Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ciki yanzu Amma kada ku damu ni zan zauna a wannan guri na jira dawowarku Domin ina da tabbacin cewa sai kunyi nasara akan yarima walisu kuma har ku dawo nan gurin tare dashi Kada ki damu ni zan kula da kaina daga nan har zuwa sanda zaku dawo Abinda yasa zan zauna a nan gurin kuwa shine tun kafin na baro gida Sihirin tsafina ya nuna mini cewa ban isa na iya shiga cikin fadarsa ba Ku kadaine duk duniya zaku iya shiga cikin ta duk da irin matakan tsaron da suke cikinta Yana gama fadin haka saiya dagawa walisa hannu yace Yanzu duk wata tattaunawa da muke ta kare saiku tashi ku tafi aikin dake gabanku Daga yanzu banason jin komai daga bakinku yana gama fadin haka saiya juya musu baya tareda yi musu nuni da su tafi kawai Koda ganin haka sai dukkansu suma suka juya masa baya Suka nufi wannan babbar tekun ba tareda shakkar komai ba Koda suka isa bakin tekun sai kawai suka daka tsalle sukayi nutso akasan sa kamar kifaye suka fara tafiya acikinsa Kuma duk su ukun sai suka cure a guri guda ba tareda sun rarrabu ba Suka dinga ninkaya acikin wannan ruwan sanyin Tun sarki fadarul munnar yana hangosu daga inda yake har suka bace masa da gani saboda nisan da sukayi Tunda suka shigo cikin wannan tekun sai gabaki daya dorunonin ruwan da suke cikin tekun sukayi burus dasu sukayi kamar basu gansu ba Aikuwa koda suka dauki tsawon lokaci suna tafiya acikin ruwan Sai sukaji sanyin wannan ya fara ratsa jikinsu gabaki daya jikinsu ya fara karkarwa saboda sanyin da yake ratsa jikin nasu Koda dorunonin ruwan sukaga halinda su walisa suka shiga sakamakon sanyin wannan ruwan Sai dukkanin yunkuro aguje kansu domin su saka musu wawa Ta yadda sai sunyi gubduwa gunduwa da jikinsu aikuwa ana haduwa a tsakiyar tekun sai suka kachane da yaki Mai matukar muni ko wacce dorina guda daya zata iya hadiye su walisa da katon bakinta Amma a haka saboda dakakkiyar zuciyar dasu walisa suke da ita sai sukaki yarda su basu damar da zasu cutar dasu Sakamakon addu'o'in da suke karantawa sai ya zamana Cewa duk sanyin tekun ya soma disashewa kamar wanda aka sirkashi da ruwan zafi Don haka sai walisa, marfuza da sarki aryan duka su ukun Suka zamewa halittun alakakai saboda irin fadan da sukeyi A wannan lokacin suna fadan ne iyakar karfinsu da kuma burin ganin karshen sahibul ukub Koda suka dauki dogon lokaci suna wannan dauki ba dadi Sai wata irin hatsabibiyar dorina mai matukar naci ta shammaci walisa ta doki hannunta wanda ke ruke da takobi Take takobin ta sulmuye kasa ta fada cikin ruwan kawai sai dorinar ta kara daka tsalle a cikin ruwan ta bude katon bakinta da nufin tazo tayi mata loma guda Koda ganin abinda ke shirin faruwa ga walisa sarki aryan baisan sanda ya daka tsalle ba a saman ruwan yazo ya shuri gimbiya walisa kamar yarinya karama Ya dauketa daga gurin kawai sai dorinar ta cafki iska ta nutse kasa Yana direta sai yayi nutso a kasan ruwan tabi wannan dorinar yana mai yin addu'a azuciyarsa Aikuwa takobinsa na sauka ajikin ta sai ta huda jikin jini yayi feshi Ta sulale kasa matacciya itama walisa saita kwanto sandar hassanul basari daga gadon bayanta domin tasan yanzu shine lokacin daya kamata ta zama itace makamin yakinta Kawai ta afka tsakiyar