Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
laptop taki tashi, ta gefen ido ta kallesa ganin ya mike daga inda yake zaune, taga sallan isha zai yi, sai da ya idar sannan ita ma ta tashi ta tafi tayi sallan, nan ma babu kalan addu'ar dabata yi ba kan Allah ya taɓa zuciyarsa ya koma hotel dinsa, after a while ta mike ta dauke darduman ta linke ta ajiye, ya mike ya kamo hannunta yana kallonta yace "Why are you uncomfortable kamar kina tare da stranger a gidan nan ne Khaleesat?" Tayi dariyar yake tace "Stranger kuma Ya Abdul? Ai kai ba stranger bane, kai yayana ne, kuma da ai ka sha kwana gidan nan farkon da na zo kasar, kana kwanciya a parlor ni kuma in kwanta a daki" Yace "Kinsan da haka kike dari dari?" Ta sunkuyar da kanta ganin kallon da yake mata, zuciyarta ya dinga bugawa, har ji take kafafuwanta suna neman kasa daukarta, ya matso da ita dab da shi har tana iya jiyo breathing dinsa, calmly yace "Kinsan menene yasa nake kwanciya a parlor a sannan?" Ta girgiza masa kai without looking at him don she is soo uncomfortable with him drawing her closer to himself, yayi kasa da murya yace "Saboda u were still a baby sannan" Ta daga idanuwanta da kyar ta kallesa amma ta kasa cewa komai, yace "Yanzu kuwa ke ba baby bace, how old are you?" Ta kasa basa amsa, ya ɗan mata tsawa yace "Tambayarki nake?" Ta hadiye wani abu da kyar tace "I am 20" yace "To a sannan ina keeping distance between us because i was still grooming you" Ta kauda kai seeing how closer he was coming to her, juyo da kanta yayi yace "Meye haka?" Muryarta na rawa tace "This is against the teaching of islam Ya Abdul, ni ba muharramarka bace" Yace "Oh really? Dama wani ne zai aure ki ba ni ba ashe?" Ta kasa ce masa komai lkci daya hawaye ya cika idonta, duk tsiyar da yake mata da yaga hawaye idonta yake calming down, ya jawota jikinsa yayi kasa da murya yace "Kin zata ke irin matan da zan yi using inyi dumping ne Khaleesat? You are diff from them, ke matar da zan aura ce" Ta kasa basa amsa hawaye na zuba idonta, ita kanta tasan Abdul so na aure yake mata, a shekarun da suka yi tare iyaka yakama mata hannu babu dadi babu kari, amma daga 2 years back labarin ya sauya har bata son ya zo inda take don sai ya mata wasu abubuwa dake damunta, in ya tafi ta sha kukanta kuma ta kan yi kwana da kwanaki bata dawo dai dai ba, amma bai taɓa attempting saninta ba, muryarsa ne ya dawo da ita daga tunanin da ta tafi, as if whispering yace "I have tried Khaleesat, i abstained from doing anything that will distabilize you all this years because i want you to have the best education ta yanda zan iya nuna ki a ko ina as my wife, amma kullum ina jin urge dinki a raina I've tried so many times to ignore the urge, but menene ya rage yanzu? You have just a year and few months to round up, aurenmu kuma ko yau aka ce a daura babu abinda zai hana daurasa, i came all the way from Nigeria because all this days my feeling for you is distabilizing me and making me go nut Khaleesat, so now trust me, relax and keep calm pls baby gal" Khaleesat ta dade bata shiga tashin hankalin da ta shiga a sannan ba, don sarai ta fahimci inda maganarsa ya dosa, kuma lkci daya yake magana yana cire mata hijab din jikinta, common ya taɓa ta idan taki ta karfi yake yi mata balle wnn, gashi gaba daya yanayinsa ya canza alamar ya fara fita hankalinsa ma, ta kamo hannunsa