Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ai ta soke shege balle babu, tace Babu Ya Zaid, yace good, ki shirya ynz, tace a shirye nake sai dai brkfast yace dont worry zamuci a chan, ta juya tace ok bari na kira Aunty Badiyya, da sauri ya fincikota yace dont ever mention her name to my face again, ya saketa ya shige daki a fusace, be son ganinta ko sunanta be sonji, dukda suna zaune cikin gida, shi sakinta ma zaiyi, ya dauko giyarsa cikin firij zai bude, da sauri Maysah ta yi sauri isowa ta amshe gwangwanin, ta kalleshi ta girgiza kai, tace its too early Yazayd, na shirya muje koh? haka kurum ya ji zuciyarshi tayi fes,Zabin tsoho ta wanke mai duk wani baqincikin da badiyya ta sashi,shi ya san ba sonta yake ba, amma kallonta ma sashi farin ciki yakeyi, ya ce Muje Rumah, murmushi ta sake, yace me sa idan nace miki Ruma kike murmushi? Tace saboda Tsoho kadai ke kirana da sunan, Yayi murmushi shima yace kice mazajen ki kadai ke kiranki da sunan, koh? Ta sa hannu ta rufe fuska, ya miqe tare da riqo hannunta, oya muje Zabin Tsoho, ta kalleshi tayi murmushi, a ranta tace nakusa Zama zabinka. Akan idon badiyya suka fita, hankalin ta ya tashi, har ynz jikinta a kumbure yake, da sauri ta lalubo wayar ta ta doka ma Bokanta kira, ya na dauka ya fashe da daria, dama jiran kiranki nakeyi don na san dole ki kirani, cikin tashin hankali tace boka, na gama aiki, aikinm ya karye, jiya zayd dukan kawo wuqa ya min da mahaifiyata, ya kuma korata, kuma yanzu kan idona suna fita da matarshi, ka taimakeni, boka ya fashe da daria, yace ai ba wani taimakon da zan miki, ni na karya asirin da na ma Zayd, ke duk asirin dana yi a rayuwata sai dana karyashi, sbd mutuwata nake jira, banda lafia kuma nasan mutuwata na kusa, taimakon da zan miki be wuce na ce miki ki je Asibiti ki fara neman magani, dif ya kashe wayarsa Badiyya ta shiga juya maganganun Boka, abun da ta ka gane shi ya karya Asirin Zaid amma ba ya ga nan ba ta gane komai ba. Duk inda Zaid yayi da Maysah na gefenshi, sunyi kyau matuqa, kallo daya zaka musu kasan sun dace da juna, sai tambayanshi akeyi Dr. Zailani, who is she? Kai tsaye yake ce musu she's my wife.. Kaduna Ya na dawowa ta sha gabanshi, tace wai meye haka? Meyasa kakeson aiko min direba? Mu kwana gida daya amma ka na baqin cikin yi man magana? Nidai in har ka na son wani abu daga gareni ni zaka fada mawa kar ka qara aiko min direba, bakinta ya matse da karfi,ta sake ihu, yace ba na hanaki rashin kunya ba? Ni tsaranki ne? Kika qara min haka sai na lallasa ki cikin gidan nan, ya jefar da ita kan kujera, ta shiga murguda baki tana matsa. Kwallah, a ranta kuwa cewa takeyi na tsani wannan Jawad din. ****** Misalin karfe 12 da rabi na dare, Jawad na zaune na shan cofee yana rubutu kan dining, fadila dake bacci a dakinta taji kamar an duro ta windonta, ta miqe ta leqa, hantar cikinta ta kada sakamakon wasu da ta gani su 2 zuwa 3 ba ta tabbatar ba dai, da bindigogi a hannu, cikin kidima ta wawuro wayarta ta rasa wanda zata kira, kawai sai ta danna emergency number 911 dukda ba ta da tabaccin yana aiki, cikin saa aka dauka cikin rudu amma a hankali ta ke sanar dasu abun da ta gani, wani gari take? Tace kaduna, ta ba su full address, sukace nan branch din lagos ne amma ynzu zasuyi alarming kaduna As soon As possible, kyarma takeyi bata son yin kwakwaran motsi sujita, tana kallo