Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
su sake haihuwa ba. Maryam din Ama na da shekara 7 Hajjo ta qara haifan Yan biyu mata, Hassana da Hussaina, Aishalle kam kamar ita aka ma haihuwan nan murna kamar mene, tace wlh Yaya Hajjo ke er baiwa ce, daga yan uku sai yan biyu dama ni, tace kema Allah xai baki.... ***** Hannun hajjo saqale da nashi, kuka take tayi jin abun da ke fita daga bakin mijinta, Hajjo na so na zame miki Gata har qarshen rayuwarki, amma da alamu kwanana yana gab da qarewa, tace wai rabiu me kake cewa haka? Cuta ba mutuwa ba fa? Hajjo kenan sati biyu kenan ina fama da ciwon cikin nan, nidai dan Allah kayi shiru, Hassan ne da qanenshi suka shigo dakin ganin mahaifansu na kuka yasa suma suka fara kuka, Da qyar rabiu yace hassan Allah muku Albarka, jeka kira mun babanka, da gudu ya fita sai gashi ya dawo da Musbahu da Aishalle a rude, Asha Rabiu ciwon ne haka? Sannu yace yaya ka yafe man idan na taba bata maka, Yaya ga Amanar iyalai na, na san zaka kula mun dasu, Kafin Musbahu yace wani abu rabiu ya cika yace ga garin ku nan, Tashin hankali. 4⃣🏡GIDAN GANDU🏠by 💕Biebee Isa💕GIDAN GANDU🏠by 💕Biebee Isa💕by 💕Biebee Isa💕Biebee Isa💕Biebee Isa💕Inalillahi wa ina ilaihir rajiun, shi ne abunda Musbahu ke maimaitawa, Hajjo kuwa don rudu kasa kuka tayi, Musbahu yayi qrfin halin fita kiran maqota don a suturceshi cikin awa da be wuce daya aka kai Rabiu gidanshi na gaskia, kafin aka zo zaman makoki, Karime ta dan rude da farko amma daga baya sai ta gyagije wai Allah ke kama maqiyanta ta hanyar kashesu. ****** Bayan Arbain; Musbahu ya rungumi iyalan marigayi qaninshi, dukkansu ba wanda be zuwa makaranta banda Hassana da Hussaina. ******** Bayan wata 5 Aishalle kince kina son muyi wata magana? Tace eh Mallam, daman wani abu na hango, yace me ke nan? Tace Me zai hana tunda Yaya Hajjo tagama Takaba me zai hana ka aureta? Ina ganin ta hakan ne zaka fi kula da ita kuma ka riqe amanar da qaninka ya bar ma, ya tsura mata ido, dama chan yayi wannan tunanin amma yana tsoron abun da zaije ya dawo shisa ve gaya ma kowa ba, kaii amma Allah yayi ma Aishalle albarka Akwai da kaifin tunani, yace Aishalle kin tabbata wannan shawarar taki har ranki? Don ni bana so nayi abunda zai bata ranki, tayi murmushi Maigidana kenan, kamanta hallacin Hajjo a gareni? Ko kirkinta da kular da ta bani ka mance wlh wannan abu har raina, don a qasar nan banda kamarku. Yace toh shkn, na amince, tace ka taso muje mu kai qoqon barar mu, yayi daria yace Aishalle baki da dama. Karime dake labe bakin kofa ta na jinsu idonta ya rufe tsabagen tashin hankali, kishi da Hajjo? Aiko zaayi yaqin basasa na biyu a gidan nan, keji wannan hegiyar mayyar, dan taga na barta ta zauna shine har da gayyato hajjo, ganin sun kusa fitowa ne yasa ta shige dakinta da gudu. ****** Hajjo jin maganar tayi bambamraqwai, ya zaayi ta auri yayan mijinta? Kuma Mijin Yaya karime? Aishalle tayi sauri tace donAllah yaya hajjo kar ki baza mun qasa a ido, kinsan duk wnda zaki aura a bayan mijina yake, kuma so kike kiyi aure wani gurin ya rabaki da yaranki? Auren