Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
8 / 11
lafe a jikin shi, Tuni ya sau ajiyar zuciya, ta zaunar shi kamar mai rada tana mishi sannu da isowa,ta zame takalmin shi,ta cire socks din,Murmushi kawai yake mata,,taje ta kai kayan kitchen ta dawo,, hau,Kusa dashi ta zauna tana hura mishi iskar bakin ta, "Sannu,.hannun ta ya kamo," Kinyi kyau,tai murmushi, "Muje kai wanka,zaka ware,Allah sa ka ci abinci baka bar min kan ka da yunwa ba,ta wani marai rai ce, Jawo ta yai,da halamar jin dadin kulawar da take nuna mishi tun fitar shi zuwa yanzun,,. Bayan yai wanka,Ta zuba mishi abincin da Fadeela ta taho musu dashi,,bashi ya sakko ba sai Kusan 11,da mamakin shi Zahra na parlour, Yai turus,," A,ke bakiyi bacci bane har yanzun?? A kai kaice ta kalle shi, Ta watsar,"Bana bacci da wuri ni,,Ya kada kai, kan ya kulo kofa,ya mata sai da safe,,Da sauri ta sha gaban shi,,"Nifa yunwa nake ji,,Ya kalle ta da mamaki,,"Yunwa kuma??..Ta daga kai,,"Ince Sa'a ta aiko miki abinci da yamman nan??Ta daga kai, "Ba na ci ne,dan bansan mey aka bar bada min ba wallahi, yai murmushi, A ledar da na baki babu abin ci??..Ta fara marai rai ta,ita a dole so take ta bawa Sa'a haushi in ta rike shi,,"Kayan zakin zanci na kwanta?..Tab..A hasale yace" Toh ki kwana da yunwa..Ya haura sama ya barta nan,,Tai kwafa,"Ba dan kai nai ba,,. Washegari sukuku Suka tashi,barin shi da yake ga yau ba Sa'a gare shi ba,dan kwana 2 nan,sun musu wuyar fassara, babi guda Suka ware musu a Rayuwar su,,. Zahra ba zama,dan jummai tace kar tai sanya,,sai dai gaba daya lamari haka ya tafi sukuku,dan barta da kyallin chan, bangaren tarairaya an baro ta a baya,. Da yazo ma Sa'a sallama harda kukan ta,, Dakyar yai ta lallashi,, dan ji tai wani mugun kishi ya tokare ta a makoshi,sai da tai ta Inalillahi tukun ta samu sa'ida,Ashe haka kishi yake??Ashe mugun ciwo ne??..Lalle dole in ka kasa control da shi yai maka illah,Ranar bacci sai barawo ga Sa'a,,. Ita kam yana shigo wa dakin yasha freshener,sai dai sirrin kamshin Sa'an shi daban ne,,Shi ko hade ran da Zahra take bai kula ba,,fatan shi Allah bashi ikon adalci... Gashi dai Yayi Iya yinshi ganin yayi Adalci, amma abin yaci tura,,Sa'a kadai ya mallakawa kanshi da zuciyar shi,, duk itama Zahra ya yaba da yadda ya riske ta,sai dai d"ai da'i da sallah ta gagara tashi,, Har ya dawo tana yadda ya barta,bata da niya ma bare ya taimaka mata,,Yai murmushi, ya tuno da Sa'a, Zai latti a masallaci tace yaje zata Iya,sannan ya dawo ya tarar ta a kan sallaya,,baya yai kawai ya koma parlour,, Bangaren Sa'a kawai ya sawa ido,,Yana murmushi, yaje tashin ta yaji tana karatun Qur'ani, Tuni yaji tausayin ta, Allah dai yasa tai bacci yau,,.Sai da yaji zubar ruwa a bayan gida ya koma dakin,zanin gadon ya yaye ya sanya wani,,kan ya dan kishin g'ida,,Bacci ya sure shi,,Farka wa yai ya ganta a kwance itama,,kare mata kallo yake,Tana da kyau na nuna wa Sa'a, a dabi'a tana da ita mai kyau,ya rasa meye dalilin da yasa karfi da yaji Zahra ta chanja hali??..Yanzu yar gatse gatse ce,,Tashi yai ya shiga bandaki ya watsa ruwa,ya fito ya shirya,9:20.,yasan yau kam bamai kawo musu abinci, dan jiya ma Hajiya bata kawo ba,duk da yai wa kowa cefanen ta da yamma. By Feenat Ja'afar & Hauwa