Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
7 / 11
cikin wata doguwar Riga ta net Golden da ratsin Orange,, sai ta temaka wajen kara haskaka mata fatar tai wani yellown kyau,,ga wani arnan Hill Orange da Pose ,,sai dan mayani data rufa a gefe,,Fuskar nan ta Gaji da kyau,Ko Zahra sai da ta firgita ba Hafeez, dan tunda biki ya karato ta fara gyara da dogon hijab da Nikaf take fitowa su gaisa..tayi kyau ainun,,ga wani tsadadden murmushi da take sakar wa,sabanin Zahra da ta nemi fara'ar ta ta rasa,,Hafeez ya tafi duka,,A ranshi fadi yake"Tsarki ya Tabbata ga Allah,, Ya ma manta da jama'ar hall din kamar an tsikare shi ya tashi,ba ko kunya yai wajen ta,,tana ganin haka tai saurin dukar da kai tana murmushi,Tuni aka hau flashes ta ko'ina,, in ran Zahra yai dubu toh ya baci.., haka suka jera har mazaunin su. By Feenat Ja'afar & Hauwa Damary [1/19, 2:25 AM] Feenat Ja'afar BARIKI...IYAWA 42_Ta dan kalli Zahra a takaice,sanye take da Baki da Arsh na net itama,tai mata kyau,kamanin ta na fulanin usul ya fito,kai inba kallon tsoro ta mata ba sai tace suna yanayin kama da Hafeez, Ta sau mata murmushi cikin kissar ta,,A Yatsine ta jutar da kai,dan bazata juri ganin Sa'an ba,,.Kai ita sai yanxu ma take da na sanin zuwan ta Dinner... A Bangaren Sa'a, tun daga kallon da Zahra tai mata tasan zasu dama.. Wannan shine karo na farko da taga Zahra,,dan koda sukaje gidan su kin fitowa tai su gaisa,,. Har aka tashi Dinner Zahra bata cikin walwala,har Aunty maryam yayar Hafeez ta fara mata nuni da hannu kan ta saki fuska,sai dai ina,ji take kamar ta sau ihu,dan tadin su suke tamkar rada rada,,ga wani munafikin murmushi da suke sakar wa juna,,koya juyo kan tasa baki sai dai ta tabe baki,, Tuni ta kara jin haushin Sa'an a ranta.. Yai yin Duniya dakyar ta shiga mota Wai shi zai kaisu da Sa'a, ganin Sa'an ta hakimce a gaba,yasa ta ja Tasleem suka shiga baya tana turo baki,,Zahra ya fara sauke wa,wanda dama Allah Allah take ya sauke ta,,Sa'a ta dago mata hannu halamar bye bye,,"Sister good nyt,,Tai mata banza tare da doko kofar,,Duk yana kula dasu,,Sai dai ganin Sa'an ta cigaba da fara'ar ta yasa bai ce komai ba,, Tasleem ta kallo su,,"Kai Matar yaya kin ganki kuwa??Ta kallo Hafeez ya kashe mata ido 1,,da sauri ta dauke ta dawo da kallon ta Tasleem,,Tace "Na kai Yayan ki kuwa??..Tai dariya,," Kai Aunty na kin fishi,,Wallahi u look so Gorgeous..Kunyi keda aunty Zahra...kai Bros kai samuwa,..Suka kyalkyale mata da dariya,,.Sai santin Sa'a suke ita da Yayan nata,har abun ya fara bawa Sa'an mamaki,ganin basuyi wa Zahra haka ba,kuma Bilhakki tai kyau itama.,Kai badan Tasleem ba,yau da sai 12 zai tafi,dan bai Gaji da kallon sahibar ba.. Suna tafiya ta makawa Aminu kira,yana dauka ya hau mata tsiyan nashi,,chan tace" Abu daya zaka min Aminu, yace "ina jin ki amaryar mu,,tai murmushi, kan tace,,"so nake kai duk yadda zakai na rigata zuwa gidan Hafeez.. In kamin wannan kamin komai a rayuwa.. Yai murmushi.,Dan tuna wa da Hafeez da yai,Shima dazun ya gama mai mitar su fara dakko Sa'an shi, dan ita yake so ta zama uwar gida..Da karfe ya furta "Done.., Kaga uwar gida sarautar mata..ta kada idanu tace" Dadina da kai Aminu