Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
1 / 6
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels LINZAMIN SHAIDAN Complet (M) Nazir Adam Salih Made by Shuraih Usman @http://fb.com/hausaebooks INZAMIN SHAIDAN-01 . A cikin irin ni'imantattun ranakun nan ne ma'abota lullumi da sassanyar iska mai sa ka manta kofar shiga gidanku ne na fito daga namu gidan sanye da 'yar fingila-fingilar riga ta shan iska zuwa kofar gida. In da na fito din gindin katangar wani gida ne in da duk sa'ar da rana tayi yamma sai inuwar katangar ta mamaye gurin musamman ma idan akace karfe biyar na yamma ta dan gota. Fitowa ke da wuya sai na hangi benci babu kowa a kai dan haka sai na nufi inda bencin yake da niyyar na zauna domin taren daddadar iskar dake busowa daga gabas zuwa yamma. Kai bani kadai ba hatta kananan kwari da kudaje kokarin kai kansu suke ga inuwar dan hutawa. A dai-dai lokacin ne to naji anyi min sallama. 'Amin wa'alaikumussalam'' Na amsa game da juyawa lokaci guda. Wani dan saurayi ne mai fuskar matsorata ke yi min sallamar. Saurayin dogo ne mai dogon baki, sanye da doguwar riga fara, tashi ka fiye naci sanye a dogon kansa. Shekarunsa zasu iya yin dai-dai da nawa, to amma me yiwuwa na bashi koda watanni ne. ''Kaine Nas?'' Ya tambaya kai tsaye ba tare da ya 'bata lokaci ba. ''Na'am, ni ne''. Nace dashi ina dubansa. ''Zauna mana'' Nace dashi gami da nuna masa bencin da hannuna. Sannan lokaci guda sai na zauna ina mai sauraron ya zauna, domin tabbas nasan wannan shima ire-iren abokaina ne makaranta da suka saba kawo min ziyara lokaci-lokaci. ''Nas ba zama ne ya kawo ni ba''. Yace da ni gami da sakin wani busashshen murmushinsa na kure adaka. ''Wani kakana ne yake son magana da kai''. Kusan dakiku biyar ban amsa ba, domin kallonsa kawai nake yi ina mai kokwanto anya kuwa naji abin da ya fada dai-dai? ''Kakanka fa kace?''. Saurayin ya gyad'a kai. ''Kwarai kuwa''. Yace da ni. ''Yanzun nan yake son ganinka, dan tun jiya nake zuwa nemanka Allah bai sa na same ka ba sai yanzu''. Na dubeshi cikin mamaki. ''A ina kakan naka yake?''. Saurayin yayi murmushi yace. ''Kada ka damu. Shin baka san SIDI MAI JAKA bane?''. Na dube shi cikin mamaki a karo na biyu nace. ''A'a nasan shi mana. Dama kai jikansa ne? Amma ba'a unguwar nan kake da zama ba ko?''. ''Kwarai kuwa, shekaran jiya na dawo daga Kaduna. Kuma ni makarancin littattafanka ne, to shine nazo dasu da yawa, sai shi kakan nawa ya gani shine yake tambayata wai me muke ji idan mun karanta littattafan nan? A take a gurin na ce dashi ya saurara na karanta masa yaji. To shine shekaran jiya da daddare na karanta masa littafinka ''NAIRA DA KWABO'' ina gama karantawa sai na ga ya fara kuka, shine to ya takura akan wai dole sai na kirawo masa kai, domin an sha bashi labarin cewa akwai wani yaro marubuci a unguwar nan''. . ''Tashi mu tafi''. Nace da shi. Zaka yi mamakin dalilin tashi na lokaci guda. To amma zuwan nawa gurin dattijon shine tushen duk wani labari da zaka ji daga baki