Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels **************HATSABIBAN SADAUKAI ***************CIGABAN ZUBAR DA JINI ***************1 PART A LBR ***************HABIBULLAH KBR Tace lallai na yarda cewa ke yarinya ce baki san menene mulki ba Inaso ki sani babu abinda mutum baya iya yi indai yana da sarauta a hannunsa Bayan haka hakika kin bani kunya tunda har kika nuna cewa ni bazan iya biya miki bukatunki ba ke kinsan wacece ni da kuma irin karfin ikon da nake dashi Kodajin haka sai marfuza ta mike tsaye yadda suna iya jin numfashin juna Tace kwarai kuwa abindana fada daidai ne kuma wannan hukunci da kika yanke idan har bakiyi gaggawar barinsa ba to zaki tafka babban kuskure wanda nan gaba sai kinyi nadamar aikata shi Domin har yanzu baki san wadannan mutane biyu ba wato sarki aryan da gimbiya walisa Ina tabbatar miki cewa duk abinda kike takama dashi to suma suna dasu Tana gama fadin haka saita wuce tabar sarauniya suzaila a tsaye tana kallonta WANNAN SHINE ABINDAYA FARU A BIRNIN DURGAN ***** ****** ******* ****** Al'amarin yarima walisu kuwa lokacin daya kama hanya ya tafi neman gawar sadauki hassanul basari Saidaya kewaye duniya acikin abinda bai wuce mako guda ba Amma ko kadan bai sami koda labarin inda gawarsa take ba Kwatsam wata rana yana tafiya kawai sai yaga zoben hannunsa Yayi jajur sabanin yadda ainihin launinsa yake Koda ganin wannan al'amari sai ya bushe da dariya yace Tunda har ban sami ganin hassanul basari ba ai hakan ba wani abu bane Domin komai kankantar makiyi ba'a raina shi Ba komai ya gani ba face hoton gimbiya walisa tun daga lokacin data baro birnin shawana Har zuwa sanda ta kwanta barci bata sani ba dokinta ya dauketa ya kaita can birnin durgan Koda gama ganin wannan al'amari sai ya bushe da dariya yace Amma wannan yarinyar ta yaudari kanta yanzu da wannan dan guntun karfin sihirin nata zatace zata iya hanani abinda naga dama Tabbas kin tabka babban kuskure arayuwar ki Amma kuma babu abinda nakeso a rayuwata kamar makiyi don haka bazan bari sarauniya suzaila ta sami nasara akanki ba dolene yau na cika alkawarin dana daukarwa kaina na fara fita farautar rayuka tunda har walisa ta sami lafiya Kuma dolene na farkar da ita daga wannan barcin da take inaso da idanunta ta dinga ganin jini yana fallatsi asama Yana gama fadin haka sai take ya runtse idanunsa ya fara karanta wadansu dalasiman tsafi masu karfin gaske Faruwar hakan keda wuya sai take wani farin haske ya fita daga cikin idanunsa ya tashi sama sannan ya tarwatse acikin iska kamar bai taba wanzuwa ba Cikin dakiku kadan wannan hasken ya isa birnin durgan kai tsaye ya wuce zuwa cikin gidan kurkuku Har cikin dakin da aka tsare gimbiya walisa Koda zuwan hasken sai take ya shiga cikin kirjinta ya kewaya duk cikin jikinsa Firgigit gimbiya walisa ta farka daga barcin da take a firgice Kawai sai ganinta tayi acikin kurkuku daure cikin murtuka murtukan sarkoki Kuma bata san sanda tazo wannan kurkukun ba ai kuwa nantake ta takarkare ta kwarara uban ihu Sannan ta fara kokarin kwance sarkokin dake jikinta Cikin mamaki sai taji kamar an zare mata dukkan jijiyoyin jikinta taji hatta hannunta ba zata iya dagashi ba Koda ganin haka sai ta fara kokarin amfani da karfin sihirinta domin ta tsinka sarkokin dashi amma nan ma sai taji kamar an daure harshenta domin daga shi ma ta kasa bare ta furta kalaman tsafi guda daya Da ganin wannan al'amari