akwai saurin gane karatu..suka kyalkyala dariya..Ummi ta karba. Washegari da misalin 10am aka daura auren Zahra da Hafeez,kan suka rankayo Gidan su Sa'a,, Murna a cikin Hafeez sai an tona,,Wai yau shine mallakin mata 2? musamman Sa'an shi??,,.Wayyo dadi,banda godiya wa Allah babu abunda ya ke. Da yamma kwa Aminu ya cika alkawari, sai da suka jera motocin daukar amarya kan suka cewa su aunty Maryam Wai suzo su kai su za'a karbo amanar Sa'a, duk da Hajiyan taso ranfo su,dan a dole ita fa Zahra za'a fara kaiwa,yadda aka fara daura auren ta. By Feenat Ja'afar & Hauwa Damary [1/19, 3:39 AM] BARIKI...IYAWA 43_Kwarai su Aunty Maryam sunji dadin karramawar da dangin Sa'a suka musu,,kayan gara nasu turum haka aka yi musu tsaraba,zo kaga kukan tausayi wajen zahra da mama da Baba,kai ko tafiyar Fadeela basuyi haka ba,,musamman Baba,,haka ya kankame Sa'an shi suna kuka yana mata fadan ta zauna da abokiyar zaman ta da mijin ta lafiya,,Aunty Maryam sai murmushi take musu,Gaskiya familyn Sa'a ita kam sun mata,dan ta fuskan ta akwai Tarbiya...Da kyar Aunty Maryam din ta banbare Sa'a ita da Fadeela,, suka kai amarya Gidan ta,, Dan gin su Zahra basu kara barke wa da lamarin ba Saida suka ga Wai anyi sama da amarya,,wato sama ya bata ya ajiye tasu a kasa,,Dan su basu zo Jere ba,dangin Baban su ne,suma maza kawai,,Aunty Maryam ce kadai bata tabe baki cikin su,kowa da abinda yake tofa wa,,basu gama mamaki ba sai da suka dira bangaren Sa'an,, a haka suna musu kallon talakawa zo kaga uwar dukiyar da aka narka mata,,dan mai gidan Baba ne ya dau nauyin Gado,wani dan uban su Chinese bed milky brown,,komai na bedroom din milk n brown,tsarin ra'ayin Hafeez kenan,,yana son daki haka ko Blue.. Parlourn ta kwa an zuba wasu uban su kujeru ledar, green ne da ratsin dan milky kadan,sai grass carpet Shima green da milk,center table da wani dan tray an sa mishi Apple na roba masu kyau greens,sai Set na kayan kallon ta na plasma screen TV katuwa,flowers ne masu design din Royal tree,,sun kawata parloun sosai,,ya sanar ta bai son tarkace a parlour,shi yasa ta sanar da yan Jere fridge a kai mata kitchen,, show glass asa ta a daki,,.. Su Kansu dangin Zahra baki suka saka dan ganin komai yaji cikin tsari da wayewa.. Sai dare aka kawo Zahra,,abinda ya kara burge Sa'a ta kuma kara tabbatar da Lalle ita ne uwar gida shine, ana zuwa Saida aka hauro da Zahra saman ta,aka musu fada su zauna lafiya,tunda itace Babba,,Tuni Zahra ta kulaci su Aunty Maryam,,ya zasu ce Wai itace Babba, bayan ita aka fara daura aure da ita?? Kowa ya watse sai tsiraran Qawayen amare da Tasleem data makale a dakin Sa'a, dan tun Ran sakun Lalle take hararar ta, Wai dan taje Sa'a tasa an mata Lalle..Fanfo kawai Qawayen Zahra suke mata,Wai sai ta tashi tsaye,dan kishiyar nan tata Lalle da gani kam yar BARIKIN Asali ce. Ango yazo bayan yan rakiya sun rako shi,suka wuce da Qawayen Amarya,Ya kira Zahra sama,Da kamar baza ta zo ba,sai dai ganin yana jiran ta,, Komai na Kayanta Ja take da muradi,,Sunyi kyau sosai,dan auren Gata aka mata,musamman da take yar fari,,Sai dai duk da ken nata tana zuwa saman na Sa'a ta sau baki,,amma Lalle an mata ba zata,,Saima taga