Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
10 / 11
kin dawo??. Ta daga kai tana Murmushi,,. Kallon Zahra take yadda tai d'ai d'ai a cinyar shi da duk Rabin jikin ta,,. Wani malolon kishi ya tokare mata makoshi,,. Ciki tai tana musu bari ta huta,.. Ta fara fuskan tar chanji a Hafeez kwarai tana kula,da a da ne da yanzu ya biyo bayan ta,. Ta cire kayan ta tare da Ciro maganin ta sa a side bed,.Ta fito a wanka sai Gashi,,. Kallon ta yake,Fatar nan a mur mure,, sai shining take,,ta dan kara kiba kadan,,.Ya riko cikin ta tabaya,,. Kallon su yake a mudubi tare da ajiyar zuciya,,. Shi indai bai dangana da jikin Unique din shi ba bai samun nutsuwa, Gashi Zahra ta dakko mishi wani sanabe,Wai kamshin jikin shi take so,,Haka zai na bata lokaci agun ta,yasan kwarai Unique din shi mai hakuri ce,,dan bata taba complain ba a kan hakan,,duk da Gashi yau girkin ta ne,. "Missed you Janeeman,. Tai Murmushi tare da juyo wa,,.Ta shafo fuskar shi" Missed you too Pyaree,,.Yai Murmushi tare da riko kugun ta,, Na matso naga kin fara min rakin masu ciki kema,,kokarin kunce mata towel yake,amma sai ta rike Kam,,Ta fara gazawa da mitar Hafeez,, Ai ba sai ita zata Haifa mishi yara ba,ganan Zahra ta wadatar,,Kallon ta yake ganin yadda ta sauya,, ya fuskanci a yan kwanakin nan in yai mata irin maganar nan sai ta sauya fuska,,it means bata son zancen haihuwa ko mey??.Cika ta yai ya zauna kan gado,ba tare da ta tanka shi ba ta fara Shafa mai,, shedan ya fara hura mata zuciya,,sanar ta yake Hafeez fa gori yake miki a fakaice,,. Tuni ta kara cika da masifa,.kiris take jira ya kara tofa wa,,ganin tana Neman fita hanyar da ba ta ta yasa ta fara karanto adu'ar Neman tsari daga shedan,,. Ta rintse ido, a hankali taji nutsuwar ta na dawo wa,.Da yanzu ta tafka kuskure babba, wato masifa wa Miji..,Drawern ta ta bude tana son daukar kaya taji ya kara rukun kumo ta,,. "Fushi kikai Ada??.Da sauri ta kada mishi kai da murmushi, Ya juyo da ita,Kallon shi take cikin ido,Shima haka,,." Ina son yara ne musamman daga gare ki, ba laifi bane dan na fada,,Tai murmushi, tare da sadda kai kasa,ta Sani bai fita son yara ba a yanzun,kodan ta tsallake gurin Zahra, sannan ta wanke kanta daga zargin tana planning,,. Dago habarta yai,tare da manna mata salon shi dake mantar ta bacin rai,,.Tuni suka Lula Duniyar su tasu kadai. Yau ta tashi da murnar haihuwar Fadeela, Direct chan ta nufa,,an sake mata gida kamar yadda Hajiya Rabi ta nema,duk tayi laushi tunda taga yadda Alhaji ke rawar kai da Fadeela,,. Ita kwa har a labour sai da ta Roka mata Allah ya bata itama.. By Feenat Ja'afar & Hauwa Damary [1/27, 10:57 AM] Feenat Ja'afar BARIKI...IYAWA 60_Takarda yake dube,Gashi Sa'an ta na gidan Fadeela,ya kira wayan ta ya shiga bata kusa,,. Turus ya tsaya tare da kwaso su ya zube a kan gado,,Plygyl ya gani da sauran tarikicen mugun gunan da likita ya rubuto ma Sa'a,, Gasu nan har ta kusa shan rabi,,budewa yai ya fara karanta wa,,Duk da bai fahimci komai ba, amma ya ga an rubuta mai ciki Kar ta sha in yana first trimiser,.Tuni wata zuciyar ta fara fada mishi na hana daukar ciki ne,,deba yai Ya sakko kasa,sai huci yake,Tana gado tana waya