Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
2 / 11
naja..dan hutun farko,saida malaman su suka zo gidan su Sa'a, dan ka'ida in anyi hutu suna kai ziyara gidan dalibai masu ilimi,,toh fa,akaga malaman larabawa a gidan su Sa'a, yara suka cika,, tuni ta fara dagun kai,, tun daga nan martabar Sa'a ta kara sama cikin yaran arear,,wannan ne ya kara sa qaunar ta a gun iyayen,,ita kam fadeela day take so,,nan take yi. Tana ss1.,amma in ka ganta,zaka rantse wata katuwar budurwa ce,,komai ya kan kama,,samari suka fara mata cha..tuni kai ya fara gilgilwa,,basu ke gaban ta ba,,burin ta da yawa,, musamman kanan samari,tafi raina su,, toh wanda take nema suma ba'a barsu a baya ba,,sai kaga Alhj babba dashi,amma yazo yana rawar jiki wa Sa'adatu,, ganin yadda take, yasa suke sau mata kudi,,da taci naci,ta fatattake ka,, da kudin samari ta kafu,, dan ita batajin nan da shekara 5 ma zatai aure,,tun baban na taka mata burki,har yai shiru,,yakai ya kawo kayan da Sa'a take sawa yanxun ko yar wani mai kudin albarka., Ga BARIKI sai abunda yai gaba,,akwai lokacin da taje super market ita da fadeela,, suna cikin siyayya saiga wani Alhj sunzo shida matar shi siyayya,,tunda yaga Sa'a,ya kasa sukuni,,tuni matar ta fara tsaki tana hararar su Sa'a,, Sa'a ta kallo ta ta watsar,,sai a lokacin ta kula da yanayin Alhjn,,tai murmushin mugun ta.. Tuni ta fara kwarkwasa,tana wani yauki,,tamkar bata san Alhjn nayi ba,,da taxo dai dai wajen shi da gan gan ta yarda kwalin corn flakes,, tana wani fari ta tsuguna zata dauka,da sauri Alhjn yarigata,, sai washe baki yake,, "sanun ku yan mata,, tai wani fari ta saci kallon matar,duk sai huci take,,tai wani far da ido" Yauwa Alhj,, tuni fara'ar shi ta karu,, har ya manta da matar shi na gun,,iya wuya matar nan ta kawo.. Da karfi ta katse shi.. "Wai Alhj meye haka?ya juyo,." Mey.. mey..mey nayi,,taja tsaki sai kaje ka biya ai,,ka wani tsaya a gaban yar cikin ka kana bari,,ya kallo Sa'a.. Ta sau mai wani shegen murmushi tana far fara ido..tuni ya sake washe baki,, dan takaici kira take"Alhj, magana nake,, amma ina,shi ya tafi,,ta kalli su fadeela da tsabar takaici.. Tace"shegu karuwan banza kawai., ta bangaje fadeela ta wuce tana huci..Sa'a tana ganin ta futa ta hade rai "Baba, mama na maka magana,,tuni yasha mur" haba yan mata,, tai gaba tana taku zuwa wajen biyan kudi,,da sauri ya shiga gaba.."Aa aa.,bari zan biya duka..tai wani murmushi, kai maza abar su,,ita duk dan matar tayi,kawai daga ganin su zata fara ya tsina musu fuska.bata san wace ni ba,,taja baya ya biya kudin..zata dau ledar ya dauka har tasun ya rike,,ta kauda kai tana dariya..suka fito daga super market din, matar tana ganin su ta fito amota. By Feenat JaJa'afar & Hauwa Damary [12/23, 7:49 AM] Feenat Ja'afar BARIKI...IYAWA 7_Magana take amma shi hankalin shi yayi kan Sa'a.. Tuni ta kule ta tsaida Taxi,,Sa'a ta nuna mishi ita,,kan yai wajen tana dagawa matar yatsu cikin shakiyanci..tuni ta kara kuluwa..tace mai taxi yaja,,shikwa Alhj yana ganin haka ya koma wajen su Sa'a,, "Asma'u muje na sauke ku mana,, tai far da ido,, toh mun gode,, tuni ya hau rawar jiki,, suna tafe yana musu tadi,,ita duk ya ishe ta, amma ta maze,,a layin su ta nuna kofar wani gidan kasa,.nan ne gidan mu,,yasau baki yana kallon gidan, yace" toh sai kin ganni,,ta kada mai kai,,har yaja mota yana daga musu