sai nantake wata kwallar takaici ta zubo mata Kuma ta fara dana sanin barcin daya saceta akan dokinta Domin ta tabbata shine silar zuwanta wannan kurkuku Babban abinda yafi damunta shine rashin sanin inda take da kuma wanda ya kawota wannan wuri Tana cikin wannnan hali ne kawai sai taga wani irin farin haske ya ratso cikin ginin dakin da take ciki ya shigo cikinsa Take fuskar dan uwanta yarima walisu ta bayyana acikin hasken Yana kyakyata dariyar mugunta kuma daga hatta sautin dariyar tasa tana ji ba iya hotonsa take gani ba Amma duk ragowar hadiman da suke cikin kurkukun da sauran fursunoni basa sanin abinda yake faruwa Daga can sai yarima walisu ya murtuke fuskarsa kamar wanda aka turo masa da sakon mutuwa Take ya dakawa walisa tsawa yace Yanzu ke banda rashin kunya irin taki da wannan dan guntun sihirin naki kike tunanin zaki iya tunkarata? Ke wacece kuma wanne mataki kika taka a tarihin rayuwar ki ? Ni kuwa nine hatsabibin kuma tantirin boka wanda ba'a taba samun kamarsa ba Fiye da shekaru dubu biyu baya nine wanda ya gagari manyan sadaukai da manyan bokaye Sai da takai har bauta mini suke domin ni buwayar sadaukai ne Nine wanda ganinsa yafi ganin mutuwa muraran agaba tashin hankali To ke kuma tayaya kike tsammanin zaki iya samun galaba akaina Bayan yanzu haka kin fada tarkon wata kankanuwar sarauniya…… . Kafin ya gama fadin haka tuni tayi sauri ta tari bakinsa tace Karya kakeyi, kamar yadda kake fada cewa kaga zamani mai yawa To hakan bashi bane zai nuna maka cewa kai dauwamamme bane Kuskuren da kake tafkawa a rayuwarka shine na cewa babu hatsabibin sadauki kamarka Hakanne ma yasa a baya hassanul basari ya sami galaba akanka Bayan haka ina shawartarka daka gaggauta fita daga cikin jikin dan uwana…… . Kafin ta gama fadar haka tuni hoton komai ya bace Duk wannan tattaunawa da suke yi yana tsaye a kan iska suke yinsa Domin hoton fuskarsa kawai ya tura mata aikuwa koda yaji irin maganganun data fada masa sai Take ya canja hanyar tafiyarsa ya nufi birnin durgan Kasancewar shi ba karamin tantirin matsafi bane cikin dakiku kadan ya bayyana a birnin Yadda abin ya kasance shine A cikin tsakiyar yinin rana yayin da mutane suke tafiyar da harkokin kasuwancinsu Akowacce rumfa kuwa zaka tarar da dakarun sarauniya suzaila a tsaye agabanta Suna kallon duk irin cinikin da mai rumfar yake domin da zarar ya tashi daga kasuwar zai raba ribar tasa ne gida hudu ya dauki kaso guda ragowar kashi ukun kuwa ya baiwa dakarun sukaiwa uwar gijiyarsu Idan kuwa har ya kuskura yayi gardama take zasu kamashi su tusa keyarsa wajen sarauniya anisa Ita kuma da zarar an kaika gabanta take anan zata sa ayanke maka hukuncin kisa domin ko kadan bata da tausayi Wannan dalilin ne yasa gaba daya suke matukar shakkarta kuma suke mata biyayyar dole domin sunsan cewa jayayya da ita daidai yake da sayen mutuwa da kudinka Kuma ko kadan wadannan dakaru basa karbar cin hanci ko kuma tauye mata kudi Saboda sun san sharrinta da kuma son dukiyarta Suna cikin wannnan hali ba zato ba tsammani sai take Suka dinga ganin kasar birnin tana darewa biyu Gidaje suna ruftawa cikinta Nanfa gari ya hautsine da guje gujen mutane da kuma iface ifacensu Wata irin walkiya da tsawa suka cika birnin gaba dayansa Ana cikin haka kawai sai gani sukayi wasu irin kananun kwari masu dan karen kyau suna fitowa daga cikin karkashin kasa Koda mutane sukayi arba da wadannan kwari