Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ta kai kanta kasa don kunya, duk sukayi daria, Zaid da kanshi ya kai kanshi kasa gurin da Jawad ya ajiye motarsa, don wani karfi yazo mai, dama fargaba ce ta maida shi haka. Suna isa gidan Jawad ya zube a parlo, Maysah ta yi hanyan kicin tace bari ta hada abinci, Zaid ya shige toilet don ramuwar wankan da baiyi ba na kwana 4... Indomie ce ta dafa musu, haduwa sukayi kan table duka, zuba ma Zaid ba tare da ta kalleshi ba, tundazun yake son karantar ta, fir taqi yarda su hada ido, Fira sukeyi Jawad na basu labarin dawowan Mu'ammar, Xaid yace muma dai gobe za muje Maiduguri, Maysah ta dago kanta suka hada ido aikuwa idon zaid akanta, da sauri ta kawar da kanta tana murmushi. Wayar Jawad tayi qara, yace ohh god, ya dauka, yace hello baby, m so sorry, fadila tace shine kaki nemana koh? Jawad ya shiga bata haquri, yana wani narkewa yana shagwaba, yana fada mata how much he missed her, baki bude Zaid da Maysah suke kallonshi, ji yanda yake magana kamar mace, Jawad ya kalli zaid da matarshi ya murguda musu bakih, yace baby bari naje daki, wannan yayan naki da matarsa sun sa min ido, Zaid ya kaimai dukkan wasa, yace kato da kai kana shagwaba, jawad ya sa handsfree yace baby kinji bros nace min kato koh? Fadila tace ravu dashi baby,ai kasan ka fi jariri zama baby koh? Zaid ya bishi da gudu shi kuma ya shige dakih yana daria. Maysah ma darian ta ke, Zaid ya tako har gabanta ya na mata wani irin kallo, da sauri ta tashi ta fara hada kwanonin da suka bata, Zayd ya riqe hannunta ya juyo shi gareta, ya hada idanuwansu, Zabin Tsoho kin qi kallo na, kin ki nuna min farincikin da kike ciki na rashin samun cutar nan. Yace i am so sorry for pushing you away, i dint mean to hurt u, but i want u to understand that its for ur own good. Maysah tayi murmushi tace na fahimceka va sai ka min bayannin komai ba, Zaid yace dole na fahimtar dake, don kar kiyo tunanin wani abun daban. Yanzu gobe zamuje na kaiki gurin tsohonki koh? ta gyada kai, tace nagode, Zaid ya hadeta da jikinshi ya rungumeta tsam, a hankali ya rada mata a kunne yace thank u for everything, i pushed u away but u stayed, kinsan matsala na amma kika yi kasadar zama dani, u were willing to damn d consequences nd take d risk, i cannot afford to loose u, Zabin tsoho i cannot live without u, U are a Blessing to my life, I love you Rumaysah, Maysah da hawaye ya gama wanke mata fuska, ta qara rungumeshi tsam, farinciki take tayi, tana gode ma Allah.. A rannan ta ga soyayyah a wurin Zaid har ta na ta mamakin dana Zaid yana magana? Maiduguri Motarsu na tsayuwa fadila tazo ta rungume Jawad shi kuna ya dagata sama, baby i missed u, Zaid yace ku dai kuka sani, da sauri Fadila tazo tana dari Yazayd ina wuni ya amsa yace sai ynz aka ganni? Tayi daria ta rungume Maysah, tace sannu da zuwa Maysanmu tace yauwa Eleerhnmu,Baby zo ki cire mun wani abu a ido da sauri fadila tayi kan Jawad tana sannu muga idon, Zaid ya kalli Maysah ya