suka daure maigadi, suka nufo parlorn. Ji yayi ansa mai wani abu kamar bindiga akai, ya dagi da sauri, Inalillahi wa ina ilaihir rajiun yace, ya daga hanayenshi sama alamar surrender, yace kar ku kasheni, zan baku kudih wlh, daria suka fashe dashi, we dont need ur money rich boy, all we need is ur life, but before den sai ka dauko mun signed contracts din da zakayi a Niger Delta, cikin Jawad ya duri ruwa, yace pls lets talk dis out, buge mai kai yayi da bindiga, yace zaka dauko min ko sai na tarwatsa kanka da harsashi na? Jawad yace Aa, Alamun jiniyar mota na waje yaji, ya leqo cikin kidima ya ce boss, ga masu bakin kaya, ya dago da mamki yace ya akai suka san muna nan? Dd u call anyone? Jawad yace ai bansan da zuwan ku ba, kai da waye a gidan nan, da sauri yace ni kadai ne, a zuciyarshi yana me roqon Allah kar fadila ta fito, yes boss dama oga yace shi kadai ne be da mata, kawai mu kashe shi mu gudu kafin su shigo, ji sukayi ance we are advicing u to put ur guns down, ur hands behind ur heads, come towards us slowly, u try to make a wrong move we fire, you are surrounded, i repeat u are surrounded, a hankali sukayi yadda polisawan sukace suka fita a hankali, signal dayan yayi suka arce a guje, babban police din yace hold ur fire, no one shoots, we need dem alive nan suka bi su a guje, tuni suka dire, polisawan suka bisu. Ya jawad ya yu hanyar fita don ganin meke faruwa, Tana fitowa ta ga wani ta window yayi saitin bayan Jawad da bindiga, da sauri ta rugo gunshi da karfi tace Yajawaddddd, juyowan sa yayi daidai da harbin, jin harbin bindiga yasa sauran polisawa sukayi gurin da sukaji harbin, Ganinta yayi kwance jini ya malale wurin da karfi yace Fadilaaa ya rugo da gudu ya tsugunna gaganta ya tattaro ta jikinshi, yana kuka yace stay with me fadila, dont leave me please, i got u, jini na bulbula daga bakinta da qyar tace Yaa jaawaadd dif ta dauke, cikin tashin hankali da karfi Jawad yace Someone Help!! Ambulance! We need an Ambulance! _Bibilicious Biebee_ 5⃣2⃣ 🏡GIDAN GANDU🏠by 💕Biebee Isa💕Gidan Gandu🏠by 💕Biebee Isa💕 by Biebee Isa💕Biebee Isa💕Da gudu wani polive ya shigo, yana tambayan jawad sir are u okay? Cikin tsawa yace we need an Ambulance u stupid idiot, cant u see? Da sauri poloce din ya kira Ambulance, cikin mintunan da basu wuce Goma ba sai ga Motar taimakon Gaggawa, akai akai jawad ya matsa a dauki fadila a sata cikin mota fir yaqi sai dai shi ya daga abarsa ya kai mota, a motar ma tana rungune dashi har suka isa asibitin 44 dake kaduna da sauri akayi da ita Accidents and Emergencies, aka amsheta, Dr ya ba Jawad wasu forms yayi signing zaa ma matarshi operation don ciro bullet din da ke cikin kafadarta, da sauri ya sa, aka ja gadon fadila bayan an sa mata oxygen akayi theatre room da ita, jawad na biye a baya, zai shiga dakin wani security da ke tsaye bakin kofar yace sir u cant come in, jawad yace try to stop me, ya raba ta gefenshi ya shige, nurse na ganinshi tace sir, u cant be here wani hararan da ya wurgi nurse din dashi ya sa ta matsa mai, Ganin haka Dr yace let him, nd lets get to work. Haka suka duqufa aiki kan fadila, jawad kuwa sai Addua yakeyi Allah ya tashi kafadun matarshi, she cant die. Maiduguri Isowarsu kenan, straight dakin Mamanshi Aunty Nuratu yayi da ita, bata tunanin ta taba shigowa sashen, duk sai taji kunya, Hanifa ta gaishe da Aunty Nuratu da ke