Damary ®ONLINE HAUSA WRITER'S. [1/22, 7:02 PM] Feenat Ja'afar BARIKI...IYAWA 48_Parlour yai,kamshi yaji ya karade gida,ga nan kofar glass din parlourn Sa'an a bude,,ya lumshe ido yana shakar kamshin,,gudu gudu,Sauri sauri ya karasa saman nata,,bata parlour, sai yai daki,Halamun kashe shawer yaji,Ko'ina sai kamshi ke tashi,a gadon ya kishin gida tare da jawo rigar baccin data cire kan ta shiga wanka yana shaka,,Ta bude kofa,daure da Towel babba,, har ga Allah ta tsorata, dan bata ji bude kofar shi ba,A razane take kokarin komawa bandakin kan ya kira ta,, Towal har yana kokarin kunce wa,,Gaban ta ya fara dukan uku uku,,Da sauri ta rintse ido, kawai haushi ma ya bata,,Sai fa tayi da gaske wannan kishin Hafeez din kar yai mata cikas,Jawo ta yai,bama ruwan shi da lemar dake jikin ta, harda sakar ajiyar zuciya, Da sauri ta nemo hankalin ta ta fara kiciniyar zame wa,sai dai ina,ya kara kan kame ta,"Ka rufan asiri Fa Baby,,. Wallahi ba ruwa na,,ya dan sassauto ta,"Gaisa wa fa nazo muyi,ko ya Haram ta,da sauri ta daga mishi kai,,.."La'ila Ha'illalahu,,..Da sauri Suka juya jin muryar Zahra,,kallon Hafeez take da tuhuma,dan ita a zaton ta daga badaki suke,dan duk jikin shi ya jijike da ruwan jikin Sa'an,, Ta maka wa Sa'a harara,,"Haka zamuyi da dake??,..Ni zaki gwadawa BARIKAN ci ranar kwana na,,. "ke dan Allah ya isa,mey ta miki na BARIKI??,.. Ba tasan lokacin da Shima ta maka mai harara ba tana hawaye," Nidai aka shiga hakkina Wallahi ban yafe ba,,tai kasa tare da mako musu kofa..Sa'a ta dau hijab tana kokarin sawa ya rike,,Da sauri taci mur,,"Ina kwana,,,kaje pls yanzu zan sakko,.ka kuma rarrashe ta,dan baka kyauta ba,,Yai dan karamin tsaki,,"Mey nai ne Wai tukun??Ta karbe hijab din ta,"kaje zan fada maka inna sakko,abinci na dining,,Ta fara janshi a hankali, yana kaiwa tsakiyar parlourn ta juya da gudu ta rufe kofa,,.Toh mey suke nufi dashi??Suna nufin sun fishi sanin addini da adalci kome??..Yai kwafa,tare da sakkowa kasa,,. Dakin Zahran ya nufa,ta hada kai da gwiwa sai nadar kuka take,ya zauna a bakin gado abin na bashi mamaki,Toh mey yai na kuka har haka??..Dan ya taba Matar shi shine ya shiga hakin nata komai??..Yadai daure yace"Yanzu Zahra dan abun nan danayi ne har na chan chanci kimin fitsara?,,Tuni ta kara kuluwa,,"Au,dan abu ma ka dauke shi??,,wato dan kaga ina bacci shine zaka silale harda zuwa ka mata wanka??..Da sauri ya dago,."Wanka kuma?ke bana son shirmen nan naki fa,,.Gani kikai mun fito a bandakin komai??ta kada kai..yace"Toh ban son zargi,,Gaisuwa kawai naje muyi,,.A ranta tace"Oho,dan tsabar BARIKI ne yasa ta rungume shi kenan?.. Badan na shigo ba Allah ne yasan abun da zata mai,,Ta goge hawayen ta,,duk da haka bata gamsu ba sai da tace"Amma ran kwanan ta ni Ai sai 10 ko 11 nake ganin ka,,Ya girgiza kai,, Ashe haka mata biyun suke??..Tab,shikam bamai sa mishi Tension,,. "Zan gyara Toh, ki shirya kizo Dining muyi break,,yai waje bai jira mey zata ce ba,Da azama tai bandaki tai brush ta dan watsa ruwa, powder kawai ta mitsika,,. Dakyar ta tattara nutsuwar ta ta Shafa mai da dan light make up,, sai dai tai kyau,,ta feshe turare masu kamshi kan ta zabo wata shadda milk mai dan laushin jiki,tasha aiki da zare brown da stones, Riga da skirt ne,ta