Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
5 / 6
idan na ci TUBANI haka yake yi min wannan tsiyar sai ka ga yana neman sa ni barci lokacin kwanciyata bai yi ba'' ''Haka ne'' Na ce da shi ina mai mamakin yadda za'ayi mutum yaji barci lokacin kwanciyarsa bai yi ba ''Ina suka nufa da su Jabir ke nan?'' Na tambayeshi cikin doki domin na fahimci cewa labarin ya fara sauya salo Sidi mai Jaka ya sake jan doguwar hamma mai barazanar hadiye duk abin da ke kusa da shi ya ce ''Haba Nas ai ya kamata yanzu ka fara gane yadda nake hada zarurrukan labarina In ka lura da kyau ai karshen wannan zaren labarin ke nan dole ne sai na saka masa dan uwa kafin na jona shi da wannan mu ci gaba'' ''Ina sauraronka'' Na ce da shi Sidi mai Jaka ya dubeni na dan tsawon lokaci sannan sai ya fara da cewa ''Nas dauki zuciyarka da tunaninka baki daya ka mayar da su can wata rugar fulani kimanin kilomita dari da shirin daga birnin Gongola'' ''Gongola kuma?'' Na tambaya cikin mamaki ''kwarai kuwa ai a can ne zan sako maka sabon zaren labarin Kasan kamar gizogizo na ke wajen iya saka zarurruka... To sai dai ni ban iya rubutu ba''. Sidi mai Jaka ya yi shiru na dan lokaci, sannan ya dora. . Wata ruga ce Nas, wacce ke zaune ita kadai a tsakiyar wani daji. A daren wani lokaci da ya wuce ba karamar riga bace, domin akwai fulani makiyaya sama da talatin da biyar a rigar. To amma da zamani ya tsawaita sai ya zamanto babu kowa a rigar, daga Malam Ja'e sai matarsa Gudidi. Malam Ja'e yana zaune a rigar ne shi kadai a halin yanzu, domin sauran 'yan uwansa Fulanin rigar tun sama da shekara goma suka bar rigar. Akwai dalilin da ya sa Malam Ja'e yake zaune a rigar. Na farko dai tun suna 'kanana shi da 'kannensa, iyayensa suka zo da su rugar. Iyayensa ne suka fara zama a gurin tun daga lokacin ne fulani sukan zo su yada zango na 'yan watanni ko shekara su wuce. Haka nan wasu kuma su maye gurbinsu, domin Allah ya albarkaci gurin da fadamu da kuma koguna da yalwar abincin dabbobi sama da shekara ashirin da wani abu iyayen Malam Ja'e suna gurin. Ran nan, katsam! Sai Allah ya yiwa iyayen Ja'e rasuwa, a lokacin duka-duka bai fi shekara goma sha biyar ba a duniya. Haka nan watansa uku kacal da auren Gudidi diyar wani sarkin riga da ke kimanin kilo mita uku daga rigarsu Ja'e. Mutuwar iyayen nasa ta sauya masa al'amari, domin sa'ar da Rani ya kawo kai sai 'yan uwan ubansa suka nemi da su yi gaba suga abin da hali zai yi, domin duk da yawan fadamun da ke gurin abincin dabbobinsu ya fara yankewa, saboda yawansu. Aka kada aka raya, Ja'e ya buka kasa ya ce sai dai su tafi su barshi a gurin, domin bai taba yin nisa da kabarin iyayensa. Tun daga lokacin Ja'e ya share gindin zama na din-din-din a rigar. Duk an watse an barsu daga shi sai wani takadarin 'kanensa marar jin magana. Tun wannan 'kanen nasa yana 'karami ake fama da shi domin a kullum kwanan duniya sai ya tsokani manoman 'kauyukan da ke daf da rigar fada. Tun iyayensa na da rai suke fama da wannan takadarin yaro, dan haka sa'ar da iyayensa suka mutu sai duk Janhurun wannan 'kanen na Ja'e ya dawo kansa, domin a lokacin yaron ya zama saurayi, ga shi kuma dogo 'karkarfa, kullum sai sunyi fada da matar Ja'e. Wani sa'in sai