gyaran gadon da zayyad zai ajiyeta, ta amsa don ba ta tuna ranar da Hanifab ta gaisheta ba, sannu ya kafan ta amsa, Zayyad ya shimfideta kan gado ya fita yayi sassan tsoho, tsoho da kansa ya zo gaida hanifa a dakin Aunty Nuratu, yayi mamakin yadda kafar ya kumbure, ya yi umarni da Baba Hassan da ya kira me dorin kafa. Har gida akaje dauko me daurin kafan, hajia babba ta riga ta gyara dakin da Hanifa zata sauka, sai ji tayi ance sun iso har an kaita dakin Aunty Nuratu, Ashar ta sake tace ba zai sabu ba, ta fita Aunty Abida Maman Hanifa ta rufa mata baya sukayi sassan Baba Hassan, Masifa ta so saukewa ganin tsoho tsaye ya sa ta yin shiru, Zayyad ya gasiheta ta kalleshi a gyatsine ta amsa, ya gaida aunty abida ta amsa, Tsoho yace bari ya koma sassan sa, tsoho na fita Hajia babba tace kai dan wulaqanci, ban taba ganin mugu kamar ka ba, kaje ka aje yarinya chan qasar kabilu ba uwa ba uba ko leqen gida ba ta zo ba har watanin 8, don mugunta, ba ka kula da ita, sai da kayi sanadiyar turgudewarta zaka kawo mana ita nan? Toh ba zaiyu ka ajiyeta nan ba dakina zan tafi da ita don ta samu kulawa, ba Zayyad ba har Hanifa sai da taji ba dadi, yace kiyi hquri hajia, bari a maidata chan dakin naki ta juya fuuu, tace da dai ya fi, Aunty Nuratu na zaune ba dai ta tanka ba, Maman hanifan ma ba ta ji dadi ba, sumsun tavi bayan mamanta, hanifa ta kalli mijinta ciki tausayawa, a ranta tace bawan Allah, haqurin shi yayi yawa, yace hanifa bari akai ki dakin hajia ko? Batace komai ba, ya dagata sama, a hankali tace kayi haquri Yaya, murmushi yayi ya fita da ita. Ko da me gyaran yazo dakin hajia babba akayi dashi, yace zaa ja kafan a gyara, zayyad na gaban Matarshi, hajia babba tace kai dalla mallam zoka fita zaa ja mata kafa, kayi wani kane kane, hanifa ta kasa haquri tace haba hajia, me yayan ya tsare miki ne eyi? Tun dazu na yi shiru na kyaleki? To ba inda zaije ta qarashe tare da murguda ma kakan nata baki, bakih bude hajia babba take kallon hanifa, ita da ta san hanifa ta tsani Zayyad amma gashi ynz sai kareshi takeyi, Zayyad yayi murmushi ya shafi kumatun hanifa yace bari dai na jira a waje, hanifa tace no yaya, hold me pls, Zayyad ya kalli hajia babba da har ynz bakinta a hangame yake sbd mamakin hanifa, yace ma mai gyaran bismillah, mai gyara ya kama kafan hanifa ta kwallara ihu tare da janye kafar, har cikin kwakwalwar shi yaji ihun nan, hajia babba ta kalleshi tace ai sai ka riqeta kar ka min tsaye a ka. Zayyad ya zauna ya riqe hanifa, me gyara ya cigaba da jan kafar, shi ko harda hawaye don jin yadda hanifa ke ihu. ******** Suraj da Bilkisu sunzo Maiduguri don duba hanifa, hanifa da bilkisu suka kulle a dakih suna firan yaushe gamo, suna ba juna labarin rayuwarsu bayan aure, Bilkisu tace lallai hanifa dole ki sauko ki nuna ma Yaya zayyad so a zahiri da badini, don ya yi hquri dake ba kadan ba, idan kuma kikace zaki tsaya jan aji wannan fatitin zai aura, a maidaki yar kallo, hanifa ta ja numfashi tace wlh Bilkisu na yi nadama, duk abubuwan da nake mishi be taba fisho dani ba, Ni so nake mu koma gidanmu, tunda naga tsoho da mamana ban marmarin gida, naji sauki wlh, Bilkisu ta yi daria tace kamr kinsan for a 2nd bansan yin nesa da Yasuraj, don wlh Ya suraj ya qware a iya love, suka chafe tare da kwashewa da daria. Cambridge England Shopping tazo ita kadai don zaineema na lectures, ta gana siyan