Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ta biyosa sai ya fasa bude kofar, ya juya yana kallonta keeping a serious face yace "Me ya faru?" Ta kauda kai taki cewa komai, mayar da makullin yayi aljihunsa zai bar wajen ta wani kallesa tace "Ni dai ka bude min kofa zan tafi makaranta" Yana gyada kai yace "Ohhh, ohk kin boye makullinki ne don in zama door keeper dinki dama?" Taki kallonsa don bata ma san me zata ce masa ba, ganin da gaske barin wajen zai yi ta marairaice tace "Makaranta zan tafi fa" Ya juyo yace "Be a good girl and beg politely first....." Shiru tayi tana bin sa da kallo har ya koma cikin parlor ya zauna kan kujera, Ta dake da kyar tace "Please ka bude min. i am going to school" Yace "Ban ji ba" Takaici yasa ta dauke kai taji ranta ya kara ɓaci, ganin lokacinta kawai take ɓatawa ta sake juyowa trying to be calm tace "Plss ka bude min kofa i am going to school" Ɗan murmushi yayi ya mike ya dawo bakin kofar ya ciro makullin a aljihunsa yace "Never knew u can be this Obedient" Ita dai bata kallesa ba, ya bude kofar yace "In kika sake yin dare baza ki shigo gidan nan ba sai dai ki kwana bakin ƙofa ko kuma a Garage..." Bata tankasa ba ta fice daga parlon with annoyance almost brushing his shoulders, ya bude baki yana bin ta da kallon mamaki yace "Ohh, is this ur thank you??" Tuni har ta kusa titi abun ta, ta ja tsaki feeling so fed up with him. Bayan Khaleesat sun fito daga aji Safiyyah tace "Kinsan me Khalee?" Khaleesat ta juya ta kalleta, Safiyyah tayi dariya har da kyakyatawa tace "Wai Ya Musty ke tambayata ko kina da saurayi" Sai da gaban Khaleesat ya fadi, Safiyya bata fasa dariyar da take ba tace "Wallahi kuwa, he chatted me up yesternight wajen karfe sha biyu, bari ma in nuna maki ki ga, ni ko nace masa baki da kowa wallahi" Sai a sannan Khaleesat ta kalleta tace "Ban gane bani da kowa ba Sophie?" Safiyyah tace "To kina da shi ne? To in kallon saurayinki kike ma Abdul to ni wallahi kallon ɗan daba nake masa, ni dai nace ma Ya Musty bakya kula kowa saboda karatu don haka baki da saurayi, kema kin dai san da Ya Musty na da mugun hali da tuni na fesa maki ni da bakina baya shiru, ai ko don wannan er banzar matar tasa zan so ya kara aure, kuma ace kawata ya aura huhuhu za a ga rashin nasiha da jahilci wajena" Khaleesat ta mike tana gyara Veil din jikinta tace "Zan tafi gida sai gobe" Safiyyah ta tsuke fuska tace "Ban gane zaki tafi gida ba daga na kawo maki maganar arziki" Khaleesat tace "Wallahi da na sani babu abinda zai sa in bi ki gida jiya Safiyyah, haba fisabilillah, put ur self in the wife's shoe in kece aka ma haka zaki ji dadi?" Safiyyah tace "Godforbid, her shoes will never size me sef kafin in sa kafata ciki Khaleesat, ai ni bani da mugun hali kamar ta, kina ga fa ko tsayawa ta amsa gaisuwarki bata yi ba ta wani ƙara waya a kunne ta wuce daki ita er iska, sannan bari kiji jiya iya cikina ta ajiye abinci a kitchen bayan nace mata nan zaki kwana kuma ta sani, ni dai wallahi in kika ce baki son yayana nice kawai baki so, Ya Musty bai da wani aibu wallahi, ga arziki ga Ilimi ga kyau, baza ma ki ce ya taɓa auren wata er iska ba wai ita Surayya, ɗan saurayi da shi" Khaleesat tace "In matarsa kike son tura ma haushi ai kema zaki iya aurensa tunda he is ur cousin brother kuma da aure tsakanin ku" Daga haka Khaleesat ta bar wajen tayi wucewarta, Safiyyah tace "Oho dai wallahi ce masa zan yi kin amince sai dai ki mutu, haka kawai kin makala ma kanki ɗan daba kina kiransa da wanda zaki aura, ki auresa ki ci uwar me da shi, wannan har duka sai ya dinga nakada maki babu me kwatarki in ku ka yi aure" Khaleesat na isa gida taga babu motar Housemate dinta a parking space, jingina tayi jikin entrance din apartment din nasu, gashi ta gaji sosai ga yunwar da take ji, babu wanda ta saba da shi a Neighborhood din balle ta shiga gidansa, balle su turawa basu