Ja'e ya dawo daga kiwo sai ya tarar 'kaninsa ya yi mata dukan tsiya ya daure ta a cikin daki. Wani sa'in sai ya yi ma ta tsirara haihuwar uwarta sannan zai barta a haka Ja'e ya sameta. Idan Ja'e ya tambayi dalili sai yace. ''Bata da kunya ne shi ya sa. Kuma kullum sai ta yi min 'kwauron miya idan za ta zuba min dumame''. Babu abin da Ja'e zai iya domin 'kanen nasa ya gama tsoratashi, ya sa masa arwa, gashi dai a doke bai dakuwa, domin akwai ranar da Ja'e ya taba 'kokarin nuna masa cewa shi fa a gabansa yake amma sai wasan ya baci domin kanen ya daga Ja'e ya buga shi da 'kasa ya taka sannan ya zaro babarbariyar wuka ya dora a doron wuyan Ja'e ya ce ''Idan ka sake shiga hanyata sai na yanka ka na aure matarka Tun daga ranar Ja'e ya tsorata da shi. Wata rana katsam! Sai 'kanen nasa da rana ana hunturun sanyi sai ya ce da Ja'e ''Ja'e ni zan shiga duniya, na ga wainar da ake toyawa'' Ja'e ya dubi fuskar 'kanin nasa a tsorace ya ce. ''Duniya wajen ina?'' Ja'e ya dubi fuskar 'kanin nasa a tsorace ya ce ''Duniya wajen ina?'' ''Nima kaina ban san ina zani ba. Zan shiga birni ne domin naji an ce mutanen birni na can suna ci da rabonmu''. Saurayin ya mike tsaye, sannan ya saba sandarsa a kafada ya ce. ''Sai abin da hali ya yi. Me yiyuwa wata rana in na waiwayeku na taho ma da burodi na san sau daya ka taba cin shi''. Tun daga ranar Ja'e bai 'kara ganin 'kaninsa ba. Ya yi murna da hakan, domin kusan shekaru goma sha biyu da tafiyar 'kanen nasa ya yi zaman lafiya da matarsa, su yi kiwon dabbobinsu, suyi noma. Malam Ja'e bai damu da duniya ba, sai dai kuma abu daya ke damunsa, tun da yake bai taba haihuwa da matarsa Gudidi ba''. . Sidi mai Jaka ya yi shiru sa'ar da ya kawo nan yana dubana. ''Na gama baka hoton abubuwan da suka faru a wancan tsawon zamani. Bari kuma na jona maka da sabon zamani . ''A wannan safiya Nas Ja'e ya tashi tun sassafe ya fara shirin tafiya gona domin uban ruwan da aka kwana ana tafkawa an dade ba a yi irinsa ba ''Gudidi ina kike ne? Gara fa mu hanzarta tun kafin hantsi ya hudo''. Gudidi ta fito daga cikin bukkar dauke da buhun irin geron da za su shuka, gami da Akusa guda biyu a kanta na dan abin da za su jefa a bakin salati idan sun je gona. ''Mu tafi ko''. Gudidi ta ce cikin gurbatacciyar Hausa. Suka kama hanya abinsu tinkistinkis. Malam Ja'e na gaba ya saba sungumi a kafada, ita kuma dauke da Akushi da buhun irin butar duma ta ruwan sha. Duk kusan inda ka duba a gurin kore shar yake da ciyayi, hanyar da suke bi a yanzu tana da dan fadin gaske, domin hanyar an saba binta da Amalanken shanu, amma duk da fadin hanyar sai ciyawa gambar da ke gefe tayi sahu-sahu ta fara barazanar rufe hanyar. A dai-dai lokacin da da suka kawo daf da wata mahada hudu ne to suka ji gurnanin mota. ''Me ce wannan?''