Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ukub zai iya tasowa harma ya nemi hanyar da zai fishi karfin sihiri Sai take ya sihirce kogon tsafin tsafin ta yadda koda bayan ransa bai isa ya shiga cikin kogon ba Ba'a dade da yin haka ba shine sahibul ukub ya kashe mahaifinsa don ya mallaki sirrikan tsafinsa kuma duk saidaya mallaka abu dayane bai mallakaba wannan abin kuwa ba komai bane face wannan kogon sirri Likacinda su sarki aryan suka bayyana tsulum acikin wannan kogon sirri Kai tsaye sai suka wuce da gimbiya walisa walisa kan wani dan karamin gado na katako suka kwantar da ita akansa Cikin sauri aryan ya dubi marfuza yace menene ya faru ga gimbiya walisa Nantake marfuza ta kwashe labarin komai ta fada masa ba tareda ta boye masa komai ba Tun daga sanda dakaru suka kamo gimbiya walisa suka kaita kurkuku har zuwa lokacin da yarima walisu ya bayyana harda sanda taje ta dauko gimbiya walisa daga cikin kurkukun Daga karshe ta sanar dashi cewa tayi mamakin yadda taje ta tarar da gimbiya walisa afarke alhalin an sanya mata cutar dogon barci Kodajin wannan labari yayi sarki aryan ya girgiza kansa yace Aikuwa yanzu take zamuyi mata magani acikin kogon dutsen nan domin ta dawo cikin hayyacinta Kuma Ina da tabbacin cewa babu wanda ya farkar da ita daga wannan cutar barcin face yarima walisu Domin shine kadai zai iya karya sihirin tsafin 'yar uwar ki sarauniya suzaila Cikin mamaki marfuza ta dubeshi tace tayaya kasan wannan sirri alhalin baka gani da idanunka ba Bayan haka ta wacce hanya kake ganin zaka iya yi mata magani idan har ta tabbata yarima walisu ne ya saka mata wannan cutar ta kamewar jijiyoyin jiki? Dajin wadannan tambayoyi sai ya gyada kansa yace tabbas hakane banida sihirin yarima walisu Amma inaso ki sani wannan ba aikinsa bane aikin 'yar uwar ki ne Shi nasa aikin kawai shine farkar da ita daga dogon barcin da aka saka mata don taga yadda yadda zai bazar da birninku gaba daya Shi tun farko dama bashi da burin hallakata don haka nema ya kyaleta tun a karonsu na farko da ita . Dan gane da tambayar ki ta farko kuwa yanzu zan nuna miki amsarta ta zahiri akan idonki Yana gama fadin haka sai yasa hannuwansa ya tashi gimbiya walisa zaune daga kwanciyar da take Duk da cewa idanunta abude suke amma ko kadan ba zata iyayin magana ba saboda karfin gubar da take jikinta Sannan ya karanta wadansu dalasiman tsafi guda uku ya tofa acikin kwayar idanunta Nantake wani haske ya fito daga cikin idanun nata ya daki bangon kogon Sai ga hoton komai ya bayyana ajikin kogon tun daga sanda yarima walisu ya bayyana akanta har da irin tattaunawar da sukayi da ita Sannan kuma hoton komai ya bace shima hasken ya dauke Sarki aryan ya juyo ya fuskanci jaruma marfuza yace yanzu dai kin gani da idanunki kuma kin tabbata yarima walisu bashi bane ya sanya mata wannan cutar ba Game da tambayar ki ta biyu kuwa shine hanya daya zamubi mu karya wannan sihirin da yake jikinta Hanyar kuwa itace dolene mu mu bada jinin jikinmu mu zubashi acikin kwalba sannan mu dura wannan garin maganin aciki mu bata tasha Kafin ya gama bayanin da yake mata tuni tasa waata 'yar karamar wuka ta yanki hannunta da ita Sannan ta zaro kwalba acikin jakarta ta zuba jinin aciki Da ganin haka sai shima sarki aryan