da Jummai ya shigo,da sauri ta katse ta,. Dake tayi science, sannan bangaren ta karan ta a Deploma a pharmacy,, Ya zube mata magungunan,. "Na meye wannan Zahra?Ki waren wanda yake hana shigar ciki,.Tuni ta harbo jirgin shi,.Tai murmushin mugun ta,, kan ta daga flygyl,,. "Wannan flygyl ne,400g,Yana Iya zubar da ciki koda na kwana d'aya ne,.Ta daga dayan,sarai tasan na dan infection ake rubuta shi tace pills ne,,dayan kuma na infection,,. Huci yake kamar wanda zaici babu,,ya kwashe su har yana warta,,.Da gwalo ta bishi,," Jeka dai,,kai ba mai yar goal ba,ba'a taba jin kan Ku ba,yau maji ma gani Ai.. Missed call taga nashi,da azama ta hau kira,. Dafe yake da kai a hannu,"mey yasa Sa'a zata mishi haka??.wato dan ya barta aiki shine ta samu damar raina mishi hankali.., Wayan ta katse shi, yasan ita ce,dan ringing tune nata daban ne,,yai tsaki,da kamar bazai dauka ba,,. "Am sorry Habeebe,muna chan hidimar aiki,Ya kake... "Ki dawo ina son ganin ki yanzu,A tsorace ta waro ido,dan jin yadda yake magana fada fada,,sannan ba ita gare shi ba,,.Da marai rai ta tace" Ok,. Ta kalli Ummi da. Fadeela, "Zan je na dawo,,suka daga mata kai,dan duk sunga sauya war ta,kuma sun San da wa take waya,. Ta dau mukullin motar ta ta fice. A saman ta same shi a daki,yai kicin kicin,Zahra najin sallamar ta ta labe a gefe dan jin mey zai wakana,,.Yadda ta tarar shi ya bata tsoro, ganan mugun gunan ta a watse kan gado,. A rabe ta zauna a bakin gado,," Baby hope dai lafiya kake?,,. Cikin daga murya ya fara fada,ta inda ya shiga ba tanan yake fita ba,,.Kai tai kasa,dan tsabar al'ajabi,Bai taba mata haka ba sai yau,,Tuni hawaye ya fara zirya a fuskar ta,. "Mey zakice game da wannan??. Ya nuno mata magani,,sai ta zata dan taje asibiti bata fada mishi bane yasa hakan,,." Kai hakuri,naso fada maka,Sai..."Kimin shiru,tambayar ki nake na meye??.Baki sake take kallon shi,,. Sai dai yai nisa,,ta girgiza kai "Na infection ne,.Yai Murmushin cin rai ganin ta ma raina mishi hankali,. Kai ya kada," Daga yau na soke aikin ki a gidan nan toh..Da sauri ta tashi tana waro ido,. "Hafeez mey nai haka da zafi ne??." Au tambaya ta ma kike??. Ta girgiza kai tan hawaye,"Kai hakuri,wallahi ban San zuwa asibiti na zai bata ma ba,.Yai Murmushin takaici,."na dai sanar ki na soke aiki,kinga sai ki zauna zaman Tara yaran yanzu,.Amma Sa'a ban San lokacin da kika daina so na ba,,ta dago da sauri,.Waje yayi dan ganin kukan nata na k'aruwa,.zahra dake labe a kasa da sauri ta zauna a kujera..waje yayi ta bishi da dariyar keta.. A gado ta zube tana mai kuka mai tsuma rai,.Wato maganin ne ma na planing??. Ta kuma sanar shi na meye yaki yarda,,. Tai mai Isar ta har magriba kan ta tashi ta goge ta shiga wanka,,.Tana fito wa ta tsantsara uwar kwalliya kamar mai zuwa party,,kai in ka ganta baka ce ita tasha kuka ba,. Riga da skirt ta dakko,skirt din ya wuce cinya mai yalwa Green da ratsin baki baki,,.Sai top din shi Mai yankekken hannu,.Ta tufke gashin ta sai kamshi take tai kasa,.Lokacin Zahra na kitchen, sai fitowa tai taga mace ta daura d'aya kan d'aya tana waya,."Eh sai dai goben,,InshaAllah da wuri zan zo,.. Suna hada ido ta sau mata Murmushi,. Zahran