. Gudidi ta tambayi mijnta Ja'e cikin mamaki. ''Kamar kukan mota''. ja'e ya ce da ita cikin shakka. Domin sai ya yi shekara bai ga mota ba...domin in ba birni yaje ba ba zai taba ganin mota ba a nan gurin, domin tun da yake bai taba ganin mota ba, yana ganin Amalanke amma ba mota ba. Tun da Ja'e yake sau biyar kawai ya taba ganin mota a birni. Sautin motar ya dada matsowa inda suke. Nan da nan suka ratse daga hanyar suka yi cirko-cirko suna jiran su ga abin da zai bullo. Suna nan tsaye kuwa sai suka hango katuwar motar baka ta nufo inda suke. Ja'e ya dubi matarsa Gudidi cikin mamaki. ''Me yiyuwa Malaman boko ne....domin wani abokina a birni ya gaya min cewa suna bi rigariga suna koyawa fulani karatun boko''. Motar ta zo daf da su kamar za ta wuce. Ja'e ya fara daga wa motar hannu. Ga mamakinsa sai ya ga tayi cak! a gabansu ta tsaya. ''(Hande in boni) na shiga uku..''. Gudidi ta ce a tsorace, domin ta sha jin labarin 'yan yankan kan mutane da ke bin 'kauyika da rigage. Malam Ja'e ya yi kasake ciki ya duru ruwa yana duban motar a rude. Wata zuciyar na cewa da shi ya ruga ya shiga cikin daji... Sai dai kuma idan ya ruga ai ga matarsa Gudidi. Ja'e ya yi mutuwar tsohuwa a gurin, gashi kuma wani abin 'karin tsoro ga al'amarin ba ya iya ganin mutumin da ke cikin motar sabo da yanayin duhun gilashin tagar motar. Ga shi dai ni'imtacciyar iskar damina mai dauke da kwayoyin ruwa sai busawa take yi gwanin dadi a cikin dajin, amma duk da haka Ja'e gumi yake yi tun daga sama har zuwa marainansa a jike suke saboda kaduwa. Tsawon lokaci suna tsaye, itama motar na tsaye, sannu a hankali sai kofofin motar baki daya suka bude lokaci guda. Numfashin Ja'e ya dauke sa'ar da ya ga wasu irin mutane masu kusan kama daya, suna sauka daga motar kowannensu sanye da bakaken kaya. Ja'e ya 'kirga su a ransa, su hudu ne mutanen. Ja'e ya gama yanke 'kauna, mutuwa zai yi, domin ko shakka ba ya yi 'yan yankan kai ne. Akushin da ke hannun Gudidi ya 'kwace, abincin ya kife a cikin ciyayi. Gudidi ta zagaya bayan Ja'e ta rike kafadarsa jikinta na rawa. Wani 'kato daga cikin mutanen hudu ya rabu da sauran ya matso daf da Ja'e, sannan ya cire tabaransa suka yi ido hudu da Ja'e. ''Yaya Ja'e! Har yanzu dai kana nan da tsoron nan na ka?''. Wata sassanyar iska ta kada tsirran da ke dajin. Ja'e yaji gabansa ya fadi sa'ar da yaji muryar. . ''Shin baka gane ni bane Ja'e?''. Nan da nan Ja'e ya jefar da sungumin da ke kafadarsa ya dubi fuskar mutumin Bakinsa na rawa ya ce. ''Ko ina....a ko....ina, indai ina da rai, idan naji muryar nan sai na gane mai ita... Na gane ka bawan Allah kai ne dan uwana na jini 'kani na Gambo !'' ''GAMBO kuma?'' * Sidi mai Jaka ya fashe da dariya sannan ya ce Da a ina hankalinka ya ke? Yanzu ashe kai Nas har abada ba ka iya gane yadda na ke saka zaren labarina?'' ''To amma ai ya kamata tun farko ka fada mana sunan 'kanin Ja'en'' Na ce da shi ''In da ban yi hakan ba kuma na bada kai.. Ai hakan shine labari'' Sidi mai Jaka ya ce Sannan ya ci gaba ''Kai dai biyoni mu dora da wannan labari Wata daya da 'yan kwanaki da zuwansu rigar ku..'' ''A'a ai kuma ka tsallake baka bani labarin abin da ya faru ba sa'ar da Ja'e ya gane cewa dan uwansa Gambo ne ya dawo'' Sidi mai Jaka ya shafi fuskarsa da busassun hannayensa ya dubeni ya ce ''Wani lokaci mutane na ban mamaki Yanzu ace dai ku in za a baku labari sai an baku labarin komai da komai har 'kurunkus!? Haba Nas ai idan aka ce sai an fadi komai da komai na labari to sai ayi kwanaki ana yi har wuyan mutum ya fara ciwo Tsoho kamata Nas bai kamata ace ya cika yawan magana ba'' ''Hakane'' Na ce da shi lokaci guda kuma ina mai mamakin yadda