wani irin Expression na mamaki, bai yi wata wata ba kawai ya sauke masa fist dinsa a kirji har sau biyu, ya wani cakumosa yace "Are you insane? How dare you??" Khaleesat ta zaro ido ta mike cikin tashin hankali ta riko Abdul tana zaro ido with shock, lkci daya ta kalli Housemate dinta da ya tsaya yana kallon Abdul baya ko kiftawa kuma bai yi attempting rama abinda yayi masa ba, da kyar tace "He is my boyfriend, I don't think u have any problem with this, who are you? And where do you know us from? You have no right to intrude!" Housemate dinta dake kallonta ya sauke idonsa kamar bazai ce komai ba, sai kuma calmly yace "My bad! And i am sorry, i thought u were in danger, i am only here to drop some books, sorry about that plss" Khaleesat ta wani kallesa tace "Do i know u from anywhere that warrant u intruding?" Ya girgiza kai yace "Not at all... I am sorry" Kallon Abdul yayi, bowing his head gently at the same time yace "I am sorry, dude" Daga haka ya ajiye book din hannunsa ya juya ya nufi kofar parlon ya fita waje, that was when Khaleesat realized she was half dressed all this while, dukawa tayi ta fara kuka a hankali ta hade kanta da kujera tana jin kanta na wani irin sara mata, wani kallo Abdul yayi mata yana huci, kawai ya dau wayarsa ya nufi kofa ya fice daga parlon kamar zae tashi sama, ta bi sa da kallo hawaye na sauka idonta, mikewa tayi da sauri ta nufi window tana duba waje taga babu motar Housemate dinta har ya tafi, sae Abdul da ta hango yana tafiya down the street, dawowa parlon tayi tana goge hawayen dake sauka idonta ta dau Hijab dinta ta wuce daki da sauri, har wajen karfe tara na dare Khaleesat ta kasa tashi daga saman darduman da take zaune ga wani ciwo da kanta yake mata, jawo wayarta tayi a hankali, tun daxu take son kiran Abdul amma ta kasa kiransa saboda tsoro, daga karshe tayi gathering courage tayi dialing numbersa har ya katse bai daga ba, ta sake kira nan ma bai ɗaga ba, tasan ba lallai ya ɗaga ba dama, ajiye wayar tayi ta kwanta gefen gado wasu sabbin hawayen na zuba idonta. Da safe duk da yanda Khaleesat ke jin ta wani iri kamar zata yi rashin lafiya haka nan tayi shirin makaranta ta saka Facemask dinta sannan ta bar gidan, ta kusa awa daya a makarantar kafin Safiyyah ta shigo, Khaleesat ta zauna gefenta tana kallonta tace "Why are you sitted here Khalee? Is the lecturer not around?" Khaleesat ta sauke idonta bata ce mata komai ba, Safiyyah ta sauke Facemask dinta ganin swollen eyes dinta cike da damuwa tace "Subhanallahi, what is wrong Khaleesat? Kukan me kika yi? Ko jikin Mama ne?" Khaleesat ta girgiza mata kai hawaye na taruwa idonta, hankalin Safiyyah ya tashi tace "Innalillahi, don Allah me ya faru? Is everything ok?" Khaleesat ta girgiza mata kai tana goge idonta a hankali tace "Abdul ne ya zo" Safiyyah ta gwalo ido tace "Abdul kuma?? Yaushe? Kuma me ya maki kike kuka?" Khaleesat tace "He came yesterday evening" Safiyyah tace "Ji jaraba, to me ya zo yi? Kuma me ya faru da ya zo din?" Safiyyah na jefa mata wannan tambayar taji hankalinta ya tashi lkci daya, let it not be what just crossed her mind now, tunda tasan ko wanene Abdul, ta kamo hannun Khaleesat da sauri cikin tashin hankali tace "Ko ya maki wani abu ne? A gidanki ya kwana???" Khaleesat ta girgiza mata kai a hankali tace "A'a" Safiyyah bata san sanda ta sauke wani ajiyar zuciya ba, can tace "Toh meye kuma na kuka don ya zo, ko rashin mutuncin da ya saba ya shuka maki?" Khaleesat na shessheka a hankali tace "He met my Housemate" Safiyyah ta bude baki tace "Kai don