tafi kishi dashi akan komai yau agaban idonta suna nane da juna hawayen takaici suka gangaro mata.....
Acan kasan zuciyarta tace amma ba komai munu kwantarda hankalin ki wannan ba permanent abu bane zai wuce cikin kankanen lokaci akwai lokacin da zaki maye gurbin hajiya salma kema ki dama kamar yanda ake damawa da ita ki mallaki dukanni dukiyar ta...... Tayi murmushi tare da jan doguwar hajiyar zuciya hummm!!
Tana cikin wannan wasikar jakin mahaifiyarta ta shigo dakin tare da yin sallama tamike a zuciye yazaki shigo mun daki ba neman izini hajiya Aisha ta ce idan ma nayi sallamar zakiji ne kin lula cikin tunani sai faman murmushi kike kamar wata sabon kamun hauka....."naji meya kawoki dakina?"
"Na jima da zuwa naga banganki ba banga su Ashrab ba nace bara nagani ko bacci kike ashe idonki biyu..... Ina su Ashrab ne naga dakinsu ba kowa aciki suna ina ne?"
Ta dago idanuwanta da suka canja cikin kankanen lokaci tace suna bayan gida na mayar dasu can saboda banga amfanin su ba shi isa na mayar dasu can jikin hajiya Aisha har rawa yake tace inalillahi wa'innah ilaihi raju'un kina da hankali kuwa munubiya wannan wace irin rayuwace yara da gidan ubansu a mayardasu dakin masu aiki ita hajiyar tana aikin me?
Saida ta gama sannan munu tace kin gama bambamin naki to wannan ra'ayi nane ba na hajiyan ba kuma babu wani wanda ya isa ya ce ba hakaba...... Idan kin gama sai ki fita kuma bana son da kuskure ki kara tayar da zancen su Ashrab agidan nan idan kuma ba haka ba wallahi kinsanni sarai....... Gaban hajiya Aisha yafadfi damm!! Dan kuwa tabbas tasan halin yar'ta zata iya yin komai dan haka sum-sum ta bar dakin amma zuciyar ta cike da tunani kala-kala"
Hajiya salma ta manta da rayuwar su Ashrab kwata-kwata babu kuma wani mai tayarda zancen su agidan saboda shine umurnin damunu ta bayar.....
Haka aka fara hidimar bikin hajiya salma da BASSAM yan'uwa sai shige da fice akeyi a gidan amma babu wani awanda ya ko tanbayi Ashrab da Farha kowa sabgarshi kawai yakeyi.......
Abangaren su Ashrab kuwa tana can daki rungume da yar'uwarta yau sun tashi jikin Farha yakara rikicewa gashi kuma babu magani sai kuka takeyi sosai tarasa yanda zatayi da ita ta kwantar da ita tace bara naje na gayawa mum tabawa baba direba a siyo miki magani..... Ta mike tana sharar kwallah ta nufi kofar fita daga dakin ta ja sosai tajita gam takara jijjigawa kofar arufe take gam da makulli anrufe ta baya Ashrab cikin tashin hankali ta shiga bubbuga kofar tana kiran baba direba Amma kasancewar suna baya babu kowa haka ta gaji da bungun kofar ta koma koda taje gun yar'uwar tana kuka mai tsuma zuciya tace sun rufemu FARHA ba kowa anan saidai muyi hakuri Farha tana daga kwance hawaye suka gangaro mata yuwu suna zuba ga jikinta yayi zafi zau alamar zazzabi mai zafi yakara rufeta cikin dan kankanen lokaci tafara suma hankalin Ashrab yakai kololuwar tashi duk ta rike ce babu abunda take saidai kuka babu wani mataimaki..... Barantana yakawo masu dauki........
TAKUCE A KULLUM
LAURAT M BELLO
SHARE
VOTE& COMMENT..............
=؞?=ؕ?=؞?=ؕ?=؞?=ؕ?=؞?=ؕ?=؞?
B A N G A R E N A H
( p a r t o f m e )
=؞?=ؕ?=؞?=ؕ?=؞?=ؕ?=؞?=ؕ?=؞?
S T O R Y &