Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
suna masu kallonsa da idanunsu Domin ganin samansa sukayi sumul kamar ba kan tsauni ba Kuma a samansa gaba daya babu bishiya ko tsiron tsirrai guda daya ma'ana dai filine fetal ta yadda babu wani abu da zai boye maka Koda sukaga wannan fili sai duk jikinsu yayi sanyi domin sun san tabbas ruwa baya tsami banza dole akwai dalilin faruwar hakan Cikin sauri suka zare makaman yakinsu suka rukesu da hannuwansu domin zaton koda yaushe za'a iya kawo musu farmakin bazato Suna tafiyane cikin sanda kuma duk su ukun sun jingina jikinsu a guri daya sunki yadda su rarrabu don gudun kar a shammacesu Hatta kasar guri idan zasu taka basa yarda su bada gaba dayan karfinsu agurin don gudun tsautsayi Suna cikin wannan tafiyar ne kwatsam ba zato ba tsammani sai sukaga kasa ta tsage ta haifar da wani wawakeken rami mai girman gaske dukansu suka fada cikinsa Dukkansu sai suka kwarara uban ihu mai karfin gaske Suna ruftawa cikin ramin ne sai shi kuma dutsen ya koma ya hade kansa kamar bai taba budewa ba Su kuwa su gimbiya walisa acikin iskar sai suka ruke hannayen juna ba tareda sun yarda sun cika hannayen junansu ba Haka dai sukayita yawo a saman iska suna saukowa kasa ba tareda sun sauka kan kasa ba saboda zufin da ramin yake dashi Zurfin wannan ramin kadai atakaice zaikai zurfin gaba dubu Kuma ba hakar mutanen wannan zamanin ba saidai hakar mutanen farko wato samudawa sannu a hankali suka sauka a kasan dutsen Koda suka sauka kasansa sai suka cika da mamaki sakamakon ganin girmansa domin girmansa kusan kamar gari guda yake Kuma gaba ki dayansa babu wata matattakala wacce zaka kama domin fita daga cikin wannan tsaunin Saboda tsananin mamaki marfuza bata san lokacin da tace Wannan wanne irin dutse ne? Dajin wannan tambaya sai sarki aryan yayi tsaki yace Ai dukkan mu baki ne a wannan guri don haka babu wanda zai iya baki amsa sai abinda idanunmu suka gane mana Walisa tace kwarai kuwa maganarka gaski…… .. Kafin ta gama fadar abinda zata fada sai kawai ta jiyo hucin sautin harbin kibiya Cikin sauri ta daka tsalle daga inda take ta kaucewa harbin kibiyar Kawai sai kibiyar taje ta cake ajikin bangon bangon dutsen gaba dayanta Koda ganin wannan abu daya faru sai dukkanninsu suka waiwaya domin suka daga inda wannan kibiyar take amma basuga kowa ba agurin Daga can sai sukaji an bushe da dariya wacce ta amsa kuwwa agaba daya cikin kogon dutsen ta yadda ba zaka iya tantance daga inda sautin dariyar yake tahowa ba Daga can sai sukaji ance barkanku da zuwa kogon hallaka Kogon da duk wanda ta shiga cikinsa bai isa ya fita daga cikinsa araye ba Idan akwai mai wasiyya acikinku saiya fada domin mu isar masa da ita Dajin haka sai sarki aryan ya daka wa muryar tsawa yace karyarka ta sha karya Ko wanne irin bala'i aka tana da acikin wannan ina tabbatar maka da cewa dole sai mun tarwatsa shi kuma mun fita daga cikinsa lafiya ba tareda dayanmu ya rasa rayuwarsa ba Kuma sai mun tarwatsa dukkan zaluncin da kukeyi mun wuce lafiya ni da abokan tafiyata.