Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
Yayi smilling back tare da bude booth din badiyya da uwarta sukayi kiciniyar saka kaya a booth gogan ko fitowa beyi ba. Suka shiga motar, ko kallon arziqi be ma uwar Badiyya ba yace, Ina wuni mama,Ita ko a ranta cewa take Ashe diyyata bata yi karya ba, Zaidun nata hadadde ne, ta amsa cikin wani murya sai da diyya ta juyo ta kalleta. Zaid ya ja mota sai gidansa dake Maitama. Ta zage ta dafa Tuwon semo miyan agushi da yaji ganda, ta kai kan dinning ta ajiye, tun dazu take zaman jiranshi, har bacci ya dauketa kan 3sitter, Sun iso gidan suka dinga kwankwasawa shiru, Zaid ya kwala ma maigadi kira yazo jikinsa na rawa, yace kai wata ta fita daga gidan nan? Yace auu akwai mutum ciki? Zaid yace ba tambayar da na maka ba kenan, yace Yallabai indai ka bar mutum a nan to ta na ciki, don tun da safe ina nan zaune ba inda naje. Zaid yayi tsaki ya ciro keys ya kalli su badiyya yace muje Badiyya da ta gama cika tayi fam kamar ta pashe ta ja akwatinta uwar na biye da ita a baya, suka zagaya baya, zaid ya sa mukuli ya bude wani qofa ashe ta kichin ne, tun daga kicin din suke jin wani daddadan k'amshi, har suka iso parlorn, kwance ya ganta tana bacci, kallo daya ya mata ya dauje kai, idonsa ya sauka kan dinning yaga kulolin abinci, ya tabe bakih, Diyyan ta kade ganin tsaruwar gidan, ya kalli uwar diyya yace feel at home mama, ta sakar mai murmushi ok son, ya kalli diyya yace bari na shiga na yi wanka, tace dear, ai da ka barih kacih abinci yar matarka, ta qarashe tana zolayarsa, ya dan bata rai yace nahhh, you go ahead, ya ja briefcase dinsa yayi dakihnsa, suko nan suka dire kayansu suka nufa kan table, Diyya na bude kular miya taji wani qamshi, nan da nan miyonta ya tsinke, sai da ko ta lasa, ta zuba a plate, ta sam mamanta, nan suka hau ci, daman mulmula biyar ne, diyya da Maman ta suka kwashi tuwon nan tassss. Cikin bacci taji ana buruntu tayi sauri ta tashi, idonta ya sauka kan Diyya da mamanta, Gabanta ya yanke ya fadih. Diyya ta juyo ta ganta tsaye, Auu Rumaisah kin tashi? Zo ki kwashe kayan nan ki kai kicin, sannan kizo ki shigar min da kayana dakihna, ki nuna ma mama dakinta, Hantar cikin Maysah ya bada Kulululu. Meke shirin faruwa da ni? Ta tambaya kanta. _Bibilicious Biebee_ 2⃣4⃣ 🏡GIDAN GANDU🏠by 💕Biebee Isa💕Gidan Gandu🏠by 💕Biebee Isa💕 by 💕Biebee Isa💕Biebee Isa💕Biebee Isa💕Ji ta yi abun kamar a mafarki nan ta tsaya kamar robot, tsawan da badiyya ta mata ne yasa ta dawo hayyacinta, ko ba kya ji ne? Cewa nayi zo ki kwashe kayan table din nan, Sannan ki kwashi kayan chan ki kai dakih, Maysah ta hadiye wani mugun miyau, jiki ba qwari ta tako ta harhada kwanukan tayi kichin, Tuwon da ta tuqa domin ta da mijinta, ga wasu nan sun cinye tas, ita ko ko a bakinta, gashi wani yunwa takeji, daman niyyarta sai ya dawo zasu ci tare gashi an cinye, tuni hawaye suka bi kuncinta, ta dawo parlorn ta ja Akwatin su tayi hanyar wani dakih, kasancewar Gidan 3bedrooms ne, Badiyya