hannu,ita kam yake kawai take mishi,,yana kule wa tai tsuka,,"ji yadda yake rawar jiki,,yan wahala.. Ita dai fadeela binta take da kallo..suja dauka suna tafe,,saiga wani dan unguwar su Aminu,yace"BARIKI.. Tace"IYAWA.. Yai dariyar keta..kai Allah barmu da BARIKI.. Tai murmushi "Amin Aminu,,yace" Wane garan aka kara wanka, tai fari,"kasan ku maza,,sai a hankali.. Nasan zai dawo..zan sa yara suna min gadin kofar gidan nan,so nake tashin farko ya bani kudin gyaran gida..Aminu mutumin ta ne,a duk unguwar a maza dashi kadai take hulda,,duk a dalilin qawar ta ummi.. Yai dariya "BARIKI ba imani,,yai kuma tanan za'a fara,tace" nagaya fiya rawar kai ne wlh,, yace"a sassauta mana,,tai murmushi "wanda bai kawo kanshi ba ba..sukai dariya.. Kan chan ta wuce gida,,tuni fadeela tai gida ita kam,,da sallama ta shiga,,aka cire gyale,,"mama mun dawo,,ta kalle ta,," sannu,ta fara bude kaya,,ta ware wa su mama kayan shayin da ta siyo,ta dau nasu da kayan cosmetic,ita dai mama kallon ta take "wai ni Sa'a na tambaye ki,,ta kallo maman" toh,, "ina kike samo wannan uban kudin haka?tai murmushi" mama kullum tambaya 1 kike min,,"wlh ni ba wanda nake roka yake ban kudi,, fadeela sheda ce,,ta girgiza kai,, "ni dai kimawa Allah kar kice zaki saida mutuncin ki a banza,, dan wlh koni uwar ki lamarin ki ya fara bani tsoro.. tai wani murmushi "mama,ta kallo ta," wlh hannu wannan, ba saurayin da yaga fuska bare ya taban,,na kuma miki alkawari, indai nice,toh zan rike mutunci na.. Ta kada kai "Allah ya muku albarka,. Sukace " Amin. Washegari kuwa sai ga Alhj yazo gidan da ta nuna mishi jiya,,tuni dama tasa yara zaman jira..in wannan sun gaji su bawa wannan,, ya yafito daya,,"Nan gidan su Asma'u? Ya kada kai "amma bata nan,bari a kira ta,,dan har sunan karyar data bashi ta sanar da yaran,,da gudu yai gida,sai gata ta dawo a islamiya,," BARIKI., tace "ya akai Tj,,ya rada mata" mutumin yazo,,tai murmushi "ku tashi toh,an jima zan neme ku,,tai gida..tuni ta cire kayan islamiya tasa na karya,aka mitsika powder,, ta zari gyale" mama ina zuwa, tai waje,uwar ta girgiza kai,, Allah mai halitta,, ta rasa Sa'a halin wa ta biyo a duniya,,wlh bata da kaffara, ko yanxu akai wa Sa'a aure a gidan mata 4 tsaf zata zauna..ita kanta wani sa'en tsoron BARIKI irin na yarta take.. "Alhj sannu da zuwa,, ya washe baki," yauwa Asma'u, ya gajiyar ku ta jiya?tai fari,"Tabi lfy,, "ina aunty,,yai murmushi,, tuni yaji ta kara shiga ransa,, Ya zamo kusan kullum Alhj sai yazo,,wahalar yau daban ta gobe daban, Alhj har ya mallakawa BARIKI waya,lokacin rike mai kyau sai ya'yan manya,,ranar da ya cika sati,yazo da kudi,wai zai bata ai gyaran gida dan zai turo manyan shi tambaya.. Saida cikin ta yai kululu..amna ta wayen ce..ya dakko damin kudi kuwa ya bata. ana haka washegari suna tsaye sai ga wata yar BARIKIN gaske ta fito a gidan,ta kalli Sa'a"BARIKI,.. Tai mata banza,,tace" Sa'a, dake nake fa,,tai mata kallon banza.."Bance kifita harka ta ba ne? Alhj ya sau baki,,Sa'a kuma,.ta kallo shi da yake"Sa'a fa,,ta daga kai, "aa ni ba wannan bama,kamar BARIKI naji an kira ki,,ta hade rai" eh Suna na kenan, ya hadiyi yawu.. Anya kuwa tafiyar shi zata wu davyar BARIKI? Da gani wacce ta fito a gidan sun nan ba yar kirki bace,,take ta kallo shi, ganin tarkon ta ya danu"Alhj lfy?ya kada kai "a ba komai,inaga zan tafi,, tai murmushi.." Toh