… . yana cikin fadin haka sai walisa ta rufe masa baki da hannunsa don kada ya sake yin magana Itama ta fada cikin daga murya tace ai duk wasu maganganu da zaka fada karyane Kuma bazaiyi tasiri akanmu ba saidai akan kananun jarumai idan har kun isa mazaje ku fito muyi gaba da gaba daku domin yakin buya yakin tsoro ne Koda gama fadin haka sai ta sake jin an bushe da dariya daga can kuma sai sukaji ance Ku kwantar da hankalinku a sannu zaku ga mutuwa akan idanunku ba sai kun tsokanota kusa daku ba koda akazo daidai nan amaganar sai take sautin komai ya dauke aka daina jinsa Da jin haka sai duk suka dubi junansu sukayi wata inkiya da hannayensu Sannan suka ci gaba da tafiya ba tareda fargabar komai ba Saida sukayi tafiya mai dan nisa sai sukaji kasa ta fara tsagewa da dukkan bangwayen dutsen kamar zasu rufto su fado kansu su dannesu Koda ganin haka sai duk sukayi sauri suka hade jikinsu guri guda suka suka gyara rukon makaman yakinsu a hannunsu Sannu a hankali saiga wasu irin gajerun aljanu suna fitowa daga cikinsu Su dai wadannan aljanu 'yan kananu ne wadanda gaba daya girmansu baifi na bijimin sa ba kuma bakunansu dogayene kamar irin na ungulu saidai suna da tsawo sosai haka suma kunnuwansu fala fala ne masu matukar fadi bayan haka wadannan aljanun suna da matukar tsananin yawa Kai da kaga wadann zaka san cewa jinsine na aljanu masu shan jinin bil'adama Kuma ko kadan basu da tausayi sannu a hankali wadannan aljanun suka gama fitowa daga cikin ginin sukayiwa su walisa kawanya Nanfa dukkanninsu suka tsaya suka fara kallon kallo atsakaninsu Daga can sai aljanun suka afko kansu walisa da nufin suyi musu gunduwa gunduwa da sassan jikinsu Nantake suma su walisa suka afka kan aljanun suna masu karaji da kururuwa Nanfa aljanun sukayiwa su walisa rubdugu aka ruguntsume da masifaffen yaki atsakiyar kogon dutsen Sai gashi aljanun suka kaiwa su walisa farmaki da ta ko wanne bangare da sama da kasa Domin su kacalcala su walisa su shanye jinin jikinsu Nanf gurin y cika da karar haduwar karafa d zarar makamansu walisa sun hadu da jikin wadannan aljnun sai aji wata kara ta tashi kal !! Kamar sautin haduwar karf da karfe tareda tartsatin wuta Suma kuma dodannin da zara sun kawo wa su walisa hari da bakinsu idan suka kauce suka sami kasa sai kaga bakin nasu ya huda kasar gurin yayi dan karamin rami Domin shi kansa bakin nasu kaifi ne da shi da kuma tsini kamar takobi Nanfa gurin ya yamutsi karar karafkiyar karafa ta cika dodon kunne Ihu tareda gurnanin aljanun ya cika kunnuwa sai ga su walisa sun zama kamar an ajiye mage a tsakiyar dubunnan karnuka Nanfa su walisa suka barbazu atsakiyar aljanun kowanne daga cikinsu ya fuskanci bangari guda cikin mugun nufi da burin ganin ya tarwatsa su da karfin tsiya Nanfa sukaci gaba da kai farmaki cikin bakin zafin nama ,juriya da bajinta kamar jikinsu bana jini da tsoka bane haka suka dinga ratsawa ta cikin aljanun rike da makamansu tsirara suna kai musu sara da suka ta dole suka dinga budawa kansu hanya da karfin gaske Kamar sun kasance shaidanu amma duk wannan kokarin da sukeyi sai ya tashi abanza Domin basa iya kashe ko guda daya daga cikin aljanun Su kuwa aljanun burinsu kawai shine su kafa bakinsu ajikinsu walisa domin su zuke jinin dake jikinsu Koda su walisa suka fuskanci nufin aljanun sai suka kara zage damtsensu wajen yakai aljanun Don daga baya ma sai suka dinga daukar aljanun da hannuwansu