halittun tana mai kai musu mahaukatan duka da kaifin jikin sandar Duk wanda ta daka daga cikinsu take zakaga sandar ta tsargashi gida biyu Jini yayi tsartuwa daga jikinsa ya malale acikin ruwan Kafin adauki wani lokaci mai tsawo tuni sun gigita dorinonin da rabon goron mutuwa Idan ka kalli saman ruwan babu abinda zakavgani face gawarwakin su Wadanda suka cika saman ruwan gaba daya sukayi rututu suna yawo a samansa Duk hasken da ruwan yake dashi sai gashi yana rinewa da jini Don haka koda sukaga yadda suke asarar 'yan uwansu da kansu suka dinga daukar hanya suna guduwa domin ceton rayukansu Amma duk da haka sai su walisa suka toshe musu kofofin tsira duk inda suka shiga Sai su bisu kashe saida suka tabbatarda cewa sun kashe gabaki dayansu ko daya baiyi saura ba Sannan suka kuma suka ci gaba da tafiya acikin ruwan kamar kifaye har suka isa Inda tsuburin yarima walisu yake a tsakiyar tekun Da isarsu wannan guri sai duk suka maida makamansu cikin kufe Suka kama tsaunin suka dinga hawa kansa kamar kadangaru Ba tareda ko daya daga cikinsu ya fadi ba saida suka shafe sa'o'i hudu suna hawa sannan sukaje karshensa Inda ya kasance mai matukar fadi da girma sai kace wani babban birnin Akan tsaunin kuma wata iriyar dankareriyar fadace mai girman gaske Wacce tun a jikin bangon gininta na waje zaka san cewa gurine wanda aka kashe dukiyoyi masu dumbin yawa wajen ginashi Gabaki daya zanen da akayiwa bangon fadar ado dashi anyishine da zallan danyen zinare Sai sheki yake da daukar idanu Gababki daya jikin wannan fadar babu wata alama da zata nuna maka cewa ga hanyar da zakabi ka iya shiga cikin fadar Domin ko ina ajikinta a sumulmule yake kamar kwai koda ganin wannan fadar duk sai suka tsaya sukayi cirko cirko abakin ginin Suna tunanin hanyar da zasu bi su shiga cikinta sid suka dan jima suna tsaye ba tareda wani yace d wani uffanba Sannan walisa tace yanzu acikinku ajwai wanda yasan hanyar da zamubi mu shiga cikin wannan fadar? Koda jin wannan tambayar duk sai sukayi shiru suna nazari daga can sai marfuza tayi murmushi tace Ai dukkan mu nan babu wanda yasan hanyar da zamubi don shiga wanna fadar a halin yanzu Don haka abinda ya kamata muyi shine kawai mu fara bincike inyaso daga karshe sai mu yanke hukunci Dajin haka sai sarki aryan yace kwarai kuwa maganar marfuza gaskiyace Ba tareda gardamar komaiba dukkansu suka amince da shawarar marfuza Suka cigaba da neman kofar wannan kogo saida suka kwana suka yini suna bincike ba tareda sun sami ko 'yar karamar alamaba wacce zata nuna cewa ga hanyar shiga kogon A safiyar kwana na biyun ne suna zaune akan tsaunin da suka tabbata da cewa idanunsu ba zasu nuna musu kofar wannan fadar ba Sai suka tsugunna sukayi alwala sukayi nafila acikin nafilar ne suka roki ubangiji akan ya nuna musu Hanyar shiga wannan fadar ai kuwa basu gama rufe bakinsu ba Sai suka ga wani irin haske ya daki bangon fadar Take bangon ya amsa kuwa sannan sukaga yana budewa da kansa Sannu a hankali sai sukaga wata iriyar katuwar kofa wacce aka sana'anta ta zallan dutsen lu'u lu'u ta bayyana Koda ganin wannan al'amari sai dukkansu suka kamu da farinciki Suka mike tsaye suka karasa bakin kofar suka tura kofar da hannunsu Ai kuwa take sai sukaga kofar ta bude babtareda