yawan magana zai sa shi ciwon wuya in har manyamanyan Tubanin da ya hadidiya ba su sa shi ba'' Nas, ina son ka dauka a zuciyar ka cewa tuni Gambo da yaransa sun yi wata guda a maboyarsu''. Sidi mai Jaka ya ce da ni. ''Na dauka to''. Na amsa masa. ''Yauwa Nas..... To wata safiya, wacce ta zamto ita ce safiyar su ta talatin da uku da zuwa rigar. Gudidi matar Ja'e na zaune tayi tagumi a gindin runbu, daddadar iskar safiyar damina na bugun fuskarta. Katsam! Sai ta ga kyakkyawar Malamar asibitin nan da su Gambo suka zo da ita ta fito da sauri daga cikin bukkar da take kula da marar lafiya. Tana fitowa farfajiyar sai ta fara keta amai a cikin shuke-shuken duma da kabewa. Gudidi ta dubi kyakkyawar matar cikin tausayawa sabo da kakarin aman da take yi. Gudidi ta yi kamar ta tashi taje kusa da ita, domin ta tallafa mata, amma tsoro da fargabar kashedin da Gambo ya yi musu ita da mijinta Ja'e ya hanata. Gudidi ba za ta taba mantawa da ranar ba. Domin sa'ar da mijinta Ja'e ya gane cewa dan uwansa Gambo ya dawo, sai aka zubosu a 'katuwar motar aka dawo da su riga. Sa'ar da suka dawo rigar duk sai suka sa su a gaba kamar za su hadiye su. Gudidi bata taba jin fargaba a rayuwarta irin ta ranar ba, domin duk da cewa ta gane Gambo amma hankalinta bai kwanta da shi ba. Ta tuna da wani zamani da ya wuce a lokacin ma Gambo ko rabin haka bai kai a girma da kwarjini ba, dan 'kauye, amma duk da haka sai ya dankara mata shegen duka ya yi mata tsirara, in kuwa haka ne to me za tayi tsammani daga Gambo wanda ke tare da wadannan mutane masu kamar shaidanu a yanzu? ''Bukkoki biyu kawai kuke da su a rigar nan?''. Ita ce tambayar farko da Gambo ya yiwa dan uwansa Ja'e sa'ar da aka dawo da su rigar. ''Su...ke nan''. Ja'e ya amsa masa bakinsa na rawa. ''Ina son yanzu nan duk ku kwashe tarkacen ku daga ciki....yanzu-yanzun nan ba sai an jima ba!''. Ja'e ya dubi dan uwansa a tsorace ya ce. ''Babu komai a ciki...amfaninta a garemu daman sai lokacin rani a ciki muke ajiye korika..'' Gudidi tayi matukar kaduwa sa'ar da gambo yasa aka dauko wani mutum daga bayan motar ranga-ranga kamar matacce. Haka nan suka dauko wani irin sangalalin gadon siriri marar nama. Gudidi bata taba ganin irinsa ba. Aka shiga da mutanen da gadon cikin bukkar. Ba'a jima ba kuma sai Gambo ya sake sauko da wata kyakkyawar mata budurwa daga cikin motar dauke da 'katuwar jaka fara. Kallo daya gudidi ta yiwa matar ta tabbata da cewa matar a cikin takunkumi take. Gudidi tayi matukar tausaya mata. Bayan an shigar da matar ne bukka to sai mutuanen hudu suka zagaye gudidi da mijnta Malam Ja'e. Sannan sai dan uwansa Gambo ya dubeshi ya ce da shi cikin kakkausar murya. ''Daga yanzu har zuwa lokacin da zamu bar rigar nan bana son in sake ganin wani a cikinku ya leka ko da dai-dai da bayan rigar nan... Kada kuma wani a cikinku ya kusanci waccan bukkar da muka sa mutanen can biyu a cikinta''. Gambo ya yi dan shiru yana duban Ja'e. ''Ina fatan ka fahimta?'' Ja'e ya gyada kai a tsorace, sannan bakinsa na rawa ya ce. ''Bamu da abinci....gashikuma muna son muyi shuka...''. Gambo ya dubeshi na tsawon lokaci, sannan ya ce....... LINZAMIN SHAIDAN-14 . Ja'e ya gyada kai a tsorace, sannan bakinsa na rawa ya ce. ''Bamu da abinci....gashikuma muna son muyi shuka...''