which was her wish since yesterday sai taji wani farin cikin da tunda take bata taɓa jin irinsa ba a rayuwarta, 80% a cikin dari na damuwarta ya ragu cikin lokaci kankani, kallon agogo tayi taga sha daya ya wuce sosai, the weakness she is been feeling since this morning immediately vanished, mikewa tayi tana share hawayenta ta dau medium box din kayanta.... Karfe biyu Khaleesat ta gama duk abinda take, har sallan zuhur tayi, Lyft din da tayi ordering kawai take jira, tana zaune gefen gado xuciyarta fal da tunani kala kala, babban burinta a yanzu bai wuce ta ganta kusa da mahaifiyarta ba, in yaso koma me zai faru daga baya sai ya faru, kallon wayarta tayi taga Safiyyah ce ke kiranta, tun daxu da safe ta kirata amma sbda damuwar da take ciki ko picking bata iya tayi ba, Khaleesat ta daga kiran ta kai kunne, Safiyyah tace "Khalee me yasa baki shigo schl ba yau? Are you okay?" Khaleesat ta sauke boyayyen ajiyar zuciya tace "Ummanmu ce bata da lafiya Sophie" Safiyyah tace "Subhanallah, amma ya jikin yanzu?" Khaleesat tace "Da sauki" Safiyyah tace "To Allah ya bata lafiya, plss nasan ki kar ki sa ma kanki damuwa kawata addu'a kawai zaki dinga mata, nasan kilan kina nan kina ta kuka ko?" Khaleesat dai tayi shiru bata ce komai ba, Safiyyah tace "In sha Allah in mun gama lectures zan taho" Khaleesat tace "I am sorry ban kira ki na gaya maki ba i will be leaving for Nigeria by 3pm" Da mamaki Safiyyah tace "Zaki tafi Nigeria? Abdul ne ya siya maki flight ticket?" Khaleesat ta sauke idonta tace "Uhm" Safiyyah tace "Is it that critical Khaleesat?" Khaleesat tace "To da sauki dai, amma kinsan bazan samu rest of mind ba in ban je ba" Safiyyah tace "To kina airport yanzu ne?" Khaleesat tace "Aa ina jiran Lyft ne yanzu zan tafi" Safiyyah tace "Toh shikenan mu hadu a can kawai sai mu yi sallama, bari in nemi Uber nima" Khaleesat tace "To nagode Sophie" Da haka suka gama wayar, Khaleesat ta mike bayan Lyft dinta ya iso, tana rike da trolley dinta da handbag ta fito daga dakin ta kulle kofa, sanye take da Maroon Abaya sai veil dinta, tana tafiya a hankali ta karaso cikin parlorn, ya ajiye wayar da yake yace "Kin shirya?" Without looking at him tace "Eh" yace "Kin yi ordering ride ai?" Tace "Eh" yace "Ohk" Mikewa yayi ya ciro 1000 Dollars ya mika mata yace "Sort ur self out with this" Girgiza masa kai tayi tace "Aa Nagode" Yace "C'mon, u didn't beg me Halysaah" Ƙin kallonsa tayi kuma taki amsan kudin, ya dau handbag dinta da ta ajiye saman trolley din gabanta ya bude zip din jakar ya sa mata kudin tare da wani farin takarda, ta ɗaga kai tana kallonsa, ya koma ya zauna yace "Allah ya tsare, my regards to ur Mom and everyone back home, Allah ya bata lafiya" Da kyar tace "Ameen nagode" Yace "Zaki ga digit na rubuta maki a takarda, idan kun sauka Airport sai ki kira number kice masa kun sauka" Ta kasa cewa komai, after few seconds ta dau handbag dinta cikin sanyin murya tace "Nagode " Yace "U are welcome, wishing u a Safe trip" Tana jan trolley dinta a hankali ta nufi kofa, tana bude kofar ta fita ta daga kai tana kallonsa taga