danyi dauri a saukake single, ta sake fesa turare,,,ta kalli mirror kayan ya kamata,tai murmushi kan ta fito parlour,, Dai dai shi kuma ya fito a dakin Zahra,,Ya Ilahee,, Rokon Allah take ya saukaka mata kishi.,, Kallon ta yake yadda take wani rausaya kamar bata son taka benen, murmushi ta sau mishi da taga ya dan harare ta,, wato fishi shi adole yayi??Ta ja mishi kujera,ba musu ya zauna,.kan itama taja ta zauna,,ta daura hannun ta a kunne halamun " Sorry?Yadda ta langwabe kai bai San sanda ya sau fuska ba,,Ya kai hannu zai kama hannun ta,da sauri ta zame,Tana dan dariya kadan tace mishi"Kai Baby mu akwai Neman fada,,ya dan harare ta kadan,,Tai murmushi, "Allah ni na yafe gaisuwar nan taka nan gaba,,zan na sakkowa mu gaisa,,Ya kara hararar ta,,. Tai murmushi,, yace" Toh ni ban yafe ba, Ba wacce nake tsoro,,Tace "Toh,it's Ok,,Bazamu kuma ba,amma kaima ka kiyaye mu,,Ya dungure mata kai,,Dai dai Zahra ta fito,,.Turus ta tsaya,,ita kam mey zatai wa Matar nan ne ta fita har kar ta??..Tai kwafa kan ta karaso,,Kujera ta ja ta kusa dashi ta zauna,ta dallah wa Sa'a harara,.ita kwa sai tai mata murmushin Da yafi komai ci mata rai, wannan munafukin murmushin Sa'an ba karamin tsanar shi tai ba,," Sis ina kwanan mu??Ba kunya ta amshe,,ta juyo kan Hafeez da wata murya tace"Baby An tashi lafiya??Ya yage baki,, "Lafiya Unique,, Da sauri Zahra tace" Au,Ina kwana Yaya?,,Sa'a ta kunshe dariyar ta,kai Lalle wannan Baho ce amma??Ya kallo ta da mamaki,,Ashe fa ko gaida shi batai ba koh??Ya kada kai, "Lafiya lau,,Ya kuka tashi??Zahra tadan harare shi cikin wasa,"sai yanzun zaka San ya na tashi Fisabilillahi Dear??Suka zuba mata ido shida Sa'a,, ta cigaba cikin gwalli," Dakyar fa nakai kaina bandaki,, Ta kallo Sa'a, ganin yadda take kallon ta yasa ta cigaba da fi'ilin ta,ita adole zata bawa kishiya haushi,,bata San bada kanta take ba,..Banza Yai da ita yana zuba Tea,,Tuni zuciyar Sa'a ta fara tafarfasa,,amma ko a fuska bata sake ta gane ba, sai ma murmushin kara tusa bakin ciki da take mata,, Amma dan ta kashe zancen yasa tace "Toh kiyi serving namu gashi Baby na jin yunwa,.ta harare ta kadan kan ta fara zuba wa Hafeez din,,da in ranshi yai dubu ya baci..Ganin bata zuba mata ba yasa ta jawo ta zuba,ta hada tea Baki kawai,,Ya kallo ta, murmushi ta sau masa,Tuni kwa ta yaye mishi kunci,,duk loma 1 sai ya kallo ta,, Sai kwa ta sau mishi murmushi, shaf sun manta da Zahra,,. Tsaki tai,ta tashi tai kitchen,indai dan ta mata break ne toh ita zatai launch din ta,yar BARIKI kawai,.Ai kamar jira yake ta kauce ta fara bashi a baki,,,Gogan ya ware harda zuba musu pic,,Tace suje kitchen su Taya sis aiki,ba musu ya bita,sai ganin su tai suna dariya, Sa'a tace" Sis,dame zamu tayaki??tai mata kallon banza,,"Na yafe,,tai murmushi kan tace"Ok,ta juyo ga Hafeez, "Baby,bari na wanke kwanika,.ya kada kai," Toh muje na Taya ki kwashe wa,,Ta kallo Zahra,"No tnks, ka Taya 6s,.tai waje,. Tana hawa sama tai kitchen ta kulle,kuka ta fara,tai ta wanke fuska,ta dauraye kwanikan ta,,kan tai daki,,ta kwanta bacci,kiran sallah ne ya tada ta,,ta tsaya gaban madubi,Allah ya sota fuskar ta washe,,kai Kishi bala'i ne,Ya Allah ka saukaka mana. By Feenat Ja'afar & Hauwa Damary ®ONLINE HAUSA WRITER'S. [1/22, 10:39 