Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
3 / 6
ba su fahimci abin da kake son fada sosai ba shi ya sa ka ji an fashe da dariya''. Ganbo jikinsa na rawa idanunsa jajur kamar gauta ya hadiye zuciyarsa da 'kyar, domin da an ci gaba a haka to da jikin wani a cikinsu ya yi tsami. Jimawa kadan Gambo ya nisa ya ci gaba. ''Dole ne mu bi hanyar da shima ya bi ya samu, domin in ba haka ba to sai dai mu mutu a wahale''. Jabir ya dubeshi ya ce. ''To kai sai kwana-kwana kake ka 'ki ka bamu maganar a mike ko ma gane abin da kake son fadi. Mece ce hanyar daya bi?''. ''Fashi!...... Fashi mana!!'' Gambo ya amsa kai tsaye yana dubansu dai-dai kamar Malami a gaban dalibansa. Jabir yace da shi. ''Kazo da sabuwar bidi'a''. ''Yanzu in ban da shirmenka yaushe ne wadanda ko dan kin harbi bamu da shi zamu tafi fashi...'' Gambo ya girgiza kai cikin sauri. ''Indai dan wannan ne kada ka damu kanka, ina da aboki inyamuri a can cikin kasuwar gwari, na san a dubu hamsin sai ya bamu hayar bindigogi biyar da aron mota marar lamba, wacce koda abin Allah ya kiyaye rana ta baci ta 'yan sanda ba za su taba gano daga inda motar ta fito ba balantana ma har ga batunmu''. . Ya sake yin shiru yana nazarin fuskokinsu, kowa a cikinsu wasikar jaki yake karantawa. To amma akwai wani yanayi a tattare da fuskokinsu daya 'kara masa kwarin gwiwa. ''kunga wannan itace damar mu ta 'karshe, ko dai muyi arziki, ko kuma mu mace a berayen masallaci. Ku dubi yadda dan iskan nan ya kera wannan makeken gida gari guda, ga matarsa kyakykyawa kamar balarabiya, amma mu gamu duk a bushe kullum ta ci ba ta ci ba''. Ya danyi shiru yana dubansu. Abin da ya gani a fuskokinsu ya gamsar da shi, dan haka ya mike tsaye yace. ''Nine ja gaba na wannan tafiya, duk wanda ke iya yin fashi a cikinku to ya mike tsaye in ganshi, wanda ko bai iyawa gara tun da wurwuri ya kama gabansa domin jin sauran sirrinmu hadari ne''. . ''Kyakykyawar mace kamar balarabiya''. Jabir ya maimaita kalmar Ganbo a cikin zuciyarsa. Nan da nan sai wani zazzafan gumi ya fara barkowa akan goshinsa, jikinsa ya fara tsuma, domin kyakykyawar macen da aka ambata a cikin bayanin sai ta tuna masa da abar 'kaunarsa Tani wacce duk wani 'kokari na buga-bugar rayuwa dan ita yakeyi. Jabir ya sha jin ciwon korarsa da aka yi a jami'a. Haka nan kuma har yanzun nan abin na fado masa lokaci-lokaci, musamman ma idan suka yi kicibus ko kuma idan ya hangi wasu daga cikin...INZAMIN SHAIDAN-07 . Ko kuma idan ya hangi wasu daga cikin abokan karatunsa To amma duk ta wannan kamar shafar mai ce a gurin Jabir in har za a kwatanta da irin zafin ciwon rabuwarsa da Tani da yake ji a cikin zuciyar ta sa musamman ma idan ya tuna da irin rabuwar da suka yi. ''.... Me zaki yi da dan iska irin Jabir....'' '.... Ke dai kin zubar da mutuncinki wallahi....''Mutane fa duk daukar yar iska suke yi miki saboda kina yawo da Jabir.. Maganganun cece-kucen da dalibai sukayi ta yiwa Tani a kansa ne suka yi ta dawowa zuciyarsa Wadannan abubuwa baza su taba rabuwa da zuciyarsa Jabir ba domin a kullum idan ya tuna da irin wulakancin da bakaken maganganu da zagi da turanci da duk Tani ta hakurce tace taji ta gani shi take so Sai Jabir yaji duk duniya babu abin da zai iya sakawa Tani da shi koda kuwa ransa zai bata sai dai yayi iya 'kokarinsa Dan haka a yanzu da Gambo ya ambaci kyakkyawa