Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
4 / 11
kam dan Allah Baku yarda dani bane baba? Yai mata dakuwa" ungo naki,,yar kota,, kimin bayani ya akai kika samu motar nan mai tsada haka,tace "Baba bafa abun mamaki bane dan dan siyasa yai kyautar mota,, wlh ba abunda akai,,kuma bari na kira a gaban ka kaji komai,. Taje ta dakko waya,,ta bugawa Alhaji tasa a hands free,,"Assalam Alaikum.. ya akai Sa'a,, ta gyara murya,,dama godiya na bugo na maka,,yai murmushi, " kinfi gaban nan Sa'a, ina son halin rike alkawari,, tace"Wlh ban San haka kawai za'a Iya min kyautar mota sukutum ba ba tare da nayi wani aiki ba,,yai dariya,"ke kwa kikai aiki,,tunda kin gyara min Matan gida na,, sannan kun tafiyar da abun campaign bisa amana,kar ki damu,,.yi wa kai ne,,sai dai ina fatan baki samu matsala a gida ba??ta kalli su baba,,"Alhaji na samu,,dan basu yadda da wannan kyautar ba ta fisabilillahi,,Yace "kar ki damu,gobe da dare zan samu baban naki da maganar,, tace" aa ba sai kazo ba,gashi a kusa. Baban ya karba,ya mishi bayani,shi saboda Allah yai,da kuma ta gyara tsakanin iyalin shi,.sannan shi wannan bai dauke ta a wata kyauta da Sa'a ta fi karfi ba..dakyar ya yarda da Sa'a ta rike motar,da sharadin babu gantali sosai a mota.. By Feenat Ja'afar & Hauwa Damary [12/27, 2:01 PM] Feenat Ja'afar. BARIKI...IYAWA 19_Lalle Sa'a, yarsu tana daga cikin wayan da suka zo Duniya cikin Sa'a,, fatan shi Allah ya cigaba da kare mishi Sa'adatun shi..Lalle kam taci sunan masu sunan nata "SA'ADATU SA'AR MATA..(na Damary en Feenat).. Washegari gidan su Ummi aka fara sauka,, dan tunda ta sa rai da mota tai joining class inda ake training, cikin 4 days kwa ta Iya mota,,da mamakin ta data shiga taji tana zugar ta..." Wayyo dadi..da gudu ta shiga gidan su Ummi, ba ko sallama "Qawata...Ummi.,woo fito kisha kallo..ta fito daga kitchen da mamakin sammakon Sa'a yau,,,dan sai 9 suke da lectures,,suka ci karo" Sa'a,. Lfy?maman Ummin ma ta fito,,jin sun wani kwalla musu ihu a cikin gida.."Lfyn Ku kuwa yaran?ina ai har sunyi waje,.ta girgiza kai "Allah ka shiryi Sa'a da Ummi,.. Tai kitchen dan duba abinda Ummin ta bari a wuta..da karadi suka shigo gidan"kai shegiyar gari..kin Faso mu da yawa,yau dole mu tada kura a schl.. "Duk dan uban da bai tayamu celebration ba bamu bashi,..suka kyalkyala dariya., mama ta fito,," zanga ranar da zakuyi hankali yaran nan.. Suka kallo ta,kan ta gaida ta, tace"oh Wai murnar ta meye wannan? Da sauri Ummi tace"Mama mota fa mukai?wanda zai aure ta senator nan ne ya siya mata..da sauri Sa'a ta kallo ta, sai ta kanne mata ido, "tace mama karya take wlh,,ni saboda Allah ya ban dan na mishi campaign din partn su..ta kallo Ummi, " kullum sai na ce miki ban son karya,,ta kalli mama"mama nasan kin yarda dani tamkar wacce ta Haifa ko? Maman ta kada kai, ta kallo Ummi tare da Harar ta"ni zuba mana abinci in kin gama,,ta kalli mama tare da mata murmushi.. Sukai kitchen. Tuni karya ta karu wajen Sa'a,, ansa bikin fadeela itama,,tuni suka hau shirye shiryen biki,.za'a ai nata kan nasu Ummi,, Ranar ta fito a gida, tabi layin su Aminu a kafa sukaci karo dashi,,da