Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
4 / 6
hana shi fita da akwatin. ''Ka kula da kyau!''. Itace kalma ta 'karshe da Gambo ya fada masa. Daga nan sai ya juya a guje, sauran suka bishi a baya kamar tunkiya da 'ya'yanta, cikinsu ya gama durar ruwa. . Tsawon mintuna biyu Jabir na tsaye cikin duhun dakin yana sauraren guje-guje da harbeharben iska na jami'an tsaron da suka shigo gidan. Daga inda Jabir ke tsaye yana iya hangen farfajiyar da ke bayan gidan ta cikin gilashin tagar dakin. Ya kuwa yi imanin babu wanda ya isa ya hango shi, wannan shi yasa ya kashe kwan lantarkin da ke dakin. Tun a karon farko da Jabir yaji 'karar harbin bindigar ya gama tunanin hanyar da zai bi ya tsere. Jabir ya riga ya gama fahimtar gidan, ya san cewa yana fita ta cikin tagar dakin tafiya kadan zai yi a farfajiyar gidan ya riski inda rumfar injin bada wutar lantarkin gidan take, ya san cewa rumfar injin bada wutar a jingine take da katangar gidan, wanda hakan ya dada kara masa 'kwarin gwiwa domin yasan rumfar zata taimaka masa matuka wajen haura katangar. To amma abin da yafi damunsa a yanzu shi ne dan tattakin da zai yi a farfajiyar gidan kafin ya kai ga katangar. Jabir yasan abu ne mai sauki 'yan sanda su hange shi, domin duk ilahirin farfajiyar gidan a haske take da 'kwayayen lantarki kamar rana. To amma dole ne yayi kasadar wucewa domin itace kawai mafita. Sai dai kuma kafin ya haura katangar dakin zuwa waje yana bukatar lekawa ya tabbatar babu wani jami'in tsaron da ke labe yana jiransa. Jabir yaci gaba da leken waje ta tagar dakin, lokaci guda kuma yana tunanin hanyar da su Gambo za su bi su tsere''. ''Su suka jiyo!''. Jabir yace a ransa. Sannan ga mamakinsa sai ya nemi kansa yana mai addu'ar Allah sa ma a kamasu shi kuwa ya tsere. ''Ta6! Da yau ya baiwa masoyiyarsa Tani mamaki. Har yanzu tana 'kaunata''. Yaci gaba da tunani. ''Gaskiya duk abin da zan yiwa Tani ban biyata ba''. Jabir yaji gabansa ya fadi sa'ar da ya tuna alfashar da ta shiga tsakaninsa da masoyiyarsa Tani a yammacin ranar. ''Tsautsayi ne!. Yace da kansa. ''Hakika tsautsayi ne...da kuma shaidan.... To amma dai daga wannan ba za su 'kara ba har sai idan sunyi aure. Yau dai zata faru ta kare. Kudi dai ga su an sami na auren Tani....saura fita da kudin. Hakika fita da kudin nan shi ne rayuwata....''. . Wadannan guntattakin tunani masu kama da kururuwar shaidan su suka yi tasiri a zuciyar Jabir, suka kuma karfafa masa gwiwa. Jabir ya jingina jakar da ke hannunsa, a nan sai wani murmushin bazata ya subuce masa, sannan sai ya ce da kansa. ''...LALLAI RANAR AURENA DA TANI ZA'A YI TA'BARA!!''. . Jabir ya sake lekawa. Hakika a yanzu ya tabbata babu kowa a bayan gidan. ''Me yiwuwa jami'an tsaron can farfajiyar kofar gidan suka tsare, wasu kuma su shigo su binciki abin da ke faruwa. Domin karfin gwiwar da Jabir ke samu a ransa shi neLINZAMIN SHAIDAN-10 . Domin 'karfin gwiwar da Jabir ke samu a ransa shi ne, ya tabbata jami'an tsaron lalube kawai suke a cikin duhu tun da dai harbin bindiga kawai suka ji a gidan ba su da yakinin abin da ke faruwa. Jabir ya bude katuwar tagar gilashin ta alfarma wacce tuni daman ya san yadda ake budeta ba tare da ta bada wani 'kwakkwaran sauti ba, wannan kuwa tun sa'ar da attajirin ya gaiyace su liyafar