kamar balarabiya sai Tani ta fado masa Ba tare da yayi tunanin makomarsa ga Ubangiji ba bai kuma tuna da cewa duk wanda yayi fashi idan aka kama shi harbewa za a yi ba abin kawai dake zuciyarsa a wannan lokaci shine wannan kawai itace mafita hanya daya zai sakawa Tani da ita abin da tayi masa .. Zan sai ma ta motocin hawa...na gina ma ta katon gida mahadi ka ture...in bata duk abin da take so na jin dadin rayuwa...'' Ya fara lissafo abubuwan da duk zai ma ta in har aka sami kudi Da wannan tunani sai Jabir ya ciri tuta a cikin sauran mutanen domin shi ya fara mikewa tsaye wanda hakan na nufin ya yi amanna ya kuma amincewa da shi za a yi FASHIN! . Wani tattausan murmushi ya subuce a gefen bakin Gambo sa'ar da ya ga Jabir ya mike tsaye. ''Da kyau namiji!'' Ya zuga Jabir. Sannan ya dubi sauran mutanen biyu suka mike kusan lokaci guda ba tare da sun dubi juna ba. Gambo ya fashe da dariya, sannan yace cikin 'karaji. ''Shegun duniya! Ashe kowa yana son kudi''. Abu daya da bai sani ba shine manufarsu ta sha bamban da ta Jabir, abin kuma da bai sani ba shine inda babu Tani a zuciyar Jabir to ba 'karamar kaduwa zai yi ba, domin bazai taba mika wuya ya tashi ba. . Sidi mai Jaka yayi shiru lokaci guda kuma ya dube ni yana 'kokarin ganin irin yadda na ke bin labarin. ''Nas ka ji yadda sannu a hankali na ke gangarowa zuwa inda muka tsaya ko?''. Na gyada kaina na ce. ''Kwarai kuwa....yi maza ka 'karasa min wannan ko ma koma kan wancan labarin na da, domin duk ya fi wannan dadi''. ''Haka ne''. Sidi mai Jaka ya ce. Sannan sai yaci gaba gami da share gumi akan goshinsa. Nayi mamakin abin da yasa shi gumi da goshin magariba. ''karfe uku dai-dai bayan sati guda da yin alkawarin, cikin talatainin dare mutanen uku suka gama hallara cikin dakin suna jiran zuwan gambo. Ko wannensu tsaye, sun cakaraicakarai kamar zakaru sai kaiwa da komowa suke yi kowannensu rike da karan sigari suna bulbula hayaki sama abinsu. Wanda ke hangen tagar dakin ta waje , ba abin da zai hanashi kawo gudunmawar bokitin ruwa a guje, domin zai dauka ko gobara ake a dakin, to amma duk hayakin sigari ne. Yau ce ranar da suka ajje domin shiri na 'karshe, dan a washe garin ranar ne suke shirin kaiwa gidan attajirin harin bazata wanda daga wannan hari ne suke sa ran cewa kowa a cikinsu ya yi hannun riga da talauci. Amma jiranda suke yi yanzu abin ya fara damunsu, domin tun jiya da suka rabu da Gambo yace dasu su zo su jirashi, shi kuma zai zo musu da dukkanin bindigogi da sauran abubuwan da suke bukata. Makon da ya gabata basu bata shi a banza ba, domin kullum sai sunyi shawagi a 'kofar gidan attajirin suna kula da irin kai kawon da motocin maziyarta suke yi, sun kuma lura da cewa kullum Mai gidan baya dawowa sai 'karfe goma sha biyu na dare, wannan ita tasa suka yanke shawarar kai harin 'karfe biyu na dare domin sun tabbata a lokacin ya shiga barci. Duk kusan wani shiri dai an gama shi tun jiya, to amma yanzu rashin zuwan Gambo ya fara damunsu. A dai-dai lokacin da suka fara fargabar ko ba lafiya ba, sai suka ji tafiya an nufi dakin sadadaf! Akwai wani abu a yanayi na tafiyar daya fara basu tsoro. Kwatsam sai suka ji an bugo kofar, Gambo ya fado dakin daga shi sai diras, jikinsa duk faca-faca da kwata, dauke da 'kullin tsummokara him! a kansa kamar wanda ke tafe da kayan alhaki. Yana zuwa sai ya jefar