Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
6 / 6
ya boye mana sun wuce yadda kake tunani''. Uche ya mike tsaye ya ce, ''Ina zuwa. Nan da minti ashirin zan dawo, ka san bana ajje kudi a gida... Idan kana bukatar abin sha ka bude firji gashi can''. Uche ya fice daga dakin cikin sauri. . ''A OFISHIN JAMI'AN TSARO!'' Suka dubi Uche cikin kaduwa. ''Gambo fa ka ce?'' Wani sajan ya tambaye shi. Uche ya gyada kai ya ce. ''Kwarai kuwa...yanzu haka yana dakina... Ni daman ina ganinsa na gane hotonsa da ku ka buga a jarida... Ya zo yana yi min wasu zantuka wai yana son ya ranci kudi a gurina... Gashi nan dai shirme kawai.... Shine na ce bari in zo na sanar da ku...'' Mintuna goma bayan haka, sama da 'yan sanda goma suka cafke Gambo. Abin da ya fi batawa Gambo rai a lokacin shi ne amanarsa da Uche ya ci. Jami'an tsaron suka taru jingim! A 'kofar gidan Uche. Sa'ar da 'yan Sandan suka fito da Gambo kowa da bindigogi. Uche ya juya zai shige gidansa yana murna sa'ar da ya ga an sa Gambo a cikin mota. Sai yaji busasshen hannu ya ratso ta cikin duhun dare ya dakumi kafadarsa. Wasu tika-tikan 'Yan sanda ne guda shida 'Me na yi muku...lafiya?'' Wani sajan ya yi masa busasshen murmushi ya ce Lafiya kalau Muje ka nuna mana dakunanka muna bukatar bincike a ciki'' ''Don me? Uche ya tambaya zuciyarsa na harbawa Katon dan sanda ya daga hannu ya kwadawa Uche mari fau Ya ce Kada dauki Jami'an tsaro mahaukata mana Shekara nawa muna lura da duk wani motsi na ka...ka ce baka san Gambo ba amma ai sau uku ke nan muna ganinsa a gidanka Uche yaji kamar katanga ce ta fado masa a baya. . Karfe tara da rabi na safe su Lanto da sauran mukarrabansa guda biyu suna zaune a gindin inuwar wani katon rumbu suna karta sai suka ji sautin injin mota Nan da nan suka mike Tani da ke zaune ita da Gudidi a can gefe guda itama ta dubi hanyar cikin mamaki ''Shege Lanto ya ce yana dariya cikin murna ''Ka ga dan iskan nan ban da kudi ma har da wata motar ya sake damfaro Inyamurin can Cab Lallai yau wayo ya hadu da wayo CUTA TA DAU CUTA! . Kowa bai san kowa ne ba'' Tun kafin motar ta gama tsayawa su Lanto suka tari gaban Landirobar fara mai duhun gilashi kofofin motar suka bude Kafin kiftawa da bismillah! Su Lanto sun yi ido biyu da hancin bindigogi sama da guda goma sha biyar. Lanto ya daga hannu sama cikin kaduwa. Wani dogon 'Dansanda ya lalube bindigoginsu. A dai-dai lokacin ne to Lanto ya hango Gambo dumu-dumu a cikin ankwa 'kafa da hannu. Gambo ya dube shi ya yi masa murmushi ya ce. ''Sa'armu ta kare Lanto.... Uche ya bata ruwa ba dan ya sha ba..... 'Kurunkus!.... TA LEKO TA KOMA!!'' Tani ta shige cikin bukkar da gudu inda Jabir ya ke kwance ta rungume shi tana kuka tana cewa. ''Jabir ga su nan sun zo...za su rabamu Jabir! Na shiga uku! Jabir ya ya zanyi da rayuwata....''. Ta fashe da kuka tana girgiza shi. ''Tashi ka dubeni Jabir....duba na 'karshe Jabir!.... Ga 'Yan sanda nan a waje''. Tani ta dada jijjiga shi ta kwalar rigar da ke jikinsa sai taji nauyi. Ta dafa 'kirjinsa.... BABU NUMFASHI! . ''Jabir''. Ta fashe da kuka. A dai-dai lokacin ne 'Yansandan biyar suka shigo cikin bukkar dauke da makamai. Tani ta dago kai fuskarta sharkaf da hawaye jikinta sai rawa yake yi kamar mazari ta ce da 'Yansandan. ''Ba kwa bukatarsa.... YA MUTU!!''