. Gambo ya dubeshi na tsawon lokaci, sannan ya ce. ''Duk abin da kuke bukata na abinci mai dadi muna da shi....Zancen noma kuwa ka manta da shi, babu rabon ku yi wahala a wannan shekara. Dabbobinka kuwa na yarje maka ka fita da su nan bayan rigar nan tun da dai damuna ce na san akwai abincin da zai ishe su ba sai kayi nisa ba''. Gambo ya yi shiru, sannan sai ya zaro bindiga daga aljihun kwat d'insa ya dora ta a daf da fuskar Ja'e ya ce. ''Ina fatan ka san wannan?''. Ja'e ya gyada kai jikinsa na rawa, domin ya sha ganin doguwarta a gurin maharba. ''Kana iya yin gudu idan ka so... Amma kar ka zargeni idan ka sami kanka a kiyama a cikin dakika guda... Kada kuma ka manta duk inda za ka zagaya kiwo jama'ata suna lura da kai... Da zarar kayi niyyar gudu to sunanka matacce''. Gambo ya numfasa sannan ya dago kai ya dubi Gudidi ya ce da ita cikin busasshen murmushi. ''Gudigudi! Ke kuwa daman kin san halina....!''. Wannan kawai ya isa ya gama tsorata Gudidi tun daga ranar suke zaman wakafi, bata motsawa nan da can. Gara ma mijinta Ja'e sukan barshi ya dan zagaya kiwo bayan gida. . Bayan kaman wata 3 da gudu tafito Malamar Asibitin ta ci gaba da sheka amai cikin ciyayi. A dai-dai lokacin da Gudidi ke 'kokarin tashi domin taimaka ma ta ne sai ta hangi Gambo ya nufi inda Malamar asibitin ta ke nan da nan Gudidi ta sauya niyyarta ta farko. Amma ga mamakinta sai ta hango Gambo na ma ta alama da hannu akan taje yana kiranata. Nan da nan jikinta na rawa ta gyara tsumman zaninta ta nufi inda yake. ''Me ke damunki?''. Gambo ya tambayi Tani ya yin da Gudidi ta 'karaso ta tsaya daga can gefe. Tani ta mumfasa ta ce, ''Ji nake yi cikina shi kadai yana birkitawa''. Gambo ya dubeta na dan lokaci... Bai yi mamaki ba dan cikinta ya birkita, domin shi kansa ba kasafai ya fiye son shiga bukkar da Jabir yake ba, domin 'kafarsa ta fara doyi, saboda har yanzu alburushin bindigar na ciki ba a cire su ba, ga shi kuma har yanzu ya kasa magana. Gambo ya dubi Tani ya ce da ita. ''Ki bi Gudidi ku tafi ku dan zagaya... Kuna iya fita nan baya ku dan sha iska, zama guri dayane da kuma iskar da kike shaka a cikin bukkar can suka ruda miki ciki''. Gambo ya dan yi shiru sa'annan ya harari Gudidi ya ce. ''Gudidi ga ta nan ku tafi tare ku dan yawata''. Har suka fice daga rigar Gambo na kallon Tani. Wani abu mai kamar tausayi ya dan yi zarya a zuciyarsa. . Wata daya da 'yan kwanaki duk ta rame. Sa'ar da Gambo ya tabbata sun fice daga rigar sai ya yi fito da 'karfi. Nan da nan su Lanto suka shigo rugar. Tun kusan asuba suke zaune a bayan rugar akan ciyawa suna karta. Gambo ya dubi mutanen uku ya ce. ''Al'amura fa sun rikice.. Kun ga dai dan iskan nan har yanzu yaki ya bude baki balantana ma ya yi mana magana... Ya ya kuke gani, kun ga dai 'yan kudin ma duk sun kare, dan ina kyautata tsammanin in har muka kara wata biyu a rigar nan dole ne sai mun fita daga maboyarmu domin mu nemi 'karin kudi'. Gambo ya yi shiru yana dubansu cikin damuwa. Lanto ne ya fara magana a cikinsu. ''Ni a gani na abin da zamu yi sai mu dan 'kara hakuri, domin abin da kawai muke bukata shi ne ya fada mana inda ya boye kudin, yana fada mu gama da shi, sai kawai mu 'karasa shi ya huta da wahala, mu ma mun huta....''