyi masa gunduwa gunduwa Koda ganin abindake shirin faruwa sai nantake sarki siddarul hussab yayi kukan kura Lokaci guda ya ciccibi dokin daya danne shi ya daga shi sama yayi wulli dashi can gefe daya ya turmushe wasu dakarun Sannan ya shuri takobinsa yayi katantanwa a tsakiyar dakarun dake kewaye dashi Ai kuwa take sai gasu duk sun zube kasa babu kafafu da hannaye a jikinsu Sannan yasa kafarsa dukkansu ya bangajesu da ita Kafin yayi wani yunkuri tuni wasu dakarun sun kara yanyameshi kamar kiyasai saboda matukar yawansu (HAR NA TUNA LOKACIN DA NAKE KAN GANIYAR SADAUKAN TAKA TA TABBAS NIMA NA SHEKE DAKARU DA YAWA A FILIN DAGA WADANDA BANSAN ADADINSU BA GASKIYA DOLENE TARIHI YA TUNGA TUNAWA DANI DON NIMA BUWAYAR SADAUKAI NE) Koda dakarun suka kara yin rubdugu akansa sai ya sunkuya ya bugi kasa da hannayensa Kuma ya yi tsalle yayi alkafira sau uku a sama sannan ya dawo kan kasa fuskarsa tana wani gyatsine alamar cewa yana cikin tsananin bakin ciki burinsa kawai shine yaga yayiwa wadannan dakarun muguwar barna koda kuwa zai rasa rayuwarsa Koda dirarsa akan kasa saiga kawunan wadannan dakarun da suka kewayeshi suna zabtarewa daga jikin gangar jikinsu suna faduwa kasa Ita kuwa kasar gurin tuni itama ta dade da rinewa da jinin dakarun in banda karnin jini babu abinda hanci ke ji Sai kuma karar karafkiyar karafa, sai gashi sarki siddarul hussab yana nunawa dakarun sumamen cewa tsohon kashi ba wasa bane kuma shima bai gaji sarautar birnin a banza ba sai daya sha gagarumar wahala ya kafsa da manyan mazaje da matsafa TAYA SARKI SIDDARUL HUSSAB ZAI IYA GAMAWA DA WADANNAN DAKARUN SUMAMEN? SHIN DAKARUN SUMAMEN SUNA SAMUN NASARA AKANSA KUWA ? SHIN ALJANI DARGATUL AMNAR YANA ZUWA BIRNIN AMNATUL KAIS KUMA HAR YA AIWATAR DA UMARNIN UBAN GIDANSA ? ME YARIMA WALISU ZAI GANO ACIKIN HALWAR TSAFIN DAYA SHIGA? SHIN YAUSHE SU GIMBIYA WALISA ZASU FITO DAGA CIKIN KOGON DUTSEN DA SUKA FADA DON JIN AMSOSHIN WADANNAN TAMBAYOYI SAI MU HADU AKASHI NA GABA NA CIGABAN WANNAN LABARI MAI SUNA HATSATSABIBAN SADAUKAI DAGA NAKU HABIBULLAH KBR LIKE ,COMMENTS AND SHARE*******************HATSABIBAN SADAUKAI CI GABAN ZUBAR DA JINI *******----------3 PART C---- LBR *********HABIBULLAH KBR Hakika a wannan ranar dakarun harin sumamme sun tabbatarwa d kansu cewa yau sun gayyaci guguwar annoba da hannunsu Ana cikin wannan haline kwatsam sai ga jarumi yarmuna yazo gurin da kansa Koda yaga irin muguwar barnar da sarki siddarul hussab yakeyiwa dakarunsa Sai ya fusata ya kwarara uban ihu, nantake ya zari wata kibiya daga cikin kufensa Ya dorata akan baka sannan ya tabe ya harbawa sarki siddarul hussab Ita akan kirjinsa Nantake kibiyar ta taho da gudun gaske ta cake a tsakiyar kirjinsa ta faso ta gadon bayansa jini yayi fitar burgu daga gurin Cikin sauri ya dago da kansa don yaga wanda yayi masa wannan mummunan harbi Ai kuwa sai sukayi ido biyu da jarumi yarmuna alokacin fuskar kowa tana gyatsine Kawai sai sarki siddarul hussab ya daka tsalle daga inda yake Bai bayyana a ko'ina ba sai daidai kan jarumi yarmuna take ya daga takobinsa sama Ya kai masa mummunan sara adaidai dokin wuyansa da nufin ya tsarge masa kai