da kayan tim! a tsakar dakin, tun kafin kayan su taba 'kasa mutanen uku suka yi tsalle gefe guda cikin kaduwa suna duban ikon Allah, yau ga Gambonsu a tsaye daga shi sai diras! Sai warin kwata yake yi kamar mushe. Gambo ya dubesu, suma suka dubeshi, irin duban da yara kan yi wa macijin wasa na roba, Gambo bai yi magana ba sai ya fara matsawa cikin dakin, nan da nan mutanen uku suka fara 'kokarin samin gurin tserewa domin ko shakka babu Gambo haukacewa yayi. . Abin da ya fara zuwa zuciyar Jabir shi ne, yanzu haka yawan tunane-tunanen zuwa fashin ne yai wa 'kwakwalwarsa yawa ta tasamma zauta shi, domin daman ya fahimci a iya kwana bakwan nan da suka wuce Gambo ko rintsawa sosai ba ya yi, wani lokacin ko da rana idan ya kwanta ya dan runtsa sai kaga bakinsa yana motsi. ''Matsoratan banza..... Dan Allah ku bani wando insa, ku da nake tsammanin gobe ya war haka muna can mun ritsa wannan dan iskan amma kuke tsoron mahauci''. Su Jabir suka dubeshi cikin shakka. Jabir ne ya fara magana bakinsa na rawa. ''Meye ma'anar yawo cikin wannan uban daren daga kai sai diras, ga jikinka duk kwata in ba hauka ba?''. Gambo ya sake bushewa da dariya a karo na biyu ya dubesu ya ce. ''In banda haukanku ta yaya kuke tsammanin zan iya kawo bindigogi biyar tun daga kasuwar Gwari har zuwa nan?.... Ba kwa tunanin 'yan sanda dake ta sintiri ko ina cikin wannan dare ko....''. Mutanen suka bushe da dariya sa'ar da suka fahimci hikimarsa. ''Shege Gambo! Lallai ka isa mayaudari ga fa 'yan sanda basu damu da su kula mahaukaci a bakin hanya ba kuwa''. Jabir ya ce. Gambo ya zaro bindigogi biyar cikin 'kullin tsummokaran ya mikawa kowa sannan ya ce da su. ''Ina fatan kowa ya rike yadda abin zai kasance ko?'' Suka gyada kai baki daya. ''Na fada muku....'' Gambo ya ci gaba. ''Wadannan bindigogi duk za ku rike su kawai don barazana tawa ce kawai mai alburushi idan yayi mana taurin kai zan harbe shi da 'kwaya daya jal.... Kuma ya riga ma ya tsufa, dan haka ina ganin dan na dankarawa tsohon 'kokon kansa alburushi taimakonsa nayi.... . . ''Nas' Sidi mai Jaka yai kirana, sannan yace da ni. ''Zaka yi mamakin irin yadda mutanen zamani ke kafircewa, su zamo marasa hankali duk saboda rayuwar duniya...Ka dubi samarin nan dai ka gani wadanda ko 'kwakkwarar satar ma basu iyawa duk da yake dai dama batattu ne, to amma kaji yadda lokaci guda duk suka rikide suka canja kamanni duk wai sabo da kudi suka zama rikakkun marasa imani..''. ''Haka ne''. Na ce da shi cikin zakuwa domin naji kamar labarin ya daina gundurata. ''A can cikin gidan tsohon barawo attajiri''. Sidi mai Jaka ya ci gaba. . ''Attajirin na can kwance shi da kyakkyawar amaryarsa mai siffar larabawa, babu abin da ya dame shi a duniya, bai kuma ta6a ma kawowa ko da dai-dai da gamin gafara ba wai sata zata saci sata! ''Kai baka jin barci?''. Laila matarsa ta ce da shi idonta a lumshe tana murmushi. ''Yuashe mutum zai iya barci kina kusa da shi''. Attajirin ya ce da ita. Sannan sai ya kamata ya rungumeta a 'kirjinsa yana sunsunar daddadan turaren da ke gashin kanta. ''To meye rayuwar duniyar?''. Ya tambayi kansa. ''Ai ka sami kudi.....kawaika hole shi ne rayuwar.... Ni kam daga yau na daina harkar kasuwar dare.....''