sai duk suka manta da tashin hankalin da suke ciki Suka tsaya suna kallon kwarin Koda wadannan kwarin suka gama bayyana sai kasa ta hade komai ya koma yadda yake da kamar babu wani abu daya taba faruwa Yayinda mutane suka ga wadannan kananun kwari sai take sukaji sun kamu da tsananin sha'awarsu Nanfa suka fara rububin kama kwarin domin su kai gida su ajiyesu saboda su kawata gidajensu dasu Babu abinda zai baka tausayi face kaga mutum ya wahala kafin ya kama Amma da zarar yazo hannunsa sai kaga dakaru sunje sun sa masa duka har sai sun kwace abinda yake hannunsa Kafin adauki lokaci mai tsawo tuni mutanen sun kama kwarin da yawa a cikin hannayensu Suna rububin tafiya su ajiyesu ai kuwa ana cikin wannnan hali ne kawai Sai gani sukayi wadannan kananun kwari sun fara huda jikkunansu suna shiga ciki Suna cinye naman jikinsu domin yawo suka dingayi acikin jikinsu kamar yadda jini yake yawo Wohoho nan fa hankalin mutane ya kara dugunzuma suna ihun neman taimako amma babu damar hakan Suna cikin wannan tashin hankaline kwatsam sai sukaga wata irin tsawa da walkiya ta taso daga sama Acikin walkiyar ne kawai suka hangi wani mutum yana saukowa Hannunsa ruke da wata iriyar sandar tsafi kallo daya zakayi masa kasan cewa ya cika hatsabibin gaske Ba kowa bane wannan mutumin ba face yarima walisu ne da kansa Ahankali har ya sauka atsakiyar birnin durgan alokacin da mutane suketa faman ihu da neman taimako sakamakon cin naman jikinsu da wandannan kwarin suke Wani abin tausayin ma shine babu wanda yake da ikon taimakawa wani acikinsu domin kowa ta kansa yakeyi saidai kaga mutum ya fadi kasa yayita shure shure har ya mutu Ai kuwa koda bayyanar yarima walisu sai take mutane suka fara tahowa gurin da yake domin ya taimaka musu Abinda basu sani ba shine duk wannan abu da yake faruwa shine ya haddasa musu shi Koda suka kusa zuwa. Dai dai inda yake sai nantake wani irin bakin duhu ya sauko ya mamaye birnin yadda hatta tafin hannunka ba zaka iya gani ba wannan sandar ta hannunsa kuwa ta rikide ta zama wata iriyar sarka mai kaifin gaske kamar reza Kawai sai ya fara cizge kawunan mutane da ita Nanfa birnin gaba daya ya cika da ihun mutane da iface ifacensu Babban abin tashin hankali ma a sannan shine mutane basa sanin lokacin da suke cusa kansu cikin hallaka Duk sa'adda yarima walisu yayi cilli da sarkar hannunsa sai dai kaga tana fizge kawunan mutane kamar ana sassabe agona Jini kuwa ya dinga kwarara ako ina na cikin birnin domin hatta kwatocin cikin kasar sai da suka rine saboda yawan jinin da yake gudana Koda aka dauki lokaci ana cikin wannan yanayi sai gidajen birnin gaba daya suka fara rusowa suna fadowa suna danne mutane Wasu mutanen ma su suke kai kansu inda zasu hallaka ba tare da sun sani Wannan bala'in ba a guri daya ya tsaya ba harda gaba daya sassan birnin Domin a wannan lokaci sarauniya suzaila na zaune acikin turakarta Ta ajiye a binci agabanta tana ci kawai sai taji kasa ta fara girgiza burbushin bulo yana zubowa Koda ganin wannan al'amari sai nantake ta zaro madubin tsafinta Ta shafe shi domin taga abinda yake faruwa Kawai sai gani tayi madubin tsafin nata yaki yayi aiki koda ta matsa abincike sai nantake yayi bindiga ya tarwatse Da ganin wannan al'amari sai ta kwarara ihu wanda ya kara firgita sauran mutanen da suke cikin gidan sarautar Cikin sauri ta shuri makamanta na yaki da kuma gurayenta ta falfalo da gudun gaske ta