abokin shi,, tuni ta hade rai, Shima yana ganin ta ya hade rai yaja ya tsaya,,tai mai wani kallo kan ta dawo kan Aminu, "angon mu,,ya akai? Yai murmushi bayan ya kare musu kallo duka,," lfy lau,, yau ina motar na ganki a kasa?ta yatsine fuska,, tana chan gidan da ake ajiye ta,, Da sauri Hafeez ya kallo su,ta maka mishi harara tare da kawar da kai.. Duk yana kallon su Aminu.. Hafeez yai dan tsaki,,"malam kazo mu wuce ni,,ta tabe baki "ai ni ban tsayar da wani ba anan., ta murguda baki ba tare da ta kalle shi ba,,ya kalli layin yaga ba jama'a kan ya dawo kanta" dallah rufen baki a wajen,,ke har kin kai ki tsayar ni da?.tuni ta kankance ido ta nuno shi da hannu "kar ka kara ce min dallah chan..ya zaburo kamar mai jira," ance dallah din,,mey zakiyi?ta matso itama"kaima Dallah chan toh,,Aminu mai zai inba dariya ba,,Bai san mey yasa jinin su bai hadu da juna ba,tun haduwar su ta farko,,kuma yasan duk din su ba masu son fada da jama'a bane.."sarkin yan tusa kai a mutum, ban damu da kai ba ka bi ka damu dani,yai murmushi "ke a fada miki tusa kai,, macen da tsabar rashin kamun kanta ba wanda bai Santa ba,,da sauri ta kallo shi,zata tanka Aminu ya shiga tsakanin su,," Wai Ku hala kuna ganin hanjin juna koh??taja baya,, "kaci Sa'a wlh yau Dana fada maka wacce har ka mutu bazaka manta ni ba.. Taja tsaki tare da daga wa Aminu yatsun ta ta wuce,,tuni ya cije lebe tare da rintse ido,, ya bala'in tsanar tsaki,,kan ya bude ido har tai nisa,," amma ya kamata kasan ba abu mey kyau kuke ba,,ache kullum kuka hadu sai kun bar abun fadi?kwanaki naji mey ya faru a super market ai a wajen Ummi,,na rasa mey ke damun ka kwana 2 nan..ya kallo shi,shi kanshi bazai ce mey ke samun shi ba,, shida maganar bakin shi ma gagarar shi take,,amma ya rasa indai suka hadu da Sa'a in basui ba baya ma jin dadi.. Haka akai bikin fadeela sukuku da ita,, idan ta tuno kalaman Hafeez,, ta tsani a sha da ita a rayuwa, gashi bata rama ba yazo abu na damun ta.. Sun samu hutun makaranta a dai dai lokaci,dan yau suka fara shirin biki,ranar Aminu yazo Yace suzo suje rakasu zabar kayan taron,ta tambayo mama suka fito,,da ganin Hafeez tace ta fasa zuwa,,Ummi ta kallo Aminu,, da sauri ya fito,,"kar ki mana haka Sa'a pls,,kin San dole sai da ke a lamarin nan,, ya kamata ace abokin na da ta Ummi sun hada kai a bikin nan,dan kusan kune kan taron nan,ya kallo Hafeez "Dan Allah Ku taimake ni a gama lfy,, ta hade rai kan ta shiga,.ya sauke ajiyar zuciya.. A wajen masu decoration tai tsaye taki zama ganin kujerar kusa da hafeez,,duk suka zauna aka kawo musu drinks,Hafeez ya dau mai strawberries da blue barriers,sai kallon shi take tana yatsina fuska kamar taga kashi,,yai murmushi kan ya tashi,,yazo zai wuce ta gaban ta ta Matsa tana tsaki,ya kar kada kwalin yaji da ragowar guntun,ya saita bayan ta ya watsa mata kan yai waje,,taje ta zauna.. Sun gama kenan zasu fita Matar cikin da mijin ta suka tsayar da su Sa'an, Aminu yai gaba" kinyi staining ta bayan ki fa,,ta nuno Sa'a, take gaban ta ya fadi,,tana mai rokon Allah yasa Aminu baiga ba da Hafeez, yau da karyar ta ta kare..,toh amma da mamaki fa,a satin nan