. Ya ci gaba da cewa kansa. ''Nasan dai dan abin da na tara ya isheni ni da 'yar matata....gara na hakura na sa matata a gaba''. Shi kansa yana mamakin irin masifar 'kaunarta da yake yi, domin a 'yan kwanaki kadan da suka gabata shi bai san menene so ba, to amma yau ya fahimci ashe ada ba 'karamin rashi ya yi ba. ''Darling!''. Laila ta 'kirashi a tsorace. Ya gama shagala cikin tunani dan haka bai ji kiran da tayi masa na farko ba, har sai da ta sakalo wuyansa da kyawawan hannunta ta girgiza shi sannan ne to ya dubeta cikin mamaki. ''Dar...lin.....g ni kamar motsi na ke ji a waje...''. Ya kashe idanu cikin murmushi ya ce, ''Shuke-shuken dake gidan nan ne ace mutum ya gaza jin motsi...? Ke fa wallahi ba kya rabo da shagwaba....''.Laila ta sake 'kankameshi cikin tsoro ta kuma cewa. ''Motsi-motsin takun sawu na ke ji cikin falo...''. Ya dada rungumota 'kirjinsa ya ce. ''Kwantar da hankalinki Lailar duniya....kina nan gabana babu abin da ya isa ya same ki....Me yiyuwa ma duk a banza ki ke damun dan kyakkyawan kanki da tunane-tunanen wofi.... Yanzu haka ma 'yar kyanwarki ce ke jin yunwa ko kuma............ Kalmar ta subuce daga bakinsa sa'ar da suka ga 'kofar dakin na budewa da kanta ahankali-ahankali. ''Na Shiga Uku!LINZAMIN SHAIDAN-08 . ''Na shiga uku!!'' Laila ta ce 'kasa-kasa Ta dada 'kankame shi kamar zata tsaga shi gida biyu saboda tsoro Sannu a hankali kofar dakin ta gama budewa sannan sai suka fara shigowa daya bayan daya wannan na bin wannan kamar 'ya'yan carbi Tsawon mintuna suna dubansa kwance kan gadon ya yi mutuwar tsohuwa yana dubansu kowanne fuskarsa a boye cikin bakin 'kyalle ''Da...wacce...kuma kuka zo.'' Ya tambayesu bakinsa na rawa Hakan ya bata masa rai domin bai kamata namiji kamarsa ace wai bakinsa yana rawa ba tun da abin ya ke yiwa wadansu ne shi ma aka yi masa. ''Kudi muke so. Ko ranka da na matarka Gambo ya ce da shi cikin tsawa. Nan da nan nadama ta darsu a zuciyarsu domin jiya jiyan nan matarsa Laila take cewa da shi ''Alhaji kudin nan a kaishi banki mana ai sun yi yawa a barsu a gida..'' Ita bata san dawan garin ba ke nan? A bu na farko daya fara zuwa zuciyarsa shi ne ko zai mutu ba zai basu kudin ba Wannan shine kuskurensa na farko. . ''Malam ba bata mana lokaci muke so ba, tashi ka kaimu inda 'karafen suke...''. Tsohon barawon ya dubi sababbin barayin kowanne da bindigarsa a hannunsa..... Ya fara nukunuku....Bai aune ba sai yaji an kwada masa tafi. ''Wayyo Allah!''. Laila ta fara ihu. Jabir jiki na rawa ya kara mata fankwan bindigar a goshi, domin a lokacin da ta sake ihu babu abin da zai iya yi dan bindigar babu komai ciki fanko ce. Sauran mutanen uku suka hau attajirin da duka tim! tim!! da mangari da bindiga, to amma abin da basu sani ba shi ne ya saba da duka, abinka da tsohon barawo. Jini ya fara fita ta bakinsa ta hancinsa. ''Ko dai sun kashe ni a banza, domin ba za su taba samun kudin ba, amma a 'kalla dai Laila ta samu'' abin ke nan dake cikin zuciyarsa, matarsa Laila, kamar yadda Tani take a zuciyar Jabir. ''Ku 'kyale shi haka!'' Muryar Jabir ta ratsa dakin. Gambo da sauran mutanen biyu suka bar dukan attajirin suka dubi Jabir cikin mamaki. Jabir ya dubi attajirin kwance rub da ciki a tsakar dakin jini na zuba ta baki ta hanci. Ya durkusa daf da kunnen attajirin yace. ''In ka so kana iya fada mana inda kudin suke mu kwasa muyi tafiyarmu mu barku lafiya....in kuma baka ma so ba, to zamu bar ka din dai lafiya muyi tafiyarmu, amma duba ka gani?''