mijina ne mafita gareki, hajjo ta harareta, hussain da ya shigo yace Umma danAllah ki auri babanmu, shiru tayi sai chan tace Allah ya hada kawunnan mu. Suka amsa da Amin. Ji sukayi ance idan ka isa Allah ya tsinen, ni zaka ci wa mutumci? Hajjon zaka aura? Qanwata? Yayi murmushin takaici, yace ynzun kika san cewa qanwarki ce? Ai aure be haramta tsakaninmu ba, kuma kamar anyi angama, ta chakumo wuyanshi, tace kuran sai ka saken, ya ce so kike na sakeki? Wani dan guntun tunani tayi tace da sauri aa kar ka saken danAllah, amma yasin da sake ba zata sabu ba. Daria yayi ya ja hannu Aishalle sukayi qofa ta juyo ta fara zagin Hajjo, Musbahu ya leqo yace qara ce mata uffan a bakin Aurenki wlh kuna kika tafi kin tafi kenan. Dif kakeji kamar an dauke wuta, sai murgude murgude da harare hararen da takeyi, ba halin magana. Oh su karime ashe ana san auren😜...... Ana idar da Sallahn jummaa aka daure Auren Hajjo da Musbahu..... ****** Bayan Shekara 15. A halin yanzu Hajia Babba(karime) Haihuwan ta 10 Shida sun rasu saura Abida, Sadiya, Zainab, sai Usman haushinta daya yaranta maza duk sun rasu daya kawai ya rage mata. Hajiya Ama(Aishalle) yaranta Aliyu, Umar Abubakar, Maryam, Rabi'u sai Auta Nuratu. Tun Da aka yi Auren Hajjo da Musbahu ko batan wata bata taba yi ba, Yaranta da Rabiu basu da bambanci da yaran Musbahu a cikin Gidan. ****** Dalilin da ya sa na tara ku anan shine; Na yanke hukuncin hada aurenku duka, kasancewar ku Maza duk kun gama makaranta ga Sanaar ku kunayi, ya kalle Mudassiru da Labaran yace matsayin qannai na kuke, amma aure be haramta tsakanin ku da 'yayana ba, saboda haka kai Mudassir kaine babba, na baka Abida, kai Labaran Sadiya ce matarka, karime sai faraa take tayi, don tasan sai yanda tayi dasu mudassir din Musbahu Zailani ya cigaba da cewa, Hassan Maryam ce taka Hussaini kuma Nuratu, Gambo kuma na baka Zainab. Aliyu kuma zaka auri Hassana, Umar kuma Hussaina, Abubakar kuma akwai diyar Alhaji Mai dala'ilu Hafsat, yace ya baka ita charaf Karime tace Wa?? Ai kuran baku isa ba, Hafsatun da ke son Usman? Kuma mun gama magana da mahaifiyar yarinya tace ta ba usman Hafsatu, Wlh ba wani Habuvakar, karime sanin dukian Alhj me dalailu ne yasa ta ke son hada danta da diyarshi, Shi dama Abubakar ya fita daban cikin gidan, yace Baba a bar ma Usman din, duk daya ne, don be son Auren yanzu musamman na zumunci, ya cigaba da cewa ni dama ina son na qaro ilimi, , yace toh shkn da kai da Usman din duk daya ne, Allah ya ba da xaman lahya. Suka amsa da Amin gabaki daya, Karime tace yauwa Alhaji maganan Zainab da Gambo, ya xaayi ka hadata da gambo? Bayan kasan hajjo bata qawnar jinina? Wani kallo da ya watsa mata ya sata nustuwa lokaci guda.. ***** Sunyi qoqarin fahimtar junansu, kowa yayi naam da hadin da aka mai, Zainab kuwa tana son Gambo qwarai da gaske amma Karime tana laantar wannan hadin, Gambo ma yana danne zuciyar sa, don duk dakin Hajia babba ita kadai ce ta fita daban, Hajia Hajjo(mama hajja)da Goggo Ama suka lallasheshi kan yayi haquri yama babansu biyayya, Haka dai yayi haquri ya chusa ma kanshi son