Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
sanyi ya kawo maki mafita" a hankali Khaleesat tace "Ki tashi mu je aji" Safiyyah tace "Oh baza ki ce Ameen ba??" Murmushi Khaleesat tayi tace "Wani mafita kenan Safiyyah? Cewa zaki yi Allah ya canza min halayyarsa kawai...." Safiyyah ta tabe baki ta mike tace "Mu je" Khaleesat ta mike suka bar wajen a tare... Khaleesat na sauka Uber din da ya dawo da ita gida ta nufi apartment dinta, dai dai sanda Co-tenant dinta ya fito daga cikin motarsa dake inda aka tanadar domin parking, sau daya ta kallesa ta dauke kai tana ci gaba da tafiyarta toward their apartment, ya bi bayanta yace "I've waited all day long, i forgot some paperwork a cikin gidan gashi zanyi Submitting tun daxu" Ba tare da ta juyo ba tana ci gaba da tafiya tace "Serves you right" Kallonta yake yana biye da ita, ta ciro makulli a jakarta ta bude kofar ta zare makullinta sannan tayi shigewarta ciki ta nufi dakinta da makullin... Bayan Khaleesat ta idar da sallah ta sauya kaya ta fito parlor don daura girki, bata gansa a parlon ba, kuma bata ji alamar ya shiga dakinsa ba, ta nufi tagar living room din tana leka parking space, ganin babu motarsa ta karasa gun kofa ta murda taji a kulle, kallon inda ta ajiye makullinsa daxu da safe tayi taga ya gani har ya dauke, wucewarta tayi zuwa kitchen. Wajen karfe tara na dare Khaleesat ta gama karatun da take ta jawo wayarta ta bude WhatsApp dinta don ganin ko Neighbor dinsu Aunty Sha'awa tayi replying sakon da ta tura mata amma sai taga bata yi reply ba har sannan kuma ta bude message din, ajiye wayar tayi ta mike ta dauke darduman da take zaune kai, ta dau hijab ta saka sannan ta fito parlor zata debi abinci, Zaune taga House mate dinta a parlon yana operating laptop dinsa, without looking at him ta tafi kitchen, after some minutes ta fito, ya daga kai yana dubanta yace "Can i have some of ur food if you don't mind?" Mamaki ma ya bata, har da baza ta tanka sa ba sai kuma ta tsaya tace "Duk na baya da kake diba gaya min kake halan?" Ya ɗan buda ido yana gyada kai yace "Haka ne kuma fa, i just decided to ask politely today" Bata sake bi ta kansa ba tayi tafiyar ta daki, in har sai tace ya diba to ashe bazai ci ba. Washegari da safe Khaleesat na kitchen tana ma kanta snacks da zata kai school don har yamma suke da Lecture gashi suna da er jarabawan da za su yi ranan da safen, Housemate dinta ne ya shigo parlon, tun jiya da daddare da ya fita sai a sannan ya dawo gidan, har zai tafi dakinsa sai kuma ya tsaya yana kallon Handbag dinta da makulli dake ajiye gefen jakar, karasawa yayi ya dau makullin sannan ya juya ya fice daga parlon gaba daya closing the door gently ya kulle da key, Khaleesat tafi minti sha biyar tana duba makullinta bayan ta fito daga kitchen, tun daga dakinta har parlor zuwa kitchen babu inda bata duba ba amma bata ga alamar makullin ba, she can't even tell ko ta fito da shi parlor, she was so confuse gashi tayi latti, daki ta koma sai da ta birkice ko ina amma babu alamar makullin, how comes will her keys disappear just like that, tunda ta fara karatu a kasar bata taɓa misplacing makulli ba banda wani lkci da Safiyyah ta yar mata guda daya, ko gyara dakin da ta birkita bata yi ba ta dawo parlor looking so frustrated, tsaye tayi trying to calm her brain ko Allah zai sa ta tuna inda ta ajiye keys din, ta ɗaga kai da sauri tana kallon kofar parlon jin ana budewa, House mate dinta ne ya shigo living room din da wasu takardu a hannunsa, sai da ya kulle kofar ya zare makullinsa sannan ya karasa cikin