Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
2 / 6
ba... Amma kuma hakan baya nufin mun rabu da ke...zan neme ki idan kin karasa karatunki, duk inda kike sai na nemeki dan a duniya bani da kamarki Tani.... Na san ke kadai kike kaunata a duniya....kin ga dai kowa ya tsaneni saboda halina, amma ke kike sona...''. . Ya danyi shiru, sannan sai yace. ''Tani Darling, sai wata rana!''. Ya juya zai fice daga dakin karatun. Sai Tani tayi caraf! ta rike hannunsa tana kuka, tace. ''Jabir....ka yi min rai dan girman mahaliccinka...wallahi idan ka gujeni Jabir bazan taba yin aure ba a duniya....dan kai kadai ka dace da ni....'' Ta fara kuka wi!wi!!. ''Cool down Tani. Ba gudunki zan yi ba alkawari ne duk inda nake ina tare da ke...kin ga Tani auranki ina kaunarsa a raina, amma komai yanzu sai da kudi...to ni bani da su, dama wannan karatun kadai na dogara sai gashi yau an koreni.... Ni namiji ne Tani, zan shiga duniya kafin ki kammala karatunki, duk inda kudin auranki yake doron 'kasa sai na nemoshi...'' Tani ta sake fashewa da kuka. Ta dago kai da niyyar ta sake lallashin Jabir, to amma abin da ta gani a idanunsa shi ya gargadeta da cewa babu wani abu da zata ce da Jabir wanda zai sa yaki barin makarantar. Dan haka cikin kuka sai ta zare zoben azurfar da ke hannunta wanda itama mahaifiyarta ce ta bata ta kama hannun Jabir tasa masa zoben. ''Ga..zobe na nan..Jabir..Ka tuna da ni dan Allah..kullum ina tare da kai..Ka rike alkawari Jabir..ni matarka ce in Allah yaso Ina Nan Ina Jiranka. INZAMIN SHAIDAN-04 . Ga....zobena nan....Jabir....Ka tuna da ni dan Allah.....kullum ina tare da kai....Ka rike alkawari Jabir....ni matarka ce in Allah yaso.... Ina nan ina jiranka Jabir, komai tsawon lokaci ba zan gaza ba, har sai ka dawo gareni''. . Ta kara fashewa da kuka. Jabir ya dubeta cikin takaici, sannan sai yace hawaye na 'kokarin subucewa daga 'kwayar idanunsa.... Bai bari ta gani ba sai kawai ya juya yana cewa. 'lNa rike alkawari matata''. Itace kalma mafi dadi da faranta zuciya da ta taba ji a rayuwar ta. A haka suka rabu tana kuka kamar ranta zai fita. . 'Ga goro!!'' Wata yarinya ta 'kwalla talla a zauren gidan. Sidi mai Jaka ya dubeni. Nayi mamaki sa'ar da na ga har yanzu idanunsa da kwalla. ''Nas, kullum yaran nan sai sun kawo talla gidan nan, sun dauka ina da mata, basu san ni kadai nake zaune ba''. ''Basu da tunani ne''. Na ce da shi ba tare da ni kaina na fahimci ma'anar abin da nake nufi ba, domin na matsu ya ci gaba. ''Nas, in dai kana biye da ni a cikin wannan labari, to ka san ko ban fada maka ba, tabbas Tani dole ta shiga matsanancin hali?''. ''Har bayan da ta gama karatu bata sake kula wani mutum ba da sunan soyayya. Ga shi dai kullum sai matsin lamba take samu daga wurin iyayenta na 'kauye akan ta samo miji, ta samo miji, abin ya ci tura. Domin sam a kullum Tani gani take kamar Jabir zai dawo ma ta, amma gashi wasa-wasa yau shekara biyu babu shi babu alamarsa. A wannan yammaci ne to da nake baka labari Tani ta tashi daga aiki, tana 'kokarin tsallaka titi domin zuwa kasuwa sayen wasu kayan masarufi katsam! Sai taji ance. ''Tani na dawo''. Ta juya firgigit! Zuciyarta kamar zata fasa 'kirjinta, domin ko kafin ta juya ma tasan duk duniya babu mai wannan muryar sai JABIR. ! . ''Jabir ruhina!'' ''Jabir....wayyo! Allah, ban gaskata idanuwa na ba''. Tani tace a rikice, ''Nine Tani.... Ai nace miki alkawari ne sai na dawo gareki...''