na. Lokacin da muka 'karasa zauren gidan dattijon na zaune akan kujerar katako yana jiran zuwanmu. Tun kafin mu karaso gareshi ya fara yi min murmushin marhabun. Kallo daya nayi masa sai naji ina kaunar dattijon a raina. To saidai kuma bana kaunar irin warin daudar dake fita daga jikinsa. Ga dukkan alamu dattijo Sidi Mai Jaka ya dade rabon da suyi musabaha da sabulu. Dattijon dogo ne fari, haka nan kansa fari fat da furfura, gami da dogon farin gemu, wanda ya dace da doguwar fuskarsa, gami da fashin goshin dake fuskarsa. Kayan da suke jikin dattijon duk tsummokara ne yagaggu, haka nan kuma idan kayi nazarin irin kayan dake jikinsa zaka fara tunanin lallai ba irin kayan wannan karni da muke ciki bane. Dattijon sanye yake da farin tabarau, me yiwuwa na kara gani ne, shekarunsa zasu kai saba'in da doriya a duniya. Hakan shi ya sani matukar mamaki sa'ar daya dube ni yana murmushi, domin duk kusan hakoransa suna nan ras a bakinsa babu wanda ya fita. ''Sannu da zuwa samari''. Yace da ni. Sannan sai ya dubi saurayin daya tura kirana. ''Dan bamu guri zamu gana''. Saurayin yayi biyayya ya fice daga zauren kai tsaye. A dai-dai lokacin ne ni kuma ke zaune ina ta faman nazarin zauren gidan. Babu wani abin ku zo ku gani, komai irin na da can ne. Yanayin ginin, rufinsa kai duk wani abu dake gidan na wancan 'karnin ne. . "Naji dadin zuwanka Nas. Ko da yake na san yanzu cike kake da mamaki?'' . ''Kwarai kuwa Baba''. Nace dashi cikin ladabi. . "Sunana Sidi mai Jaka, kamar kuma yadda me yiwuwa zaka sami labari a gurin iyayenka, ni ba asalin dan garin nan bane, zuwa nayi.... Koda yake sa'ar nan ba a haifeku ba....'' Na gyada kaina gami da murmushi. ''Jiya wannan jikan nawa dana tura kiranka ya karanta min wani labarinka daya tayar mini da hankali Shine to yanzu na 'kiraka muyi cinikin wani labarin idan zaka siya....''. Maganar ta girgiza ni. To amma sai na dauka wasa yake, dan haka sai kawai nayi dariya ban amsa masa ba. Sidi mai Jaka ya muskuta a hankali yana dubana, sannan sai ya cire tabaron dake fuskarsa yana kallona kamar wanda ke tsammanin zai sami wani abu a ciki, dan lokaci sai ya mai da shi idanunsa yace. ''Kamar yadda kake gani a yanzu ni talaka ne, ina bukatar taimako, don haka in kana so to sayi na sayar maka wani labari da me yiwuwa ya isa ka maida shi littafi''. Na dago a hankali na dubeshi a karo na farko nace. ''Baba da gaske kake?''. Sidi mai Jaka yayi dariya, sannan yace. ''Haba dana, zan 'kira ka har nan na fada maka 'karya ne ? Ai kasan dattijo kamata baya fadan 'karya, domin ita KARYA LINZAMIN SHAI'DAN ce. . Kai dai in kana so ka saurareni da kyau mu gani daga nan zuwa sallar magariba.....kona zo maka da labarin da me yiwuwa da kanka zaka ga ya dace ka biyani''. Na muskuta cikin mamaki da 'kosawa, domin tuni ya fara gundurata. Dan na sha jin irin labarin tsofaffun nan rikitattu wanda gigin tsufa ke sa su shirme. ''Yanzu in ba haka ba wannan tsoho wane labari yake da shi da har ya isa a saya?''