kamar sunfi nata haskuwa,,Ya kalle ta,, "ki zauna bari na kira Sa'adan,,ta tabe baki kan ta zauna.,yai ciki yana ta zumudin arbawa da sahibar shi,, Akan sallaya ya tarar ta, ta daga hannu sama tana mai kwararo mishi godiya daya nuna mata itama ranar ta,tana mai fatan Allah kawo na yan baya. Murmushi yake yana mai kara yaba halin Sa'a, tabbas yasan yai dace,Sa'an shi da ya kira da "Unique,,Ta juyo tana mai murmushin kunya tare da dukar da kai,,ya kare wa dakin kallo,komai yayi kamar an tambaye shi,,takowa yai tare da tsuguna waa gaba ta..Hannun ta ya kamo ganin taki tashi,Karo na farko da ya fara gigin taba hannun ta,,Wani irin abu yaji yana tsirga mishi,,yayin da ita ma taji makaman cin haka...ya sauke ajiyar zuciya,a hankali ya tada ta tsaye "Muje parlour ina son magana daku,,Ta kada kai. Bayan ya bude taro da adu'a ya fara musu bayanin abinda yasa ya Tara su,sannan da fadan kowa ta zauna da kowa cikin Aminci.. Ya kallo Zahra.." Sa'a uwar gidan ki ce,so duk wani girma natane a gidan nan,,kiyi respecting nata..ya juyo gun Sa'a,, "Amm Unique, ta kallo shi da murmushi, Shima ya maida mata,," Ganan Zahra,duk da nasan kin dauke ta a matsayin yar uwa,pls ki kara akan Nada..Ta daga mishi kai,,Ya kallo Zahra,"Da mai magana??.. KAMAR jira take kuwa tai zaraf.."Nifa ban gane ba da naji ana kiran ta uwar gida na?? Ina ce ni aka fara aura kamin ita?Ya kallo Sa'an, ita kuma tana kallon zone tare da kokarin cire wa..ya dawo kan Zahra.. "A ka'ida,wacce aka fara kawo wa ita ce uwar gida, bawai wacce aka fara aure ba,,Am I clear?Ta kara tabe baki tare da hararar Sa'a ta gefe,,ya cigaba," So tunda kin fahimta,My Unique, ta dago kai,"Kwana nawa kike ganin za ana yi?Ta kalli Zahra, "Sis, nawa nawa yake tambaya?Da sauri Yace" Ok, sorry,,Nawa kuke ganin za ai??Sa'a tace 2 sai Zahra ta rigata da sauri.."Uku yayi,,Ya kallo Sa'a, "Unique 2 naji kince ba,,ta kada kai tana wani yauki,,yai murmushi kan ya kallo Zahra data kule,"biyu it's Ok,dan zai fi min nima,,ya kamo hannun Sa'a," Yayi ba?Ta jijjiga kai, ya dawo kan Zahra, Tuni ta mike,tace"Yadda kuka ce,Yanxu sai ka taso a fara ta kaina.,Da sauri suka dube ta,har Sa'a na Neman dariya,,yai murmushi A ranshi yana"Lalle hasashen Fodio gaske ne,da Yace duk dangi ba mai fitsarar Zahra. By Feenat Ja'afar & Hauwa Damary [10/2, 7:20 AM] Feenat Ja'afar: [1/21, 5:19 PM] Feenat Ja'afar BARIKI..IYAWA 44_Ya sake kallon Sa'a, ta mike itama tana wani rausaya "Baby ka raka ta,Kila tsoron sauka take,,yai murmushi ya kallo Zahra,da zumudi ya mike," Atoh muje na rakaki ki kwanta,,na ma manta ne,,Baki sake kawai take kallon Sa'a, wacce tai hanyar daki tana tafiya tamkar hawainiya,,Da sauri ta juya tai kasa tana hawaye,, Hafeez yana kiran ta ko oho,,ya tabe baki,, In ta shine dama bai son motsawa yau ko kadan a wajen Sa'an shi,, da azama ya dau abinda ya taho dashi nata ya shiga da sallama,, kai duke tana sake mamakin karfin hali irin na Zahra,,Wai kuma a haka gaba da bayan ta bafulatana,, wannan Ai bada kai ne ma wallahi, sai ta Rena mata wayo ma,,. Duk kan wani ala'ada sun gabatar cikin wayewa,,a yau,yasha mamakin Sa'an shi akan ilimin addini,,Dukkan wata Amsa gamshasheya ya same ta