living room din ya ajiye takardunsa kan kujera without looking at her yace "Good morning Housemate...." Bai tsaya yaji amsarta ba yayi wucewarsa daki yana cire jacket din jikinsa, Khaleesat ta bi sa da kallo har ya shige daki ya kulle, zaunawa tayi gefen kujera ta dafe kanta da taji har ya fara ciwo, yanzu ina ta jefar da mukullin nan for God sake gashi lokaci na ta wucewa, after few minutes sai gashi ya sake dawowa parlon, har sannan bai yarda ya kalli direction dinta ba, taga yayi wucewarsa kitchen ya fito rike da ruwan gora ya sake komawa dakinsa ya kulle, wayarta dake jaka ne ya fara ring ta bude jakar ta ciro wayar taga Safiyyah ce, dagawa tayi ta kai kunne Safiyyah tace "Ya baki shigo schl ba har yanzu, duk latti na yau na riga ki shigowa makaranta, ko kin manta muna da test ne" Khaleesat ta sauke ajiyar zuciya tace "Ina sane Safiyyah" Safiyyah tace "Na fa ce akwai tutorial da zaki min kafin mu shiga test din" a hankali Khaleesat tace "Zan taho yanzu" Safiyyah tace "Don Allah ki taho, wallahi ba abinda na sani a course din kema kin sani" Khaleesat ta ajiye wayar bayan Safiyyah ta katse, agogon wayarta ta kafa ma ido, bayan wasu yan mintuna ta mike after gathering courage to do what her mind is telling her, walking slowly ta nufi dakinsa, tsaye tayi tana facing kofar, a hankali ta kai hannu kofar tayi knocking tana turo baki, Yana jin knocking din ya kalli kofarsa, gyada kai yayi letting out a grin, sai da ta sake knocking din sannan yace "Waye wannan?" Exactly yanda take yawan fada, Shiru tayi bata ce komai ba ta kara turo baki, ya mike ya tafi gun kofar ya bude yana kallonta daga sama har kasa da alamar mamaki, tuni ta kauda kai, still keeping a surprise face yace "Madam hope nothing??" Trying to sound a little polite tace "I need you to open the door for me" ya gyara tsayuwa yace "I don't understand, dama a hade makullinmu suke? Where is ur key?" A takaice tace "It's fine, no long talk" Juyawa tayi zata bar wajen, yace "Ko baki ga naki bane?" Ta wani kallesa tace "Banda haka ai da ban zo nan nace ka bude min kofa ba" Yace "Ohh i see, does this mean u are careless too?" Barin wajen tayi ta koma parlor ta zauna, ya gyada kai with smile of satisfaction sannan ya koma daki ya dauko makullinsa ya fito, sai da ya shigo parlon yace "Ta yaya ma zaki yi misplacing a whole bunch of key sai kace allura, this is kind of weird" Daukar handbag dinta tayi ta nufi kofar yana budewa ta fice daga parlon tayi wucewarta without turning her back, ya gyada kai yace "Zaki dawo ai, zan ga ta inda zaki shigo gidan" Kulle kofar parlon yayi still smiling, ko ba komai ya rama abinda ta masa jiya. Safiyyah na kallon Khaleesat tace "To ko ya shige cikin Couch ne makullin?" Khaleesat tace "Ta yaya zai shiga kujera?" Safiyyah tace "Kuma har kitchen din kin duba?" Khaleesat tace "Babu inda ban duba ba fa" Safiyyah tace "Toh kawai kiyi ma agent din gidan magana su baki wani makullin mana" Khaleesat tace "Gani nake kamar dogon process ne hakan, kuma ai biyu ne makullin kika yar min da daya shine na dauko spare key din nake using, to shima gashi ban gansa ba yanzu" Safiyyah tace "Kar ki wani damu kanki, makullin na nan zaki gansa, kawai kin mance inda kika jefar ne, amma definitely it's either in ur room ko kuma parlor, yanzu jira zaki yi sai sanda housemate dinki ya dawo ki koma gidan kenan?" Khaleesat tace "Wani housemate? Shi da ba kwana ma yake a gidan ba, kuma ba shi da exact time da yake zuwa" Safiyyah tace "Kai haba, to a ina yake kwana?" Khaleesat ta zaro ido tace "Kin ji ki da wani