bude gidan ne Jabir ya koyi hakan. Sai da ya shafe minti guda tsaye yana sauraro kamar ungulu, sannan zuciyarsa na bugawa sai ya yi shahada ya zura 'kafarsa ta hagu, sannan ta dama. Akwatin rike kam-kam a hannunsa ya haura katangar ya dirga a farfajiyar da ke bayan gidan ba tare da yayi wani 'kwakkwaran motsi ba. Jabir na dirga sai ya nufi saitin inda injin bada wutar yake. Ba gudu yake yi ba, haka nan shi kuma ba a hankali yake tafiya ba, zuciyarsa na bugawa ya nufi gindin injin domin a kowanne lokaci tsammani yake zai ji harbi ko kuma kuwwa a bayansa. To amma sa'ar da ya kai ga gindin injin bai ji komai ba a bayansa, Jabir yaji wata sassanyar iska mai dauke da 'kamshin turbaya ta daki fuskarsa, ya daga kansa sama sai yaga ashe hadari ne bakikkirin a sararin samaniya. . Tunanin Tani ya sake mamayar zuciyarsa. Yanzu haka tana can tana barci, domin ya san abin da suka aikata a yammacin ranar bai barin zuciyarta da wuri. Jabir yaji numfashinsa ya dauke saboda abin da ya gani. A jingine a jikin rumfar injin wani dogon tsani ne. Jikinsa na bari ya ajje akwatin a jikin katangar, sannan ya dauko tsanin ya jingina a jikin bangon. Cikin sauri ya dauki akwatin sannan ya juya ya yiwa farfajiyar kallo daya. Sannan ya hau tsanin cikin sauri ya nufi saman katangar. Jabir yayi tsaye na 'yan dakiku yana nazarin bayan gidan. Kamar yadda yayi tsammani babu kowa a bayan gidan domin gidan da ke fuskantar bayan wannan gida wani 'katon kango ne an zagaye shi da katanga, sai kuma wata 'katuwar kwata mai fadin gaske wacce duk kusan ko ina a rufe yake da tubalin siminti. Jabir yayi ajiyar zuciya, sannan har zai dirga sai ya ga kuma ai bai dace ba ya bar tsanin jingine a jikin bango, domin duk dan sandan da ya kawo ga gindin katangar na iya fahimtar abin da ke faruwa cikin sauri, wanda hakan na iya sa dandazon 'yan sanda su tuso shi a gaba. Jabir bai shiryawa hakan ba dan haka sai ya zura 'kafarsa ta dama da niyyar wai ya ture tsanin ya fadi kasa. Ashe tsautsayi ne ke jiransa. Abu biyu suka faru ga Jabir kusan lokaci guda. Na farko yaji kamar kwarankwatsa ta fado masa a kan cinya, yayin da alburushin bindiga sama da guda biyar suka farfasa cinyarsa, sannan kuma sai sautin harbin bindigar da ya gauraye daren. ''Ah.... Tani....!''. Jabir ya 'kwalla 'kara gami da kiran sunan masoyiyarsa Tani, sa'ar da yaji wani irin ciwo da bai taba jin irinsa ba ya soki cinyarsa. Nan da nan ya rikito daga katangar ya fado bayan gidan. Jabir bai fado kasa ba sai da ya wuce kai tsaye cikin katuwar kwatar ta cikin wani gurbin tubali da ma'aikatan share muhalli suka cire a yammacin ranar domin share kwatar. Jabir ya fada akan tarin takardu da ciyayi na shekara da shekaru dake cikin kwatar babu shara. Haka nan sun hana ruwa bi ta ciki, wannan shi ya rage 'karfin faduwar da Jabir yayi. Ya daga kansa cikin firgici ya duba saman katangar, ya san da wuya, 'yan sanda suyi tsammanin sun same shi. Har yanzu akwatin na nan makale a hannunsa daraf kamar mayen 'karfe!. Jabir ya shafi cinyarsa yaji tuni har ta jike da jini. ''Na shiga uku... Tani sabo da....ke na ke wannan....'' Jabir ya ce muryarsa a shake. A dai-dai lokacin ne to Jabir ya fahimci ashe in ka dauke dai-dai inda ya fado duk kwatar a rufe take da tubalin siminti. Nan da nan