Zainab don ya lura tana sonshi. A haka akayi aurensu, nan cikin gidan aka fidda ma kowa gidansa ciki da parlo, aka aje amare anan. Abubakar har ya tafi qasar Rasha(Russia) don karatu. A qasar Russia ya hadu da Yarinya me suna Raijana, course mate dinshi ce, yau da gobe suka shaqu, har suka qullah soyayyah tsakankinsu, har Abakar ya yanke hukuncin aurenta, Raijana ta gabatar da Abbakar ga mahaifinta, dayake mamanta ta dade da rasuwa, fir babanta yaqi wai bazai aura ma dan Africa diya ba, ta dage ta nace tace wlh sai ta aureshi, yace shiko idan ta nace sai ta aureshi, to ba ruwanshi da ita, ya yafeta, da yake sun yan chan sun dauki soyayyah da mahimmanci ta tsallake mahaifinta ta ja hannun Abbakar, Haka sukaje wani massalaci aka daura aurensu.Haka suka gama karatunsu, sukayi shirin dawowa NIGERIA, yace su zo suyi ma babanta sallama, suka nufa gidanshi amma yana ganin su ya musu korar kare, yace beson qara ganin Raijana, haka suka wuto Nigeria guiwa a sage. ******* Zaune suke a parlorn M.Zailani gabaki daya ana cin Abincin Gandu, yayi sallama hannunshi riqe dana Raijana, duka suka zubo musu idanu, Umma Hajja ta fara ganeshi da sauri ta miqe tana tafa hannu ga Abbakar ga Abbakar, gunta ya nufa don tun kafin ya girma ita yafi sani don tana sonshi kamar ita ta haifeshi, ya rungumeta ta shafa sumar kanshi, ya nufa M.Zailani ya zube ya na kwasar gaisuwa, kafin ya nufi Hajia Ama yana gaidata farinciki ya mamayeta amma kawaici ya hana ta nuna, ta amsa, sannnn ya Gaida Hajia Babba ta amsa cikin yatsina. Ya gaida yanuwanshi, Idon M.Zailani kan Raijana da take tsaye bakin qofa, yace Abbakar wacece wanchan, yayi murmushi ya kamo hannunta ya kawo ta gab da baban nashi, cikin turancinta tace Good Afternoon Papa, cikin turancin yan da yace hawwayu? Tace fine papa, Yace Abubakar wacece wannan? Abbakar ya murmusa yace Matata ce, Duka dakin suka hada bikin wurin cewa MATARKA?5⃣🏡GIDAN GANDU🏠by 💕Biebee Isa💕GIDAN GANDU🏠by 💕Biebee Isa💕 by 👂💕Biebee Isa💕Biebee Isa💕Biebee Isa💕Hjia babba ta fara tafe hannayenta biyu tana salati, Abbakar kafira ka auro ka kawo ta cikin gidan nan?wani mugun harara ya jefeta dashi, Hajia Ama tace yanzu daman baka da wayau, Abbakar ya dafe kanshi, Umma hajja tayi saurin miqewa ta ja hannun Raijana tayi waje da ita, sassan ta ta kaita ta shigar da ita dakih, ta debo mata abinci ta mata alamun ta ci sbd ba ta iya turanci ba, Raijana tayi murmushi tace thank u, Umma hajja ta komo cikin babban parlo, Abbakar xube gaban babanshi, yace Baba ka yafe mun, bana son aikata sabo ne yasa na aureta, kuma musulma ce, ta rabu da mahaufanta saboda ni, baba idan na rabu da ita ban mata hallaci ba, na kuma ci amana, shiru ya gifta na wasu yan lokkuta M. Zailani yace shikenan Allah ya maka Albarka, na yafe maka, amma daga yau ba wanda zai qara auren bare, kuma ni zan zaba ma kowannenku mataye da mazaje, yace nagode baba, Abbakar ya matsa gun mahaifiyansa Hajia Ama, yace Ama danAllah ki yafe mun, tace bakomi Abbakar Allah ya bada saman lfy. Yace Umma hajja ina raijana? Tace tana chan daka, ya nufe dakin tana ganinshi ta