jikinta na rawa tace "But kwanakin da suka rage ai basu da yawa ko Ya Abdul, why not be patient pls..." Ya kalleta da idanuwansa da suka kada strictly yace "I can't wait any longer" Muryarsa kadai sai da ya tsoratata hakan yasa tayi gum da bakinta, tana jin zuciyarta kamar zai fito daga kirjinta tsabar tashin hankali, kafin ya rabata da kayanta tayi kasa da murya still holding his right hand tace "Ohk pls ka bari inyi wanka tukun, kai ma ai ka yi" Ya dinga kallonta da idonsa da suka yi ja, ta sunkuyar da kanta trying to control herself kar ta fashe da kuka tace "I won't take long" Saketa yayi ya koma gefen gado ya zauna, tana tafiya da kyar ta nufi bandaki tana kallon wayarta dake gaban dressing mirror, ta ɗan kallesa, taga bin ta yayi da kallo, ta dake da kyar tace "Zan dau shower gel dina" Gaban mirror dinta ta nufa, dai dai sanda ya fara cire rigar jikinsa da sauri ta dau wayarta da wani Container din lotion da tayi pretending shower gel ne sannan ta shige bandaki ta kulle kofa, tap ta bude jikinta na rawa hawaye na sauka idonta ta fara dialing number Salem, yana fara ring ya daga, da kyar tace "Plss i want to speak to my Housemate plss" Salem yace "Oops wllhi bama tare yanxu" Ko rufe baki bai yi ba tace "Don girman Allah ka turo min lambarsa yanzu" Yace "Ohk let me send you" Yana katse wayar ta dinga kallon screen dinta tana jiran shigowar lambar Housemate dinta, her body was just shaking, ga wani bugawa da zuciyarta yake, cikin few seconds sai gashi ya turo mata lambar, da sauri tayi dialing ya fara ringing amma har ya katse bai daga ba, ta sake kira nan ma bai daga ba, sau uku tana kiransa bai daga ba, ta saki kuka ta durkusa kasan bandakin tace "Na shiga uku" Sake dialing number Salem tayi, yana picking tace "Pls bai daga ba ko zaka..." Salem bai jira jin sauran bayaninta ba yace "Bari in tura maki number Ajay, nasan dama ba lallai Jay ya daga ba don ba ko wani kira yake dauka ba, sai kice ma Ajay ya basa suna tare yanzu" Tana gyada kai da sauri tace "Ohk to Nagode" yana katse wayar sai gashi ya turo mata number Ajay, tayi dialing number da sauri hannunta na rawa, ai kuwa yana fara ringing da few seconds aka daga, da kyar tace "Plsss ina son zan yi magana da Housemate dina ne" Shiru taji yayi as if processing the voice, sai kuma a takaice yace "Waye wannan?" Ta fara shesshekar kuka muryarta na rawa tace "Don Allah kayi hakuri ka rufa min asiri ka basa ina son zan masa magana" Yace "Me ya faru?" Cikin kuka tace "I need his help plss" katse wayar taji yayi, hankalinta in yayi dubu ya tashi a moment din nan, ta shiga uku ta lalace, yanzu ya zata yi, ko dai ta kira Safiyyah, number Safiyyah ta duba da sauri tayi dialing amma har ya katse bata daga ba, ji tayi kamar za a bude kofar bandakin tayi saurin tsoma wayar hannunta cikin ruwan da ta fara tarawa a bath tub a gigice, ashe kunnenta ne ma yaji kamar an taɓa kofa amma ba kowa gun kofar, ta ciro wayarta taga screen din yayi baƙi, ta dinga yarfe ruwan da ya shiga tana kokarin kunnawa amma yaki kunnuwa, hade kanta tayi da bath tub hawaye masu zafi na sauka idonta.... *End of free pages, za mu ci gaba da update a payment group* *For continuation of the book Halysaah, pay 500 into 3276052019 Fcmb Hauwa Bello Jiddah* _And ur evidence of payment via 07087865788_✍🏻 An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels

Chapter 16 of 16