yayi ta 'yan maza ya fara jan ciki, ya nufi cikin kwatar. Jabir ya san in dai har sa'a tana tare da shi in da rabon ya sake ganin masoyiyarsa Tani babu abin da zai hana shi bullewa a dai-dai inda suka baro direbansu yana jiransu. Loakcin da Jabir yayi tafiya mai nisa a cikin kwatar, sai yaji numfashinsa ya fara daukewa kamar zai suma. Abin da ya fi damunsa shine jinin da ke zuba a jikinsa, ga kuma nauyin akwatin Sa'ilin ne dabarar boye akwatin a magudanar ruwan ta fado masa.... . A can cikin duhun dare a jikin wata 'katuwar katangar waya da ta zagaye wani lalataccen lambu, su Gambo ne zazzaune a cikin jibgegiyar motar 'kirar Landiroba. Zai yi wuya wani mai wucewa a 'kasa ko a cikin mota ya iya ganewa cewa akwai mutane a cikin motar. Duk kusan gine-ginen da ke gurin kangwaye ne ba'a 'karasa gininsu ba. Hakan shi ya basu damar boye motar a bayan wani tsohon kango, wanda daga inda suke suna iya hangen bakin titi. Wannan dabarar Gambo ne ya kawo ta ya ce da su su bar mutum daya a cikin motar domin koda za ta baci dasun zo sai tafiya. To sai dai a halin da ake ciki a yanzu basa bukatar waccan tsohuwar shawarar ta gudu, domin akwai abin da suke jira. Gambo ya muskuta a bayan motar, ya dubi sauran mutanen uku, biyu a kusa da shi, sai kuma direbansu a gaban mota. Gambo ya lura da cewa duk sun yi mutuwar tsohuwa, numfashi ma da 'kyar suke shaka, sun yi zugum kamar gumaka. Hannun direbansu akan dan mukullin motar. Gambo ya dada musgutawa ya ce da sauran a tsorace. ''Ina jin harbin da suka yi sun sami Jabir''. Mutanen uku suka dubeshi kamar kurame. Basu ce da shi komai ba sai hadiyar yawu suke yi suna huci kamar macizai. ''Mu bashi 'karin mintuna biyar idan bamu ganshi ba sai mu wuce''. Hakan da ya ce ya sa daya daga cikin mutanen magana a karo na farko. ''Amma kuwa da mun yi aikin banza..... Ya babu kudi, ga asarar ran dan uwanmu Jabir, ga kuma laifi....?''. ''Ka cika shirmen banza....! Gambo ya ce da shi a fusace. ''In banda shirmen ka wa ya san cewa mu muka yi fashin?''. A ka sake yin shiru a cikin motar, kowa na sakar zuci. Wani na tunanin me yiyuwa fa rayuwarsu ta zo 'karshe ke nan, domin da zarar an kama su to kwanansu ya 'kare ke nan. Wani kuwa tunani yake yi da bakin cikin asarar da suka yi, domin yana kyautata tsammanin Jabir ya shiga hannu idan kuwa haka ta tabbata sun yi sallama da samun kudi ke nan. Ya zargi kansa da wautar da ya yi, domin a dai-dai lokacin da suke 'kokarin tserewa daga gidan ya so ya cika aljihunsa kafin su fita, amma tsoro ya hana shi. Mintuna hudu suka wuce kamar wasa. Mutanen hudu zaune cikin duhun motar suna ta ta sukusuku kamar kaji a akurki. Wani 'kwa'k'kwaran motsi a daf da su ya sa su zabura lokaci guda kowa hannunsa ya kai kan bindigarsa. ''Kamar motsi nake ji''. Wani daga cikinsu mai suna LANTO ya ce a tsorace yana jujjuya bindigarsa da ke hannunsa kamar yar tsana. ''Ba kai kadai kaji ba...!''. Gambo ya ce da shi a fusace, amma cikin rada. . Gambo ya lura da fuskar Lanto ya ga a bala'in tsure ya ke. Ya yi mamaki in har Lanto zai iya harbi da bindigar da ke hannunsa idan bukatar hakan ta tashi. Direban ya kai hannu zai tashi motar jikinsa na rawa. Gambo ya yunkuro daga bayan motar cikin zafin nama ya buge hannunsa. ''Ka da kayi gaggawar tashin motar ka tona mana asiri. Wa ya sani ma ko Jabir din ne?''