ta cire bakinta ta kwala mata kira, jikina barih ta zo da sauri in kai wannan akwatin dayan dakin, wanchan akwatin ki kaishi wanchan dakin ta nuna dakin kusa da Zaid, waiyo Allahnta, dakinta take nufi zata kai kayan Badiyya, to ita ina zata kwana? Muryar badiyua ya katseta yace ke ki min sauri, hakan ko Maysah tayi, Maman badiyya tayi daria woo diyata baki da wasa, Badiyya tayi daria tace ai mama Yar aiki muka samu, tunda tayi qoqarin shiga gonata ga hukuncinta, ai naso auren nasu ya dore ya dade da ta mun bauta har sai naga wannan kyaun ya disashe, amma duk da haka zan moreta na sati 1, tunda lokacin aurensu zaiyi expire. Suka dau shewa tare da kashewa. Nan suka zauna suna kallo ba Maghriba balle Ishai, ita ko bayan sallah ta shiga kichin ta gyara, sai da ta qara tuqa tuwon don akwai sauran miya. Wuraren qarfe 11 maman ta ma diyarta sallama ta shiga daki don huta gajiya, Badiyyan ma ta shige dakih da watsa ruwa, tun dazu maysah ke kichin zaune, har ta fara gyangyadi, bacci kawia take sonyi, jin ta daina jin hayaniyarsu yasa ta leqowa parlor, ba sa nan, zuwa tayi ta kashe tv din, ta dauko throwing pillow ta ajiye a kasa ta kwanta ta re da chusa hannayenta tsakankani cinyoyinta alamun sanyi. Nan bacci yayi awon gaba da ita. Ko da ya fito parlor ya kunne wuta ganin ta yayi kwance, kallo daya ya mata ya dauke kai, dayan dakin ya shiga, kwance ya ga Maman Badiyya daga ita sai Underwear tana waya, bata yi wani yunqurin suturtace jikinta ba shima be damu ba, yace mom ina Badiyya, tace tana dayan dakin, ya rufe yana mamakin dayan dakin kuma, dakin ya nufa ganinta yayi xaune gaban dressing mirror tana shafa, ta mirrir ta hangishi, myzayd ya dai, ya dan bata fuska, yace kinsan dakin yarinyar nan ce nan ko? Tace toh me kake nufi? Yace gata chan kwance parlor, tace y do u care? Yace i dont, but its not fair a zo gidan ta a fidda ta wajeh, badiyya ta qwale ido, kar dai Zaid taussyin yarinyar nan yake, in haka ya faru ita kam ta kade. Ta dai daure tace ya kake so ayi? Yace ki koma dayan dakin ita kuma ta dawo dakinta. Tace ni gaskia ba zan iya kwana da mama ba, kwana take ta na waya, ya danyi tsaki, tace sai dai ko dakin ka, ya yi hanyar fita yace ko ina zaki kwana ki kwana, just leave dis room,. Parlorn ya koma, da qarfi ya dinga cewa Keh, keh tashi ki koma dakih, cikin bacci taji kaman muryan shi, da sauri ta miqe tacw Yazayd ina wuni, ka dawo lpy? Yayi hanyar dakihnsa yace ki shiga dakinki, nan ta daskare ganin badiyya ta fito da wata irin shegiar nyt gown tayi dakin mijinta. Hawaye suka shiga reto wlh da ma kwanciyarta tayi a parlor ta bar mata dakin, ds ta bar wata ta shiga dakin mijinta. Tana gani badiyya ta shige dakin Zaid tare da kullewa. Maysah ta zube kasa tana kuka. Da ta ga hakan ba zai fisshe ta ba ta shige dakih ta dauro Alwala ta hau Sallah. Kwanciya yayi kan gadonsa, ita ma badiyya ta haye, nan suka fara iskancinsu, Zaid na ganin badiyya na qoqarin wuce gona da irih yayi saurin