game da Sa'a, murmushi kawai yake kara mata,,jin yadda take fidda harrufa kowanne da hakkin shi,,babu ta bangaren da Sa'a ta Gaza mishi,.. Kyau Ilimin addini Ilimin Boko Wayewa Ga Iya zama da mutum, a yau kadai yasan zatai adalci,. Hmm Bariki ce Hafeez. A gaskiya shi bai taba jin salon kamshin Sa'a ba a Duniya,,duk inda ta gifta kamshi ke tashi, ga wani shining da ta kara yi,ansha wankan lalle da madarar shanu,,ita kam tana girma ma abubuwa Natural,, Yabon kyaun ta yake,har Saida ta fara jin ko ta zama wata Queen ne,,laushi da santsin fatar ta ya kara hura wutar da ke ruruwa a sassan jikin shi,, ko da da yai zaman waje yasan ya tsallake dokokin Allah, burin shi yai aure kamin ya mallakawa Matar shi ta Sunnah dukkan kaunar shi da gaskiya,,komai karo da karo,,sabbin shiga,duk sai ta gigita shi,, dan tabbas tasha gyara Iya gyara,,Wannan dare a gare su sun ware mishi shafi daban a rayuwar su,,Duk da tai juriya,amma Hafeez din ta sai Da yasa ta data sanin gyaran datai mai yawa..Waras ta samu yabo da kirari wanda har yanzun da take kan sallaya murmushi take in ta tuno su,,Bazata gushe ba,tana mai alfahari da kai Budurcin ta gidan Miji,,a ganin ta, duk wani ji da kai,ko isa a gun Y'a mace,Toh Indai ta tsallake wannan siradin,toh she's lucky,, In ta tuno da Daren jiya.,sai taji tana fatan Ina ma ita kadai keda Hafeez? Ina ma ita kadai ya zama mallakin ta.,Bata zata ba taji hawaye ya taho zirrr,,Kan ta goge taji hannun mutum,,A tsorace zatai baya ya ruko ta,, Ta tsinne kai a jikin shi tana sauke ajiyar zuciya,, dan shaff ya shammace ta bata ji ya shigo ba,,ya cikata yana murmushi, murmushin da tun jiya yaki ya kau a fuskar shi,, lalle bai ji kom ba da ya kira Sa'an shi da "UNIQUE"... Zame wa yai ya kwanto a cinyar ta, Tuni ta kara sunne fuska cikin kunya,," Ina kwana??...murmushin shi ya karu,ba tare da ya amsa ba,shafo fuskar ta yai,,Yace"Ya kike??Ta kada kai itama da murmushi, tamkar sirikan juna haka suke ta murmushi, sai dai shi daga Ya shafo fuska, sai sumbaci hannun ta, lalle ya tsaru a fatar ta,,Sa'an shi Zuma ce,,ta kuma harba mishi Sonta,,ga ta da wata Ni'imar dumin jiki da Allah ya hore mata,,shi yasa yanxu kawai burin shi yaji shi jikin Sa'an shi,, ko hannun ta ya taba Dumi ne,,yaja doguwar ajiyar zuciya,, ji yake tamkar ya maida ta ciki dan So,,kokari yake ya kalli fuskar ta su hada ido,amma fir ta ki,,Yana matukar mutunta mace mai kunya,,shi kyau ma take mishi yaga mace tana kunya..Indai jiya ke bata kunya toh,dan ko shi yasan ya kasa Sarrafa kanshi,,amma yasan akan Sa'a ne,,don abu ne ya kuma hadu Da Tsantsar so...Hannun ta yakai hanci yana shakar kamshin su,,tai murmushi,,har kunnen ta ya Gaji da yana kamshin nan. Ita kwa Zahra tana sauka daki tai tai ta rubzar kukan ta son rai,,Lalle Hafeez, tun yanxu ya fara rawar jiki akan wata karuwar Banza,,Da sauri ta tashi ta goge hawayen ta,Zubur ta mike,Kamar wacce aka tsikara da allura,ta zuge jakar ta,. "Dani kike zance,,guntun titi kawai,,Ta fara kade kaden magun guna tana sha,,duk tasan an mata gyara a gida,,"indai ta nan ne,Ai Sa'adatu Sorry,,dan wallahi sai na maida ki Mowa,,Hmm Lalle Zahra,Sa'a Ai ta Riga da ta kafa Govnatin ta. By