fashe da kuka, Abbakar ur family is against our marriage ryt? Ya rungumeta yace dont cry, dy are not like dat, i explained evrything to dem, and dy understood me, u have nothin to worry abt. ***** 30 years later.. Baba Mudassir da Aunty Abida(first daughtern karime) na da yara 7, Tahir, Fatima, Noorayne, Zayd, Farida, Haneefa sai auta Ahmad, Baba Labaran da Aunty Sadiya na da yara 5, Yusuf, Khamis, Mu'ammar, Yusra , Bilkisu. Yaran Aunty zainab(diyar karime) da baba Gambo(dan Hajjo) 2, Samir, Samar. Baba Usman kuwa da Aunty hafsat diyarsu daya Ni'ima sai da suka shekara 15 da aure suka haifeta. Baba Hassan (dan Hajjo)da Aunty Maryam(diyar Aishalle) na da yara 4, Imran, Faisal, Munira, sai auta Nasir, Baba Hussaini da Aunty Nur yaransu 3,Irfaan, Zayyad da Raffiyah, Baba Aliyu(dan Aishalle) da Aunty Hassana (diyar hajjo) nada Yara 3, Aisha, Nabila sai fadila, Baba Umar da Aunty Hussaina na da yara 2 daga Suraj sai Islahulkhair. Uncle Abbakar da Aunty Raijana(er mutanen Russia) diyarsu daya tilo Rumaysa'u....********* Yawancin jikokin M.Zailani sunyi aure, shike hada auren jikokinsa, Be hada auren jikan dakin Hajjo da jikan karime ko jikan karime da na Aishalle, hada yan daki yakeyi (misali dan baba hassan da diyar baba Hussaini) ko kuma diyar (Baba labaran da dan baba mudassir) shi a ganinshi hada auren jikokin Karime da jikokin hajjo ko na Aishalle matsala zai haifar don yana sane da gaban dake qulle tun kafin a haifi yaransu, amma ya kan hada jikokin Aishalle da Jikokin hajjo aure don su yasan Akwai yarda da amincin junansu. A qaidar gidan M.Zailani namiji daya gama karatun degree dinshi zaa mai aure, sai ya dauki matarshi ya tafi da ita duk inda zai kaita, mace kuwa da ta gama sakandire ake mata aure ta qarasa gidan mijinta. Jikokin gidan kama sukeyi don da wuya ka tsame wannan kace yana da kyau wannan be dashi, duk kakansu su ka dauko wurin kyau da haske, Sai dai kowa da halinsa, suna gaban da suka ga kakkaninsu sunayi, yan dakin Umma hajja da hajia Ama kadai ke zaman lafiya, Amma baka ra'ban yan dakin hajia babba, don da kun wuce sai ta zagi kakarku. Maza 7 zasu kammala degree dinsu ko wa da fannin karatunshi, gabaki dayansu suna Oxford University, Mata 6 kuma ke jarabawar qarshe, kuma da sun gama za a hadasu Aure, matsalar gidan baka soyayyah don baka san da wa zaa hadaka ba, amma ba zaa rasa wanda kake burin a hadaku dashi ba.. Wannan kenan. Kowa da halinsa, Islahulkhair ba ruwanta da kowa, maganaa be dameta ba, Yan dakin Hajia babba ke mata laqabi da er jiji da kai, Fadila kuwa ba ta da haquri ko kadan, idan ka mata laifi nan zata wanke ka tas, shisa Haneefa da bilkis ke shakkunta, Ni'ima kuma gata nan dai lafiyarta lao amma idan ta maka abu sai ka zata me ciwon hauka ce, abunta dai kamar sakarya, kuma Qalaw take, Rumaysah kuwa haqurinta yayi yawa, matsalarta daya Nawa, bata abu cikin hanzari, ko abinci su keci kowa sai ya tashi ya barta, yan dakin Hajia babba ba irin zagin da ba sa ma mahaifiyarta kasancewar mahaifiyar ta er wata qasace, kyanta dai ya fi tada musu hankali, suce mata mayya Aljanna, ko