itama tai yake,.kitchen ta koma tana cije lebe,. Wace irin jarababbiya Allah ya hadata da ita??. Ji kamar ba da ita akai dazu ba??. Tai kwafa,ta gani Ai.. 8:pm ya shigo,.Kallon Sa'an yake,ta bala'in mishi kyau,,.Ta kallo shi,. Da sauri ya dauke kai,. Zahra ta kulu Iya wuya,.sannu da zuwa ta mishi fuskar ta sake,.ya amsa yana kallon ta,,. Da yaga zata kallo shi sai ya dauke kai,.. Suna cin abinci sai dan tsakura take,,yana kula da ita,,.sai dai bai son mata magana ta ga ko ya sakko,.Amma duk tausayin ta yake,. Yasa Unique din shi kuka,. Suna gama cin abinci tai musu sai da safe.. Da kallo ya bita har ta kule,,.Ya sauke ajiyar zuciya,,Zahra ta buga plate kan wani tana tattara wa,."Anya Sa'a haka ta bar Hafeez kuwa??.Anya baza tabi shawarar Jummai ba na iyaka tsakanin shi da sa'a ba??.. Tai kwafa,.. Washegari sunan Fadeela, da wuri ta tafi,.Yaro yaci sunan Baban shi,,harda Hajiya Rabi a wajen hidima,in ka ganta gwanin tausayi duk tai laushi,,tunda taga ba sarki sai Allah ta fauwala wa Allah komai,.Dan Fadeelan bata da bace,. Anyi suna an tashi lafiya,.Ta dawo gida da jin haushin Zahra, dan sai da tai Dama bata je mata ba,. A gaban su Aunty Maryam take mata feleken ita bata son kaza da kaza,an kawo abinci ma bata son warin curry..Hmm sai ita halin ta. Ita ke gare shi, duk tayi kicin kicin,kiris take jira ya kula ta tasau mishi kuka,dan kwarai ya bata mamaki jiya,. Shima dake Namijin Duniya ne haka ya daure yaki lallashi, sai dai da aka zo kwanciya kamar kullum ta lafe jikin shi, anan komai ya sai tu.. Dan baya Iya hakurin Iya jure rashin ta kusa.. Washegari warai aka koma kamar ba Ai ba,.sai ma wani nan nan da yake da ita,.Batun aiki ta share shi,.Wai aka ce fadan masoya ba fada bane,. Sabe ya sakko da ita tana bayan shi,. Dariya suke yi tamkar basu bane jiya da shekaran jiya,. Da azama Zahra ta koma daki,.Tabbas zargin ta ya zama gaskiya,.Dan ita sun sha fada daga baya sai an kai ruwa rana ashirya., Dan ita in tai fada da Miji toh fa kowa sai ya Sani,.Dan zata hau fishi ne har a shimfida,. Yayin da shi kuma sai ya basar ta.. Amma sa'a Duniya,cikin ruwan sanyi ta mantar shi komai. Yana Office tace mishi zata unguwa,. Yace sai ta dawo,.So take ta kai ga likita,dan sanar mishi changing da take ji kamar yadda yace,.Ta koyi nawa kwana biyu,ba ita ta bar gidan ba sai dab da yana dawo wa,. Dai dai zata bi junction Shima ya taho,.yana ta mata horn ina,bata kula ba,.sai ya samu kanshi da bin ta ganin tayi hanyar asibiti.. Tai parking.,Shima yai a dan nesa da ita,.Binta yake ba tare da ta kula ba,,.gaban shi sai faduwa yake,.a tunanin shi Sa'a ta hakura tunda ya barta aiki,.Ashe ta daura daga inda ta tsaya,. Toh zai ga likitan mai planing din,zaiji uban mey yasa zaiwa Matar shi planning ba tare da yardar shi ba... Anti Nital tabi, yaga a sama an rubuta /Family Planing,. Kwanar yaga tayi,.da azama ya bita dan ganin inda ta dosa. By Feenat Ja'afar & Hauwa Damary ®ONLINE HAUSA WRITER'S. FEENAT JAAFAR'S MOBILE BLOG JUST ANOTHER BLOG BARIKI IYAWA 7 [10/2, 8:08 AM] Feenat Ja'afar: [1/28, 10:28 AM] Feenat Ja'afar BARIKI...IYAWA 61_Ita Hakima ce,bata bin layi,,dan da shigar ta ma sai ka