Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
Tace Aa Amma, Amma tace liar, na ganki kina kuka, kamar jira take ta fashe da kuka, Amma ta rungumeta sai da ta yi me isarta, tace Amma Yazayd Dan iska ne, Mashayi kuma Maz--- Amma ta dakatar da ita ta hanyar sa mata hannu a bakih, Sai kuma ta mata murmushi tace Maybe ke xaki kubutar dashi daga sinful acts dinshi, ki nuna masa hanya madaidaiciya, Amma how? I cant, Amma tace shhh, mya Baby i trust u, u can even do more, Have Faith kinji? Ta gyada mata kai. Tace Oya tashi tsoho ya aiko A kiraki nace kina wanka, tashi kijei, jikih ba qwari ta daura dankwali ta fita. Amma ta bi bayan tillon diyarta da ido, tausayinta ya mamayeta, Allah ga Baiwar ka nan, Allah ka shige mata Gaba Amin.. ****** Tsoho ya kalleta yace Rumah Nah, ba tare da ta kalle shi ba tace Naam Tsohona, yayi murmushi yace yau ko kallona ba zakiyi ba? Ko har ynz fushin akeyi dani? Ta qaqalo murmushi, haba Tsoho nah, wani irin fushi a na zaune kalau, ya girgiza kai yace Rumah kenan, my favourite among them all. Tayi murmushi, yace A tunanin ki na shiga tsakaninki da farincikin ki na hadaki da baki'n ciki, A Ganinki na hadaki da kunama me zafin Halbi, na san xakice anya Tsoho na sona? Ya hadani da Mashayi kuma Mazinaci? Maysah na san abinda nakeyi. Allah yayi yarinya me hankali, me tunani, me hangen nesa, da sanin ya kamata uwa uba ga ki da Hakuri, kinyo gadon kakarki Aishalle, Auren Zaid Jihadi ne, ke kadai zaki iya hakuri da halayenshi, ke kadai zaki tsaya tsaye a kansa har Allah ya sa ya bar halayensa, kuma nayi istihara tun kafin nayi hadin nan, naga Aurenku Alheri ne, Kece Rufun asirinsa. Rumah kin fahimce ni? Maysah ta daga kai tana kuka, tace eh Tsoho, Allah ya bani iko Allah ya sa hakan yafi zama Alheri tsoho yace Amin Rumah nah, sannan Abu na gaba, munyi magana da Mudassir yace Zaid zai fara housemanship dinshi Nextweek a Abuja a nan National Hospital, Asibiti ta bashi Gida, Amma na baku daya daga cikin gidaje na na Maitama, na yanke hukuncin dake zai tafi, sai ki fara Shirin tafia, gaban Maysah ya bada Hinqim tace Allah kaimu. Yace Amin, Gani yayi sai Kyarma takeyi, hakan yasa yace toh kina iya tafia, sannan Akwai Taron duka Gida Gobe da Safe Misalin Karfe 10 na safeh. Tace toh Tsoho Allah kaimu Goben. Yace Amin Ta miqe guiwa a sake ta bar Dakin tsoho. ****** Wallahi da an san yanda na tsana ganin Fadila da ba a yi gigin hada auren nan balle a daura, wlh na kijininta, Bilkisu tace ni wai ya ma za a aura mun Azzalumi kamar Suraj, ji dai randa ya kamamu ya zane, wlh na tsaneshi, Mu'ammar da yake ganin kamar ya fi su tashin hankali, babban tashin hankalinsa kuwa shine ganin an daura auren Hanifa da wanninsa, Zaid kuwa ba abunda ya damesa, chatting dinsa yake da Diyyan Shagali. Amira kuwa ta maidasu TV sai kallo take wannan yace ka za wannan yace kaza. Aunty Saadiya tace hajiar mu kice wani abu mana, toh dan ubansu sun ishe mutane da surutan banza su saman ido mana suga yanda zan warware alamarin nan, jira nake na ji ta bakin Alhaji, sai