Cikin bakin zafin nama ya kaucewa saran amma duk da haka sai da kaifin takobin ya yankeshi a kafadarsa Tabbas in ba don yayi saurin kaucewa ba da tuni an manta da shafinsa Take jarumi yarmuna ya dakawa dakarunsa tsawa ya umarcesu dasu matsa su bashi guri Aikuwa take duk suka buda musu fili dagashi sai sarki siddarul hussab atsakiyar fili Sunayi musu kida Daga can sai duk su biyun sukayi kukan kura suka afkawa junansu da masifaffen yaki mai matukar muni Wanda saidaya firgita gaba daya dakarun da suke kewaye dasu Domin kuwa gumurzu ne na banbance aya da tsakuwa da kuma kece raini Tsakanin tsohon kashi da kuma sabon kashi, kowannen daga cikinsu Yana mai kaiwa abokin gwaminsa farmaki saida suka shafe fiye da sa'o'i uku suna fafatawa a tsakaninsu A sannane dafin dake jikin kibiyar da jarumi yarmuna ya harbi sarki siddarul hussab ya gama mamaye jikinsa Jiri ya soma dibarsa, ya dinga ganin abubuwa zuwa gida hudu Wannan itace damar da jarumi yarmuna ya samu har ya dinga dankara masa sara tako'ina ajikinsa tun yana maidawa yarmuna martani har yazamana cewa ya kasa yin hakan Koda ganin wannan nasara sai yarmuna ya maida takobinsa cikin kube Kawai ya kalli sarki siddarul hussab ya bushe da dariya Yace Yakai wannan sarki ka sani cewa kuskurenka guda dayane a duniya Wannan kuskuren kuwa shine barina a raye tun ina karami baka sa an kashe ni Kuma tun a wancan lokacin bani da burin dayafi naga na mallaki karagar mulkinka Wannan daliline yasa na dage wajen baiwa kaina horon yaki Kuma na dinga tare dakarunka inayi musu fashi, To ka sani cewa Da wadannan kudaden dana kwata. Ahannun dakarunka dasune nayi amfani na tara wadannan dakarun Kuma gashi yanzu dasune nayi amfani wajen rusa karagar mulkinka Duk wadannan maganganun da yake fada sarki siddarul hussab yana jinsa Daga can kuma sai ya dago da kansa a hankali yace Lallai na yarda cewa yanzu kayi nasara amma ina mai tabbatar maka da cewa ba zaka dade ba akan wannan karaga domin mulki da zalunci basa taba dorewa Kodajin wannan batu sai ran jarumi yarmuna ya baci Don haka sai yayi kukan kura ya zare takobinsa danufin ya sarewa sarki siddarul hussab kai Ai kuwa kafin takobin ta sauka akan wuyansa tuni shima ya daka tsalle ya zaro wata allura ajikin damararsa ya cakawa yarmuna ita a idonsa na hagu Shi kuma yarmuna yasami nasarar tsinke kan sarki siddarul hussab Take kansa ya tsinke daga jikin gangar jikinsa ya fadi kasa da murmushi akan fuskarsa Shi kuwa yarmuna saiya kwallara ihu saboda bakin cikin rasa idonsa guda daya da yayi Tun daga wannan rana jarumi yarmuna ya kwace karagar mulkin birnin amnatul kais da karfin tsiya ya zama sarkin garin Kuma ya kafa mulki na zalunci tsantsa wanda ko kadan babu tausayi ko tausayawa talakawa acikinsa Akullum burinsa shine ya mamaye nahiyar gaba ki dayanta ako'ina ya kafa karagar mulkinsa Ya ajiye wakili Kuma duk tsawon wannan lokaci ya manta da wasiyyar da sarki siddarul hussab yayi masa akan cewa bazaiyi tsawon raiba akan wannan karagar mulki Wannan shine takaitaccen tarihin sarki yarmuna da yadda ya kwaci mulkin birnin amnatul kais Lokacin da aljani dargatul amnar ya nufi nahiyar bakaken fata