Allah, cikin gidan ya gansa? To ke ma dai wallahi baza ki iya karyan kare kanki ba kice masa kawai baƙon Housemate dinki ne shi tunda bai san Nancy ta tashi a gidan ba, to sai kika ce masa me?" Khaleesat na gyada mata kai tana goge hawayen da yaki tsaya mata tace "Haka nace masa, amma ai kin sansa kinsan halinsa, he even fought with my Housemate" Safiyyah ta zaro ido tace "Fight? To akan wani dalili?" Khaleesat tace "Kema kinsan yanda yake yi ai Sophie, kawai wai zai yi kissing dina ni kuma naki yarda sai ga Housemate dina ya shigo shine yayi approaching dinsa seeing what he was doing to me, hakan da yayi ne yasa Abdul yayi fada da shi, he hit him so hard" Safiyyah tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, to Housemate din ya rama ne?" Khaleesat ta girgiza kai a hankali tace "Bai rama ba, kawai hakuri ya basa" Safiyyah tace "Wallahi in ance min Abdul na shan giya ni bazan musa ba, cause his actions portray that, kawai daga ganin mutum ka fara fada da shi kamar wani ɗan daba, kuma in banda rainin wayo zai zo me yasa bazai ce maki zai zo ba kawai sai dai ki gansa kamar an jefosa a gidan?" Khaleesat tace "Wai fa ce masa da kika yi bani da lafiya shine yasa ya taso ya taho, da na sani da ban ce kice masa haka ba" Safiyyah ta bude baki tana kallon Khaleesat don ita ma sai a sannan taga da basu ce masa haka ba tunda ba isasshen hankali ke garesa ba, Safiyyah ta sauke wani ajiyar zuciya tace "To yanzu Housemate din naki fa? Hope he didn't hurt him?" Khaleesat ta fara goge wasu sabbin hawayen idonta tace "Kinsan menene ya dameni?" Safiyyah ta girgiza kai, a hankali Khaleesat tace "Maganganun da na gaya ma Housemate din nawa, meanwhile he was just trying to be protective ganin kamar Abdul molesting dina zai yi, ni kuma abinda yasa nayi masa haka don kar Abdul din ya zargi mun san juna da Housemate din nawa, cause i told him frnd din Nancy ne kuma ni ban taba ganinsa ba" Safiyyah da ta kasa rufe baki tace "Wasu irin maganganu ki ka gaya ma Housemate din naki?" A hankali Khaleesat ta gaya mata duk bakaken maganganun da ta gaya ma Housemate din nata, Safiyyah ta dinga mata wani kallo cike da takaici, can tace "To shi katon banzan da kika fadi bakaken maganganun a kansa hope yayi considering dinki at the end of everything?" Khaleesat ta girgiza kai tace "He walk out on me, na kirasa sau biyu jiya yaki dagawa, kuma har yanzu bai kirani ba" Safiyyah ta ja tsaki tace "In ma ya ɗaga shi babban ɗan iska ne, kada Allah yasa ya daga, kuma shi Housemate din naki kun sake haduwa bayan abinda ya faru jiya?" A hankali Khaleesat tace "Shi ma tunda ya bar gidan jiya har yanzu bai dawo ba" Safiyyah tace "To wallahi ki kirasa don mutumin nan yafi karfin walakanci a wajen ki" Khaleesat ta fara wani hawayen tace "I don't have his Number" Safiyyah tace "Ban gane baki da lambarsa ba?" Khaleesat tace "Wallahi, even when i was going to Nigeria kawai hadani yayi da wani mutum ya bani number mutumin amma bai bani lambarsa ba" Safiyyah tayi shiru, can ta sauke ajiyar zuciya tace "Ki tashi kawai ki koma gida kilan Allah zai sa ya dawo sai ki basa hakuri, Abdul kuma kar ki kuskura ki sake kiransa in ba haka ba in tsine maki wallahi" Duk da bakin cikin da Khaleesat ke ciki sai da ta ɗan yi murmushi, a haka ta koma gida ta bar Safiyyah a school din bayan Safiyyah tace ta kirata duk abinda ake ciki, in ma Abdul din ne ya sake dawowa gidan ta kirata zata taho..... Throughout ranan Khaleesat bata ga Housemate dinta ya dawo gidan ba har karfe takwas na dare, ta rasa me yasa ta kasa samun nutsuwa