. ''Masoyan biyu suka yi shiru na dan lokaci suna duban juna kowa na kokarin ganin sauyin fuskar dan uwansa bayan rabuwa. Jabir dai yayi matukar kaduwa da ganin irin yadda Tani ta dada kyau da kwarjini, gashi kuma ta mulmule ta dada kiba sai 'kyalli take. A bangaran Tani kuwa, tana duban Jabir sai taji zuciyarta ta rubza, domin kai da ganin kodaddiyar kwat dinsa mai kamar dasta kasan yana cikin mawuyacin hali. Haka nan kuma takalmin dake 'kafarsa a yanzu tun zamanin zamansu a makaranta ta san shi da takalmin. A da takalmin na cinyewane gurin 'yan matan jami'a, amma a yanzu da Tani ta dubi takalmin sai taji cikinta ya murda, domin yaso yayi kama da rubabben danyen nama. . ''Ai sai mu shiga ciki ko.... Gida na yana ciki...'' Tani ta nuna 'kofar asibitin da hannunta. ''A nan kike aiki ne?''. Tani tayi murmushi tana duban kodaddan takalminsa mai kamar kwale-kwale. ''A nan nake aiki, gidana kuma yana ciki... Ni kadai ce aciki'. Jabir ya dubi agogon hannunsa. ''To kije zan shigo na same ki nan da awa daya... Yanzu ina sauri akwai wani (meeting) da zamu yi, amma ki jira ni zan shigo nan da 'karfe biyar...'' Murmushin dake fuskarta ya subuce. ''Haba Tani, ba guduwa zanyi ba....ki tuna fa ni na fara yi miki magana baki ganni ba''. Tani ta sake jifansa da irin murmushin nan da rabon daya ga irinsa tun suna jami'a. ''To shikkenan Jabir, idan kazo sai ka zagaya can bayan asibitin, gidajen suna daga can ciki. Nawa shine mai lamba (28)'' ''To sai na zo''. Jabir yace da ita. . Tana nan tsaye ya hau dan acaba. Haka nan bata motsa ba har sai daya bace, sannan tayi ajiyar zuciya ta juya a hankali ta koma asibitin zaman jira, domin tuni ta manta ma da cewa kasuwa zata sayayya. A kwai wani yanayi a fuskarta wanda rabon da aga irinsa a fuskar tun farkon haduwarsu da Jabir....''. . Sidi mai Jaka yai atishawa gami da hamdala. ''Idan baka manta ba Nas dazu na baro ka ne a inda Tani take zaune a lambun gidanta, inda har nake cewa me ma?'' Ya tambaye ni. ''In babu ji to akwai jimami''. Na bashi amsa. ''Da kyau Nas, ashe dai duk kana fahimtar zarurrukan labarina ba bata lokaci nake ba...'' ''To zaman da take yi yanzu cikin wannan dan madaidaicin lambu dake gidan, Jabir take jira. Tuni har ta fara tsammanin ma bazai zo ba, dan haka ga mamakinta sai taji hawaye ya fara zuba. ''Hello Darling''. Akace da ita daga baya. Tani ta juya firgigit!. 'Oh! Jabir na dauka baza ka zo ba''. Jabir ya dubi adon data caba bayan rabuwarsu dazun nan. ''Lallai har yanzu tana sonsa''. Yace a cikin zuciyarsa. ''Gani kuwa na zo''. Ya janyo wata farar kujera dake gindin bishiyar goba zai zauna. Sai Tani tace. Haba Jabir zo kusa da ni ka zauna mana'' Ta matsa masa kan bencin ya zauna Duk da yake jikin Jabir har wari yake yi.... Amma Tani ji take yi warin kamar wani turare ne mai sabon salo na kamshi Suka yi shiru na tsawon lokaci suna duban juna sannan kuma hadari yana kallon rana tuni har ya fara dakushe hasken ranar yammacin Tani ta kama hannunsa ta dora akan cinyarta cikin farin ciki tace ''Jabir a yau zuciyata tafi nono fari Tunda ka cika alkawari ka dawo gareni gashi kuma ga dukkan alamu har yanzu ina ranka dan ga zobena har yanzu a dan yatsanka..duk kuwa da cewa yau shekara biyu ke nan rabona da kai'' Jabir ya dubeta cikin farin ciki