Idonsa na kan wayarsa da yake dannawa, kulle kofar parlon tayi, taga Lyft din dake jiranta ta nufi wajensa. A Airport Khaleesat suka hadu da Safiyyah, Safiyyah na rike da hannunta tace "Tun yaushe ne Umman bata da lafiya?" Khaleesat tace "Jiya Aunty sha'awa ke gaya min" Safiyyah ta sauke ajiyar zuciya tace "To Allah Ubangiji ya bata lafiya" Khaleesat tace "Ameen" Safiyyah tace "Lallai Abdul ya fara hankali da yayi tunanin biya maki jirgi kije ki duba Umma, nayi mamaki sosai wallahi" Khaleesat ta ɗan yi murmushi da iyakarsa lips, Safiyyah tace "Yanzu kwana nawa za ki yi?" Khaleesat tayi shiru at first, sai kuma tace "Sai dai naje tukunna in sha Allah" Safiyyah tace "Toh Allah ya kai ku lafiya, don Allah ki gaida min Umma da jiki" Safiyyah na fadin haka ta jawo handbag din Khaleesat ta saka mata dala dari tace "Plss manage this kawata" Khaleesat ta ɗan bude baki tace "Haba meye haka Sophie" Sophie bata tsaya ta saurareta ba ta daga mata hannu tana murmushi ta bar ta tsaye wajen, Khaleesat dai ta bi ta da kallo. Khaleesat was more than shock bayan ta amshi boarding pass dinta ganin ticket din Business Class ya siya mata, Business class fa? Kikkifta ido tayi ta sake kallon ticket din sosai to confirm, taga Business class din dai ne still, sosai jikinta yayi sanyi, tana jan kafa da kyar ta shiga jirgin, this is the first time she will be traveling Business class, wata Flight Attendant that gave her all the maximum attention ta yi leading dinta har zuwa Seat dinta a cikin jirgin da fara'a tana welcoming dinta, bayan wani ɗan lokaci jirgin ya tashi, Khaleesat ta ajiye Amenity kit da aka bata ko duba abinda ke ciki bata yi ba tana bin ko ina na Business class din da ido, the Flight from Baltimore Washington International to Amsterdam Schiphol Airport in North Holland for Layover was smooth and comfortable, duk zuwanta Amurka bata taɓa tafiya feeling so comfortable like this ba, bayan few hours aka sauya masu jirgi zuwa Nigeria a nan North Holland, Khaleesat tayi shiru da mamaki jin announcement na cewar Lagos Nigeria jirgin ya nufa, ticket dinta ta sake dubawa taga ashe haka ne a jiki, bayan tafiyar kusan awa bakwai jirgin nasu ya sauka a MMI Airport Lagos.
[5/3, 6:15 PM] khaleesat Haiydar 📚✍️: ✨✨HALYSAAH✨✨
By _Khaleesat Haiydar_✍🏻
6.....
Bayan Khaleesat ta dau trolley dinta a cikin airport after going through custom ta tsaya cikin airport din tana tunanin yanda zata yi cause karfe shidda saura ne na asuba, should she check for available flight to Kano? To nawa ne ma a account dinta before she think of doing so, ko dai kawai ta tafi Motor park ta hau mota zuwa kano, dollars din da Housemate dinta ya bata ne ya fado mata a rai don gaba daya ta ma mance, ta bude handbag dinta ta ciro kudin tana kallo, takardan da ya saka mata hade da kudin a jaka ya fadi kasa, ta duka ta dau takardan tana kallon numbers din jiki sai kuma ta mayar cikin jaka tare da Dollars din, masallacin dake cikin Murtala Muhammad International airport ta tafi don yin sallan asuba, tana ta zaune cikin masallacin bayan ta idar da sallah tana azkar