su zage kakarta Ama, tafi duka jikokn gidan kusanci da Tsoho (M.Zailani) saboda yanda take kuka dashi, tayi mis tausa, da fita, har yaqi cin abincin GANDU yace Na ta zaici.. A halin yanzu suna ta fama da Jarabawa ta NECO... ******* Gida ya kachame, yau baqin turai zasuzo, shiri ake tayi ba babba ba yaro, shekara 5 kenan rabon su da gida, Har masu aure 'yan nesa da kusa sunzo, misalin Qarfe 2 daidai suka shigo gidan, Waiyo Allah, Akwai maza Hurul Ayn dama? Ko wannensu najin kanshi, sai dai su basa yar tsama da junansu, ba ruwansu da beef din iyayensu ko kakaninsu, son junan su suke kasancewar sunyi shekara kusan 6 guri daya inda ba su da uwa ba uba... Sallama sukayi a parlorn Tsoho, Murna ya lullube iyaye da kakaninsu, zube wa sukayi gaban tsoho suna kwasar gaisuwa, kafin kowa ya nufi iyayensu, a ka gaigaisa.. Tsoho yace Sarkin Gida ka kaisu cikin Sashensu kowa ya zabi daki, yace ku biyoni suka ja Akwatinnansu suka nufa sashensu, ko wannensu ya dauki daki suka shige don huta gajia..Wurin 5 yanmatan Gidan suka shigo don yau evening paper sukayi, Babban parlo suka shige suka ga yayyinsu suna fira da tsoho, kowacce ta nufi yayanta ta rungume, Tsoho yace oh Allah, ko Sallama babu? Ku tashi kuje kuyi wanka kuci abinci kafin ku zo a gaisa ko? Suka ce toh, suka fice, har ta kusa bakin qofa yace Rumah, ta juyo tace naam tsoho, idan ba ki gaji zuwa anjima ki min wannan hadin shayi tace angama tsoho bari nayi laasar, yace yauwa er albarka. Zayyad ya bita da ido, wacece wannan tsoho? tsoho yace duk ba ku san juna ba, zumuncin ku ya tabarbare, kowa nashi kawai ya sani, dan wannan daki be san dan wannan dakin ba, Zayyad yace ayi haquri tsoho, ayi mana uzuri shekara 5 rabon mu da gida, mun san juna matsalar baza mu sheda juna ba, Tsoho yace Allah shi kyauta. A ranshi kuwa ya ce dole zan chanza wannan rashin zumunci, na san abun da zanyi, ko kun qi ko kunso sai kun zama TSINTSIYA MADAURINKI DAYA, Ya kalli Mu'ammar yace yaushe Zaidu din zai dawo? Muammar Ya tabe bakih chan yace nan da wata 3, tsoho yace wai saboda mene baku dawo tare ba? Inace duk tare kuka fara karatun? Samir yace kwantar da hankalinka nan ba da jimawa ba zai dawo cikin yanuwanshi. Tsoho yace akwai abunda ba kwa so na sani, Suraj yace kasan ko sun boye ma ni me fada ma ne, yace toh Allah sa dagaske ne, suka ce hakan ne ma. Yauwa da kunyi bautan qasa sai Aure ko? Muamaar yace Aifa maganar kenan Aure Aure mundawo GIDAN GANDU kenan, duk suka sa daria....6⃣🏡GIDAN GANDU🏠by 💕Biebee Isa💕GIDAN GANDU🏠by 💕Biebee Isa💕by 💕Biebee Isa💕Biebie Isa💕Biebee Isa💕 Yau basu da paper, suna gida, Fadila ta shigo Sashen Uncle Abbakar, Aunty Raijana na zaune na kallon wani Fim, Aunty Maisah fa? Cikin hausarta da har yau be fita tace ki dubata dakih, ta shiga, tsakih ta buga da qarfi, Oh Allah haka zaki qare dai, don fa kiyi sauri ki shirya ya sa na kiraku tun dazu, amma ji beki shafa ki keyi, Maysah tace sorry riga kawai zansa tace wlh ki same mu sassan Baba Hussaini, bari naga Islah ta shirya, ta iske Islah ta shirya suka dai ta ke jira, Islah tace lemmie guess maysah