ta gama period dinta,kuma a zuwan farko baici har ya bata ta haka ba,,Ya ilahi.,,Ummi ta juya,ta kalla,.kan ta kada kai, dan tana ganin lokacin da Hafeez din ya watso mata Jan lemon,,tace"Ke kwantar da hankalin ki,lemo ne fa,,da sauri ta kalli Ummin, "Lemo kuma?ta rintse ido, "wlh Hafeez ne ya zuban,indai lemo ne,, tai kwafa,mu zuba indai nice... Allah yaso ta Ummi after dress ta dauro,, ta kallo ta" bani abayar ki ki karbi gyale na..da sauri suka kebe a cikin shagon sukai musanye..dan kunya koh masu shagon bata kalla ba tai waje..a dai dai windown shi ta tsaya tana huci..kan ta nuno shi da hannu"wlh ka dau bashi ..ta bude mota tana ta huci,,Aminu ya kallo shi yaga sai murmushin mugun ta yake,,toh mey kuma ya faru? Dan yana zaune baiga mey Hafeez din yai ba..Ummi ta shiga tana kallon Aminu,,ta daga mishi kafada,,ya kada kai tare da cewa.. "Allah ya shirye Ku wlh,,kui ta abu kamar wasu yara kanana,, yai tsaki,,.har akaje gidan kunshi ba wanda ya tanka wa dan uwan sa,,basu suka gama ba sai kusan 5,aka karbo head din su da kayan sawa a wajen mai guga na sawar gobe.. Hafeez tunda yazo kwanciya yake tunanin abinda yai wa Sa'a dazun,sai yaji bai kyauta ba,,shi dan tsokana yai mata badan tozar ci ba,, duk da tana bashi mugun haushi in sun hadu amma yana son yaga sunyi fada..sai dai yai alkawarin bazai kulata ba gobe bare suyi abun fadi a wajen partn.. Yau tunda suka tashi aka shiga busy,,sunsha gyaran amare sai kyalli suke,, hannun nan yasha kunshi,, tamkar duk dun sune amaren,, qawayen su suma duk sunsha kyau,,tun 4 ta koma gida ta kira Ali mai kula da motar ta ya kai mata ita Wanki,tai latti bata bashi da wuri ba,ya karbi mukulli jiki na bari yai gaba,dan yasan zai fadata yau da motar da yamman nan,,ta buga wa Ummi waya cewar a gida zata shirya,,tace " Dan Allah toh Sa'a kar ki latti,,8 sharp,pls.ta kashe waya,dan tun jiya take ji da fada. By Feenat Ja'afar [10/27, 12:07 PM] 💍🛍🍬Salma🍬🛍💍: [6/2, 5:38 PM] Feenat Ja'afar: Feenat Ja'afarSalma🍬Salma🍬🛍💍: [6/2, 5:38 PM] Feenat Ja'afar: Feenat Ja'afar🛍💍: FEENAT JAAFAR'S MOBILE BLOG JUST ANOTHER BLOG  BARIKI IYAWA 3  [10/2, 5:57 AM] Feenat Ja'afar: BARIKI...IYAWA 20_Har yau da abun da ya faru a party,,sai da tai kuka mai Isar ta kan ta tashi ta cire kayan ta,, tana mai kara tsanar Hafeez a rayuwa.. Mari??wlh ko uwar da ta haife ta bata taba mata ba,,ta Shafa wajen,, a hankali ta furta"Allah ya isa wlh,,badan ta nuna masa yau BARIKI ba da tuni an sha da ita ta warke,,wa ta isa gaba tai wa fa fa kuma?? Shima yana zuwa gida ya tarar da su Hajiyan tashi a parlour,Tasleem da Zahra,, gaba daya gefen rigar shi ya jike,,yai sallama ba wal wala a fuskar shi,,suka bishi da kallo har ya shige dakin shi,,. Direct bandaki ya shiga ya cire ya watsa ruwa,jikin shi har ya fara dankon exotic din,, ruwa na sauka a a kanshi kawai hasko yadda take ta kuka yake da kokarin tada mota,,"Anya kana da hurumin takura wa baiwar Allah nan kuwa Hafeez? Jiya ka mata 1,ta rama,mai ya kaika da Marin ta??Ba halin ka bane wannan,, ya kada kai,,shi kanshi bazai ce ga dalilin da yasa yake biye wa Sa'a ba har haka,, a Schl din su da mata da suka