tunkudeta, idonta ya kada yayi jaaa, cikin dakusheshen muryarta tace please Zaid, just once, pls Zaid, ya miqe tsaye yace kinga abunda ke hadani da ke ko?nace miki bana so, yayi shigewarsa toilet, Badiyya ta fita hayyacinta ta shiga murqususu a kan gado, har ya fito kallo daya ya mata ya kawar da kai, da qyr tace Zaid pls help me Help ne i need u, ya ce ok, briefcase dinshi ya dauko, ya ciro wani magani ya dago fuskanta ya titila mata ko minti 5 ba tayi ba ta fara bacci. Ba ta farka ba sai 11safe. Ranta a bace ta waiga ta waiga ba Zaid, ta ha ba brief case dinshi. Ta jayo wayanta ta kwada mai kira, A lokacin kuwa ya na zaune a office ya na duba wani patient, kiranra ya shigo, yaqi dauka sai da ta mai 3missed calls, a na hudun ne ya kalli patient din yace excuse me, ya dauki wayan Hello Diyyana, cikin fada ta fara fadin Zaid y are u doing dis to me? Isit bcoz i lov u? Cikin mamaki yace me na miki diyyata? U knw i wont hurt u knowingly, tace i asked u to help me not to doze me off, ya danyi murmushi yace dats d only help i cud give u, I told u na tsani Zani, ki yi haquri har muyi aure mana, yanxu dai ina diba patient, sai na dawo ba tare da ta ce komai ba ya kaahe wayarsa. Baqinciki ya tokareta Wato ya tafi Aiki ya barta kwance a nan kamar kayan wanki,Bata taba ganin Dan iska irin zaid ba, wato baka zina amma kana shayeshaye? To meye bambancin dambe da fada? Zaid ka bini a sannu tayi kwafa ta shige toilet. Tun da tayi asuba ba ta koma ba, ta na kichin tana hada musu breakfast don ta san Zaid zaije office, wurin 7 ta shiga wanka, ashe har zaid yayi tafian shi, ba ta sani ba, tana ta zama jiransa ba shi ba alamarsa, duk yan gidan dai bacci sukeyi. Qarfe 12saura badiyya da uwarta suka fito suka hau kan table suka kwashi abinci, Maysah ta zo tana gaidasu ba wanda ya amsa, da ta gaji ta miqe zata tafi Maman badiyya tace ke Rumaisa jeki soya mun doya zallah bana son me qwai din nan, haka maysah taje ta sake wani soyen. Haka dai Maysah ta yini ta na bautar Diyya da Mamarta.. 5days later. Haka rayuwan Bayin Allahn nan ya cigaba da gudana duk gidajen nan ba Zaman Arziki, Ba me kula kowa, Amira kullum sai ta ma Samir magana a takiace ya ke bata amsa, Zayyad kullum sai ya ma Hanifa magana ko tana da buqatar wani abu ko kallo be isheta ba, Jawad ko kula fadila ba yayi, trust fadila ita ma harkan gabanta takeyi, ko abinci daidai cikinta takeyi, Bilkisu da Suraj kamar mage da bera, kullum sai ta mai rashin kunya, Islahulkhair bata qara saka Mu'ammar a idonta ba har ta saba da zaman kadaici, Maysah kuma na yin bautar karuwa da uwarta, Zaid ko lasan abincin ta be ta bayi ba, ita kuma bata taba gajiya da aikinsu ba, Kullum sai tsoho ya kirata bata taba nuna mai komai ba nan zai ta mata nasiha yana samata Albarka.... Bibilicious Biebee Yau Juma'ah misalin qarfe 11 na safe Ya shigo gidan tana bacci a parlor taji ana qwanqwasawa abun har ya dan bata tsoro, ta miqe ta nufa qofa ta bude, Mu'ammar ne tsaye, tayi mamakin ganinsa