ya sa wukar ya yanki nasa hannun shima ya zuba jinin a cikin kwalbar data zuba nata jinin Yace da mata Gaskiya nayi mamakin yadda kika kasance mai saukin kai sabanin 'yar uwar, tunda har kika sake aminta dani duk da cewa nayi yunkurin hallaka ki abaya Ina mai neman afuwarki akan wannan kuskuren dana aikata Kodajin haka sai take fuskarta ta fadada da wani murmushi tace Menene zai hanani yarda da wanda na kasance ina mutuwar kaunarsa fiye da rayuwata Ka sani cewa koda yau dinnan na mutu to zan mutu cikin farin cikin ganin jinina da naka sun hadu aguri daya Dajin abindata fada sai sarki aryan yayi shiru bai sake bata amsa ba Kawai sai ya bude tafin hannunsa yayi wasu siddaru faruwar hakan keda wuya saiga wani kullin garin magani ya bayyana atafin hannunsa Cikin sauri ya ya kwance maganin ya durashi acikin kwalbar jinin nasu Sannan suka bude bakin gimbiya walisa suka dura mata shi Ai kuwa bata gama shan maganin ba sai gashi ta fara yin aman dafin daya shiga jikinta har dama na harbin da kunama tayi mata a yayin fafatawar su Sannu a ahankali sai gashi ta fara motsa jikinta, Daga can kuma sai gata ta mike zaune sosai ta zauna da kafafunta Kawai sai ta juyo ta kalli su sarki aryan da jaruma marfuza tace Ina mika godiyata agareku bisa ceton rayuwata da kukayi.. Caraf sai marfuza ta tari bakinta tace ni bana bukatar ki gode mini Domin tun farko nice ya kamata na gode miki tunda kece kika fara ceton rayuwata lokacin da nake gangaren mutuwa Dajin haka sai walisa tace duk da haka dolene na baki hakuri bisa abin daya sami birninku Domin duk nice silar haka in ba don na sauka acikinsa ba da haka bata faru ba kuma ina mika ta'aziyata agareki bisa ga rashin 'yar uwar ki da kikayi Koda jin haka sai kwayar idanunta suka ciko da kwalla tace Duk abindaya faru baki da laifin komai 'yar uwatace ta ta janyo domin sune suka daukoki da kansu alokacin bakya cikin hankalinki Yanzu dai zama bai kamamu ba dole ne mu ci gaba da bibiyar dan uwana don ganin inda ya nufa kuma mu hanashi aiwatar da shirinsa na gaba Dajin haka sai mamaki ya kama ya kama marfuza tace da ita Shin dama wannan azzalumin mutumin dan uwanki ne kuma kuna da dangantaka dashi? Walisa tace Kwarai kuwa maganarki haka take sai dai shi dan uwana yarima walisu mutumin kirkine kuma tare aka haifeni dashi kuma muka karbi horon yaki tare Saidai kuma duk wannan abinda yake faruwa shima bada sanin sa yake ba Take ta kwashe labarin komai ta fada mata Sarki aryan ya dubi gimbiya walisa yace Yake wannan jaruma akan me zaki ce mu fita daga cikin kogon nan bayan kinsan cewa yanzu haka dan uwanki yana nan yana neman mu kuma nan gurin da muke shi guri mafi sirri da zamu zauna acikinsa kuma mu tsira daga sharrinsa Dajin haka sai take walisa tayi murmushi tace Ai kuwa ni dolene na fita daga cikin wannan kogon tunda har na riga na sami lafiya domin yanzu ba wasan buya na fito ba Idan har na zauna anan ba zan taba cikawa mahaifina burinsa ba Tana gama fadar haka sai kawai ta runtse idanunta tareda buda tafin hannunta ta karanta wasu dalasiman tsafi masu matukar wahalar karantawa Nantake take saiga duk makaman yakinta sun bayyana akan tafin hannun nata Koda ganin haka sai sarki aryan ya dubeta yace ai shikenan muma a shirye muke da muyi karo da