Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
kuwa su marfuza sai hankalinsu ya tashi suka kara zage damtse wajen yakar kadar Kuma a wannan lokaci babu abinda yake tayar musu da hankali face rashin samun iskar da zasu shaka akasan ruwan Ita kuwa kadar sai ta kara haukacewa gurin kawo musu mugayen hare hare yadda duk wanda yayi kuskure ta sameshi take duk kashushuwan jikinsa zasu kakkarye kuma ya mutu Bisa wannan daliline yasa hankalinsu ya kara dugunzuma fiyeda kowanne lokaci Don haka koda suka fuskanci idan suka kara daukar dogon lokaci a kasan wannan ruwan zai kai ga cewa bama zasu iya jure rashin shakar numfashin da suke ba Don haka duk su biyun sai sukayi ninkaya suka daki ruwan dukkansu suka taso samansa Take itama kadar ta biyosu saman ruwan amma kafin ta gama tasowa su marfuza sun rigata Don haka koda tasowarta sai duk gaba dayansu suka haye kan gadon bayanta wanda fadinsa yafi kaurin manyan bishiyar kuka guda biyu Wannan tasowar da kadan yayi saman ruwan shine ya baiwa gimbiya walisa wacce ta tsaya a makogaron kadan damar da itama zata shaki numfashi Domin inda ace an kara daukar wani lokaci mai tsawo a kasan ruwan za'a iya kaiwa ga lokacin da ba zata iya jure rashin numafashi ba Har ta fada cikin kadan Don haka sai walisa ta saka hannunta na dama ajikin kugunta Na hagun kuma yana ruke da takobin ta kwanto wata 'yar karamar wuka ajikinta Ta dinga cakawa ajikin makogaron kadar ai kuwa sai kadan ya dada gigicewa ya manta da batun su sarki aryan da suke zaune a saman kansa Ya dinga birgima a saman ruwan Su kuwa su marfuza sai suka yita sukan jikinsa da makaman da hannunsu Saidai kuma duk da cewa suna saransa da kuma sukarsa kuma makaman nasu suna tasiri ajikinsa sai hakan ya zama na banza domin duk abinda sukeyi masa jinsa yake kamar susa suke masa ajikinsa Ana cikin wannan haline kawai sai kadan yayi wani irin gunji mai karfin gaske Take jikinsa ya fara rikidewa zuwa siffar wani irin rikakkiyar gamsheka Mai kawuna biyu girmansa kadai ya isa abin tsoro da kuma firgitarwa Koda komawarsa zuwa siffar gamshekar sai take ta kumbura jikinta tayi jifa dasu marfuza da suke kanta zuwa kan wannan tsuburin Take dukkaninsu suka yi sama suka fado akan tsuburin Saboda buguwar da suka yi saida suka ji kamar kashushuwan bayansu duk sun kakkarye Take wani jini yayi fitar burgu daga cikin hancinansu da kuma bakinsu Cikin karfin hali suka mike tsaye suna masu dafe kugunsu Da kuma gyara rikon makamansu Ita kuwa gamshekar sai ta taho kasan wannan tsuburin dasu marfuza suke kai Kawai sai ya ajiye kawunan nasa guda biyu akasan tsuburin Sai ga kawunan guda biyun sun hade sun zama guda daya Sannan ya fara kokarin amayar da walisa daga cikin makogaronsa Take walisa ta fado daga ciki bakin nasa jikinta duk yana faman wani irin maiko mai kauri Tana dira a kasa sai gamshekar ya kawo mata duka da katon kan nasa da nufin yayi mata rotse Cikin bakin zafin nama ta daka tsalle sama ta koma can gefe daya Kan nasa ya sami duke take dutsen da yake gurin ya dagargaje kamar an nikashi Cikin sauri gimbiya walisa ta ruga da gudun tsiya shima macijin sai ya bita suka kasa tseren gudu suka dinga hawa kam dutsen kuma har a sannan bai daina kawo mata sara ba Koda suja kusan zuwa karshen tsuburin sai kawai su jaruma marfuza