na san abunyi, Amma sun tasa ni gaba sai babatu suke tayi, ba sai na sa musu ido ba, Aunty Abida tace ynz dai haquri zamuyi gabaki daya, Sai mu jira muji me baban zaice gobe. Kun gane koh? Duk suka gyada kai, Amar yace hajia me zakiyi ke goben, ni burina a warware auren nan kawai, hajia tace kai dai ka bari sai Goben u shud all trust ur Grandma. Hajia Babba Ta kalli inda zaid ke zaune tace dan gidana Yaya dai banji kace komi bs? Ya kalleta ya watsar yace ban da ta cewa, tace wai ni mesa kake man haka ne? Miqewa yayi yace Jawad ka kirani idan baba ya dawo ya fice daga parlon, hajia babba ta hau masifa ina sonka kana gurxa man, sai wulaqancin tsiya shege me qiran samudawa, kowanensu sai da ya dara.. Gabaki dayan su sun Hallara parlorn tsoho suna zama jiranshi, da sallama ya fito daga dakinsa suka amsa mai, kujerarsa ya zauna aka fara kwasar gaisuwa, sai da aka gama kafin yayi gyaran murya tare da gajeruwar Muqadima, yace Ahhh A jiyan ne aka daura auren Jikokina su 12, Allah sa Alheri, 'yan dakin hajia Ama da Umma Hajja kadai sukace Amin, Hajia Babba kuwa sai hura hanci take tayi, abu na farko, ya kira Hanifa yace taso nan, ta miqe ta nufeshi ya ciro wata envelop ya miqa mata kamar ba za ta amsa ba ta amsa yace dubu 50 ce sadakin ki ne, jiki ba qwari ta koma mazauninta ta xauna, haka ya kira Bilkisu, Islahulkhair, Amira Fadila da Rumaysah ya danka musu sadakin su a hannu, Sannan yace Ahh gobe lahadi, nasan gobe yan mazan zasu koma bakin aikinsu, to na yanke hukuncin kowannensu zai tafi da matarsa, Jikokin Hajia Babba suka zuba mata ido alamun zasu yi magana hannu ta daga musu alamun suyi shiru, bari taga iya gudun ruwanshi, Tsoho ya cigaba na bada kudadde zaaje Dubai a ma yanmatan kayan daki da na kitchen, da kuma lefe kuma na mallaka ma mazajen Gidaje a duk garin da suke aiki, Sannan kuma na chanza ma kowa mota nd kuma. Toh ina umurni da matan su Shirya, gobe zasu bi mazajensu... Hajia Babba tayi karaf tace kagama? Haba Alhaji? Ran tsoho a. Bace yace Karime menene haka? Tace bangane kowa ya bi mijin shi ba? Sbd me? Daga daurin aure jiya, sai kace an gaji da su,,, ta cigaba da bambami, Tsoho ya fara tarin karya kamar xai shife, tarin da karfi, kuma sai Allah ya kawo mai atishawa me zafi, ai nan hankalin kowa ya tashi, Hajia karime ta rude, sannu Ahaji, Baba hassan ya ruga firij ya dauko ruwa yana fadin Baba sha ruwa, ya ture ya shaqe murya yace ba ruwan da zansha ai haka take so ta ga karshe na koh?toh bazan sha ruwan va, ku barni na mutu kawai tunda ba za a mun yadda nakeso ba, ai nan ta fita hayyacinta, ta fara cewa ya haquri Alhaji, danAllah ka sha ruwa, wlh ko ynz kace su tafi zasu wuce, daman wai naga ba a shirya ba ne, amma yadda kace hakan zaayi, Allah ya huci zuciyarka, danAllah ka sha ruwa, Tsoho ya kurba Ruwan nan taro ya watse bayan an Tsaida maganan gobe kowa xai wuce da matarsa.. ***** Mu'ammar kamar zai yi hauka, fadih yake Hajia wai menene haka? Bangane ba? Ya akayi kika amince masa? Hajia babba tace dan ubanka so kake mijina ya mutu, haquri