tambaya, ta yaya ni kuma zan sani? what is my business with him da zan san inda yake kwana" Safiyyah tace "To kawai mu je gidanmu ki kwana" Khaleesat tace "Kina ganin babu matsala hakan?" Safiyyah tace "Wani irin matsala? To gidanta ne ko na ubanta da za a samu matsala? ta shi mu tafi jare" Safiyyah na gaba Khaleesat na biye da ita a baya suka shigo parlor da sallama, Surayya matar cousin brother din Safiyyah dake zaune parlorn ta daga kai tana kallonsu, Safiyyah tace "Sannu da gida Mom Aslam" Surayya ta ci gaba da danna wayar hannunta tace "Yauwa" Khaleesat ta zauna kan kujera ta gaisheta, Surayya ta amsa without looking at her tana danna wayarta, Safiyyah tace "Ai kin ganeta Mom Aslam, kawata ce kuma Coursemate dita Khaleesat" Surayya tace "Ohk" Safiyyah tace "She will be passing the night here, makullinta ne ya ɓata" Surayya ta daga wayarta da ya fara ring ta kai kunne hade da amsa sallama ta mike ta bar masu parlon, Safiyyah ta kalli Khaleesat tace "Tashi mu je ciki" Mikewa Khaleesat tayi ta bi bayan Safiyyah zuwa dakinta, Safiyyah na idar da sallah ta canza kayan jikinta tana kallon Khaleesat dake zaune saman darduma tace "Bari in samar mana abinda za mu ci a kitchen" Kai kawai Khaleesat ta gyada mata, Safiyyah ta fita daga dakin... Khaleesat was so uncomfortable a gidan cause it's a home that she is not welcome, ko daga irin tarban da aka mata tasan she isn't welcome, karatun da take ta yi na boko ne ke while din mata lokaci, Safiyyah kuwa tun da suka ci abinci take ta bacci har yanzu da magrib yayi, Khaleesat tayi alwala sannan ta fito ta tasheta, bayan sun idar da sallah Safiyyah tace "Bari in je in ga me waccan matar ta girka" Ita dai Khaleesat bata ce komai ba tana ci gaba da azkar dinta, Safiyyah ta fita daga parlon, Surayya na parlor tana ba yaronta Cereal da ta hada masa, Safiyyah ta karasa parlon tace "Aslam yanzu ya tashi ne, ban gansa tun daxu ba" Surayya tace "Ehh" Safiyyah ta ɗan masa wasa sannan ta wuce kitchen, abinci ne iya cikinta taga Surayya ta ajiye mata a kitchen din, Safiyyah ta fi minti biyu tsaye kitchen din tana kallon abincin, can tayi kwafa ta dau plate ta juye ma Khaleesat kawai ita idan ya so ko cornflakes ne sai ta sha anjima, ta fito kitchen din kenan sai ga Cousin brother dinta ya shigo parlor, gaishesa tayi ta amshi ledan hannunsa yace "Leave it, kije ki ci abincin ki" Tace "Ai ba nawa bane ba ma, kawata zan kai ma, ni sai dai in sha cornflakes tunda abincin iya wannan ya rage" Surayya dai kallonta kawai take, Musty yace "Wace kawarki?" Safiyyah tace "Khaleesat, she lost her house key shine ta zo zata yi spending night din a nan" Musty yace "Oh Allah sarki, ba ayi abincin da yawa bane?" Safiyyah ta karkace masa plate din sosai tana nuna masa tace "Iyakarsa kenan aka bari a kitchen, tun da rana muka dawo kuma" Musty yace "Ohk, me ku ke son ci let me get it yanzu a restaurant" Safiyyah ta ɗan yi murmushi ta ajiye plate din saman center table kusa da Surayya tace "Bari in tambayi Khaleesar abinda zata ci" Surayya ta bi ta da wani kallo har ta shige daki, Safiyyah na shiga dakin tace "Khaleesat ki fito ku gaisa da yaya Musty nace masa kina nan" Khaleesat ta daga kai ta kalleta tace "Is it necessary Safiyyah?" Safiyyah tace "Ban gane is it necessary ba, yayana ne fa, kuma nace masa kina nan, ai ya kamata ki gaishesa dai ko" Khaleesat tayi shiru, can ta mike suka fito daga dakin tare, tana tsaye daga jikin kujera ta gaida Musty ba tare da ta kallesa sun hada ido ba, ya amsa da fara'a yana kallonta, Surayya dai fuskarta babu yabo babu