girgiza kai yace Wadannan koh? Tayi daria, Handbag dinta zata dauka Zaid yayi saurin dauka, ya rataya shi a hannunshi, Sannan ya juya gun fadila tace ke da mijinki ku kwaso mana kaya idan kuna gama love din, ya kama hannun maysah ya riqe, tace Yazayd ka bani handbag dina, ya kashe mata ido yace come nd get it, tayi murmushi, sukayi hanyar Sasshen tsoho hannunsi riqe da juna. Sukayi Sallama. Tsoho ya tashi ya hade su biyu ya rungume yana hawayen farinciki, Zaid yace tsoho naji jikinka da zafih, lafia? Tsoho yace kai tafi chan, kalaw nake zaka ja min wani zafin jiki. Zaid dai ya share, suka zube kasa suna kwasar gaisuwa... ****** Su duka 12 su na zaune gaban Tsoho, Kallo daya zaka ma Tsoho kasan cewa yana cikin farinciki, murna, da Annashuwa. Tsoho yace Alhamdulilah naji dadi, kun bani mamaki, ina mai Alfahari daku, Ina mai farin cikin ku nawa ne, Da farko zaku ga kamar tsana ce ya sani hadin auren ku da waenda kuka ki jini, ko ku ka tsana, toh ba haka bane, Na yi hadin nan ne don sama muku dauwamamen farinciki tsakaninku, Matayenku sune gatan ku, sune abun Alfaharinku, sune Rufin Asirinku, ya nuna Mu'ammar yace matar da ka tsana kamar me itace ta zama me ceton ranka don jinin jikinta ta baka to Islahulkhair itace GATANKA, kai kuma Surajo Bilkisu ta tsare maka kanta da rayuwar aurenta duk da tsanar da take maka amma hakan be sa ta kauce hanya ba, ka ga kuwa itace abun ALFAHARINKA, kai Zayyad na san kai ba ka zafafa abun ba tun farko, ka yi haquri ka riqe matarka da mutunci, baka ta ba kawo kararta ba, ka shanye duk wasu bakin cikin da ta ke dasa maka, ni ina alfahari da kai, sbd duk cikin zuriyata babu mai sauqin hali kamarka, ta dalilin haka yasa Allah ya jarrabeta da sonka, gashi kuwa yanzu son ka kamar ya haukatar da ita, ya kalli Hanifa duk sukayi daria, Tsoho yace Hanifa Zayyad ne NISF HAYAT dinki, ya kalli Amira yace mutane da yawa sun dauke ki mara lafia, sbd hallaiyarki ta neman magana, fada, da rashin ta ido, ni nasan ba haka kike ba, nasan Jikata mai hankali ce, nasan ke me ta ido ce, na san ke me son a zauna lafia ce, Shi ya sa na baki Samir, Don nasan shi yafi kowa sonki a da har ma a yanzu, shi zai kula dake, Samir shine HABIBI na gaskia. Ya kalli Jawad yace Bayan aurenku sai na fara tunani anya banyi gangancin hada abokan fada aure ba? Mata da zafin kai take, miji da zafin kai yake, tuni na ke kasa kunne naji an kirani ance daya ya halbe daya, nan ma akayi daria, amma sai labari ya sha bambam, wai ashe kawar fada ce ta amsar ma abokin fada bullet, kuma a lokacin ba sa shiri, sai ynz na gano cewa bawai shiri ne ba kwayi tun farko ba, kun kasa gane cewa son junanku kuke tun farkon haduwan ku da juna, amma kiyyaya ya hanaku gani, tabbas ku Abin KWATANCE ne ga Al'umma, ya kalli Zaid, yace Zaidu na tsoho, aurenka da badiyya rubutaccen alamari ne, ido na sama ka sabida na san ba a hayyacinka kake ba, aiki sihiiri ke dauwainiya da kai, amma sai na ce bari na bari duniya ta koya ma hankali, na barka