nagode..yaushe zan ce zasu zo..ya kallo ta "aa ki bari zamuyi waya.. Tai murmushi"a gaida aunty na..koh kulata bai ba. Tun daga nan bata kara ganin kafar Alhj ba,dan tunda ta fuskanci da gaske yake tahada plan na rabuwa dashi cikin sauki..saida ta sake layi kan ta koma makaranta. By FeenaJa'afar & Hauwa Damary [6/2, 5:59 PM] Feenat Ja'afar: Feenat Ja'afar. BARIKI...IYAWA 8_Gashi har ta kammala secondary school dinta a Mamudo..iyanxu kam, karya ta ninka ta da,,BARIKI da Yanga da kisisina ya gaba,, cikakken zubi kuwa ya da zati Allah ya bata,, shekarun ta 17,amma in ka ganta,zaka zata tai 20,dan komai yaji cif cif,,kugun nan tamkar dame shi akai,ga mazaune,, ta ko'ina tayi MashaAllah.. Shi yasa take zan zaren ta son rai,,tamkar in taje makaranta karatun yanga da Iya tafiya, salo da sauran su ake koya mata,, duk yan Matan unguwar nan so suke suyi kawance da bariki,,likafa ta ci gaba,,tun a ss2 ta bude account,,dan a yanxun Business take,bata saye da siyarwa ba,, no.,ta saita gidan aure,, Tunda mazan yankin suka gane tsoron BARIKI suke,sai su kuma suka samu abun yi.. Akwai lokacin da a wata unguwar gaba dasu,wani dan siyasa Matan shi sun hana shi sakat,,yai nasihar a banza,,sun maida mishi gida kamar filin dambe,,Ranar suna office yake bawa abokin shi lbr,,"yanxu duk dabara ta ta kare,, ya kallo shi,kan yai dariya,"kasan mey?ya girgiza kai "ina ga ina da dabara,,tuni ya gyara zama,," in baka manta ba gidan Dana zauna da,ya kada kai "a unguwar, akwai wata Yarinya,," BARIKI sunan ta,, ita indai da kudi,toh aikin ta saita mata ne,,ya kalle shi da halamar tambaya,, "ban fahimce ka ba?? Yai murmushi,"a unguwar kaf,ba wanda baisan BARIKI IYAWA ba,,yarinyar tayi,ga diri ga kwainane,, ya harare shi" toh ni kuma mai zai hadani da wata bariki??mtsww kai ana abin kirki ka sako mana wani zance..yai dariya "ka jira ni tukun,,waya ya dauka,kan yai dailing wata number, kan yasa a hands free,," Daga chan aka dauka,"Aboki ya akai??yai dariyar keta"kaga na BARIKI sai yayi,,Shima ya kyalkyale da dariya,,"kai baka mantuwa abokina,, yace"ya zan manta,,da fatan har yanxu komai normal?? Yai dariya,, "kai BARIKI Duniya ce wlh,banga mai Matan unguwar nan suke tsoro har yanxu sama da BARIKI ba,, madam dina lukus kake ji, tunda akai wannan batu..yai dariya" Ya kamata a koma a karawa BARIKI jari,, suka sake kyalkyale wa da dariya..bayan sunyi sallama shi dai Muktar da kallo yake binshi,, ya ajiye waya yana"BARIKI BARIKI,, "tukun kasan wace BARIKI kan kaje gare ta,, Mutumi na dan nace BARIKI ba ina nufin karuwa ce ba,,ya girgiza kai," Tasan takan Duniya ne,,wannan abokin nawa,shekara 1 data wuce Matar shi ta tsuro mishi da hali iri iri,,da halama da zigar kawaye,,ga ta kamar ta yana son ta,,tuni ta hau iskanci irin na kowa ya samu inuwa,Wai dole yai shanya,,har karar ta yakai wajen iyaye, amma ba abunda ya sauya,,Ranar muka hadu,nace yau a gidan shi zanci abinci,,bai min musu ba muka je,, a parlour muka tarar ta ita da qawaye,,suna firar shi abokin nawa, fadi suke"Wlh mazan Saida haka,,in ka nuna musu bakka mutunci anfi dai dai tawa dasu..ya kalle ni na kalke shi baki sake,,.mukai sallama tana ganin mu ta tabe baki,, qawaye kowa yai hanyar sa,,tana gani mun zauna tai tsaki ko gaisuwa babu ta tafi,, ya kallo ni duk kunya ta ishe shi,,nan yahau kame kame,,nace"Ku nan hala Baku San da