suna ciccibar su duk girmansu suna yin jifa dasu Amma da zarar aljanun sun sauka akasa sai kaga sun tashi sun murmure kamar wani abu bai taba samunsu ba Saida suka shafe fiye da sa'a guda suna wannan bakin artabun A sannan ne su walisa suka fahimci cewa tabbas idan aka cigaba da wannan yakin a haka to zasu iya gajiya Kuma da zarar sun gaji shikenan dodannin zasu sami nasara akansu Kodayin wannan tunani sai kawai ta kwallara uban ihu ta tarwatsa wadanda suke kusa da ita da karfin tsiya sannan ta dawo inda su sarki aryan da jaruma marfuza suke suka kawai tayi musu wata iriyar inkiya da 'yan yatsun hannunta Sannan suka ci gaba da yakin da suke yi ba tareda sun tsagaita ba Suna cikin wannan haline ba zato sai wani aljani ya shammacesu yasa bakinsa ya caki cinyar jaruma marfuza Nantake marfuza ta kwallara uban ihu sakamakon tsananin zafi da zugin da taji Koda ganin abinda ya faru sai sarki aryan ya daka tsalle daga inda yake yasa kafarsa ya naushi wannan aljanin saboda karfin dukan saida aljanin ya tashi sama sannan ya fado Cikin sauri sarki aryan ya yagi jikin rigarsa ya daurewa jaruma marfuza wannan ciwon da yake kan cinyarta ita kuma walisa saita dinga karesu ita kadai da takobin dake ruje atafin hannunta bayan sarki aryan ya gama daurewa marfuza wannan ciwon sai duk su biyun suka mike tsaye sukaci gaba da fafata sabon azababben yaki Wanda yafi na farko domin a wannan lokaci suna yin fadan ne domin su gano lagon wadannan aljanun ne don su gaggauta kashesu Wani irin sabon salon yaki suka canja wanda acikinsa suka dinga tsalle tsalle da kwance kwance a tsakiyar dubunnan dodannin suna masu kai musu sara da suka ta kowanne bangare ba tare da sanin takamaiman gurin da zasuyiwa aljanun lahani ba Ai kuwa basu dade da fara wannan sabon artabu ba wani aljanu ya sake kawowa marfuza cizo a kan cinyar daya cijeta da farko Koda ganin abinda yake shirin faruwa batasan sanda ta daga takobinta sama ta sara ta a tsakiyar karan hancin aljanin Aikuwa faruwar hakan keda wuya sai gurin ya dare jini yayi tsartuwa Nantake alljanin ya sulale ya fado kasa matacce ba tareda ya koda shura ba Cikin sauri ta juyo inda su walisa suke tayi musu ishara da wannan lagon data samo Dajin haka sai dukkanninsu suka zage damtse suka dinga saran tsakiyar hancin aljanun babu kakkautawa Take gurin ya cika da sautin ihun wadannan aljanu da kuma gurnanunsu Saboda yadda su walisa suka bude kasuwar rayuka acikin tsakiyar kogon Nanfa gawarwakinsu suka barbazu atsakiyar kogon duk inda ka duba babu abinda zaka gani face su da kuma jininsu wanda ya malale agaba daya cikin kogon kamar an bude magudanar ruwa Kafin cikar rabin sa'a har sun gama karar aljanun 'yan kalilan ne suka tsira su din ma da sukaga uwar bari sai suka dinga bacewa suna shigewa cikin karkashin kasa don su tsira da rayuwarsu Koda ganin wannan nasara da suka samu sai dukkanninsu suka nutsu ba tareda sun mayar da makamansu cikin kube ba Daga can sai kawai sarki aryan ya mayarda takobinsa yace dasu Ai da alama wadannan halittu ba zasu dawo ba domin suma yanzu sun san cewa mu ba kanwar lasa bane Don haka dolene suyi shakkar kara tunkarar mu Dajin wannan batu sai suma duk suka mayar da makamansu acikin kufe Sannan jaruma