ka aureta, ko da ba ka samu ciwon nan ba, amma ka ji jiki, don fargaba ya maida ka wani abun. Tun filazal na san cewa ba wacce ta dace da kai Sai Rumah, abu daya ya banbamta ta duk sa'ointa, Haquri, na san cewa ba wacce zatayi haquri da halayyen Zaid duk cikin saointa sai Ruma, duk da kai baka damu da ita ba don idon ka na kan Badiyya, ta zauna da kai, ta yi haquri da halin da ta tsinci kanta a cikin gidanka, ta ma matarka da sirikarka bauta, ta tsaya kusa dakai da kake tunanin lokacin rabuwarku tayi. Zaid, Rumaisa'u ce _GATANKA_ itace _SIRRINKA_ itace ABUN _ALFAHARINKA_, itace _RAYUWARKA_. Toh farinciki nah shine yanxu duk kun gane abun da nake son cimmawa a farko, kun ga hangen da nake muku? ku kasance masu rufama juna asiri, ku dauki juna daya ba bare a cikin ku, banda nuna wannan ba dan Sashen mu bane to ba ruwana dashi, duk daya kuke a guriba, dukkanku nawa ne, inasonku duka, ku kula da junanku, ku tsaya ma junanku a matsalolinku, a tare suka ce InshaAllah Zamu zama abunda zakuyi Alfahari damu, Suraj yace tsoho Allah ya ja da rai, ya nuna maka jikokin mu, Tsoho yace anya kuwa surajo? Na tsufa da yawa, Allah ma ya sa naga yaranku, suka ce zaka Gani InshaAllah, Jawad yace Tsoho Zabinka Alheri ne wlh,dama ka kara xaba min wata, ka ga sai na ga Alheri masu yawa ta kowani gaba, Fadila ta wurga mai harara, da sauri yace sorry Baby dama Misali nake badawa. Duk sukayi dariya yace mun gode da ziyarar da ku ka kawo mana, ina so ko wanne ya shirya ya koma gidansa da bakin aikinsa zuwa Ranar Jumaa, Allah ya muku Albarka, suka amsa da Amin, duk suka tashi, daya bayan daya suke rungume tsoho, yana sa musu Albarka. Gidan Gandu 6⃣0⃣ 🏡GIDAN GANDU🏠by 💕Biebee Isa💕Gidan Gandu🏠by 💕Biebee Isa💕by 💕Biebee Isa💕Biebee Isa💕Biebee Isa💕fita suka fara yi, Tsoho ya cire bakih ya kira Maysah, yace Ruma in ganki mana, tace to tsoho, Zaid ya tsaya shima, tsoho yace sai a barni da Ruma ko? Zaid ya shafa kai ya fita yasan maganarshi zaayi, Tsoho yace Ruma, ya maganar shaye shayen Zaid? Har ynz yanayi? Ta danyi shiru ta sadda kanta kasa, Tsoho yace na fahimci kina son boye sirrin mijinki, hakan na da kyau, amma ki fada min, Har yanzu Zaid na shan giya? A hankali Maysah tace, Eh tsoho yana sha, balle idan ransa ya baci, sai ya sha gwangwani ya Kai 20, tsoho ya gyada kai yace haka ne, ya ciro wani garin magani a aljihu, yace ki barbada mai a lemu, ko abinci, InshaAllah idan har ya sha, toh InshaAllahu ko kamshin Giya ba zai so ba, balle yayi marmarin sha. Maysah ta amsa cikin jin dadi, tace Nagode tsoho Allah ya qara girma, yace Amin Ruma nah, ya miqo mata jarida yace ansa ki karanta min, ta ansa tace i miss dis, ta shiga karanta mai Newspapern. ******* Hajia Babba ta dura Ashar, tace wallahi ba za ta sabu ba, rabon da naje Hajj tun shekara biyu da suka wuce, yanzu kuma yace da Aishalle zai tafi, ba zai sabu ba, ta miqe kamar zata tashi sama ta nufi Sasshen Tsoho. ****** Zaid ya kalli Tsoho yace tsoho baka da lafia, gaya min, jikinka