fallasa take tura ma yaronta Cereal a hanci maimakon baki ba tare da ta sani ba, Khaleesat ce kadai ta lura da hakan, Safiyyah na murmushi ta kalli Khaleesat tace "Wai yaya yace me za mu ci zai fita yanzu ya siyo mana" Khaleesat taki cewa komai, Safiyyah tayi fari da ido ta fara lissafo masa abubuwan da zai siyo masu, Surayya ta ajiye bowl din Cereal din hannunta kan Centre table ta ciro Aslam daga kekensa tace "Mu je in maka wanka Aslam" Daga haka ta bar parlon tayi wucewarta daki, Khaleesat dai ta sunkuyar da kanta, Muryar Musty da taji yana mata magana yasa ta daga kai ta kallesa, yace "Su kenan iya abinda Safiyyah ta lissafo za a siyo maku Khaleesah?" Kai kawai Khaleesat ta gyada masa, bayan nan ta juya ta koma dakin Safiyyah jiki a sanyaye. 07087865788✍🏻 [5/1, 5:20 PM] khaleesat Haiydar 📚✍️: ✨✨ HALYSAAH ✨✨ By _Khaleesat Haiydar_✍🏻 4..... Khaleesat ta zauna gefen gadon dakin Safiyyah duk jikinta a sanyaye, jawo wayarta tayi tana duba agogo taga karfe bakwai har da rabi, sam bata ji zata iya kwana gidan nan ba, tasan probably yanzu House mate dinta na gida, to ya ta iya? Hakan dai zata koma gidan tayi masa knocking, the thought of this made her weak, shigowar Safiyyah dakin yasa ta daga kai, Safiyyah ta rike haɓa tace "Kinsan kuwa shegiyar matar nan bata ajiye mana abinci ba, ai ko sai ga yaya Musty kamar an jefosa kuma night shift fa yake yi wallahi, kinga ko ba komai sai ta hadiyi zuciya ta mutu don bakin ciki yau, abincin da na lissafo masa ko rabinsa baza mu iya ci ba kuma kwalelenta sai dai in har shi yayi dubaran siyo mata nata daban, ban taɓa ganin me tsinannen hali kamar matar nan ba tirr, ni ai na zata in mutum zai taho wata kasar barin baƙin halinsa yake a gida, to ita dai da nata ta taho wallahi" Khaleesat tayi murmushin karfin hali tace "Lallai kam, kinga ni kuma tafiya zan yi fa, da ma bai siyo abincin ba, yanzu Housemate dina ya kirani yace he is back home" Safiyyah ta bude baki da mamaki tana kallonta, can tace "Ban gane ba, yaushe kika samu number Housemate dinki har ya kira ki? Wallahi ban yarda ba kawai so kike ki tafi, bari ki ji in dai don Surayya ce nima fa zaman hakuri nake da ita a gidan nan Khaleesat, mugun halinta bai da part 2, gwara kawai kiyi zamanki in ma shekara zaki yi a nan babu yanda ta iya tunda ba gidan ubanta bane kuma warmly Ya Musty zai yi welcoming din ki" Khaleesat tace "Sophie ni fa tunda Housemate dina ya dawo bazan kwana a gidan nan ba, dama bani da kayan da zan canza sannan na ma manta na bar kaya a washing machine kin ga bani kadai bace a gidan, may be zai yi laundry shi ma" Safiyyah ta hade rai tace "A takaice me kike nufi kenan? Kina ji ina lissafa ma Ya Mustapha abinda zai siyo mana don walakanci ki ce ke zaki tafi? shima ai bazai ji dadi ba idan ya dawo da abincin yaga kin tafi kuma saboda ke ya fita ya siyo don in dan ta nice sai dai yunwan ya kasheni in bai ga dama ba" Khaleesat ta ɗan yi murmushi tace "Zan jira ya dawo, sai in tafi da abincin gida kawai" Safiyyah da har ranta ya ɓaci tayi mata banza ta tafi ta dau wayarta tana dannawa, Khaleesat dai bata sake cewa komai ba, komin fushin Safiyyah ita kam baza ta kwana gidan nan ba, after a while Ya Mustapha ya dawo gidan da abincin da ya siyo masu, Safiyyah ta mike ta nufi kofa bayan ya kirata a waya, Khaleesat ta bi ta da kallo har ta fita sannan tayi murmushi, Safiyyah ta karasa dinning table ta dau abincin da Cousin din nata ya ajiye masu ta koma daki, iya wanda zata ci ta cire ta bar ma Khaleesat duk abincin, Khaleesat tace "Ya zanyi da abincin nan me yawa