dauka Matar wani Babban mutum din ce,Direct ta shige data tabbatar ba kowa,,Shima da fara'a ya kallo ta, dan gwanin Kallon News ne,kuma yasan Sa'a,.Ta fara mishi bayani kenan sukaji an banko kofa,.Da azama ta mike lokacin da tai arba da Hafeez,,. Shi kam bai wata wata ba ya chakumo Dr,. "Da sa hannun wa kake wa mata ta planing??. Dr ya zaro ido,," Hala baka hankali??..kaga an rubuta planing a office dina??..Ya rike hannun shi tare da kokarin ban bare wa,,.Amma ina,Hafeez ya rike shi tamau,. Sa'a ta fara Hawayen takaici,,. "Hafeez yaushe ka fara min Titsiye a rayuwa??..Ya juyo yana hararar ta.." Ki bari,zan zo kanki kema Ai,.Zanji dalilin zuwan ki nan?.Allah ya bawa Dr Sa'a ya ban bare da kyar..,"Ya kamata kana bincike kan ka hau zargi,,.Ya daga mishi hannu,"A kaga malam,kayi na kudin ka,dan duk randa zan kara ganin ka da mata ta court ce zata raba mu..Dr Dariya ma ya fara,Ganin sai wani dage wa yake,,.Tabbas yana son mutum mai kishin Matar shi,. Yace"Toh madam din ka tana dauke Da ciki yanzu haka..,Ya maka mishi harara,"Kar ka layan ce min malam,ba shi zai hana na yarda da kai ba,.Yai murmushi tare da dafa kafadar shi,."Abokina ka nutsu,,.Kaga kasa Matar ka kuka,.Mu fidda zancen wasa,.Tabbas likitan Mata ne ni,bari in ma gwari gwari,kuma ina planing, amma ba ga Matar ka ba,,.Ita nata planing din Samun ciki muke,Kuma da dukkan Alamu mun dace,,.Ya kallo Sa'a, "Madam,inda muje ki kwanta,,.Ya dafa Hafeez," Calm down,. Ka zauna please,. Ya zauna da niyar Ganin gudun ruwan shi,,.cewa yai Sa'a ta dan daga rigar ta ta mike sosai,.Hafeez ta kallo da shi kuma yake Kallon Dr,,yai Murmushi, "Scanning zan yi,so ka rintse ido, Tashi yai ya tsaya a kan machine din,.Likita ya girgiza kai yana masa Dariya,.Da kamar minti 5 ya dago kai,,." You see,,Ganan Babies din ku a cikin madam,,.Matsowa ya karayi baki sake,,Likita ya sake daura abin a kan marar Sa'a., Tuni hawaye ya silalo mata,.Da sauri Hafeez yakai hannu zai goge mata ta gantsara mishi cizo da harara,ba shiri ya sau kara,.Likita sai Dariya yake sha,,.Nuna mishi har Heartbeats na Babies din ya fara harbawa,,. Hannun ta ya ruko,"Am Sorry my chocolate,,. Tuni ta sau dariya ita da likita,.Ta kan kame hannun shi suna Kallon yaran yan yiri yiri a alon Machine din,.Dr ya juyo bayan sun gama.."Toh yanzu zamu shiga court da dalili,,.Yai Murmushi, "afuwan,Yanzu Unique ma Courtn kanta ce.,Toh amma Dr.,pills din Dana gani kwanaki ka bata fa kuma na planing? Ya kallo Sa'a,." Madam,wane pills kuma??.Ta kada kai, kan ta mishi bayani,.Yace "Abokina Ai wannan Antibiotics ne na bata,koda in akwai infection, ba mai flygyl ba??Ya kada kai,,." Kuma ance Shima yana zubda ciki..Yai dariya"kai madam sai kin dage,, Mutumin ki Ba dama ne,,.Yanzu dai wancan sun wuce,,Ganan wannan,,.Yanzu zata fara sha dan inganta lafiyar yaran,.cikin zumudi tace"Dr Watan su nawa??..Ya kallo Hafeez, "Madam fa ta fika dauki,kaji wata nawa take tambaya,. Yai Murmushi,tare da kallo Sa'an," nidai nasan basufi 2 month ba,,.Ya gyada kai, "Suna cikin week6 ne,,. Sukai Murmushi, sai kuma ta dukar da kai,ita kunya. Suna fita a asibiti ya bita a baya har suka je gida,.Tana fitowa ya dauke ta