hankalinta yaki kwanciya, ko tunanin Abdul bata saka a ranta ba tun bayan barin ta school daxu da safe da Safiyyah tayi encouraging dinta kar ta sake kiransa, but she was so restless ganin Housemate dinta bai zo gidan ba, she wish she had his number ta kirasa, wajen karfe goma saura wayarta ya fara vibrate ta jawo a hankali tana duba screen din taga Safiyyah ce, Safiyyah ta kirata yayi sau 6 daga barinta school da safe har zuwa yanzu, Safiyyah tace "Is he back Khaleesat?" Khaleesat ta girgiza mata kai a hankali tace "A'a bai zo ba" Safiyyah ta sauke ajiyar zuciya tace "Kilan sai gobe zai zo gidan, ki kwantar da hankalin ki pls" Khaleesat dai tayi shiru bata ce komai ba, Safiyyah tace "Plss kar ki wani damu kanki da yawa kawata, hope kin ci abinci?" Khaleesat tace "Na ci" Safiyyah tace "To kiyi kwanciyarki, good night" A haka suka rabu, Khaleesat ta ajiye wayarta ta lumshe ido duk da tasan ba baccin zata yi ba.......
*Continue making your payment before the end of free pages fanss, in ba haka ba aji shiruuu...*😃
07087865788✍🏻
[5/8, 6:48 PM] khaleesat Haiydar 📚✍️: ✨ ✨HALYSAAH✨✨
By _Khaleesat Haiydar_✍🏻
11.....
Tun da gari ya waye Khaleesat ta kira Safiyyah tace mata bazata shigo school ba don tana son tayi bacci, Safiyyah tasan sarai bata yi baccin kirki ba kenan daren jiya, har mamakin yanda Khaleesat ta iya saka abu a rai ya dameta take, Safiyyah tace "Shikenan kawata, after our classes zan zo ko da yamma ne in sha Allah" a hankali Khaleesat tace "To Allah ya kai mu, Nagode" Daga haka suka yi sallama ta ajiye wayar ta koma ta kwanta. Wajen karfe hudu na yamma Khaleesat ta tashi daga baccin da take, bandaki ta shiga ta wanke baki sannan tayi wanka ta dauro alwala ta fito, tun wayewar gari babu abinda ta ci har zuwa sannan, rabonta da abincin kirki zae yi kwana uku yau tun dai faruwar incident din few days ago, bayan ta idar da sallah ta shirya cikin kaya marasu nauyi ta fito parlor ta tafi kitchen ta hada shayi kawai sannan ta koma dakinta, laptop dinta ta jawo ta kunna zata saka movie ko zata ɗan samu nutsuwar abubuwan dake damun ta a rai ta hanyar kallon film, daga karshe ma ta fasa kallon ta dauko takardunta ta fara karatu, nan ma taji bata fahimtar komai a karatun, rufe takardan tayi ta kwantar da kanta gefen gado ta lumshe ido with different thoughts running her mind, it's not as if she is disturb don Abdul bai daga kiranta ba ko bai kirata ba, kawai dai bata ma san abinda ke damunta bane in particular, bayan lokaci me tsawo ta sauke ajiyar zuciya ta bude idonta ta jawo wayarta ta bude WhatsApp, status taga Abdul yayi updating few hours ago, ta bude hoton da yasa taga har ya ma koma Nigeria cause a field din kwallo yayi hoton da abokansa dukkansu sanye da jersey, ko kadan bata yi mamakin komawarsa Nigeria ba don zai ma iya abinda yafi hakan, da taji shiru har kwana uku dama ta zargi ya koma, dai dai nan taji an bude dakin that is opposite her's, sosai gabanta ya fadi don tun ranan sae yau Housemate din nata ya zo gidan, ta kalli agogon wayarta taga karfe biyar har ya gota, ta ajiye wayar ta dago kanta, tana ta zaune har bayan 15 mins da shigarsa daki sai kuma ta mike tsaye tana jin jikinta ba karfi ta dau gyalenta tana tafiya a hankali ta nufi kofarta ta bude ta fito corridor, sai kallon kofar dakin nasa take gabanta na faduwa, ta rasa courage din karasawa bakin kofar, she stood der for some minutes daga karshe ta lumshe ido ta bude tana tafiya slowly ta isa bakin kofar nasa ta tsaya, ta kai hannu tayi knocking a hankali kamar tana tsoron kofar, komawa gefe