bata shirya ba, Fadila ta yi dan guntun tsaki tace ke da kika san komi, yaya Suraj ya shigo dakin yana Sisi bani earpiece dina, islah tace bro donAllah bari mu dawo zan baka, yace kinga dai ki-- shiru yayi da idonsa ya kalli fadila, murmushi ta mai tace Yasuraj ina wuni, ya mayar mata da murmushin yace wacece wannan? Tace fadila ce, lalala haka kika qara girma, kai murmushi ta mai, Yace ina zaku ne? Islah tace walimar Quranin qawarmu, ya kalli fadila yace tohm muje na kaiku koh? Ta dago kai suka hada ido da sauri ta sunkuyar da kanta, Islah tace wai sarkin Nawa muke jira, wacece sarkin nawa kuma? Maysah ta shigo dakin tace iyayen mita gani nan, Yasuraj ina wuni? Ya sakar mata murmushi ya ganeta don fuskar aunty Raijana gareta, yace Rumaysah wai duk kun zanqale banda su o'eh Islah ta turo bakih tace kai koh yaya? Ban ma yi missing dinka ba, yace liar, ku tashi muje, suka nufa parking lot motar da Tsoho ya ba kowannensu bayan dawowarsu, ya bude ya shiga Islah ta bude gaba zata shiga yace ke zaki shigo ki isheni da surutu koh? Ko ma baya jareh, Eeelerh dawo gaba kinji suka tsaya kallon kallo waye kuma eelerh anan? Ganin Fadila yake kallo yasa ta gane da ita yake, ba musu ta shiga gaba, Maysah da Islah suka shige baya, Ya kalleta eeelerh ina zamu ma? Jikin ta yayi sanyih ta gaya mai, bini bini yake jan ta da fira, Islah cikin rada tace maysah kin ga abunda na gani? Ita ma cikin murya qasa qasa, ngani, Yasuraj ya fole, suraj ya kallo su ta mirror yace gulmanmu, me kuke cewa? Sukayi daria, suka iso gidansu Fatima Bobboi wace ake ma sauka din, fita su Islah sukayi, fadila zata fita taji Yasuraj ya riqe mata hannu juyowa tayi cikin tsiwa taga yana kallonta ba shiri ta kai kanta qasa, a hankali yace I love you fadila, Kallonshi tayi da sauri yace Fadila will u marry me? Murya na rawa tace, Yasuraj kasan dai we are not allowed to fall in love koh? Kayi sauri ka cire wannan tunanin don baka san wacce tsoho zai baka ba, yace fadila, yanzu ba a auren dole, all m asking is for u to let me love u, nd i promise u, u wont regret it, ya qare matse hannunta, yace pleaseee, a hankali tace i love u yasuraj, ya sake ajiyar zuciya. Islah ce ta durquso ta window, hey are u coming on not? Suraj yace shes not byebye, Fadila tayi mata gwalo, Rumaysah tace ke ma dai ina ruwanki ki zo mu shiga ciki, in yaso sai muce ma bobboi tana love cikin mota. Sai da Suraj ya tabbatar ya gina sonsa a ziciyar fadila kafin yace ta shiga ta mata Allah sanya Alheri ta kira su Islah su zo su wuce. ****** Nikam Mu'ammar ka gaya ma hanifan? Ya dan tabe fuska yace kasan bana son raini, but zan aika Bilkis, Jawad yace kana bani mamaki wlh, kana son abu amma girman kai dinka ba zai barka ka furta ba, kuma idan gudu kake kar tsoho ya hadaka da wata, dama ka bar tunanin nan, dan a kanmu Culture dinnan na auren hadi zai tsaya, fine ba xa mu aura bare ba, but a bar mu mu xabi na cikin gidan da kanmu, amma idan kaga zaka tauye ma kanka haqqi ka auri wacce baka so den goodluck wit dat, Guy, ya ka dauki zafi ne haka, yace Allah bana son bacin rai, wai hadin Aure