PM] Feenat Ja'afar BARIKI...IYAWA 49_Yau sati guda,kai karar Zahra 3 wajen Hajiya,yau kam ta kudiri musu zuwan ba zata,shi yasa ko Zahran bata sanar wa ba..Da yamma ne,Lokacin kowacce na dakin ta,, sallama tai,kan Zahra taji,,Da gudun ta ta fito,ta kan kame ta,,Tace"Toh bari mu zauna tukun,Ta cika ta, Suka zauna tana kallon ko'ina, a share amma ba kamshi,ba wari,,Ta kallo ta lokacin da ta dakko Lemo,ta ajiye.,"kai Hajiya naji dadin zuwan nan Allah,. Ta zauna,chan tace "Au,.taje ta dakko cup,Sannan ta zauna zaman gaisuwa,.Bata tashi ba sai da ta zube mata korafe korafe sun fi a kirga, ita kanta sai da ta Gaji,,. Ta kallo ta," Rakani dakin yar uwar taki toh Zahra, ta bata rai,"Hajiya a kira ta ta sauko man,.Tai murmushi, "Aa,bari itama naje dai,.Sukai saman,,Ba ko kwankwasa wa Zahra ta ja glass din,,Turus sukai,Lokacin da suka tarar tana rera kira'ar ta mai zakin sauraro,cikin Suratul Yusuof,,earpiece ne a kunnen ta, ya zame mata dabi'a karatun Qur'ani da safe da yamma.,inkwa bata cikin tsarki,toh tana tare da Earpiece a kunne ko ta kunna Mpn ta tana bi cikin nutsuwa, A jikin ta taji kamar mutum a kanta,a firgice ta mike,,.Zahra ce tana wani yatsina,sai Hajiya a gefen ta, Cikin fara'a ta cire Earpiece din cikin nutsuwa,da tsabar girmamawa tace" Sannu Da zuwa,.ta mike tare da nuna mata waje"Bissmillah, Zahra sai harara take aika mata,,Hajiyan ta zauna,Zahra ma ta zauna a kujera kusa da Hajiyan, ita a dole mai uwa a gindin murhu,. "Ina wuni Hajiya?Fuska sake ta amsa mata,Ina su Tasleem?.."Tana Gaida ku,da tare zamu zo,,Ta dukar da kai cikin kunya tana murmushi...Woo Sa'adatu BARIKI.. Tashi tai ta nufi kitchen, sai gata dauke da flate da cups da ruwa da lemo,,Tana zuwa ta durkushe gaban ta, da murmushi fal fuskar ta, ta tsiyaya mata ruwa,ta tsiyaya lemo,Ta dau lemon da girmamawa ta mika mata,. Cike da fara'a ta karba," Sannu,,tai murmushi. Ta tsiyaya Tace"Sister ga ruwa,,Ta tabe baki kan ta karba tana yatsina, duk Hajiyan tana kula da su,,tasan kurba zata ajiye Sa'an ta karba da sauri ta ajiye,,.shiru har yanxu Zahra ba taji an fara bam bami ba,sai ma fadan da Hajiya ta musu dukan su,kan ta tashi,,Sa'a Tace"Toh mun gode,a gaida su Tasleem,Tai murmushi, "Zataji,. Suka fito ita kuma ta koma da sauri,.Har sunje bakin mota ta karasa da dan saurin ta,..Tadan rissina kadan," Hajiya,ta juyo,mika mata ledar, karba tai tana kallon Sa'an, Tace"Ku gaida gida,Tace"Da wahala haka??Toh an gode,Sa'an tai kasa da kai,,Hajiyan tai murmushi,"Allah ya muku albarka,. Suna tafiya ta juya,Zahra ta dauro bayan ta.. "Chusa kai ba kwarjini,,.Chak ta tsaya, kan ta juyo da murmushi a leben ta, Hannu ta mika leben ta kan tai kissing hannun ta nuna Sa'a dashi" Muahh,,Kan ta juya,Tuni ta kara kuluwa,,"Karuwar kawai,,Ta daga mata kafada,,kan ta haye saman ta tana kara bata haushi ta baya,,. Ta bita da harara,ba abunda yafi kona mata rai sama da yadda kota takale ta bata kulata,sai dai ma ta bita da wannan murmushin da ta kira da munafuki,,. Yau watan su guda,duk yadda Zahra taso taga sabani tsakanin su ta kasa,Sa'a ta tsare gaba ta tsare baya,,.A ko yaushe Hafeez rawar kafa yake akan ta,da girkin ta da ba nata ba,,.Sai dai yau da Jummai tazo ta bata dabara,,girkin Sa'a ne, amma taci uwar kwalliya da dogayen brown din nyty,,Yau tasan duk tsiya sai Sa'a ta kwana kukan takaici,. By Feenat Ja'afar ®ONLINE HAUSA WRITER'S.  