sun sha wata wahalaba Duk da tsananin girman da kofar take dashi sannan suka kutsa kai suka shiga cikin fadar ME ZAI FARU A CIKIN WANNAN FADAR? SHIN YARIMA WALISU YANA FARKAWA DAGA BARCIN DA YAKEYI? DON JIN AMSOSHIN WADANNAN TAMBAYOYI SAI MU HADU A KASHI NA GABA DAGA NAKU HABIBULLAH KBR LIKE COMMENT AND SHARES******************HATSABIBAN SADAUKAI CI GABAN ZUBAR DA JINI **************7 PART A LBR ****************HABIBULLAH KBR Suna shiga cikin fada sukaga wani haske ya dallare musu idanu Saboda tsananin hasken da yake cikin fadar ba komaine yasa fadar take da haske ba face Cikinta gaba daya an kerasu ne zallan dutsen lu'u lu'u Saboda tsananin kawata fadar da akayi sai dukkansu Suka zama zallan 'yan kauye suka kama waige waige da dube dube Tamkar basu taba ganin kayan kawa ba saida suka shafe sa'o'i hudu suna ta shiga sakuna acikin fadar basu hadu da wani mugun abun ba A wannan lokaci ne suna cikin tafiya kwatsam sai suka tsinci kansu a cikin wani katon daki Suna shiga cikin dakin sai kofar sa ta maida kanta kulle Sannan ta saje da jikin bango yadda ba zaka taba sanin ta yadda zaka bude ta ba Akarshen dakin ne suka hangi wata kofa wacce ta nan ne zasu ketare su fita daga cikin dakin Koda kofar ta gama rufe kanta sai wani duhu yazo ya lullube dakin yadda ko tafin hannu ba zasu iya gani ba Dakin kuma yayi tsit baka jin sautin komai Da ganin wannan al'amari sai duk suka tsaya cak Suka zare makamansu suka ruke su da hannu sannan suka ci gaba da kutsa kai cikin dakin duk da cewa basa iya ganin abinda yake cikin sa Suna cikin wannan hali ne suka hangi wasu jajayen abubuwa guda biyu kamar fitilar itace a dan gaba dasu Da ganin wadannan abubuwa sai sarki aryan yace dasu walisa ku jirani Bara na dauko mana wadancan fitilun domin mu dinga haska gabanmu saboda hakan zaifi mana sauki wajen tafiya tunda acikin duhu ba zamu san abindake gabanmu ba Yana gama fadin haka sai ya nufi inda wannan haske yake Yana zuwa yakai hannuwansa da nufin ya daukesu ba zato ba tsammani sai yaji an gabza masa wani mahaukacin duka. Agadon bayansa Saboda karfin dukan saida ya fadi kasa da rub da ciki Jini yayi fitar burgu daga cikin hancinsa da bakinsa Ba komai bane yayi masa wannan dukan ba face wani dan karamin batayin aljani Wanda gaba dayansa an halicce shi ne da wuta wadannan haske da sarki aryan ya gani ba komai bane face kwayar idanuwansa Take batoyin ya mike tsaye daga kwancen da yake yayi wani irin karaji gami da kuruwa Sautin karajin nasane ta cika kunnen su marfuza kuma ya ankarar dasu akan abinda yake faruwa Kafin suyi wani yunkuri tuni batoyin ya wangame katon bakinsa Ya huro musu wata wuta daga cikin bakin cikin bakin zafin nama duk su biyun suka daka tsalle sama kamar an harba sifirin suka kaucewa wutar daya watso musu Ta samu bango take gurin da wutar ta zuba ya tarwatse wuta ta kamaci ganga ganga Koda ganin sun kaucewa wannan harin daya kawo musu saiya daka tsalle sama ya kawo musu wani mummunan sara da wata takobi da take hannunsa da nufin ya tsargesu biyu Cikin bakin zafin nama suka sunkuya takobin tasa ta wuce ta saman kansu Sannan sukayi sulu suka je inda sarki aryan yake suka daukeshi suka direshi a gefe daya kafin batoyin ya sake kawo musu wani harin tuni walisa ta jefeshi