Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
11 / 11
yaki tafiya,.Baba Gashi Ba wanda ya Sani ko a gidan su Zahran,.Zan sa hannu kawai gudun Kar abinda ake gudu ya faru,..Yace"Gashi nan zuwa,.. Tunda ta fara wayar zahra take kallon ta tana hawaye,.Sa'a wace iri ce??..Mai saka alkairi akan sharri??.. Tun samun cikin nan kullum sai ta mata gori akan shi,.Ta wa Sa'a abu dayawa a zaman su,.Duk da zata rama,. Ga niyar ta ta zuwa wajen malam.,amma Sai gashi yanzu ita ke dawainiya da ita harda hawaye,..Wani irin kuka ta saka mai cin rai,. Kila ma Allah ne ya kamata da hakin Sa'a, ga fitar da tai ba tare da izinin Hafeez ba,Gashi ta kuma tsallake iyakar Allah,. Duk da ta gude Allah da ta gudo da Kila achan ma zata mutu a gadon Boka.. Kuka take Sa'an na aikin lallashi,ita a zaton ta Zafin ciwo ne,.it a ranta tama manta da Zahra kishiyar ta ce,gani take tamkar Fadeela ce a gaban ta a haka,ga ciki yai sama ba halamun zai sakko kasa...Hawaye take tana lallashin ta,."Zahra kiyi hakuri kiyi shiru,InshaAllah yanzu za'a shiga dake,.Ina tsoron sa hannu ne alhalin babu wani Babba a kusa.. By Feenat Ja'afar & Hauwa Damary [1/29, 2:11 PM] Feenat Ja'afar BARIKI...IYAWA 65_Amma bari na fado wa Dr sai su fara shiri.,kai ta kada mata, ta bita da kallo har ta fita,.Ba'a jima ba sai gata ta dawo,tace "Ga nan Baba a waje,.ki daure ki samin numbern ko mutum d'aya ne a gida,Ta mika mata wayan,.Iyanzu tama daina jin ciwo,sai Sai abinda ba za'a rasa ba,.Numbern Mamy ta bata,.Ta tashi,Kamin tai dailing ta ruko hannun ta,." Sa'adatu, juyo wa tai kan ta amsa,,.ta kallo Nurses din,"Dan Allah sisters Ku dan bamu waje,.Suka kada kai sukai waje,.Zama tai tana kallon ta,. Hawaye take,."SA'ADATU dan Allah ki yafe min duk abinda na miki,.Ashe da gaske yar uwa kika dauke ni,.Nasan hakin ki Dana Hafeez ne yake tambaya ta yanzun,.Nasha binki da sharri kina tsallake wa,.Gashi yau har ta kaini da aikata Babban aiki,.Wanda nasan yau inna mutu wallahi wuta zani Sa'adatu... Kuka ta kara fashe wa dashi,Da sauri Sa'an ta ruko ta,. "Zahra ni baki min komai ba,. Inma kinyi wallahi na yafe miki,.Amma ki Sani.,Ba'a yanke rabo da Rahmar Allah, Kar ki kara ambatawa kan ki wuta Zahra,.. Murmushi tai wanda yafi kuka ciwo,." Sa'a meye hukuncin wanda yaje wajen Boka a wajen Allah??.Ta kallo ta,. "Boka Zahra,.Allah yai mana tsari dasu,. Tace" Amin,.Sa'a jiya da yau naje gun Boka, tare da taimakon shaidan da Muguwar Qawa,.Sa'a nayi shirka wa Allah Alhalin nasan hukunci,. Sa'a Bani da sallah ta kwanaki Arba'in,. Ga tsinuwar mala'ikun Allah dake bina har na dawo dan ban tambayi Hafeez ba,.Taya in na mutu yau,zan ce ina Aljanna??,.Taya ya Sa'a.. Nan ta hau bata labarin yadda sukai da Shi.,da tafiyar Jummai da gudowar ta har zuwa Ganin da ta mata,."Allah kadai ya cece ni a yau,da Tuni na tafka kuskuren da har na mutu bazan Iya goge wa ba.,.Kuka take kamar ba ita ke labor ba,.Da tsananin tausayi Sa'a ke kallon ta,. "Ki gode Allah