fito daga cikin gidan sarautar Tana gama fitowa daga cikin gidan sarautar ne shima gaba dayansa ya rufto kasa ya ruguje Ai kuwa da fitowarta sai ta tarar birnin gaba daya ya cika da gawarwakin mutane ko ina ka duba babu abinda zaka gani face jini yana ta kwarara kamar ruwan famfo Ai kuwa cikin azababben gudu ta nufi can inda yake jiyo sautin ihu yana tashi Wani irin gudu takeyi idan ka ganta sai ka zata akan iska take tafiya Tafiya kadan tayi kawai ta iso cikin tsakiyar kasuwar garin kuma ta hango yarima walisu yana ta yiwa mutanen ta kisan wulakanci Koda ganin wannan al'amari sai take ta daka tsalle ta tashi sama Sannan ta runtse idanunta ta fara karanto wadansu irin dalasiman tsafi na musamman masu matukar wahalar karantawa Ai kuwa faruwar hakan keda wuya sai wasu irin zabga zabgan kibiyoyin tsafi suka fara fitowa daga cikin karkashin kasa Wasu kuma daga cikin sararin samaniya kamar ana ruwansu Dukkan wadannan kibiyoyi sai suka taho kan yarima walisu da gudun gaske domin su shige jikinsa Cikin matukar zafin nama shima ya karanta wadansu dalasiman tsafi irin nasa Faruwar hakan keda wuya saiga wasu irin murtuka murtukan garkuwowi sun bayyana sun kewayeshi Ai kuwa koda kibiyoyin suka sauka ajikin garkuwoyin sai take dukkansu suna narke tamkar ruwa Adaidai lokacin ne sarauniya suzaila ta karaso daidai inda walisu yake Ta daga takobinta sama cikin azababben karfi ta kai masa sara da nufin ta raba kansa gida biyu Koda takobin ta sauka ajikinsa sai take ta kama da wuta kamar garwashin wuta Saida zafin wutar ma ya kona tafin hannunta don haka bisa dole ta saki takobin tata ta fadi kasa Kafin ta kara wani yunkuri tuni yarima walisu ya nunata da dan yatsansa Take wata irin iska mai karfi ta fito daga cikin yatsun hannunsa ta shureta tayi sama da ita kamar takarda ta dinga wujijjigata Koda ganin halin data shiga sai kawai yayi mata wani murmushi mai nuna tsantsar mugunta Sannan ya juya mata baya ya cigaba da zaluncin da yakeyi tana ji tana gani amma bata ikon yin komai Nanfa ya canja salon irin kisan da yake musu ba irin na da ba Abin kuwa daya dingayi shine diban mutane,maza da mata yara da manya harda dabbobin garin ya dingayi da wata irin iskar tsafi mai karfi yana daga su sama da ita suna ta faman ihun neman taimako amma da zarar sunyi kololuwa a sama sai kaga iskar ta tsinkasu tayi musu filla filla Saidai kawai kaga jini da sassan jiki suna zubowa kasa daga sama kamar ana ruwan sama Dukda tsananin rashin tausayi irin na sarauniya suzaila a wannan rana saida taji tausayin mutanen ta yayi matukar kamata Kuma ta fara nadamar zaluncin data dinga aikatawa a baya domin yanzu ta tabbatar da cewa mutuwa zatayi bata isa ta kubuta daga sharrin wannan azzalumi ba Nanfa ta fara tunani acikin zuciyar ta kan labarin wani hatsabibin boka da iyayenta suke bata mai suna sahibul ukub Da irin tsananin zaluncin sa da kuma labarin cewa masana sun tabbatar da cewa zai sake bayyana bayan shekaru dubu biyu Kafin ta gama yin wannan tunanin da takeyi har ya gama kashe mutanen birnin gaba daya ba kajin sautin komai face iskar da take dauke da ita Nan take ya fizgo sarauniya suzaila daga sama ya doka ta da kasa sai da kura ta tashi sama sakamakon karfin dukan da yayi mata shatar alamun jikinta suka bayyana akan kasa Kawai sai ya kara dagota sama fuskarsa a murtuke kamar wanda bai taba fara'a ba a rayuwarsa Yace ke wacece a duniyar tsafi da