chilak,.Da dariya suka shigo,Zahra ta sau baki tana kallon su,.Ganan ciki ya mata ham a gaba,,dan ya doshi 7month,,.Kiciniyar sauka take amma yaki sauke ta,Ganin Girkin Zahran ne,,.Har sama ya kaita a haka,Wai baison ta wahala hawa stairs.. Tai murmushi, itama kenan ta shiga sahun su Ummi..Sakalo wuyan shi tai..tana yai alkawarin babu mai jin cikin ta ko twins take dauke dasu,in sunzo a bazata yafi.. Yai Jim" anya zan Iya??.ko Aminu sai Y'aji,,Tai Murmushi, "BBC kenan??..kace Duniya taji kawai..Yai Dariya, za su sha mamaki,ba mai ji toh Mom twins,.. Tasa hannu ta rufe fuska, Wai ita kunyar karya..Ya dungure mata kai yai waje.. Dan yasan Zahra an hau 90.. "Kiyi da jikin ki mana Zahra,tun kan su dawo,.ta daga K'afa da kyar,,Duk da gaban ta sai faduwa yake amma bazai hana ta zuwa inda zata samo yancin ta ba,,EDDn ta cikin satin nan zai tsaya,.Amma tunda Ta kyalla taga yadda abin Hafeez yake gaba akan Sa'a tace Ba taga ta zama ba,,.Dan tun kan ta haifi D'a, ya daina daukin shi sosai,.a Ganin ta Sa'a farraku tai mata da Hafeez da cikin tun kan yazo Duniya,,.Zuwan ta na biyu kenan wajen malamai,da taimakon Jummai. By Feenat Ja'afar & Hauwa Damary 62_Sanye yake da Babbar malun malun,Yaci uban rawani,,.Ganan wasu manyan charbi da maka makan littafai, kai ka dauka Qur'ani., Da Ganin fuskar shi yafi kama da irin yan Duniyar nan,amma in baka kula ba sai ka mishi Kallon Malami,,.Ya washe baki yana kallon Jummai,. Dama yana ganin Zahra ya karanci matsalar ta,,. Yace"Kishiya koh?.Da sauri ta kalli Jummai tana hadiyar yawu,,. Kai ta kada mishi,,. Ya gyara zama a wayan ce yana kare wa Zahran kallo,.Wai,chakwala dadi,. Yana son harka da Matan aure,bare kuma mai juna biyu,. Yasan akan kishiya,mata sukan yarda da wannan Halin nashi,.Bare Zahra,da gani ta k'agu.. Sai dai yau,yana da Mai debe mishi,.Bayan ta gama kwararo mishi bayani ya kallo Zahran,. "Kuna sake da taimako alhalin kuna da kishiyoyi,,.Ki duba ki.,duk ta miki dabaibayi da mijin Ku,zakiga baya rawar kai akan ki,Toh da baki zo da wuri ba,D'an ma da zaki Haifa bashi ba uban sa,.Tuni ta yarda har ta fara zufa,.Fadi take,." Yanzu malam ya za ai?,,. Ya hadiye yawu lokacin da ya kalli bakin Zahran,. Sai wani marai rai ce wa take mishi,.Ya kallo Jummai,. Yace Zahran ta jira su a waje,.Dakyar ta tashi,tai waje,.Ya kallo Jummai,. "Ina kika samo wannan yar dakwala dakwalan?,. Tai murmushi,." Nidai na sanka da cika aiki malam,.A taimaki Qawata,.Ya shashe baki,.tare da Shafa gemu,."Kin tabbata bata da gardama??.Ta kada kai, "indai akan kishiya ne toh batta gardama,,.Tana kashe ko nawa ne,.Yai murmushi.." Kizo min gobe da ita.,Zakiga aiki da cikawa.. Tana fita ta kora mata bayani,."Gaskiya Jummai zan so yau ayi ta ta kare,dan Kinga yadda nake,Gashi dakyar gobe ya kuma bari na fita,kuma weekend yana gida,.Tace"wannan mai sauki ne,.kedai Allah ya kaimu.,ta kada kai badan taso ba,.Gidan su ta wuce,.Kamar kullum su Mamy suna zaune da Auntyn su suna Fira,.Agajiye ta zauna tana haki,. Mamy ta kallo ta. "Yanzu Zahra baza ki sallama wa yawo ba haka??..ko tausayin kanki bakya ji??..Ta kallo ta,. Ruwa Auntyn nasu ta bata,haka ta daga ta kwankwade,.. Sai da ta