domin gabatar da kudurin uban gidansa wato yarima walisu Bai isa birnin amnatul kais ba sai da dare ya raba mutane suna ya sharar barci abinsu Don haka sai kawai yaga idan yace zai yakesu a wannan dare Duniya zataga kamar yayi yakin cikin tsoro ne, Don haka sai ya sami wani katon tsauni wanda yake kusa da birnin ya zauna akansa har zuwa safiya mutane suka fara fitowa daga gidajensu Saida kowa ya gama tashi daga barcin da yakeyi ya kama sabgoginsa yanayi sannan aljani dargatul amnar ya kada fuka fukansa ya tashi sama ya dira acikin birnin amnatul Shi kansa sautin kada fuka fukan saidaya haddasa guguwa agurin Koda mutane sukayi arba da shi sai suka firgice suka fara iface iface suna gudun ceton rayukansu Kuma adaidai wannan lokacin ne wani irin duhu irin mai dum dum dinnan ya mamaye birnin gabaki dayansa Ai kuwa take mutane suka kara furgicewa fiye da ko yaushe Shi kuwa aljani dargatul amnar sai ya wanzu yana mai shayar dasu gidauniyar mutuwa Da zarar ya bude bakinsa saidai kaga harshesa ya karawa kansa tsawo ya fito daga cikin bakin Yana tsinkewa mutane kawunansu kamar an saka resa Alokaci guda sai ya cirewa mutum dari kawunansu ya taune acikin bakinsa Saidai kaji sautin karyewar kashushuwa rukukus kamar mutum ya sami kuli kuli Babu abinda zai baka tausayi a wannan lokacin face yadda zaka gangar jiki babu kai ajikinta tana gudun ceton rai bayan kuma ta tabbatar da cewa mutuwa zatayi babu makawa Nanfa dakarun birnin suka dinga ciccidowa tako"ina domin su baiwa birninsu kariya amma da zarar Sun yi arba da irin kisan da aljani dargatul amnar yakeyi musu Sai kaga sun zubar da makaman yakinsu su falfala da gudu Amma duk irin gudun da zasuyi sai ya bisu ya kure musu gudu ya lankwame su Ana cikin wannan haline aljani dargatul amnar ya runtse idonsa ya karanta wasu sirrikan tsafi Faruwar hakan keda wuya sai ga wuta ta kama gabaki daya Sassan birnin har da gabaki daya gidajen dake cikin garin Kuma wutar mai tsananin karfi har tsiri takeyi asararin sama Nanfa wutar ta kara gigita duk wani mai rai acikin garin Suka fara kai kansu da kansu har inda aljani dargatul amnar yake ba tareda sun sani ba Nanfa jini ya cika garin ya zamana babu abinda kunnuwa sukeji face Koke koken mutane yara da manya maza da mata, Jini kuwa ya dinga shatata yana gudu acikin kwatocin garin yana gurbata da kasa Kamar an bude magudanar ruwa Hakika tashin hankali bashi da dadi kuma ba'abin nema baneba Domin shine kadai abinda yake iya sakawa mutum ya zauce Ya manta matsayinsa, dukiyarsa da danginsa domin kowa a sannan ta kansa yakeyi Saida mutanen birnin baki dayansu suka mutu ya zamana babu mai rai a cikin su Kawai dargatul amnar ya bushe da dariyar farinciki kan nasarar daya samu akaron sannan ya juya da nufin ya kama hanya ya tafi ba zato kawai sai yaga wani saurayi ya dako tsalle ya faso wani tubalin gini Wanda wuta takeci asamansa ya fito daga ciki hannunsa ruke da wasu sharba sharban adduna guda biyu yana mai kwarara uban ihu irin na manyan mazaje Ba kowa bane wannan saurayin ba face sarki yarmuna da kansa Tun kafin ya dira akan kasa ya daidaici dai dai tsakiyar kirjin aljani dargatul amnar