. . ''Motsin daga cikin 'katuwar kwatar can ne....''. Lanto ya ce bakinsa na rawa. Tsawon da'ki'ku babu wanda ke iya koda numfashi a cikin motar ballantana wani 'kwa'k'kwaran motsi. Idanunsu na 'kokarin hango abin da ke motsi a cikin 'katon kwatamin ta cikin duhun daren ne. Sannu a hankali sai suka hango kan mutum ya dago, sannan sai gangar jiki da 'kyarda-'kyar mutumin da ke cikin kwatamin ya janyo ciki ya fito bakin ramin yayi 'ko'karin ci gaba da jan ciki, amma hakan ya gagara. Nan da nan ya kife rub da ciki baya ko motsi kamar ya mutu. . ''Jabir ne!''. Gambo ya ce da su cikin doki. Nan da nan ya bude bayan motar a hankali bindigarsa a hannunsa, sannan ya nufi inda Jabir yake kwance. lanto ya biyo shi a baya. Suna zuwa basu bata lokaci ba sai suka ciccibeshi suka tafi da shi cikin motar. . ''Wayyo 'kafata!'' Jabir ya ce muryarsa cikin rada, domin in ba dan Gambo ya tallabi kansa ba da ba zai taba jin abin da yake fadi ba. Tun kafin su isa ga motar suka kwantar da Jabir a bayan motar. ''Anyi ba a yi ba!''. Gambo ya ce yana duban Lanto. ''Me kenan?''. Lanto ya tambaya. ''Babu jakar kudin....''. Gambo ya ce lokaci guda kuma ya yi shiru yana duban 'katon kwatamin da suka dauko Jabir. ''Zo muje mu gani''. Lanto ya bishi a baya babu kalma, domin ya fahimci abin da Gambo ya ke nufi. Sun dade suna birkita takardun da ke kwatamin amma ba su ga komai ba sai guma guman duwatsu. Cikin sauri suka koma gindin motar. Jabir na kwance a bayan motar yana faman kakari. Mutanen uku suka yi tsaye a kansa suna jiran su ji abin da shugabansu Gambo zai zartar. ''ina mafita ke nan?''. Gambo ya tambayesu. ''Mu 'karasa shi kawai mu bar gurin nan! Domin duk da'ki'ka daya cikin hadari muke.LINZAMIN SHAIDAN-11 . ''Ina mafita ke nan?'' Gambo ya tambayesu ''Mu 'karasa shi kawai mu bar gurin nan Domin duk dakika daya cikin hadari muke kara shiga'' Lanto ne ke bada shawarar Gambo ya yi kamar bai ji abin da Lanto ke fadi ba Maimakon ya dubeshi sai ya rankwafa ya kara bakinsa kusa da kan Jabir ya ce ''A ina ka baro kudin ?'' Shiru Jabir bai motsa ba Gambo ya sake maimaita tambayar har sau uku shiru! A fusace sai ya kama kwalar rigar Jabir ya girgiza shi da karfi ''Ah! kafata!!'' Jabir ya 'kwalla kara... Amma kuwwar ihun ta ratsa shirun da ke dare ne... Lokaci guda kuma aka saki wata 'kwakkwarar aradu, sararin samaniya ya haske da walkiya, ''A ina kudin suke?'' Gambo ya tambaya a fusace yana kara girgiza Jabir''. ''Na....bo....ye....su''. Da 'kyar da kara kunnensa a bakin Jabir Gambo ya fahimci abin da yake cewa. ''A ina ka boye su...'' Ya tambaye shi gami da dada girgiza shi Amma ina! Jabir bai sake motsi ba, ya suma. Gambo ya ja da baya sauran suka ja da baya sannan Gambo ya rufe bayan motar ya ce. ''Ku mu bar gurin... Ina tsammanin 'yan sandan can sun jiyo ihun'' Da gudu-gudu suka shige cikin motar. Tun kafin su gama zaunawa sosai har direban ya fisgi motar a guje. Koda suka fara tafiya sai Lanto ya dubi Gambo ya ce ''Yanzu mene ne mafita?''. Gambo ya dubi fuskar Lanto tayi sharkaf da gumi ya ce. ''Asibiti zamu nema...a duba mana shi...a dawo da shi hankalinsa, in ba haka ba munyi sallama da kudin ke nan.... Dole ne ko ta ya ya, ko ta halin kaka sai ya fada mana inda ya boye kudin...''