zaman BARIKI ba? Ya girgiza kai "wace haka?nai murmushi,, biyo ni mu fita tukun,, tuni ya zari mukullin mota, By FeenaJa'afar & Hauwa Damary [12/24, 12:08 AM] Feenat Ja'afar. BARIKI...IYAWA 9_Wato a unguwar mu akwai wata Yarinya BARIKI.. Ita aikin ta kawai a dauke ta sojan haya., indai zataji dumus,toh fa gidan ka ya gyaru ya gama,, yanxu wajen ta zamu,, ni zan ma iso,akwai wani Aminu Aboki na suna dasawa sosai,,. Suna zuwa ya nemi Aminu a waya,,sukaci saa kuwa tana gida,, Suka koma inuwa jiran ta,, chan sai gata ta fito tana taku tamkar hawainiya,,baki ya sake yana kallon BARIKI,, lalle taci sunan ta,, Ji yadda take wani yauki,,. Ta karaso da sallamar ta, cikin muryar nan ta masu Duniya"Sannun Ku,, Sukai yake,,"yauwa BARIKI,, Aminu yace "ganan Aboki na ya kawo abokin shi ai mishi gyara,,tai murmushi, tare da kallon su da wannan kallon nata,,sai suka zama kamar wasu sokaye a wajen ta,, Aminu ya kallo su" Ku karan to mata, "Ni zan wuce,ga nan bakin ki,tai murmushi, tare da daga mishi yatsun ta 2" see you,, ya gyada kai, sukai sallama ya tafi,,Duk abunda ke faruwa suka karanto mata,tai murmushi,, "yane toh,, tai musu wani kallon kasa.,tuni ya gano mai take nufi,,rafar dubu 10 ya bata,,"ki fara da wannan,, ta juya su tai murmushi,," bakka matsala,, "Abu 1 yanxu zaka min,ya gyara tsaiwa,," kasa min numbern ka,,sannan duk inda zata fita,ka sanar ni,ya gyada kai,, tai murmushi "Baka da damuwa,,ana haka saiga wata Qawar Matar wanda aka bada contract dinta tazo wuce wa,,da sauri ya kallo abokin,," tafa kwabe,,ganan Qawar ta,, suka kalli Sa'a, tai murmushi "ai tama taimaka min wajen aiki na,,Wai salma kake nufi? ya gyada kai,, tai murmushi," kai kamar baka ganta ba,, sannan yau,kar kaje gida sai karfe 10 dare,, nasan daga nan,gidan ka zata..zata sanar da Matar ka,cewar ta ganka tare da BARIKI.. Daga nan, zata fada mata koni wacece,, ina so in ka koma,ka sauya mata fuska,,da sauri ya kallo ta,, tai murmushi "I know what am doing,,, ok?ya gyada mata kai,,nasan zata fara tambayar a ina kakai dare?kasan amsar bata I guess.. Ya kada kai" ki sanar ni dai,,tai murmushi,. Zamuyi waya,,dan yanxun haka ina da wajen zuwa,,ni zanji da sauran aikin..sukai kada kai tare da mata sallama,,,. Direct kwa salma gidan Qawar ta tayi,,da mamaki ta bude ta shigo,dan dazun ta tafi,,"da fatan ba mantuwa kikai ba??Tace "hmm zakiga mantuwa,, kin San kwa ina naga mijin ki? Ta kada kai tare da gyara zama tana zaro ido,," Toh a wajen BARIKI,,Bakya ramin kanki sai na wata,,tuni ta fara tunanin ina take jin BARIKI? Ta cigaba. "Ke kinga damin kudin dake hannun ta?kuma wlh mijin ki ne ya bata,,.ta kallo ta" kinyi shiru ina miki magana, "ko zaki ce baki gane wa nake nufi ba?Kin manta Nazeer saurayin Mamy da suka hada soyayya da wata ta daga karshe ya kita ya koma gun ta?ko zakice Baki tuna wacce tasa aka mana A tule ba lokacin bikin Hafsa dan mamy tai mata tsaki??Ita tuni ta hau zufa,,dan tuno da wacece BARIKI,,tuni ta mike,,ta kade in har mijin ta ya auro mata BARIKI,,tasan koda kwarkwasa saita Kore ta a gidan nan,,ta zauna," Qawata meye abun yi??ta zam,,"ki fara tada mai wuta tukun na,,na 2,gobe yana fita muhadu muje har gida muci mata.. Dama wlh har yanxu ina cike da a tulen data sa aka mana. Haka ta barta kan sai goben. Sai 10da kwata ya shigo gidan,,kamar yadda BARIKI Tace kuwa tana ta zarya a