da sandar da take hannunsa Aikuwa sandar na sauka ajikinsa sai take ya zagwanye kamar ruwa ya narke, Sannan walisa ta dauki sandar tasa suka ci gaba da tafiya acikin gidan suna kutsawa ta cikin dakuna daban daban WANNAN SHINE ABINDAYA FARU GASU WALISA BAYAN SUN SHIGA FADAR YARIMA WALISU ***** ****** ******* Al'amarin yarima walisu na ainihi kuwa tun lokacin daya kirkiri wani sabon yarima walisun Shi kuma ya sami guri ya kwanta domin yin barci saboda tsawon lokacin daya dauka ba tareda yayi barci ba Sai kawai yayita shara barci abinsa kamar bazai taba tashi ba Saboda tarin barcin da yayi yawa a idonsa sai daya shafe wata guda da kwana uku Yana wannan barcin ba tareda ya farka ba sai a cikon kwana na ukun ne da tsakar rana ya farka daga barcin da yakeyi Koda farkawarsa sai kawai ya iske walisun daya fitar daga jikinsa Ya kurawa madubin tsafin ido sai faman dube dube yake da kuma nazari kan wasu abubuwan Koda ganin haka sai take yayi nuni da hannunsa zuwa kan madubin tsafin Take sai madubin yabar mazaunjn da yake ya dawo nasa hannun Cikin sauri sabon walisun ya juyo don yaga wanda ya karbi madubin Kawai sai yayi ido biyu da mai gidansa walisu cikin sauri ya rissina yace gaisuwa nake a gareka ya mai gidana Ba tareda yarima walisu ya bashi amsa ba ya ci gaba da kallon madubin tsafin Acikin madubin ne yaga abubuwan da suka faru gasu Walisa tun a lokacin da suka fada cikin ramin da wuta takeci acikinsa Har zuwa sanda suka shigo cikin fadar tasa koda ganin abinda ya faru sai ya takarkare ya kwarara uban ihu wanda yasa gaba daya komai dake cikin fadar saidaya kama girgiza Hatta su walisa saida suka jiyo wannan sautin Shi kuwa walisu na biyu take jikinsa ya fara kyarma da rawar dari kamar wanda aka jefa acikin kogin kankara saboda tsananin razana Cikin sauri walisu ya cakumi kwalarsa yace ka tabka babban kuskure Da har ka zauna zaman kallonsu ba tareda ka kashe su ba tun kafin su shigo cikin wannan fadar ba Don haka barinka zaman lura dasu da nayi kuskure ne agareni babba Yanzu dole ne kabar duniyar nan Dajin haka sai jikinsa ya fara kyarm yace Ya shugabana ka gafarta mini kada ka rabani da wannan duniyar taku Domin yanzu na san mahimmancinta ni kuma nayi maka alkawarin da kaina zan fita ba zan dawo ba sai dauke da kawunansu Dajin wannan batu sai take ya takarkare ya sheke da dariya daga can kuma sai ya murtuke fuska Yace ai kuwa ka makara domin yanzu baka da amfanin komai agareni Yana gama fadi haka sai take ya nunashi da yatsansa faruwar hakan keda wuya sai take walisun na biyun ya bace bat Yace shirmen banza ai ka gama amfani a wajena ni da kaina zan tunkaresu Gaba da gaba domin na nuna musu banbancin dake tsakanin mu Na rantse da gunki larazub kaf cikinsu babu wanda ba nine zan shayar dashi gubar mutuwa ba Yana gama fadin sai ya takwankwashe kafafunsa ya shiga yin wani sabon binciken acikin alkaluman tsafinsa WANNAN SHINE ABINDAYA FARU GA YARIMA WALISU BAYAN FARKAWARSA DAGA DOGON BARCIN DA YAYI ******* ********* ******* Su kuwa su walisa bayan sun kashe wannan batoyin sunci gaba tafiyarsu Kamar masu tafiya acikin gidajensu saboda yakinin da suke dashi kan taimakon Da ubangiji zauyi musu sai sukayita tafiya acikin wannan fadar suka fita daga cikin dakin da batoyin