kowanne irin kalubale koda kuwa zamu iya rasa rayuwar mu Koda gama fadin haka sai duk suka hada hannuwansu guri daya atare suka suka karanta dalasiman tsafinsu take sai wata iriyar guguwa mai karfi ta ta taso ta debesu gaba daya tayi sama dasu KUYI HAKURI A CIKIN KWANAKIN NAN INA EXAM NE BA KODA YAUSHE NAKE ZAMA RUBUTU BA SHI YASA KUKAGA INA YIN TSALLAKE BA KAMAR YADDA NA SABA KWANA 3 BA SHIN INA SU WALISA SUKA NUFA? WANNE HUKUNCI YARIMA WALISU ZAI DAUKA ? MU HADU AKASHI NA GABA LIKE AND COMMENTS*************HATSABIBAN SADAUKAI CIGABAN ZUBAR DA JINI ****************1 PART C LBR HABIBULLAH KBR Lokacin da iska mai karfi ta zuke su gimbiya walisa basu bayyana ako ina ba sai a kan turba cikin wani irin daji mai tsananin yawan sahara wanda basa iya ganin karshenta Kuma awannan lokacin ana tsaka da zafin rana dajin gaba daya ya cika da zafin rana Hatta ita kanta iskar da take kadawa agurin zafi take fitarwa da turiri saboda tsananin zafin rana Inda ace za'a ajiye danyen kwai agurin cikin dakika uku zai dafa kansa Babu abinda idanu suke iya gani face dogayen doron sahara wadanda sukayi tsiri asama kuma dole sai anbi ta kansu domin cigaba da tafiya In badon da takalma masu tudu ajikin kafafunsu ba da basu isa su iya jurar tafiya acikin wannan saharar ba Koda bayyanar su a wannan guri sai duk suka dago da idanunsu suka kalli junansu suna mamakin bayyanar su a wannan guri mai matukar wahalar rayuwa Abinda basu sani ba shine haka ka'idar wannan kogon tsafi yake Duk sanda nemi tsira alokacin da kake daf da hallaka to dolene idan ka fita daga cikinsa ya kaika guri mai hatsarin gaske Wannan shine dalilin dayasa suka tsinci kansu acikin wannan daji Cikin sauri gimbiya walisa ta kalli sarki aryan tace Shin acikinku akwai wanda yasan cikin nahiyar da muke? Dajin wannan tambaya sai duk suka gyada kawunansu alamar basu sani ba Kawai saita girgiza kai tace yanzu dai na fuskanci cewa mun tsirane ta wani fannin amma awani bangaren bamu tsira ba Don haka ya zame mana dole sai munyi kula kuma munyi taka tsantsan da rayuwarmu Kafin ta gama fadin haka tuni tuni jaruma marfuza ta shige gaba ta ci gaba da tafiya Sarki aryan da gimbiya walisa ma sai duk suka bita abaya ba tareda sanin inda zasu je ba Ai kuwa suna fara tafiyarne duk jikinsu ya fara fada musu Domin wannan saharar ta fita da ban da wacce suka sani domin ita tana da matukar laushi Hakan ne yasa gaba daya dudduniyar kafarsu take nutsewa acikin ta da zarar sun daga daya kafar tasu Zafin gurin kuwa ya dinga ratsa har cikin takalman nasu yana yana laso kafafun nasu Wohoho hakika Ita wahala ba'a sabo da ita domin duk sanda ka shiga cikin ta saika raina irin wacce kasha abaya Basu dade da fara tafiyar ba duk sukaji jikinsu ya fara gajiya Kafafunsu sun fara gajiya da tafiyar da suke kuma babu abindake daga musu hankali face idan suka hangi gabansu suga basa iya ganin karshen saharar saidai doron da saharar tayi masu mugayen tsayi agabansu Bayan haka ga itama iska wacce take kadawa acikinsa mai zafin gaske da kuma hucin zafin da take fitarwa Ita kanta wannan iskar ta isa ta hana abubuwa masu rai rayuwa acikin wannan daji Haka dai su marfuza sukayita tafiya acikin saharar ba tareda dayansu yace da daya kala ba kamar wadanda aka daurewa