kawai zakuyi ku tafi dasu din, bayan sati 1ko 2 ku danqara ma shegu saki 3 3, da dadin bakih da jan magana suka amince da tafiar Hajia Ama da Umma Hajja ne zaune parlorn Umma Hajja su ka tasa Jikokinsu gaba suna musu nasiha me ratsa jiki da ban haquri, tare da jadadda musu haqqin zaman tare da na auratayya, Da kuma ban Haquri, duk wanda yyi haquri zai ci ribar rayuwa a karshe suka samusu Albarka, sannan sukayi umarni da yanmatan suje su hada kayan buqattunsu kafin a aiko musu da wasu, haka suka miqe suna matsar Kwallah kowa yayi sashensu don shirya kaya.. RANAN _Bibilicious Biebee_ 2⃣1⃣ 🏡GIDAN GANDU🏠by 💕Biebee Isa💕Gidan Gandu🏠by 💕Biebee Isa💕by 💕Biebee Isa💕Biebee💕Biebee Isa💕Tsoho ya kalli Aunty Nuratu da Aunty Zainab yace ku zaku raka Rumah Abuja dukda shi Zaid din yace sai Gobe litinin zaiyi reporting so tafianku sai gobe, ke Abida da Hassana zaku raka Islahulkhair gidanta da ke Zaria, Hussaina da Sadiya ku zaku raka Amira gidanta dake Bauchi, Raijana da Maryam ku xaku raka Fadila gidanta dake Kaduna, Yusrah da Rafiyyah kuma zasu kai Bilkisu gidanta dake Kano. Zayyad kuwa zai dauki matarsa Hanifa su tafi chan gun aikinsa a lagos... Ban san tashin hankali, Amare kawai nace a kai gidajensu bance ayi tsegunguma ba, ku tashi ku tafi, Allah ya tsare hanya. Suka amsa da Amin, nan fa aka fara bankwana masu kuka nayih, barin ma Islah, rumah da fadila da suka rungume juna suna kuka, sun ba kowa tausayi, don shaquwarsu ya wuce misali, ko tsoho kansa sai da ya share hawaye. Da qyar aka tura Fadila motar Ya jawad Aunty maryam da Aunty Raijana suka shiga baya, jiki Ba qwari ya Jawad ya zo ya durqusa gaban tsoho Tsoho ya mai Adduan Allah ya tsare, haka ma akayi da Islah Aunty Abida na huran hanci ta shiga motar don bata son tafian nan take ba. Haka Ya Muammar ya shiga motar bayan tsoho ya mai Addua, Yaya Yusrah, da Yaya Rafiyya suka ja Bilkisu zuwa motar Suraj, inda yaje yayi bankwana da kakaninshi kafin ya shiga motar Tsoho yace to ku tunda tafiar ku hanya ce kuna iya tafia. Allah ya bada zaman lafia ya kawo kazantar dakih, ba wanda ya tanka mai, Suraj ne ya fara jan motar sanna Mu'amar ya bi bayanshi sai jawad ke qareshe, Convoy sukayi suka bar gidan mudai sai dai muce safe journey. ****** Baba usman ne ya kebe da samir inda yake cewa Samir kaga kai da na ne, sbd Zainab kanwata ce ita ke bi mun, Akwai shaquwa tsakanina da Mahaifiyarka, ina so ka riqe min Amanar diyata Amira, donAllah kayi haquri da halinta, quruciya ce da sakarci ke dawainiya da ita A sannu zata dawo daidai, Samir ya hadiye miyau me dacih, wato kowa yasan Amira bata da wayau, har ana hada shi da Allah yayi haquri, wato yayi ta haquri shi yana cutuwa, da qyar yace ba komai baba, yace yauwa Samir Allah bada zaman lafia, Anya ba zaku bar tafian nan gobe ba ku bi jirgi? Yace aa bari mu ta tafia ynz, ina da abunyi gobe a office yace toh Allah muku Albarka, Samir yayi bankwana da kakaninshi, ya kwashi Amira da Aunties dinta biyu da zasuyi mata rakiya zuwa Bauchi state. ****** Gudu suke ta shatatawa, ba me