. Gambo ya gyada kai cikin gamsuwa ya ce. ''Ka fadi gaskiya Lanto.... Sai dai kuma abin da nake fargaba shi ne idan abin nan ya dauke mu tsawon lokaci a ina zamu sami kudin da zamu ke sayo maganunnukan da take bukata da kuma abinci?''. Lanto ya dubi shi cikin murmushi ya ce. ''Ina inyamurinka da ya baka hayar mota da bindigogi? Ai ina tsammanin in aka tsara masa halin da ake ciki zai iya yin motsi''. Gambo ya fashe da dariya, ya yi tsalle ya dafe kafadar Lanto yana cewa. ''Lallai kanka yana ja dan samari''. * A can bayan rigar, a gindin bishiyar kanta, Gudidi zaune kusa da kyakkyawar matar, ita tana kuka Tani ma tana kuka. Tun sa'ar da suka dan bacewa rigar Tani ta kwashe duk labarinta ta fadawa Gudidi. To amma a yanzu kukan da Tani take yi yana da wata manufa daban. ''Ki yi hakuri, komai mai wucewa ne in Allah ya yarda, zai kawo mana 'karshen wannan masifar''. ''Abin....ya yi min yawa....sun rabani da 'yan uwana....sun nakasa masoyina.....gashi kuma....'' Ta sake fashewa da kuka kamar ranta zai fita. Gudidi ta rude, tausayin wannan mata ya mamaye ma ta zuciya. ''Baiwar Allah ki bar kukan haka nan ya isa...ke da ba lafiya ce da ke ba''. Tani ta dago fuska ta dubi Gudidi idanunta sharkaf da hawaye ta dafa kafadar Gudidi ta ce bakinta na rawa. ''Baki gane...dalilin kuka na ba Gudidi.... CIKI NE DA NI! Ban ga al'adata ba. Cikin Jabir ne a jikina!!!''. Ta sake fashewa da kuka * Sidi mai Jaka ya dada jan doguwar hamma. ''Matsalar Tubani ke nan Nas Wani lokacin haka yake yi min irin wannan lalatar.. muddin na ci Tubani to barci ya dinga damuna ke nan'' Ba abin da ya fada na ke sauraro ba abin da ke raina shi ne da ya ce da ni.. WAI TANI TANA DA CIKI!.. . Wane irin ciki kuma?'' Sidi mai Jaka ya matsa idanunsa da busassun 'yan yatsunsa ya ce ''Ka manta masha'ar da suka aikata ita da Jabir? Na dauka na baka labarin dazu kafin sallar magariba?'' ''Oh! Na tuna haka ne...'' ''Yauwa Nas.. To yanzu kuma zan sake katse wannan zaren labarin mu koma can gaba..' ''Bayan watanni uku da yan kwanaki...'' Na dubeshi cikin damuwa na ce ''Amma Baba tsallaken naka ya yi yawa.. Ya ya za ka tsallake ka koma bayan watanni uku bayan kuma baka bani labarin abin da ya faru daga wata daya zuwa na ukun ba..?'' Sidi mai Jaka ya fara soshe-soshe ''Nas yanzu ashe in za'a baka labari sai an yi ta fadar komai da komai? In ban da abin ka ai duk tsawon wata daya zuwa na uku ba wani abu da ya faru muhimmi duk zaman jiran Jabir suke yi amma a banza domin ya ki ya bude baki balantana ma ya yi musu maganar komai.. To sai dai kuma cikin Tani ya fara girma'' Sidi mai Jaka ya dan yi shiru.. Sa'annan ya ce. ''Nas, bari na tsallae da kai zuwa wata uku domin kaji yadda zata kaya... Wannan shi ne zaren labarin mu na biyun 'karshe...''. Sannan ya ci gaba. ''A wata safiyar Laraba, wacce ta zo dai-dai da watan su na uku da kwana goma sha uku a rigar. Tani na zaune ta sa Jabir a gaba tana zubar da hawaye, domin ta san koda Allah ya kubutar da su daga 'kangin da suke ciki da wuya idan har 'kafarsa zata sake amfanuwa, domin 'kafar da aka harba ta kumbura suntum! sai doyi take yi tana zubar da ruwa...abin da ya fi damun Tani shi ne Jabir ya 'ki koda bude idanu balantana ma ya yi magana. A cewar Gambo; da zarar Jabir ya yi musu magana za su tafi su barta da abin 'kaunarta Jabir! To amma a wannan safiyar Laraba sai Tani ta sunkuya daf da fuskar Jabir ta ce. ''Jabir.... Darling....!''