Tunda baki yarda dashi ba,.Sannan ki gode Allah Tunda kin tuba kin kyautata niya,.Allahu Gafurur Raheem ne Zahra,. Tabbas kin Tafka kuskure, Amma baki idda ba... Shigo war Dr ne ya katse su,." Ga nan Baban ya sa hannu,.sannan ya kira Baban Mai gidan,.Kar Ku damu,Lafiya za a fito da ita.., Yace Sa'a ta fita zasu kimtsa Zahran dan wuce wa Operation Room,. Da kuka Suka rabu da Zahra,ita fa gani take in ta shiga bazata fito ba,.Burin ta tace wa Hafeez ya yafe mata.. Tana fita Abba Yace"yanzu na kira shi Alhajn su Hafeez din, Sai Ku kimtsa,Ganan na basu advance kan a fito da ita,dan 10k kawai gare ni a gida.., Ta kada kai "Baba mun gode,.Bari naje gida,dan dakko kayan ta da abin bukata.. Ya kada kai,.. A hanya Suka hadu da Mama,ta fada mata inda Baban yake., Tana bude gida waya ta fara sawa a chargy Allah ya so ta da wuta, Dakin Zahran a bude,ta shiga,kaya ta debo set uku,karaf kaf ba zani sai skirt sai doguwar Riga,. In ba shadda ba,duk dinki ita kan batta a skirt, ganan ranar zani tazo,..Tana bude Dayan Side din ganan kayan baby duk na mata sai unisex,. Sa'a tai murmushi,. wato itama mace take so kamar ta?..Allah basu Nagari shine fata...Allah dai yasa Zahra ba tai tarun Banza ba..,Ta fito ta haura sama,.Kayan ta masu Riga da zani ta dakko guda 2,ta dau pillow da sauran abin nema,.Abincin da tai kan ta fita ta juyo duka,,.Ta Bude ma'ajiyar kudin ta ta dakko kudi,Na Adashen da suke a office ne,jiyan nan ta dauka,tana burin rabawa 2.,ta kaiwa su Baba,d'aya tai wa Zahra siyayya,.30k ta dauka,ta maida sauran,.Ta kulle gidan ta fito Chargern mota ta sauya,ta kunna wayan,.Kamar mai jira aka kira,.Hafeez ne,duk hankalin shi a tashe,. " Unique yau ina kuka shiga ne haka??.. Na kira Zahra wani yana dauka Wai a gidan shi ta bari!.Bata gidan ne??.Damm taji gaban ta ya fadi,. Wato dan iskan bokan ne ya dauka??,.wace karya zata mishi dan wanke Zahra ita kuwa a yanzu???..katse ta yayi,."Hello,.Da inda inda ta amsa,."Amm..Dama,.Am,Tun dazu nake kiran Ka yaki shiga,.Zahran ce dama..Da sauri ya katse ta cikin fada.."Wajen wani katon ta bar wayar tayi??..Kenan bata gidan??.."Aa,,Dear Ka saurare ni,.ina ai ta inda yake shiga ba tanan yake fita ba,."Dan taga bana gari ta sirki wani iskanci koh.. "Hafeez tana Theater Room..Sit yai dan jin ta ambaci sunan shi da kuma Theater Room..Sai kuma ya dawo ya rikice..," Mey ya same ta??..Haihuwar ce??."Eh.Amma yanzu za'a fito ma InshaAllah,. Ka mata adu'a.., Ce mata yai ta kashe ga Abba yana kiran shi...Katse wa tayi,,Tai ajiyar zuciya,. Hafeez akwai kishi,Tuni idon sa zai rufe..,Tana tsoron yasan abin nan,Allah yasa Bokan nan Kar ya tona wa Zahra asiri,Tunda ga Jaka,Takalmi,Gyalen ta duk suna gidan shi. By Feenat Ja'afar & Hauwa Damary [10/2, 8:16 AM] Feenat Ja'afar: [1/30, 1:52 AM] Feenat Ja'afar BARIKI...IYAWA 66_Baba mai gadi ta sanar wa abinda ake ciki,.Tana kokarin fita da mota sai ga nan Jummai, rike da Jaka 2 a hannun ta,. Fitowa tai a motar Ganin kanta