ba tare da yace mata komai ba ya raba ta gefenta ya shige ciki bayansa ta bi da kallo, ya shige wani dakih. Zamanta tayi a parlo ta kunna TV, Wayarta tayi qara fadila ce ta dauka sis yane? Tace lapya ya gida,? Tace hmn ga gida nan, ina Ya Jawad? Fadila ta tabe bakih, yau wurin 10 ya shigo gida naga ya hada kayansa qila Maiduguri zaije, Islah tace kuma bakwa magana? Fadila tace ni ko iskar da deboshi ba sani ba, Islah zata ce wani abu taga Mu'ammar ya fito da dan jakka a hannu ya na waya, okay kana qofar Gidan? Gani nan fitowa ya bar parlorn ba tare da ya tankata ba. Islah ta fashe da kuka, fadila na tambaynta ta kashe wayar gabaki daya. Bayan Jumaa Suraj ya fito da dan akwatinsa ya kalli bilkisu dake lunch yace Ni na tafi Maiduguri, tayi tsalle tace wa zaka bari a gidan nan? Yace ke mana, tace kambu, ai baka isa ka barni ba, tare zamu tafi ko wallahi ba zaka dawo ka sameni ba. Yace toh ki yi yanda kikeso, don ni kam ba inda zaki bini, ya fita tare da rufe kofar wajeh ya ja motarsa. Ihu bilkisu ta sa ta dinga tsine tsine. Maiduguri Jawad da Mu'ammar sun iso Maid lafiya kasancewar tare suka taho, Jawad ya biya ya dauki Mu'ammar straight Sashen Hajia Babba suka nufa, Ta na ganinsu ta hau murna, ga mutanen Garin Gwamna, sannunku da zuwa, daman kuna tafe, Mu'ammar yace ba dole ki ganmu ba, ai nan Zuwa mukayi don a raba auren nan, don tun da aka kaita ban kwana gidana ba, Hajia babba tayi daria tace shege Ammar, kuzo ku ci abinci sai muje ayi magana. Suka qarasa ciki, suka ci abinci ko wannensu yayi sashensa, Aunt Abida ta rungune Jawad, Son haka kayi baqih? Yace Umma ba dole ba, ina kwana gida daya da maqiyyana ai dole na ke chanza kala, tace Ina danuwanka? Yace wai ba zai samu damar zuwa ba week din nan don shine Dr on call saturday nd sunday, but yace idan an raba auren zai sa yarinyar a jirgi, tace toh shkn, Abunda sai mu jira muji me Hajiar ta shirya. Mu'ammar ya kira Jawad yace kai mu hadu Sashen Tsoho kar labari yaje mai mun iso tun dazu ba muje mun gaida shi ba, yace toh muje.. Ko da suka isa Sashen Tsoho, Suraj na nan zaune suna labari da tsoho Sallama sukayi, Muammar ya daure ya ba Suraj hannu suka gaisa, banda jawad din da ya dauke kansa ya maida hankali gurin gaida tsoho, Tsoho yayi murnar ganinsu, ya dan zolayesu da Angwaye kun sha qamshi, aiko suka sha kunu dukansu, suka miqe zasu fita yace ku zauna mana muyi hira, haka tsoho ya dinga jansu labari, ina matayenku,? Ince dai ba wata matsala koh? Shiru suka mai. Sallamar Hajia Babba ta katse musu hanzari, Anty Abida da Aunty Sadiya na biye da ita a baya, Bakih har kunne tsoho yace Karime kinga Angwaye koh? Ta tabe bakih, tace Alhaji magana nake so yi, ya dan gyara zama yace wace irin magana kenan?Alhaji Auren da a aka ma yaran nan nakeso a warware shi gabaki daya banda na Amira da Samir yanxu, tsoho ya kalleta sosai. Yace saboda me? Ai idan na daura aure, ba warwara ba sakih duk rintsi duk wahala ya qullu kenan sai mutuwa zata raba, Hajia