cewa juna qala. Balle duk motan ba sa shiri, dama dama motar Suraj Rafiyya da Yusrah Kawayene su kan taba hira. Amma tsohon nan akwai hadin doya da manja. In banda dole me zai hada Aunty Abida da Aunty hassana a mota guda? Haka dai suka daure kowa na kai zuciya nesa har Allah ya kawo su Kano lafiya Unguwar Nassarawa GRA, Gida ne da ya amsa sunansa Gida, a yau ne Tsoho ya mallaka ma Ya suraj gidan nan, ko da suka iso maaikata sun gyara gidan sun kalkale, Fadila da Islah suka fito don kama ruwa, Aunties ma duk suka shigo banda Jawad da Ammar, Yaya Rafiyya tace ku Jawad ba za ku shigo ba? Ya gimtse fuska ganin An kawo bilkisu gidan waninsa be ganin zai iya shiga yace no yaya wadannan ma su fito mu tafi kar maghriba ta mana, yaya yusrah dai ta tabe bakih, tace ina kano ina kaduna? Mu'ammar ne ya yi qoqarin shiga ya dan leqa gidan, auntt tace ku ku muje ko? Kun san tafia mun da nisa, duk suka mimiqe, Islah ta kama hannun Bilkisu ta mata Sallama tace Allah ya hada fuskokin mu da Alheri, Harara bilki ta jefeta dashi, Fadila ko kallo bilkin ba ta isheta ba suka bar dakin, Bilkisu ta rungume Yayanta ta na kuka, Yaya pls kar ka tafih, bana son nan, Muaamar ya share mata hawaye a hankali yace dont cry sis, kin manta abubda Hajia babba tace? Dis is for a short period of time okay? Jus take care of urself Ta gyada kai u too, Suraj na kallonsu ya tabe bakih ya kaufa kai. Mu'ammar ya fita. Haka suka qara daukan hanyan Zaria, in less dan 3hours suka iso Zaria, Cikin gari sukayi Kuyambana Lowcost, inda Tsoho ya ba Mu'ammar gida, haka dai suka shiga gidan suka firfito har yan motansu Jawad, shima dai ya fito, suka nufa ciki, Akwai dan Kurah a gidan suka kakkabe, don shi Mu'ammar ya qiyin waya a zo a gyara. Bayan sun dan huta ne su Jawad suka musu Sallama hardasu Aunty Abida da Hassana don gobe zasu bi flight din maiduguri kuma ta kaduna zasu tashi, Islah ta sha kuka sosai, don ba wanda aka bar mata daga ita sai Muaamar, tana kallonsu suka shige mota suka nufa Kaduna, suna barin gidan shima Mu'ammar ya bar gidan don bejin xai iya kwana under same roof with wata idan ba Hanifa ba. Nidai Bie nace Islahulkhair u are on ur own oo😉 Gab da Isha'i suka shigo Garin Gwamna, sai da Jawad ya biya dasu Mr Biggs sukayi take away, ya kuna tsaya a One Eleven ya siyo musu Kaza da Masa kafin yayi Unguwar rimi Lowcost dadi inda Tsoho ya ba Jawad Gida me dan karen kyau. A gajiye suka shiga gidan, gidan yayi kyau matuqa. Nan suka zauna a parlo suka huta. Samir ya kira Jawad yace yadai kun isa? Yace shigowar mu kenan, shima Samir din yace mu ma ynz muka shigo bauchi, Allah huta gajia sukayi bankwana... WasheGari Ya Suraj ya kai su Yaya Raffiyya Airport don yau zasu wuce Maiduguri bayan su mai nasiha sosai,haka ma Samir ya kaisu Aunties dinsu Airport, Jawad ma ya yankan musu Tickets din komawa Maiduguri... Maiduguri Haka ma aka kawo Yazayyad da Hanifa Airport su biyu rak bayan ta sha kuka sosai, suna zaune suna jiran jirginsu da zai tashi zuwa lagos. Shi ko Zaid ya kwashi Aunty Nuratu da Aunty