Feenat Ja'afar & Hauwa Damary ®ONLINE HAUSA WRITER'S. [1/21, 5:21 PM] Feenat Ja'afar BARIKI...IYAWA 45_Bacci suka koma,cikin daddadan sanyin safiyar,, Sai 10 suka tashi,Shima ji tai ba mutum a kusa da ita,,sanye yake cikin Farar shadda, an mata aiki da brown din zare,,ya daura hulal shi yar zanna brown da milky ajiki,,sai kamshi yake tashi a jikin shi,, ta lumshe ido a hankali ta kara budewa,,yai mata kyau ainun,,Ta mika mishi hannu da Shagwaba,, bai wata wata ba ya kamo,,Tun jiya yake shan shagwaba, gashi Aminu sai waya suke mishi zasu gaisuwar sirikai,,ya sumbaci hannun ta,, "Ga abinci Hajiya ta aiko,,En Aminu suna ta kira..Ta rausayar da ido,," Ai da ka tashe ni,,yai murmushi,, cikin 10 mints tai dan wanka,ta shirya cikin Brown less, da ratsin milk,,Batai wata kwalliya ba,dan sauri suke,,Ya sauka ya tarar da Zahra har ta gama cin nata,,ta hakimce a kan kujera tana kallo,,doguwar Riga tasa ta Attamfa, tai kyau itama,,sai dai a hakika ba kallon ne a ranta ba,dan tun da ya kwankwasa mata kofa tai sallah ta kasa koma wa bacci,,hatta hawan shi sama ta gani bayan ya bude an kawo abinci,,. Rike suke da hannun juna suna murmushi, sai wani langwabe kai take a kafadar shi cikin salon ta,,Tuni Zahra ta fara cika tana batsewa,,taja dan karamin tsaki ta cigaba da kallon ta,, Hafeez ya kalle ta,,"A Zahra,,kin tashi ne??Tai mai banza,, Yace"Magana nake fa??kan ta daga kai,.Ko gaisuwa babu,, Wai ita a dole sun bata haushi jiya,,Sa'a tai murmushi, Lalle yarinyar nan batta da wayo,,dan tsabar ta kara bata haushi tace"Sister in kwanan mu?Zahran ta kallo ta fuska a tamke, Lalle Za'a gwada mata BARIKI,, sai ta dauke kai ba tare da ta amsa ba,, Hafeez ranshi ya baci,cikin fada Yace"Ke baki Iya gaida mutane ba sai mu zamu gaida ki??Ta kallo shi, ganin ya fara kumfar baki ta gaida shi yai mata banza yaja Sa'a kan dining,,Tashi tai ta tafi daki,tana"kar ka amsa,a ranta.. Sun ciyar da juna cikin kulawa da kware wa a so,,yana fita ta rufe sauran tai sama tare da tsantsara hadaddiyar kwalliya,taja dauri,,. Da akwai wuta ta sanya turaren wuta tare da kullo glass din saman dan kar ya fice,,ta shiga ta hau gyara har ta gama ta kira mama da tsabar kewar su..tana in Fadeela tazo a bata sakon. Tana sama taji hayaniyar baki,,Ta fito tare da daga labilen jikin glass din kadan,,su Aunty Maryam ne da wasu dangin su Hafeez din baki da sauran cousins din su,suna gaisawa da Zahra da tai zirif ta fito parlour kar a bata mata daki,,Tana ganin dangin su ne ta fara yake baki suna fillanci,,Dan autan Aunty Maryam Habeeb mai koyan tafiya,yaron mai kiriniya ne sosai,,Yana sauka yai wajen TV stand din ta,,ba kunya ta debe remote din ta tana nifa kar kamin ta'asa,,Sa'a duk tana kallon ta,, duk da batajin abinda take fada,ta kalli yanayin Aunty Maryam,Duk da yake take amma in ka kula zakaga ta sauya,,ita kam Tasleem dama binta kawai take da ido,,sai ta kashe kallon ma duka,,tana cigaba da musu tadi,,ita mai yan uwa harda fada musu abunda ya faru bayan tafiyar su,,kowa kallon mamaki yake Binta dashi,,mamaki suke Zahra tamkar ba yar gidan Aunty Sadiya ba,,wannan Ai abun kunya jiya ta tafka,,Sa'a taga tana dai ta kumfar baki,sai ta sauke