take Sa'a a iskanci, toh amma mey yasa yafi jin zafin nata??ya kada kai,. "Dis is d 1st,and InshaAllah d last,,ba zai kara yadda makamancin hakan ta kara hada shi da Sa'a ba kuma,tunda an gama biki, toh Alhamdulillah.. Hafeez Shehu Umar yan asalin Jigawa ne,,kakan su aiki ya kawo shi Kano,, anan yai aure mata 3,har ya haifi yara bai waiwayi komawa Jigawa ba,, Allah ya bashi yara guda 11,,Baban su Hafeez shine na 5 a gidan,,yana da kanne mata 4 da Yayye maza 6,,Familyn suna da matukar hadin kan da bazaka gane wannan dan wane daki bane,,duk Matan Sun zauna lfy cikin Aminci da juna,,sai dai dan abinda ba'a rasa na yau da kullum ba,,duk gidan mutane 2 ne sukai boko,sauran duk muhammadiya sukai,, Shehu da Sadiya aurar gidan.. Shehu yanxu da ya zama Alhaji Shehu,yana da mata 1 da yara 4,,Aunty Maryam,Umar,Hafeez da autar su Tasleem,, Su gidan su Hafeez gidan yan boko ne kamar yadda baban su yai boko har ya mallaki kujerar perm sect,,saboda haka rayuwar su ta tafi cikin waye wa,,kowa na kaunar kowa,,Haj Fati itace Maman su Hafeez,,Mace ce mai fada,musamman akan gaskiyar ta,,shi yasa yaran sunfi shayin ta akan baban su,, dan shi kam mai sanyi ne,, Hafeez tun tasowar shi ba mai shiga shirgin jama'a bane,asali ma Aboki 2 gare shi,daga Aminu sai kwa Zunnu,, Musamman mata basa gaban shi,,tun kan ya tafi makaranta a indai, cikin birnin Hyderabad,,Artist ne,, tun a secondary yake da burin zama,,Allah ya taimake shi akai wa Baban shi hanya a a Sarojoni Naidu school of Arts and Communication,,. Tunda ya dawo aka Matsa mishi da zancen aure,,ai shekaran shi 34,meye meye,Yace"shifa bai da Matar aure,,tuni Hajiya Maryam tace ga Zahra,yar gidan kanin Baban shi,,amma fir Yace "shi batai mai ba,,Haj Maryam tace kwa an gama magana,,tunda zance yaje gun Zahra ta kasa sukuni,,dan Allah ya zuba mata dama son shi,,komai nashi burge ta yake,, shikam a nashi bangaren baiga kalar mafarkin shi a Zahra ba,,duk da su duk dangin su ba laifi suna da kyau,musamman gidan su Hafeez din,,dan Baban su a Yola ya samo Maman su,,kakan su kuma fulanin Jigawa ne,,. Ranar ya samu baban shi da zancen Zahra, shifa batai mishi ba,, baban Yace yai hakuri,dan zance har ya shiga family.. Tun daga lokacin ya dauke kafa a gidan su Zahra, sai sai ya gaida baban su a waje ya arce,, ko kula tai da hakan,haka kawai sai ta wanko kafa tace tazo wajen Tasleem, ko bata ganshi ba sai ta kwana. By Feenat Ja'afar & Hauwa Damary [12/28, 1:18 PM] BARIKI...IYAWA 21_Washegari ma bai fita ba sai 11 Aminu yazo ya raka shi da abokan shi Gaisuwar Sirikai,,.Aminu yai mamakin yadda yaga ya sau rai,tuni ya dawo Hafeez din shi na da,, sunsha shadda sai kamshi suke suka shiga,,Aminu Yace su fara zuwa gidan su tukun,.dai zasu karya kwana suka ga Hafeez ya tsayar da mota,, sanye take cikin hijab dogo kusan kasa ruwan kasa mai hannu, da nikaf,amma ta dage shi saman kanta,,rike take da Qur'ani da littafai na addini,tafe take fuskar ta babu walwala., ido ya kara kar kade wa,, Aminu ya kallo shi"kai ma wa Allah kar ka kulata, muje dan Allah tunda bata ganmu ba,..da sauri ya kallo Aminun, kan ya kalle shi da mamaki"Wai da gaske