zafi, ka bari na duba ka, tsoho yace kai zaidu ka bar kira min ciwo, nace ma kalau nake koh? Tsaya ma ka gani, tsoho ya miqe ya na gudu a hankali, yace kagani koh? Zaid dai murmushi yayi ba wai don ya gamsu da abunda tsoho yace ba, sai kawai don kar ya matsa mishi da tambaya, ya ce toh nagani, tsaya muyi hoto, tsoho kuwa ya gyara zaman gilashin zaid ya kashe musu hotuna yana posting. Hajia Babba ta shigo ko sallama babu, tace Alhaji me nakeji haka a cikin gida? Wai Hajj zaku kai da Aishalle? Wannan wani irin rashin Adalci ne? Ta rufe ido sai masifa takeyi, Zaid yace kaka kiyi shiru mana, ki bari zan biya miki Hajj, tace kai dalla rufawa mutane baki, saura sati 2 su tashi wuri ya qure, Wannan rashin Adalcin har ina? Wallahi Alhaji kaji tsoron Allah kar ya tambayeka, hayagagan da ihun da hajia babba keyi ya janyo hankalin mutanen gidan, kan kace wani abu parlorn tsoho ya cika tam, yan cikin gida suka cika parlon, ganin idon mutane be sa Hajia Babba daina yayyafa ruwan rashin mutunci ba, Ran Tsoho ya baci, yace karime mina miki na rashin Adalci? Allah shaida ne ina bakin kokari nacewa na ba wa kowa haqqinsa cikin ku 3, bayan shekaru 2 na ke zuwa hajj, kuma ina daukar daya daga cikinku, ya kalli yan dakin yace ku shiga maganar nan, shekaru 6 da suka wuce da hajjo na tafi, bayan shekara 2 na tafi da karime, bayan shekara2 da wa ya kamata na tafi? Duka dakin aka amsa da Hajia Ama, Tsoho yace madallah, karime gaya min, me nayi na rashin Adalci? ta manta shaf da ita akaje last amma da yake masifa na cinta sai ta fara borin kunya, eh ai dama ka fi sonta, ba tun yau kake min haka ba,Allah dai na kallon ka, Tsoho ya miqe tsaye don zuciyarsa na mishi zafih, gashi be da isashen lafia, ba tu yau ba, daurewa kawai yakeyi don kar ya tada ma Iyalansa hankali, tib ya fadi kasa. Gabaki daya suka yo kanshi, hajia Babba ta sake ihu, zata yo kanshi, Zaid ya fizgota cikin zafin nama ya fitar da ita waje, ya dawo ya kullo kofa, baba hassan ya shiga neman layin Dr Munnir, da sauri Zaid ya shiga ba Tsoho taimakon gaggawa, masu kuka nayi, tsam ya dauki tsoho kamar jariri yayi cikin daki da shi ya shimfideshi kan Gado, ya shiga shafa mai ruwa a hankali, ya sauke gauron numfashi yace yana numfashi, duka dakin sukace Alhamdulilah, Hajia Babba kuka takeyi daga waje, Alhaji na tuba wlh, kar ka mutu da bakin cikina, wlh bazan kara tada maka hankali ba, xan zauna da Aishalle lafia, nayi Alqawari zan zauna da kowa lafia, ku bude man dan girman Allah, ku taimaka ku bude man, kar Alhaji ya mutu, Auren saurayi da budurwa mukayi, muna son junanmu, mutuwa ki fara daukeni, kar ki dauke Alhaji, karki dauken farinciki na, Ta dinga sambatu,duk da suna cikin tashin hankali, hakan be hanasu murmusa wa ba, ana haka sai ga Dr Munnir ya nufo sashen, ganin hajia babba a waje tana ihu ya sa gabanshi faduwa, badai tsoho Zailani ya mutu ba, ya qarasa gurinta yace hajia lafia? Hajia babba da majina ya gama mata facafaca da fuska ta share hawaye tace kulleni