ya jefa masa wadannan addunan na hannunsa Take duk addunan suka nutse acikin kirjinsa, Maimakon aljani dargatul amnar yaji zafi kawai sai yayi murmushi Ya sa hannunsa ya zaro wadannan addunan daga jikin kirjin nasa Take kirjin ya koma ya hade kamar wani abu bai taba samunsa ba Da ganin haka sai sarki yarmuna ya kara fusata ya sake dako wani tsallen a sama yana watsa Masa nau'ikan sihirce sihirce nau'i daban daban duk abin daya jefo idan ya sauka ajikin dargatul amnar sai nan take kaga ya lalace ya daina aiki ya zube kasa daga can kuma sai ya saka hannuwansa Ya cafo sarki yarmuna ya matse shi da hannunsa aikuwa nantake sai kashushuwan jikinsa suka dinga kakkaryewa ji kake kararasssss Saida yayi daga daga da jikinsa babu kyan gani sannan ya zubar da diddigar jikin nasa a kasa sannan ya tashi yaci gaba da tafiyarsa Yana mai kyalkyala dariyar murna wacce ta amsa kuwwa a gabaki dayan rusashshen birnin WANNAN SHINE ABINDAYA FARU GA ALJANI DARGATUL AMNAR BAYAN YAJE BIRNIN AMNATUL KAIS **** ***** *****- ***** Can kuwa al'amarin su jaruma walisa bayan sun sami nasarar yaki Da wadannan hatsabiban dodannin sun sami nasara akansu Har suka sami guri suka zauna suna hutawa sai kawai duk sukaji cikinsu Ya daure yana murdawa alamar cewa yunwa taci karfinsu Kodajin haka sai duk suka tuna cewa babu wanda yaci abincin karin kumallo acikinsu Kodajin wannan yanayi sai dukkansu suka dauko jakunkunan guzurinsu Suka kwance sukaci abinci suka koshi a sannan ne suka ga duk abincin nasu Ya kusa karewa, koda ganin haka sai hankalinsu ya dugunzuma ya tashi Domin sun san cewa idan ya kare basu da inda zasu sami wani abincin acikin wannan kogon Don haka dolene su san hanyar da zasu bi su fita daga cikin kogon da wuri Bayan sun zauna sunyi hirarsu sosai sai kuma suka kara tashi tsaye suka kama hanya sukaci gaba da tafiya abinsu Awannan lokaci gaba daya har sun manta da wahalar da suka sha a baya Kuma burinsu kawai shine su gaggauta ficewa daga cikin wannan kogon dutse Saida suka shafe sa'o'i hudu suna tafiya basu sake haduwa da wani abin tashin hankalin ba sannan sukazo jikin bango na karshe a cikin kogon Da zuwansu daidai wannan bango sai sukaga bangon ya dare gida biyu kamar an bude littafi Ya samar da wata wawakekeyar kofa a saman kofar an rubuta SANNUNKA DA KOKARI YA KAI BAKON WANNAN GIDA KA SANI CEWA KAINE KADAI MAHALUKIN DAYA TABA SHIGOWA CIKINSA KUMA YA FITA ARAYE SABODA HAKA MUNA MAI TABBATAR MAKA DA CEWA DUK ABINDA KASA A GABANKA NAN GABA KADAN SAI KA CIKASHI BISSALAM MUNA MAKA FATAN NASARA koda suka gama karanta wannan allon sanarwar sai take hoton allon ya bace Da ganin haka sai duk sukaji farinciki ya turnuke su don haka sai suka dubi junansu Sannan suka saka kafarsu ajere suka fice daga cikin kogon Aikuwa suna fitowa sai sukaji wani farin ciki ya kara turnuke su Kuma sai suka tsinci kansu a cikin wani daji mai cike da tarin ni'imar abubuwan marmari kala daban daban Da ganin haka sai jaruma tayi murmushi tace Ashe dai da rabon zamu sake shan iskar wannan daddadar duniyar tamu? Dajin haka sai gimbiya walisa tace kwarai ma kuwa gashi nan kina gani da idonki Gaskiya muna da matukar