yake suka nufi daki na gaba Suna zuwa bakin kofar sai suka saka hannunsu suka tura sai Sukaji kofar a kulle gam ko alamar motsi batayi da ganin haka sai dukkansu suka ja da baya sannan suka taho da gudu Lokaci guda suka daka tsalle suka dake kofar dakin da kafafunsu Koda suka daki kofar sai sukaji kamar kafafunsu zasu karye Saboda zafi da radadin da sukaji don haka duk sai suka tattara karfinsu Guda suka fara aikin tura kofar, nanfa damatsansu suka kukkumburo sukayi burdin burdin kamar jijiyoyin bishiyoyi saboda mikewar da kwanjin hannayensu sukayi sai da hannuwan rigunansu suka faffarke Saida suka jima suna aikin tura wannan kofar ba tareda ta fadi ba Har saida jikinsu gaba daya ya jike sharkaf da gumi bisa dole duk hajura da tura kofar suka tsaya a gurin sunata faman haki Kamar wadanda suka yini suna gudu acikin rana bisa dole suka hakura da tura kofar suka tsaya cak suna nazarin yadda zasubi su bude wannan kofar Suna cikin wannan tunanin ne sukajiyo wani irin sauti yana fitowa daga wani cikin wannan kofar Cikin sauri marfuza ta juyo ta dubi su aryan tace Shin kuna jiyo wannan sautin da yake fitowa kuwa ? Dajin wannan tambayar sai aryan yace Kwarai kuwa amma wannan sautin bana bil'adama bane Na wata iriyar babbar halittar ne kuma wannan halittar dolene ta kasance babba mai matukar kwarjini da karfin damtse……… .. Kafin ya gama fadin abinda yake bakinsa Tuni sai sukaji an daki murfin wannan kofar Cikin sauri duk su ukun sukayi alkafira a suka kace daga gurin Alokacin ne sukaga kofar tayi sama kamar an buga kwallo Kofar tayi sama saboda karfin dukan sannan ta fadi acan gefe daya Da ganin wannan abu daya faru sai duk su walisa suka kamu da tsananin mamaki Suka tsaya a inda suke suna jiran suga ko menene zai fito Suna tsaye a wannan guri kawai sai sukaga irin maridi mai kirar mutanen farko ya fito daga cikin dakin Hannunsa guda ruke yake da wani irin almudi mai cike da hakora zako zako wanda ana dukan mutum dashi take zai dagargaza masa fuskarsa Koda bayyanar wannan wannan maridi sai ya cika dakin gaba daya saboda girman jikinsa da kuma kaurinsa Kawai sai ya bude hancinsa ya fara shinshine shinshine domin gano ko menene acikin wannan daki Yana cikin shinshine shinshinen ne kawai ya hangi su gimbiya walisa a gefe daya a tsaye Hannunwansu ruke da makaman yaki koda ya hada ido dasu Sai kawai ya rugo da gudun gaske zuwa kansu karfin gudun nasa ne .yasa kasar dakin ta fara girgiza kamar zata dare komai ya rufta karkashinta Kafin maridin ya isa inda suke tuni suma sun taho da gudu Zuwa kansa ba tareda tsoron girmansa ba suna haduwa kuwa sai take suka kaure da mahaukacin yaki a atsakaninsu ya zamana suna kaiwa junansu mugayen hare hare Kamar wasu tsofaffin abokan gaba cikin tsananin zafin nama, juriya da bajinta Nanfa guri ya hargitse da gumurzun maza suka saka maridin a tsakiya Tako'ina suna masu kai masa zafafan hare hare shi kuma yana karewa aduk sanda ya kawo musu suka kauce duk abinda ya daka take yake dagargajewa kamar ana daka kuli kuli Shi kuma ko kadan yaki yarda su sami damar koda lakutar jikinsa Kafin a dauki lokaci mai tsawo tuni wannan daki ya hargitse Katangu suka dinga zubowa daga samansa in badon su walisa nada matukar zafin nama ba da tuni dutse ya dannesu