bakunansu an rasa wanda zaice da wani kala Ba komai ya jawo hakanba face tunane tunanen da suke yi mai zurfi kan wacce irin kalubale zasu fuskanta acikin wannan dajin Saida suka shafe sao'i hudu suna tafiya acikin wannan dajin bisa kafafunsu alokacin ne sukaji wata iriyar yunwa mai karfi ta kama cikinsu a yayinda sukaji cikin nasu yanata murda musu Bisa dole duk suka tsaya suka sami guri da nufin su zauna su dan huta Har sun zauna ba shiri sai suka mike tsaye saboda ji sukayi zafin gurin ya kama mazaunansu kamar zai konasu Sarki aryan ya kallesu yace aikuwa dole babu yadda zamuyi saidai muci wannan abincin a tsaye Yana gama fadin haka sai ya kwanto jakar guzirinsa ya bude ya fito da abinci Kawai sai yaga jaruma marfuza ta kura masa ido sai a sannan ya tuna cewa ita bata taho da abincin guziri ba Kawai sai ya kalleta yayi mata murmushi akaron farko yace Bai kamata naci wannan abincin ni kadaiba dole sai kinzo munci. Dajin haka sai taji wani farinciki ya shiga zuciyarta Don haka batareda musu ba saita tafi wajensa Har takai hannu da zummar ta faraci sai taji gimbiya walisa ta ruke hannunta ta baya Cikin sauri ta juyo da kanta ta kalleta sai taga walisa tayi mata murmushi sannan tace Haba yake wannan budurwa mai karamci ai tunda kika ceci rayuwata Nima ya zame mani dole na baki kulawa kamar yadda kika sayar da rayuwarki kika ceci tawa Ina neman alfarmar kizo muci nawa abincin tare kodajin haka sai suka raba mata hankali ta rasa ina ya kamata taje Na farko dai shi sarki aryan tana matukar kaunarsa kuma cin wannan abinci tare dashi zai kara mata kusancine a gareshi Ita kuwa gimbiya walisa ta ceci rayuwarta alokacin da shi sarki aryan yake kan gangarar halakata Nanfa suka raba mata tunani ta rasa gurin daya kamata taje Daga can sai tace ai wannan abu mai sauki ne duk sai mu hada abincin aguri guda sannan muci Kodajin wannan hukuncin nata sai sukayi murmushi sukace kwarai kuwa maganarki gaskiya ne Ba tareda gardamar komai ba suka hada abincin nasu suka tsaya atsayen sukaci suna nishadi tsakanin su kamar sun kasance 'yan uwan juna Cikin kankanin lokaci suka cinye abincin suka sha ruwa sannan suka ci gaba da tafiya Saida la'asar ne kwatsam suna tafiya sai suka ji wata iriyar guguwa mai karfi tana kadawa acikin saharar kura ta turnuke cikin sararin samaniya sai kawai suka hango sahara tayi tsiri asama ta nufo inda suke da gudun gaske Koda sukayi arba da wannan guguwa sai suka ruga da gudu domin tserewa wannan guguwar Kaico hakika wahala bata da dadi kuma duk sanda mutum yaga hallaka zai iyayin abinda bai taba zaton yinsa kuma kaima mai karatu idan aka sanar dakai zaka iya zaton cewa karyane Nana aka kasa azababben tseren gudu tsakanin su da wannan guguwar domin ceton rayukansu Gaba daya ma sai suka manta da laushin wannan saharar Suka dinga gudu kamar suna tafiya akan doron kasa kamar kiftawar kibiya Domin suna gudun ne kuma suna hadawa da amfani da karfin sihirinsu Duk da cewa suna amfani da sihirinsu saiya tashi abanza domin duk sanda suka juyo bayansu sai suga guguwar tana daf da riskarsu Kai duk da karfin gudun nasu duk sai ya zama na banza domin guguwar kara kusantarsu take Koda suka fahimci cewa lallai wannan gudun ba zai kai musu ba sai suka fara tunanin wacce hanya ya