dinta, can ta ciro wayarta a handbag ta duba agogo taga karfe bakwai da minti goma, dollars din jakar ta sake cirowa ta kirga taga dala dubu ce, kallon kudin ta dinga yi jiki a sanyaye don bata yi tunanin har haka ya bata ba, ta dau white paper din dake dauke da digit tana tunanin to ko digit dinsa ne wannan din, kati ta siya ta Ussd sannan tayi dialing number a wayarta, sai da ya kusa katsewa aka daga, daga daya side din aka yi sallama ta amsa, amma sai taji kamar ba muryarsa bane, ta dai ce "Ina kwana?" Yace "Hajiya ko kece kika taho daga America?" Tace "Eh" Yace "To barka da isowa Hajiya, ina ta sauraren kiran naki dama tun daxu, kina cikin airport din ne yanzu?" Tace "Eh" Yace "Ohk to gani nan tahowa ba da dadewa ba in sha Allah" Bayan ya katse wayar ta kalli screen dinta, to waye kuma wannan, maida kudin tayi jaka ta ciro nose mask dinta ta saka sannan ta mike ta fito daga Masallacin da trolley dinta with handbag, bayan wasu mintoci sai gashi ya sake kiranta, ta fito outside of the airport, yana hangota ya nufota ya gaisheta da ladabi har da bowing kansa yace "Ya hanya Hajiya?" Ta sauke idonta tace "Lafiya Alhamdulillah" With respect yace "Ga mota can Hajiya, zaki je hotel ki huta zuwa karfe daya na rana don Flight dinki zuwa kano na karfe Biyu ne in sha Allah..." Khaleesat was speechless ta dinga kallonsa babu ko kiftawa cike da mamaki, can kuma ta kalli lafiyayyen motar da ya nuna nata, tuni ya karasa ya amshi trolley dinta ya tafi ya bude booth ya saka, sannan ya bude mata bayan mota yace "Bismillah Hajiya" Sauke idonta tayi kasa taji kafafuwanta sun mata nauyi amma a haka tana tafiya a hankali ta tafi ta shiga back seat sannan ya kulle motar, ya zaga ya shiga driver seat, Hotel me tsada sosai that isn't far away from the airport ya kai ta, sai da ya tabbatar tayi check in har zuwa dakinta sannan ya bar hotel din, tana shiga babu jimawa wata ma'aikaciyar hotel din ta kawo mata lafiyayyen Breakfast, ita dai Khaleesat ba um bare um um, gaba daya kanta ya gama kullewa, tashi tayi ta bude trolley dinta ta dau Shower gel zata yi wanka. Khaleesat na bacci wajen karfe daya da minti ashirin vibration din wayarta ya tasheta, ta jawo wayar a hankali tana duba me kiranta taga mutumin da ya kawota Hotel ne, ta mike zaune sannan tayi picking call din ta kai kunne tayi shiru, daga daya bangaren yayi mata sallama sannan yace "Hajiya fatan kin shirya in taho in dauke ki, flight din naki nan da minti talatin ne in sha Allah" a hankali Khaleesat tace "Toh" Yace "Gani nan tahowa yanzu da izinin Allah" Yana katse wayar Khaleesat ta sauka daga saman gado taje tayi alwala a bandaki, tana idar da sallan Azahar sai ga kiransa, ta dau trolley dinta da handbag ta bar dakin hotel din ta sauko downstairs, yana hangota a Reception din hotel din ya tafi da sauri ya amshi trolley din hannunta, ya karbi makullin dakin ya kai ma Receptionist, sannan suka fita haraban hotel din ya bude mata back seat bayan ya saka trolley dinta a booth, cikin mintuna kadan suka isa MMI Airport, sai da ya tabbatar ta amshi boarding pass dinta sannan yayi