tsaye tai cikin gida,Binta tai taga Iya gudun ruwan ta,. Kofa take ta ja taki bude wa.."Hala da gadon Ubale a gidan nan ne Jummai??. Ta juyo baki sake tana kallon ta,. Harde take da hannu a girji, ta hade girar sama da kasa., Sai tai mata bala'in k'warjini,. Dan Tunda suke zuwa gidan Sa'a basu ishe kallo ba bare tai musayar yawu dasu,. Kai ta girgiza mata,. "Wajen Zahra nazo.. Rai hade tace"Uhmm, daga nan fa??.Duk rashin mutuncin Jummai sai ta zama kamar wata doluwa a gaban Sa'a,. " Jakar ta na kawo mata,. Baba mai gadi ta kwalawa kira,cewar ya kulle mata gate ya zo kuma, Tace ta bata jakar,.Ba musu ta miko mata,. Maimakon ta karbi ta Zahran, sai ta warce ta Jumman,. Yayi dai-dai da zuwan Mai gadi,. Matsowa tai da zummar kwace jakar ta taja baya.. Hannu ta nuno mata,.tare da kada mata su,. "A'a.,ta kada mata hannu halamar gargadi," (Don't even think about it),.Tai mata wani kallo.." Dan Kinsan Allah? kika yarda kika matso sai kin yaba wa A'ya zakin ta a gidan nan,.. Chak ta tsaya,baki sake ta kasa magana,. Ta kallo Baba maigadi,wanda ya dakko katuwar gorar shi,. Jira yake Tace "Ass,ya sau aiki.. " Baba in tai k'wak'waran motsi Ka bigen yar iska,.Ya kada kai "An gama Hajiya,. Tuni ya Matsa gaban Jummai yai (ready)da sandar shi,. Zazzage jakar tayi,kudi Suka zubo da tarikicen magun gunan ta,.Ta zuge munafukin zip din cikin, sai ga sarkar Zahra ta fito,. Wanda akallah zatai 250,haka Abban su Hafeez ya sa musu,.Ta makawa Jummai harara,."Macuciyar Allah ta'ala kawai,.. Jummai ta hadiyi yawu,.. Tace" Da kika boye sarkar,ce mata zakiyi dan wannan chanjin ne kudin sarkar??.Ta girgiza mata kai.., Sa'a tai kwafa,."Allah ya so ki baki siyar ba,da wallahi na Lahira sai ya fiki kwanciyar Hankali,."Ashawo kawai,.Ta warce jakar Zahran tana kara hararar ta,. Gyalen Zahran ne aciki da wayar ta, ta dago tana zare mata ido..,"Ina kudin da ke jakar ta'ta kan kije Saida sarkar??..Da tsananin mamaki Jummai take kallon ta, a zuciyar ta tana "Wai ina Sa'a tasan duk wannan abun?.."Tambayar ki nake?..A yatsine tace. " wane kudi??.."Au tambaya ta ma kike?.."Eyee??.. Ni zaki gwada wa BARIKI??.. Tai kwafa,. Kudin jakar jumman ta tattara ta mikawa mai gadi,."Baba kirga min su da sauri..,Da sauri ya lissafa,."Dubu Asirin ne da Bakwai da Dari uku,.Ta kada kai,. "(Good),.Baba ware min Ashirin da biyar aciki,.Ya kada kai, tuni Jummai ta zaburo,,."Wallahi baki isa ba,Dubu ashirin ne nata,.Toh Wai ma ina ruwan ki da harkar mu??..Sa'a tai wani murmushin mugun ta,. Tace" Karamar Yar iska kawai,.Ba kince babu ba??..Nasan Na Zahra dubu Ashirin ne,.Biyar din cikon na Taxi ne,.Sannan,daga rana irin ta yau, Baba idan Ka kara Ganin kafar ta a gidan nan na baka izinin Ka karya shegiya,. Yace"An gama Hajiya.,Jummai tai mata kallon Banza,. "Ai ba wajen ki nake zuwa ba Malama,. Wajen k'awata nake zuwa,.Kai ta girgiza mata, tana murmushi, Da key din motar ta ta nuno ta " Idan Jummai ta fito a cikin Uwale da halaliya,toh