Sa'a nake gani??Aminu yai karamin tsaki,."Dan Allah ja muje,da wace in ba ita ba,,sauran abokan da basu San komai ba suka fara "ko dai ta tafi da shine? Aminu ya kallo shi, sai dai da mamakin shi yaga Hafeez din yai murmushi kan ya tada mota,. Sun dawo daga gaisuwa ya tsare Aminu da tambaya., " Wai dan Allah da gaske Sa'a na gani dazun??ya kyalkyale da dariya,,"Aa yan biyun ta ce,,.ya hararo shi, "Bar zancen wasa, Allah da gaske nake,, Wai ina amaryar ne?? Aminu yai murmushi, yana fatan abinda yake zai faru.. Ya kada kai yana murmushin mugun ta..dakwa wannan drama zatai dadin gani,.Ummi ce ta fito ita da Kanwar ta,. Da murmushi take musu sannu da dawo wa.." Yauwa amarya,. Itama da mamaki take kallon shi,, ganin jiya a wajen Dinner irin rabuwar da sukai,, Aminu ya kanne mata ido,,ta sukui da kai tana murmushi,, ya kallo ta,,"Amarya,dan Allah na tambaye ki man?ta kallo shi,, "ok, Allah sa na Sani,,ya gyara zama,, kan ya kallo Aminu," ba ruwan ka,,tashi ma ka bamu waje,,.yai murmushi,, "indai Sa'a ce,kasan ko Ummi bazata fada min ita ba...zaka neme ni nasan..ya tashi yai daki cire babbar Rigan shi,, dariya take ta ciki ciki," kufa haka kuke keda mijin kin nan,komai ma dariya ne,ta kunshe baki tana"I am sorry,, ina ji, ya kada kai "Wace Sa'a? Sai taji tambayar tazo mata a bazata,, tace" me kace pls¿? Yai murmushi,, "cewa nayi wace ce Sa'a?? Tai murmushi,." Sa'adatu.. BARIKI.. Oh whatever Dana Sani ta qwarai ce,,.Hafeez, kai ne baka San BARIKI ba, baka San rayuwar ta ba,,ni dai abinda na Sani Sa'a mai Sa'a ce cikin mata,,nan ta fara bashi lbrn ta wanda ta Sani,karaf kaf bana sharri,,"abu 1 na Sani da Sa'a, bata barin ta kwana,, sannan mace ce mai amfani da baiwar da Allah ya bata,,amma fa ta hanya tsaftachaciya Hafeez,, ya kada kai da gamsuwa da bayanin ta,,"Amma mey yasa ta zabi sunan BARIKI da kuma wannan sanaar? Ta kada kai "na fada maka tana amfani da baiwar ta wajen Gina kanta..bayan wannan ta girgiza kai" Ban San komai ba,,ya kada kai,, "dama Sa'a tana zuwa islamiya??what I mean,dama ta saba ko yau ta fara??dai dai Aminu ya fito,"Har yau tambayar nan ake?yau fa ka sauya abokina? Yau ranar hala ta Sa'a ce? By Feenat Ja'afar & Hauwa Damary [12/28, 3:45 PM] BARIKI...IYAWA 22_Tai murmushi kan ta tashi tai kitchen tana kiran Qanwar ta.. Ya kallo Aminu"Dan Allah kaban naka details din da ka Sani a kanta,,ni kaina bazan ce ga abinda yasa na damu da ita ba a yau kadai ba,,Aminu yai dariya"Ba yau kadai ka damu da ita ba,.ina kula da kai,,har Allah Allah kake Ku hadu da Sa'a I know u fa..Ya kada kai,, duk abinda Ummi ta sanar mishi haka Shima Aminu ya sanar mishi,,"tun zuwan su Sa'a unguwar mu na Santa,, a lokacin bata fi yar 7 to 8 yrs ba,,tun a wancan lokacin ina ganin ta a islamiyar unguwar mu har yau din nan Hafeez,, en u know what?? Ya girgiza mishi kai,, a shekara 6 ta gama tai sauka,,sannan ta haddace littafai da dama da kake ganin ta haka,,sosai tasan abinda take yi,,yanxu haka ta gama amma bata daina zuwa hadda ba da daura wa wasu duk ran weekend, shine yau lahadi ka ganta,toh chan ta nufa,,nayi imani Hafeez ba haka ka dau Sa'a ba,,shi yasa