suka dako tsalle daga inda suke tsaye suka kaiwa gamshekar mugun sara da nufin su datse kansa Koda makaman nasu suka sauka ajikinsa sai wata irin kara ta tashi kamar haduwar karfe da karfe Cikin zafin nama gamshekar ta shammacesu su biyun ta kanannadesu Da jelarta yadda ba zasu iya kwacewa ba kawai sai ta sulale ta koma cikin tekun da gudun gaske domin ta cinyesu aciki Koda walisa taga abinda yake shirin faruwa ga abokan tafiyarta sai ta kwallara ihu Kawai sai ta falfala da gudu tabi wannan gamshekar da gudu tana mai karanta wata addu'a acikin zuciyarta Bisa mamaki sai taga tana tafiya a saman ruwan kamar akan kasa kuma cikin wani irin mugun gudu Kafin ta riski gamshekar tuni Tayi kasan ruwa gaba daya ta daina ganinta nantake itama gimbiya walisa ta nutsar da kanta gaba daya zuwa kasan tekun Tabi hanyar da gamshekar tabi suka kasa gagarumin tsere da ita Tun suna iya saman ruwa saida suka nutse can kasan tekun Adaidai kasan ne walisa ta hango wani irin katon gida mai girman gaske Da zuwan gamshekar wannan gidan saita shige ciki zuruf Cikin rashin tsoro da kuma dakakkiyar zuciya itama ta kutsa kanta cikin gidan Tana shiga cikin gidan ba zato ba tsammani sai taji an dake ta baya Take tayi sama sannan ta tumu da kasa Kawai sai taga wannan gamshekar ya zo ya rufe hanyar gaba daya ta yadda babu ta inda zata iya bi domin fita daga ciki Da kuma har a sannan su marfuza suna kanannade ajikin jelarta Don haka sai walisa ta mike tsaye cikin yarda da kanta tana mai gyara tsayuwarta Kuma har a sannan bata daina karanta addu'o'in neman tsari da kuma neman taimakon ubangijiba acikin zuciyarta Kawai sai gamshekar ya sake kawo mata wani dukan da dukkan karfinta Cikin zafin nama ta kwallara kabbara da karfi sannan ta sanya takobinta ta sari jikin jelar tasa take jelar ta gutsure gabaki dayanta Su sarki aryan suka fado daga jikin jelar acikin wani irin mawuyacin hali mai kama da mutuws da rayuwa cikin sauri walisa ta debesu ta kaisu can gefe daya kawai sai gamshekar tayi wani irin mahaukacin gurnani Kawai ta taso kan walisa gabaki daya suka kachame da masifaffen fada Sai gashi a wannan lokaci albarkacin addu'ar da takeyi suna samun wadatacciyar iskar da zasu shaka kamar akan doron kasa suke fafatawar Kuma a wannnan lokacin saita rikirkita gamshekar da wasu mugayen hare hare Cikin kankanin lokaci ta rikitashi gidan da suke ciki ya fara rugujewa saboda artabun da suke yi Nanfa guri ya dada rincabewa da wannan bakin artabun da sukeyi Ana cikin haka ne kawai walisa ta karanta wata addu'a ta tofa ajikin takobinta Sannan ta kaftawa gamshekar sara aikuwa take jikinsa ya dinga narkewa kamar mai acikin wuta ya soma ihu yana karaji Cikin sauri walisa ta dauko su sarki aryan a kafadarta Kafin ta fito daga cikin gidan tuni ya gama rugujewa zai fado kansu ya turmushesu gaba daya ita kanta gimbiya walisa saida wani dutse ya bugeta akan ta Saboda buguwar da tayi ne yasata ta fadi kasa sumammiya Ba zato ba tsammani sai ga sarki fadarul munnar akan aljaninsa sun faso ta cikin ginin gidan sun shigo sun debesu gaba daya Sannan suka taso saman tekun suka luluka Cikin gajimare kamar kiftawar ido Kafin kace meye wannan tuni sun kule acikin iska an daina ganinsu gaba dayansu Kawai sai sarki fadarul munnar ya dora kan gimbiya walisa akan