kamata su bi domin suga sun kubuta daga sharrin wannan guguwar Nanfa duk su ukun suka fara magana da junansu cikin alkaluman tsafi domin ko kadan bakinsu baya motsawa Kuma ba tare da suna kallon junansu ba Walisa ce ta fara magana cikin alkaluman tsafin tace Kaicon mu da wannan gudun da mukeyi wanda bamu da tabbacin tsira acikinsa Dolene mu yi tunanin hanyar daya kamata mubi domin ceton rayukan mu Dajin haka marfuza tace gaskiya ne maganarki amma acikinku wacce hanya kuke ganin zamubi domin muga mun sami nasarar kubuta? Caraf sai sarki aryan ya tari bakinta yace akwai hanya guda daya wannan hanyar kuwa itace dolene muma mu kirkiri tamu guguwar wacce zata je ta tunakari waccan dake bayanmu Dajin wannan shawara tasa duk sai suka amince da ita Nantake suka hada baki a tare suka karanta dalasiman tsafi suka bugi kasa da hannayensu Faruwar hakan keda wuya sai nantake wata iriyar guguwa mai karfin gaske ta taso daga bangaren da suke Itama ta nufi wacce ke bayansu cikin azababben gudu har tana dunkulewa asama tamkara curin nakiya Tana gudu tare dafitar da wani sauti mai karfi Wohoho aikuwa koda guguwoyi guda biyun suka hadu sai wata irin sautin kara mai karfi ya tashi tareda tashin walkiya har saida su walisa suka saka hannuwansu suka toshe kunnuwansu dasu domin gudun kar kunnuwan nasu su sami matsala Cikin sauri suka dakata da gudun da sukeyi suka juyo bayansu domin suga abinda yake faruwa Ba komai suka ganiba face haduwar goguwoyin guda biyu atsakiyar fili suna rigima da junansu Kamar sun kasance mutane ko kuma dabbobi Daga can kuma duk su biyun sai sukayi bindiga suka tarwatse Ganin wannan abu daya faru sai duk sai suka ji farinciki ya turnukesu Suka tsaya agurin suna faman haki saboda gudun da suka sha Abinda basu sani ba shine har yanzu tsuguno bata kare musu ba akwai sauran aiki agabansu ko kuma ince fafatawa atsakaninsu Bayan dakiku kadan da tarwatsewar wadannan goguwoyin sahara guda biyu Sai kuma suka hangi wata sabuwar kurar ta sake turnukewa asama Nanfa suka zuba ido domin suga menene zai faru awannan guri Sannu ahankali sai sukaga wannan kurar saharar ta soma dunkulewa guri guda kamar curin bishiyar dabino Yana karawa kansa girma da fadi kuma suffar jiki tana kara bayyana ajikinsa Kafin cikar wasu dogayen dakiku tuni wannan saharar ta rikide ta koma siffar wani katon mummunan maridi mai matukar girma, tsawo da kuma kauri wanda tunda su walisa suke arayuwarsu basu taba ganin halitta mai matukar girmansa da kwarjinininsa ba Koda halittar ta gama cika suffar wannan maridi sai duk su ukun suka kalli junansu cike da mamaki acikin zukatansu Jaruma marfuza bata san lokacin data ce hakika yau mun kawo kanmu tsakanin mutuwa da rayuwa ba Dolene sai wata babbar sa'ar ce zata fitar damu daga cikinsa ,dajin haka haka sai walisa tace kwarai kuwa, maganarki gaskiya ce Kogon nan da muka shiga ba kogon tsira bane saidai akirashi da kogon hallaka Shi kuwa sarki aryan shiru kawai yayi yana kallonsu domin ya kasa cewa komai saidai nadamar shiga cikin wannan kogon da sukayi kawai yake acikin zuciyarsa Suna cikin wannan halinne kawai sukaji maridin ya bushe da wata mahaukaciyar dariya mai karfin gaske Wacce ta amsa kuwwa da amo acikin dajin gabaki dayansa Wani irin tururin zafi ya fita