. Jabir ya mike tsaye cikin hanzari ya cakumo gashin kan matarsa Laila ya dora hancin bindiga a goshinta ya ce. ''Na baka minti daya, ka zabi daya, ko kudi ko na fasa ma ta 'kwa'kwalwa..... Ban san harbin kyawawan mata ba, amma yanzu zan fara... Zan 'kirga maka goma in baka tashi ba....''. Ya dada dannan hancin bindigar a goshin Laila sannan ya fara lissafi. ''Daya......biyu.....uku.....h udu.....biyar.....'' ''Kayi min rai dan Allah!''. Atttajirin ya mi'ke tsaye jiri na d'aukarsa..... ''Ku 'kyale ta ni ku kashe ni.....''. ''babu ruwanmu da kai.....ita zamu kashe in baka wuce gaba ba...'' ''Shida....bakwai....''. ''Ah! Dan Allah bari muje ku diba''. Gambo ya dubi Jabir cikin girmamawa. Suka bishi a baya mutanen uku rike da shi. Jabir kuma rike da Laila. Wani dan 'karamin daki suka shiga, suna zuwa suka yi ido biyu da 'katuwar loka ta katako jingine jikin bango. ''Gashi nan.... Ku diba ku bar min Laila....''. Attajirin ya ce da su cikin takaici, domin ko shakka babu sun gama tagaiyara shi....daman an ce wai garin banza a farau-farau din banza ya ke 'karewa.... A 'kalla dai baza su kashe masa LAILA ba! Mintuna biyu suka balle 'kofar. Nan da nan numfashinsu ya dauke baki daya, kudin dake ciki kamar budar ido. Ga Jabir ganin kudin tamkar mutumin da bai taba ganin falki bane, ba zato ba tsammani kuma sai ya tsinci kansa a bakin teku. A dai-dai wannan lokacin da duk wannan kuma ke faruwa ne Laila ta dubi Jabir bakinta na rawa ta ce da shi 'kasa-'kasa. ''Zaku bar ni ba za ku kashe ni ba.....? Tsoron mutuwa....nake ji?''. Jabir ya dubeta. Ga mamakinsa sai yaji tunanin abar 'kaunarsa Tani ya fado masa cikin zuciya. Nan da nan sai yaji zuciyarsa ta karaya ya girgiza kai ya ce. ''Kada ki damu....babu mai taba.....'' Mummunan sautin bindigar da ya ratsa dakin shi ya hana shi 'karasa mata maganar da yake fada ma ta. Jini ya fallatsa akan fuskarsa. Da farko ya dauka shi aka harba, amma cikin kaduwa sai yaga kyakkyawan gangar jikin Laila ya sulale ya fadi kan sawunsa. Jabir ya yi tsalle gefe sa'ar da attajirin ya 'kwalla 'kara mai tsananin 'karfin gaske. Jabir ya dubi Gambo a tsorace, hayakin da ke fita daga bakin bindigarsa ya ishi Jabir amsa. . . ''ME....Yasa....Ka...Kashe Ta....?'' . Sidi mai Jaka yai shiru yana dubana. A dai-dai lokacin ne to aka fara kiran sallar magariba. . ''Kash! Nas ga shi kuma lokacin sallah ya yi... Na katse shi cikin kaguwa bakina na rawa ME YASA TO YA KASHE TA ? ''Sai ka bari to sai mun dawo daga masallaci... Kai da dazun nan kake cewa labarin ya fara gundurarka....??. Na katse shi cikin 'kaguwa bakina na rawa. ''Me yasa to ya kashe ta?''. ''Sai ka bari to sai mun dawo daga masallaci.... Kai da dazun nan kake cewa labarin ya fara gundurarka.... To mene ne kuma yanzu na damuwa....? Ka je kawai, kada ka damu Nas'' . Tun kafin na 'karasa gidan Sidi mai Jaka na hango shi bisa buzu zaune a 'kofar gidan yana jan tasbaha kansa babu hula, haka nan duk da duhun daren da tuni ya gama shigowa hakan bai hanani hangen kansa ba fari fat cike da furfura kamar an yi masa barin garin alli. Lokacin dana 'karasa 'kofar gidan sai na ga ashe har da kwanon abinci a gabansa. ''Assalamu alaikum''. Na yi masa sallama Sidi mai Jaka ya shafi kansa da hannunsa mai carbin, sannan ya dubeni cikin murmushi. ''Har ka dawo?''