. Nace cikin zuciyata ina kokarin mikewa tsaye. To amma banyi hakan ba don gudun kada yace na raina shi ko kuma na muzantashi a matsayinsa na dan adam. ''Kada ka gudu 'dana, nasan abin da kake tunani, kana tsammanin bani da hankali ko? To ba haka bane, saurareni da kyau, idan kaga labarin da zan baka duk bata lokaci ne to sai ka tashi kayi tafiyarka''. Dattijo Sidi mai Jaka yayi shiru yana dubana. Ga mamakina sai na ga 'kwalla ta fara tsartu tsakanin fuskarsa da gilashinsa. 'Dana da ace na iya rubutu da bazan taba baka labarin nan ba, da ni zan rubuta kayana, don nasan ko nawa zan sayar maka shi a yanzu to ba riba sai faduwa''. Na dubi agogon dake hannuna, a dai-dai sa'ar da dattijon yayi shiru. Ina da alkawari da wasu samari da zasu zo nemana da karfe shida na yammacin, dan haka sai nace da shi. ''Baba ka bari to da magari ba sai na dawo ka.....'' Ya katseni sa'ar da ya daga busassun hannayensa sama. ''Nas kada kayi gajen hakuri......kada ka raina ni...abin da nake so da kai shine, bani mintuna goma kawai na fara kwararo maka labarin, idan kaji duk shirme ne bai birgeka ba, babu kuma ma'ana, to nayi maka uzuri kana iya tafiya abin ka''. Banso ba domin nasan kawai 'bata lokaci zan yi.... To amma tun da yace minti goma.... To minti goma ba su kasheni....'' ''Ina sauraronka to''. Na ce da shi ina duban farin gemunsa. ''Yauwa Nas, ko kai fa..... Sai kace ba marubuci ba...?'' Sannan sai ya fara da cewa. . ''Shekaru Ashirin Da Biyar Da Suka Shude.....'' LINZAMIN SHAIDAN-02 . 'Nas ina son kadauki zuciyarka ka maida ita can baya kimanin shekaru kusan ashirin da biyar ke nan da suka wuce Haka nan Nas ina son ka aiyana cikin zuciyarka cewa a cikin wani babban asibitin kashi na kudi kake'' ''Duk nayi abin da kace'' Nace da shi. Har yanzu tunani nakeyi tababbe ne amma shi ko a jikinsa, sai kawai ya daga kansa yaci gaba. ''A cikin wani katon asibiti ne zarurrukan labarin suka fara 'kulluwa. Tun goshin magariba na ranar garin ya yi baki kikkirin, domin a cikin watan Augusta ne, dan haka da zarar gari ya bata rai sai kaji an saki ruwa babu ko wani 'kwakkwaran gargadi. To amma sabanin sauran ranaku a wannan ranar tun magariba ake ta rugugin aradu kamar sararin samaniyar zata fashe gida biyu, har zuwa karfe tara na dare ana barazanar amma ba'a saki ruwan saman ba sai tara da minti ashirin na dare. Da yawa daga cikin ma'aikatan dake a sibitin basu ji dadin ranar ba, domin wasu ruwa yayi musu dukan tsiya akan hanyarsu ta zuwa gurin aiki, domin karbar wadanda suke aiki tun karfe biyu na rana har zuwa tara na dare. Ya yin da kuma suma wadanda ke tafiya gidajensu a lokacin suka ci dan banzan dukan ruwa, musamman ma wadanda gidajensu ba'a cikin harabar asibitin suke ba. Ba'a taba asibitin da ya tara 'kwararrun likitoci ba irin wannan duk fadin kasar nan haka nan matsala in dai ta kashi ce a jikin mutum koda kashin dagargajewa ya yi in dai yana gurin bai zube ba to za'a mayar da shi su hadashi guri guda tamkar yadda kake hada zararrukan labarinka guri guda ka kawo karshen matsalar. Ba