gabaki daya sun mutu Koda suka dauki lokaci mai tsawo suna wannan fafatawar sai wannan maridi ya fusata Ya dinga hadawa da kai musu naushi gami da bugu hannu da kafa Wanda inbadon suna zulle zulle da gocewa ba da gabaki dayansu lokaci guda zai mitststsike su Sai da suka shafe sa'a guda a haka suna wannan yakin Ba tareda da daya daga cikin su ya sami nasarar koda lakutar jikin juna ba Da zarar makamansu sun hadu da makanin da yake hannunsa Sai dai kaga wani irin tartsatsin wuta ya tashi nanfa sautin karar karafkiyar karafa ta cika dodon kunne Koda su sarki aryan suka fahimci cewa tabbas karfin su da iya yakinsu Ba zasu kwacesu ba a hannun wannan maridin sai suka dinga karanta addu'o'in neman tsari acikin zukatansu Faruwar hakan keda wuya sai sukaji wani irin gagarumin karfi ya shiga jikinsu kamar zasu iya nada gammo su dauki duniyar gabaki dayanta Aikuwa sai nan da nan suka sakash a tsakiya suka dinga hada masa naushi da bugu tako'ina Cikin kankanin lokaci duk wannan girman nasa sai ya zama na banza Domin mayar dashi sukayi kamar karamin yaro sai gashi suna ta saran jikinsa babu kakkautawa jini yana shatata kamar an bude magudanr ruwa Aikuwa nan da nan dakin ya cika da jini maridin ya dinga kwarara ihu domin neman taimako Suna cikin wannan fafatawar ne walisa ta shammaceshi Ta tafi da gudu ta taka wani rusasshen sannan ta daka tsalle sama kamar ta kasance tsuntsuwa Ta dira a tsakiyar kirjinsa ta daga sandar dake hannunta Ta caka masa ita a tsakiyar kirjinsa take sandar ta huda tsakiyar kirjinsa ta nutse aciki Jini yayi feshi daga cikin kirjin nasa nantake ya kwarara uban ihu saboda tsananin zafi da zugin da yaji Cikin sauri ta zare sandar ta dira akan kasa bisa kafafunta Shikuwa maridin sai ya sulale ya fadi kasa matacce Ba tareda bata lokaci ba su walisa suka ci gaba da tafiya suka fita daga wannan dakin ta cikin kofar da maridin ya bude musu suka shiga daki na gaba. Suna shiga cikinsa sai suma gansu acikin wata tangamemiyar fada wacce tafi duk wadanda suka wuce a baya girma da kawatuwa A tsakiyar fadar kuma babu komai face YARIMA WALISU Cikin gagarumar shigar yaki ya tsaya cak ko motsi bayayi Ya dunkule hannayensa guda biyu fuskarsa kuwa ya rufeta da wata hular karfe Wacce ta rufe fuskar tasa gaba daya babu abinda ake gani face idanuwansa Gaba daya kayan dake jikinsa launinsu launi ja ne haka ma makaman yakinsa Ya rata wasu takubbai guda biyu ajikin kugunsa sannan a gadon bayansa ya daure sandarsa ta tsafi. Kallo daya zakayi masa kasan cewa a matukar fusace yake da kuma shirin AYITA TA KARE Koda su walisa sukayi arba da yarima walisu sai suma suka tsaya cak suna mai fuskantarsa Gimbiya walisa ce a kan gaba sai kuma marfuza da sarki aryan Na take mata baya nanfa suka tsaya suka fara kallon kallo a tsakaninsu irin wanda ake cewa KAR TA SAN KAR ME ZAI FARU A WANNAN FAFATAWAR TASU? SAI MU HADU A KASHI NA GABA DON JIN CIGABAN WANNAN LABARI DAGA NAKU HABIBULLAH KBR LIKE, COMMENT AND SHARE***************HATSABIBAN SADAUKAI TAKUN KARSHE CI GABAN ZUBAR DA JINI ******************7 PART B LBR **************HABIBULLAH KBR Lokacin da aka tsaya akayi kallon kallo tsakanin yarima walisu dasu gimbiya walisa Sai kawai yayi musu wata ýar karamar dariyar mugunta Yace lallai