ki kara sako kafar ki a layin nan ma kadai inda kiga??.. Ta dawo kan Baba,"Ka ajiye min wannan jakar,Ka bata sauran chanjin Ta,. Sannan kan na kirga(10),Ta bace min da gani anan,.Tace"D'aya,.. Ya duk'ar da kai "An gama Hajiya,.. Kan Jummai yai.," Maza tattara kan wa'adin ki ya cika,. Sa'a tace"Biyu,.Kallon banza ta tsaya yi mata,."Uku,.Ba tsammani taji Baba ya rafka mata Gora a gadon baya,Ai ba shiri ta hau tattare kaya tana Kunkuni,.Sa'a Tace "Hudu,.. Baba ya sake sakar mata wata,.Ba shiri tai magana" Toh Ka dakata man na hada,.Da mugun ta Sa'a tace"Biyar,. Ai kwa ya kara dagawa zai muka mata,datai wani uban tsalle sai tai gefe,."Allah ya isa wallahi,. Sa'a tace"Shida,.Sai kwa Baban yai kanta da gora,.Haba wa.,Jummai K'afa mai naci ban baki ba,.Sai ta runtuma Gate a guje tana kiciniyar bude wa,. Sa'a tana dariyar mugunta Ta kwala da karfi,."Takwas,.Ai baba ya samu moriya, tuni ya kara sau mata aka,.Ihu ta kwala, "Wayyo,Toh Ka bude na fita man,.Harda yar kwallar ta,.Baban yace " Ba kin tsaya taurin kai ba??..Ni dan Tauri ne,.Sa'a ta kara kwalo wa"Tara..,Dai dai baba ya bude mata,amma da yake Shima chali-chalin kansa ne sai da ya muka mata,.Sa'a mey zatai inba dariya ba,. Har kasa..Fadi take "Ki tsaya man,Yar Kot'ar nan..Sai abi wani sarki kuma,.. Da Allah ya isa ta shiga Taxin da ya kawo ta,dama tace ya tsaya,..Har ta bar unguwar tana Allah ya isa,. Sa'a ta zo gun Baban, Shima sai Dariyar keta yake bayan fitar jumman,. Kudin ya bata,." Kaji Min Y'a da taurin kai Hajiya..,Sa'a tai dariya,"Ai nasan bazata dawo ba,. Dubu (2)ta ware,"Ungo Baba, kaima Allah ya sha dakai,.Bani kayan ma kawai nakai ciki,. Ya duka baki har kunne,."Wai Wai Wai,.Hajjaju Harda mu??..Tai murmushi,. "Toh Allah ja da kwana,.Allah ya sauki Yar uwar ki lafiya.. Tace" Amin,.Sai Lokacin ta tuna da asibiti, da sauri ta sa kayan aciki,ta boye sarkar ta kullo tai asibiti.. By Feenat Ja'afar 67_Tana zuwa duk yan uwan Zahran sun zo,.Su Aunty Maryam,. Suka tare ta suna mata sannu,.Tasleem da Auntyn su Zahran Suka Taya ta debo kaya..Tambaya suke an shiga??.Suka ce"Wai sai(9),.(In charge)din ne sai yanzu yazo,. Ta duba agogo, (8:43)..Tai ajiyar zuciya,. "Toh Allah yasa Ai a Sa'a,. Suka ce " Amin,. (8:55)Suka garo ta daga labour Room,. Tayi lamau,kamar mai bacci,.Cewa tai a tsaya tukun,.Duk Suka iyo kanta,."Sannu Zahra,.Ta daga musu kai,.Sa'a take kallo,.Kan ta ce ta duko kanta kadan,kamar mai rada tace"Sis ya Tambaye ni koh??..Ta girgiza mata kai,. Hawaye ta fara,"Nidai kira min shi dan Allah,Nace ya yafe ni. Sa'a ta dago,."Kiyi hakuri sis,.kinga Doctors na jira a theater room,. Amma nayi alkawarin zan nema miki(Right now)..Ta goge hawayen ta, "Nagode,. Allah ya kaddara haduwar mu,..Sai ta karyar mata zuciya ta fara itama kuka,. Kowa Kallon su yake, musamman Aunty Maryam da tasan Sa'an Basa shiri da Zahra,. Ta rike Sa'an aka gara Zahran,. Sai fatan a fito lafiya. Hafeez din ta kira,.duk da wayan shi biyu tun zuwan