Sophie?" Ba tare da Safiyyah ta kalleta ba tace "Wannan kuma ke kika sani" Khaleesat bata son jan maganar yayi tsayi kawai ta mike ta dau veil dinta da handbag sannan ta dau ledan abincin tace "Sai mun hadu gobe, thank you so much dear" Safiyyah tace "Kinyi order din ride ne?" Khaleesat tace "Sure" Mikewa Safiyyah tayi suka fito dakin a tare, dai dai fitowar Mustapha parlor shi ma, yana kallonsu da mamaki yace "Ya aka yi kuma?" Safiyyah ta langwabar da kai tace "Her Housemate is back, shine kawai zata tafi gida wai" Yace "Isn't it late?" Safiyyah ta kyabe baki tace "Nima dai haka nace mata" Ya kalli Khaleesat da ta sunkuyar da kanta, yace "Kiyi hakuri ki bari gobe mana Khaleesah, yanzu ai dare yayi...." Khaleesat ta ɗan yi murmushi ta dago kai cikin sanyin murya tace "Akwai abinda nake son zan yi ne idan na koma gida" Mustapha ya daga kafada yace "While, if you insist...." Ta gyada masa kai tace "Nagode" Safiyyah ta wani harare ta, Mustapha yace "Zan koma aiki ne dama, mu je sai inyi dropping din ki ko" Khaleesat bata yi expecting offer din nasa ba, ta ɗan kallesa tace "Na riga nayi order din Lyft ai...." Safiyyah ta mata wani kallo tace "Haka kuma you can cancel it ai ko...." Kasa cewa komai Khaleesat tayi, lkci daya ta zama uncomfortable, Mustapha dai kallonta kawai yake, after few seconds a hankali tace "Ohk" in response to Safiyyah, Kofa Mustapha ya nufa, Safiyyah tayi kasa da murya tana kallonta tace "Ke in zaki saki jiki ki saki jiki, a ko da yaushe sai kin nuna ke er.... Ya ma sunan wannan unguwan naku a kano?" Khaleesat ta dinga kallonta, can ta juya ta nufi kofa tana tafiya slowly, Safiyyah ta fara dariya kasa kasa tace "Good night girlfriend" Ko tankata Khaleesat bata yi ba. Yana zaune cikin motarsa yana jiranta har ta karaso, ta bude gaban motar ta shiga, sai kallon entrance din gidan take tana fatan kar matarsa ta fito ta gansu, ya tada motar suka bar garage din, sai a sannan ta sauke boyayyen ajiyar zuciya tayi fastening seat belt dinta a ranta ta dau alwashin wannan shine zuwanta na karshe gidansu Safiyyah, bayan sun hau saman hanya taji yace "Where do u stay?" Idonta na kan titi ta gaya masa, yace "Co-living kike yi kenan?" Tace "Um" Yace "Menene yasa baki dawo ku zauna gidana tare da Safiyyah ba instead of living alone with a stranger?" Ko rufe baki bai yi ba tace "Ai yawanci ni kadai ce a gidan, my Housemate is not always around" Yace "Ok then" After almost a minute yace "Kema er kano ce?" Tace "Um" Yace "Wani anguwa?" Tayi shiru, sai kuma ta ɗan kallesa ta gefen ido taga kallonta yake at the same time yana tuki, ta sauke idonta kasa ta gaya masa, she is so uncomfortable with him, Yana gyada kai yace "Ohk, i am also from kano, Sharada to be precise" Ita dai tayi shiru bata ce komai ba, cikin minti 13 ya kawota gida, ya juya yana kallonta bayan yayi parking, daukar ledan abincin tayi tace "Nagode sosai, Allah ya saka da alkhairi" Wayarsa taga ya mika mata, ta daga kai ta kallesa, yace "Ki sa min digit dinki sai mu dinga gaisawa, in kina bukatar wani abu kuma feel free to ask me anytime" Khaleesat ta sauke idonta, ita da ta sani babu abinda zai kai ta gidansa yau, da kawai dawowarta tayi ta zauna bakin apartment dinta ta jira har sanda Housemate dinta ya ga daman dawowa ya bude mata kofa, muryarsa ya dawo da ita duniyar tunanin da ta tafi ta daga kai da sauri ta kallesa, bata ma san me yace ba taga dae yana kallonta, da kyar tayi stretching hannu ta amshi wayar ta sa masa digit din nata, yayi dialing, ita dai kanta na kasa, wayarta dake cikin jaka ya