Posted by Feenat FEENAT JAAFAR'S MOBILE BLOG JUST ANOTHER BLOG BARIKI IYAWA 6 [10/2, 7:32 AM] Feenat Ja'afar: [1/23, 12:51 PM] Feenat Ja'afar BARIKI...IYAWA 50_Tana jin horn din Motar Hafeez ta dan budo kofa,,ta fada gado ta rike ciki,,yana shigo wa ta kwala ihu,,"Zan mutu wayyo Mamy,,Dai dai Sa'a ta fito zata sakko tarar shi kamar yadda ta saba,,da gudu yai dakin Zahra,, tam ta tamke ido tare da rike ciki,, Ita Wai mutuwa zatai ya kai ta gida,,Turus Sa'a tai,.Kai da gani kasan karya ne,,amma shi ina,ya rude da jin tana ambatar mutuwa,,Da sauri Sa'an ta karasa,tare da kamo Zahran"Sannu sis,Cikin ne??..Hafeez ya kallo Sa'an, "Unique dan rike ta na kira Dr Seuss, Da sauri ta rukunkumo shi,," Nidai kar ka tafi,.zan mutu,,....Kut...Humm humm,.Lalle,Turnuku kenan,Wai Fadan Ibilisai,,Yaro bai ga ba,bare ya raba,Sa'a ta kan kance ido ta ciki,Lalle Zahra bata San wace ni ba??..Amma yau,zan fara ware mata True colour na Wallahi, Daure wa tai bata nuna musu ba,sai ma sannu da take ta kwararo mata ba adadi,,Sune har 9,amma dai dai da second,zahra bata daina kururuwa ba..shifa har ga Allah bai gano karya Zahra take ba,dan tana da ciwan ciki,musamman lokacin period. "Unique!.. Ta kallo shi, " Na'am Baby,,.Kije ki kwanta,in ya ware zan taho,,ta kada mishi kai., "No Baby,,Kawai ka kwana da ita,,Kaga ciwan nata,,Ya kalle ta zai magana tai murmushi," It's Ok,,sis Allah baki lafiya,,Ta juya tana daga mishi hannu,, Tafiya take da wani irin yana yi, sai yanzun ya kula da kayan jikin ta,, Riga da wando ne yan kanti,wandon Brown robber ne,ya dan bude ta kasa,sai rigar mai net 2,Orange,ta baya tai zalolo,ta dame mata kugu,ta gaba ta dage,,tai parking din gashin ta a tsakiya tare da daura siririn gyale Orange,,Da kallo ya bita har ta rufe kofa,,Ya lumshe ido,, Zahra ta na kallon shi,a ranta tana "Yau kam sai gani daga nesa,.Ko minti 5 Sa'a batai da fita ba ta ware,,tare da daura kan ta a kafar shi,,. Sa'a na shiga daki tai wani murmushin mugun ta,, Tuni ta hau changing kayan jikin ta.,''Zahra kinyi na kudin ki,,en my time start now!!.. Ko'ina tabi ta kara fesa daddadan turaren ta,,ta dawo daki ma haka,,Ta duba agogo 10 saura. Dube ta fara,ta hango gwangwanin Air weak a mirror,,.. Tadi take mishi,,tamkar ba ita ta gama ihun yanzu zata mutu ba,nufin ta ta janye hankalin shi,sai dai ina, gaba daya shi hankalin shi yana ga Unique Ladyn shi,dan tunda suke yau ya taba ganin ta da English wears,, Murmushi yake yana kallon kofar waje,ji yake kamar ana janshi sama wajen Sa'an shi.. Duk Zahra na kula dashi,Tuni ta mike a cinyar tashi ta fara huci,," Wato har yanzun kwakwalwar shi naga Sa'a?? Gangar jikin shi ce kawai a nan??Tai kwafa tana kokarin cire doguwar Rigar saman Suka ji an kwala ihu,,.A zabure ya mike,kamar Sa'an shi yake ji fa??Zai waje Zahra ta tare hanya,,"ina zaka kuma?? Ya kallo ta yana kallon kofa,,"Bakiji Kamar ihu bane a gidan??Ta maka mai harara,,"Ni banji ba,,Yayi dai dai da lokacin da Sa'a ta kara sakar wani ihun. By Feenat Ja'afar ®ONLINE HAUSA WRITER'S. [1/23, 2:02 PM] Feenat Ja'afar BARIKI...IYAWA 51_"Ahhhhhhhhhhhh....wayyo