yace ''Tani a kullum kwanan duniya bani da wani buri da ya wuce auranki..'' Tani ta katse shi ''Daman maganar da nake son ji ke nan daga bakinka Jabir domin wallahi iyayena dake gida sun takuramin (last week) ma da naje kauyen gaishe da su baka ga irin fadan da suka yi min ba to amma ni ban ga laifinsu ba domin kasan gulmace-gulmacen kauye wai har cewa akeyi sun daure min gindi na dawo birni ina zaman karuwanci na ki yin aure zan tsufa a haka. Wai dan kudin da nake kai musu idan naje ganin gida duk a karuwanci nake samu. To kaji fa wannan abu Jabir, amma duk da haka na dake, domin a kullum ina ji a jikina cewa Jabir sai ka dawo gareni, to gashi ka dawo... Ya maganar auren mu?''. Jabir yaji kamar an kwara masa ruwan sanyi a baya sa'ar da Tani tayi shiru tana dubansa. Hannunta ri'ke da dan yatsansa mai zobenta. A dan takin dakika sai zuciyarsa ta dawo masa da hoton sa'ar da take sa masa zoben alkawarin a dakin karatu a zamanin zamansu na jami'a. ''Tani masoyiyata....'' Jabir yace a sanyaye. Akwai wani irin yanayi dake fuskarsa da ya fara bata tsoro, dan ta fahimci tun zuwansa lambun kamar in tana magana ba saurarenta yake yi ba haka dai yanayinsa kamar wanda ke yawan tunanin wani abu. ''Tani... Sanin kanki ne ina 'kaunarki, matukar 'kauna, tun da nake ban taba soyayya ba akan wata 'ya mace sai ke.... Ina son nayi miki albishir da cewa na sha wuya bayan rabuwarmu dake duk akan neman yadda zan sami damar da zan aureki a mutunce ba a tsiyace ba, amma ban samu ba.... To amma nan da awa ashirin da hudu zan samo wannan damar...'' Tani ta dubeshi cikin damuwa tace a sanyaye. ''Haba Jabir, kada ka takurawa rayuwarka a kaina.....daga yau wahalarka ta kare, kayi farin ciki ya mallakina, domin a yanzu haka ina da kudi masu yawan gaske dana ajje maka a banki, tunda na fara aiki nake tarawa, kuma kasan albashinmu na likitoci yana da tsoka, dan haka in kana so yanzu ma mu shiga cikin daki na baka cek din kaje ka karbo duk naka ne masoyina...'' Ta danyi shiru tana dubansa cikin farin ciki, sannan sai ta dada cewa. ''Kayi amfani da kudin gurin al'amarin aurenmu''. Jabir ya dubeta cikin mamaki, idanunsa cike da dumbin kauna yace. ''Nagode Tani sahibata, na yaba da kokarinki... Amma kudinki naki ne, ki ajje kayanki dan ba zan karba ba, nafi son na aureki da gumi na, idan na karbi kudinki na zama mata maza kenan'' ''Haba Jabir ai ba haka bane...'' Jabir ya girgiza kansa, sannan ya rankwafa kusa da ita yace. ''Irin yadda nake sonki Tani, so nake ayi bikin da ba a taba irinsa ba a duk 'kasar nan.... Kuma ina tabbatar miki da cewa gobe war haka ina da kudin da zan maida wannan mafarki naki gaskiya, shi yasa nace dake ki ajje kudinki, domin duk da dai ban san adadinsu ba ni nasan basu fi na shan askirin ba a ranar bikinmu da ke...'' . A dai-dai lokacin ne hadarin yammacin ya taso. Nan da nan lambun ya game da iska kamar zai dauke su sama. Zuciyar Tani cike take da tunani da fargaban rashin fahimtar bayaninsa, ta kankameshi lokacin da taji iskar ta fara kadawa kamar zata dauketa. ''Hadari Jabir mu shiga daga ciki''. Numfashin Jabir ya dauke sa'ar da yaji tattausan jikin Tani a jikinsa, don haka maimakon ya saketa sai ya 'kara matseta gam a jikinsa. Da haka suka ratsa a hankali ta cikin iskar da shukeshuken furannin dake ta rangaji suka shige dakin. . ''Nas wannan shine kuskure na