labulen ta ta fesa Air weak,,ta hakimce a parlour,, komai take kallo cikin tsari an jera mata,,Tai murmushi da ta tuna da Hafeez din ta,,Yace "Komai Unique kamar kin tambaye ni tsari na...kwankwasa glass din ne ya dawo da ita,ta kara kallon kanta jikin glass din kan ta bude,,Da fara'ar ta ta tare su,," A Aunty,,Sannun Ku da zuwa,,Qanwata,,Tasleem ta wage baki,,Habeeb yana ganin ta ya bangale baki,,ta mika hannu tare da karban shi tana"Oyoyo Habeebe nah,, Missed you,, Tuni kwa Aunty Maryam din suma suka hau murmushi,, da fuska duk ba fara'a,, tun zuwan ta take son yaron lokacin da taje gaida ta,,. "Bissmillah., Ku zauna,, harda yan tsofi 2,da jiya basu zo kawo amare ba yan uwan Baban su Baffa Modibo,,saboda haka Tuni tai kasa su kuma suka zauna a kujera suna yaba tarbar data musu,,da girma mawa ta gaida su,, Saboda haka fuska sake suka amsa,,barin ma Aunty Maryam,, ganan Habib sai tsayuwa yake a kanta yana tabo daurin dankwalin ta,,chakulkuli ta fara mishi a wasa,sai ta dau hankalin sauran yaran,,data tashi sai suka biyo ta,, Lalle,Shimfidar fuska,tafi ta Taburma,,Ta kwala kiran Tasleem a hankali,. Takwara cire gyale ta ajiye a kujera ta bita kitchen,, Aunty Maryam ta kalli yan uwan nasu da cousins din ta,," Allah yarinyar nan yar mutunci ce,,ga Waccan uwar fitsararrun tarbar da ta muku,,ko ruwa babu sai shegen mita ya Taga courtu,,.. tai shiru ganin su Tasleem,,Tasleem dauke da Cups na glass, Yayin da yaran ta basu flates guda 4 cike da hadadden Doughnuts da cake,ta bawa Habib exotic babba daya ya rike,ta debo wasu Drinks din da ruwa a flats,,"Aunty kuyi hakuri mun barku,, Tana murmushi tana tsiyaya musu,,kamin ta mika musu,,Tashi tai ta kunna kallo,,Ta kallo su Inna Balki,," Inna Wanne kuke so,,Inna tai murmushin jin dadi,,tace"Muda zamu tafi,Ta kallo Maryam, "Mairamu kishiya ta na son mu jima hala,,tai murmushi, Kan ta kallo Sa'a," sa musu na Dan ibro,dan she really enjoy his Movie show,,Sa'a ta kada kai da murmushi, itama tana son Film din ibro,shi yasa ma ta siyo wani film da ya jima amma tana son shi,,NA MAMAJO...Ta kallo Habbeb daya kin kumo kwali ya kawo mata,,Wai ta bude mishi,,ta dau cup din Tasleem ta zuba mishi,,Tasleem tace,"Ganan su innan mu,jiya basu samu zuwa ba,,Da fara'a ta kalle su,,"Aiya,,Sannun Ku inna,,ya taro??suka ce Alhamdulillah, chan aka fara show na ibro Abin dariya,,Ta yafico Tasleem, tana tashi Habeeb ma ya tashi,sai glass cup din hannun yaron ya subuce,Tuni ya fashe,,Ta juyo da sauri tana"Subhanallah,Habeebe,,hope bakaji ciwo ba??Shima yaron duk yai kamar zai kuka,. By Feenat Ja'afar & Hauwa Damary ®ONLINE HAUSA WRITER'S. [1/21, 5:23 PM] Feenat Ja'afar BARIKI...IYAWA 46_Hanun yaron take duba wa,,Wai koya yanke,,Aunty Maryam ta taso,"Dama ban so ki bashi glass cup ba,,gashi ya fasa,Habib da kiriniya,,ta kallo ta,"Kai Aunty,ni tsoro na ma kar ya yanke,,ta Kar kade mishi jiki,"Aunty rike min shi na kwashe,ya make kafada,,Tace"Sorry yanxu zan dawo,,ta shafi kumatun shi lufulufu,,"That's my Boy,,Aunty tai ma Tasleem da ka kan ta karbo tsintsiyar,fir ta hana ta,ta share tai moping wajen,,Sai mamakin kirkin Sa'a suke,. 