Allah... Inalillahi... Da gudu ya fito, har yana tun tube,,itama Zahra ta biyo shi da kira..a tsaye ya same ta a kan gado..daga ita sai wata guntuwar rigar bacci pink,mai hannu siriri da breast cup,da wandon ta iyakar shi cinyar ta, Shima kuma duk net ne,,da gwangwanin air weak a hannun ta halamar zata daki wani abu...da sauri ya karasa Shima ya Dane gadon,,tana ganin haka ta kan kame shi,, " wayyo Baby,bera..bera ne..tana nuna mishi bayan kofa..tamkar Zahra zata hadiyi zuciya taji,,ita kam ta gamu da muguwar yar BARIKI,, ji tsinannun kayan jikin ta??yanxu shikenan Kila ta wargaza mata plan.. Da ihu ta kwalla mishi kira,,suka saki juna suna kallon ta,, Da sauri yace"Zahra ki shigo mu kwana a nan.,dan kinsan wlh nima tsoron Bera nake,,.tuni ta fara hawayen bakin ciki,ta juya zata tafi ya kira ta,.a zaton ta ko cewa zai jirani,sai yace"Dan turo mana kofar please,,.ya wani marai rai ce, Sa'a ta sau mata gwalo,tare da kashe mata ido daya,Ta rungumo Hafeez din da wani salo,,Tuni gogan ya sau ajiyar zuciya...kafa ta sa da masifa ta bige kofar, "Bazan rufe ba,macuci kawai..Ina,shi bai ma san tana yi ba,,Daki tai da gudu,sai kwa kofa ta tafi luuu ta rufe kanta..Ya kara kan kamo ta,,." My Unique,. Love you,, Nan ta biye mishi,sai da ta mantar bayanin bera kan ta zame tace"After Dinner,.. Yau kam ta nuna mishi ainahin wace Sa'adatu BARIKI, Duk wani abu da tasan zatai ta faran ta mishi a daran nan tayi,,Sai da ta tabbatar babu wani gibi da yarage na nauyin shi akan ta,,Hmm Sa'a Sa'a, Lalle she's Unique a wajen shi,,. Fir Zahra taki fitowa Break,shikwa kamar jira yake Suka kara yin sama bayan sun gama cika tankin su,,dan yunwar cikin ta ta fito 12,ganan abinci a cikin flaks din ta,ba kayan Sa'a ko 1,sai dai kofar glass din a bude tana Iya jiyo dariyar da suke kyalkyala wa,,Tai kwafa,tana gama cin abincin ta makawa Jummai kira,,"Banza kawai,wannan dabarar taki banda ciwan zuciya ba abinda ta sa ni,,Jiya kwanan kuka nayi,sai da nai Dana sanin aikata hakan wallahi,, Daga chan Jummai tace "Ki jirani anjima kadan,,. Sai bayan la'asar suka sakko kasa domin cin abinci,tana kallo a parlour,da sauri ta dauke kanta,dan wannan fitsarar bazata juri ganin ta ba,zuciyar ta zata Iya bugawa,a kujera ya zauna,1 setter,hannun su rike da juna,Sa'an ta zauna a hannun kujerar,, Ta kalle ta,," Sis,ya kwanan jikin??Ta maka mata harara tare da sauya tasha ta manna mata,,ta kallo Hafeez, "Baby,koh dai jikin ne ya dawo??Yai murmushi," Zahra bakya ji ne??Muna miki ya jiki..Ta kallo shi,, "Au jiki?kasan da jikin ka barni ni kadai?,na mutu ko nai rai baka da asara,, Yai kicin kicin"Ke Maintain fa,,Ina ce ware wa kikai kina ta dirka firar ki,sai da na tabbatar kin warke kan na tafi,.Baki sake take kallon shi, Dan haushi kasa masa magana tai,,Sa'a tace, "Baby yunwa,,ta ruko hannun shi tana marai rai ce fuska.." Oh sorry,.Muje,.Sun zauna ya kallo Zahra, "Kizo muci man,ko ta dazu zaki mana??..Da kamar kar ta tashi,sai dai kuma ta taso,,Sa'a tai serving nasu,ta tura wa Zahra nata,su kuma ta zuba musu flate d'aya,, A baki take bashi,shikwa Tuni ya kara narke wa kamar yaro,,Zahra in banda chaka cokali ba abinda take tana hararar su,,in ta bashi loma d'aya, sai ta kai loma d'aya itama,tare da aika mishi