samu nutsuwa tukun ta Iya gaida su,.Mamy ita dai sai fada take akan ta hakura da fita haka, indai ba Wai haihuwar Titi take nema ba,. Bayan sun shiga daki take sanar da mamy Wai Sa'a tai mata farraku tsakanin ta da Hafeez, kuma wallahi itama bazata barta ba..Hannu tasa a haba Mamyn tana kallon yar tata,." Zahra ina fata Baki bi hanyar bata ba koh??..Ta kallo ta da rashin fahimta,. Ta cigaba "A kullum ina fada miki ki kara hakuri,.Ki fawwala wa Allah lamarin ki,.sannan kisa a ranki babu mai miki abu sai da ikon Allah.. Kishiyar ki mai saukin kai ce,a gani na inkin bita zakiji dadin zama da ita,.Ki fidda zargi cikin lamarin ki,, Sannan ina rabaki da Qawayen banza Zahra, wallahi su suke kai mutum su baro,..Nasiha take mata mai ratsa jiki,kan ta guji bin malaman Tsibbun nan,Ta kuma kuji sharrin Qawaye Marasa kan gado,.Duk nasihar ta ratsata,amma banda ta Sa'a, dan ita ganau ce ba jiyau ba..Tabbas Sa'a ba haka tabar Hafeez ba,.A haka a ta jogana ta shiga gidan Meenat Qawar ta,. Duk da ta zubar ta da.,tunda ta samu Jummai,. Basa shiri da meenat, dan takan tsage mata gaskiya duk daccin ta, sai dai ba taje gidan ta ba,.takan gaya mata Sa'a Yar siyasar Duniya ce,zama da ita sai Ka koyi hakuri da Iya kaima siyasa,sannan a yadda ta kula da ta yi a hankali zasuyi zaman lafiya da Sa'an, toh fa anan sukai Baran Baran,. Ita Wai data hada kai da kishiya.toh gwara ta sallama mata mijin.. Da fara'ar ta meenat din ta karbe ta, duk da karshen rabuwar su da fada suka rabu,.Amma tasan Zahra tasan Value nata,.Dole gaba zata neme ta,. " Ya kamata ki ajiye fita Zahra haka,.kinga kafar ki kuwa??,.Tai dan tsaki,."Ke barni.,fitar ta dole ce,. Nan ta koro mata bayani duk da tasan ba yarda zatai ba,. Murmushi tai tare da girgiza kai,. "Zahra,a kullum bazan Gaji da baki shawara ta Gaskiya ba,koda kuwa zamu b'abe…Sa'a ta fiki Tattalin Hafeez,.a kan ido na ina gani,kefa?Gani kike Wai duk abinda take Wai a Ganin ki karuwa ce,.Dole kiga Tasku Zahra, dan Namiji na tarai rayar mai Taryar shine Zahra,.In yayi rawar kai a kanta,itama tana yi akan shi,.Ki duba abinda idon Basira,. Wallahi ki gujewa muguwar Qawa,zata kai ki kawai ta baro ne,.Shiru tai,a duk zance tana dauka,amma mudin an sako Sa'a, toh fa sai taji tana mai jin haushin maganar ma.. Karshe sai shiru meenat ta mata.. Duk ta mata gargadi akan Kar ta koma wajen Bokan nan,dan duk malamin da zai fada maka haka wallahi Boka ne..Toh taji wannan. Sai dare Hafeez ya dauke ta sukai gida,.A daran yake fada mata gobe zai tafiya kwana d'aya.. Washegari gida ita kadai,Sa'a taje barkar Ummi data haihu da asuba,.Tana zaune,tun jiya take jin dan milmil,amma taki nuna wa kowa,.Duk Sa'an har daki ta mata sallamar ta fita.. Tariyo zaman su da Sa'a take,. Bata taba takallar sunyi fada ba,.Bata taba rama sharri da sharri ba,.sai dai tai abinda zataji haushi,.matsalar ta d'aya??.. Data mallake Hafeez ita kadai... Sallamar Jummai ce ta katse mata tunani,. By Feenat Ja'afar & Hauwa Damary 63_Ta kallo ta, "Tunanin mey kike haka ina ta kwankwasa kofa da sallama?? Tai ajiyar zuciya," Kin Sani Ai Jumee.,Ta tabe baki., "Keda kike da maganin tunani,sai kinje kin kashe kanki a banza