marfuza ta sami guri ta zauna ta fara kokarin sakawa raunin dake jikinta magani Da ganin haka sai suma su gimbiya walisa suka sami guri kusa da Ita suka zauna domin su huta Sai bayan sun zauna agurin suka lura da yadda yanayin cikin dutsen ya canja zuwa duhu Ganin haka sai suka fuskanci cewa tabbas rana ta fadi don haka dolene su sami guri su zauna domin su yada zango su kwana agurin in safiya tayi sai su tashi su ci gaba da tafiya Da ganin haka sai walisa ta dubi jaruma marfuza tace Sannunki jarumar gaske tabbas na gamsu cewa ke ba karamar jaruma bace don har kin wuce yadda nake zato Dajin haka sai marfuza tayi dan guntun murmushi sannan tace Ba haka bane nima ai dolece ta tilastani na ci gaba da wannan yakin don bana so na barku da wahala Nandai sukayita hira atsakaninsu daga can kuma sai suka dauko abinci sukaci suka cika cikinsu sannan suka raba kwanciya barci domin su samu su huta idan safiya tayi sai suci gaba da tafiya Amma sai suka raba daren gida biyu ma'ana Gimbiya walisa da jaruma marfuza zasu kwanta suyita barci abinsu har zuwa tsakiyar dare shi kuma sarki aryan sai ya tsaya yayita zaman gadinsu Idan tsakiyar dare yayi sai ya tashi gimbiya walisa sannan shima yaje ya kwanta ita walisan ta zauna taci gaba da gadinsu Ita kuma marfuza sai sukayi mata uzuri domin ta samu ta dan huta saboda ciwon dake jikinta Haka kuwa akayi kamar yadda suka tsara haka al'amarin ya kasance Wato a wannan guri shka samu sukayita sharar barci abinsu domin su huce gajiyar dake tsakaninsu Basu farka ba saida safiya tayi sannan suka tashi suka debi makaman yakinsu da dukkan komatsansu suka kara nausawa cikin kogon dutsen sai bayan sunyi tafiya mai nisa ne suna tafiya a wannan lokaci gimbiya walisa tana ta faman kalle kalle da dube dube acikin kogon kwatsam saiga wani katon mulmulallen dutse ya gangaro daga sama zai turmusheta kuma shi wannan dutsen daya zo akanta zai fado Kuma idan har hakan ta faru take anan dutsen zaiyi daga daga da naman gimbiya walisa Cikin sauri sarki aryan da jaruma marfuza suka fara kwallawa gimbiya walisa kira domin ta kauce amma ina Ko kadan bata iya jinsu ba domin ta fada cikin tunanin dan uwanta yarima walisu da kuma mahaifinsu wato sarki fadarul munnar ME ZAI FARU SHIN GIMBIYA WALISA TANA MUTUWA TA SILAR WANNAN DUTSEN? DON JIN AMSA SAI MU HADU A KASHI NA GABA DAGA NAKU HABIBULLAH KBR LIKE, COMMENTS AND SHARE********************HATSABIBAN SADAUKAI CI GABAN ZUBAR DA JINI ***********************2PART C LBR *********************HABIBULLAH KBR lokacin da su jaruma marfuza da sarki aryan suka dinga kwallawa gimbiya walisa kira domin su ankarar da ita cewa ga dutse nan yana tunkarota Koda suka fuskanci cewa hankalin gimbiya walisa baya jikinta sai kawai nantake duk su biyun suka falfala da gudu kamar kiftawar ido kafin dutsen ya sauka akan ta Tuni sunzo sun janye ta daga gurin take kuwa dutsen ya dira akan kasa Daidai gurin da ya fadima saida ya wawake ya haddasa wani rami wanda za'a iya bunne mutum biyu acikinsa Cikin bacin rai sarki aryan ya daga hannu da nufin ya mari gimbiya walisa Amma koda hannun nasa ya kusa sauka akan fuskarta sai yaji ya kasa Bisa dole ya sauke hannun nasa tareda nadamar daga mata shi Da ganin haka sai