cinyarsa Yasa hannunsa yana shafa kanta, baisan sanda wata kallar tausayi ta zubo masa ba Domin duk wannan halin data shiga shine ya sakata aciki Wannan dalilin ne yasa yaji ya kara kamuwa da matsananciyar soyayyarta Haka dai aljanin yayita gudu dasu asararin samaniya Cikin kankanin lokaci ya ketare wannan tekun ya yada zango dasu acikin wani daji Dirarsu keda wuya sai wannan aljanin ya kafa musu tanti Sarki fadarul munnar da kansa ya zauna ya sakawa su jaruma marfuza magani ajikin ciwukan da sukaji Sannan ya koma kan gimbiya walisa ya daure mata gurin da jini yake zuba daga goshinta Sannan ya dauketa ya shigar da ita dasu marfuza cikin tanti Sannan ya fito wajen tantin ya tsaya yana mai gadin su su sarki aryan basu jima ba suka fara dawowa hayyacinsu Marfuza ce ta fara bude idanunta koda ta ganta acikin wannan tanti sai ta mike tsaye zumbur a razane tunda bata san sanda aka kawota wannan wuri ba Kawai sai taga duk ciwukan da suke jikinsu an diddinke musu su kuma an saka magani Da ganin haka saita cika da mamaki cikin karfin hali ta mike tsaye tana mai dafe gadon bayanta ta leko wajen tantin Kawai sai ta hangi wani kyakkyawan dattijo ya juya musu baya cikin gagarumar shigar yaki Koda dattijon ya jiyo motsi a bayansa sai kawai ya juyo suka hada idanu da marfuza Koda tayi arba da fuskar sa saita kame kyam kuma ta cika da mamaki sakamakon ganin yadda suke matukar kama da gimbiya walisa da walisu kamar an tsaga kara Banbancin kawai shine tsufan daya farayi Kawai sai sarki fadarul munnar yayi mata murmushi yace sannu da kokari jaruma marfuza zaifi kyau ki koma cikin tantin Dajin haka sai marfuza ta koma cikin tantin sarki fadarul munnar Ya bita abaya suka shige ciki Suna isa suka iske har su walisa ma sun gama farfadowa Koda walisa ta hangi mahaifinta saita falfalo da gudu ta rungumeshi Sannan tace ya abbana menene ya raboka da gida kabiyo bayanmu? Idan har burinka shine ka taya mu zuwa neman walisu zaifi kyau ka koma gida domin karkasha wahala mu kadai ma zamu iya dajin wannan batu sai yayi murmushi yace yarinyace ke baki da kaifin tunani Ina tabbatar miki da cewa inbadon nazo akan lokaci ba da tuni gini ya fado muku ya turmushe ku gabaki daya Yanzu dalilin biyo bayanku da nayi shine inaso mu takaice gabaki dayan tafiyar dake gaban ku Mu riski walisu acan inda yake domin ayita ta kare ni yanzu ban damu ba Koda takai ga cewa zai rasa rayuwarsa akokarin rabashi da ruhin boka sahibul ukub Dajin wannan batu sai hankalin walisa ta dugunzuma tace Ya abbana ka daina wannan batun da kakeyi domin ina da tabbacin cewa ubangijin zai bamu taimako akansa Ina fatan kaima zakayi imani da ubangijin musulunci domin tuni muma mun fahimci cewar tsafi karyane kuma zaluntar kaine Babu wani ubangiji na gaskiya face Allah madaukakin sarki Kodajin wannan batu sai jikinsa yayi sanyi yayi ajiyar zuciya Sannan yace yake 'yata bazan tilasta miki ba akan ki bar addinin musulunci ba Domin nima nasan akwai kamshin gaskiya acikinsa Amma har yanzu lokacin yin imani na baiyi ba inaso ne na dada tabbatar da karfin ubangijin musulunci Idan har ya bamu nasara akan takadirin boka wato sahibul a take zan ajiye addinin tsafi kuma na karbi wannan addini Yanzu dolene mu zauna anan don kuyi jinyar raunikan dake jikinku Inyaso. Daga baya