a dade ba sai ruwan ya fara karfi. Hakan ce ma tasa da yawa daga cikin ma'aikatan da ke aiki a asibitin masu motoci sai tsayawa suka yi a ranar suna jiran ruwan ya tsagaita kafin su tafi duk kuwa da cewa lokacin tashinsu ya yi. . A dai-dai wannan lokacin da ake sheka uban ruwan ne wata Malamar asibiti ta shigo farfajiyar cikin sauri dauke da lema a hannunta, amma duk a banza domin ruwan ya gama jikata jagaf. Ta ratso ta tsakanin shuke-shuken furannin da suka yi sahu-sahu ko ina a farfajiyar asibitin ta nufi inda dakin 'karbar 'yan hatsari na gaggawa yake, inda kuma anan ne yake aiki. ''Daman ke na ke jira wallahi.... Nasan ruwan nan ne ya sa ki makara. Dubi fa har kusan tara da rabi.....''. Wata Malamar asibiti da ke tsaye jikin wata 'kofa ta gilashi tace. ''Haba Falmata, duk gaggawarki ki dai ai kya bari ruwan na ya dan tsagaita..... Baki ga fa nima da yadda na 'karaso ba.....'' ''A'a Asabe wallahi tafiya zan yi..... Kin ga yarinyata yanzu nasan tana nan tana cin uban kuka a gida..... Ni kam tafiya zanyi...... Allah ma yasa daman tun safe dana ga alamun hadari na zo da rigar ruwa...''. Cikin 'yan mintuna sai ga Falmata sanye da rigar ruwa. ''To Allah bamu alheri Asabe, ni na tafi''. Da haka ta fice ta shiga cikin feshin ruwan. Asabe ta bita da kallo har sai da ta bace a cikin 'kananan 'kwayoyin ruwan. Sannan sai ta saki tsaki ta juya zuwa cikin dakin gaggawa da majinyata ke kwance. . Dakin dogo ne, mai tsayin gaske, akwai dan bangare da aka ware a cikin dakin ta hanyar katange gurin da gilashi, wanda anan ne Malaman Asibitin da ke kula da marasa lafiyar suke zama. Sauran gurin kuma gadaje ne sama da guda goma sha biyar. Kusan kowannensu dauke yake da majinyata ana kara musu ruwa kafin a shiga dasu dakin da za'ayi musu aiki. Wasu hannayensu a rugurguje, wasu 'kafa a balle, ko kuma 'kafafuma gaba daya, wasu ko suna ihu suna ''Wayyo Kwankwasonsu!'' Kai abin babu kyan gani Nas. Asabe ta fara bin gadajen da majinyatan suke kwakkwance tana dubansu gami da yi musu allurori. Koda yake banda Asabe ma akwai wasu (Nurses) din guda biyu wadanda duk suma anan suke aiki. 'Daya bahaushiya ce, dayan kuma namiji ne inyamuri, sunansa Peter. . Aka saki wata katuwar aradu wacce ruguginta ya girgiza dakin. Haka nan kuma yasa Asabe dan jinkirtawa da tsinin allura a hannunta dan gudun kada taje tayi ba'a dai-dai ba. Dan hakika tsawar ta girgiza ta......don in har akwai abu daya da ta tsana a duniya tsawa ce. A dai-dai lokacin ne 'kofar dakin majinyatan ta bude, sannan suka fara shigowa daya na bin daya a baya, kai kace tafiyar tururruwa. Su hudu ne suka shiga dakin sanye da bakaken kwat-kwat da wando. Ko wannensu sanye da bakin tabarau, fuskokinsu kuma duk bakakene masu gizo da duzuduzu din gashin baki kamar ciyawa, in ka dauke daya daga cikinsu wanda shi fari ne matashi, baifi shekarunka ba Nas. Lokacin da suka shigo dakin tafiya suke irin ta fatalwa. in har haka ya dace na fada, domin su kansu Malaman Asibitin basu san da zuwansu ba sai kawai jin numfashinsu suka yi a kansu. Asabe ce ta fara juyowa sannan sai sauran Malaman Asibitin suma suka juyo cikin mamaki. Mutanen hudu suka dubi Malaman Asibitin da fuskar katako. Nan da nan sai mamakin Malaman Asibitin ya fara narkewa zuwa fargaba. ''Me.....kuke so....?''