parlour,, da Dane,ko 8 ya shigo tana daki a kwance,,tuni ta yai kicin kicin ya hade rai,, tana ganin haka gaban ta ya fadi,,kan tai magana wayar shi tai kara,ya kalle ta a wulakance yai tsaki kan ya zauna a kan kujera yana murmushi,, "BARIKI,.. Yai dariya tamkar ta fada mishi wata Kalmar mai dadi,," kai ke ai ta daban ce,,yanxun dawo wata,, yai dariya yana Shafa haba tare da kallon yadda Matar shi ta daura hannu aka,,"nima tamkar na dawo inajin wannan tattausan muryar taki mai mantar min da komai,..yai Jim halamar yana saurarar ta,,ya kyalkyale da dariya,..tuni Matar ta sau kuka,,ya kalle ta ya watsar,,"Dan Allah asa ranar auren nan da wuri,,..ji yai an warce wayar hannun shi,, ya bita da kallo,tuni ta fara ban bami "Wlh ta Allah ba taki ba,,Banza karuwa kawai,,daga chan tai murmushi kit ta kashe wayar..a razane ya tashi,ya warce wayar shi,," wlh in kika kuma zagin masoyiyata a gaba sainai mugun saba miki,,"mey kika Iya ke in banda kullum ki bata min?sannan na samu mai wanke min zuciya da tattausan lafazi ki zage ta?? Kai ta girgiza mai "Dan Allah baban Najib kai hakuri,,wlh na daina,, ka rabani da BARIKI,, gwiwa biyu ta zauna tana rokan sa..ya fizge rigan shi tare da wuce wa daki..,,yana shiga ya danna sakata ya hau dariya.. Yaushe rabon sa Aisha ta mai abu ta bashi hakuri?? Kai ya manta,sai yau a dalilin BARIKI.. Yana son Matar shi.. Amma duk ta sauya hali..zai juri ganin ta a haka har yarda BARIKI tace By FeenaJa'afar & Hauwa Damary [12/24, 12:54 PM] Feenat Ja'afar. BARIKI...IYAWA 10_Ya danna kira ya sanar ta ya akai,"ka barta zuwa gobe da safe,,nasan zata ce zata zo wuri na,,ko tasa azo,, kai mata gargadin wannan kan ka fita,,. Washegari ma bai sauya ba,yau Aisha harda su gaisuwa, wanda rabon ta da yi tun Kan ta sauya hali,, yai mata banza,,zai fita cikin sanyi tace baka karya ba,,ya harari wajen abincin, "No zan karya a waje,,sannan ban yarda ki daga daga nan ba,zan Iya dawo wa kowanne lokaci.. Yai waje yana dariyar keta,,a kujera ta zube,,tunda take Abban Najib bai taba mata haka ba,,Wai har abinci bazai ci ba.,ta share hawaye,Kila ma wajen BARIKI zai ciwo,,kai amma su salma sun mata huduba marar kyau,, gashi ta kwabe mata,, waya ta dauka,kan ta kira salman," karki zomin gida,munafukai kawai,,kit ta kashe wayar ta,, yanxu ta ina zata fara? Acikin kwana 2 duk ya sauya mata hali,Waya da BARIKI, text kuwa ba'a magana, ranar yana wanka ta saci numbern bariki a wayan shi,da sauri ta fita,,sai sa ya yay kan ta kira BARIKI,, a yangance ta dauka,, "Amm Aisha ce,,tai far " wacce kenan? Duk ta rasa abun fadi, dan ji tai ta mata kwarjini tun a waya..sai kawai ta kashe,,.bashi ya dawo ba sai azahar,, kuka ya same ta tanayi reras,, tana ganin shi ta tashi,, dan dazun nan aka kara karanta mata wace BARIKI yar unguwar su,,"Baban Najib,,dan Allah ka auri kowa banda sa'a,, kayi hakuri bazan kara ba,, ya kallo ta kamar yai dariya.,a ranshi yana tunanin "Wai meye da BARIKI ne da yasa mata ke tsoron ta?? Ya basar" Gaskiya bazan Iya fasa auren Sa'a ba,, dan tun yanxu tai min alkawarin zaman lfy da kwanciyar hankali,, bazan fasa ki koma min yar gidan jiya ba.., tuni ta hau rantsuwa ta daina,inta kuma ya auri BARIKI,, da wannan ya samu lfy a gidan shi,,yace da yamma muje zan raka ka.. Yamma nayi suka je gidan su BARIKI,, a lokacin tana gida ana drama da ita,,wani kanin