murmushi,,. A haka har Suka gama,abincin da Zahra bata ci ba kenan,,Kitchen din Zahran Suka shiga,Suka kuskure bakin su,,yai ma Zahran sallama kan zai fita shi kam,,sai da suka zo dai dai kofa,ta dai dai ci Zahra na kallon su kan ta rungumo shi,," Ka kula min da kan ka,tai mishi kiss a gefe gefen kumatun shi,kamar irin larabawan nan,,shikwa sai yage baki yake,, Zahra bata barke da lamarin ba,sai da ta ga Sa'an na wani shagwabe fuska,,"Please Baby,,Come back soon,,U know am gonna missed you.. Shikwa harda dan bubbuga bayan ta halamar lallashi,, Yana "InshaAllah my Unique, Love you,,Yama manta da zahra na wajen,,Ta cika shi tare da dan bashi light kiss a lips, tare da goge bakin dan Jan baki ya taba" Love you too Baby,,.Dakyar Suka ban bare yai waje,ina Zahra huci kawai take,.Ta dawo daga rakiyar .. Tarar ta a tsaye tana huci,,.Dariya ta fara harda rike ciki,,.Tuni Zahran ta kara kuluwa..Ta rasa mey zata ce,sai cewa tai, "Karuwar Kawai,,ai ba sai Kin nunan kin Iya BARIKI ba,dama nasan da abar ki kika zo,,.ta harare ta tare da kama kugu.. Tako wa tai tazo gaban ta,tare da dafa kafadar ta,,da sauri ta zame hannun tana harar ta..Murmushi tai kan ta kada kai. By Feenat Ja'afar & Hauwa Damary ®ONLINE HAUSA WRITER'S. [1/23, 3:54 PM] Feenat Ja'afar BARIKI...IYAWA 52_"Kwarai,fadi da ihu ki kara da wayyo Allah,,Rausaya take da kanta,,tamkar wata K'adangaruwa "Sa'adatu nake,,,tai murmushi da ya baiyana kyawawan hakwaran ta,, ta rausayar da kai gefe,, kan tace"BARIKI IYWA Ba,," ehe."BARIKI ikon Allah ba,ta nuno kanta da hannun ta"Ni din nan da kike gani na wlh naci dubu sai ceto,, of course,Karuwa nake,amma A wajen Hafeez,,,. Kara dafata tayi,kan tace"Ya kamata kisan fa Qawata "BA'A FAFE GORA RANAR TAFIYA,,sama taka kar kija da BARIKI wallahi,.Dan ke da kanki kince da Bariki na na shigo,,kinga kenan babu wani guntun salon BARIKIN ki da zakiyi ya firgita ni..Ta sauke hannun ta kasa kan ta dan ja baya,,Ki sararawa kanki,gudun kar ki shiga gona ta,.dan duk tsiya ta bazan shiga taki ba,.Jiya kin min d'aya,kar ki kara mai maici..Ta dafa kafadar ta ta matso dai dai kunnen ta,kamar mai rada,tace"Be a good girl.. Ta dana mata hannu,kan tai gaba tana jujjuya mata wani gu.. Daskare wa tai,tama rasa na cewa,.Tasan dai a doke, karya take ta daki Sa'a, dan a dire take, ta fita kauri,sannan komai yinshi take Cikin cire shakku,.Daki tai,.Tana daura wa da kunce wa,,tana haka Jummai tazo ita da wata Qawar ta,,Anan Suka lalace suna kunce wa suna Daura wa, Wai nan duk mafita da zasu ja da Sa'a suke nema.. Parlour Suka dawo,lokacin Sa'a ta sakko jera abinci,,tun daga habaicin da suke ta gano su,saboda haka inda suke ma bata kalla ba,,tana jera abincin ta tana wakar "Charaman Dudu,.Ta juya tana kada musu bayan ta,, Suka tafa,Jummai tace. "Fago guda kenan,Tana jin Su,,aiki ta hau,tana kamalawa ana magriba,tai sallah,tukun ta hau make up,,ta dakko wasu shegun kaya,,Jeans ne skirt din,iyakar shi gwiwa, ya dame ta tam,.ta juya tana kallon bayan nata,,tai murmushi," Ga Fago fa ya fito,,tai murmushin keta,kai Lalle Jummai, tama bata dariya,.Tasa rigar Green mai garen hannu,sai Top din na jeans,sanin Hafeez yafi son ganin gashi a tsefe yasa ta dau damarar gyara shi,.tai parking din a