. Asabe tace dasu cikin 'karfin hali. Ko kusa ko alama basu yi mata kama da mutanen da ta saba gani ba. Farin saurayin dake cikinsu ya dube ta da kyau, sannan sai yace, cikin wata irin sassanyar murya. ''Marar lafiya muka kawo muku''. Kusan minti biyu Malaman Asibitin basu tanka ba. Can dai daga 'karshe Asabe tace. ''Yana ina?''. ''Yana cikin mota yana zubar da jini''. Saurayin yace da ita. Lokaci guda kuma ya dubi sauran mutanen uku dake tsaye kamar gumaka idanuwansu a boye cikin tabarau yace. ''Ku shigo musu da shi su tsaida jinin''. Tun kafin ya rufe bakinsa suka juya suka sake ficewa cikin uban ruwan da ake shekawa, sannan sai saurayin ya juyo ya dubi Asabe ga mamakinta sai taga yayi mata murmushi yace. ''Kada ku damu da shirunsu, haka nan Allah yayi su kamar kurame''. In har murmushin da ya yiwa Asabe farin ciki, to wuka akan wuyanka ma zata iya saka ka farin ciki. . ''Yal......yalla6ai kun san fa bama karbar mutum indai hadari ne sai anzo da 'yan sanda''. Peter yace gami da share gumi. Ko shakka babu yasan wadannan mutanen basu da cikakkiyar gaskiya. ''Kada ka damu dan samari, ko nawa ne zamu iya biyanku, amma ku mance da maganar 'yan sanda duk wannan bata lokaci ne kuma bata taso ba. Majinyacin namu yaji rauni sosai, harbinsa akayi a 'kafa''. Yayi shiru yana duban fuskokinsu gami da jin dadi cikin zuciyarsa dan ganin duk sun gama tsurewa. Shi kuwa yasan alkawari ne ko a mutu ko ayi rai sai an cirewa dan uwan nasu alburushin da suka sami matsugunni a cinyarsa, domin mutumin yana da matukar muhimmanci a gurinsu, in ba dan haka ma ba da tuni sun harbe dan banza. Yace cikin zuciyarsa. ''Yallabai ai dole ne sai an kawo 'yan sanda.....da'' Peter ya sake cewa bakinsa na rawa. ''Shut up!''. Mutumin ya buga masa tsawa. ''Mun san cewa mafi yawan asibitocin kudi kukan 'karbi 'yan hadari ko da kuwa ba a zo da jami'an tsaro ba....shi yasa muka zo nan, don haka dole ne na maimaita, ''DOLE NE! KU MAGANCE SHI KO KUNA SO KO BAKWA SO, KAJI KO!!''. . Peter yaji kamar 'kafafunsa ba za su iya daukarsa ba don haka sai ya nemi wata kujerar roba dake nan kusa da shi ya zauna. ''Kayi hakuri.....yallabai''. Yace dashi muryarsa na rawa. ''Ya kuma rage naka'' Mutumin yace, sannan sai ya harde hannayensa a 'kirjinsa yana kallonsu da fuskar katako. Duk fa abin nan da ake yi a kunnen wasu kadan daga cikin majinyatan masu rangwamen jigata ake yi, to amma duk da hakan bata hana wadanda ke shan azaba ci gaba da gurnaninsu ba, domin su bama a cikin hankalinsu suke ba. Asabe ta rikice tsantsa dan ji take kamar zata fadi. Har yanzu ruwan ake ta tafkawa kamar da bakin teku. 'Kofar dkin ta bude da 'karfin gaske, sannan mutanen uku suka shigo dauke da wani sunyi cali-cali, mutumin sai ihu yake yana cewa, ''Wayyo 'kafata!''