daga cikin bakinsa kamar an bude ruwan da yake tafasa Cikin sauri duk su ukun suka juyo suka kalleshi alokacin da yake kyakyata wannan dariyar Kawai sai gani sukayi wannan maridin ya wangame bakinsa Cikin wata iriyar kakkausar murya mai kama da kukan jaki Ya sake bushewa da dariya akaro na biyu yayi tayi kamar bazai dainaba daga can kuma Saiya tsuke bakinsa kamar an aiko masa da sakon mutuwa ya murtuke fuskarsa ya kallesu gaba daya wasu 'yan mitsi mitsi agabansa yace Lallai yaro yaro ne yaku wadannan tawagar matattu hakika gaba dayanku kun yaudari kawunanku da har kuke zaton cewa zaku iya tsira daga tarkunan da mai gidana yarima walisu ya kafa muku To gaskiya kun tabka babban kuskure arayuwar ku don haka duk wani guje guje da kukeyi anan gurin zan kawo karshensa na rantse harda darajar mai gidana yarima walisu Sai na kawo karshen duk guje gujen da kukeyi kuma daya daga cikin ku bai isa ya tsira da rayuwarsa daga sharrina ba Koda maridin yazo nan azancensa sai su gimbiya walisa suka kalli junansu atare sannan kuma sai suka bushe da dariya Atare kamar ba zasu daina ba wacce dariyar tasu saidata baiwa maridin mamaki Daga can kuma sai suka tsuke bakinsu ga barin yin dariyar Suka tsaya cak agabansa ba tare da shakkar komai ba suna masu gyara tsayuwarsu domin tunkararsa Daga can walisa tace Kai banda ganganci irin naka tayaya zaka tunkari abindaya gagari mai gidanka Ai inda ba kasa nan ake gardamar kokawa Tana gama fadin haka sai nantake ta ruga da gudu zuwa kansa tana mai kwallara ihu da karfin gaske Take suma su sarki aryan suka rufa mata baya cikin karaji da kururuwa irinta manyan sadaukai wadanda suka saba kwarmatsuwa afilin daga kowannensu takobinsa tana ruke ahannunsa tsirara koda ya rage baifi saura taku uku ba atsakaninsu dashi ba sai suka daka tsalle sama daga inda suke suka kaiwa maridin wani irin mugayen sara da sukansu Cikin zafin nama maridin yasa hannuwansa guda biyun Ya damke su gimbiya walisa dasu ta yadda ba zasu iya fita daga cikin sa YAYA ZATA KASANCE SHIN SU WALISA ZASU KUBUTA DAGA SHARRIN WANNAN MARIDIN? TAYAYA YARIMA WALISU YA IYA GANO INDA SU GIMBIYA WALISA SUKE KUMA HAR YA IYA AIKO HADIMINSA? YA LABARIN SARKI FADARUL MUNNAR MAHAIFIN SU WALISA SHIN YANA FITOWA DA KANSA SHIMA DOMIN NEMAN DANSA NA CIKINSA WATO YARIMA WALISU KAMAR YADDA WALISA TA FITO? DONJIN AMSOSHIN WADANNAN TAMBAYOYI SAI MU HADU A KASHI NA GABA NA WANNAN KAYATACCEN LABARAI MAI SUNA HATSABIBAN SADAUKAI LIKE AND COMMENTS*****************HATSABIBAN SADAUKAI CI GABAN ZUBAR DA JINI ******************2 PART A LBR HABIBULLAH KBR Lokacin da wannan maridin ya sanya hannuwansa ta damke su gimbiya walisa Sai ya ruke su kamar ýar tsana acikin tafin hannun nasa Sannan ya kare musu kallo irin na raini saboda kankantar da sukayi masa Kawai sai yayi tsaki sannan ya bude bakinsa ya daga su sama da nufin ya watsa su acikin bakin nasa ya taunesu gaba daya ya hadiye duk da yasan ba zasuyi masa maganin yunwar sa ba saida hannun nasa ya kai daidai bakin nasa zai watsasu Kwatsam ba zato ba tsammani sai duk su ukun suka rikide jikinsu ya narke suka zama yashi Shima kuma yashin sai ya zube akan kasa ya saje acikin saharar da take wajen Daga can sai yashin ya tashi ya bi iska sannan ya sake rikidewa zuwa