.Shiru na dan lokaci bai ko motsa ba.... To amma yana numfashi. ''Jabir...''. Ta sake kiran sunansa muryarta a raunane. Ga mamakin ta sai Jabir ya bude idanu ya yi mata murmushin yake. Tani taji numfashinta ya dauke. ''Jabir...!'' Ta kara kunnenta a dai-dai bakinsa domin taga yana 'kokarin fada mata wani abu. ''Tani kada ki daga muryarki sama har su gane cewa da ni kike magana...''. Jabir ya yi shiru yana matse idanu saboda tsananin ciwo. Sannan ya ci gaba. ''Tani...kiyi hakuri ki fitar da tunanina daga zuciyarki...domin bani da wani amfani a gareki, ban dace da ke ba..... na lallata rayuwata, na biyewa shaidan da rudanin zuciya, na yi kuskure.... Tani wadannan mutanen da kike gani marasa imani ne.... 'Yan fashi ne, haka nan nima ina daya daga cikinsu...''. Jabir ya yi shiru. Tani ta dubeshi tana kuka. ''Magana ta 'karshe Tani ita ce koda wasa kada kice musu munyi magana da ke....domin da zarar kin fada musu to sunanki matacciya! Duk abin da ake ina jinku shiru kawai na yi domin kudin da muka sato ni kadai na san inda suke, da zarar na fada musu inda kudin suke bani da wani amfani a garesu, kashe ni za su yi su kashe ki. Ina sonki Tani.....ina 'kaunarki....gara na mutu a haka da inyi magana da su, domin ina yi kashe ki za su yi.... Wannan shine abu na 'karshe da zan yi miki amatsayina na masoyinki.....!''. . A can bayan rigar Gambo da Lanto suka shiga cikin motarsu, sannan Lanto ya tuka suka nufi wani 'kauye inda a nan zai sauke Gambo shi kuma ya dawo gida. ''Daga 'kauyen babu wuya zan sami motar da za ta shiga da ni birni cikin dare''. Gambo ya ce da Lanto sa'ar da suka fara tafiya a cikin motar. ''Ina kyautata tsammanin hakanmu ta kusa cimma ruwa...domin Tani ta ce da ni jiya ya fara bude idanu.... Na ce da ita da zarar ya fara magana tai kirana....''. Gambo ya yi shiru. ''Kamar nawa kake jin za ka ranto a gurinsa?''. Lanto ya tambayeshi. ''Dai-dai misali dai.... Zan ranto kudin da zai iya saya mana abinci da maganunnuka a 'kalla na wata uku..''. Gambo ya numfasa lokaci guda kuma ya ci gaba. Lanto ya ragewa motar gudu sa'ar da suka kawo daf da wata mahada-hudu. ''In dai ka bi da shi a hankali ka nuna masa romin al'amuran da wuri zai hadiyi 'kugiyar.... Ka san Inyamuri da son sata?''. Lanto ya ce da shi....''. * Sidi mai Jaka ya dubeni ya ce, ''Wannan zaren labarin 'karshensa ke nan, dama ba shi da tsayi. Bari kuma in saka maka zaren 'karshe na wannan labari''. ''Ya ya na ga duk kamar sauri kake yi ka gama bada labarin?''. Na tambaye shi. Sidi mai Jaka ya amsa kai tsaye. ''Barci na ke ji Nas, Tubanin nan da na ci duk ya yi min bake-bake a ciki kamar wanda na hadiyi kyandira... Gashi kuma. LINZAMIN SHAIDAN-15 . Sidi mai Jaka ya amsa kai tsaye. ''Barci na ke ji Nas, Tubanin nan da na ci duk ya yi min bake-bake a ciki kamar wanda na hadiyi kyandira... Gashi kuma dadin labarin yana neman ya yi maka yawa...'' Sidi mai Jaka ya dada jan doguwar hamma sannan ya ce. . ''Nas ka mai da zuciyarka can cikin wata kasuwa ta Gwari a cikin Kaduna..''