walisa tace menene ya hanaka idda nufinka akaina? Dajin haka sai kunya ta kama sarki aryan kawai sai yayi yake tareda sosa keyarsa yace Haba ai har abada hannu na bazai taba yin gangancin shafar wannan fuskar taki ba kuma nayi imani da cewa Duk abinda ya koro bera daga rami har yazo ya fada cikin wuta to tabbas yafi wutar zafi Don haka na fuskanci cewa ba komai kike tunani ba face yadda akayi ke da dan uwanki kuka zama kuna farautar juna kamar wasu dabbobi Cikin mamaki walisa ta juyo ta dubeshi tace tayaya akai kasan hakan ? Kawai sai yace ai labarin zuciya fuska ake tambaya Don haka duk abinda yake cikin zuciyarki akan fuskarki na gani Suna cikin wannan zancen ne sai sukaga wasu irin duwatsun masu yawan gaske suna gangarowa daga bayansu zasu turmushesu, koda ganin wadannan duwatsu sai dukkanninsu suka bar wannan tattaunawar da suke Suma suka nufi hanyar da take gaba dasu cikin azababben gudu Wohoho nanfa aka kasa Azababben tseren gudu tsakaninsu da wadannan mulmulallun duwatsun domin su ceci rayuwarsu Domin sun tabbatar da cewa wadannan duwatsun turo musu su akayi kuma wani ne yake sarraf su Sai gashi a wannan lokaci su walisa suna gudun da basu taba yin kamar sa atarihin rayuwarsu ba Domin a wannan lokacin basu da damar da zasuyi amfani da karfin sihirin tsafinsu Sai da suka jima suna wannan gudun domin har idanunsu sun rufe yadda basa kula da abin da yake gabansu Kawai sai ganinsu sukayi a bakin wani tafkeken rami Wanda suna kara koda taku daya daga imda suke take zasu fada cikinsa Kuma da zarar sun fada din babu wanda zai tsira daga cikinsu Koda ganin wannan katon ramin duk sai suka tsaya sukayi cirko cirko Suna kallon ta hanyar da zasu bi su ketare shi kuma har a sannan Wadannan mulmulallun duwatsun basu daina binsu ba Kawai sai suka hango wata siririyar gada acan gaba dasu wacce fadin bai wuce takun mutum daya ba Da ganin wannan gadar sai dukkansu suka kara falfalawa da gudu suka nufi gurin da wannan gadar take Duk da sun san cewa gadar bata da karfin da zata debi mutane fiye da daya Amma sai duk suka haye kanta basu tsaya bata lokaci ba Kuma basu daina gudun da suke yi ba har saida suka je tsakiyar gadar ba tareda wani abu ya same su ba Koda suka je tsakiyar kan gadar sai suma wadannan duwatsun duk sukayi bindiga suka tarwatse kamar gari Yabi iska kamar basu taba wanzuwaba, Kuma adaidai lokacin ne su gimbiya walisa suka ga wannan gadar ta fara jijjiga kanta a sama tana kokarin karyewa Tareda wata irin hadaddiyar curin dunkulen bakar wata data kama akasan gadar Wacce indai mutum yayi sakaci ya fado cikinta tun kafin ya sauka akanta ma zai babbake ya kone kurmus saboda tsananin zafin wutar Itama wannan gadar saita kara kaimi wajen jijjiga kanta asama Ta yadda duk wani abu da yake kanta zai fado kasa Koda su walisa suka fuskanci haka duk sai suka hada hannayensu guri guda suka ruke ba tareda sun yarda sun cika ba sannan suka ci gaba da gudun a haka basu daina ba Haka itama gadar bata daina girgizar da take ba nanfa suka dage iya karfinsu domin suga sun kai karshen gadar don tsira da rayuwarsu Kuma inda matsalar take shine mutum biyu ko uku basu isa suyi tafiya akanta a jere ba saboda kankantar ta Dole saidai mutum daya bayan daya, daga