farko..... Allah ya rabamu da sharrin shaidan...'' Sidi mai Jaka yace da ni. Nace ''Amin'' Sannan yaci gaba. ''Lokacin da suka shiga dakin Tani bata tsayar da su a falon ba sai ta wuce da su zuwa dakin kwananta suna zuwa sai suka fada kan gado har yanzu rungume suke da juna..'' ''Allah raba mu da sharrin shaidan'' Sidi mai Jaka yace Ni kuma na sake cewa ''Ameen'' ''Hankulansu suka gushe shaidan yayi amfani da tsantsar kaunar dake tsakaninsu ya shagaltar da su suka manta da Ubangiji musamman ma ita Tani wacce har ta. INZAMIN SHAIDAN-05 . Shaidan yayi amfani da tsantsar kaunar dake tsakaninsu ya shagaltar da su suka manta da Ubangiji musamman ma ita Tani wacce har ta gama jami'a bata taba taba namiji ba balantana wani abu ya shiga tsakani amma a wannan ranar sai shedan ya shammacesu yasa su akan mummunar hanyar da daga karshe ta barsu cikin nadama. . Karfe shida na yammar suka dawo cikin hankulansu Tani ta fashe da kuka tana cewa. ''Jabir.....na...shiga uku....ya ya muka yi haka...?'' Jabir ya gyara rigarsa bai iya hada idanu da ita ba sai yace ''Sai goben'' A haka ya fice daga dakin ana iskar Tani ta sake fashewa da kuka tana cewa ''Yau ya zanyi da kaina? na tsani kaina na shiga uku Bata gushe ba tana cikin wannan hali har aka fara tsuga uban ruwan saman kamar da bakin kwarya Feshin ruwa ya fara zubowa akan fuskarta ta tagar dakin shi yasa ta tashi zaune gaban rigarta ya jike sharkaf da hawaye da kuma feshin ruwa Zuciyarta na bugawa ta dubi agogon dake manne a jikin bangon dakin karfe goma saura kadan. Ita kanta bata san abin da ya rudesu suka yi wannan masha'a ba. Shin Kauna ce ? Yaudarar kai ce ? Sha'awa ce ? Sakaci ne ? Ko kuwa rabon wahala ne ? Tambayar ke nan data dorawa kanta. Bata sami amsar ko daya ba sai ta sake fashewa da kuka. A dai-dai lokacin ne taji talfon din dake kan dan karamin teburin da ke fuskantar gadon daga arewa ya dauki ruri. ''Wanene kuma wannan?'' Ta tambayi kanta. Da farko ta dauka Jabir ne ya bugo mata wayar daga wani wurin. Nan da nan ta mike zumbur! daga kan gadon ta nufi teburin a hankali kamar mai zaben danyan kwai, sai ta dauki talfon din tace. ''Hello....Jab....'' Aka katseta daga can bangaren da cewa. ''Tani, ni ce Asabe...''. . Sidi mai Jaka ya dubi fuskata yace. ''Yanzu kam na san ka fara yadda da cewa lallai da na iya rubutu to da ba 'karamin marubuci za a yi ba ko?'' Nace da shi ''Tabbas haka ne''. ''Nas kaga fa yadda sannu a hankali nake harhada maka zarurrukan labarina ina kulla maka su guri guda kamar gizogizo to bari na karasa kulla maka wannan zaren''. Na ce da shi ''To''. Yaci gaba ina saurrare. . ''Nas, Allah ya halicci Tani da zafin nama, dan a cikin 'yan mintuna ta gama shiryawa ta suturta kan ta cikin kayan ruwa bakake na leda, sannan ta fito cikin gaggawa, domin in har ana sabo to ta saba da irin wannan gaggawa na dare... Tunanin abin da ya afku tsakaninsu da Jabir shi ya mantar da ita cewa zafa a iya bugo mata waya daga asibiti. Lokacin da ta shigo cikin ruwan da kyar take tafiya saboda karfin ruwan da kuma iska, amma bata damu ba domin abin da suka aikata da Jabir ya gama busar da zuciyar ta. To amma duk da haka sanda aka buga wata uwar aradu gami da walkiya sai taji tana mai ina ma ace Jabir na nan kusa da ita ya dan tallafeta. Lokacin da ta karaso cikin (Emergency room) din tayi mamaki domin ga al'ada tun daga 