karime ta harzuqa, Kai Alhaji kar ka raina mana wayau mana, Auren da aka daura don a sama maka lapya yaran nan suka amince, ba sa son junansu amma tunda ka warke yanzu dole za a raba, ko wannne a bashi wacce yakeso, Tsoho ya kalle ta sosai, cham ya kwada ma Sarkin Gida kirah, sai ga Mallam Iro ya shigo jiki na rawa, Tsoho da idonsa yayi jaaa yace je ka kira min Kowa. mallam iro ya fita, yaje ya kira duka yan gidan cikin mintuna kadan kowa ya hallara parlorn tsoho, parlorn yayi tsit ana jiran aji abinda tsoho xaice, ya kalli hajia Babba da take murnan haqanta ya cimma ruwa, yace Karime maimaita abun da kika fada, ba kunya ta maimaita, Tsoho ya miqe ya shiga dakih sai chan ya fito Da Alkurani izzu 60, ya riqe ya ce ni Musbahu Zailani, nayi rantsuwa da kuranin nan, duk randa daya daga cikin maauratan nan da aka daura aurensu jummar da ta gabata, ya saki matarsa ko da saki days ne, to Na saki Karime saki 3, kuma na tsine ma mahaifansa, Inallilahi wa ina ilaihir rajiun kowa ke maimaitawa, Banda Hajia babba da ta sake Ihu na shigesu, Alhaji Me yayi zafih haka? Yau na banu, ta fashe da kuka, ita tasan ba zata iya rayuwa ba tsoho ba,(lol)shima tsohon ya san karime na sonsa, ta dinga kururuwa, Hajia Ama da Umma Hajja suka jinjina kai. Ya kalli su Mu'ammar da jawad da suka kidime iya kidima yace Ku gaya ma yan uwanku saqo na, idan har kuna so na tsinewa iyayenku, na kuna saki kakar ku toh ga takarda nan ku rubuta wa matan ku saki. Ya ce ku tashi ku tafi na sallame kowa. Jiki ba qwarih aka fara watsewa, banda karime da tako kusa da Tsoho, don Allah Alhaji kai man rai, tun kuriciyar mu baka saken ba sai ynz? Ka san ina sonka, don Allah kar kai min haka, yace karime ina sonki, ba xan sakeki ba , amma da yaran nan sun saki matansu, to kema a bakin aurenki fah, da sauri tace wlh ba me sakar kowa, ai auren nan mutu ka raba, Allah ya basu zaman lapya ya hada mana kawunannasu, Tsoho yayi murmushi ya san karime ciki da bai hakan kadai ne maganinta. Yace Amin karime ta👻 Tafia sukeyi amma ba me ganin gabansa, Mu'ammar yayi tangartangar zai kife Jawad yayi saurin taro shi, yace haba mana Mu'ammar, calm down mana, Mu'ammar cikin fushi yace Calm down? Ana nufin idan na sake yarinyar nan za a tsine ma uwata? don na san ko ya tsine ma baba ba zai bishi ba, don ba shi ya haifeshi ba, Amma dagaske yake sai ya tsine ma er sa ta cikinsa, uwata? Wallahi na tsane yarinyar nan, ba na sonta bana qaunarta, Kamar yanda nima Bana son Bilkisu kuma bana kaunarta ba, jawad da Mu'ammar sukayi saurin kallon me furucin nan, Suraj ne ya nufosu, ashe yana jinsu, Jawad ya tunzura, yace ance maka ita ta na sonka ne? Ni jawad ni kadai takeso, zaka qarasa rayuwarka da matar da ba ta sonka, nd its going to kill you inside dat she loves me alone, Suraj yayi murmushi ya juya dubansa ga Mu'ammar yace let me make one thing straight, Islahulkhair is my only sister, ina sonta fiye da kaina, Idan na sake naji ka mata wani abu wlh baza mu kwashe da kyau