Zainab da Maysah a mota suka bar gidan bayan Tsoho ya kebe da Rumarsa ya qara jaddada mata, sun kusa wajen Garih ne ya latso wayarsa ji kawai sukayi yace Na kusa dags bisani kuma suka ji ya gangara bakin titi ya parker, ba wanda ya tanka mishi, ta gilashin mota ya hangota, ya kalli Maman Samir da ke zaune gaban mota yace Aunty Zee dan koma baya, mun qara samun pasinja, tace pasinja kuma? Be tanka ta ba ya bude murfin kofa duk suka bishi da ido gurin wata suka ga ya nufa, Ta sha Ado sosai ta na janye da Akwatin Trolley, Gaban Maysah ya buga sakamakon wacce ta gani ba kowa vace illah wannan da suka ga ta na bacci kan Gadon Yazayd, wacce sukayii fada da Amira, toh wacece wannan?to ba kowa bace illa Baddiyan Shagali, Da sauri Maysah ta fara maimaita inalillahi da ita zaa Abuja? bude booth yayi ya tura Akwatin Diyyan Shagali, kafin ta zo ta bude gidan Gaba ta fada tana me karya jiki da feleqe ta juya baya ta bi su da kallo daya bayan daya ta watsar, bata da niyyan tankasu, duk irin tsageranci na Zaid sai yaji be ji dadin hakan da tayi ba, a hankali yace Dear, My Aunties, ta dan juya tare ds yin kicinkicin da fuska tace Ina kwananku? Aunty Nuratu ta kasa haquri dai tace Zaidu wai Wacece wannan???? _Bibilicious Biebee_ 2⃣2🏡GIDAN GANDU🏠by 💕Biebee Isa💕 ⃣ Gidan Gandu🏠by 💕Biebee Isa💕by 💕Biebee Isa💕Biebee Isa💕Biebee Isa💕Zaid ya danyi gajeran tsaki yace Aunty sunanta Badiyya, Aunty Nuratu ta yi shiru da bakinta haka suka dauki hanyan Abuja, Gudu suke ta shatatawa, sun tsaya sun ci abinci a kano kafin suka dauki hanya kuma. Lemmie help u wit ur seatbelt, ta galla mai harara tace i dont need ur Help, Zayyad ya yi murmushi ya saka nashi belt din, Jirginsu ya fara tafia Matuqar tsoro ta tsorata, ba yau ta fara hawan jirgi ba amma ta tsorata da tashin Jirgin yau, bata san tym din da tayi saurin dafa YaZayyad ba da jirgin ke niyyan tashi tare da rintsa ido, Zayyad yayi murmushi yace Ashe yarinyan na da tsoro, da sauri ta janye hannunta daga nasa ta galla mai harara, be tankata ba, illa ya ciro Chalbin shi a aljihu ya fara Ja. Haka suka daidaitu a sama suna tafia har bacci dai sai da tayi a kafadun YaZayyad ba tare da saninta ba, Cikin Awa daya da yan mintuna suka iso LAGOS, hanifa ta gaji sosai, Cab ya tsaida musu suka hau, har gidansa da ke wani unguwan da sai na tambayo sunansa😉 Gida Gida ne self contained, ya biya me tazi din ya kwashi kayan shi da nata ita ko handbag ta dauka, Nidai nace Waiyo Allah Zayyad Bawan Allah, be dau abun da Zafih ba, idan ta qi bada kai ka zane ta kawai👻 Zayyad Hussaini Zailani Matashi ne dan kimanin Shekaru 29, yaro ne kyakyawa wanda be da matsala ko kadan, hak'urin shi ya wuce misali, Yana aiki ne a Birnin Lagos A wani Companyn Oil And Gas. Rokonsa daya Allah ya bashi Zaman lafia da wannan er Zafin kai ni dai nace Amin. Sai dare suka iso Abuja, Straight sai da yaje Garki ya ajiye Diyya yace mata sai yazo, kafin ya dauki hanyar Gidan da Tsoho ya mallaka mai dake Maitama, Gida ne na 'yan mala'u masu brush da cinyen kaza, gidan ya tsaru iya tsaruwa, Su Aunty nuratu suka shige dakih da huta gajia. Zaid Mudassir Zailani tsaran Zayyad ne amma Zayyad ya bashi kwana 14, ya na da kwalin degree na likitanci, A gobe ne zai fara HouseManship a National Hospital Abuja, Zaid be da wata matsaala in banda ta shaye shaye da kuma tsageranci, Toh gashi an hadashi da Salihar Mace, toh ko ya tafian nan zaiyuwu?