har zaki hada karfin sihirinki da nawa? Kuma wanne irin mataki kika taka a fannin sihirin tsafi ?? Ki sani na hadu da manyan matsafa da kuma sadaukai wadanda suka shafeki aduk fannin da kike takama dashi fiye da shekaru dubu biyu baya bayan haka inaso ki sanni hatta kakanninki suna daga cikin wadanda suke bauta mini a wannan zamanin saboda karfin iko na Amma saboda rashin kunya kece zakizo da wan dan guntun tsafinki kice zaki tareni Saboda haka dolene kema ki dandani zafin mutuwa akan harshenki Koda gama fadin haka sai take ya hura mata wata iriyar iska acikin hancinta Faruwar hakan keda wuya sai take jikinta ya fara kumbura saidata kumbura sosai Sannan kuma a hankali naman jikinta ya dinga zagwanyewa akasa kamar kitse Adaidai lokacin da walisu yake yiwa sarauniya suzaila wannan bayani ashe tuni sarki aryan ya iso wajen Amma koda yaga abinda yake faruwa a wannan birni sai nantake ya sami guri a bayan wani rusashshen gini ya buya Ana cikin hankane kawai ya jiyo sautin motsi abayansa cikin sauri ya waiwaya Kawai sai yayi arba da jaruma marfuza abayanta ta goyo gimbiya walisa cikin wani irin yanayi mai ban tsoro Cikin mamaki ya dubi marfuza cikin alamun zargi yace me kika aikata ga gimbiya walisa ki gaggauta sanar dani yanzu take Nantake marfuza ta kwashe labarin komai ta sanar dashi Koda jin haka sai hankalinsa yayi matukar tashi ya dubi marfuza yace Lallai akwai bukatar muyi saurin yi mata magani amma ba'a wannan gurin ba Don haka dolene muyi kundumbala yanzu mu bar filin nan Koda gama fadin haka sai ya mikowa jaruma marfuza hannu a karon farko ta ruke Take taji wani irin farinciki ya kamata domin bata taba tsammanin zuwan wannan ranar ba har saida fara'a ta bayyana akan fuskarta da ganin wannan hali data shiga sai yace kinga yanzu ba lokacin wasa bane ki cire duk wani abu da yake ranki domin zamuyi gudun mutuwa ne Yana gama fadin haka sai suka runtse idanuwansu suna masu karanta wadansu dalasiman tsafi Sannan suka fito daga inda suke boye suka falfala da azababben gudu wanda a iya fasaltashi da gudun tauraruwa mai wutsiya acikin wannan rufe idon suke zabga wannan gudun Ta gaban yarima walisu suka gifta a lokacin da ya tsaya yana kallon yadda sarauniya suzaila take zagwanyewa Duk da irin karfin gudun da sukeyi sai da yarima walisu ya gansu Don haka sai shima ya rabu da sarauniya suzaila agurin ya bisu shima cikin azababben gudu domin ya riskesu ya kamo su NIMA KAINA NASO ACE NA BISU DOMIN NA SAMO LABARIN YADDA ZATA KASANCE SAI DAI MATSALAR MASOYIYARA TA HANANI SA IDO DA SHI SABGAR MANYAN HATSABIBAI DON KAR TA KIFE DANI SAI NAJI DAGA GAREKU TO KAKA KARA KAKA YAYA KUKE GANIN ZATA KASANCE ? SHIN YARIMA WALISU YANA RISKARSU YA KAMA SU? HAR SAI YAU SHENE ZAI GANE CEWA GIMBIYA WALISA 'YAR UWAR SACE? SHIN SARAUNIYA SUZAILA TANA MUTUWA KO KUWA BATA MUTUWA ? SHIN SARKI ARYAN ZAI KARBI SOYAYYAR JARUMA MARFUZA? DON JIN AMSOSHIN WADANNAN TAMBAYOYI SAI MUN HADU A CIGABAN WANNAN LABARI MAI SUNA HATSABIBAN SADAUKAI CI GABAN ZUBAR DA JINI DAGA NAKU HABIBULLAH KBR LIKE AND COMMENTS*****************HATSABIBAN SADAUKAI ***************1 PART B CIGABAN ZUBAR DA JINI LBR ***********----HABIBULLAH KBR Lokacin da aka kasa azababben tseren gudu tsakanin su jaruma marfuza wacce ke goye da gimbiya walisa aga don bayanta da yarima walisu kuwa Sai suka dinga gifatawa ta cikin manya manyan dajujjuka masu matukar hadarin gaske Suna gudun ne