yana da kyau ka kyautata niyar ka akan mutum,, Ya kada kai,, tare da rintse ido,, bai son a daina bashi lbrn Sa'a, Dan yana sashi nishadi,,take yaji wani abu na yawo a kwakwalwar shi zuwa jikin shi.. Ya bude ido ya kalli Aminu da wani yanayi,, "yaushe take tashi a makarantar? Ya kallo shi ya kyalkyale da dariya,tuni ya kule,, "kaifa dan iska ne wlh,, ni ka fadan nai gaba malam,.ya tsagaita dariyar kan ya fada mishi lokaci,, tuni ya kalli agogon hannun shi ya mike,," sai mun hadu,,ya kwalawa Ummi kira"na wuce,,,ta fito tana dariya,"sai ina?ya hararo Aminu,kan Yace mata"inda kuka aike ni,,ya dau key din shi ya fita,,suka sheke da dariya,,sun San wataran za'a Rina haka,. Tana woo wa kwanar ta dage nikaf din ta,,sauri take dan wata irin yunwa take ji,,daga kan da zatai ta hango shi yana fito a mota yana tahowa wajen ta, da sauri ta sauke Nikaf din ta juya bayan ta tana salati da faduwar gaba..ta shiga 3 indai ta bari Hafeez ya ritsata a gun nan sai dai wata ba Sa'a ba,, gashi a ka'idar ta in zata islamiya ba mai Binta a baya a masu take mata baya,,ta waiga taga gidan su Tj a bude da sauri ta kule tare da turo kofa,,d sauri ya bita yana kira,, "Sa'a ki bude dan Allah,, magana zamu yi,,cikin tsiwa tace" ba a bude ba,,kasan dai ramako nai ai,,wlh kama kauce kan na Tara maka yaran unguwa suma Atule,, yai murmushi,, toh na tafi bude,,wlh ba abunda zan miki,,tace"waxaka maida Yarinya,,na San ka ai,,ka tafi kawai,ba maganar da zanyi da kai,,taji shiru,,sai da ta kusa minti 10 taji shiru kan a hankali ta zare sakata a hankali zata leka ya turo kai ciki da sauri,,taja baya tare da kwala ihu,,zatai cikin gidan da sauri ya ruko hijab dinta,,ganin hijab din zai matse mata wuya yasa ta tsaya,. "Cikan hijab,yai murmushi tare da sa dayan hannun ya cire nikaf din da sauri,,ido ta zaro kanta nuno shi da hannu" wani salon wulakancin ne wannan komai?ya girgiza kai, "ka cikan hijab toh,ban son iskanci,, ta warce nikaf din ta,.jin ihu yasa Tj da kanin shi suka leko,," su waye?,,ta dallah musu harara,,"Jisu a gun,,toh Aljanu ne,,kallon bakin ta kawai yake,,akwai Iya fadan gan gan ga tsoro,, Tj ya murguda baki, itama ta murguda mishi,,Yace"Kuje ba komai,,suka kada kai,, ya juyo kan ta da take hararar shi,, yai murmushi, duk da haka yaki sake mata hijab,, bata nufa kawai sai ganin shi tai ya zube mata a kasa yai kalar tausayi,, da sauri taja baya tare da zaro ido cikin mamaki,,. Da sauri tace "meye haka?ya kada mata kai,," I am really sorry Sa'a,,wlh Sa'adatu believe me,, ban taba daukar hannu na taba wata da sunan duka ba,,koda kwa Qanwata ta ce,,but thank God, ba wanda ya gani,daga ni sai ke,sai Ummi da Hafeez,, tuni ta fara hawaye,,dan tuno yadda taji a jiyan,,tare da rintse ido,, take wani karfi yazo mata ta kwace hijab din ta da karfi,, cikin kuka tace"how could you? Ko kasan ko iyayen da suka haifo ni basu taba mari na ba a rayuwa,,ta goge hawayen ta,,"no bama haka ba,, Hafeez, duk da ba wanda Ya gani, amma zubar mutunci nawa ne,,da sauri Yace,"I know,, but pls I am so sorry,,nasan na miki ba dai dai ba, amma in kin duba duk mun ma juna pls,,ta girgiza kai, "ka Sani