🤔 Ko da Jawad ya kai su Aunty Abida Airport bayan tashin su straight Office dinsu ya nufa, Jawad Mudassir Zailani Matashi me ji da kanshi dan kimanin shekaru 27 ya karanta Industrial Chemistry, ynz haka yana Aiki a NNPC kuma tauraruwarsa na haskawa don yana da himma da qwazo, Jawad na da zafih be son raini kwata kwata, gashi an hada shi da Macen da ba a tabata ta kyale duk girman mutun. Toh ku biyoni dai muje. Samir kuwa tunda ya kaisu Aunty, ya tafianshi Office, Samir dan kimanin shekara 27 ya karanta Engineering, samir na da sanyin zucia, be da matsala, Samir Injiniya ne wanda ake damawa dashi a garin bauchi, Matashi ne ko shekara daya be rufa da fara aiki a Bauchi ba, Amma ko ina damawa ake dashi, balle gwamnati da ke bashi kwangiloli, Samir Gambo Zailani kenan Matashi me ji da kudi, Young Billionaire. Toh ya zaman shi zai kasance da Psychic lilsismeeranshi?🤔 Hmmm Mu'ammar Labaran Zailani, Matashi me shekaru 28 a dunia, Ya hadu iya haduwa, Shima dai Injiya ne amma na jirgi, wanda ake kira da Air Police Engineers, Mu'ammar na aiki ne a nan Air force Aviation da ke Zaria, Mu'ammar dan zafin kai ne, Shi ya sa abu a gaba to sai ya cimmai, in ko ba haka ba ya shiga damuwa, Tunda ya iso Zaria ya bar Yar baiwar Allah ita kadai ciki, ita kadai ta kwana, ya tare gidan wani Abokinsa Ahmad, don shi gani yake ba zai iya kwana gida daya da Islahulkhair ba, don ya na mata tsana me zafih, toh su Amar ga shawara idan zaka k'i mutum ka k'i shi saisa saisa don ba a san wanda gari zai waya ba. Suraj Umar Zailani dan shekara 27 a dunia, Matashi ne dogo kyakyawan gaske, ya Karanta Architecture, Yana aiki ne a nan kano mostly Gwamnatin kwankwaso ta tsaya mai wuri zanen Tituna masallatai, makarantu d.s, Suraj ya qware ta fannin zaneh, ko mutum zai zana shi tsaf, Suraj na da kirki yana da haquri amma abu kadan ke bata mai rai baya son raini ko kadan, Arch. Suraj kenan Angon Bilkisu er baba labaran. Da Daddare 9:30pm;; Samir ne ya paka motarsa ya fito, da take away a leda ya yi hanyar parlonsa, zaune take gaban kofar parlorn, gashi dare ya farayi, kawai ganinta yayi zaune, sai da ta bashi tsoro, ita kuwa tana ganinshi ta miqe da sauri, Ta nufo shi ds niyyar rungumsshi, Ya gimtse fuska tare da matsawa baya, Bigbrosamir, tunda safe ka bar gidan nan, ina ta kiran ka ka qi dauka qarshe ma ka kashe wayanka, ina taji tsoro nikadai a gida, be tankata ba ya raba ya bude kofa ya shiga ciki, ledar take away din hannunsa ya ajiye kan dinning, ya shigewar sa dakih donyin wanka. Zuwa tayi ta bude ledar taga kazah ce da Fresh Yoghurt, ta nufa kicin ta dauko plate tayi dakin samir dashi, tym din ya fito wanka ya na tsane kansa da dan qara min