kakan su yazo daga Nguru,amma irin in za'a bi da aure tsakani,, yazo akan lalle lalle BARIKI ta fidda Miji,,tunda fadeela ta fitar,,tuni ta fitsare "Ni fa banni da tsayayye,, atoh ko ina da wallahi ba zanyi aure yanxu ba,,baki ya saki har iyayen suna kallon ta,, dake bala'eene yahau ta da masifa,," kedin wa?dama duk iskancin da kike tatawa a garin na samu lbr,toh dole ki tsaida haka ki samo na aure,,ta kalle shi, "toh na tsaida,,yai murmushi," ko ke fa,,a ina yake?ta hade rai,, "kai man,, ba shiba hatta iyayen sai da suka zaro ido,, ya tashi," ke banson iskancin banxa,,Tuni ta fara burburwa tana kukan gaske,,"ni wlh kai nake so,, kuma kai zan aura,,baban ta ya doka mata tsawa,"Sa'a bama son iskanci fa,, "ta kara jiniya" wlh shi zan aura,, ni shi nake so,,tuni tsoho ya sau kuka,,Lalle ya yarda BARIKI ce yan nan,, kuka yake yana"Allah ya isa saude,,ki kalle ni kice ni zaki aura?jikar jika ta?cikin kukan karya tace"Toh Haram ne?nidai kai za'a abani, ba shiri yai hanyar waje yana goge kwala, "InshaAllah anyi na karshe,,da sauri baban ya bishi," Baba kai hakuri ka dawo,,dole ta bi umarnin ka ai,,har suka fito kofar gida tsoho na kuka"ai ni ba ruwana da harkar yarka daga yau,,Ashe da gaske "BARIKI ce haka??Wai ni zata aura??Alhj Muktar suka kalli juna,tuni dariya tazo musu,,a karshe dole baban tasha ya raka shi ya koma inda ya fito..yana fita ta ware tana dirkar dariya.. Ladi ta fara tafa hannu,ta nuno ta da hannu" anya Sa'a,, ta kallo Maman tasu,"mama mey nai? Ta kar kade jikin ta,, ta sauke ajiyar zuciya "ba komai Sa'a,, Allah ya shirya mana ke.,tace " Amin.tai waje wajen kiran ta,,. Dariya ta samu suna dirka, tana ganin shi ta gane shi,,tuni ta hau murmushi, "yau an tuno Haj Ahmad? Yai murmushi" Manya a Baku naku daban,ttai wani fari,,tuni Alhj Muktar ya gyara tsaiwa, kai shikam BARIKI ta mishi,da aure ba contract ba. By FeenaJa'afar & Hauwa Damary [9/13, 8:10 PM] ๐Ÿ’๐Ÿ›๐ŸฌSalma๐Ÿฌ๐Ÿ›๐Ÿ’: [6/2, 5:38 PM] Feenat Ja'afar: Feenat Ja'afarSalma๐ŸฌSalma๐Ÿฌ๐Ÿ›๐Ÿ’: [6/2, 5:38 PM] Feenat Ja'afar: Feenat Ja'afar๐Ÿ›๐Ÿ’: BARIKI...IYAWA 11_Abinda ya kawo su suka sanar mata,tai murmushi, da gani mutumin zai sau hannu, tuni ta yarda,Alhj yace da daddare zai dawo,sai su tsadan ce,,tai murmushi, dan tuni ta harbo jirgin shi,,kai ta kada,,sukai sallama tai gida,,Maman su ta kalle ta, "Sa'a, ta zauna tana amsa wa,," In tambaye ki man?tai murmushi, "toh mama, tace" ke ko tsoro bakya ji wataran wata tai miki illah akan mazan su?tai murmushi, "mama Allah bazai bawa kowa galaba a kaina ba,,kedai kimin adu'a,.. Ta kada kai" Yauwa, dama ina son fada muku,makaranta zan shiga,,cikin satin nan,, Maman ta kalle ta da mamaki,,Wai yaa ita take wa kanta komai tamkar da namiji mai aiki,,in bata manta ba, kwanan nan aka kawo takardun gidan Sa'a data siya da kudin ta,, ta girgiza kai "Allah ya kara kare mata Sa'an ta a ko'ina. Washegari plan ya fara,Alhj Muktar ya sanar mata Matan shi zasu walima,ya gaya mata lokaci da venue,, tuni ta gama tsara komai,, a chan unguwar da ke gaba dasu ne,,Bikin na manya ne,,an ciki kowa ya zauna a kan kujera mai gaba tar da walima kawai ake jira,,filin gidan babba ne,yadda in mutum ya shigo sai ka kare mishi kallo bai karaso ba,, tunda mota ta tsaya ake kallon bakin kofar,, sanye take cikin wata bakar Riga da ratsin purple doguwa kirar Dubai,, ankai tela ya kara