tayi kamar mara gaskiya waiting for his response, jin shiru bai amsa ba ta sake knocking din a hankali, ta jira for like a minute again taga dai ba a amsa ba, babu abinda yayi crossing mind dinta sai ko yana bacci ne, but bacci da yamma haka? handle din kofar ta kai hannu gently without thinking twice ta bude kofar tana kallon cikin dakin with throbbing heart, a edge din gadon dakin ta gansa a duke yana operating laptop dinsa da alamar abinda bai gama ba ranan da ya bar gidan yake karasawa, ya daga kai ya kalleta sai kuma ya ci gaba da abinda yake yi, she felt really really bad, ashe yana ma jin tana knocking din, da tasan yana ji ya kyaleta da bazata fara bude kofar dakin nasa ba, ya mike tsaye yace "Good evening Halysaah" Taki amsawa kuma taki yarda ta kallesa, da kyar tace "Dama kana ji kaki amsawa?" Har muryarta ya fara rawa, ya ɗan bude ido yace "To na sani ko saurayinki ne Halysaah?" Nan da nan hawaye ya cika idonta ta juya ta bar bakin kofar ta kullo masa dakin ta koma nata, dukawa yayi ya ci gaba da abinda yake yi a laptop, tana komawa daki ta fara kukan da bata san dalilinsa ba, she felt really hurt kuma tayi da ta sanin zuwa dakin nasa, tana nan a yanda take har shidda saura sannan taji yayi knocking kofar dakinta gently, daga kai tayi tana kallon kofar sai kuma ta hade rai, lkci daya ya bude kofar tare da sallama, sai dai daga nan bakin kofar ya tsaya yana kallonta yace "I was trying to finish a power point Housemate, how are you doing?" Ta sauke idonta a takaice tace "It's fine" Yace "Baki je makaranta ba yau?" Ta gyada masa kai looking toward a different direction, yace "Why?" A takaice tace "Ba komai" Yace "Ok, hope everything is okay?" Sai a sannan ta daga kai ta kallesa sai kuma ta dauke kai don kar ma ta fara kukan dake taruwa idonta, bayan like 10 seconds yace "Saurayin da ke maki fada a waya ne guy din nan ko?" Ta kasa cewa komai at first, sai kuma muryarta na rawa tace "Kayi hakuri da abinda ya faru" Ya ɗan buda ido yace "No it's fine Halysaah, ai ba ma abinda ya faru, but where did you know him from?" Tayi shiru ta kasa cewa komai tana share hawayen idonta, yace "I am intruding ko?" Ta girgiza masa kai kawai, yace "Ohk can we talk if you are comfortable Halysaah" She kept mute Kamar me nazari, can kuma a hankali tace "Ohk" yace "Then meet me at the parlor" Daga haka ya juya ya fita, ko da Khaleesat ta fito parlon bata tarda sa ba a ciki, ta zauna kan kujeran parlon tunani iri iri na yawo a kanta har ta rame a kwana ukun nan, bayan some minutes sae gashi ya fito daga kitchen with a cup of coffee, ya karaso cikin parlon ya zauna yana kallonta yace "You look pale Housemate, are you okay? Ko ya maki wani abun ne?" Khaleesat ta daga kai ta kallesa, sai kuma ta girgiza masa kai a hankali tace "He left immediately u left too" Yace "Oh really? That's weird" Ita dai tayi shiru, ya ɗan yi murmushi ya ajiye coffee din hannunsa yace "Amma baki ci abinci ba" Nan ma tayi shiru tana kallonsa, yace "Naga kamar its been a while da kika yi girki a kitchen, so me kike ci a gidan?" Ta sauke idonta, he could see tana cikin damuwa sosai, yace "Tun ranan da ya tafi bai dawo ba kenan?" Tace "Um" Ya kalli agogon wrist dinsa yace "Do u mind me taking u out for dinner?" Kallonsa Khaleesat take babu ko kiftawa kuma bata ce komai ba, ya mike yace "Get ready, let me get my car key" Yana fadin haka ya mike ya tafi dakinsa ta bi sa da ido, Khaleesat ta fi minti uku zaune parlon tana contemplating on weather to go out with him or not, what if Abdul bai bar kasan ba kawai