sukayi duk suna ciki, DonAllah su bude ka ceto min shi, ba zan iya rayuwa bashi ba, kuran ya mutu sai na bishi, de munnir ya shiga kwankwasawa, Zayyad yazo ya bude mai, wuf hajia babba ta shige tana ina Alhajin, Zayd yace karku bari ta shigo, su jawad suka tattare ta, ita ko kira take, Alhaji kar ka mutu wlh ka mutu sai na biyoka ka yafe min, Dr munnir ya kalle mutan dakin yace he needs fresh air, Baba Gambo yace duk ku fita, Ya tasa qeyarsu Hajia Ama yace Mama mu tafi, ya farfado, ku barshi ya huta pls, duk suka yi hanyar waje, Maysah na tafia tana waiwayen tsoho, Zaid ta ma Alamu da ido, tace take care of him. ***** Dr Munnir zaune gaban tsoho, yace Alhaji donAllah ka daina fadar mana da gaba, u cant be cheating death anymore, ka tsufa, ba ko da yaushe zaka dinga dacewa idan ka fadi kasa ba, wata rana idan ka farfado lafia wata rana ba zaka farfado lafia ba, Wannan ba shine kadai hanyar da zaka samu Zaman Lafia a cikin Zuri'ar ka ba, tsoho yayi murmushi yace Dr kenan, ka yarda dani wannan shine lokaci na karshe da zanyi karyar mutuwa, nayi na farko na ci nasara, wannan ma na ci nasara, don na tabbatar maka da cewa wannan ne hanyar shiryiwar karime, na tabbatar maka Karime zata zauna da kowa lafia kamar yanda tayi Alqawari, tana sona fiye da komai, ganin zata rasani ya sata nadama, Amma InshaAllah ba zan sake yin haka ba, ko don na bar tada ma Zuriyata hankali ba, dis is d last, it will never repeaf itself again. Dr yace Alhamdulilah Allah ya sa hakan ne Sanadiyar hadin kansu tsoho yace Amin. Zaid da ya shigo dakin yanzu ya ji su tsaf, murmushi kawai yayi a ranshi yace wannan Tsoho da dubara yake, ga karfin Hali, Allah dai ya ja da rai, Amma komin banza ya tsoratar da hajia Babba, yayi daria. Su tsoho na ganin zaid sukayi shiru, ba su san ya ji su ba. Tsoho ya wayance da cewa Zaidu je ka kira min kowa, Zaid yace toh Tsoho mai dubara, Tsoho da Dr suka bi bayanshi da kallo, tsoho yace likita ko ya ji mu ne? Dr yace anya? Da kyar ne gaskia.. ****** Hajia Babba kulle cikin dakinta taci kuka har idanuwanta sun kumbura, idon nan yayi luhu luhu abinka da farar mace, nadamar gaske ta shigeta, tunani takeyi tun da aka auro Aishalle da Hajjo ba wacce ta taba ko harararta, ita ke musu tijara da nuna isa, ita ta adabe su, ba su taba mata laifin komai, basu taba tankata ba ko da kuwa zata rufesu da duka, fiye da shekaru 50 suna fama da ita, to meyasa ba zata daina wannan halaiyarta ta zauna dasu lafia ba? Duk sun tsufa, ta son Alhaji na sonta, kuma yana sauke duk haqqoqinta da ke kansa, amma ta danne gaskia saboda kishi, Nadama ya shigeta ta fara istighfari da neman yafiyar ubangijinta. ****** Nasiha me ratsa jiki Tsoho ya shiga yi ma daukacin zuriarshi, na su ji tsoron Allah, su bi junansu, su hada kansu, su zama tsintsiya madaurinki daya. Hajia Babba ta doka sallama a nutse a kofar parlorn, duk hankalinsu ya koma kanta, ta shigo kanta a kasa kamar wata sabuwar Amarya, Gaban Hajia Ama da Umma Hajja ta tsaya ta durqusa