ba, dat reminds me, M married to your sister Bilkisu, Hurt my Sister and i will hurt yours. Don Er uwa ba ta fi Er Uwa ba. And to you Dummy ya kalli Jawad, kai ma kasani fadila ba ta sonka bata kaunarka, ni kadai takeso nikadai ke zuciyarta, kaga we have one thing in common. So i can leave wit this. Nd da kake ikirarin bilkisu ba za ta taba sona ba, yayi dan daria ka manta ni Architect ne? Toh idan ka manta bari na tuna ma I am an Architect, i will do what i do best, I will Redesign, Rebuild and Reclaim her Heart. Yana kaiwa nan yayi tafiarsa ya bar su tsaye kamar Robot. _ Bibilicious Biebee_2⃣6⃣ 🏡GIDAN GANDU🏠by 💕Biebee Isa💕Gidan Gandu🏠by 💕Biebee Isa💕by💕Biebee Isa💕 Biebee Isa💕Biebee Isa💕 Ransu in yayi dubu ya baci, ko wannensu ya wuce dakinsa ransa na mai Zafih, Jawad na shiga dakih ya kira Zaid, ya Zayyane masa komaibda abinda Tsoho yace, Zayd yayi dan jim, chan kuma sai yace shidai ya sani, ni banda matsala, tayi ta zama da igiyar aurena, ba sai na kulataba? Asubar fari Mu'ammar ya baro borno motar haya ya hau, ko Jawad be san ya tafi ba, ba zaria Yayi ba, Abuja ya nufa, sai dai muce Allah ya tsare. Badiyya zaune gaban Bokanta, ta muskuta tace yanzu kai boka ka na nufin na baro Abuja na zo Maiduguri kuma ba biyan bukata? Wlh na matsu da Zaid, kamar nayi hauka, Boka yayi daria yace Diyyan shagali, yanzu ya kike so nayi? Na gaya miki hakan ba zai taba yuwu ba, Zaid ba zai taba kusantarki ba indai har ba aure kukayi ba, Daniska ne amma baya zina, Abu daya zance miki, ki sashi ya aureki, kar ki bar Garin nan ba tare da kin samu karbuwa wurin danginsa ba, tace ta yaya? Yace ki kutsa, ni kuma zan miki aiki, dukda wannan kakan nasa dan iskan kansa amma na ga Aure tsakaninku, tayi murmushi yauwa gatana shisa nake sonka, haka ta cika mai al aljihu, sukayi sallama bata yi ko ina ba sai gidan Mubahu Zailani, ko dar ba ta ji ba ta tambayi sassan Hajia Babba aka nuna mata, ta shiga dakin da Sallam bayan ta gyrara tsayuwar gyalenta, Hajia Babba ta amsa daga cikin daki, Badiyya ta ma kanta masauki kan sani lafiyayyen kujera, Hajia Babba tace tou ina muka samo Yar Gayu? Badiyya tayi murmushi ta risina hajiarmu ina wuni, Waiyo Allah dadi xai kashe hajia babba ta ji yar gayu tace mata hajiarsu, nan badiyya ta gaidata cikin barikanci, ta amsa, sai dai ban shaidaki ba, Allah sarki hajiarmu Badiyya ce K'awar Zaid ce ni amma ni a zahiri ni Aurenshi nake so nayi sai dai naji ba a auren bareh a gidannan Hajia babba ta jinjina kai tace eh haka ne, Badiyya ta zamo ta riqe kafat hajia babba ta na roqonta ta taimaka mata, lokaci daya ta siye zuciyar hajia babba da zantuttuka masu dadi har hajia babba taji za ta tsaya ma Badiyya tunda tace zaid din na sonta, ta shafa kanta tace karki damu Badiyya abun da wuya, amma zan miki kokari har Allah ya sa a dace. Da Sauri diyya ta rungume hajia babba tace kai Amma nagode hajiarmu, Allah ya ja rai, ya barki da tsoho, ai kamar an tsundumata a Aljannah taji dadi, Badiyya ta cikata da