. ''Ku dorashi a can''. Asabe tace da su gami da nuna musu gado. Zuciyarta sai wasi-wasi take, ko shakka bata yi tasan duk yadda akayi mutanen nan basu da gaskiya. Me yiwuwa ma 'yan fashi ne, domin in ba haka ba yaya zasu kawo mutum an harbeshi kuma su hana a 'kirawo 'yan sanda. ''Wayyo!....oh! ......ah!.....'kafata......'' Tunaninta ya katse sakamakon ihun marar dadin ji dake fita daga makogwaron mutumin. ''Ku tsayar masa da jinin mana kun tsaya sai kallonmu kuke kamar wasu aljanu.... Ko baku taba ganin mutane bane!!''. 'Daya daga cikin ba'ka'ken mutanen nan ya buga musu tsawa. ''Sai an 'kirawo likita''. Asabe tace tana dubansu a tsorace zuciyarta nata wasi-wasin yadda zata sami hanyar tsira daga hannun wadannan masu kama da iblisai. ''A ina likitan yake?''. Saurayin fari ya tambayeta. ''Mace ce.... Anan baya gidanta yake.....sai dai ko in buga mata waya....''. Mutanen hudu suka dubi juna suna zance da idanu, domin a yanzu sun fahimci cewa ashe duk cikin wadanda suka ritsa din ma babu likita....in kuwa har suna so a cire masa alburusan da ke 'kafarsa to dole ne sai sun sami likita. ''Ku tsaida masa jinin..'' 'Daya daga cikin mutanen yace... INZAMIN SHAIDAN-03 . In kuwa har suna so a cire masa alburusan da ke kafarsa to dole ne sai sun sami likita Ku tsaida masa jinin. Daya daga cikin mutanen yace gami da nuna daya Malamar Asibitin da kuma Peter da hannunsa ''Ke kuma 'yar tsakuwa muje ki kirawo likitan naga ai kina da kan talfon a nan ma ko?' Yace yana mai nuni da kan wayar dake kan tebur a cikin dan zagayayyen gilashin da aka ajiye a matsayin Ofis Mutumin da suka zo dashi sanye da kaya bakake irin nasu fari ne mai tarin gashin baki fuskarsa sai faman naso take yi da gumi kamar funkaso mai miya A daidai lokacin da Malaman Asibitin suka nufi gadon da yake yana murkususu sai wani abu ya fado daga kan gadon zuwa dandamalin tsakar dakin Malaman asibitin suka dubi abin cikin kaduwa dan tun da suke basu taba ganin mummunar BINDIGA irin wannan ba. ''Ah!'' Daya Malamar asibitin ta rufe bakinta cikin kaduwa zata yi ihu. Idanun Peter suka firfito kamar idanun kwado a hantsi. Asabe ta fara juyowa a hankali dan ganin abin da ya fado, sai taji an tsikari 'kugunta da wani abu mai tsini. Numfashinta ya dauke sa'ar data ga farin saurayin nan ne a bayanta dauke da bindiga yana murmushi. ''Muje ki kirawo mana Likitar....barikuma in gargade ki babu yaudara, kiyi mata magana da irin muryar da kika saba magana da ita, idan kuwa kika sake ta gane cewa wani abu na faruwa to kada ki raba daya biyu, ni bani da asara dan na harbi kyakkyawan 'kugun nan naki da alburushin bindigata.. . Tuni mun kashe wasu a baya kinga kuwa 'karin wata gawar ba zai zama aiki ba, tun da likkafani dai kin san yana araha''. Asabe ta nufi gurin talfon din cikinta na 'kugi, bakinta ya gama bushewa don tasan tsakaninta da mutuwa NAS bai fi ni din nan da kai ba. Asabe ta dauki kan talfon din ta buga. Bayan yan dakiku sai tace a cikin kan talfon din. ''Tani ce....?''