gabansu, ta kamo hanayensu tace Aishalle, Hajjo, na dade ina baqanta muku rai, na dade ina chuzguna muku, na chusa ma jinina kiyayyar jininku, na rabasu, na saka tsana mai karfi tsakanknsu, na dade ina shiga rayuwarku, ku yafe min, ku gafarta mun, kuka sukeyi dukkansu, hajia Ama tace kiyi shiru yaya, na yafe miki, Allah ya yafe min, Umma hajja tace bakomai yaya dama ban taba riqe ki a raina ba, kar ki manta ke yar uwa tace, na yafe miki. Suka rungume juna su 3 suna kuka, duk parlorn aka hau kabbara, sunji dadin wannan abu, ba wanda ya kai tsoho farinciki, Hajia babba ta miqe ta koma gaban tsoho, tace Alhaji ka yafe min, nasan duk nice sillar shigar ka damuwa, nice kadai matsalarka, Alhaji ka yafe min, tsoho baki har kunne, yace Karimeta, ai ba ki min komai ba, na san duk abun da kikayi saboda ni ki kayi, kishi na kikeyi, amma kin wanke kanki, Allah ya yafe mana gaba ki daya, uwargida ran gida in baki ba gida, karime ta musbahu mutu ka raba, hajia babba ta rufe fuska wai ita kunya, aiko su jikoki suka hau tafi suna sowa don jin kirarin da tsoho ya ma hajia babba. Nan kowa ya shiga neman yafiyan wanda suka bata ma wa, duk aka yayyafe juna, Kowa murna yakeyi barin ma tsoho da ya fi kowa jin dadi, ko yanzu Allah ya dauki ransa be da fargaban komai, Burinsa ya cika, ya hada kan Zuriyarsa kaf, ya maidasu Tsintiysa madaurinki daya, sai fatan Allah ya basu dauwamamiyar farinciki, ya kara hada kansu, ya barsu tare cikin so da kauna. Allah ya bar Zailani Family. Gidan Gandu 6⃣1⃣ 🏡GIDAN GANDU🏠by 💕Biebee Isa💕Gidan Gandu🏠by 💕Biebee Isa💕by💕Biebee Isa💕Biebee Isa💕Biebee Isa💕 A karshe Baba Hussaini ya rufe taro da addua aka watse, kowa sai murna da farinciki. Yau juma'ah duk sunyi shirin komawa gidajensu, Hajia Babba ta shirya musu kayan miya, kamar daddawa, kuka, kubewa busasshe da sauransu, kowa da kullinshi, Amira tace ai su wlh ba sa so, ai ni da bigbro ba ma shiri da tuwo, so ba abunda zamuyi da daddawa hajia babba ta hararesu, tace ai ke ba a muku abun arziqi, da ke da mijinki kamar ragowan yunwa, Amira zatayi magana Samir yace yi shiru lilsismeera, ta ga na fi tsohon mijinta ne, Hajia babba tace kai yaro, Musbahu ya wuce ka, ka ga dan saurayi son kowa kin wanda ya rasa, duk suka sa daria, Zayd yace yauwa Ruma ya ma sunan abun nan da kike samun a tea? Me kamshin nan, tace oh kanumfari, yace yauwa shi hajia ki bamu inaso, Hajia babba tace gaskia bandashi, sai dai in kakar ka Aishalle na san tana harka da kayan yajin nan, Hajia Ama da ke zaune ta na kallonsu tace eh akwai Kanumfari guri na, bari na je na kullo muku, Zaid yace ba sai kin tashi ba, a ina kika ajiye muje mu dauko ni da Ruma, ta musu kwatance ya ja hannun matarsa suka fita., Fadila tana ta jin dadi don ta nason tuwo, Jawad yace ina zaaje da wadannan tarkacen? Fadila tace Baby kaduna mana, yace wallahi ba zaa sa min mota yayi ta warin daddawa ba, ta turo bakih tace hajia babba kina jinshi ko? Hajia tace kai dallah chan ka bar dadi, ina ma amfanin wannan