mata sallama da murmushi fuskarsa yace "Toh Allah Ubangiji ya tsare Hajiya, idan kun sauka kanon za a karasa dake gida in sha Allah... We will keep in touch" a hankali Khaleesat tace "Toh Nagode, Allah ya saka da alkhairi" Yace "Ameen Hajjaju, nagode kwarai, Allah Ubangiji ya kai ku lafiya" A haka suka rabu ta nufi Departure lounge walking slowly, bayan kusan minti ashirin jirginsu ya tashi zuwa garin kano. Suna sauka kano Khaleesat ta fito daga cikin airport gabanta na faduwa, sai gyara nose mask din fuskarta take tana waige waige, yanzu ina ma ta nufa tukun, tasan ko da wasa bazata nufi gida ba dai, wayarta ya fara ring ta duba da sauri gabanta na ci gaba da faduwa, wata lamba ce ke kiranta tayi picking tayi shiru, taji an mata sallama ta amsa, mutumin ya gaisheta yace "Hajiya Hamisu ne ya aiko min lambarki, naga jirgin ku ya sauka yanzu, yace za a karasa dake gida, kina ta ina yanzu?" Tace "Na fito outside of the airport" Tahowa taga mutumin yayi zuwa inda take tsaye bayan ya hangota, nan ya kai ta har motar dake jiranta, motar shigen wanda ta shiga a Abuja ne, mutumin ya bude mata back seat ta shiga tace "Nagode" Yayi bowing kansa yayi mata sallama yace "Allah ya kai ku lafiya" Tace "Ameen Nagode" Drivern dake mazaunin driver ya gaisheta yana tambayarta ya hanya sannan ya tada motar suka fita daga airport din yace "Ina muka nufa Hajjaju?" Khaleesat ta ɗan yi shiru kamar me nazari, sai kuma tace "Hotoro zaka kai ni" Yace "To Allah ya kai mu lafiya" Suna isa dai dai kofar gidan da ta nuna masa ya tsaya, ya bude motar ya sauka don fiddo mata Trolley dinta a booth, bude motar tayi ita ma ta sauka tana gyara facemask dinta, ta amshi akwatinta a hannunsa sannan tayi masa godiya ta shiga cikin gidan da sauri, Baaba Gaje dake zaune tana tankade garin tuwo ta daga kai tana kallonta, Khaleesat ta ɗan sauke Facemask dinta tana murmushi tace "Baaba sannu da aiki" Baaba Gaje ta ajiye rariyar hannunta tace "Khaleesatu? Daga ina kuma haka?" Khaleesat ta duka nan gabanta har sannan tana ɗan murmushi tace "Makaranta" Baaba Gaje tace "Ikon Allah, to ai ko minti ashirin banyi da dawowa daga gidanku ba kuma ba ace min kina hanya ba" A hankali Khaleesat tace "Baaba ya jikin Ummanmu fa?" Baaba Gaje tace "Kaddai ba a san kin biyo hanya ba kika taho Khaleesatu?" Khaleesat ta gyada mata kai kawai, Baaba Gaje tace "Ikon Allah, to ai jikin nata da sauki er nan, shi Awdul din ne ya biya maki kudin jirgi kika dawo?" Khaleesat ta girgiza kai gabanta na faduwa tace "Bai san na dawo ba Baaba" Baaba Gaje tace "Ikon Allah, to bari in kira Parida, ko kuma ke ki kirata da kanki, Gwara da kika yi dubaran zuwa nan kada Salubabben uban nan naki ya sa ki a bakin duniya mu shiga uku, Ga tabarma taho ki zauna ki huta, irin wannan tafiya me nisa haka, naji ance Amurkan har yapi legas nisa ko? Kira Paridan mu ji yanda za ayi" Khaleesat ta zauna gefenta ta bude handbag ta ciro wayarta, duk da yanda gabanta ke faduwa haka tayi dialing din lambar kanwar Ummanta Aunty Farida, Baaba Gaje tace "Auu to ai Parida ba waya a hannunta wai an sace a