kayab da suke buqata ta fito wajen Mall din, ta na tafia da ledojin ta a hannu tana jiran Cab, Ji tayi ance Islah don girman Allah ki saurareni da sauri ta juyo ta kalleshi, kallo daya ta mai ta ga ya rame ya yi duhu, ganin bata ce komai ba ya sashi fara magana kamar haka; Dalilin da ya sa na zo london shine ina so na manta da Hanifa, ina so cireta a raina, don nayi mata zazzafen so, sbd son hanifa da nakeyi har pricking fingers din mu mukayi muka sha jinin juna, its hard for me to forget her easily, ganinki kuma na bata raina i dont want to hurt u shisa na bar Gidan don i dnt knw wat i will do to u idan ina ganinki a matsayin matata, shisa na bar kasar ba tare da na gaya ma kowa inda zani ba,don kar a tilasta min na dawo, i chose to come to London dan na saba da garin, i chose to be alone just to forget hanifa nd come back to u, mu fara rayuwar mu mu biyu, nd wallahi i forgot every single thing abt her last 3 months, i taught my self how to love u sincr den, ynz kece nakeso, kece zuciyata ke tsanannin so,Son da ban taba ma yi ma wata ya mace, wlh ko son da nayi ma hanifa be kai kwatan wanda nake miki a yanzu ba, wlh lokaci daya sonki ya shige ni, kece nakeso ki zama uwar yayana, i want to spend d rest of my life with u Islahulkhair. Tun tuni na siya return ticket to Nigeria, flight ina in d next two weeks, i wannid to come home to u, i want us to start a new life, nd unfortunately i saw u here, Islah pls ina fatan kin fahimceni da dalilaina, Islah da idanuwanta sukayi ja, ranta a bace, Mu'ammar din nan ya ma gama raina mata wayau, tsaki ta buga ta juya ta cigaba da tafia, ya biyota a baya haba hanifa, kar dai baki gamsu da maganganu na ba, ya riqota tace let go off me, ka raina ma kanka hankali, u Stomped on my pride d moment u left me, i dont want nythn to do with u jus lemme be pls, girgiza kai yayi yayi saurin rungumeta ya na hawyae, i cant leave without u, forgive me pls, Islah ta ture shi da qarfi, da gudu ta qarasa gaban motan polisawan dake parke, Mu'ammar ya bita da ido don ganin me zatayi. Ta ce officers, someone's bin chasing me, i dont knw him? He's embarassing me, suka fito suka ce We'll deal wit him, suka nufa amar suka kama shi, daya da ga cikin officers din yace, why are u chasing her? Ya kalleshi cike da takaicin abun da ta mai yace she's my wife, da sauri tace he's lying m not, officern ya kalli Amar yace keep off, yace da Islah wenever he bothers u again u knw wat to do, ta gyada kai tace i will call u ryt away. Good u can go, ta kwashi ledojinta ta yi gaba zuciyarta fal da farin ciki, Amar cike da bacin rai ya juya beson inda yake jefa kafanshi ba, ya nufa titi wurin tsallaka titi ne wata mota tayi gaba dashi, chan gefen titi a kaga Amar kanshi ya bige da wani qarfe, kan shi na zubar da jini, da sauri aka kamshi a ka sa shi cikin mota akan idon Islah akayi komai, taso tayi tafiarta ganin shi ya miqe da kafarsa, amma rashin imaninta bekai nan ba, ta tsaida mota ta ce ya bi bayan motar chan. Abuja Shigowarshi kenan, ya ji wayarsa na kara, da sauri ya ciro wayar daga Aljihu, Jawad ya gani ya dauka, hello jawad?daga bangarensa ya na kuka yace brother m scared? Zaid ya ce me ya faru jawad? Me ya sameka? Yace its fadila, she's bin shot, took a bullet for me, Inallilahi wa ina ilaihir rajiun inji zayd, is she dead? I dont knw, tun qarfe 11 aka fiddota daga