cimar da ka ke ci, banda tsotseka ba abunda yake kara ma a jiki, ka dage da cin abincin gargajiya, irinsu tuwon masara ko kayi kumari, amma sai wani abu da sunan ko dadi babu, ya sunan abun ma? Ko guiza yake? Duk suka fashe da daria, yace haba hajia sai ki bamu kunya, pizza ake cewa, tace kai ni rabani da abincin mayu da aljannu, duk suka fashe da daria. Mu'ammar yace indai ta ni ne to gaskia ki bar kayan warinki, ba maso koh Khairi? Islah ta sunkunyar dakai tana daria, Hajia babba tace yan Ingilan burauba, kun ma kanku, Ta kalli su Zayyad da suraj tace Wai ku tsaya ma, idan kunsan ba kwaso ku aje min kayana kar ku je dashi chan ku ajiye min nayi asara. Suraj yace mu muna cin tuwo gidan mu gaskia amma ba sosai ba, sai muna marmari ko honeybunch? Bilkisu tace eh muna so hajia babba, Zayyad yace no ni ina cin tuwo, ban son shinkafar nan, Umma hajja tace ai ni burgeni kakeyi Zayyad ba ruwanka da zaben abinci, kai dan gargajiya ne, yace gaskia ni komai aka dafa ci kakeyi, hajia babba tace kaji dadinka. Nan suka dan taba fira, sukayi sallama kafin suka nufa Sashen Tsoho don yi mai Sallama. Nasihar ce dai ya qara musu, a karshe ya sa musu Albarka, suka shirya tafia, Mu'ammar da suraj da jawad da Zaid suka dauki hanya daya. Samir ya dauki hanyar bauchi, Zayyad kuma aka kaisu Airport. ***** Zaria Tunda ya shigo gidan yake kwala mata kirah, a parlor suka yi kicibus, tace YaAmar lafiya wannan kira haka? Yace close ur eyes, ba ta mai gardama ba, ta rufe idonta, ya sa mata wasu takardu a hannu yace ta bude idonta, ta bude Tickets to Cambridge England ne, ta zaro ido tace yaya? Yace i told u, m ready to sacrifice everything, akwai time zaki koma skool, nd i will apply for masters, still kuma i will find a job, we'll start allover there, we will build our home, nd i will give u the joy and happiness u truly deserve. Dadi ya kashe Islah ba ta san lokavin da ta rungumeshi ba tare da manna mai kiss a baki, tace i love u yaAmar, yace i love u more swrhrt. Abuja Time din da ya shigo gidan bata nan ta je skul, ya gaji sosai ya fada dakih, yana si Yayi baccin rana amma ya kasa, giyyarsa ya ciro cikin fridge ya bude zai sha kenan ta shigo da sallama, da sauri ya boye kar ta gani, DonAllah ya daura mai wani irin kunyarta, ba ya so ta ga yana shan giya, shiyasa tunda suka dawo daga Maiduguri yake sha a boye, ta ganshi ta ga me yakeyi. Amma ba ta nuna mai ta gani ba, sai a sannan ta tuno da maganin da tsoho ya bata. Ta qudiri a ranta yaum zatayi amfani da maganin, Allah dai ya as a dace. Yace Yaxayd ina wuni, duk ya bi ya daburce yace lafia lau, banji shigowarki ba, tace ina ta sallama ba amsa ai, ganin ya kasa sakewa da ita ya sa tace bari taje ta rage kayan jikinta, ta fita, tana fita ya kwankwade giyyarsa, daki ta shiga bayan ta cire hijav dinta, ta bude kayan ta, ta ciro ledan maganin da tsoho ya bata, ta shiga kichin ta shiga hada musu lunch, cikin jug din sobo ta juye maganin nan tas, ta kai dinning, zuwa tayi ta shiga