hand towel, dagowan da zaiyi ya ganta tsaye, dan guntun tsaki ya sake, tace bigbrosamir ga abinci kazo muci, kamar ba zai tankata ba yace ni na koshi, wannan nakine, Tace Allah ko? Toh nagode, ta zauna kan kujera kamar zai yi ihu don takaici, ya daure dai yace Amira i want to dress up, ba tare da ta kalleshi ba tace go ahead mana, m ur wife ryt? Ganin idan ya biye mata ranshi zai baci ya zira jallabiyanshi ya koma toilet, ta gama cin kazarta ta sha yoghurt ta kai plate kichin, ta shiva dayan dakin ta yi wanka tare da sa nughtgown, ta koma dakin Samir, har ya kashe wutan Dakin ya kwanta yana latsa waya, Gadon ta haye, da sauri ya miqe tare da kunna side lamp, ya daure fuska, ke Amira Lafia?? Tace menene bacci zanyi, Yace ki fita mana ki koma dayan dakin, tace jar uba, ni kadai ral cikin dakih, to ba zan iya ba, ka fita ka barni ni kadai na haqura ynz u expect me to sleep all alone? Hell No, wlh nan zan kwanta, samir kamar zaiyi hauka don takaici, a hankali yace Amira pls ki fita, tace lallai bari ma ka gani, ta gyara kwanciyarta kan gado, Cikin daga Murya yace Amiraaaa ta dago sosai dan taji muryan sa kamar me shirin yin kuka, yace please leave, tace nifa na gaya ma i aint going anywhere, ya miqe ya dauki pillow yace Please Amira dont make me hate you 2⃣3⃣ 🏡GIDAN GANDU🏠by 💕Biebee Isa💕Gidan Gandu🏠by 💕Biebee Isa💕 by 💕Biebee Isa💕Biebee Isa💕Biebee Isa💕Mamaki ya rufe Amira, Toh me yayi zafih haka? Ya samir me na maka haka har kana kira min kalmar Tsana? Be tankata ba ya dauki pillow ya bar dakin parlo ya nufa ya kwanta kan doguwar kujera, Ba ta san lokacin da ta fashe da kuka ba, a rayuwarta yau ne a ka taba mata abu ba tare da ta rama ba, yau ne aka mata abu ta tsaya tana kuka ba tare da daukar mataki ba, in banda Yasamir wa ya isa ya takata haka? Waiyo Allahnta, ya zatayi? Ga wani son samir da ya shigeta farat daya, haka ta dinga rubzar kuka har bacci yayi awon ga ba da ita. Kaduna Ko da Jawas ya iso gidan karfe 10 da wani abu, xaune ya iske hakimar wato Fadila a parlor ta na kallon Series din nan na "Married Again " Dakinsa ya wuce straight ita kuwa bayan sallamar da ta amsa mai ko kallonshi ba tayi ba. Ta cigaba da kallonta tana kada k'afa daga bisani ta miqe tayi kicin don dafa indomie. kichin din shaqe yake da kayan Abinci ko mi akwai don Tsoho sai da ya cika su da komai na abinci kama daga kayan miya, nama, kaxa, kifi, kai harma da o tolotol o👻 Lagos Shigowar sa kenan Gidan ya nufa dakih, ka sancewar gidan 1bed room ne amma dakin me girma ne, kwance take kan gado tana hawaye, ya cire bakih ya kirata yace Hanifa, hanifa, banza tayi dashi kamar bata san yanayi ba, da yaga ba zata kulashi ba ya shigewarsa toilet din dakin, ya yayi wankansa ya dauro Alwala yayi shafa'i da wutr, yazo ya chanza kaya zuwa na bacci, ya hau gadon ya kwanta, kukan ta takeyi ba ta fasa ba, Shi filazal baya son kukan mace, ya daure dai ya ce Hanifa donAllah kiyi shiru, bana son kukan nan naki, ko me yayi zafih maganinshi Allah, kiyi haquri mana, cikin tsiwa ta miqe tace kai mallam