. ''Nice Asabe ke magana daga (Emergency room). Muna son ganinki da gaggawa, majinyaci ne a hannunmu yana shirin mutuwa, kuma gashi kece a kurkusa''. Saurayin dake kusa da ita ya dube ta da fuskar katako, sannan sai ya dada tsinkara mata bakin bindigar yace. ''Kada ki bata mana lokaci, don in ya mutu duk tare za'a binne ku da shi!!. Barazanar dake muryarsa a lokacin ta isa tasa mace mai ciki ta haife. . Sidi mai Jaka yayi shiru a karo na farko tun sa'ar da ya fara labarin, ya dube ni yana murmushi, sannan lokaci guda sai ya dubi tsohon agogonsa (Omega) wanda shima me yiwuwa tun kafin a haifeni suke tare da agogon. Ya tattare tsumman rigarsa ya ce dani. ''To Nas gashi har tsawon minti ashirin da tara ana labarin baka motsa ba... ya ya ka gani na iya ci gaba ko kuwa tafiyar zaka yi?''. Na dubeshi cikin kaduwa domin ban taba tsammanin irin wannan labari zai iya fita daga bakin wannan yan'kwanannen tsoho mai farin gashi ba. ''CI GABA'' Nace da shi cikin 'kaguwa don jin yadda zata 'karke. ''To ya akayi daga 'karshe? Likitan ta zo?''. Na tambaya ina dubansa. Sidi mai Jaka ya shafi farin gemunsa yace. ''Ka cika garaje dan saurayi Nas, kai dai biyoni a hankali, da sannu da sannu a hankali zan jera maka zararrukan labarina kamar yadda injin masaka ke yiwa auduga, daga 'karshe kuma na hada zararrukan labarin na dinke su guri guda. Da ace nine kai, ma'ana da ace na iya rubutu to da ba 'karamin marubuci za'a yi ba'' 'Haka ne''. Nace dashi cikin 'kaguwa ya ci gaba. . Sidi mai Jaka ya lalubi aljihun tsumman rigarsa ya fito da goro, ya balgata ya jefa a baki sannan sai yaci gaba ''Nas a matsayinka na marubuci indai kana biye da ni sannu a hankali tun daga farkon labarin nan zaka fahimci cewa tun da muka fara akan zare daya kawai muke tafiya. To yanzu zan aje wancan zaren guda daya wanda ke dauke da mutane takwas Likitoci Uku da wasu mutane biyar zan dauko wani sabon zaren in yaso daga karshe idan na gama saqa shi sai na hada bakinsu da wancan na farkon na kulle'' 'Haka ne'' Nace da shi a karo na biyu cikin kaguwa ''To Nas ina so ka kaimun zuciyarka wani yalwataccen gida ma'abocin lambu mai dauke da wadatacciyar iska ni'imantacciya A cikin lambun wata kyakkyawa ce ta gaske daga cikin kyawawan mata na zamaninta A wannan yammacine tana zaune ita kadai a cikin wannan lambun zuciyarta rabi da rabi ita ba'a farin ciki ba haka nan ba'a bakin ciki ba to amma masana magana sun ce wai ko babu ji akwai jimami to lallai kuwa akwai jimamin a tattare da wannan mata Nas To amma kafin naci gaba bari in baka hoto da tarihi na wannan kyakkyawar mata Nas Doguwa ce fara siririya amma ba can ba tana da wasu irin juyayyun Idanu masu kyau na mamaki wadanda ke dauke da wani sihiri mai karfin gaske da kan cafe zuciyar duk wanda ya kalli kyakkyawar fuskar matar Me yiwuwa ka ji ina cewa matar ka yi tsammanin ko ta taba aure? To ko kusa ba haka bane tunda take bata taba aure ba a rayuwarta domin tun tashinta tasa karatun boko a gaba duk