kuka,ka Sani a bakin ciki,ka dauran tsanar da ban San lefi na ba,. Ta goge idon ta tare da nuno shi da masifa,."Ban waje na wuce kawai,,tashi yai,dan yasan ba kula shi zatai ba yanxun., yana kauce wa ta fita tana daura Nikaf.. Ya bita da kallo har ta sha kwanar gidan su. By Feenat Ja'afar & Hauwa Damary [10/2, 6:02 AM] Feenat Ja'afar: [12/29, 3:39 AM] Feenat Ja'afar BARIKI...IYAWA 23_Tana zuwa kofa taga mota a kofar gidan wata mai kyau,, da mamaki yau kuma wata samu haka??ta shiga,suna tsakar gida an shimfida taburma a inuwa,,harda Baba da a ka'ida iyanxu baya gida,,ta cire Nikaf din tare da sallama,,baban Yace"Kaga yar halak, walaikum salam,ta kalli bakon, tuni ta hade rai,, baba Yace"kin dawo mama ta?ta daga kai,"Baba lfy?yau nagan ka a gida?da fara'a Yace"a, baki gane bakon namu bane?ta kallo shi, dan jaraba kuwa kirrr ya kafe ta da ido,."Ban gane shi ba Baba,, bakon yai murmushi,, "lalle Sa'a,, Duniya da alkawari kuwa?ta harare shi a takaice,, ta basar,, baban yai murmushi," shekara 3 kam baici ki manta Ali ba,,dan wajen mai gida na da ya tafi kasar waje karatu,,naga har gidan nan yana zuwa kan ya tafi?tace"au, na gane,.bari na shiga ciki,,baban Yace dama fita zamuyi yazo gaida su Maman ki ne,,ta kada kai, Baban yai waje,,zata shiga Ali ya bita da kallo,,lalle Sa'a ta sake girma da kyau, wlh karan nan bazai bi ta kanta ba,,baisan dame ya ragu da Sa'a take kinshi ba?ya girgiza kai lokacin da ya tuno rabuwar su ta karshe da ta furta mishi ba aure a gaban ta yanxu,..yai murmushi, yanxu kam yasan akwai,,shi a yanxu gani yake irin su Sa'a ne kadai ajin auren shi a garin,,gashi Wai dan tsabar takaice Wai bata ma gane shi ba..yai kwafa,yasan ta inda zai bullo mata ai,, inta San wata,bata San wata ba. Shi kwa Hafeez tunda dare yai ya nemi nutsuwar shi ya rasa,, jin wannan abun da ke yawo a jikin shi sai karuwa yake,,ya kasa sukuni sai tunanin Sa'a,,. Duk da bata yafe ba,but at least ta gano yai nadama,, ya hasko lokacin da ya cire mata Nikaf dinta,, Ya salam,Ashe Sa'an karshe ce,amma mey yasa da bai kula da kyan nutsuwar ta,,ga ba karamin kyau hijab din ya mata ba,, yai murmushi, "Hafeez mey ke kanka ne yau 4d first time?? Sa'adatu.. Kamar an tsikare shi ya tashi tare da lalumar wayan shi,, ya kalli agogo 9 ma batai ba,, Aminu ya kira,,bugun farko ya dauka,,"Nifa tsiyata da gauron mutum baiya sanin dare yayi masa,. Dan tsaki yai" commot ni temako zaka min,,ka nemi gauro kuma,dan nima na kusa aure,.ya kyalkyale mishi da wannan dariyar da take kulal da Hafeez,, kan ya tsagaita, "kai shegen kaya,har an dai daita da Zahra ne??Hafeez yai tsaki, "wace haka?dan Allah be serious, numbern Sa'a nake so kaban..yace"eyeee?mey kace?ya kara tsaki,"kai fa dan wulakanci ne,zakace bakaji mey nace bane? Aminu ya ci mur kamar yana kallon shi, "meye dan na tambaya, nasan mey zaka karta mata,haka kawai kasa gobe tazo ta sauken kwandon bala'i a gida..toh da sake,.ji yai kamar ya bishi ta wayar ya rufe shi da duka..sai dai yasan halin Aminu,sai ya hana shi tsaf,,tuni ya dawo lallami,," no wlh ba abinda kake tsammani bane pls, gaisawa kawai zamuyi,,pls,.ya kara kecewa da