mota" Khaleesat ta daga kai tana kallonta, Baaba Gaje tace "Abinda zai faru kawai ga garin tuwon nan ki karasa tankade min ga can murhu na dora ruwan tuwo in yayi ki min talgi ki tuka tuwon in ya silala ki kwashe, ga kuma kayan miya can bai dai da yawa ki jajjaga ki kada min miyar kuka, ni kuma sai in koma can Mariri yanzu in sanar ma Ummanku kin zo" Khaleesat tace "Toh Baaba" Mikewa Baaba Gaje tayi ta figi yakunennen gyalenta a igiyar shanyan dake ɗan karamin tsakar gidan ta yafa tace "Bara inje, dama ina da canjina dari da hansin sai in roke masu ɗan sahu su kai ni ko Farawa ne sai in karasa Maririn da kafa ta" Khaleesat ta bude handbag dinta amma sai taga Dollars kawai, ta daga kai ta kalli Baaba Gaje tace "Wallahi bani da kudin Nigeria a nan Baaba, amma bari in ciro a POS yanzu sai in baki kudin adaidaita sahun" Baaba Gaje tace "Aa yi zamanki kiyi aikin da na sa ki, minti nawa ne nan da Mariri, kawai dai ga wanke wanke can bakin kwararo ki wanke min har su, ki share tsakar gidan nan, in yaran nan suka dawo islamiyya ki dauraye masu Uniform dinsu, dakin ma na nan sunyi kaca kaca da shi babu kyan gani" Daga haka ta fice daga cikin gidan bayan ta saka slippers dinta, Khaleesat ta cire mayafin abayan jikinta ta dora kan akwatinta sannan ta ci gaba da tankaden da Baaba Gaje ta bar mata, Baaba Gaje makociyarsu ce a can unguwansu Mariri kafin 'ya yanta su siya mata wani ɗan kararramin gida a nan Hotoro Tsamiyar boka ta dawo tana zaune da jikokinta biyar tana dubasu, zaman mutunci da amana Baaba Gaje suka yi da Mahaifiyar Khaleesat da ta dauki Gajen tamkar uwa. Wajen karfe shidda saura Khaleesat ta gama duk aikin da Gaje ta loda mata sannan ta dora ruwan da zata yi wanka a sauran rushi, zaunawa tayi kan tabarma ta jingina da bango don ta gaji likis, Housemate dinta ne ya fado mata, ta dai yi shiru staring into space, after a while ta sauke idonta a hankali ta mike ta shiga da kwanukan da ta wanke cikin dakin Gaje, dai dai nan Gaje ta shigo cikin gidan da Aunty Farida, Khaleesat ta tafi da gudu ta rungume Aunty Farida cike da murnan ganinta, Aunty Farida na kallonta tace "Ke kuma da wa kika yi shawara kika biyo hanya Khaleesah? Abdul din ne yace ki taho?" Gaje ta daga hannu sama da sauri tace "Aaaa tace bai ma sani ba" Aunty Farida na kallon Khaleesat da mamaki tace "Ban gane bai sani ba??" Khaleesat ta marairaice ta kauda zancen ta hanyar cewa "Aunty ya jikin Ummanmu?" Aunty Farida ta kamo hannunta suka zauna saman tabarma tace "Ai jikin Umma da sauki sosai Khaleesat, gashi har an sallamemu a asibiti, wa yace maki bata da lafiya ne ma tukun?" Khaleesat da har hawaye ya ciko idonta tace "Aunty Sha'awa" Gaje tace "Lahh ha ila, wato Sha'awa bazata dena munafurci ba ko? Wato bazata canxa hali ba ko? Da kaina fa sai da na jaddada mata kar ta gaya maki ko kin mata sako ta wassol don kar hankalinki ya tashi, ashe sai da munafukar ta zaga ta fada maki" Aunty Farida tace "Toh Allah ya kyauta, kwata kwata Sha'awa bazata canza ba" Khaleesat da hawaye ke cika idonta tace "To Aunty ta yaya zan ga Ummanmu yanzu?" Aunty Farida tace "Kar ki damu kiyi zaman ki nan wajen Baaba Gaje, gobe da safe in za mu tafi asibiti sai mu fara biyowa ta nan da Umman tunda asibitin Malam Aminu kano ne" A hankali Khaleesat tace "Toh Allah ya kai mu Aunty" Sai bayan Magrib Aunty Farida ta bar gidan bayan ta ci tuwon da Khaleesat tayi ma Gaje, sosai Khaleesat taji ta samu rest of mind bayan taji jikin Ummanta da sauki, bayan Isha Gaje ta gyara mata ɗan lungun da zata kwanta a dakin ta daura mata net din sauro tace "Allah dai ya rabaki da cinnaku" ita dai Khaleesat tayi murmushi kawai bata ce komai ba, ita matsalarta ma zafi, ko ya zata yi da zafi yau gashi karamin dakin wani ɗan mitsitsin window ne kawai ke garesa, su bakwai kuma zasu kwana a ciki, Khaleesat ta gama shirin kwanciya don tayi wanka sannan ta shiga net din ta kwanta, ta amshi maficin da gaje ke mika mata ta cikin net din, tun dawowarta sai a sannan tayi subscription ta shiga WhatsApp dinta, Message din Safiyyah dake tambayarta ko ta isa lafiya kadai tayi ma reply, bata yi mamakin rashin ganin message din Abdul ba don she isn't even expecting his message, ajiye wayar tayi ta gyara kwanciyarta ta lumshe ido, Housemate dinta ne ya fado mata, she have no access to him balle ko godiya ma tayi masa, bata yi tunanin da ta fito zata tafi airport bazai tambayeta phone number dinta ba, ko Airport din ma bata yi tunanin bazai yi offering yace zai kai ta ba, juye juye kawai take yi a net din idonta a rufe, after a while of thinking bacci ya dauketa. Washegari Khaleesat ta gama yi ma Baaba Gaje duk aikace aikacen gidan, ta hura gawayi ta daura ruwa tayi ma kananun jikokinta wanka sannan ta dama kunu, Baaba Gaje ta fita siyo masu kosai a titi, har karfe goma Khaleesat bata ga Aunty Farida sun zo gidan da Ummanta ba, gaba daya ta damu taga Ummanta, Baaba Gaje tace "To ke sai ruwan ya salance zaki je kiyi wankan? Ba fa wani gawayin" Khaleesat tace "Zan yi" Daga haka ta mike ta tafi yin wankan, tana fitowa daga wanka taga takalmin da Aunty Farida ta zo da shi jiya a bakin kofa da wani takalmin daban wanda ko ba a fada ba tasan na Ummanta ne, da sauri ta shiga dakin Baaba Gaje taga Ummanta da Aunty Farida a zaune, tsallake Aunty Farida tayi ta tafi gun Ummanta da gudu cike da farin cikin ganinta ta durkusa gabanta ta rungumeta, Aunty Farida tace "Ko dai baki da hankali ne?" Baaba Gaje tace "Toh da sauki dai kam" Ita dai Umman sai kallon Khaleesat take, gaba daya Khaleesat ta ma mance wai Umma bata da lafiya tsabar farin cikin ganinta, a hankali Umma tace "Meyasa zaki biyo hanya Khaleesah? Abdul din ne yace ki dawo?" Khaleesat ta kamo hannunta cike da damuwa tace "Umma ya jikin?" Umma tace "Naji sauki Alhamdulillah" Khaleesat tace "Aunty Sha'awa tace min ko magana fa baki yi" Baaba Gaje ta rike haɓa tace "Oh ni 'ya su, kun ji er iska ko? Wallahi Sha'awa da kyar taga annabi, babu yanda bamu yi da ita ko da wasa kar ta gaya maki ba ashe sai da ta zaga ta fada, har ce mata nayi tace maki tayi tafiya ko da zaki buga nata wassol" Khaleesat ta daga kai ta kalli Baaba Gaje tace "Ni ce na kirata don ina ta magana bata