kuwa da cewar da kyar iyayenta suka barta saboda yawan zagezage da gulmace-gulmace da iyayen ke sha a gari ana cewa sun daure mata gindi ta ki yin aure Wanda daga karshe a haka har dai da kyar ta gama karatun ta na jami'a mai tsayin tsiya domin kuwa karatun aikin likita ta koya Tana 'yar shekara ashirin da takwas ta gama karatunta domin ko da can ma bada wuri aka sata a makaranta ba sai da tayi kusan shekara goma ba kadan a ka saka ta To dan haka sa'ar da ta gama karatun sai manema suka fara fitowa daga ko ina dan neman aurenta to sai dai kuma akwai matsala daya Wannan mata da na ke baka labari iyayenta a wani kauye suke anan jihar Kaduna dan haka sa'ar data gama karatun sai ta ga a gaskiya saninta ya wuce na samarin kauye dan haka ba ajinta banesu kuma bata iya aurensu Haka dai aka yi ta yawo da 'yan kananan maganganu ana zargin iyayenta ana cewa sun batata'' . Sidi mai Jaka yayi shiru yana dubana sannan sai yace ''Nas a duniya gaba daya babu abin daya fi 'Da shiga rai....musamman ma idan aka ce shi kadai Allah ya baka'' Nace da shi ''Haka ne. Gaskiya ka fada'' . Sannan Sidi mai Jaka yaci gaba. ''To wannan mata ita kadai Allah ya baiwa iyayenta. Mahaifinta attajiri ne na kauye, sana'arsa noma da kiwon dabbobi. Ba'a dade ba sai 'yar tasa kwaya daya a duniya mai suna TANI ta samu aiki a wani babban asibitin 'kashi na kudi dake birni. Bayan anyi ta jayayya daga karshe dai iyayen nata suka barta ta fara aikin, amma sunce ta nemi mijin aure nan da shekara daya, in kuwa ba haka ba to zasu bata dan 'kauyen da ta tsana. Wannan gargadi na iyayenta shi yasa Tani cikin tsaka mai wuya, domin ita tun daga zamanin karatunta a jami'a har zuwa yanzu bata taba ganin wanda take 'kauna ba sai sau daya, a sa'ilin da take jami'a akwai wani saurayi sa'anta domin shima zai yi ashirin da takwas a duniya. 'Dalibai da dama sun yi mamakin ganin yadda kamilar budurwa kamar Tani take masifar kaunar saurayi Jabir, domin Jabir yana daya daga cikin manya-manyan tambadaddun makaranta. Jita-jita na cewa ma wai yana daya daga cikin 'yan haramtacciyar 'kungiyar asiri ta jami'ar ta 'yan ta'adda. Tani ta mance da dukkan surutan jama'a suka ci gaba da soyayyarsu da Jabir. Duk inda zasu tafi tare suke zuwa. Ko ina zata Jabir yana kusa da ita, hakan tasa dalibai da dama 'yan bogi suke shakkar yiwa Tani magana, domin kowa yana tsoron Jabir'' 'Nas''. . Sidi mai Jaka yayi kirana yana tsotse-tsotse. 'Wasu lokuta duk irin yadda mutum yake sai yaga rashin sa'a a rayuwarsa''. 'Haka ne''. Nace da shi. ''To irin wannan rashin sa'a ita ta fara samun Jabir, domin yana shekararsa ta 'karshe aka kamashi yana satar amsa dumudumu, daga nan kuwa suka koreshi gidan ubansa''. ''A ranar da aka koreshi da yamma yazo ya sami Tani a dakin karatu ta kifa kai akan teburin karatun tana ta cin uban kuka. Jafir ya dafa kafadarta yace. ''Don't worry Tani (kada ki damu) . Ni da ke sai Allah ke rabawa, amma ba wani shege ba. Tani yau zan bar makarantar nan, bazan kuma sake dawowa

Chapter 1 of 6