ita kwa tana Shana war ta,.Yanzu ki tashi.,dan ina da wajen zuwa,.Ta kalli Jummai.. Ba wata kyakyawa bace,fuskar nan taci bleaching, kan nan Dan kare da attachment din gashin kanti,.kai da ka ganta Kaga yar Duniya,,kuma ita Zahra ta zaba a matsayin Qawa,. Farkon haduwar su a saloon ne tun ana saura 3 month bikin su,a time din taje Shampoo na sallah., Baje kaya tai tana wa Matan wajen Talla da bayani,Wannan duk iskancin kishiya kikai amfani dashi sunan ta sorry,,ita tasan makamar kishiya,tai ta zurma su..anan Zahra ta zurmu,bata aure,auren ta 3 duk ya mutu,dan da zancen hakane,toh yaci ta zauna gidan Miji.. Taja gauran numfashi, tare da kada kai,"Jummai anya zani kuwa?.Dan yau banjin dadi kadan, sannan wallahi gani nake ma kamar mutumin nan fa Boka ne,.Jummai tai tsaki.,a zuciyar ta tana tunanin Kar Zahra ta kwafsa mata,dan har sun shafci kudin da za'a fadawa Zahran,na kan ya zama nata.. Da sauri ta dawo wajen ta, " Waya fada miki Boka ne??.Malama inma zaki ware ki ware,ita ina take??..kika San ita wajen wane bokan taje??..Nan tai ta zugo ta tare da zugar shedan,suka hadu suka sha tunanin ta har ta amince,. Tana cije ciwo har suka je kwalta suka tsaida keke Napep sai wajen Boka.. "Yauwa,Jummai kice ta shigo,.ta kallo Zahra," ki kula,kiyi yarda Yace,dan wannan ce kadai damar mu da abinda ke jikin ta..Yanzu ki kawo sarkar naje bakin asibiti na sayar, dan dole mu cika mishi kudin shi,,.Tai Jim,dan sarkar auren su ce.,Abban su Hafeez ya sai musu,amma tanaji tana gani ta cire,sai zugata take.Ai Wai biyan bukata yafi dogon buri,,. Ta shiga ciki,da sauri ta fito,dan Ganin dakin baki kirin dashi,.sai da ya kara mata magana tukun ta shiga da sallama,. Ya amsa.,a rabe ta zauna tana karanto ayatul kursiyu,, Ta zauna,,.Ya taso yazo kusa da ita,.Zaki tashi ki cire gyalen ki,sai ki kwanta akan gadon Nan, ya nuna mata wani gu tare da haska mata da waya,,gaban ta ya fara dukan uku uku,"Gyale malam??.Yace "eh.,saboda komai ya ratsa Ku keda yaron,,.Ta kada kai tana Dari Dari,.tun kan ta zauna ya matso,.Da sauri ta tashi,." Malam mey za ai ne??."Kinga, ba'a magana a dakin nan,yana kokarin kamo ta ta Matsa da sauri tana,"Amma Allah ya isa,.Ashe wajen dan iska ta kawo ni??..Da sauri ya biyo ta,ina Ai ko nauyin cikin ta bataji da gudu tai waje,.ba gyale bare takalmi,jakar ma ta manto ta dakin,.Allah yasa doguwar Riga baka ce a jikin ta, ta kunce dan kwalin,.Tafiya take bata ma San ina zata ba.,Ga wani azababben ciwo da yafi na tun jiya yana ratso ta,.Wani mai Taxi ne ya shigo layin da fasinja,.Dakyar take daga kafar ta, ta zauna a baya tare da sanar shi inda zai kaita,..Tun tana cije wa har ta bara gantsare wa tana yarfe yatsu,.Mai Taxi ya kula da ita,.Da sauri ya tsaida mota yana masifa,."Dama nakuda kike kika shigo min mota salon ki haihu mun aciki??..Toh wallahi fito,Fito maza.,Dakyar take motsa baki,."Dan Allah ka karasa ni gida,.Yace"aa..fito.na yafe kudin ma,.Gashi dai tsakanin su da gidan baifi kwana 2 ba, ga unguwa sabuwar unguwa ba kowa,.Haka tana ji tana gani ya dire ta nan,. Ta sawo kan motar ta kenan ta hangi wata a chan nesa rike da kugu a durkushe,,. Daga gani Matar na jin jiki,,Sauri