'kofa zata jiyo surutun Asabe da Peter suna ta musu, to amma yau taji tsit!. Tani ta shigo dogon falon ruwa na diga a jikinta, sannan ne to itama Allah ya nuna mata masu fuskar katakon. . ''Shigo daga ciki likita... Kada ki bata mana lokaci, so muke ki ceci dan uwanmu cikin daren nan..... Alburusan bindiga ne a cinyarsa zaki cire.... Ki kuma tabbata bai mutu ba, domin yana da matukar muhimmanci a garemu''. Tani tayi turus! Cikin kaduwa tana kallon yanayin da ake ciki. Mutanen hudu suka zira mata idanu kamar mayu. Tani ta dada matsawa cikin dakin jikinta na rawa. Kallo daya ta yiwa fuskar Asabe wacce ke tsaye kan marar lafiya ita da Peter ta tabbata ba lafiya. Haka nan kana kallon fuskar mutanen tafi kama da fuskar abin tsoro a cikin mummunan mafarki. ''Malama matsa mana ko so kike ya mutu!?''. Farin saurayin dake cikinsu ya buga mata tsawa. ''Amma fa kun san fa bamu karbar mutum sai an zo da 'yan sanda....Kuma....'' Tayi shiru lokacin da taga dukkaninsu sun zaro bindigogi kamar budar ido. ''Kiyi masa aiki muka ce! In kuma kika sake ya mutu kina wannan yangar to kwanakinki sun kare....''. Cikin rawar jiki Tani ta matsa zuwa kan gadon. Asabe da Peter suka dare suka bata guri ba tare da dukkaninsu sun dubi juna ba. Tani ta dubi mutumin dake lullube da farin mayafi yana gurnani. ''Kun tsaida jinin?''. Tani ta tambaye su, kafin Asabe ta bada amsa sai mutumin ya motsa da jikinsa kadan sai hannunsa na hagu ya fito. Sannan ne to Tani taji kamar an caka mata wuka a 'kirji. Tani tayi lau zata fadi, daya daga cikin mutanen yayi sauri ya riketa gami da girgizata, sannan sai ya kwada mata mari tas!. ''Dan ubanki baki taba ganin marar ladiya ba ne?! Idan fa ya mutu wallahi kashe ki zamu yi''. Tani ta hadiye ihun dake makogwaronta Marin da yayi mata shi ya hanata sumewa Hawaye na zuba ta kama hannun mutumin dake kwance ta sake dubawa domin ta dada tabbatarwa abin da ta gani a hannun ''Na shiga uku'' Tani tace a sanyaye idanunta kamar zasu fado Ko shakka ba ta yi a makale a dan yatsan hannun dake rike da shi zoben da ta bai JABIR NE! Hannunta na rawa ta yaye farin kyallen da ke fuskar mutumin Duk da yake yayi badda bami da gashin baki haka nan bai hanata gane fuskar JABIR abin begenta ba A karo na farko tun sa'ar da Sidi mai Jaka ya fara labarin sai ya dubeni ya bushe da dariya yace ''Na bada kai ko? Ka ce da baza ka saurareni ba sauri kake yi Nayi wa tsohon murmushi sannan nace Kai gaskiya an bada ni dan ban ta6a tsammanin Jabir ne mutumin da aka kawo asibiti ba Sidi mai Jaka ya sake fashewa da dariya ''To Nas in banda abinka da ka san Jabir din ne? Ba sai da aka koma daga baya aka sako maka zaren labarin ka san shi ba?'' ''Haka ne Baba'' nace da shi. ''Yaya kuma Tani tayi?''. Sidi mai Jaka ya dubeni ya ce. ''Nan inda na tsaya shine 'karshen wannan zaren labarin, dan haka dole mu ajje shi gefe guda har sai shima mun sa'ka masa wani zaren sannan mu had'asu guri guda mu 'kulla, sai kaga mun ci gaba da tafiya a kai''. ''To amma Baba ai da zan so in ji yadda Tani tayi da ta fahimci cewa Jafar d'inta ne''. ''Da sannu a hankali zaka ji, amma dole ne yanzu ka bini mu sa'ko wani sabon zaren kamar yadda nace ma baya kafin mu 'kullasu..... In ban da abin ka da ba raina ni ma kayi ba''. ''To ina saurarenka''. ''Yauwa Nas, haka nake so da kai... Ga wani sabon zaren nan to.... Ina son yanzu ka manta da zancen Tani ka bani aron zuciyarka na mai da ita can tsakiyar birni shekara daya da rabi bayan an kori Jabir daga makaranta....''