saurara min, ina ruwan ka da kuka na? In kaji zafih ka sakeni, yayi murmushi yace banji zafih ba Allah ya baki haquri, have a Sound sleep, yayi kwanciyarsa tare da juya mata baya, takaici ya sa ta saki wani kukan da qarfi, shi ko yayi saurin runtse idanuwansa, da yaga taqi shiru pillow ya dauko ya fita sitroom, tsoro ya mamayeta kamar tace ya dawo, Amma taurin kai da irin zuciyar Hanifa ya sa ba ta nuna komi ba, amma harga Allah tana tsoron kwana dakin nan ita kadai, haka ta kwanta rabin ido daya a rufe rabi a bude (lol) Zaria Taci kuka har ta qoshi, tayi sallah ba adadi, a tsoroce take, tun jiya rabon da taga Mu'ammar, haka ta kwana cikin tamfatsetsen gidan nan ita kadai, hankalinta ya gama tashi, da qyar ta dafa Taliya tacih, ta kira Wayan Maysah a kashe, ta kira fadila ta ci saan wayar ta kunne yake, amma ba a dauka ba, kasancewar wayar na chan dakin ita kuma fadilar tana parlor tana kallo, wani kukan ya subuce mata, gashi ba ta san kiran Umminta don kar hankalinta ya tashi, Dare kuma Ya Tsala, haka Islahulkhair ta kwana tana kuka, da ta ga kanta na neman Bugawa sai ta dauko Alkurani mai girma ta shiga karatu. Shi ko Mu'ammar na nan Gidan Abokinsa Ahmad, ya ma manta da yana da wata mata a Gida. Kano Ya shigo da sallama ta na jinsa amma tayi biris dashi, ya qara doka sallama tayi banza dashi, qarshe ta hau karkada kafarta, da qarfih yace keee bilkisu, ba ki jin ana sallama ne? Ko ba ki iya amsawa ba? Cikin tsiwa ta kalleshi ta haraeshi, tace naji kana sallama, na iya amsawa, ban dai ga damar amsaka bane, fuuu ta wuce dakinta, zuciyarsa tayi k'una, har ya bita dakin don ya lakada mata na jaki, sai zuciyarsa ta haneshi, ya danne zuciyarsa, yayi kwafa. Ita kuwa tana shiga dakin ta dinga murna ta bakanta ma Suraj, haka ta dinga kullah yanda zata dinga chuzguna mai har sai ya saketa kafin Hajia babba tayi na ta aikin. Abuja Da Safe, Ya kaisu Aunty Nuratu Airport, bayan sun dade kan Maysah suna mata nasiha don sun lura da take taken zaid, tasha kukanta, haka suka rabu, sai da yaga tashinsu kafin ya wuce National Hospital, yaje yayi reporting dama suna expecting dinshi, aka bashi office da tag dinsa a rubuce an sa Dr. Z.M Zailani Nan take ya fara ganin patients cikin kwarewa, yanda kasan bature haka yake tafiar da Alamuransa. Har misalin karfe hudu, ya tattara yana sa yanasa yayi signing out ya tafiarsa. Hotel din da ya sauke Badiyya ya nufa, ya kirata a waya, ringing daya biyu ta dauka, yace gani na iso,sauko qasa, a yangance tace ba ni kadai ce ba fa, yayi jim chan yace ke da waye? Tace ni da mamana, shirun ya qarayi chan kuma yace yaushe tazo? Tace yau din nan, to ku fito muyi ta tafia, bayan mintina 12 sai gashi sun sauko, ta side mirror ya hangosu, ko wannensu dauke da akwati trolley, maman baddiyya ta qi amincewa ta tsufa, irin shegun matsatsun kayan nan ke jikinta, fuskan nan tasha coiling ga gashin doki a kai, wannan shine like mother like daughter. Kwankwasa mai tayi yayi winning glass da murmushi a fuskanta tace Oga a bude Booth ko?

Chapter 6 of 20