ta,. Ta Isar da sakon Zahran,. Suna nan zaune har kusan (11)Kamin aka garo ta,.Ba inda ke motsi a jikin ta,. Suka basu Babyn girl din data samu,. Zahra taje wajen Nurses din,." Ya naga bata motsi toh??.. Sukai murmushi,. "Ai an mata (Anesthesia),. Za ta Iya tashi " (any moment) …Kar ki damu,.Ta sauke ajiyar zuciya..Tace wa su Aunty Maryam zata zauna taga tashin ta,. Su kace taje gida.,Ga masu kwana da yawa,. Sannan gidan su ba kowa.. Aunty Ladi aka bari ta kwana da ita,.Dakyar da taimakon wayar Hafeez ta Iya bacci,. Dan ma ta taho da Tasleem,. Washegari sassafe ta gama komai,.Su Bahon wankan baby,ruwan zafi,.Abinci, Tun asubar fari data tashi bata koma ba,.Bacci ne tun yana diban ta har ta daina ji,.Akai Assalatu ta tashi Tasleem, da mamakin ta taga sai kiciniyar soye-soye take,.Tace Ai da ta tashe ta,. (7)Suna asibiti,.Ta tashi Alhamdulillah,Sai dai Rashin karfin jiki,. Sukai mata sannu,,ta dau baby,mashaAllah, Babyn Mai kyau da ita jinin su Hafeez, kamar su guda,. Tace"Umm,su Zahra, An samu abin nema,.Ganan Zankadediyar Budurwa mun samu,.Tai Murmushi tare da kokarin a gyara ta,. Aunty Ladi tace zata gida Tunda Sun zo,dan bata shirya ba,.Tasleem ta tafi karbo wani result,. Ta kallo Sa'a,. "Sis kema Allah ya baki Baby,.Tai Murmushi,. "Sis sai dai fatan sauka lafiya,.Ido ta waro,." Kai haba??..Ta kada kai tana murmushi,. Sai yanzu ta kula da farin Sa'an, tai wani fresh da ita,. Ga cikin duk yabi jikin ta, musamman kasa.. Tai murna kwarai har ranta,.Tai mata fatan Rabuwa lafiya,. Kan (11),yan uwa sun zo da daman su,.Kowa yana tai wa Sa'a son barka,dan kwarai ta burge su,.Ga nan mai kula zai ga cikin ya dan tasa,.Aunty Maryam data kula da cikin Sa'an taji dadi kwarai,.Tana son Sa'a, don mai son naka Ai Ka so shi. Hafeez ya kira su ta bawa Zahran Suka basu waje,.Amma sai ta rike Sa'a,. By Feenat Ja'afar 68_Azahar Hafeez ya danno Asibiti, ko gida bai je ba,.Sa'a ta mika mishi baby tare da manne mishi suna Kallon ta tare,.Zahra tuni ta fara adu'a,.Dan jin chanji a ranta,.kai gaskiya kishi jaraba ne,.Ita Sa'a bata dauki abun wani abu bama,. Kwanan su 3 aka sallame su Suka tarkata gida,.Dan fa Zahra tsaf take manne kayar ta ba ko kara,. In za'ai wanka,ta dinga"Ai hankali da idon ta,. Koda Hafeez ya nemi ba'asin waya,Sa'a ce tace"Ai ita ta bari a despensry,.Ya chake mata kudin ta na asibiti,.Fir tace Gudun mawar tane,.Baba ya kira yai mishi godiya.. Sa'an shi ta daban ce. Zahra ko ta Jummai bata yi,burin ta ta tsallake fadan Hafeez, tasan yanzu K'afa ya daga mata. Batun suna da ya tambayi Zahra ta bashi mamaki da tace Sa'a,. Kuma yaji dadi sosai. Amma tace ya rufe Kar ya fada mata sai ran suna. Dake garau take,suna ba fashi sati nayi,. Da safe taci Ado na kece raini da Wani less Din su da Sa'a ta din Ka musu na fitar suna,. Kiran wayar ta Sa'an tayi kan ta same ta a stairs,. Ta kalli mudubi, komai yaji,.Taso sarkar ta na nan yau ta Kar kwalliya,."Fashion"tasa ta fesa turare,.Mai zama