. Ya tambayeni. Ban amsa masa ba, sai da na zauna kusa da shi a kan daben da ke 'kofar gidan, domin buzun bazai ishe mu ba. ''Dan ma na tsaya sallar isha ne shi yasa ka ganni a dan makare.... Ai da tuni na dade da zuwa''. Sidi mai Jaka ya gyada kai cikin gamsuwa. ''Wannan gaskiya ne''. Ya ce da ni, lokaci guda kuma ya ajje carbin gefe guda, ya janyo kwanon abincin gabansa a hankali kamar mai jan mushe. Kwanon abincin yaji jiki, Allah ne yasan yawan shekarunsa a duniya, domin duk kusan ko'ina a jikin kwanon a farfashe yake da lambobi ko'ina. Nayi mamakin abinda ke cikin kwanon..... Wata zuciyar tace da ni tuwo ne a cikin kwanon. Ya yin da kuma cikin gaggawa wata zuciyar ta 'karyata hakan tana cewa da ni, me yiwuwa shinkafa da miya ne tun da dai da tuwo ne zai yi wuya a hado shi guri guda da miyarsa. Ba 'karamin kaduwa nayi ba sa'ar da ya bude kwanon na yi ido biyu da dan wake zuka-zuka yana min signa. 'Dan wake ne...me yiwuwa kuma idan an 'kirashi tubani duk babu laifi, domin ban taba ganin curin dan wake da girman wannan ba. A had'iye dai bai had'iyuwa lokaci guda, haka nan ma a taune yafi 'karfin a jefa shi a baki a yi masa taunar gadara, dolene a gutsura duk dun'kule guda gida uku kafin a sami damar tauna shi cikin zaman lafiya. . Na dad'a zubawa cikin kwanon da Sidi mai Jaka ya bud'e idanu cikin tsananin shakka, domin har yanzu ban gama imanin cewa d'an wake nake kallo ba. To amma gashi nasha-nasha a cikin mai, kuma wani abin dad'in tashin hankali an bad'e abin da yaji ta ko ina da 'kyar ma ake iya ganin jikinsa sai yajin. Sidi mai Jaka ya yi dariya sa'ar da ya dubi fuskata yaga har na fara gumi sabo da abin da na gani. ''Wannan tubani ke nan uban d'an wake'' yace da ni lokaci guda kuma ya d'auki kwanon ya fara zunkud'awa ya gauraya tubanin da yajin. ''Yaran zamani baku san abinci ba..''. Sidi mai Jaka yaci gaba da cewa yana zunkud'a tubaninsa. ''Ai abinci in dai ya wuce abu uku zuwa hud'u....to ana shirga zaman 'karya ke nan....''. ''Wanne da wanne ke nan?''. Tambayar ta su6ucewa bakina tun kafin na yi shirin furtawa. Sidi mai Jaka ya ajje kwanon sannan ya d'aga 'yan yatsunsa guda hud'u ya fara da cewa. ''Kaga na farko shine Tubani..... Na biyu 'Dan wake.... Na uku Tuwon tsari, na cikon hud'unsu kuwa shine Burabusko.... In dai abinci ya wuce wad'annan NAS, to al'amarin kuma ya zama ko sai ace maganin yunwa''. ''Hakane''. Na ce da shi. Ni kaina sai da kunyar 'karyar da na shara ta kamani, domin a cikin kalar abin nan da ya lissafa babu wata 'kwa'k'kwarar cimata ciki, musamman ma Tubanin domin a yadda muka yi ido biyu da shi a yanzu ya fi kama da abin tsoro fiye da abinci. . Barbad'en yajin da ke saman tubanin shi yafi tayar da hankalina. ''Bismillah Nas''. Sidi mai Jaka ya ce lokaci guda kuma ya cakumo wani sullubeben Tubani kayan 'kato guda ya nufi bakinsa. ''Uhm...uhm! Na gode''. Na ce da shi cikin gaggawa, domin wata zuciya na cewa da ni idan na sake na had'iyi Tubanin babu abin da zai hanani aman hanjin cikina. ''A haba, ba za ka ci ba Nas?''. Na gyad'a kai gami da yi masa murmushi, domin bana son ya d'auki abin da wata manufa. ''Cab! amma fa yau zan ci da rabonka... Wallahi dan baka ji dad'in daTubanin nan ke da shi bane... 'Dauki guda d'aya ka gwada ka ji d'and'ano...''