kwankwasa mai, sama sama ya ke jinta don har ya fara bacci.Tace yazayd ga lunch na gama, ka fito kaci, cikin magagin bacci yace ki bari sai anjima, ta marairaice tace plss, yace ok lemme dressup, sai da ya fads toilet ya sakar ma kanshi shower kafin ya fito, kan table ya isketa, ta yi serving dinshi, white rice ne and sauce, ya ci kadan, ta zuba mai sobo ya sha sosai sbd yayi dadi, ba a fi 5 mins ba, ya ji zuciyarshi na tashi, Warin giya yake ji, Amai ya zo mai da gudu ya fads toilet ya dinga kwarara Amai ba tsayawa, Maysah sai sannu take mishi, sai da ya kusan minti 20 kafin aman ya tsaya, ya bata tausayi sosai, ta bashi roban ruwa ya sha ya kuskure bakinshi, ta riqoshi ta kaishi daki, ji yayi dakin na warin giya, yace ki kaini dakinki, haka ta miqar dashi ta kaishi dakinta, duk ya galabaita, Sai da yayi kwana 3 kafin Aman ya tsaya, duk ya rame ya qare, sai da wani colleague dinshi yazo Gida ya samai drip, randa Zaid ya warke ya shiga dakinshi ya fiffirto da dukka kwalayen giyan da na fridge yayi waje dasu ya cinna musu wuta, Maysah na kallonshi, dadi ya rufeta, nan take ta kira tsoho ta shaida mai abun da ya faru, shima yaji dadi, yace ai Zaid kuma da Giya har Abada, yanzu ko wani ya gani yana shan giya sai yayi Amai, don kyamar giyya yakeyi yanxu, Mijinki ya daina shan giya da Yardar Allah. Maysah tace Nagode Tsoho Allah ya bar mana kai. Murmushi tsoho Yayi ya kashe wayar.. (3months later) Mrs Zaid hurry up, zaki sani latti fah, daga ciki tace just a minute Mr Zaid, yace ko na tafi? ta fito tana gyara zaman gyalenta tace ai na ma fito, Zayd ya matso yace u grw more beautiful every morning, murmushi tace ai ban kai ka ba, yace i love everything about u, murmushi tayi ta ce mu tafi kar Ka amsa query gurin Dr James, har zata shiga mota ya riqo hannunta, yace na sa miki ido wato ke ba ki san ido ba ko? Ta zaro ido tace yazayd me nayih? Oh baki san me kikayi ba ko? ta marairaice tace kayi haquri Yazayd, me nayi? Shima ya bi ya marairaice kamar yadda tayi, ya turo baki yace ban taba jin kin ce min i love u ba, waiyo Allah, kunya ta lulluba maysah, ya tsare ta da ido yace ehen ina jinki, ganin kunyanta ya motso ya saketa ya bude mata mota yace na lura akwai sauran kunyana a tare dake, a hankali zan cireshi, da sauri ta kawar da kai tare da yin murmushi. Karfe 12 ya gama ganin patients a OPD, ya kalleta yace Mrs Zaid kin gaji ko? Ta girgiza kai tace Aa, ina kallon ka ne yanda kake duba patients cikin kwarewa, kaji dadinka Allah Girma, yayi murmushi, yace dadi na da Zabin tsoho akwai Adduoi kamar mutanen da, tayi daria, yace oya ta shi muje muga patients a ward, daga chan sai mu wuce gida, ta miqe ds sauri suka fita daga office hannun su riqe da juna, suna tafia suna birge mutane, wanda Suka sansi sai suce MrAndMrs Zaid, sai su daga musu hannu, a haka har suka isa Ward, Zaid ya shiga ganin patients dinshi, ita kuma tana basu kudi sadaka, ana ta musu godia, su ka fito, daidai wani daki sukaji

Chapter 18 of 20