. Me karatu yanxu haka muna A cikin wani gida wanda ke dauke da manyan shaguna guda biyu, a cikinsu ana sai da kayan miya, kamar su Agushi, Tattasai, Busasshen Tumatir, da danyan Attaruhu, Albasa... Kai har da busasshen kifi da sauran danginsu. A cikin wani daki a gidan, wani 'katon inyamuri ya dauki jaridar cikin damuwa. ''Har yanzu ba a kama 'yan fashin ba''. Tun ranar da aka yi fashi Uche ya shiga cikin damuwa, domin sun yi da Gambo cewa da zarar fashin ya yi nasara zai dawo masa da motar da ya dauka haya a gurinsa da kuma bindigogin da ya karba. Ba 'karamar kaduwa ya yi ba washe gari sa'ar da ya karanta jarida. A ciki an bada labarin fashin da aka yiwa attajirin ya ce. ''Duk da yake sun badda kamanninsu, hakan bai hana shi gane su ba...''. Jami'an tsaro sun tabbatar da cewa shima attajirin mai tsohon laifi ne, domin ya tabbatar da hakan da kansa. A cewar attajirin. ''Tun da aka kashe matarsa LAILA, to bai damu da zama a duniya ba... To amma duk da haka ya bada sunan GAMBO a cikin 'yan fashin''. Tun daga ranar Uche ya shiga cikin tashin hankali, domin ya san da zarar an kama su Gambo, to shima kashinsa ya bushe ke nan. Uche ya zargi kansa da wauta, domin mafiya yawan lokuta ya kan dauki matakai da kulawa kafin ya arawa 'yan fashi kayan aiki. Shekarunsa ashirin da biyar yana wannan harka. Shekaru goma daga cikin wadannan shekaru shima an sha yin fashi da makamin da shi, daga baya kuma da ya ga girma ya kamashi sai ya yi ritaya, ya zama turun barayi yana kuma bada motoci da bindigogi ga abokan sana'arsa. Lokacin da ya sami labarin abin da ya faru ga Gambo, sai ya shiga damuwa. To amma daga 'karshe sai dabara ta fado masa. Ya san abin da ya kamata ya yi, domin ya tabbata al'amuran Gambo sun lalace tun da dai har ma an gane kamaninsa, an kuma buga hoton Gambo a jikin jaridu an ce duk wanda ya ganshi ya bugawa 'yan sanda waya. Attajirin da suka yiwa fashin shi ya baiwa jami'an tsaro hoton Gambo wanda suka dauka tare ranar da aka yi liyafar bude sabon gidansa. Uche ya ajje jaridar cikin damuwa. Hakika in dai har jami'an tsaro suka cafke su Gambo kafin su hadu to al'amari ya baci masa ke nan. Uche ya juya firgigit! Sa'ar da yaji 'kofar dakin ta bude. Gambo ya shigo dakin yana murmushi. Sai da Uche ya yi kusan minti guda yana kallonsa cikin kaduwa kafin ya tabbatar da sa'ar sa. . ''Gambo....!!''. Uche ya ce bakinsa na rawa. ''Ni ne dai ba wani ba... Ka dauka ba zan dawo ba?'' Gambo ya ce lokaci guda kuma ya zauna a kujerar da ke kusa da Uche. ''Ya ya ake ciki ne...shiru Gambo? In ce dai lafiya?'' Gambo ya gyada kai, sannan ya ce da Uche. ''Saurara da kyau kaji''. Kusan mintuna goma sha biyar Gambo ya shafe yana tsarawa Uche duk labarin abubuwan da suka faru. Sa'ar da ya kawo aya sai Uche ya gyara murya ya ce, ''Nawa ka ke so yanzu na 'kara ma?''. Gambo ya dubeshi cikin mamaki, domin bai taba tsammanin Uche zai amsa masa cikin gaggawa ba. ''Dubu dari biyar na ke so!''. Gambo ya amsa. Uche ya yi fito ya ce. ''Amma fa ka san da zarar kun gano inda kudin ya ke za ka kawo min miliyan biyu?''. Gambo ya yi dariya. ''Kada ka damu Uche, kudin da Jabir

Chapter 5 of 6