sa'a acikin rayuwarmu Shi kuwa sarki aryan sai yayi shiru yaki yace dasu komai ya barsu su kadai sai hirarsu sukeyi Haka dai sukaci gaba da tafiya suna ta hirarsu ,a sannan ne gimbiya walisa taji bukatar uzuri ya kamata Don haka sai ta nemi izini a gurin abokan tafiyar tata nanfa ta tafi ta barsu su biyu rak a tsaye sunata faman hira abinsu cikin nishadi da kuma raha Sannan ta zagaya bayan wani katon dutse da yake bayanta ta tsugunna ta biya bukatar ta Har ta gama biyan bukatar tata ta kamo hanya da nufin dawowa gurinda 'yan uwanta suke Kawai saita hango wasu 'yan kananun duwatsu guda biyu agabanta kadan Duk da cewa a wannnan lokaci ana zabga rana amma a kewayen duwatsun babu rana Sannan ga wasu kyawawan tsuntsaye sunata zagayawa a saman duwatsun abin ban sha'awa Koda ganin wannan abu sai take ta tuna da kalar tsuntsayen data gani acikin mafarkinta tare da wannan bakon jarumin kwanakin baya lokacin da tana gidan sarkin kasuwa yimana Kuma wadannan tsuntsaye basu da banbanci da wadancan tsuntsayen Tana gama tunawa da mafarkin nan nata kawai sai taji ba zata iya hakura taci gaba da tafiya ba Dole ne sai taje gurin wadannan duwatsun ta ganewa idonta ke meye a gurin Nan take ta kama hanya ta tunkari wadannan kananun duwatsu gadan gadan ME ZATA TARAR A WANNAN GURI? YANZU KUMA INA ALJANI DARGATUL AMNAR YA NUFA? SAI MU HADU A KASHI NA GABA****-------**********HATSABIBAN SADAUKAI *****************4 PART B LBR **************HABIBULLAH KBR Lokacin dasu gimbiya walisa suka rikide suka koma suffar katuwar mikiya Sai sukayita tsala azababben gudu kamar giftawar tauraruwa mai wutsiya Kuma suna tafiyar suna hadawa da karfin sihirinsu don takaice nisan tafiyar Ai kuwa sai suka dinga shafe tafiya mai nisan gaske cikin kankanin lokaci Suka dinga giftawa ta saman manyan birane, tsaunika, tekuna, da kuma dajijjika Cikin lokaci kankani ,saida mikiyar ta shafe mako biyu yana tafiya asararin samaniya ba tareda ta yada zango ba Kuma akan hanyarsa ya hadu da abubuwan hatsari Kala da ban daban, wadanda suka hada da manyan aljanu masu cin naman. Bil'adama, dodanni, dabbobin daji, da kuma mutane jinsin mayu Amma da zarar wannan mikiyar ta riski wata barazana daga wajen wadannan halittu cikin kankanin lokaci Take tarwatsasu da karfin tsiya ya kashe na kashewa Wasu kuma su gudu da kafafunsu domin tsira daga halaka domin sun san wannan karon basu takali ruwan sanyi ba Tsuliyar dodo suka tsokanowa kansu ko kuma ince tikitin mutuwa suka saya da hannunsu A ranar da suka cika mako uku ne suka isa nahiyar bakaken fata a nesa kadan da birnin labtarul halkam Koda isowarsu wannan sai mikiyar ta saki fuka fukanta ta sauko kasa kan turba Sannan tayi girgiza take kuwa mikiyar ta rabu gida uku wato ta rikide zuwa siffar gimbiya walisa, sarki aryan da kuma jaruma marfuza Dukkansu a wannan lokaci kallo daya zakayi musu kasan cewa a matukar gajiye suke, ko kuma once a jigace Saboda tsananin wahalar da suka sha akan hanyarsu da kuma gwagwarmayar da suka sha Kuma duk tsawon wannan lokacin babu wanda ya samu yayi barci ko kuma ya sha ruwa acikinsu har suka gama shafe wannan uwar tafiyar Koda dirarsu akan doron