tsakiya,ta tattare yai doughnut cif a tsakar kan,ta dau dan kunne barima green tasa,.tasa flat shoes din ta green,ta kunnan burner ta tsaya a kai,kayan ta suka dau kamshin turaren,ta kashe ta sake feshe turare a Dakin da parlourn, ta dau katon hijab da wayan ta,ta cilla chewing gum a baki,tana kas kas ta tako, Suka bita da ido,,Har ta sakko suna Binta da ido,,tai murmushi"Hi Guys,. Da sauri Suka dauke kai,Zahra taja tsaki,,Tai murmushi kan taja daya daga kujerun dining ta zauna,,K'afa d'aya kan d'aya ta daura tana Taunar chingum,,Waya ta dakko,ta fara game,, Zahra ta zungure su Suka ci gaba da tadin su,,. Shigo war kira ne ya katse ta, ta dubi wayan tana murmushi,cikin wata mayaudariyar murya tai sallamar,,duk Suka juyo kallon ta"Assalam Alaikum,.. Tai murmushi mai sauti dan jin abinda yace,,tace" Allah ja min Ran Namiji d'aya tilo ga mata biyu,.Tuni ta hau mishi kirarin nata dake kara fasa mishi kai har ya jima yana waya da ita ba tare da ya Sani ba,,Murmushi take cikin salon da ita kadai ke Iya sarrafa lamarin shi,,."Ya akai Toh your Royal Highness,, Da Girman kujerar ka,,yai murmushi, bakin nan yaki rufuwa, Sa'a, ta daban ce,shi yasa dan ya kira ta da "Unique, bai jin kom... By Feenat Ja'afar & Hauwa Damary ®ONLINE HAUSA WRITER'S. [10/2, 7:35 AM] Feenat Ja'afar: [1/24, 1:42 PM] Feenat Ja'afar BARIKI...IYAWA 53_Yace"On my way,,mey kika tana nadar min?,,Tai fari da idon ta, wanda ya kara kular da Zahra,,"Farin ciki, So,Kauna,,Tare da ni Sa'ada,, r all yours Janeeman,,.Ya sauke Ajiyar zuciya, yayin da yake kwana da mota,,yai horn,mai gadi ya bude,,Duk da taji shi,hakan bai sa ta sauke wayan ba,ta ci gaba da bashi Hot kalam din ta,,Ta zira hijab,,Rike da waya ya shigo,bakin nan tamkar gonar audiga,,hmm,Namiji tamkar wawa ne,mudin ya dace da mace Yar siyasa,,Bata ko kula da su Zahra ba taje ta Dane abinta,, cikin hijab din yake kokarin shiga kan tai saurin ja da baya yaga su Zahra,,huci take tamkar kububuwa,,.Wannan iskancin har ina?..Ita ran girkin ta bata isa yai mata hakan ba,,. "Sannun Ku, baki mukai??Ta ruku hannun shi suna kallon su, Jummai ce tai karfin halin gaishe shi, ya amsa kan ya juyo kan Sa'a, ta sau mishi murmushi sukai sama.. Suna hawa ya rukun kumo ta tare da cire hijab din suna kyal kyala dariya,,Ganin ta a kayan,yasa kawai ya tsaya jujjuya ta yana kallo,," Wow...U look so Beautiful in Green tonight..Tai kada ido,tare da sakalo wuyan shi, Tnks Dear,. Yace shi a kawo mai abinci nan,dan baima son sauka,.Zahra na ganin ta hau sama da abincin ta kallo su Jummai, "Ku jirani,,ta tashi tai saman. Tazo bakin kofar,ba ko sallama,, "Dear, su Jummai zasu tafi,,Ya tsaya yana kallon Sa'a, ta ajiye cokalin abincin da take bashi,kan ta tashi," Yi zaman ka,Bari a sallame su Dana Taxi,.yai murmushi, "yauwa Thanks,.Rigan shi ta dauka,ta Ciro 500,tai yo bakin glass din,.Ta yaye labule,," Sis,gashi a basu na Taxi,,en kice su gaida gida.. Harara ta maka mata,taja dogon tsaki,,kan ta juya,dan tasan Tunda ta fada a gaban Hafeez tofa bazai ba kota ce ya kai,ta juya.a hankali Sa'a tace "Umma ta gaida Aisha,,..Ta juyo tana murmushi,shi har ya cigaba da cin abincin shi,dan baida jumurin yunwa. Ranar Juma'a Yace su shirya zasu gidan su Hajiya,..Zahra

Chapter 8 of 11