sai mu tashi gabaki dayanmu mu nufi can fadar tasa Domin ban baro gidaba sai da muka tsaurara bincike nida boka na Kuma da kyar da makyarkyata muka gano inda fadarsa Take Duk wannan zance da sukeyi ashe aljanin daya dauko sarki fadarul munnar yanaji Koda yaji inda suke shirin zuwa sai ya fashe da kuka Ya fara rokon cewa sarki fadarul munnar yayi masa rai domin bazai iya zuwa fadar yarima walisu ba Saboda tsananin bala'in da yake hanyar fadar*************HATSABIBAN SADAUKAI CI GABAN ZUBAR DA JIN *******************6 PART A ********************LBR HABIBULLAH KBR Koda sarki fadarul munnar yaga yadda hankalin aljani zarikul laham ya tashi Sakamakon jin cewa zai daukesuu ne ya kaisu can fadar yarima walisu Bai san sa'addaya tuntsure da dariya ba yana nuna zarikul laham da dan yatsansa yana ci gaba da dariyar Sai da yayi dariyar ta isheshi sannan lokaci guda kuma ya tsuke bakinsa ga barin yin dariyar Yace dashi Gaskiya ka bani kunya duk da kasancewarka matashi kuma mai jini a jika amma kace kana tsoron mutuwa Ko mu da muke bil'adama bamu sa karaya ba acikin zukatan mu Ka tuna fa cewa wannan aiki da za'ayi yafita daban da wadanda muka sabayi abaya Domin zamuyi shine domin ceton duniya daga kangin zaluncinsa Ya zame maka tilas ka daukemu dukkanmu ka kaimu can fadarsa Domin ceto al'umma daga kangin da yake shirin sakasu nan gaba Mu yanzu ashirye muke da muyi wannan tafiyar koda kuwa hakan zai zamo sanadin ajalinmu Idan kuwa kaki yarda ni da kaina zan yakeka da kaina Dajin wannan kalami sai aljani zarikul laham yaji duk wani tsoro ya gudu daga cikin zuciyarsa Kawai saiyace Ka gafarta mini ya shugabana kuskure ne yasa na firgita da farko Amma yanzu ji nake kamar zan iya yakar sa ni kadai Kodajin wannan batu sai sarki fadarul munnar yayi murmushi Ko kaifa abin kunyane agareka ace kana tsoron mutuwa Da gama fadin haka sai ya juya inda gimbiya walisa ke Ya dora hannunsa akan sai ki cire duk wani tsoro daga zuciyarki Kuma kisa a ranki cewa wahalar da kikasha abaya kamar share fagece Domin yaki yana nan gaba tun kina marmarinsa harsai kin kosa da agamashi Gaskiya dolene a jinjinawa SADAUKI HASSANUL BASARI Domin shi kadai ya tunkari duk wani kalubale na boka sahibul ukub Kuma har ya sami nasara akansa ba tareda ya nemi taimako daga gurin kowa ba Dolene daga yanzu mu dauki kwararan matakai tun daga yanzu Domin tunkarar gagarumin aikin dake gaban mu, dajin wannan batu sai walisa tace kwarai kuwa yakai abbana Su kuwa su sarki aryan da jaruma marfuza sai kawai suka bude bakunansu suna mamakin yadda sarki fadarul munnar ya iya isowa akan lokaci da kuma yadda suke tsananin kama kamar an tsaga kara Don haka sai sarki aryan yaji ba zai iya jurewa ba dole ne yayiwa fadaul munnar tambaya Kawai yace dashi Yakai wannan babban namijin duniya ina da wata tambaya guda agareka kuma ina fatan zaka amsa mini ita ? Kodajin haka sai fadarul munnar yace kwarai kuwa ka fadi duk irin tambayar da kake da ita ni kuma nayi alkawarin amsa maka ita indai har ina da amsar Sarki aryan yace Kai kuwa tayaya ka iya isowa wannan guri adaidai lokacin da muke shirin mutuwa akasan teku? Dajin wannan tambaya sai sarki fadarul munnar ya bushe da dariya daga can kuma saiya tsuke bakinsa ga barin yin dariyar yace Ai duk wannan abinda nayi bai kamata