kawai sai a hadani da wacce banaso, yace wlh akwai matsala don ba yarda zanyi ba, yanzu ma Bilkis zanje nayi approaching, Muamar ya kaimai duka, kaii carefull dats my lil sis, Jawad yace na ga nima hanifan sista tace, hurt my sis nd i will hurt urs, sukayi daria daga nesa suka hango haneefa ta fito daga sassan su tana yauqi, Jawad ya miqe tare da cewa man up and tell her wat u feel, yaqwala mata kira Hanee, ta qariso tana wannan yauqi, Yajawad yadai? Yace Yayan ki ke kira, wane yayan? Ya nuna mata mu'ammar tace ok, ina Bilkisu ne? Tana sassan hajia babba, yace ok yayi gaba ita kuma ta nufa Yamu'ammar how far, yace hanee m in love, jin maganar tayi wani bambaraqwai, tace with who? With you ta zaro kyakyawan idonta tace what? Shima ya zaro mata nashi yace Yes i love haneefan Baba Mudassir tayi rau rau da fuska, Yamu'ammar namiji ne da ko wacce mace zata so, haneefa tace amma Yamua'ammar kasan tsoho--shh ya dakatar da ita, i dont care abt tsoho's decision ol i know Is dat i lob u, unless ban miki bane ba, tace Aa fa ba haka bane, yace nasan me kike tsoro, but its high time su bar wannan Culture din, munji ba zamu aure bare ba, amma a bar mu mu xabi na gidan da kanmu. Bazan tava iya auren yarinyar da bana so ba gaskia, Tace toh shkn, Allah ya bamu saa, ya dan kallota is dat a yes? Ta kashe mai ido daya nan suka zauna suna firar soyayyah.. ***** Hajia Babba tace Ahh yau Jawad a sashe na? Tunda kuka dawo so daya ka shigo dakin nan da ba ni na haifi uwarka ba kuma na riqi ubanka ba da na ce kai ba jikana bane ban san ko Aishalle ta shiga tsakani da kai ba, yayi daria, kin cika mita wlh, wai ni meye matsalarki da Hajia Ama ne? Ko don ta aure miki miji?Tsohon ma ya tsufa amma kina kishinsa har yau, ko don ta fiki kyau ne? Da yarinta? ai fa ya zunguro ma kanshi, nan ta fara zagezage da tsinuwa, yo indai kyau irin na mayu ne wlh na yarda na fi duwawu muni, Allah ya tsareni da kyaun Mayyu da Aljannu, nan ya shige dakih yana daria zaune ya ga bilkis tana ninke kayan Hajia Babba, yace Sis ya dai? Ta fadada murmushin ta, duk cikin causins dinta Yajawad ya fi burgeta, ta na mugun sonsa Yajawad ina wuni, yace me kikeyi? Hajia ta sani ninkin kaya, Ya ce duk cikin yaran gidan nan Hajia ta rasa wanda zata sa aiki sai matata? Dadi kamar ya kashe bilkisu amma ta wayance tace matarka kuma? Wace matarka? Yace ke mana, ko ba zaki aureni ba? Tayi mai far da ido, tace Dan tsoho zai baka mata, Yajawad yace ke ni rabani da wannan hadin zumuncin, ni ke nagani nakeso inaso sai dai in kece ba kyasona, da sauri tace ina sonka fa Yajawad, yace lets stick togeda, ba me rabani dake kinji? Ta gyada Kai tana murmushi. ******** Sanye yake da 3quarter hannunshi riqe da basketball ball, leqawa dakin Jawad yayi ya ga bayanan, ya leqa dakin mu'amar beyanan, tsaki yayi ya ga suraj kwance yace guy muje muyi basketball, Suraj yace uhm uhm not in d mood, Zayyad muje muyi, zayyad yace No thanks tsaki yayi yace Kar Allah ya sa kuyi, haka ya isa field din da ke bayan Sashen Hajia Ama yana bouncing ball din. Da ya hango basketball court dn ya wurga