fito da shape dinta,,anyi tuntu a ka da gashi da rabons manya,, tai nadi tamkar balarabiyar asali,, ga wani katon glass fuskar nan ta Gaji da make up,,hand bag dinta da wayar ta tasa cover da takalmin ta duk iri daya,tana zuwa wasu samari sun sha bakaken suite,da ganin su kasan bodyguards din ta ne, da suka bude mata motar suka bude mata gate,, daya ya bata jakar ta ta makala a hannu, daya ya bata phone nata,,tuni ji kake tsit waje kallo ya koma gun BARIKI,,ta tako, suma bodyguards din suka biyo ta,, da hannu ta musu sign dasu jira ta waje,,wata a wajen ta zunguri daya,,"Ita kuma wannan Matar wani Alhjn ce?kamar rada dayar ta rada mata yadda na kusa da su zasu Iya jin su,,"ke,in kinji ana BARIKI..IYAWA, toh wannan ce,,Matan guda 4 dake kusa suka kara kallon Sa'a,, Matar ta cigaba "Bazawara ce, sai dai manyan zata aura,,Budurwar wani dan siyasa ce,koh Alhj mukhtar naji ne??tuni 2 kusa da ita suka juyo,,sai dai sun kasa cewa komai,, ta cigaba, "ta taba aure,tana shiga Saida ta fidda Matan da kissa da tsabar Iyah BARIKI,, dayar ta kallo ta,," toh ke ina kika Santa?ta rike haba"waye besan BARIKI ba a tsuku kun nan?ai in kin ganta a hanya kina tafe da mijin ki ko saurayin ki boye shi,,dan maza idon su,,idon BARIKI,.. Ta zungure ta kamar gaske,,"yi shiru gat nan zuwa,,in an fita zan baki komai in details.. Suka kada kai,, Sa'a ta zauna tare da daura kafa daya kan daya,, tuni wata ta kusa da kujerar da ta zauna taja wani mugun tsaki,kan ta dau kujerar ta ta sauya waje,,Sa'an ta bita da kallo a takaice, da sauri ta sake bin Matar da kallo,,kamar ta taba ganin ta.. Matan Alhj Muktar suka bita da kallo,,suda suka shigo suna hararar juna,yanxu duk sun ware jin an anbaci saurayin wannan da kamar sunan mijin su,, wata yar safasafa ce tazo da kujera kusa da BARIKI,, "Shege BARIKI.. Tai wani mayaudarin murmushi,, kan ta furta" IYAWA.. Suka tafa,,"Yayi mai gara kan yan maza,.ana haka mai walima tazo aka hau waazi. By Feenat Ja'afar & Hauwa Damary [12/25, 12:19 PM] Feenat Ja'afar BARIKI...IYAWA 12_Tun ana raba take away uwar gidan Alhj Muktar taje wajen Matar nan mai tsaki, Matar abokin mijin su ce,,suka kebe da kujera,bayan sun gaisa take tambayar ta"Ni Maman Abba kin San yarinyar chan ne??ta tabe baki "nasan ta, muguwar bakar kilaki kenan,,ni ai bazan manta fuskar ta ba,,duk da yanxu ta kara girma, tunda ma in kina Neman karuwar hanya,toh ki nemi waccan,ta sake kallo BARIKI, ita wayar ta take,tana ta wani lumshe ido,, ta dawo da kallon ta kan Maman Abba," mey ya hadaku? Tai murmushin takaice., kan tai kwafa "akwai wani lokaci da muka je super market nida Alhj siyayya,, anan muka ci karo da ita,,wlh Alhj baiya kallon mata barin a gaba na,amma yarinyar nan in kinga kwarkwasar data dinga mishi,,ke daga karshe mantawa yai dani,,tun daga ranar Yarinyar tai gaba dashi,,Asma'u waya.. Waya Asma'u,, inaga da ta gama tatike shi ta Kore shi,shine kwana 2 naji shiru,,tun daga lokacin na daina yawo da Alhj. Tai ajiyar zuciya, inko har da gaske Alhj ita yake nema dole taci uban yar nan,,ta gidan ma yata kare bare wannan yar BARIKIN?? Tashi tai ta koma wajen ta, kan BARIKI ta fita ta rigata fita,,tashin hankali, Wai gobarar gemu,,tabbas wannan CRV Alhj ce,,sabuwa da ko su ba'a kaisu unguwa a ita,,ta cije lebe" Tab, wato tun kan ta shiga har ta fisu ikoh?ana haka Drivern su yazo, dai dai