old picture yayi uploading a status dinsa? The thought of this sent her quivers all over, Tana cikin wannan tunanin sai gashi ya fito daga dakinsa, yana shigowa parlor ta mike ba tare da ta bari sun hada ido ba ta wuce dakinta, canza kaya tayi ta dau veil dinta ta yafa sannan ta zauna gefen gado tana tunane tunane iri iri, bayan 15 mins da shigowarta dakin taji yayi knocking yace "Baki shirya ba Halysaah?" A hankali ta mike ta dau wayarta ta nufi kofa ta bude ta fita, ta samesa har ya koma parlor yana jiranta, tana isowa parlon yana kallonta yace "Where u contemplating inside the room?" Bata san sanda ta dan yi murmushi ba bata dai ce masa komai ba, yace "To mu je, this is after 6 already" Shi ya fara nufar kofar fita living room din sannan ta bi bayansa, yana tsaye bakin kofar bayan ya fita ya jira har ta fito daga parlon sannan ya kulle kofar yana kallonta yace "Why this much Deodorant Housemate?" Ta wani kallesa tace "Ni nace maka na sa?" Bai bata amsa ba ya nufi garage tana biye da shi a hankali, ita dai bata sa turare yanzu ba sai tun wanda ta saka da tayi wanka daxu, sai in ko kamshin kayanta yaji amma ba dai ita ba, bude mata motar yayi tun bata karaso ba sannan ya zaga ya shiga motar yana jiranta, bayan ta shiga suka bar Garage din, wani babban restaurant sananne ya kai ta a Baltimore, bayan yayi parking ta dinga kallon restaurant din da ta ga an rubuta The Capital Grille, sai da ya fara sauka daga motar sannan ita ma ta sauka, tana biye da shi suka shiga ciki, shi yayi offering dinta seat bayan ta zauna shi ma ya zauna ya dau food Menu dake saman table yana nuna mata na kusa da ita yace "Ki duba abinda za ki ci" Ita dai bata dau Menu din ba, yace "I am talking Halysaah" Without looking at him tace "Ko ma meye zan ci" Yace "Ohk" Tana danna wayarta yayi masu ordering abincin, mamaki Khaleesat ta dinga yi ganin amount of different type of foods that he ordered kamar za ayi karamin feast a wajen, abinci kuma masu tsadan gaske, da yawa cikin abincin da aka kawo masu sai a ranan ta fara ganinsu, duk da dai abincin turawa ne, drink ma ya kusa kala hudu ya siya masu, ta daga kai ta kallesa a karo na farko tace "Su waye za su cinye duk wannan?" Orange Crush ya dauka yana sha bai ce mata komai ba, after a while ganin bata fara cin abincin ba shi kuma sai cin abinda zai ci yake ya daga kai ya kalleta yace "Ko babu abinda kike so a nan ne?" A hankali ta dau Tacos daya, shi ko ya ci gaba da cin abincinsa, ƙasa ƙasa Khaleesat take kallonsa, ta lura yanda baya wasa da bacci haka baya wasa da abinci, because he didn't even mind she was in front of him abincinsa kawai yake ci sosai, ganin ko kallonta baya yi ta abincin gabansa kawai yake yasa ta ɗan saki jiki kadan ta fara cin abincin duk da ba sosai ba, ta ci iya abinda zata iya ci ta dau drink tana sha a hankali, sai a sannan ya daga kai ya kalleta after almost finishing his food yace "Ko dai a maki packaging abincin ki ci a gida, naga kamar kina kunyan ki ci abinci cikin mutane, or should i give u privacy?" Tana kallonsa a hankali tace "Privacy in an open restaurant? Ni nace ina kunyan in ci abincin?" Ya ɗan bude ido yace "Naga u ate just the Tacos bayan ga abinci da yawa a gabanki" Ta sauke idonta tace "Nafi son sa ne" Yana goge lips dinsa da tissue alamar ya koshi yace "Ohk, so now can i talk to you?" Shiru tayi na few seconds, sai kuma ta kallesa a hankali tace "Ohk" Ya karasa shanye drink dinsa yace "A nan America kika hadu da saurayin naki ko a Nigeria?" Khaleesat was silent, sai kuma ta sauke idonta tace "Nigeria" Yace "Ohk, but me kike tunanin yake janyo maku matsala tsakaninku?" Ta girgiza kai tace "Nima ban sani ba" Yace "Saboda ke ya taho nan daga Nigeria or he have a business here?" Ta gyada masa kai tace "Saboda ni ya zo" ya gyara zama yace "Kinga yana sonki kenan, sosai ma kuwa yake sonki, he left everything he was doing and came over just to see you, in na fahimta bai son kiyi sharing apartment da namiji a kasar nan ko?" Ita dai Khaleesat bata ce komai ba tana wasa da gefen mayafinta, yace "Sure... yana da gaskiyarsa, don ko ni bazan bar budurwata tayi communal living ba" Khaleesat ta daga kai ta kallesa, Yace "Yanzu dai kiyi kokari ki basa hakuri ku dai daita kanku, ni kuma i will think of another alternative for peace to reign between u and ur boyfriend, sannan shawaran da zan baki shine try all possible best ki dinga nuna masa abinda baza ki yi tolerating ba tun kafin kuyi aure, ya kamata ace akwai mutual understanding tsakanin ku, he look cool though kawai yana da hot temper ne and i notice insecurity na daya daga cikin matsalarku da shi, but you can definitely change him gradually Halysaah, so last maganar da zan maki ina ga ba abinda ya shafeni bane, kawai dai zan tunatar da ke Do's and don't din addininki ta bangaren relationship tsakanin mace da namiji" Khaleesat dai sauraronsa kawai take without looking at him, kuma taki ce masa komai tana kokarin fahimtar abinda zancensa na karshe ke nufi, shirun da taji yayi yasa ta daga manyan idanuwanta ta kallesa, at the same time ta kalli wa enda yake kallo a cikin restaurant din, 3 Guys ne suka shigo restaurant din gaba dayansu yan Africa, amma daya ne ɗan Nigeria a cikin su, guys din da ba yan Nigeria ba suka daga ma Housemate din nata hannu alamar girmamawa, and he waved back at them with smile on his face, Khaleesat ta dinga kallon daya mutumin da ya nufo su don ta ma ganesa, su sauran biyun kuma suka tafi yin abinda ya kawo su restaurant din, Mutumin na isowa kusa da table dinsu yana kallon Housemate dinta yace "Done with the power point?" Tuni kamshin turarensa ya cika wajen, Housemate dinta ya daga kai ya kallesa yace "Yau kuma har da kai za a ci abinci a nan kenan...." Yace "Not at all, i am getting some Steak for legend, meanwhile ashe kana nan" Housemate dinta yace "Yea, i came with my friend for Dinner" Khaleesat dai danna wayarta kawai take don mutumin yi yayi kamar bai san da Allah yayi ruwanta a wajen ba, ita ma ko kallon direction dinsa bata yi ba, Housemate dinta ya nuna masa bill dinsu yace "Get the bill cleared" juyawa mutumin yayi ya bar wajen yana tafiya irin ta ƙasaita, Khaleesat ta bi sa da kallon gefen ido, he was wearing a Jogger and a white Polo, ta dai ci gaba da danna wayarta, muryar Housemate dinta taji yace "That's my gee Halysaah, we share the same name with him...." Khaleesat ta daga kai without interest tace "Ohk" Yace "Sorry about his attitude, he isn't friendly, but i promise you he is good" Khaleesat tace "Likewise myself" Murmushi housemate dinta yayi sannan yayi excusing kansa ya mike ya nufi gun wanda ya kira da gee dinsa, daga inda take zaune taji mutumin na cewa "Kai kuma ina ka samo waccan yarinyar dake zaune kamar gunki bata iya gaisuwa ba, duk wani harkar raini ka iya ja ma mutane, that was how the other day da ka kawota karfe ukun dare a mota ta dinga kallon mutane kamar statue da aka dasa a gaban motar" Definitely yayi maganar ne ta yanda zata ji, Housemate dinta dake kallonsa yace "Ban gane bata
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 9 Chapter of 16