. Wani 'katon 'Dansanda mai ciki kamar tudun ganuwa ya matso kusa da gawar Jabir ya latsa cikin gawar da tsinin bakin bindigarsa, sannan ya juyo ya dubi Tani cikin murmushi ya ce. ''Mutuwarsa tafi masa sauki!!''. Tani bata taba jin mummunar kalma irin wannan ba a rayuwarta!''. * Sidi mai Jaka ya yi doguwar mika gami da hamma ya dubi tsohon agogon sa Omega a cikin hasken farin watan ya ce. ''Zan shiga gida Nas, lokacin barci na ya yi.... Ina fatan ka gamsu da wannan labari.... Ka kuma san cewa baka bata lokacinka a banza ba ko?''. Na dubeshi cikin kaduwa na ce. ''A'a ai baka gama labarin ba... Labarin bai kare ba'' Sidi mai Jaka ya mike tsaye ya ce ''To me kake son ji kuma NAS?'' Na dube shi sa'ar da ya mike tsaye na ce da shi cikin kaguwa. ''To ya ya kuma maganar cikin da Tani take da shi?'' LINZAMIN SHAIDAN-16 . KARSHE . ''To ya ya kuma maganar cikin da Tani take da shi?' . Sidi mai Jaka ya ce. ''Kai dai Nas kafi son sai an kai maka labari har kurun-Kus! Ai kasan dai 'Yansanda sun kame su... Ai labari ya 'kare. Tani ta koma gidansu a can kauye ta tarar da mahaifinta, amma mahaifiyarta ta rasu sakamakon ciwon hauhawar jini da ta yi ta fama da shi tun sa'ar da aka kawo musu labarin cewa 'yan fashi sun dauketa... Bayan wata shida Tani ta haifi danta na miji, amma Allah ya yi mata rasuwa a ya yin haihuwa''. . Sidi mai Jaka ya yi shiru yana dubana. ''Shike nan ko?'' Ya tambayeni ''Da saura Baba'' Na ce da shi ''Ni duk ka kare min labarin cikin gaggawa..'' ''To me kuma kake son ka sani.. duk zarurrukan labarin masu dadi sun kare sauran koda an baka su gundurarka za su yi...'' ''Ya ya kuma labarin Ja'e da matarsa?''. Na tambaya. ''A'ah! Anan aka barsu suka ci gaba da rayuwarsu''. Sidi mai Jaka ya ce lokaci guda kuma ya fara 'kokarin nade buzunsa. ''A labarin da ka bayar, na ga tun da aka fara labarin kake bayanin 'yan fashin su biyar ne, akwai Gambo, Lanto, da kuma Jabir, amma har ka 'kare ban ji ka ambaci sunan sauran guda biyun ba... Kuma labarin da aka bayar a ina ka sameshi?''. Sidi mai Jaka ya rungume buzunsa. ''Kai dai NAS ka cika tambaya da bin 'kwakkakkwafi! Kaidai kawai in za ka ji labari ka ji kawai... Nima wannan mutane biyu da kake bayani ban san sunansu ba a haka naji labarin... . In kuwa na sami labarin nima na manta... Na fada ma tun farko dattijo kamata bai yin karya sai dai dan karin gishiri dan labari ya yi dadi... Amma 'karya dai kam babu zancenta.. domin KARYA.. LINZAMIN SHAIDAN CE. . Nas Allah bamu alheri Sidi mai Jaka ya juya zai shiga gida Baba Nayi kiransa cikin sauri Na mike tsaye sannan na lalubi aljihuna na dauko takardun kudi masu yawa na mika masa na ce Ka manta baka karbi kudin labarinka ba.. Sidi mai Jaka ya dubeni cikin murmushi ya ce. ''Nas, wasa na ke yi ma.... In banda abinka tsoho kamata mai zai yi da kudi masu yawa haka? Kada ka damu, wata rana in ka so jin wani labarin, idan za ka dawo kada ka manta ka taho min da TUBANI!...'' . ALHAMDULILLAHI . KARSHE. . An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels

Chapter 6 of 6