ball din, daga chan nesa Islahulkhair ce ke skipping, ji tayi saukan Qwallo a kanta, qara ta sake na shagwaba ta dafe kanta tana kallon wanda ya jefeta da ball cikin tsiwa tace ba ka gani ne? Ya kalleta yace da kika ga ball me sa baki matsa ba, Miskilancin Islah ya tashi, ta ga idan har ta tsaya tanka mishi tana iya sake kuka ta duqa ta dauki rope dinta ta wuce warta, har ta kusa barin field din ya daga murya yace Islahulkhair tsaya wa tayi bata juyo ba, yace kin iya B.Ball? Juyowa tayi tace wat if na iya? Yace i want u to play wit me pls, kamar ba zata tanka ba sai kawai ta qaraso tace lets do dis, ya fara bata ball din suka hau bugawa, sai da yayi mata 12-0 wai ita ojoro yayi haka zatace ba ta yarda ba sai a sake, haka suka dinga yi ko daya bata ci ba, tace a qara one last time, yace Nooo nan ta yi wayon kwace ball din taje ta sa a ragar sa, yabita ya qawace ball din ta yi tangar tangar zata fadi ya tallabota suka zube a qasa suna daria sosai, yace Islahulkhair I need smeone da zan dinga games da ita bayan nayi aure, i love games, nd u fit wat i like, so u want to be my game partner nd my life partner? Ta tsureshi da ido, yace zan fahimceki idan kika ce aa coz nasan beef din da ke tsakanin Grandma dina and ur grandma, but kar fa ki manta mun hada kaka da ke da babana da mamanki Uwasu daya ubansu daya nima ina da jinin Umma hajja tatare dani so ban ga dalilin da zaisa ki qi ni ba, oh maybe ban miki ba, ya miqe ya barta kwance har ya juya, Islah tayi saurin cewa Yasamir ya juyo ta miqa mai hannu da ga kwance, ya sa hannu ya dago ta, cikin sanyin muryarta tace Yasamir m scared, yace i knw wat u are afraid of, dis Culture has to stop now, ba Zamanin daaa mu ke ba, trust me pls, ta daga mai kai tace ok. Yace I love u Islahulkhair, cikin kunya tace i love u Yasamir..👻 7⃣ 🏡GIDAN GANDU🏠by 💕Biebee Isa💕GIDAN GANDU🏠by 💕Biebee Isa💕by 💕Biebee Isa💕Biebee Isa💕Biebee Isa💕Sun gama exams qarfe 12 suka dawo gida, Maysah ta shiga wanka, ta ci abinci, ta fito da sauri tana yana gyalenta na afta dress, ta kalli mamarta tace Amma na je gurin tsoho, cikin hausarta, akwai dambun nama a kitchen ki kai mishi, da sauri ta shiga kichin ta dauko, ta nufa Sassan tsoho.Ta shiga dakin da Sallama, aka amsa ta, ba shi kadai ke dakin ba su biyu ne, ta ce tsohona ina wuni ya ce cikin sake fuska, Ruma kina lfy? Ya exams? Lahya Alhamdulilahi, ta kalli wanda suke tsaye tare dace Yazayyad ina wuni yace lfy lau Ruma tayi murmushi, Tsoho yace ki diba bedside na nan tun da safe babanki ya kawo man newspaper nace sai kin dawo zaki karanta man, ta miqe cikin yanayinta ta nufi dakin Tsoho, Zayyad ya bita da ido, ta dauko jaridar ta matso da sofa ta zauna ta shiga karanta mai newspapern nan cikin qwarewa da muryar ta mai dadi. Lumshe ido zayyad keyi sakamakkon jin muryar ta dake ratsa jinin jikinshi cikin kwanyar kansa.Nan take zuciyarsa ta kamu da son Rumaysah, duniyar tunani ya fada, ba tare da sanin ta gama har ta shiga dakin Tsoho don dauko mashi magungunanshi, Tsoho sai magana yake mai amma inaa hankalinshi baya gareshi, Tsoho

Chapter 2 of 20