theater room, sunce operation din is successful amma har ynz bata farka ba, Bro i cant loose her, Zaid cikin rudu yace Gani nan zuwa, ka kwantar da hankalinka, she's gonna b fine kajih. Ya shiga ciki suka ci karo da Maysah ta fito daga kicin yanda ta ganshi ta san cewa ba lafia,Ya zayd lafya? Yayi dan tsaki, kana yace matar Jawad ce a ka harba, maysah ta zaro ido, Fadila? Yazayd is she alright? Yace shine xanje kadunan ynz, yazayd m coming with u, ya danyi shiru, kafin yace yi sauri ki shirya, we are leaving now. ***** Tana ganin tafiansu ta sakr ajiyar zuciya, ko sallama be mata ba, dama so take ta samu damar fita balle ynz da ta quduri zuwa asibit sbd wasu manyan kurajen da ta gani a gabanta. Ta shirya ta nufi wani Prvt hospital, bata sha wahala ba ta shiga ganin likita, bayan yan tmbyoyin da likita ya mata game da kurajen, har dai ya nemi ya gani, ya sake mata wasu tmbyoyi, likita ya kalleta sosai yana son karantar wani abu a fuskarta, chan kuma ya ciro wata na'ura ya ce zai dan chaketa da allura a yatsa, zai mata test, badiyya ta miqa yatsarta bayan ya sa hand gloves ya dan diba jini tare da sawa kan strip din injin. Bayan wasu mintuna machine din yayi qara, Dr ya maida glass dinshi ya duba machine din ya dago a raxane, ya kalli Badiyya, ya ce Mrs Zaid Zailani, what m abt to tell u is - tace cut d crap n tell me wats wrong wit me, ya tabe baki yace you are HIV POSITIVE... Gidan Gandu 5⃣3⃣ 🏡GIDAN GANDU🏠by 💕Biebee Isa💕 Gidan Gandu🏠by 💕Biebee Isa💕 by 💕Biebee Isa💕Biebee Isa💕Biebee Isa💕Cikin tashin hankali diyya tace HIVn Uwarka? Ni fa ban san iskanci, ta figi jikkarta ta fice daga office din a fusace, gabanta na dukan 3uku, Dr ya dauko File dinta ya kara karanta sunanta ya tsaya yana tunanin. Tashin hankali ya bayyana karakara a fuskar diyya, ta gaza sukuni, wani asibitin ta nufa, ta na zuwa tace amata HIV test, gwajin farko ya nuna tana da cutar HIV, ihu Badiyya ta kurma tare da daura hannu a kai, sai da ta gama kururuwarta kafin ta nemi ganin likita, don neman shawara, haka liktita ya shiga gaya mata abubuwan da zata kiyaye da abubuwan da zatayi, ta fita jiki ba kwari, ta biya chemis ta siya magunguna kafin ta koma gida cike da damuwa... Cambridge England E&A aka kai Mu'ammar don har ynz kanshi na fitar da jini, Dr Miracle ya kalli wanda ya kawo shi yace yayi loosing blood sosai and dole zaayi mai karin jini, yaje ya siyo a blood bank, Orange Negative (O-)zai siyo, ko da yaje siyo jinin baa samu O- ba, mutumin yace a aunashi aga idan jinin yayi daidai da na Amar, ko da aka Aunashi, kwatakwata ba zaiyuwa a dibi jininshi a sama Amar ba, Likita yace dole ake samo jinin da za'ayi transfuse a jikin Amar before he runs out of blood, if he does, he will die eventually, Islah da ta gama jin abunda dr din yace ta qaraso da sauri tace I am (O-) i will b d one to donate the blood, mutumin da ya buge Amar yace nd you are? Da sauri tace Relative, Dr yace ok, d earlier d better, bayan an auna jininta aka jininsu yayi daidai aka dibi leda biyu na jini Islah, kafin aka bata kayan marasa lafia aka kaita dakin da amar ke kwance ya dan samu bacci, kusa da gadonshi aka kwantar da ita don ta huta bayan sun bata madara tasha. aka hada jinin a jikin Amar... Kaduna Karfe 5 ta musu a kaduna straight Asibitn da aka kwantar dasu Fadila suka nufa, Zaid ya kira Jawad ya musu kwatancen dakin, yace Amenity