12 nayi ta bar su sukai kitchen ita da Tasleem, guntun kajin jiya tasa Tasleem ta sauka kasa ta dakko miyar cikin flasks din da aka kawo da safe,ta gyara ta ta juye kajin,,Tuni kamshi ya gauraye saman,,tai cous cous mai sauki,,ta taho da sobo ta daura a wuta ganin tana da kankara da cucumber data zo da ita,kan 1 da wani abu ta gama komai,,Ta dawo parlour sun gama kallo suna ta tadin su da fulanci, duk na yabon ta,,duk da bata ji,amma 4 sure tasan yabon ta suke,ganin yadda suke kus kus suna dariya,,Tace"Aunty su Inna kwa sun shiga ciki??Ta kallo ta da murmushi,"No,mai daki na kitchen Ai basa shiga ba,,ta waro ido,, "La,Ai ba komai,Inna Ku shiga Ku ga,,ta Jere musu abinci a flasks,sai ga su Fadeela da Ummi,,ana fara kiran sallah ta ta shimfida musu Darduma,,wasu suka shiga bandakin parlour, Tace wasu su shiga ciki,Ba kyama haka ta dinga tafiyar da su,,nan wajen ta suka kai sallah suka ci abinci hade da jin dadi,basu bar gidan ba sai da ta tabbatar da kowa ya tafi da kirkin ta a bakin shi,,. Ita kam Zahra qawaye na zuwa suka kule daki,,Inna ta leko,"toh mu zamu wuce,Fatuu ba dan karar kuzo kuga dakina ma koh?Tace" Au,Ku shiga,kudai tsofin nan sai ganin gulma,,Ita kam Aunty Maryam tai gaba da danta da sauran yara,tai ma Hafeez waya cewa sun fito ya dakko su inna,yaran sai murna suke ta basu chocolate,..A mota sai yabon Sa'a su Inna suke,"Kai Hafeezu kai dacen mace mai son Jama'a, sai son barka,Sa'a tai kaza,Sa'a tai kaza,,shikam Murmushi kawai yake,Tuni yaji Sa'a ta kara samun martaba a idon shi,Tuni ya kara share mata waje a cikin Birnin zuciyar shi,, tuki yake yana murmushi,, Sa'a, Sa'a, a ranshi fadi yake"She's d Best,,.Duk da sun ma manta da iskancin da Zahra ta musu. Suna dira,suka fara bawa Hajiya labari,,a ranta tana mamaki,da Wai suka kasa gano wace ce YAR BARIKI?.. Sai dai ta bisu da murmushi, amma ita kam Zahra ce ta ta,duk tsiya,,. In banda waya,ba abinda suke,ta kira,ya kira,Su Ummi sun tasa ta gaba suna ganin fi'ili iri iri a wajen Sa'a,,. A yanxu ma waya take,su da suke kusa da itama dakyar suke jin zancen,magana take tana wani kashe ido,kai kace Hafeez din yana gaban ta,, Ta ajiye ta kalle su,,"Ya akai ne Guys,irin wannan kallo??ta tashi daga kishingi den da take,,Ummi tai Murmushi, "Wallahi Ade tausayin Kishiyar nan taki nake,,Wai kishi da Ade BARIKI?? Woo, amma fa a dan mata sassauci pls,,suka tuntsire da dariya harda shewa, " Ke,in taso zan zame mata tamkar yar uwa,buh ta sake tace zata ja Sa'ada,, woo woo,sunan ta sorry,,dan Wallahi yadda nake jin Hafeez yanxu a kokan raina...Hmm kedai abar tone tone,but he's d best, ta lumshe ido,, Fadeela tace"Ai itama da ganin ta yar yi ce,kiga fa yadda take amsa mana gaisuwa tana wani yatsina fuska,nidai dan Allah kisa da hakuri kar ki biye mata.. Ta dallah mata harara,,"An fada miki kowa ma irin ki ne,,hakuri?? Ai ban ganshi ba,indai akan kishi ce,tana Dana min,wallahi zan Dana mata nawa,in ta rissina sai mu sai saita,,but bafa fada ba,No,BARIKI kawai,ya ishe ta,, Ummi tace "Toh Allah ka bawa Zahra hakuri,dan zamuyi kuli da ita,,tai wani murmushi," Ummi kenan,,ni Ai bana fatan haduwa da kishiya Lumbu lumbu,hmm wutar k'ai k'ai ce,,Bana son ajiye makaman yaki na da wuri,gwara wacce