can kuma sai gadar ta fara karyewa tana fadawa cikin wutar Da zarar karfen ya fada cikin wutar saidai kaga nantake ya narke Tare kuma da wani sauti mara dadin sauraro ki kake yana Cuuuuuuuuu, alokacin da karfen yake narkewa, duk wannan halin da ake ciki gimbiya walisa ce akan gaba sarki aryan yana biye da ita Sannan jaruma marfuza tana biye dashi abaya, har sukaje karshen gadar Gimbiya walisa tana dauke kafarta daga kan gadar sai nan take gadar ta karye Gadar tayi kasa dasu Sarki aryan da jaruma marfuza Koda ganin abindaya faru sai nantake walisa itama ta daka tsalle ta bisu Kafin su fada cikin wutar tuni walisa ta shuri sarki aryan ta jefoshi saman gadar Sannan jaruma marfuza, duk su biyun suka fita daga cikin ramin Kash hakika rashin sani yafi dare duhu Koda ta gama fito dasu daga cikin ramin sai itama ta dako tsalle domin ta fito daga cikin ramin, Amma ina sai ta kasa domin tayi nisa acikin ramin Kuma tana daf da riskar fadawa cikin wutar Da ganin haka sai nantake jaruma marfuza ta kwanto wata doguwar igiya daga jikinta ta jefa cikin ramin Sannan shima sarki aryan sai shima ya daka tsalle ya ruke wannan igiyar ya fada cikin ramin Kafin gimbiya walisa ta fada cikin wutar tuni sarki aryan yasa hannunsa na hagu ya riko ta dashi Ita kuma gadar ta nutse acikin wutar ita kadai Cikin matukar mamaki gimbiya walisa ta dago da kanta suka hada idanu da sarki aryan Kawai sai tayi masa murmushi, itama jaruma marfuza wacce ke ruke da igiyar saita yiwa gimbiya walisa murmushi Nanfa yasa hannuwanta biyu ta fara kokarin janyo sarki aryan da gimbiya walisa Wohoho hakika gaskiyane da ake cewa karfi jari ne kuma ko wanne abu yana da rana a duniya Koda ta fara janyo su sarki aryan sai damatsan hannunta suka tashi sukayi burdin burdin Duk da cewa kuwa bata da girman jiki amma a wannan lokaci sai surar jikinta ta dinga rikidewa Suma gabobin jikinta suka dinga budewa, Sai gashi tana janyo sarki aryan da gimbiya walisa a tare Har saidata fito dasu gaba daya daga cikin ramin suna sauka akasa sai duk suka zube akan kasa suna ta faman yin haki aka rasa wanda zaice da wani kala daga cikinsu Daga can sai marfuza ta dubi walisa tace muna matukar godiya bisa ceton rayuwar mu da kikayi Amma ina da tambaya shin menene dalilin daya sa kika sayar da rayuwarki domin ceton tamu rayuwar? Dajin wannan tambaya sai walisa tace ai amsar wannan tambayar a bayyane take Idan har na rasa ku ku biyu tabbas zanyi babban rashin abokai arayuwata Domin tun daga tasowata ban taba yin aboki ko kawa ba Babu wanda na sani sosai kamar iyayena da kuma dan uwana yarima walisu Yanzu kuma kaddara ta rabani dasu kuma tazo ta sake hadani daku amatsayin sababbin abokan rayuwa Shin tayaya kuke ganin zan iya yin kasadar rabuwa daku? Koda ace ni na rasa tawa rayuwar to nayi imani da cewa ku biyun nan zaku taimaka mini ku cikawa mahaifina burinsa Kodajin wannan batu sai su sarki aryan suka girgiza kansu alamar gamsuwa da bayaninta Bayan sun dan huta a wannan guri tsawon lokaci mai tsawo suna hira a binsu kamar ma sun manta da gagarumin aikin dake gabansu Sai kawai sarki aryan ya katse hirar da sukeyi da fadin cewa Yanzu dai dukkanku kunga irin halinda muka shiga acikin wannan kogon dutse Tabbas na