Ward room 11. Ba su sha wahala ba suka gano dakin, Jawad na zaune kan gadon marasa lafiya yana sanaarsa wato kuka, duk ya tattaro fadila da ba tasan inda kanta yake ba zuwa jikinsa, ga rungumeta kamar zaa kwace masa ita, ga drip a hannunta ga oxygen a hancinta, suna turo kofa Jawad yayi saurin xame jikinsa tare da fadawa kan Zaid ta fashe da sabon kuka, ita kuma Maysah ta ruga gurin da fadila take kwance itama ta sa kukan, Zaid yace Jawad yi shiru mana, be a man, ya girgiza kai yace Brother, i cannot loose fadila, she cannot die, she took a bullet for me, dat was my bullet, zayd ya matseshi a jikinshi yana bubbuga bayan kanin nashi, gudan jininshi, yace shes going to be fine, InshaAllah, have faith, Allah zai tashi kafadunta, Jawad ya dago cikin bacin rai yace i promise u whoever did dis to my wife is going to pay, Zaid yace ya isa haka jawad, ya sakeshi ya qarasa gun gadon fadila, tare da yin dube duben su na likitoci, Zaid yace kar ka damu, bacci takeyi, kai kawai Jawad ya daga mai, Maysah ta ce Yaya Jawad Allah xai bata lafia, zata warke, u two will live to see ur kids, be san sanda murmushi ya kubuce mai ba, yana tunanin kalan yaran da wannan ma bakin tsiwan zata haifa mai. Da sauri ya qarasa kan gadon ya riqo hanunta yace fadila, i know u can hear us, wake up, i need u, i miss u, i missed everything abt u.. Zaid yace i dont think ko lunch kacih, yace rabona da abinci tun dinner din jiya, hankali na a tashe yake, Xayd yace yanzu Rumah ta tsaya a nan, sai na kai ka gida kayi wanka kaci abinci, kafin mu dawo ta tashi InshaAllah, Jawad cikin d'oki yace ok bro, Rumah bari muje mu dawo ko? Tohm yazayd Allah ya kiyaye Amin. Jawad yace Rumaysa ki kula min da matata, kar kaji komai Yayanah, zan kula maka da ita toh ngd suka fice. Maiduguri Salatin da Tsoho ya rafka ne yasa duk yan dakin zuba mai ido, Zaidu tun yaushe hakan ta faru? Zayd Yace ka kwantar da hankalinka tsoho, jiya ne da daddare, amma ynz har Anyi mata aiki kuma an dace bata dai kaiga farfadowa bane,Nima yau Jawad din ya kirani ya sanar dani shine muka taho da rumah, Tsoho ya ce InshaAllah gobe mu na nan tahowa, Zaid yace tsoho wani tafia zaka iyayi? Duk kuyi zamanku, ba sai kunzo ba, tsoho yace bazai yuwu ba, yau ma don marece yayi ne da ka ganmu amma asubar fari zaku ganmu. Zaid yace toh Allah shi kaimu. Tsoho na aje waya duk suka hada baki gun cewa lapya? Yace yan bindiga ne suka je gidan Jawad jiya har sun harbi fadila, hajia babba ta aza hannu akai wayyo mun shiga uku, Allah ya sa ba su halbi Jikana jawad ba. Tsoho ya galla mata harara. Ya kalli Suraj da Zayyad yace Fadila ce aka harba amma an mata aiki ynz haka suna asibiti, Suraj ka shirya gobe zamuje, kai Zayya ka tsaya da matarka, Bilkisu tace tsoho nima zanje danAllah, yace aa ki tsaya kiyi jinyar yaruwarki, ya kalli hajia babba yace ki shirya ke da Abida da ku zaa tafi goben, Alhaji baka gaya min ya jawad dina yake ba? Tsoho Yayi banza da ita ya fita daga sashenta Yayi sashen Hajia Ama, ya ko ci saa Aunty Hassana na zaune, yace Hassan ina Aliyu? Tace barka da maraice baba, tun da ya fita be dawo ba, yace ina Aishalle? Tace bari na kirata ta miqe ta kirata tazo ta zauna, wani tsautsauyi ya faru a kaduna jiya daddare, Dam gaban Aunty hassana ya fadi, A ranta tace Allah ka sa ba wani abu ya samu diyata fadila ba, tsoho ya cigaba Yan bidinga suka shiga gidan