suffar gimbiya walisa, sarki aryan da kuma jaruma marfuza tsaye bisa turba fuskarsu cike da murmushi Take suka kara afkawa kan maridin suja sake kachamewa da azababben yaki mai matukar muni atsakaninsu Inda ace akwai mace mai juna biyu a gurin lokacin da suke wannan fafatawar dolene na kuda ta kamata kuma ta haife dan da yake cikin cikinta ba tare da ta sani ba saboda tsabar firgita Idan kuwa futsari mutum yake ji take zai sakeshi agurin Kai idan mutum ma matsoraci ne faduwa zaiyi kasa ya hadiyi zuciya ya mutu sabida tsabar firgita Domin zata zakayi cewa kamar sama da kasa ne zasu hade awannan lokacin saboda tsabar bala'in rigimar tasu Nanfa kasa ta fara girgiza kura kuwa ta tashi ta turnuke a sararin samaniya yadda ba zaka iya ganin abindake tsakaninku ba Babu abinda ido yake iya gani face hasken giftawar makaman yakinsu Su kuwa ko kadan babu abinda ya damesu babu abinda wannan kurar take boye musu Saboda sabon da sukayi da gumurzu afilin daga Nanfa guri ya yamutse karar karafkiyar karafa ta cika dodon kunne saida suka shafe sao'i biyu suna wannan fafatawar ba tareda dayanzu ya sami nasara akana abokin gwaminsa ba Koda su gimbiya walisa sukaga wankin hula yana nema yakaisu dare Sai sukayi wa junansu wata inkiya sannan suka ja da baya atare Sannan suka daka tsalle sama daga inda suke atare suna masu karaji da kururuwa suka kai masa mugayen suka akan cikinsa da nufin suyi masa kisan farat daya Aikuwa koda makaman suka sauka ajikinsa sai suka ratsashi suka wuce kamar yadda zaka ratsa ta cikin haske ka wuce Kafin su ankara tuni maridin ya sanya kafarsa guda ya doki jaruma marfuza da ita Saboda karfin dukan saida tayi sama kamar an doka tamole (bal) sama tayi tsiri sosai Koda suka ga abindaya faru ga jaruma marfuza kuma suka tabbatar da cewa idan har ta fado dolene kashushuwan jikinta su kakkarye ko kuma ta rasa rayuwar ta Suna cikin wannan tunanin ne suka dira kan turba amma ko dakika daya basu kara ba Sai suka bugi kasa da hannayensu take suka kara tashi sama kamar an harba kibiyoyi suka ratsa cikin iska atare suka cafo jaruma marfuza zasu sauko da ita kasa Koda maridin yaga Abindake shirin faruwa sai ya sake kai musu wani saran da takobinsa da nufin ya tsinkasu gaba daya acikin lokaci guda Aikuwa kafin takobin ta sauka ajikinsu tuni sun wurkila kansu a saman sun kaucewa harin nasa Ya sari iska ji kake wuuuff!!!!!! Sautin hucin takobinsa, take suka dirgo kasa duk su biyun dauke da marfuza akan hannunsu Suna sauka kasa sai suka dire jaruma marfuza ta tsaya kyam akan kafafunta kamar babu wani abu daya sameta Nanfa suka sake tsawa su da maridin suna kallon kallo cikin nuna tsan tsar kiyayya ga junansu Suna cikin wannan kallon kallo ne maridin ya shammace ba tare da sun sani ba ya jefo musu takobinsa ta tsakiyarsu domin ta tsargesu Kafin takobin ta karaso inda suke tuni sun kauce mata Amma duk da haka saboda girmanta saidata ratsa ta tsakiyar sarki aryan da gimbiya walisa ta yanki kowannensu akan damatsansa Shi dai sarki aryan a dantsen hannun dama ta yankeshi kuma gurin yayi zurfi Ita kuma gimbiya walisa a damtsen hannunta na hagu ne Take duk su biyun suka yagi jikin rigunansu suka daure yankan takobin Ita takobin da maridin ya jefesu da Ita take ta koma

Chapter 2 of 13