. Gambo ya yi shiru yana sauraren sautin 'kananan 'kwayoyin ruwan da ya fara wanke saman motar. Nan da nan sai wani murmushi ya subuce masa. ''Wannan ruwan saman alamun nasara ne.. Fatan mu daya shi ne Allah ya sa kada dan iskan nan ya mace ba tare da ya fada mana inda ya boye kudin nan ba...''. ''Rabon Gambo da addu'a NAS, tun yana 'karami dan shekara uku''. Sidi mai Jaka ya ce da ni. Sidi mai Jaka ya yi shiru a karo na farko tun sa'ar da ya fara zuraro min labari kamar saukar ruwan sama. Kusan mintunansa ashirin yana zuba baya ko 'kwakkwaran numfashi. ''Nas, wannan shine 'karshen wannan zaren labari mai tsayin tsiya. Gashi ba wani ma dadi ne da shi ba, domin kusan kowa ne ke son zaren labari mai tsayi da kuma yawan harbe-harbe da doke-doke ba''. Sidi mai Jaka ya yi gyatsa 'kyat! Kamar an shake kwad'o. ''Ka gafarce ni Nas''. Sidi mai Jaka ya ce yana gwaggwale idanu kamar kuturu. ''Wani lokaci haka nake fama da irin wannan doguwar gyatsa idan na ci TUBANI!''. Allah ya sauwake''. Na ce da shi cikin kaguwa da ya ci gaba da labarin. ''Na so a ce ka ci Tubanin nan Nas, dan ba ka san irin dadinsa ba ne shi ya sa ka barni na cinye...''. ''Wata rana ai zan ci..''. Na ce da shi, ina tunanin yadda za'a yi na iya hadiyar Tubanin nan. To ya ya aka yi kuma bayan sun tafi da Jabir d'in?'' Sidi mai Jaka ya dubeni cikin mamaki sa'ar da yaji tambayar. ''A'ah, kada kace da ni ba ka fahimci labarin ba... Ai 'karshen zaren labarin ke nan.... Inban da abinka a wancan tsohon zaren labarin da muka bari sai da na baka labarin zuwansu asibiti da kuma duk abin da ya faru har zuwa sa'ar da Tani ta gane masoyinta...'' ''Haka ne na ce da shi ina murmushin fahimta. Yauwa Nas, ko kai fa? To irin wannan zarurrukan labari su ake kullawa guri guda su baka labari... In ka fahimci zaren labari to shi ke nan in kuwa ka sake daya daga cikin zarurrukan ya subuce maka to rikicewa zakayi''. ''Wannan gaskiya ne''. Na ce da shi. To ya ya akayi da Tani ta gane cewa masoyinta ne Jabir?''. Sidi mai Jaka ya yi tari sa'annan ya daga kai sama yana duban dan saurayin farin watan da ya fara haske sararin samaniyar Subhana. ''Wannan ka yi babbar tambaya Nas.... Domin wannan zarurrukan labarin guda biyu da zan 'kulla maka a yanzu sune bangare na takaici da kuma karyar da zuciya a duk cikin labarin da na baka a baya''. ''Ai kuwa takaici ya gama faruwa tun da dai a inda muka tsaya a wancan zaren labarin da wuya idan masoyin Tani Jabir zai kai labari''. Sidi mai Jaka ya fashe da wata busashiyar dariya. ''Kai kuwa ka cika azarbabi Nas, in banda abinka wane irin takaici ma ta gani a yanzu ai labarin da saura ka dai bari in jona maka wannan zarurrukan guda biyu daga nan sai mu ajiye su guri guda mu dauki sabon zare'' ''Zarurruka nawa suka rage mana a yanzu?'' Na tambayi Sidi mai Jaka ''Baza su wuce uku ko hudu ba... Ina tsammanin kafin nan da 'karfe tara na dare zan sake maka su na hade su duk su zama daya'' Sidi mai Jaka na gama fadin haka sai ya gyara zama ya ci gaba ''Nas ina son ka dauki zuciyarka can-cak! Ka maida ita can 'karshen wancan tsohon zaren labarin da muka saka kafin wannan.. In zaka tuna mun tsaya ne a inda Tani ta gane Jabir da zoben da ke hannunsa..?'' ''Haka ne''. Na ce da shi cikin gaggawa. ''Da kyau Nas" ''Sa'ar da Tani ta gane cewar lallai marar lafiyar da ke kwance yana ihu a gabanta ba wani bane sai Jabir, sai duk 'kwakwalwarta ta rikice. ''Na shiga uku na lalace! Jabir!!!....'' Mutanen hudu suka dubi juna. Gambo ya dubi Lanto, sannan Lanto kuma ya dubi Gambo cikin kaduwa. Gambo ya matsa kusa da Tani a gaban gadon asibitin da Jabir ke kwance ya cakumi gashin kanta da karfi ya girgizata ya ce. ''Dan ubanki wa ya ce da ke sunansa Jabir?''