fara vibrate, yace "Kiyi saving nawa digit din" Tace "Um" Yace "Good night, take care Khaleesah" Tayi karfin halin cewa "Nagode" Daga haka ta bude motar ta sauka, kallon window din kitchen na apartment dinta tayi ganin wuta a kunne, sannan taga mota a Garage, she felt relieved sanin cewar her Housemate is around, ta zaga zuwa gaban apartment din tana jin sanyi na shigarta sosai don sanyi ya fara shigowa kasar, knocking din kofar parlor tayi gently, sai da ta kwankwasa sau uku sannan taji muryarsa yace "Who is there?" Ta kauda kai a takaice tace "Somebody" Yace "Somebody? I am not expecting somebody this late" Ta wani hade rai tace "Ni ka bude min kofa in shiga gida" Yace "Ke wa zan bude ma kofa?" Kin cewa komai tayi cause she is already provoke, yace "Ohk then, i am going back to my room after all i am not a door keeper" Tana jin haka a fusace tace "Don Allah ka bude min" Yace "Ke wa?" Tace "Ban gane ni wa ba?" Yace "Ohh, tsawa ma kike min?" Ta kara marairaicewa tace "Don Allah ka bude mana" Yace "To ai ni ban san wacece ba, baki da suna ne?" Shiru tayi tana kallon kofar kamar zata fashe da kuka, Yace "Ke zan fa yi tafiyata daki in baza ki fadi sunanki in san wa zan bude ma kofata ba cikin daren nan" Ta sauke idonta kasa, after a few seconds ta dake tace "Khaleesat" Yace "Halysaah..." Wani harara ta zabga ma kofar, Kamar yana counting harufan sunan yace "Ha.. lee...saah" A fusace kamar zata yi kuka tace "Sanyi fa nake ji ka ki bude min kofa, ko don ba kai bane tsaye cikin sanyin?" Bude kofar yayi yace "Baki san da sanyin ba kika je kika yi dare a titi?" Ko kallonsa bata yi ba ta kusa bangajesa ta shige parlon fuskarta a murtuke, yace "Wajen saurayinki kika tafi kenan kika yi dare, naga ma shi ya ajiye ki a mota, Allah sa ba me sa ki kukan nan bane dai" Direct dakinta ta nufa without even looking at him abinda ya fada na sinking zuwa cikin kanta, ya bi ta da kallo yace "Ok.... ga Door keeper dinki ya bude maki kofa ko? Tomorrow is another day, better look for ur lost key in ba so kike ki kwana a waje ba next time" Tuni ta bude kofar dakinta tayi shigewarta ta sa makulli tare da jan dogon tsaki. Da safe tunda Khaleesat ta tashi take zaune tana tunanin how today will be like, taje schl din ne ko ta hakura kawai tunda bata da makulli yanzu, zaro ido tayi bayan ta tuna lecture din da za su yi ranan, she just can't miss that class don course din is a bit complicated, mikewa tayi ta shiga bandaki, wajen karfe tara ta fito parlor hoping house mate dinta bai fita ba, don jiya wajen karfe sha biyu da rabi na dare ta fito don saka abincin da bata iya ta ci ba a fridge ta gansa kwance a parlor yana bacci, har ta gama abinda zata yi a kitchen ta fito bai farka ba, tun zuwansa gidan ranan ne rana na biyu da taga ya kwana a gidan, babu kowa parlorn ta karasa kusa da tagan parlon tana leka Garage ko zata ga motarsa taga motar na nan alamar he is around, ajiyar zuciya ta sauke don da ya fita shkkn babu tafiyarta makaranta kenan, kitchen ta tafi ta hado shayi ta debi cookies ta dawo parlon, har ta gama breakfast bai fito parlor ba, sai kallon agogo take don goma ta kusa gashi bata son tayi latti, kuma ita dai bazata taɓa masa maganar ya bude mata kofa zata fita ba, goma saura minti goma ya fito parlorn, ita dai bata dago kanta ba tana ci gaba da danna wayarta, taji yace "Good Morning, Halysaah" Without looking at him tana ci gaba da danna wayarta kamar tana ma kanta magana tace "Ok" Ta gefen ido ta bi sa da kallo ganin ya nufi kofa ta mike ta bi bayansa, yana lura da

Chapter 3 of 16