.Sidi mai Jaka yace lokaci guda kuma ya jefa dun'kulen Tubanin gaba d'aya a bakinsa ba tare da ya gutsura shi ba. Hakan da yayi shi ya fi sani kad'uwa fiye da komai, domin a d'an ta'kin tunani na ke dun'kulen Tubanin na iya sha'ke d'an tsohon ya kashe shi a banza. To amma nayi kuskure.... . Na zuba masa idanu kamar macijin da ke son had'iyar 'kwai, sai dai kuma sa6anin maciji Sidi mai Jaka bai feso da kwanson komai waje ba. ''Ka bar dad'i Nas!''. Sidi mai Jaka yace da ni yana zazzare idanu har da tande baki kamar tsohon maye..... LINZAMIN SHAIDAN-09 . Ka bar dadi Nas!'' Sidi mai Jaka yace da ni yana zazzare idanu har da tandar baki kamar tsohon maye Tuni har idanunsa sun fara zubar da hawaye ''Wannan wacce irin masifa ce?'' Na tambayi kaina Tsawon lokaci mai tsawo kamar shekara a gurina kafin Sidi mai Jaka ya gama tande-tande da lashe-lashensa A lokacin da ya gama tuni ya hada gumi shakaf kamar ya hadiyi kunama ''Yauwa ko ni fa?'' Sidi mai Jaka yace gami da yin ajiyar zuciya Bai dami da wanke hannunsa ba dan haka yana gama tande yan yatsunsa sai ya goge sauran a jikinsa ''Baka sha ruwa ba'' Nace da shi cikin kaduwa domin na ga duk uban yajin da ya gama sha bashi da niyar tashi domin ya nemo ruwan sha ''Kada ka damu Nas wani lokaci haka na ke yaji bai fiye damu na ba kuma ko a banza ma ai shan yajin maganin Mura ne a gareni'' ''Haka ne..'' Nace da shi bakina na rawa Sannan sai na dada cewa ''Me yasa to ya kashe ta?'' Sidi mai Jaka ya zura min idanu yana tandar baki kamar wanda bai fahimci abin da nake nufi ba A dai-dai lokacin da nake kokarin maimaita tambayata sai ya yi murmushi yace ''Oho..! Nas ke nan naci gaba da labarin ka ko? Yanzu kuwa ai tun da na ci Tubani to babu abin da zai hanani 'karasa maka zarurrukan labarin da muka bari can baya. ''Haka ne''. Nace da shi. Sidi mai Jaka ya gyara zama, bayansa a jingine da bangon 'kofar gidan sannan ya fara da cewa.... . 'Nas mutanen duniya sai dai a barsu akan son duniya...''. ''Don me kace haka?''. ''Yauwa saboda lokacin da Jabir ya tambayi Gambo dalilin da ya sa ya kashe ta, sai Gambo ya dubeshi shekeke yana cewa....'' Na katse shi da cewa. ''Ka sauya salon labarin. Baba Sidi...''. 'Dan tsohon ya dubeni cikin mamaki ya ce, ''Ban fahimce ka ba Nas?''. ''Abin da na ke nufi shi ne, salon labarin na ka a yanzu ya koma kamar salon labarin da, irin na magabatanmu''. Sidi mai Jaka yai murmushi, sannan ya ce, ''Na fahimce ka Nas, to saurara da kyau na 'karasa maka wannan zaren''. *** *** *** . . ''Amsa kuwwar sautin attajirin ta cika dakin sa'ar da matarsa Laila ta fadi akan 'kafar Jabir. Jabir ya dubi Gambo a karo na biyu, sannan ya sake maimaita tambayarsa. ''Me yasa ka kashe ta?''. Gambo ya dubi hancin bindigarsa na tururi lokaci guda kuma ya dubi matar da ke kasan dakin matacciya ya ce. ''Tauna tsakuwa nayi, wai don Aya taji tsoro''. ''Tauna tsakuwa?''. Jabir ya tambaya a sakarce. ''Kwarai kuwa....kuma har da kariyar kanmu da kanmu''. Gambo ya ce yana duban Jabir. A lokacin ne ya lura ashe sauran mutane biyun da ke ta kwasar kudin sun dakata, shi kawai suke kallo cikin kaduwa, domin basu taba tsammanin al'amarin zai juye da kisan kai ba. ''Ku kwasa mana!!'' Gambo ya buga musu tsawa a fusace. ''Kun tsaya sororo sai kallona kuke kamar wanda ya aikata wani mummunan aikin da babu wani daga cikin ku da zai iya aikatawa.... Wannan abu nayi ne dan kare kanmu, domin mace ba abar yarda ba ce''. Gambo ya ce gami da nuna gawar Laila da ke kwance, shi kuma Attajirin kwance akan gawar sume. ''Shi dai yana iya yin shiru da bakinsa, domin in ya sake ya kirawo jami'an tsaro bashi da mafita dole ne ya yi musu bayanin inda ya samo kudin. To amma matarsa ta san komai, duk ta ga wasu daga cikin kamanninmu..... Barinta a raye hadari ne!''