Jawadu da niyyar kasheshi cikin rashin saa suka harbi Fadila a kafada, Ama da Aunty Hassana suka fashe da kuka, tsoho yace ku kwantar da hankalinku. Xaid yace da sauki gobe zamuje daku gabaki daya. Kar ku tada hankalinku. Sai da ya kwantar musu da hankula kafin ya miqe ya shige Sassan Umma hajja.. ***** Asubar fari suka dauko hanya mota biyuu akayi da babba da karama, karamar motar baba hassan ce, shike tuqa tsoho, hajia Babba da hajia Ama sai Umma Hajja, ba yanda basuyi da tsoho kan yayi zamanshi ba fir ya qih, Babban motar kuwa bus ce ta Gidan Gandu. Sai da laasar suka samu suka iso. Zaid ne ya je ya dauko su a Kawo, suka iso Asibitin. Yau asibitin 44 ta shaida da zuwan Familyn Zailani, Straight dakin suka nufa suka shiga da Sallama, Maysah ta ruga da gudu ta rungume tsoho cikin jin dadi kafin ta shiga gaida kakaninta da uncles and aunties. Ganin iyayenshi da kakkani be sa ya xame daga rungumar da ya ma fadila ba kan gado, Tsoho yace Sannu jawad ya me jiki? Ya fashe da kuka Yace tsoho ba sauki har ynz bata farfado ba, baba hassan yace Ai jawad zata farfado, Allurar ce bata sake ta ba, Zaid yace na gaya mishi ai, wasu idan aka musu anaesthesia sai bayan kwanaki 3-4 suke farfadowa. Jawad yayi saurin cewa Allah ya sa ta tashi ynz suka amsa da Amin, Tsoho ya umurcesu da suyi mata addua, nan kowa ya dinga ma fadila addua, suka shafa, Jawad ya labarta musu abun da ya faru, ya hada da cewa tsoho wlh ina son matata bana so ta mutu, ta cece rayuwana, ta mutu wlh nima sai na bita, karaf hajia babba tace ja chan sakarai, don me zaka mutu? Alhamdulilah tunda kalau kake, Ni na bi na tashi hankali na duk zatona barayin suna maka wani abun ko baka da lafia, wlh dana san haka ne da nayi zamana, wani muguwar harara jawad ya wurgi kakarsa dashi, ran tsoho ya baci ds jin magangannun hajia babba zai yi magana sai dai yayi shiru, Jawad ya hade rai tumuk ya kalli Aunty Abida yace mom get dis woman outta here i dont want to see her, Aunty Abida ta harari Jawad, tace shes my mother, mom rwly? Bakiji me take cewa game da matata ba? Dint u here me say she took a bullet for me? Mom da yanzu nine fa a kwance kila na mutu, sakkayar da zaku yi ma wacce ta ceci raina kenan? Dis shud hav bin me, she doesnt deserve dia at all,Jikin anty abida yayi sanyi, ta kalli fadila cike da tausayawa lokaci daya taji son fadila a ranta, ta ji dadin da danta ya auri jaruma kamar fadila, Hajia babba zatayi magana Zaid yayi saurin janta yace muje daga waje kakus, tace yauwa don na gaji da tsayuwa, na sha hanya a banza muje ka ban labarin yar gayu, ya ma sunanta? Dif zaid ya dauke wuta ya yi kamar be taba daria ba, ya kalli tsoho yace Tsoho ina jin ya kamata kuje masauki, don dr yacr patient bata son hayaniyya, ya'll shud get going, tsoho yace haka ne, muje masauki Gobe ma dawo, daya bayan daya suka fita, aunty abida ta matsa kusa da fadila ta mata kiss a goshi tace Allah miki Albarka nagode, jawad kadai jita yayi murmushi Yace thanks mom, ta shafi ganinshi tace take care of my daughter inlaw, yayi smile sosai yaji dadi yace i will mom. Ya kalli Aunty hassana da ta tsaya ta kurawa diyarta fadila ido tana dan hawaye, yace Mummy m so sorry, wlh bansan da zuwan fadila gurin ba, duk a zatona tana dakih, forgive me mummy, aunty Hassana ta girguza kai tace ba laifinka bane jawad, Allah ya riga da ya qaddara

Chapter 15 of 20