kudi, duk da kudi ba matsalar hajia babba bane amma bata da godian Allah. Har badiyya ta miqe hajia babba tace yauwa jikata dani da Hajjo wa yafi kyau da diri? Badiyya a ranta tace wacece kuma Hajjo? Amma a fili tace wai daman cewa akayi kyau ne da ita? Ai wlh hajiarmu kin wuce a hadaki da wata hajjo, Hajia babba taji dadi matuka, baki na rawa don bata san kalan amsar da za a bata ba ta ce Aishalle fah? Badiyya ta tabe bakih ba don ta san waye Aishalle ba tace wannan me kama farar mayu. Shewa hajia babba ta sa ta rungumi diyya tana tafa hannaye, yauwa Yar gari, da wannan kodawar da badiyya kema hajia babba taji zata yi yanda tayi don Zaid ya auri Badiyya haka sukayi sallama cikin jin dadi, Hajia Babba na zuwa dakih ta Kwalama khalil kira, Autan baba mudassir, yazo da gudunsa, ta mika mai wayar tace kira mun Zaidu, khalil yayi daria, wai hajia ba kya ganewa ne? Har hoton Yazayd a ka samiki a contact picture don ki ganeshi amma kullum sai kin kirani, cikin fushi tace zaka kira minshi ko sai na kwashi buraubaka a hannu? Daria yayi yace Maida wuqar hajia ya kira mata Zaid Bacci yakeyi misalin Karfe 2 na rana, hutu kenan na kwana 2, yanda yaji dadin weekend dinnan Diyya ba ta nan taje Maiduguri, Mamanta ma bata gida, kamar a sama yaji wayarsa na ringining tsaki ya sake, duk zatonsa wayar asibiti ce ake kiransa, haushi ya cika shi daya ga personal wayarsa ce, screen din wayar ya hasko mai Grams, guntun tsaki ya saki ya dauka,Hello Grams ina wuni?daga bangarenta kamar tana waya da wanda yake Sama ta bakwai, da karfi tace Hello Zaidu, Yanzu Yar Gayu tazo, haushi ya cikashi, wacece yar gayu? Haba wannan diya me sunan larabawa, fara me kyau, ni wlh na mance sunanta, tace min kuna soyayyah, hajia babba ta fara mai kwatamce don tsakaninta da Allah ta manta sunan diyya, tuna min sunanta mana? Tsaki Zaid yayi ya kashe wayan. Tsaf ya gane Badiyya ce, miqewa yayi ya fita daga dakin. Zaune ya ganta tana kallon Zee World. Tana ganinshi ta tashi tsaye, ko kallonta beyi ba ya yi kichin, doya ya dauko da wuk'a ya fara fira, shigowa kichin din tayi yace Yazayd ga abinci fa a dining yanzu na gama, kamar ba zai tanka ta ba yace bana ci, ki daina abinci da ni kinaji? Bata tanka ba sai cewa tayi kawo na fere ma doyan toh, shiru yayi sai da ta kara maimaita mai, yace kije na hutassheki. Jiki ba kwari ta bar kichin din. Nan zayd ya gama fera doyanshi ya soya, ya soya Kwai har da sauce dama zayd ba daga baya ba gun girki. Tana kallonshi ya xo ya bude fridge ya dauka fresh Milk yayi dakinsa, miyau ta hade me ciwo ta na ba kanta tausayi, dukda jiya dayau ba ta wahala ba, ta wala a cikin gidanta kasancewar Badiyya da uwarta basa nan.. Bauchi Bigbro Samir, ya dago ya kalleta kadaran kadahan, tace mena maka ne? Me sa ka tsaneni haka? Kamar ba kai ba? Idan ka bar gida sai dare ka ke dawowa, kamar baka son bude idanunka ka gannin, Kamar m not ur lilsismeerah, eyi yasamir? Me nayi maka ne? My heart cant dmtake dis anymore, ka fada mun