zamu dama a fagen yakin Ni ko Ke??..Kuma Allah ya bani,don Haka nake so,,ban son munafukar kishiya,Wai Ita mai hakuri,,. Ta kallo Fadeela,"Toh ke ya batun sanjan gida??Tai murmushi, "Kai Sa'a,Wallahi u r too much,, duk da kin sa Matar nan ta rissina,kinsan da bakin ta ta fada mishi Wai sai ya sauya mana gida,indai zaman lafiya yake nema,ba ko musu ya yarda," Tun kuwa da ta kalla taga cikin nan ta kara haukacewa,Ai sauri a sauya gidan nan,,,Tai kasa da kai,"Wallahi har tausayi ta fara bani,,Sa'a tai tsaki,,"Ai sai kiyi ta jin tausayin nata,,ke ta Tausa ki Ai,,Taje itama Allah ya bata rabon ta Albarka cin ki,Ai adalci ma na mata,dan kazantar da baka gani ba tsafta ce,kina ga in ta cigaba da ganin rawar kan da Alhaji yake akan cikin nan bazata hadayi zuciya ba??,,.Suka tafa "Baki kyau,,tace" Ko nai wanka,,Yanzu Ai ban fara komai ba Wallahi, zan daga mata kafa na fake da kunya ta sati guda,daga nan zan fara bude koli na a gidan nan, Suka tuntsire da dariya,tace "Kudai Ku rike dangin Miji,dan tamkar shi kuka rike,dan duk abinda kika musu zasu fada yaji,en tanan, wani sirrin rike wuyan Miji ne tamau in fada muku,,. Sai da suka Taya ta ta gyare gidan ta tsaf, sukai magriba kamin Suka tafi,direct wanka ta shiga,banda kamshin turaren wanka,babu abinda ke tashi,,Ta fito daure da Towel,ta cire hular wankan,Zara zaran kitson nan sun zubo mata kafada,ta gyara na gaban kan tahau kyali,tamkar wacce zata Dinner,,Ta dame cikin Riga da skirt din wata Holland blue da ratsin purple ajiki,,Tai kyau ainun,sai kamshi ke tashi na Amarya,,ta kullo Kofar glass din dan taji har yanxu Qawayen Zahra na nan,,tasau turaren wuta, Tuni yahau kamshin dadi,,ta feshe Air weak,tare da yarfa turaren Carpet da kujera,Tuni wani irin gamsashen kamshi ya kewaye saman,har yana dan ratso kasa,,. Kai Zahra sai fa kin dage,ji wannan hadadden kamshi,Tai murmushi," Lokacin ta ne,daga yau Ai sai ni,nayi imani in ya dani kunamar nan,sai wata ba ita ba,,Jumai tace"Toh tashi kiban kudi na,dan nasha wahala kan nasamu kayan nan,,.nan Ita tafi karfi,gani take tunda ba ita keda Hafeez din ba,Ai ba sai ta gyara ba,ita dai ta gyara chan.. Da zumudi ya shigo gidan,dan tun fitar shi yake mar Marin zuwa gidan,duk Sa'a ta gama kar kato da hankalin shi gare ta da daddan muryar ta a waya..Sai dai mey,yana shiga gidan Zahra na fitowa ta bata mishi budget,,. By Feenat Ja'afar & Hauwa Damary ®ONLINE HAUSA WRITER'S [10/2, 7:25 AM] Feenat Ja'afar: [1/22, 2:23 PM] Feenat Ja'afar BARIKI...IYAWA 47_Wai sai ya kai Qawayen ta gida,,A ranshi yana toh mey suke har yanzu da basu tafi ba??8 fa saura,,. Amma haka ya Nada,tana ta murna Wai ita ta fara danawa Sa'a Bom,dan tasan in har zai kai kowa gidan ta zai bata lokaci,,wannan plan din jummai ne,,Har dan tsalle ta buga tai daki,Sa'a ta kada kai, tare da sauke labule,dan tunda taji horn din motar shi ta leko,duk tana ganin abinda Zahra tai,,ta kada kai tare da murmushin mugun ta,,. 8:30 ya shigo,da mamakin Zahra sai ganin shi tai,,Ko ta kanta bai bi ba yai sama,,yaja glass din,,yana tunanin ya zai tarar da Sa'a, dan tunda zai shigo ya fada mata,,amma da mamakin shi da fara'ar yaga ta taho,,ta dan

Chapter 7 of 11