. ''Na baka aron zuciyar''. Nace da shi. . YACI GABA Liyafa ake yi a wani tangamemen gida 'kerarre. Gidan 'katon gaske ne, domin farfajiyar gidan idan ka dubeta da kyau zaka ga ako da yaushe a shirye take ta had'iye taron ido guda.... To amma sa6anin hakan a wannan yammacin misalin shida da rabi dai-dai. Wasu 'yan tsurarun mutane ne a ciki suna watayawa abin su, domin su kad'ai suka cancanci gaiyata a wannan asirtacciyar liyafa ta bogi. Zaka yi mamakin jin duk da wannan kururuwar dana yiwa wannan liyafa na kirata bogi, to ba wani abu bane yasa na kirata haka ba sai dan duk kusan wad'anda aka gaiyata a gurin duk 'yan bogin ne. Wannan 'kerarran gida sabo fil ne ba a ko ta6a shiga cikinsa ba sai yau. A ha'ki'kanin gaskiya wani baban 6arawo ne ko kuma idan har zan saye maka zancen in ce da kai wani maciyin kasuwar dare ne ya ci riba mai yawan gaske, dan haka sai ya 'kera wannan gida, sannan ya nemi wata zu'ke'kiyar budurwa ya aura. To wannan liyafar da ake yi tsuntsu biyu aka jefa da dutse guda. Wato liyafar shagalin bikinsa ce gami da kuma bikin bud'e wannan 'kerarren gida, wanda rabon da ganinsa me yiwuwa sai ko a cikin fina-finan mutanan 'kasar Sin. Duk inda ka duba a tsakar gidan fulawoyi ne da furanni birjik suna 'kamshi, farfajiyar an lullu6eta tsaf da irin koriyar ciyawwar alfarmar nan mai taushi da a turai ake kira da (Grass Carpet) banda wannan kuma an fitar da hanyoyi sirara wad'anda aka da6e su da dutsen alfarma mai she'kin d'auke idanu da sa ka manta cewa a cikin 'kasarka kake. Wad'annan siraran hanyoyi su zaka yi ta bi su kuwa suna yawo da kai ko ina a cikin farfajiyar gidan domin kawai ka kashe 'kwar'kwatar idanun ka. Gwanayen ginin wannan gida basu bar gefen wannan 'yar siririyar hanya ba har sai da suka tabbatar da sun 'kawata gefenta da wasu irin fitilu na alfarma masu hasken tsiya kamar rana, haka nan 'karafunan da aka yi wannan fitilu da su duk na gwal ne da narkakkiyar azurfa, sauran ginin gidan kuwa ko makaho ya laluba ya san ginin dutse da dutse ne, ba na bulo ba. Ha'ki'ka gidan kam sai dai ko mahadi ka ture. Mafi yawa daga wad'anda suka halarci wannan liyafa duk 'yan kasuwar dare ne, sai 'yan d'aid'aikun mutane da aka gaiyata wad'anda a ya yin da suka ga tsaruwar gidan sai suka fara tunanin kai lallai wane kasuwanci ya yi kyau. Liyafa tayi liyafa, tuni har an fara tand'e-tand'e da lashe-lashe, duk inda ka duba sai kaga mutane akan tattausar koriyar ciyawar sun shinfid'a dadduma, gabansu kuma kayan sha da ci ne iri daban-daban suna ta cusawa bakunansu suna santi. . To amma duk da wannan sharholiya da ake yi, a can wani 6angare daga cikin ginin gidan, wasu mutane ne guda hud'u tare da mai gidan suna tattaunawa. Mutanen a cikin wani 'katon falo suke wanda ke dauke da tagwayen kofofi na gilashi wannan shi ya basu damar ganin duk abubuwan da ke faruwa a farfajiyar gidan domin kofar daman farfajiyar gidan take kallo. Mai gidan ya mi'ke tsaye a hankali ya dubi mutanen biyar da ke lullume a cikin kujerun alfarmar da suka yiwa d'akin kawanya... July 13 at 8 INZAMIN SHAIDAN-06 . Mai gidan ya mike tsaye a hankali ya dubi mutanen biyar da ke lullume a cikin kujerun alfarmar da suka yiwa dakin kawanya ya