. Tani ta fara shesshekar kuka a firgice. Sauran Malaman asibitin na can gefe duk a kidime. Peter sai zazzaro idanu yake yi kamar ta matar kwado. Ya yin da Asabe kuma ke jin kamar zata yi aman kayan cikinta saboda tsabar tsurewa. ''A...ina kika san shi.... Eye!!?''. Gambo ya sake maimaita tambayar cikin ihu, domin sautin zubar ruwa sama bai barin aji abin da wani ke cewa sosai a dakin sai an daga murya domin ruwan ya dada tsugewa da 'karfin gaske ''Tani ta hadiyi yawu da 'kyar sabo da mummunan rikon da Gambo ya yiwa gashin kanta. ''Ma...soyi..nane... Dan Allah kar ku kashe min shi...''. Gambo ya saketa jikinsa na rawa. Bayanin ya yi matukar sa shi kaduwa, domin bai taba tsammanin haka ba. ''Ta san Jabir?''. Ya ce a ransa. ''Gawa biyu ke nan''. Ya sake maimaitawa a ransa. ''Dole ne ita ma ta bakunci lahira''. Gambo ya juyo ya dubi abokan barnarsa su uku. Duk sun yi cirko-cirko kamar zakaru kowa da bindigarsa a hannu. Jira suke su ji 'kwakkwaran sauti ko da na bugun agogo ne su fara harbi. . ''Likita...! ban san haka abin ya ke ba....''. Gambo ya ce da Tani a tausashe kamar gaske. Tani ta dago kai idanuwanta na zubar da hawaye ta dubeshi domin ta ji alamun rahama a kalamansa. ''Ku taimaken kada ku kashe min shi dan Allah... wallahi idan ku ka kashe Jabir nima mutuwa zan yi....!''. Ta fara kuka, lokaci guda kuma ta durkusa a gaban Gambo tana rokonsa. Gambo ya kama hannunta a nutse ya dago ta sama ya ce. ''Bari kuka 'kanwata....zancen mu kashe Jabir bai taso ba.... Jabir abokin mu ne ke kuma masoyinki ne, mu muna son ya rayu sabo da wasu dalilai namu... Ke kuma kina son ya rayu saboda masoyinki ne, tun da haka ne mai zai hana ki cece mu baki dayanmu ki hanzarta ceton rayuwarsa cikin gaggawa? Kin ga raunin da ke 'kafarsa ya sa ya yi asarar jini mai yawa''. . Sidi mai Jaka ya yi shiru yana dubana. ''Nas, Allah ya horewa Gambo iya kera 'karya da gamsar da mutum duk abin da yake so....''. ''Haka ne''. Na ce da shi. ''Dan haka sa'ar da Tani taji kalamansa sai nan da nan tayi ajiyar zuciya domin ta dauka duk abin da ya fada da gaske ne har zuciyarsa. ''Tambaya daya kawai muke so ya amsa mana, in dai kika magance shi ya amsa mana tambayarmu to zamu tafi mu bar miki masoyinki...''. ''Na gode''. Tani ta ce cikin kukan dadi, domin bata taba tsammanin wadannan mutane masu bakaken kaya da bakar aniya zasu 'kyale ma ta Jabir ba. Kai hatta ita kanta bata taba zaton za ta tsira ba. ''Ku kama min nan mu shiga da shi dakin aiki''. Tani ta ce da su Peter da Asabe wadanda ke tsaye gefe guda ba sa ko motsi kamar an zare musu laka. Malaman asibitin biyu suka tura gadon da Jabir ke kwance Tani na binsu a baya zuciyarta na ta sake-saken abin da ya hada masoyinta da wadannan miyagun mutanen. Gambo ya 'kiftawa Lanto idanu ya biyo shi a baya suka bi su Tani dakin aikin. Ya yin da