min reply ba" Aunty Farida tace "Ai tsabar munafurci yasa ta gaya maki ba wani abu ba" Khaleesat ta ɗan yi murmushi ta gaida Aunty Farida, Aunty Farida ta amsa tace "Amma shi Abdul yasan Umma bata da lafiya shine ko kira ya dubata bai yi ba?" Khaleesat ta sauke idonta kasa tace "Ni fa bai san na dawo ba Aunty" Aunty Farida tace "Wai ban gane bai san kin dawo ba, wa ya biya maki kudin jirgin?" Khaleesat ta daga manyan idanuwanta tana kallonsu, Sai kuma a hankali tace "Wani ne ya biya min ba Abdul ba" Umma ta kalleta da sauri tace "Wani?" Da mamaki Aunty Farida tace "Wani a ina?" Khaleesat na kokarin mikewa tace "Neighbor dina ne" Umma ta bude baki tana kallonta, sai kuma tace "Ko baki da hankali ne, waye ya biya maki kudin jirgi Khaleesah?" Khaleesat tayi shiru bata ce komai ba, Gaje tace "Bude baki zaki yi ki mana bayani dalla dalla, waye shi zai biya maki zunzurutun kudi na jirgin da naji ance ya fi miliyan daya? A ina kika san sa?" Still dai Khaleesat taki cewa komai, Aunty Farida tace "Ke bana son rainin wayo uban wa zaki ma shiru ana maki magana? Ko baki ji tambayar da ake maki bane?" Umma dai kallon Khaleesat kawai take da mamaki, Khaleesat ta koma baya ta ɗan sunkuyar da kanta a hankali tace "Ni fa nace makocina ne ya biya min, kuma ai gani yayi ina ta kuka Ummana bata da lafiya shine ya biya min jirgi in dawo in dubota" Cikin sanyin murya ta kare maganar, Baaba Gaje tace "Atoh dama ai ko ina ana samun na Allah, Allah ya masa albarka, Bature ne ko?" A takaice Khaleesat tace "Um" don bata son ma a ci gaba da zancen, Baaba Gaje tace "Ko da naji, ai sai baturen dama, wani baƙin fata ne zai biya maki jirgi don yana makocinki, ai ko mutuwa uwar taki tayi iyaka ya maki gaisuwa ya kama gabansa, to Allah ya saka masa da alkhairi, abinda ma baturen kudin jirgin ba wani kudi bane a wajensa, ji zai yi kamar naira dubu goma ya kashe fa" Khaleesat na kallon Aunty Farida tace "Aunty yanzu za aje asibitin ne?" Aunty Farida tace "Aa mu har mun dawo daga asibiti sai kuma na gobe in Allah ya kai mu" a hankali Umma tace "Toh da ya biya maki kudin jirgin zuwa wa zai maki na komawa yanzu? Kinsan dai ko hauka kike baza ki bari Abdul yaji wannan batun ba ki ja mana masifa ko?" Sai da gaban Khaleesat ya fadi, a hankali ta sunkuyar da kanta, ita gaba daya ta ma mance ashe biyan jirgi za ayi a koma, nan da nan jikinta yayi mugun sanyi, yanzu ina zata samu kudin ticket din komawa, she became so weak at once, Aunty Farida tace "Toh shi Abdul din baki ce masa Umma bata da lafiya bane?" Khaleesat da har sannan jikinta yake a sanyaye ta girgiza kai tace "Baya nan ne" Daga haka ta mike ta tafi zata shirya don zanin da tayi wanka ne daure jikinta har a lkcn, Khaleesat na cikin saka kayanta da ta fiddo a akwati 1000 dollar din da Housemate dinta ya bata suka fado mata a rai, ta zaro ido lkci daya taji hankalinta ya kwanta har sai da ta sauke ajiyar zuciya, tasan probably in ta canza har da 100 dollar din da Safiyyah ta bata kudaden za su iya maidata Amurka, she felt
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 5 Chapter of 16