take ta koma dan 5 har ta kusa,.Gashi ta bar Zahra a gida da tsohon ciki,.Ummi tayi tayi ta kai dare taki,duk da ko ta zo kusa da ita banda habaici bata abin mata,amma Hakki ne a kanta zama da ita tsakani da Allah da tausaya wa. Birki taja,kan ta fitotaiy wajen Matar da kanta ke durkushe,. "Ya salam,Baiwar Allah Daga ina haka??..Da sauri ta dago kanta dan jin muryar mai magana,. Ido ta waro dan Ganin mai murkususun...ido fal hawaye sai cije lebe take. By Feenat Ja'afar & Hauwa Damary [10/2, 8:12 AM] Feenat Ja'afar: [1/29, 1:04 PM] Feenat Ja'afar BARIKI...IYAWA 64_"Sis Zahra mey ya kawo ki nan??..Inalillahi,.Ciccibar ta ta fara,."Kiyi hakuri.,yanzu ma saurin da nake na dawo gida na barki ke kadai,.Ita dai Cije lebe kawai take,.Dakyar take fadin"Sa'a ki taimaken zan mutu,.Da sauri ta bude baya tana fadin"ba zaki mutu ba,kiyi hakuri muje asibiti,. "Ga waya na ba chargy,na mota yaki min,ban San wa zan kira ba,,Ya salam,sannu,,.Reverse tai a hankali, tana hawa kwalta ta fara gudu,.Ganin yadda take zufa yasa ta kure mata A.C,duk da bata son kamshin dake fita aciki,.Ajima kadan ta juyo,kan ta kalli titi..Ta mata sannu yafi a kirga,.Ta kara dabarar sa chargy fir wayan taki karba,. Suna zuwa ta kira Nurse da attaindance suka ciccibe ta,.Nurses Yi suke amma ina,fir cervix yaki budewa,,Ga tazo har 8Cm..Sa'a ta sai kai kawo take,har 6 shiru,sai lokacin ta tuna da Drn dake duba ta,,Tana zuwa yana kokarin tashi,.Dake yana da kirki sai ya biyo ta..Har ciki suka shiga,,Yai yan dube duben shi,,.Sai lokacin ta tuna da ta kira Hafeez ko a wayan wani ne,.Dr ya ara mata waya,,.Zatai waje Kam ta rike Sa'a Wai Kar ta tafi ta barta,.Ta zauna a gefen gadon,." Zahra kiyi hakuri,zan kira Hafeez,yasan halin da muke ciki,InshaAllah zaki sauka lafiya,.Dakyar ta cika ta,,sai dai tana fita ta cije cije ta fara mai yawa,.Matsalar protein,Sa'a ta shigo,.Likita yace ta samu,ta girgiza kai.. "Wallahi matsalar network,yace" Gashi Preeclampcia ya fara,dan akwai protein a urine din ta,.sannan ga major problem din,Bpn ta,.Tana ma zuwa awu kuwa??.Ta daga kai,.."Eclampcia, Dr ya za ai toh??Subhanallah,. Babu numbern wanda ta rike a Familyn Hafeez, duk suna waya tana mota,"Baba,.Baban ta ne ya fado mata,.da sauri ta karbi Wayan,"Dr bari na sanar da Baban mu sai yazo,.Ya kada mata kai,."Zai fi,.dan a yanzu (there is no cure for Pre-eclampcia beside delivering of the baby,.),.And wannan yaki samu wa,cox cervix nata yaki buduwa,.Ina tunanin. Cs,.shine best solution indai muna gudun Kamuwar mai duka,.Yanzu zan fita,in kin kira abinda kuka yanke zan nemi sauran Doctors sai mu shiga emergency... Ta daga mishi kai,.Juyo wa tai Ta kallo Zahra da hawaye,.Itama mai d'aya kenan, toh ina ita ma biyu,.Har ranta ta tausaya mata,.Zama tai a kan gadon tare da ruko hannun ta., Tunda taji Cs ta tsaida kukan ta,. "Sa'a, Amini dan Allah,. Ta kallo ta,," Toh Zahra,yanzu ba numbern da zamu kira sai ta Baba kawai,,.Ga wayan ki kema yana gida,.Tana jin ta ambaci waya ta tuna inda ta baro jakar tata duka.,Baba ne ya dauka take sanar shi abinda ke faruwa, Yace "ina shi Hafeez din,. Tana kuka tace" Baba baya gari,Gashi layin shi

Chapter 10 of 11