nuna daya daga cikinsu yace ''Wannan fa? Mutumin da ya nuna a cikinsu ba wani bako bane a gareka Nas Jabir ne! . ''Jabir?'' Na maimaita sunan ina duban Sidi mai Jaka ''kwarai kuwa.. Ai labarin da na ke baka in zaka iya tunawa a baya na ce da kai shekara daya da rabi ne bayan an koreshi daga makaranata ka ga wata shida ke nan kafin su sake haduwa da Tani a wancan tsohon zaren labarin da muka ajiye'' ''Haka ne'' Nace da shi ''To sa'ar da Jabir ya dawo gida da zummar tun da yanzu an kore shi daga makaranta bari ya koma harkarsa wacce ya saba don haka sai ya dada kutsawa neman abota da manya-manyan miyagun abokai Amma duk da haka dai babu wani abin zo ku gani da ya tara domin daman yan sace-sacen unguwa ne da ire-iren 'kananun damfara domin har izuwa wannan lokaci babu wani daga cikin mutanensa da ya ta6a bada kwarin gwiwar a shiga fashi. A haka suka yi ta zama har zuwa shekara daya da rabi, asara goma da shirin ga Jabir domin gashi dai ya bar makaranta a shekararsa ta 'karshe. Haka nan da yake mafarkin mallaka ma kanshi auren wacce yace tafi kowa a duniya shi ne ya gagara, dan haka adai-dai lokacin da ya fara tunanin lokacin fa ya 'kare masa, domin yasan tuni TANI ta dade da gama karatu, don haka dole ne ya san nayi. A ranar da wannan tunani ya zo kansa ne to aka gaiyaci abokansa guda hudu zuwa liyafar. . ''Wani tsohon abokin mu ne wallahi..... Amma kaji kuwa yadda ya yi bala'in (hitting)... Kai wallahi ya dace, ka shirya mu tafi Jabir duk da yake dai bai gaiyata da kai ba, amma zan so ace ka ganshi, domin sa'ar da muka had'u da shi kai kana can makaranta kana 6atawa kanka lokaci a banza''. 'Daya daga cikin abokan Jabir d'in ne ke cewa da shi haka. . ''Wannan wane ne?''. Sai d'aya daga cikinsu yace. ''Abokin mu ne wannan... Mun dade da shima duk da joni ne...''. Mutumin ya saki fuskarsa sannan yace da su. ''To ku fita mu zagaya in nuna muku fasalin gidan''. Kusan mintuna arba'in da biyar suka yi yana ta zazzagawa da su. Zuciyar Jabir cike da tunanetunane barkatai, domin duk inda aka zo a cikin gidan idan ya ga ya birgeshi sai ya fara tunanin inama ace wannan nasa ne shi da abar 'kaunarsa TANI, domin shi a tunaninsa wannan 'kayataccen gida da aka nuna musu duk duniya babu wanda ya dace da shi sai masoyiyarsa TANI. Bayan an tashi daga liyafar ne Maigidan ya tara dukkan wad'anda suka halarta yai musu godiya, sannan sai ya rako manyan abokansa har zuwa 'kofar gida. Suna zuwa sai abokanansa hud'u gami da Jabir suka ga wata mota bakikirin tana sheki 'kirar ''HONDA'' ta tsaya gaban mai gidan yayi 'kasa-'kasa da muryarsa yace. ''Ku shiga a kaiku gida....na gode, kuma daga yanzu duk sa'ar da kuke neman taimako to kuna iya samuna.... Ni kam na tsallake saura ku.... Sai ku dage''. Mutanan hud'u suka shiga gidan gaba, wani direba fari fat da shi mai siffar buzaye yaja motar suka tafi suna dagawa juna hannu har suka bar farfajiyar gidan. Lokacin da direban motar ya ajjesu a majalisarsu, sai ya bud'e bayan hondar ya d'auko 'yar madaidaiciyar akwati, ya dubi babban cikinsu sai ya mi'ka masa akwatin ya ce. ''Alhaji ne ya ce a baku''. A haka yaja motarsa ya barsu baki bud'e cikin mamaki. To amma sa'ar da suka kad'aice a d'akin d'aya daga cikinsu sai suka tarar akwatin cike take da 'yar murtala-murtala sababbi kakar! Har naira dubu hamsim. . Zancen banza ke nan! Wai zaki ya taka wuka.... Wannan matsiyacin ya rasa abin da zai bamu sai dubu hamsin? Uban dubu hamsin!''