. Ya dan yi shiru yana mai da numfashi, sannan shima sai ya sunkuya ya fara diban kudin yana zubawa a cikin wata budaddiyar jaka baka da ke gabansu. Jabir ya rasa ta cewa, dan haka shima ya durkusa aka fara kwasar kudin da shi. Amma fa duk da haka tuni al'amarin ya gama ficewa daga cikin zuciyarsa. Wani mummunan tunani ya darsu a doron zuciyarsa sa'ar daya dubi gawar Laila, yanzu idan wani ya harbe Tani abar kaunarsa yaya zai yi? Tunanin hakan kawai shi ya sa wani zazzafan gumi fara tsatstsafowa kan goshinsa, to amma duk wannan kafin su ji mummunan harbin bindigar a waje ne. Mutanen hudu suka mike tsaye lokaci guda suka yi cirko-cirko da su kamar zakaru. Cikin 'kokarin 'kin yin imani da abin da suka ji, sai dai kuma babu ko shakka sautin bindiga ne domin kafin ma wani daga cikinsu ya sami ta cewa wasu 'karin sautin harbe-harben suka sake gauraye shirun da ke daren. Daga can waje suna iya jiyo sautin sawu ana ta guje-guje. ''Yan sanda!''. Gambo ya ce da sauri cikin kaduwa yana jujjuya bindigar da ke hannunsa. ''Kai ka janyo mana. Laifin ka ne Gambo! Jabir ne yace hakan ba tare da wata fargaba ko rawar baki ba. ''Laifi na?''. Ya tambaya a fusace ''kwarai kuwa inda baka yi harbi ba wa ya san muna nan?'' Gambo ya kurawa Jabir idanu a kufule domin ji yake yi kamar ya sa gindin bindiga ya buge shi ''Ka iya bakinka Jabir...wata rana bakin ka zai kaika ga halaka!....'' ''In bakina bai kai ni ga halaka ba ai ga shi kai ka kaimu kan hanyarta'' Jabir ya ce yana sauraron takun sawun duf! duf! a zagayen gidan ''Cacar baki ba zai kaimu ba gara mu sami mafita mu tsere tun kafin su cimmana muna surutan banza'' Wani dogo daga cikinsu ya ce lokaci guda kuma idanunsa na kallon akwatin da ke kasa a cike da kudi Jabir ya gyada kai cikin gamsuwa yana duban Gambo ''Sai ka fitar da mu'' Jabir ya ce yana share gumi daga goshinsa ''Ta....ya....ya zan fitar....da ku? Kowa tasa ta fishsheshi'' ''Kada ka ce haka Gambo....'' Karar mummunan sautin da suka ji a waje shi ya katse Jabir ''Yan sandan sun shigo...'' Gambo ya ce cikin kaduwa. Nan da nan ya nufi kofar dakin a firgice Sauran mutum biyun suka bishi a baya amma Jabir na nan tsaye daf da inda tagar dakin take ''Taho mu fice shashasha' Gambo ya daka masa tsawa Jabir yayi banza da shi lokaci guda kuma ya durkusa cikin gaggawa ya rufe akwatin kudin da ke 'kasa ya dauketa, sannan ya dubi fuskar matsoratan ya ce. ''Abin da ya kawo ni ke nan, dan haka tsoro ko fargaba basu isa su hana ni fita da kudin nan ba, domin in ba dan su ba da babu abin da zai kawo ni nan''. ''Baka da hankali..... Ta yi nauyi da yawa baza ka iya gudu da ita ba''. ''Ku fita mu hadu a inda muka bar motarmu.... Zan kawo muku kudin'' . Mutananen uku sukayi tsaye na dan lokaci suna kallon Jabir, shi kuma yana tsaye yana kallonsu da akwatin a rike a hannunsa. Abinda suka gani a fuskarsa shi ya hana su sake yi masa jayayya, domin akwai wani yanayi da ke fuskarsa da ke nuni da cewa ko ta wane hali, ko wuya ko dadi babu abin da zai

Chapter 3 of 6