kusan kamar gudun iska domin idan da kana tsaye sukazo giftawa ta gurin da kake to baka isa ka iya ganinsu ba Duk da cewa idanunsu a rufe suke bai hanasu ketare duk abinda sukaci karo dashi agabansu ba Hatta bishiyoyi, gini da kuma duwatsu da zarar sunzo inda suke sai kaga sun ratsa ta cikinsu ba tareda sun tsayar dasu ba Haka ruwama komai girmansa da kuma zurfinsa saidai kaga sun wuce ta kansa Shi kuwa yarima walisu sam baya taka kasa domin akan iska yake nasa gudun Amma wani abu daya bashi mamaki a wannan lokaci shine tsananin karfin gudun da su sarki aryan suka samu Domin har yanzu ya kasa riskarsu,duk da cewa kuwa suna goye da gimbiya walisa agadon bayansu Tafiyar mako guda kuwa sai kaga sun shafeta cikin dakika guda Koda yarima walisu yaga wankin hula yana nema yakaishi dare Sai kawai yayi nuni da hannunsa zuwa garesu take wasu kananun allurai sukayi fitar burgu daga cikin yatsun hannunsa suka yi kansu sarki aryan Kafin alluran su sauka ajikinsu tuni suma sun karanta wasu dalasiman tafin daban suka tofa akan kasa Aikuwa take kasar gurin ta dare suka rufta cikinta suka bace bat Koda ganin abindaya faru sai take ya shafi zoben hannunsa da nufin ya bincika inda suka shiga Bisa mamaki akaron farko na rayuwarsa sai yaga hoton komai yaki bayyana ajikin zoben saidai ma maimakon yayi haske sai baki yayi Koda ganin wannan al'amari sai ya takarkare cikin mugun bakin ciki da bacin rai ya daga kansa sama ya kwarara mahaukacin ihu Wanda sautinsa ya amsa kuwwa a gaba daya dajin hardama wadanda ke makobtaka dashi Bishiyoyi da duwatsu suka dinga yin bindiga suna fashewa da tarwatsewa Dabbobin daji kuwa suka dinga faduwa babu gaira babu dalili suna mutuwa Ba komai ya janyo hakanba face bacin ran yarima walisu saidaya shafe dakiku yana wannan karaji sannan yayi shiru ya tsuke bakinsa ga barin ihun Alokacin da idanunsa suka kada sukayi jajur kamar angasa dan buda a wuta Wani irin turiri ya dinga fita daga kofofin gashin jikinsa Yace lallai wadannan yara sun shammace ni yanzu ne na fahimci cewa tun sanda mahaifina yake raye akwai wani abin daya boye mini inbadon haka ba babu yadda za'ayi wadannan mutane su kubuta daga hannuna Kuma nayi kuskure tun farko da ban kashe gimbiya walisa ba Yanzu ya zama dole na tashi na koma can fadata na fara bincike akansu har na gano inda suke na bisu can na yi musu kisan wulakanci irin wanda ba'a taba yiwa wani irinsa ba Yana gama fadin haka take yayi girgiza nantake kuwa ya bace bat daga gurin gaba daya ***** ****** ****** Lokacin da su sarki aryan kasa ta tsage suka shige cikinta suka bat kuwa Basu bayyana ba sai acikin wani kogon dutse mai tsananin duhun gaske domin hatta dan yatsanka ba zaka iya gani ba aciki Koda bayyanar su aciki sai duk duhun cikin kogon ya bace haske ya mamaye kogon Shidai wannan kogo da suka bayyana acikinsa kogone mai matukar tarihin shekaru Domin masana da masu bincike sun tabbatar da cewa yafi shekaru dubu uku A wannan zamanin kogon shine majalisar tattaunawar duk matsafan duniya domin samin mafita akan abindaya shige musu duhu Duk wadanda suka zauna acikin kogon babu wanda ya isa daga waje yaji sirrin da suke tattaunawa akansa ko kuma ya shigo cikinsa saidai idan sun yarje masa hakan Daga bayane boka shurul aiman wato nahaifin boka sahibul ukub ya gaje wannan kogon tsafin yake ayyukan sa na sirri acikinsa Bayan yayi tunanin cewa nan gaba sahibul

Chapter 1 of 13