BARIKI ta fito,, da sauri bodyguards dinta suka zo,suka karbi Jakarta da wayan ta,, da mamakin ta sai ta ga drivern nasu yayi wajen BARIKI yana kwasar gaisuwa,,amarya ta fito,,taga lokacin da Bala driver ke gaida BARIKI harda bata abu a Leda,,ta kalli uwar gidan nata a yatsine,, "nifa ban gane lamarin nan ba fa M Hafsa?? Ta kallo ta da takaici,, " zaki gane in munje gida,,sukai wajen mota amma Bala driver bai taho ba,,tai wajen tare da doka mishi tsawa"Wai baka ga fitowar mu bane??ya juyo da sauri,."yi hakuri Hajiya,Alhj ne ya aiko ni gun amarya,,da sauri ta kalli BARIKI wacce take kokarin shiga mota,,da sauri tai wajen,, "Amaryar wa?bodyguard 1 yace ta Alhj,,sannan kiyi hankali kar wani abu ya faru anan,,dan ya tabbatar mana tsaron ta..taja tsaki" Dallah rufen baki,,nida Tsohuwar yar BARIKIN nan nake,,karon farko BARIKI ta kallo ta a wulakance,,"eh kin San ai Alalar Gero ce,wanda bai Iya ba ta kwabe masa,, tai mata wani kallon banza kan ta ce ya suja ta bata da lokacin ta.. Tuni suka ja suka bar amaryar Alhj baki sake,,magana 1 ta mata mai harcen damo,, ji tai tamkar ta kwala ihu,,a bainar jama'a an toya ta,,jiki a salibe tai mota,,bayan ta shiga ta kallo Bala"mey ka bata a Leda?uwar gidan ta kallo ta,, "kina da karfin hali Halima,,zaki kwace ne komai ya bata?tai kwafa," lalle Alhj yaso musu wulakanci,, har ya fifita wata akan su tun kan aure?uwar gidan ta kalle ta,, "ki bari muje gida muji dalili,,ko aure zaiyi,toh wlh bada wannan yar BARIKIN ba,,dan irin wayen nan suke daura ma hawan jini..tai kwafa.. Ana dire su a parlour suka tsaya,,yau daya suka zauna Neman mafita,," Yanxu Hajiya meye abin yi?ta kallo ta da mamaki,,dan rabon da ta kirata da Hajiya tun tana amarya,,lalle BARIKI mai sa ladabin dole.. Waya ta dauka,tace "Alhjn zamu kira,,yazo muji ta bakin shi,,ta girgiza mata kai" kar ki kira shi,,barshi yazo da kanshi,,ba tace BARIKI IYAWA bace?toh mu muyi amfani da damar mu ta Matan sa mu nuna mata kuran ta.. Tuni ta rada wa uwar gida abinda zasu mai in ya dawo..tuni aka manta da kishi aka hau Neman mafita. By Feenat Ja'afar & Hauwa Damary [12/25, 1:32 PM] Feenat Ja'afar BARIKI...IYAWA 13_Bai dawo ba sai kusan Tara na dare,tuni suka kara kulewa,, yana shiga ya gansu zaune a kujera 1 suna ta huci,,ba wanda yai wa magana yai dakin shi,,da sauri suka tsayar shi, Wai Alhj mai kake nufi?yaci mur, "danayi mey? "Kazo ka wuce ba ko magana, yace" ita sallamar ba magana bace?ko kun amsa?sukai shiru,yace"Ku bani waje..amaryar ta kara tare kofa"ai wlh sai ka fada mana wace Sa'a a gun ka da har ta fara shiga lamarin dangin ku,,yai mata wani kallo,, "Sa'a kuke son Sani? Ta kada kai tare da Rike kugu,,yai murmushi" itace wacce tasan na Gaji a barni na huta,,ita ke maraba daku a matsayin kishiyoyin ta da zata samu,,Sa'a, ta wuce tunanin ki a waje na,,ta tabe baki,, "wannan kai kasani, abu daya muka Sani, mudin Zaka auro wannan yar BARIKIN, toh fa tafiya zamuyi,, koh Hajiya? Ita dai uwar gida tsabar takaici ta kasa cewa komai,,yai murmushi, " zaku Iya yin komai, amma Sa'a kamar ta shigo ta gama,,Hajiyan ta tare shi"Alhj bafa zan zauna da Wannan kilakin ba wlh,,saboda tsabar wulakanci, Wai ita zaka fifita akan mu tun yanxu? Ya harde hannu"da akai mey?tai mai banza,,ya gyada kai kan yai daki,,amarya ta kallo uwar gida,,"Hajiya. Gidan su kawai zamu mu

Chapter 2 of 11