sauran mutanen biyu kuma suka yi tsaye anan suna gadi da bindigarsu a hannu. Gambo ya dubi dan tsukakken dakin da suke ciki.... Babu komai a ciki sai wasu gadaje guda biyu da wasu 'yan mashina gami da kanta-kanta ta magunguna iri-iri daban-daban da kuma sinadarai. Tani ta janyo wata farar Jaka ta budeta sannan ta fara zuba tarkacen aikin da take bukata akan wani dan felelen faranti launin azurfa da ke hannun Peter. Tsawon mintuna hudu Tani ta yanke 'kafar wandon Jabir, sannan ta rike numfashi cikin kaduwa da abin da ta gani a cinyar Jabir. Gambo ya matso kusa ya dubi cinyar Jabir, wanda ke kwance ko motsi baya iya yi sosai. Abin da Gambo ya gani ya sa shi kaduwa, domin duk kusan cinyar Jabir raunika ne kusan guda tara guri daban-daban na alburusai. ''Wannan ba karamin aiki bane...''. Tani ta ce cikin karaya da abin da ta gani a jikin abin begenta. Wannan shine kuskure na biyu, domin tun sa'ar da ta nunawa Gambo cewa ta san Jabir ta aikata kuskure na farko. ''Me kike nufi da cewa ba 'karamin aiki bane?''. Gambo ya tambaya yana duban Tani akwai alamun zargi a muryarsa ''Aikin zai dauki kusan sa'o'i biyar kafin a gama..''Gambo ya ji tsigar jikinsa ta tashi ''Sa'a biyar? Sai gari ya waye musu ke nan a asibitin...?? LINZAMIN SHAIDAN-12 . 'Me kike nufi da cewa ba 'karamin aiki bane?'' Gambo ya tambaya yana duban Tani akwai alamun zargi a muryarsa. ''Aikin zai dauki kusan sa'o'i biyar kafin a gama...'' Gambo ya ji tsigar jikinsa ta tashi ''Sa'a biyar? Sai gari ya waye musu ke nan a asibiti wanda hakan bai taba yiyuwa. A karo na farko sai Gambo ya farga ya kuma fara jin matukar hadarin da suke ciki a jikinsa wanda a 'yan sa'o'in da suka wuce dokin Jabir zai fada masa inda ya boye kudin shi ya hana shi gano hadarin a fili. Amma a yanzu da ya fahimci cewa sai an dauki sa'o'i kafin Jabir ya iya magana da shi sai ya ga lallai akwai sake. A wannan dakika ne to mahaukacin tunani ya zo masa! ''Sai kuma....an 'kara masa jini'' Tani ta ce cikin sauri saboda ganin sauyin yanayin da ke fuskar Gambo ita a tunaninta hakan da ta ce burge Gambo ta ke yi tun da dai 'kokarin ceton ran abokin su take yi Gambo bai ko ji abin da take fadi ba Wata zuciya na cewa da shi ''Wani ma'aikacin asibitin na iya baro bangaren aikinsa ya shigo wannan bangaren a bazata duk da yake dai ruwa ake yi to amma tsautsayi bashi da kadan.. Jami'an tsaron da suka yi artabu da su na iya biyo sawunsu har zuwa asibitin.. Kai abin na da hadari'' Wannan tunane-tunane da wasiwasin zuciyar su suka sa Gambo ya sake tunani lokaci guda kuma tunanin abin da ya kamata ya yi ya darsu a zuciyarsa ''Daure masa 'kafar!'' Gambo ya ce kusan a fusace. Tani ta rike numfashi a tsorace. ''Ba...aiki za'a...'' ''Ki daure masa 'kafar na ce!'' Gambo ya ce lokaci guda kuma ya zaro bindigar sa fili. Lanto da ke tsaye a bayansa shima ya yi abin da ya ga shugabansa ya yi. Jikinta na bari idanun Tani a kan bindigogin ta yi saurin saka bandeji ta daure 'kafar cikin hikima yadda jini ba zai ci gaba da zuba sosai ba. ''Dauki duk kayan aikin da kike bukata''. Gambo ya umarce ta. Tani ta dube shi a rude cikin rashin fahimta. Gambo ya kama kwalar rigarta ya fisgota kusa da shi ya ce cikin kakkausar murya. ''Dauki duk kayan aikin da kike bukata, wadanda zasu iya tsaida