. Mutanen uku gami da Jabir suka yi shiru na d'an lokaci suna sauraron mai bambamin fad'an. Me yiwuwa su baza su iya surutu bane....babu mamaki kuma kad'uwar ganin 'kan'kantar kud'in ce ta sa su yin shiru kamar ruwa ya cinye su. Jabir ya dubi kud'in da ke gabansu, sannan ya dubi d'akin da suke zaune, 'katon d'aki ne wanda rashin kayan al'ada na d'akin ya da d'a sa shi fad'i, domin in ka d'auke gado d'aya jal d'in dake d'akin, gami da tsofaffin kujerun katakon da suke zaune akai d'akin ba komai sai tarin yanar gizo-gizo daga can saman rufin d'akin. A can gefe guda kuma tarin tsofaffin kwalayen taba ne tsibi guda. Domin a kullum kwanan duniya ba a sha ba a shanye sama da kwali biyar. . ''Kai wallahi.... wannan d'an banzan ya yi bala'in raina mana hankali ma....!''. Jabir ya muskuta, sannan ya dubi abokan nasa uku da ke zaune, biyu sunyi tagumi d'aya na bambamin fad'a, ya yi murmushi sannan ya ce. 'Kai Gambo, kada kasa jininka hauhawa a banza gado in ba na uwarka ba ne idan aka baka allura ai sai ka gode Allah... In banda abinka ina kai ina fada dan an bamu dubu hamsin? Karenmu ne ya kama? Shekarar mu nawa yau muna shirye amma har yanzu bamu tana samun dubu hamsin a dunkule ba'' Jabir yayi shiru haka nan sauran mutanen uku suka yi shiru kowa na nazarin abin da Jabir ya ce domin sun san duk abin da Jabir ya fada gaskiya ne.. Haka nan maganar tasa tamkar zagi ne a garesu gami da Allah wadai da lalaci irin na su' Sidi mai Jaka yayi shiru yana dubana ''Nas lallai gaskiya ne wato ko a cikin mutane akwai shaidani'' ''Gaskiya ne'' Nace da shi Cikin rudewa, domin har yanzu labarin da yake yi ni a fahimtata bashi da wata alaka da wancan labarin da ya baro a baya domin wan can duk ya fi wannan dadi Sidi mai Jaka ya yi murmushin yake yace ''Na san daman nan gurin (Nas) dole ne labarin ya gundure ka domin duk cikin labarin nan ya fi ko ina gundurarwa da rashin dadi to amma in har za ka bini a hankali Nas da sannu zan harhada maka shi guri guda na dauki bakin zaren labarin mu hada da wancan da muka baro a baya mu 'kulle'' ''Haka ne'' Na ce da shi Sidi mai Jaka yaci gaba. . ''Tsawon lokaci samarin hudu na zaune suna duban kudin duk ransu a bace kai ka ce kullin kashi suke kallo Gambo ne ya fara bata shirun ''To kunji abin da Jabir ya ce dole ne mu nemo inda matattun zuciyoyinmu suke mu farkar da su domin ni irin wadannan 'yan sace-sacen sun isheni lokaci yayi da ya kamata mu huta'' Aka sake yin shiru a dakin. A wannan karon Jabir ne ya dubi Gambo yace ''To ai mu kai muke sauraro.. Kawo mana mafita tun da dai na fuskanci yau duk kafi kowa kumfar baki'' Jabir yayi shiru yana murmushi. Gambo ya yi kamar bai ji abin da ya ce ba. Amma can sai ya nisa ya ce. ''Hanya daya ce mafita''. Mutanen uku suka dubi juna lokaci guda cikin mamaki. ''Mene ne mafitar?'' Biyu daga cikinsu suka tambaya. Gambo ya sunkuyar da kai kasa tsawon lokaci yana duban 'kasa, sannan sai ya dago kansa ya ce. ''Muma sai mun bi hanyar da ya bi''. Sauran suka fashe da dariya jin abin da yace, domin duk sun dauki abin shirme. Gambo ya dubesu a fusace. ''Menene kuma na dariya? Uban wa kuka tambaya mafita? Bani ku ka...'' Jabir ya katse shi. ''Zubawa ranka ruwa ka kwantar da hankalinka, ko ma fahimci juna. Gayu ne

Chapter 2 of 6