mata tace"Kayan nan sun amshe ki Zahra,. Tai murmushi tare da fadin ta gode,. Saman ta haura, dan amsa kiran Sa'a,. Tana zuwa ta tarar ta taci Ado itama da Less din nasu,.Color ne kawai ya banban ta..Ganan sarkar ta irin ta ta a dambare a wuyan ta,.Ga zobuna manya guda biyu,.Bangles na Awarwaro manya kamar Gold,. Tasha Adon Gold, sai shining take,.Sai ta gane kyaun les din a jikin Sa'an.. Tai murmushi, "Sis kinyi kyau fa,. Itama tai murmushin,. Kan ta zaunar ta kan kujera,. Ta kamo hannun Zahran,,. "(Guess what)?.Ta bude ido da Neman Sani,."(what)??..Tai murmushi,. "Kawo hannun ki,amma ki rufe ido,.Ta kada kai da murmushi,.. Sarkar Sa'an ta zaro a inda ta boye,,.Ta daura mata a hannu tare da fadin,"Tan taran.., Ido Zahran ta bude,.Aikwa Tana Ganin sarkar ta ta rukunkume Sa'an da murna..Hafeez da Tunda ya shigo yai tsaye yana kallon su a bakin kofar,.Murmushi yake,.Komai Sa'a tai burge shi take,.Yaji dadin ganin su kwarai a haka.. Karaso wa yai yana. " Kun dai manta dani a rayuwa Matan nan koh,.Suka cika juna suna dariya,. Ko Break ba wacce ta kula nayi."Ai angon karni baya yunwa,.bari (1)minutes,. Zahra rike ta tai,."No yi zaman ki Maman twins na zubo mishi..Ta kada kai tana kallon hafeez,. Yana Ganin ta fita ya ruko hannun ta,."Ya Zahra tasan ke Maman twins ce?.Tai Murmushi, kawai (Guessing )ne..kai ya kada "Kai kunyi kyau fa Allah,.. Tai murmushi tare da Ruko kumatun shi kamar Wani yaro" Mun gode,.Sunan wa aka sa ne ni?? Yace"sistern naki naki bata baki Bayani ba??..girgiza kai,. Dai dai shigo war Zahra da faranti a hannun ta shake da papee chicken,.Zahra ta taro ta tare da karbar Abincin,. "Wannan fa ya miki nauyi.. Tai Murmushi,. Hafeez yace"Baki sanar ta mai sunan Babyn ba?..Tace "Da zumudin Dana zo kenan,so nake na fada a gaban ka,Da fatan baka rigani ba?. Sa'a sai Kallon su take.,amma su sai ja mata rai suke., Tace"Hajiya aka sa Ai na Sani Tunda baza Ku fadan ba,. Sukai Murmushi,. Zahra tace" Baki chan Ka ba,.Ta rike hannun ta,. "Sunan Babyn mu, SA'ADATU Hafeez Takwarar Momyn ta..Sa'a ta waro ido,."Ni Sa'an?. Ta nuno kanta,.Kai ta kada mata,.Basui aune ba takwa kwala kara,tare da Doka tsalle,." Wayyo dadi Barni da raina,. Da sauri Hafeez ya nuno ta,. "A'a,kinyi na kudin ki Unique,.Kar ki mini illah.. Tace" Sorry.. Sorry,.Murna fal ranta ta rukun kumo shi,. Ta hado Zahran ma duka tana kwarara musu Godiya.. By Feenat Ja'afar [10/2, 8:19 AM] Feenat Ja'afar: BARIKI...IYAWA 69_Dariya suke tayi,farin ciki fal ran su,.Cika su tai ta ban kada cushion din ta dakko kudi ta mika wa Zahra,."Ga nan ajiyar ki,.Ta karba,tana kallon ta da rashin fahimta,. Ganin Hafeez a wajen yasa tai mata gwari gwari,."Cikon Sarkar Jummai,. Zakui waya dai,.Ta Ciro 5k,"wannan kuma Tukwici ne,kan Babban yazo,.Zahra tama rasa mey zata ce mata,.Ganan sarka ta amso mata,.Ashe harda Kudin Boka sai da ta lale su wajen Jummai? Har ga Allah ta fidda rai da samun su,dan tun daga ranar Jummai har yanzu bata