yaro bai san wuta ba sai ya taka nayi muku alkawarin daga yanzu Wasan buya tsakanina daku ya kare domin dukkanku babu wanda bazan dandanawa zakin mutuwa da tafin hannuna ba Kuma ina tabbatar muku da cewa koda ban kashe ku da karfin sihirina ba To zan kashe ku da zallan karfin damtsen da nake dashi…. Kafin ya gama fadin abinda yake fada tuni walisa ta daka masa tsawa tace Karyarka tasha karya baka isa kayi mana abinda ubangiji bai kaddara zai same mu ba Koda gama fadin haka sai ita dasu marfuza suka tafi da gudu Zuwa inda yake suna zuwa duk su ukun sai suka daka tsalle a tare suka kai masa duka da kafafunsu da nufin su kaishi kasaa Ai kuwa koda suka daki jikin nasa sai sukaji kamar sun daki dutse ko motsawa baiyi ba Al'amarin daya matukar basu mamaki kenan don sun san komai girman katanga idan sukayi mata wannan dukan dolene ta fadi saboda tsananin karfin dukan Mai makon ma suga alamar yaji zafin dukan sai kawai yayi musu wani murmushin mugunta yace Wannan shine iyakar karfin da kuke takama dashi? To ya kamata ku kara zage damtse domin yaki dani ba karamin aiki bane Kafin su ankara ya jefo musu addar da take hannunsa Inbadon sunyi gaggawar kaucewa ba da sai addar ta tsinke musu kawunansu gaba daya kuma alokaci guda Koda suka kaucewa addar ta tafi sai take ta tsarge wani dirkar gini gida biyu Kamar an raba takarda da reza sannan addar ta dawo zuwa hannunsa Ba shiri sai ya runtse idanunsa sannan ya nuna su walisa da tafin hannunsa Take wata bakar guguwa ta fito daga cikin tafin hannun nasa tayi kan su walisa Take duk ta debesu tayi sama dasu alokaci guda ta dinga Wujijjjigasu asaman iska tana gwara jikinsu da jikin bangon gini Kafin a dauki wani lokaci tuni sun fara fita daga hayyacinsu Suna cikin wannan halin ne suka tuna da wata addu'a da take cikin littafin da suka tsinta Koda tunawa da wannan addu'ar sai take suka karanta ta Aikuwa faruwar hakan keda wuya sai wannan iskar ta bace bat Da ganin haka sai walisu ya dinga jefo musu bala'o'i kala daban daban domin yaga sun hallaka Amma duk abindaya jefo musu kafin ya sauka ajikinsu Yake lalacewa komai karfinsa da hatsarinsa kamar irinsu wuta, kankara, kibiyoyi, bakaken aljanu, da duwatsu da dai sauransu Koda ya fuskanci duk wadannan abubuwa ba zasuyi tasiri akansu walisa ba Sai ya gyara tsawuwar sa daga inda yake sannan yayi wani murmushi wanda suka kasa gane me yake nufi yace dasu Yanzu na fuskanci gaba ki dayanku kunfi so muyi gaba da gaba Domin fuskokinku ne suka nuna haka idan har kun shirya sai mu gwada 'yar kashi Ba tareda amfani da karfin sihirinmu ba Nima nayi alkawari bazan yi amfani da karfin sihirina ba Kuma inaso kuyi alkawarin ba zakuyi amfani da sihirinku na ma'abota addinin musulunci ba Koda jin wannan batu sai su walisa sukayi sukayi shiru suna nazari akan maganar tasa Daga can kuma sai sukace sun amince suna fadin haka sai suka ruga kansa suka kai masa wasu mahaukatan hari da makamansu Cikin bakin zafin nama ya sunkuya suka sari iska sannan yayi katantanwa atsakiyarsu kamar wani shaidani Alokaci guda dukkansu ya nannaushesu akan ruwan cikinsu Sai gashi saboda karfin dukan duk sai daya tarwatsasu Tun kafin su sauka akan kasa tuni yayi tsalle yabi walisa a saman da take yasa kafarsa

Chapter 12 of 13