dariya,, "lalle Sa'a tai zarra,a takaice dai tai wining kenan?da sauri yace "eh,duk ya matso ya bashi,amma dan wulakancin sai ja mishi rai yake,." Ni in zaka ban kaban malam,,Yace"kai,wlh kai ladabi,tam,,lalle Mutumi na da magana a kasa.,bani 2mints yazo zan turo,,tuni ya sauke wata ajiyar zuciya,.kan ya kashe. "Toh in na kira ma mey zan fara ce mata??ya salam,,Wai mey hakan ke nufi ne dashi da ya kasa sukuni?kadai wannan fa shi ake kira da so?dan ya San ance so a zuciya yake,gashi shima tashi zuciyar sai tsanan ta bugawa take,,tun a ganin shi na farko da Sa'a Saida yaji haka..yai murmushi,, da ya tuno yadda in sun gamu suke rabuwa,,in tana zazzaga fada bakin ta kawai yake tuna wa, komai da gaske take yin shi,,.. shigo war text ne ya katse shi, da sauri ya duba,,editing kawai yai ya danna calling,ya sata a kunne tare da komawa da baya ya kwanta rigin gine,,caller tune ya fara ji na sheikh sudeis na Allahumma Aslihlana Duniyall....take ya lumshe ido,,a hankali ya furta" Sa'a "bai tsammani ba yaji ance " Yes,who's this? Ido ya lumshe,dan baima San ta dauka ba,,ita kwa ta bangaren ta tuni ta fara kulewa,,a tunanin ta ko yan iskan samarin tane yan naci,,tuni ta fara sababi"Malam in baka da tace wa bacci nake ji,,yai murmushi kan Yace" am sorry,, Hafeez din ki ne..tuni taji abun wani bankwara kwai,Wai Hafeez din ki,,"Hafeez dina?tace"Toh daga wace jahar?yai murmushi mai sautin da ya ratsa ranta,duk da ta gane wake magana kuwa..ya katse ta "Sa'a,tace" umm,,"nasan kin gane mai magana,,kiyi hakuri again,na nemi afuwa pls,,,ta lumshe ido,, ya cigaba"Sa'a,, da baki juyar da Marin nan kaina ba da bazan taba yafe wa kaina ba,, amma ki tsimaye ni gobe,zanzo in tsaya a titi ki Tara kema jama'a ki rama Marin ki,,Kila in munyi 1-0 nima nawa mutuncin ya zuba sai ki yafen.. Pls,,ta ja numfashi,"ni bance ba,,Yace"meye baki ce ba?tai shiru, Yace"Ok,yanxu kin yafe ni ba sai kin rama ba??cikin kaguwa tace"eh..yai murmushi, "Ok,tnks, bari na barki,. Sweet dreams,,.. Kit ya kashe,,tabi wayar da kallo,,har kwakwalwar ta taji Kalmar" sweet dreams din nan..samun kanta tai da murmushi,, kome ta tuno take ta keme fuska kamar yana ganin ta. By Feenat Ja'afar & Hauwa Damary [12/29, 4:35 AM] Feenat Ja'afar BARIKI...IYAWA 24_Yau kwana 2 da faruwar haka,Ummi ta kira ta harda fadan su,, dan wulakanci batazo an kawo ta da ita ba,sannan har yanxu taki ta leko ta,,toh wlh zata fadawa mama,, tana jin tace mama ta hau bata hakuri,,zata zo yau,,"uwar jaraba, ta ce"na kai ki?saura ki min lattin zuwa..sukai sallama, ita kanta tasan bata kyauta ba,,. Da yamma misalin karfe 4 kwa ta dau wanka cikin wani dakakken Orange din les da blue, yai bala'in mata kyau,tai ado da blue sarka ta fashion,,batai wata kwalliya ba,amma sai kyalli take na dilka,ga kunshin biki kamar yau akai mata..Mama ta kalle ta,,"ah gaskiya baki kauta ba,amma kunfi kusa,,tai murmushi, "mama zan wuce,ba sako?dan gidan fadeela zan fara zuwa,,tai murmushi," babu,Ki gaida ta kawai.,ta gyada kai kan ta fita,,. Tuki take tamkar bata so,,duk da tana dan gudu,,bata San meya sa haka kawai take jin nishadin yamma

Chapter 4 of 11