kira ta ba,.Tai murmushi, Lalle maganin shege,akace sai Dan Iska,.Jummai ta gamu da gamon ta,. Kawai sai ta Rungumo ta tana zuba godiya ba adadi,.A ranta tana rokon Allah Kar ya kara kawo ranar da zata sabawa Sa'a, dan ta mata Hallaccin da zata Iya kiran ta da YAR UWA CE kadai mai mata ba kishiya ba,. Haka Suka tafiyar da sunan su gwanin sha'awa, komai Sister, komai Sa'a,. Har aka watse lafiya.., Tabbas Zahra tasan Sa'a ta daban ce,ba yadda za ai ta hada kai da ita,.Don Bazata Iya ba,Hakan yasa ta dau damarar janyo hakurin ta na Da,ta yarfa wa ranta,..Takan gujewa duk wani cikas na zaman su da Sa'an, Duk da ta fara mata karar abubuwa da dama,.Sai dai babu ta inda ta rage wa Hafeez.. Tabbas kowanne bawa da irin baiwar da Allah yake haifar sa,.Musamman mata,kowa da irin tata salon Iya kissar,. Tanan kam,ko ita ta sarawa Sa'a,. A hankali ta siye su da yan uwan su Cikin hikima da Dabara,.Sai dai Abu d'aya ta Kudirta a ranta,,shine duk yaran da zata Haifa mata,toh fa zata damkawa Sa'a su,dan ta karantar su Darasi,Musamman na gidan Miji,. LAIFIN DADI???.. Naufal,da Nailah ne ke ta kai kawo Cikin Sittern su a parlourn,. Twins din Sa'a kenan,. Yaran gwanin sha'awa,bulo bul dasu,.Watan su(6).Amma in ka gansu ka dauka yan wata (8)ne,.Danna Button din sittern Naufal ke yi yana wakar "Twinkle Twinkle Little star,.Yayin da Nailah ke ta bangala mishi baki tana dariya tana bubbuga tata,. Da sallama ya shigo,.Daga chan kitchen aka amsa mishi,.Tuni ya karaso da sararrafa wajen yaran,wanda tun sallamar shi Suka fara murna,." Ina Matan gidan aka bar mun 2 little Angels na su kadai??..Ya cire Nailah "My little Princess,. Papa's home,.Sama ya hulla ta ya chafe,.sai dariya take bangala wa..Ya sauke ta ya dau Naufal,Shima ya masa,.Fitowa sukai a kitchen din zahra inda suke hada kwanikan lunch,. Da fara'ar su Suka fito,.Zahra dauke da karamin Cikin ta data kara Nad'a,. Jikin shi Sa'an tai kamar yadda ta saba,. Da sauri Zahra ta kau da kai,.Gudun zigin shedan,.Irin haka yasa take mar Marin yin nesa dasu,dan tasan zuciya batta kashi,kuma zo mu zauna,Tabbas wataran zo mu saba ne,gwara kazantar da bata ga ba a wajen ta tsafta ce,. Sai dai tana tunanin rayuwar gidan da bata tare da su Naufal,Ga Naina ta saba dasu,. Tai murmushi, dan tuna wa da Naina da aka kai yaye..Da tasan ta na nan da Tuni tana makale dasu Naihan.. Ta kallo Sa'a, Yadda ta maida hankali kan Mijin ta,. In Hafeez na gaban ta, toh hatta yaran ta gefe suke.,bare ita,.Tai murmushi,. Bazata kara da Sa'a ba,dan ko ta bangaren kula da Miji ta daga mata tuta,Burin su Allah ya kara hade Kansu. Alhamdulillah... Nan muka kawo karshen BARIKI IYAWA...Muna rokon Allah kuskuren da mukai ya yafe mana.. SADAUKAR WA. An sadaukar da labarin BARIKI IYAWA ga daukacin Masu karatun shi,.Da fatan an tsinci abinda ke Cikin shi. Nafisa Bashir Tanko(Feenat Ke muku fatan Alkairi. Luv All An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels

Chapter 11 of 11