kasa duk sai suka nemi guri suka zauna sunata faman haki Kuma a wannan lokaci abincin kowa ya kare babu mai koda loma daya acikin jakar guzurinsa kai hatta ruwan da zasu sha ma babu Haka dai suka zauna a wannan daji amatukar galabaice babu wanda ya sami damar koda rintsawa Kaico hakika yunwa bata da dadi kuma babu wanda yake sabo da ita Saida suka shafe dakiku masu yawa kawai suna kallon kallo a tsakaninsu ba tare da wani yacewa wani kala ba Saboda mawuyacin halin da suke ciki , Suna cikin wannan haline kawai sukaga wani murgujejen zaki ya fito daga cikin kogon da nufin fita farautar abinda zai ci kuma ya kaiwa 'ya 'yansa ragowar Koda ganin wannan zaki sai nantake jaruma marfuza ta zaro kibiya daga cikin kwarinta ta dora akan bakanta ta saita tsakiyar cikin zakin nan ta harba nantake kibiyar ta tafi da gudun gaske ta cake atsakiyar cikin wannan zakin Take zakin yayi wani gurnani sannan ya sulale kasa matacce Cikin sauri marfuza ta tashi taje ta ciccibo gawar zakin ta kafa wuyansa Abakinta ta kama shan jinin jikinsa ,da ganin haka sai suma su sarki aryan da gimbiya walisa sukayi koyi da ita Koda suka sha jinin jikin wannan zaki sai suka fara dawowa cikin hayyacinsu Sannan suka fede fatar zakin suka gyara shi daga baya kuma suka dauko duwatsun kyastu suka kunna wuta agurin suka gyara zakin sannan suka gasa shi A wannan guri suka ci naman zakin suka koshi sannan suka dawo cikin hayyacinsu Adaidai wannan lokaci ne sukaga dare yayi don haka dole suna bukatar su samu su kwana a wannan guri idan safiya tayi sai su tashi su shiga cikin birnin dake gabansu Sarki aryan ya dubesu yace yaku abokan tafiyata ai yanzu bamu da wata fargaba a gaban mu Tunda har mun iso birnin labtarul halkam yanzu zaifi mana kyau mu samu mu yada zango anan gurin idan safiya tayi sai mu tashi mu shiga cikin garin nan ido na ganin ido, Dajin wannan shawarar tasa duk sai suka yarda da ita Take kowa ya mike daga gurin da yake yayi shimfida kayan kwanciyar sa Sannan gimbiya walisa ta kalle su gabaki dayansu tayi murmushi tace Yau dai zamuyi barcin da tunda muka hadu daku bamu taba yin irinsa ba Tunda kullum acikin tashin hankali muke tana gama fadin haka sai ta runtse idanunta sannan ta dauki wani dogon sanda Idonta a rufe ta dinga zagayesu har sai da tayi musu da'ira Tana gama yin da'irar saita karanta dalasiman tsafi ta tofa akanta Aikuwa faruwar hakan keda wuya sai ga wani dan karamin daki ya bayyana Daidai da kwanciyar mutum uku acikin dakin harda shimfidu masu taushi aciki Su kuwa su sarki aryan koda sukaga faruwar wannan al'amari sai duk suka kame suka kura mata ido Suna mamakin wannan karfin sihiri nata, Har sarki aryan ya bude baki zaiyi mata tambaya sai ta tsai dashi ta hanyar cewa Ba tambaya zaka tsaya yi mini ba kawai kaje ka zabi gurin da zaka kwanta in yaso sai kayi mini tambayar da kake bukatar yi mini Cikin mamaki sarki aryan yaje can kan shimfidar da take gefe daya ya zauna sannan itama Marfuza taje ta sami gurin da zata kwanta suka bar walisa a tsaye Sarki aryan yace Yake walisa tabbas yau na dada tabbatar wa cewa kinyi mana nisa nida jaruma marfuza Kwarai da gaske

Chapter 6 of 13