yarda cewa ilimin tsafi kogi ne ni dai a iya binciken da nayi bantaba sanin da akwai wannan kogon dutsen da har sihiri baya tasiri acikinsa ba sai yanzu da muka tsinci kanmu acikinsa Yanzu kuma na yarda cewa wannan gida ya amsa sunansa gidan mutuwa Kuma gidan bala'i domin duk sihirinka ba zai kwaceka ba acikinsa koda kuwa kaine yarima walisu ko kuma ince boka sahibul ukub Kodajin wannan batu sai dukkansu suka jijjiga kansu sannan marfuza tace kwarai kuwa maganarka gaskiya ce domin ina ganin cewa hakan ne ya hana yarima walisu shigowa cikin wannan kogo Dajin haka sai walisa ta jijjiga kanta tace yake marfuza idan har haka kike tunani To ki gaggauta canja tunaninki, domin kamar yadda duk nan kuke takamar jarumtaka .To shima walisu yana jin haka domin tare dashi aka bamu horon yaki, ki sani cewa karfin damtsena, iya yaki, da kuma karfin sihirina daya yake da nasa Saidai kawai yanzu nasan yafini domin bashi kadai bane ,kai in takaice maka labari ma Shi kansa boka sahibul ukub ba kanwar lasa bane a fannin jarumtaka Tararsa gaba da gaba daidai yake da mutum yace zai nada gammo akansa a dora masa dakon duniyar nan Ba karamin sa'a bace ba zata taimaka mana har mu iyayin gaba da gaba dashi mu sami nasara akansa ba Tunda yanzu mutum biyu ne a hade yarima walisu da boka sahibul ukub Kunga kuwa dolene sai mun dage wajen kokarin cika burikan dake gabanmu Yanzu dai zama bai same mu ba dolene mu tashi mu ci gaba da tafiya Da gama fadin haka sai ta mike tsaye ta dubi su jaruma marfuza tace Idan kun shirya sai ku mike tsaye mu tafi aikin dake gabanmu Domin zama anan gurin ba aikin mu bane kuma daidai yake da hutun jaki da kaya aka koda jin haka sai dukkansu suka mike tsaye tareda gyara tsayuwarsu Sarki aryan ya kalli marfuza yace ina matukar tausaya miki akan wannan ciwon dake jikinki Kuma ina fatan bayayi miki ciwo ? Koda jin wannan tambaya sai marfuza tayi murmushi tace Ai ko kadan wannan ciwo baya damu na domin maganin da na saka masa yana da karfi wajen hana ciwo zugi da radadi Koda gama fadin haka sai tayi shiru ba tareda ta kara cewa komai ba Ba tareda da bata lokaci ba suka kama hanya suka ci gaba da tafiya acikin kogon dutsen Kuma suna tafiyar suna hira atsakaninsu kamar babu wani tashin hankali da zasu tarar agabansu, ko kuma ince kamar suna tafiya acikin gidansu Kuma suna tafiyar suna hadawa da dube dube tako ina domin suga ta inda za'a fara kawo musu hari Har sukayi doguwar tafiya basu hadu da wani abu ba na tashin hankali ko kuma cutarwa ba Don haka sai suka sakin jikinsu tun da ragowar hasken rana har saida itama ranar ta fadi gari ya soma yin duhu alamar dare yayi Da ganin haka sai walisa taja tunga ta tsaya ta dubesu tace Zaifi mana kyau mu dakata da tafiyar mu a wannan guri domin tafiya mu acikin wannan duhu babbar matsala ce agare mu Koda jin haka sai dukkanninsu suka yarda da maganarta Don haka sai suka fara duba guraren da suke kewaye da gurin da suke domin su tabbatar da lafiyar gurin saida suka tabbata babu wani abu akusa dasu sannan suka dawo suka kwance guzurinsu Suka fito da abinci sukaci suka koshi sannan suka raba tsarin kwanciya barci kamar yadda sukayi abaya amma wannan karon harda jaruma marfuza Kuma a wannan

Chapter 4 of 13