kuyi mamaki akansa ba Domin dukkanku kunsan karfin sihirin da nake dashi Saidai kuma duk wannan bai kai aikinda kukayi abin al'ajabi ba Domin kun nuna jarumtakar da ba kowanne jarumi ne zai iya yin kamarta ba Saboda tsawon lokacin da kuka dauka akasan teku kuna fafata yaki Yanzu haka abu guda daya ne yake dada bani tabbacin cewa zamu sami nasara akan boka sahibul ukub wannan abu kuwa ba komai bane face Addinin musuluncin da kuka karba nasan cewa shine kadai makamin da zai taimaka mana wajen tunkarar sa Domin tun a wancan zamanin shine makamin da ya hanashi samun danar cika burinsa Koda yazo daidai nan azancensa sai aryan yace indai kuwa har kayi imani da ubangijin musulunci zai taimake mu To mai zai hana ba zakayi imani dashi ba ? Kodajin wannan tambaya sai fadarul munnar ya hade fuskarsa kamar wanda yake cikin fushi Daga can kuma sai yayi murmushi yace Lokacin da zaka san wannan dalilin baiyi ba amma nayi muku alkawarin muddin muka sami nasara akansa to a take anan zan karbi addinin musulunci Yana gama fadin haka saiya tsuke bakinsa Bai kara cewa komai ba ya fice daga cikin tantin da suke zaune Ya koma waje ya cigaba da aikin tsaron lafiyarsu Saida suka shafe kwanaki goma sha daya suna zaune a wannan guri Sannan ciwukan jikinsu suka warke sumul don haka sai suka hada kayayyakinsu Domin ci gaba da tafiya kowanne daga cikinsu a wannan lokaci Yayi gagarumar shigar yaki domin su nufi can fadar da yarima walisu yake zaune Ba tareda bata lokaci ba suka haye bayan aljani zarikul laham Shi kuma ya bude fuka fukansa ya tashi dasu sama kamar kiftawar ido haka ya danna kansa cikin gajimare ya bace bat aka daina hangoshi Cikin kankanin lokaci ya dinga shafe tafiya mai nisan gaske Suna tafiyar suna hira abinsu kamar babu wani abu da yake damunsu Saida suka shafe sa'o'i goma suna tafiya suna dada keta hazo domin zuwa fadar da yarima walisu yake zaune Domin a wannan lokaci hatta fadar tasa ya canjata daga inda take ya koma can yammacin duniya bisa kan wani dogon tsauni Kafin mutum ya iya isa inda wannan tsaunin yake dolene ya fuskanci tarkuna kala kala Masu cike da ruwan bala'i akan hanya ,domin dolene ka ratsa ta cikin wasu sihirtattun dajijjika masu cike da nau'ikan bala'i kala daban daban kuma abinda zaka tarar acikin daji na biyu yafi abinda yake daji na farko bala'i Haka suke rukuni rukuni dole saika wuce ta wadannan tarkuna sannan zaka isa can fadarsa inda kuma nane yafi ko'ina hatsari da kuka bala'i Saboda komai na wannan fada ya fita da ban da wanda ke cikin dajijjikan dake baya Abune mawuyaci mutum ya iya ratsawa ta cikin wadannan dajijjikan har ya iya shiga cikin fadarsa ba tareda ya rasa rayuwarsa ba WANNAN SHINE ABINDAYA FARU GASU SARKI FADARUL MUNNAR BAYAN SUN TASHI DA NUFIN ZUWA FADAR DA YARIMA WALISU YAKE ZAUNE **** ******* ********* A can kuwa bangaren yarima walisu kuwa tun daga lokacin daya baro can rijiyar da abin bautarsa yake Wato gunki larazub kamar kiftawar ido haka ya bayyana abakin fadarsa wacce yake zaune acikinta Da zuwansa sai ya daga hannunsa na hagu ya dunkuleshi Take sai fadar tayi bindiga kamar ansa mata nakiya Ta ruguje gabaki dayanta da komai da komai na cikinta sannan ta kama da wuta ta kone kurmus Faruwar hakan keda sai ya bushe da dariya sannan ya juya ya bar wannan