idan da akwai abunda nake ma wanda bakaso wlh a shirye nake na barih, because i love u, i can do anything for u, kallonta kawai yayi ya watsar, zuciyanta ya shiga zafih, cikin masifa tace is dis because of Islahilkhair? Its high time da zakayi letting feelings din Islah flow kayi replacing dinshi da nawa coz m stuck here with u forever nd u have to deal with dis, U will never Get Islahulkhair back kadai ji abunda Tsoho yace, idan ka na tunanin in anyway she'd get back to u, toh stop dreaming nd wake up frm ur slumber. Ta tashi ta bar mai parlorn shi ko kalamanta sun mai zafib har be san time din da ya fara hawaye bah. Kaduna Karfe 5 na yamma fadila ta hade cikin riga da skirt na atamfa, tana kallon The Vow taji ana Sallama ta mik'e ta bude tare da Amsar sallaman, wata kyakyawar Mata da bata wuce 25 years ba riqe da wani kyakyawan yaro me kama da ita ta gani tsaye tana mata murmushi, kaman ta santa ta mata iso har parlorn Fadila ta sa hannu ta amsa yaron ta cillashi sama tace Bonbon yadai? Shi ko yaro sai kyakyata daria yakeyi, suka gaisa cikin mutunci, ta ajiye shi ta shiga kicin ta hado drink da ruwa ta dire gaban matan, suka Kara gaisawa, Matar tace sunana Amal, mu 'yan garin Gombe ne, jiya muka dawo garin nan don anyi ma mijina transfer zuwa garin nan, gidan mu ne jingine da wannan idan kin leka zaki hange katangan, Hakkin Makotaka yasa nace bari na shigo, Fadila tayi murmushi tace Allah sarki ni ma kwana 12 a nan gidan Lahhh Amarya ce? Fadila ta tabe bakih, ta chanza topic din. Ya sunanka Bonbon? Amal tace Irfaan, nima banyi 2years da aure ba, ta miqe tace bari na tafi, Fadila tayi murmushi tace InshaAllah nima zan shigo, toh shkn sai kin shigo Amarya, fadila ta bata rai nidai sunana Fadila, Amal tayi daria ta dauki Amal, fadila tayi cikin daki da sauri ta hada ma Amal kayan kamshi ta mata rakiya, Suna haraban gidan ne suka ga Mai gadi ya wangale gate, duk suka bi motar da ta shigo da ido, Jawad ne fuskar nan ba annuri, tamk'e tamau, nan da nan kamar an aiko ma Fadila mutuwa itama ta tsuke fuska, Amal na lura dasu duka, a ranshi yace wato an fara yi mishi shigeshige ko? Toh ba zai dauka ba Ya fito kamar zai tashi sama... Bibilicious Biebee2⃣7🏡GIDAN GANDU🏠by 💕Biebee Isa💕 ⃣ Gidan Gandu🏠by 💕Biebee Isa💕 by 💕Biebee Isa💕Biebee Isa💕Biebee Isa💕 Suna tsaye har ya karaso, kallon da suka wurga ma junansu ya sa Amal fahimtar irin zaman da sukeyi lokaci guda, nan da nan ta fuskanci ba jituwa tsakaninsu, Amma sai ta basar ds yake itama waiyayya ce, Amal ta bude bakinta tace ina wuni? Kwarjininta da Girmanta ya sa ya amsata da muna lpy?tace lpylao, Amal da bakinta tace Ashe Sabin Amare ne, Allah Ya bada Zaman lapya ya kwabe fitina, ya bar ku tare, ya kawo yara masu Albarka ta qarashe maganan da zolaya, Hankalin Jawad ya tashi ainun, be son lokacin da ya ce mata Toufa, wa'annan adduar sa ki nayi? Ko ce miki nayi ina sonta? Ya kallk fadila yace keee Ba ki gaya mata yadda akayi auren nan ba?

Chapter 7 of 20