jinin da ke zuba... Kada ki manta kuma ki dauki har da jinin da za ki 'kara masa.... Idan kika sake muka je kika ce dani kin manta wani abu sai na kashe shi a gabanki... Kema ki bishi a baya''. Gambo na gama fadin haka sai ya hankada Tani da 'karfi ta tafi taga-taga ta daki wata katuwar kanta ta magunguna. Nan da nan sama da kwalabe goma suka fara yiwa kamsu rotse a 'kasa. Gambo ya dubi Peter da Asabe ya ce. ''Ku bi wannan ku koma can ciki inda sauran suke kuyi jirana''. Jiki na rawa Lanto da Peter da Asabe a gaba suka fice daga dakin.''Ku daure min su kafin na zo''. Gambo ya ce da Lanto cikin karaji. . Sidi mai Jaka ya sake yin shiru a karo na biyu tun sa'ar da ya fara 'kulla wannan zaren labarin. ''Nas, na yarda kudi na iya sa mutum ya haukace lokaci guda. Yanzu ka duba ka ga yadda son abin duniya ya gama haukata Gambo cikin dan 'karamin lokaci''. ''Wannan gaskiya ne''. Na ce da shi. ''Ya ya to aka yi?''. Sidi mai Jaka ya ci gaba. . ''Bayan kamar mintuna biyar Gambo ya sako Tani a gaba fuskarta babu kyawun gani, domin babu mafi munin gani a fuskar kyakkyawar mace a lokacin da take cikin janhuru. Tani dauke take da 'katuwar jaka ta magungunuka da sauran tarkace da Gambo ya sata ta dauka duk ta watsa su cikin jakar, Gambo na biye da ita a baya yana tura gadon da Jabir ke kwance a kai. Gambo ya yi tsaye yana nazarin jama'arsa guda uku. ''Me....me za ku yi musu?''. Tani ta tambaya cikin shesshekar kuka sa'ar da ta ga su Peter da Asabe kwance a tsakar dakin an hada hannayensu da 'kafafunsu guri guda an daure tamajau kamar damin goro. ''A nan zamu tafi mu barsu Tani''. Gambo ya ce da ita. Ga mamakin Tani gambo ya sake tausasa muryarsa a karo na biyu. ''Ko...kashe shi za ku yi?''. Tani ta tambayesu cikin karayar zuciya tana duban gadon da Jabir ke kwance a kai. ''Ba lallai bane...indai kika yi abin da muka saki..''. Sannan sai ya dubi sauran mutanen uku ya ce. ''Ku taho min da shi cikin mota''. Ya nuna Jabir da hannu lokaci guda kuma ya dada cakumar Tani ya ce, ''Mu tafi cikin mota''. Akwai wani abu a muryarsa da ya hana Tani 'kokarin yi masa turjiya. Har yanzu ruwan ake tafkawa kamar da bakin 'kwarya, a wannan karon har da iska mai karfi. . Motar ta fice daga asibitin a guje, ta doshi hanyar da za ta fitar da su daga birnin. Mutum uku ne a gaban motar har direba, ya yin da Gambo, Lanto da kuma Tani suke zaune a bayan motar bata ko motsi ga dai ruwan saman da ya jika mata gashi sa'ar da suke fitowa daga dakin yana 'kokarin shigar mata idanu. Amma ba ta damu da ta goge fuskarta ba. ''In dai kashe Jabir za su yi, to nima gara su kashe ni''. Abin da Tani ke cewa ke nan a zuciyarta . Lanto ya kara bakinsa a kunnen Gambo ya ce da shi cikin rada ''Ina muka nufa kuma?'' ''Maboyarmu mana.. Kafin al'amura su yi sanyi gurin nan ya yi mana zafi yanzu'' ''Kana da maboya ne?'' Lanto ya sake tambaya. Gambo ya saki murmushim yake ya ce ''Na gama tunanin komai tun kafin mu fara komai Tabbas ina da maboya...maboyar da babu wani jami'in tsaro da ke 'kasar nan da ya isa ya gano mu a can!''. . KASHI NABIYU Sidi mai Jaka ya yaye bakinsa gaba daya kamar zai fashe da kuka Ashe wai duk hamma ce yake yi Sidi mai Jaka ya shafi fuskarsa sa'ar da ya gama doguwar hamma ya dubeni ya ce ''Wani lokaci Nas

Chapter 4 of 6