dajin gabaki daya yana mai cewa yanzu na gama da wannan fadar wani sabon mulkin zan kafa Cikin kankanin lokaci ya isa can karshen duniya bangaren yamma Cikin wani kungurmin daji mai cike da abubuwan firgitarwa Da isarsa tsakiyar wannan dajin saiya nuna wani dan karamin dutse dake tsakiyar dajin Take wannan dutse ya kumbura alokaci guda kamar an buga masa isa Ya zama wani irin zabgegen tsauni tareda tangamemiyar fada. Asamansa Duk acikin abinda bai wuce dakiku goma ba Ita kanta wannan fadar ba karamin girma ne da itaba Kai tsaye ya tashi sama kamar tsuntsu mai fuka fuki ya haye saman sabuwar fadar tasa hawansa keda wuya sai ya nuna iyakar dajin da sandar sihirin dake hannunsa Yin hakan keda wuya sai ga wasu irin mugayen halittu sunata ciccidowa daga cikin karkashin kasa marasa adadi Wanda idan mutum yayi ido biyu dasu take zai iya zaucewa idan har baida dakakkiyar zuciya Kuma wadannan halittu jinsi daban daban ne ba dayaba Bayyanarsu keda wuya sai duk suka dinga warewa kowanne yana zuwa inda jinsinsa yake suna dunkulewa guri guda Suna gama haduwa duk sai sukayi sahu sahu suka durkusa suka yiwa yarima walisu sujjada Faruwar haka keda wuya sai ya tuntsure da dariya ya kallesu gaba dayansu da kwayar idanunsa Nantake wata iska mai karfi ta fito daga cikin idanunsa Ta shuri wadannan halittu gabaki dayansu ta rarraba musu mazauni Sannan ya juya ya shige cikin fadar tasa wacce ta kawatu ainun da kayan alatu fiye da wadanda suke cikin tsohuwar fadar tasa Saidai kash !!! Komai na wannan fadar kyan dan maciji ne dashi idan har kayi kuskure akansu Komai da yake cikin tsohuwar fadar tasa a kwaishi acikin wannan Harma yafi wancan na da din amfani da karfin sihiri Yana isa tsakiyar fadar saiya iske karagarsa ta tsafi wacce aka san'anta ta da zallan haske kai tsaye ya haye kan wannan karagar tareda fuskantar madubinsa na tsafi wanda aka sana'anta shi da zallan dutsen lu'u lu'u sai sheki da walwali yake Yana dallare idanu saboda haskensa Zamansa keda wuya saiya shafi madubin da tafin hannunsa Take sai hoton su sarki fadarul munnar dasu gimbiya walisa ya bayyana ajikinsa tun sanda wannan kadar sihirin ya farmakesu a tsakiyar teku suka fafata yaki dashi har suka kashe shi D kuma sanda suka taso da nufin zuwa sabuwar adarsa domin yakarsa Da ganin wadannan abubuwa saiya bushe da dariyar mugunta Domin yasa cewa su da kansu suke kawo kansu ga halaka kuma suna shirin hutar dashi ne saboda yana da tabbacin muddin suka taka kafarsu suka shigo cikin iyakar dajinsa babu guda daya daga cikinsu wanda zai tsira da rayuwarsa Saboda yasan irin bala'in daya zuba a cikinsu Saida yayi dariyar ta isheshi sannan yace Hakika yau shekaru dubu biyu da 'ya'ya zasu maimata kansu Kamar yadda a wancan lokacin HASSANUL BASARI ya shigo cikin fadata ya yake ni Saidai kuma a wannan karon nine zanyi nasara domin har a bada bazan sake yarda na fadi kasa ba Harsai na mallaki duniya ta dawo zuwa karkashin ikona don a nan gurin zan zauna na jira isowarsu nan cikin fadata idan har sun cika HATSABIBAN SADAUKAI Kuma koda ma sun sami damar shogowa cikin fadata da hannuna zan kashesu gabaki daya na shayar da jininsu ga gunki larazub Yana gama fadin haka saiya mika hannunsa kan wani teburi dake can wani bangare na fadar Take hannun nasa ya kara tsawo kamar ana jansa yaje har inda wannan teburin yake ya dauko wani kofin zinare dake ajiye akansa Kawai saiya kafa kofin a bakinsa ya shanye ruwan da yake ciki Shan ruwan keda wuya sai yaji ya kamu da wani matsanancin barci Alhalin rabonsa dayin barci tun a ranar daya shiga jikin yarima walisu Shi kansa yayi matukar mamakin wannan al'amari don haka koda yaji wannan sauyin yanayin Kuma shima ya tabbatarwa dakansa cewa yana da bukatar ya sami hutu na tsawon lokacin daua dauka yana barcin Sai kawai ya sanya hannunsa akan fuskarsa ya shafata Take ya rabu gida biyu, ma'ana wani yarima walisun ya sake fita daga jikinsa kuma kamarsu daya sak babu banbanci Kuma duk abinda shi yarima walisun na gaskiyar zai iya yi to shima zai iya Da bayyanar wannan sabon walisun Sai na gaskiyar yayi murmushi yace yanzu nima zanyi barci na mai dadi Ba tareda an sami wani kuskure ba alikackm da nake barci Yana gama fadin haka sai wannan karagar tasa ta rikide ta koma katon luntsumemen gado Shima na haske mai taushin gaske ba tareda fargabar komai ba ya kwanta kwanciyarsa keda wuya sai barci ya daukeshi Shi kuma sabon yarima walisun sai ya sami guri ya tsaya cak ya kurawa allon tsafin ido yana kallon su sarki fadarul munnar Yana cikin kallon ne kawai yaga har sun kusan isowa bakin iyakar daji na farko Da ganin haka sai kawai shima yayi dolene ya darsa musu da tsoro acikin zukatansu Da gama wannan tunani sai ya runtse idanunsa ya karanta wasu dalasiman tsafi Sannan ya bude idanun nasa ya nuna su acikin madubin tsafin da babban yatsansa Take wata irin guguwa tayin fitar burgu daga cikin da yatsan nasa ta shiga cikin madubin tsafin nasa Su kuwa su sarki fadarul munnar a wannan lokaci suna bayan aljani zarikul laham Yana ta tsala gudu dasu a sararin sama a wannan lokaci kawai sai aljani zarikul laham yaji kamar an daure masa dukka fuka fukansa Sannan sukaji wata irin kwalleliyar tsawa daga sama wadda saboda karfinta Sai da sukaji kamar zuciyoyinsu zasu fashe su faso kirazansu su fito waje gabaki daya suka manta da wasu addu'o'i saboda dama kuskuren da sukayi kenan tun farkon tasowarsu hira kawai sukeyi sun shagala ga barin addu'o'i acikin zukatansu Kwatsam ba zato ba tsammani sai sukaga kasa dare ta haifar da wani wawakeken rami mai zurfin gaske Wanda basa iya ganin karshensa saboda zurfinsa kasan ramin kuwa wutace takeci ganga ganga har tururinta yana iya laso inda suke daga cikin ramin saboda matukar zafinta koda ganin wannan al'amari sai dukkaninsu suka shiga cikin taitayinsu domin suga me zai faru a wannan guri Shi kuwa sarki fadarul munnar saiya dakawa aljani zarikul laham tsawa Yace kai kuma tsayuwar me kakeyi anan kaja mu muyi Gaba daga nan inda muke mubar wannan guri ko bakaga irin hatsarin da yake gurin bane Dajin wannan batu sai kwallar takaici ta zubo daga cikin idanunsa Yace ya shugabana kayi hakuri anan gurin ba zan iyayin komai ba domin yanzu haka ji nake kamar an daure mini jikina da manyan sakokin bakin karfe ba zan iya komai ba face yadda shi wanda yayi wannan sihirin ya sarrafa ni Dajin wannan batu sai ran sarki fadarul munnar ya baci Take shima ya fara karanto nasa dalasiman tsafin cikin wani irin birkitaccen yare irin nasu na matsafa faruwar hakan keda wuya sai jikinsa ya fara karkarwa kamar

Chapter 10 of 13