yarda da hakan ba ma, ta kusa twenty minute a tsaye sai ga motarsa ta hango, sunkuyar da kanta tayi har yayi parking ya karaso kofar entrance din, gefe ta koma without looking at him, tun kan ya karaso kofar apartment din ya sa hannu a aljihunsa yaji babu makullin, ya ɗan bude ido still yana laluba duk aljihunsa, sai a sannan ta daga kai tana kallonsa, juyawa yayi ya koma motarsa ta bi sa da ido, ya gama dube dubensa a motar bai ga makullin ba, ai tana ganin yanda yake dube dube tasan kilan ya yar da makullin, shikenan ta shiga uku, she is soo tired, har wani jiri take ji a tsayen da take, dawowa yayi yana kallonta yace "Look Halysaah, i think i left the key at where i am coming from" Ita dai bata ce komai ba kuma bata bari ta hada ido da shi ba, yace "Ko zaki shiga apartment din Neighbor dinmu kafin in dawo" Sunkuyar da kanta tayi still keeping mute, yace "Or ain't you familiar with them?" A takaice tace "Eh" Yace "Ok i will be back as soon as possible" Juyawa yayi ya koma gun motarsa ta bi sa da wani kallo.... Khaleesat na ta tsaye har bayan wani minti sha biyar sai gashi ya dawo, yana kallonta yace "Allah ya taimake ki na gani" Wani kallo tayi masa wato ita Allah ya taimaka ma, yana bude kofar tayi shigewarta ciki ta nufi dakinta ba tare da ta juya ba, sai da ta kwanta na kusan minti sha biyar sannan ta mike a hankali ta shiga bandakinta, bayan Khaleesat tayi wanka tayi sallah tana zaune kan darduma taji yayi knocking kofar dakinta, kallon kofar take bata ce komai ba kuma bata amsa ba balle ta tashi, taji yace "Halysaah" Bluntly tace "Me ya faru?" Jin ya murda kofar dakin ta zaro ido ta mike tsaye da sauri tace "What?" Tuni ta isa gun kofar ta bude tana masa kallon tuhuma, ledan hannunsa ya ajiye mata yace "I got you food, naga kin yi laushi" Ta kalli ledan, ya juya ya bar wajen ta bi sa da kallo har ya koma parlor, sauke idonta tayi, bayan few seconds ta duka ta dau ledan ta juya ta koma dakin. Khaleesat ta bude abincin da ya kawo mata ta fara ci kenan wayarta ya fara vibrate, mikewa tayi ta bude handbag dinta ta ciro wayar, sosai gabanta ya fadi ganin Abdul ke kiran ta, zaunawa tayi gefen gado tana kallon screen din wayar har sannan gabanta na bugawa, kafin kiran ya katse tayi karfin halin dagawa ta sa handsfree sannan tayi sallama cikin sanyin murya, maimakon ya amsa sai ji tayi yace "Wato all this While ni kike jira in kiraki ko Khaleesat?" Ta sauke idonta a hankali tace "To ai cewa kayi duk sanda kake son magana da ni zaka kirani amma kar in sake in kira ka" Yace "Don nace kar ki kirani sai ki ki kiran nawa? Me yasa baki reason ne?" A sanyaye tace "Kayi hakuri" Yace "In ban hakura ba ya zan yi da ke? Ai saboda baki damu da ni bane yasa kika zama comfortable without calling me all this while, ko da bazan daga ba ai kamata yayi ki kira" Cikin sanyin murya tace "Kayi hakuri" Yace "Yaushe za ku fara jarabawa?" Tace "Probably nan da 6 to 7 weeks" Yace "I can't wait har zuwa nan da sati bakwai ban gan ki ba Khaleesat, idan na samu lokaci zan shigo anytime from now in sha Allah" Shiru Khaleesat tayi as if trying to process what he just said, yace "Hello" Da sauri ta kifta ido tace "Na'am ina ji" Yace "Me yasa kika yi shiru? Ko baki son in zo ne?" Tayi yake tace "Aa ban yi shiru ba network ne, ban ji me kace ba" Yace "Ohk, nace you should expect me any moment from now" A hankali tace "Toh Allah ya kai mu" Yace "Ameen, me kike yi yanzu?" Tace "Abinci nake ci" Yace "Ohk switch to video call" A hankali tace "Toh" Mayafinta ta jawo sannan tayi yanda yace mata. 07087865788 for more info✍🏻 [5/2, 5:50 PM] khaleesat Haiydar 📚✍️: ✨✨ HALYSAAH ✨✨ By _Khaleesat Haiydar_✍🏻 5...... Wajen karfe biyar na yamma Khaleesat ta fito parlor daga dakinta, window ta nufa tana leka garage ta ga motar Housemate dinta alamar yana gidan, juyawa tayi ta tafi kitchen zata yi disposing takeaway din da yayi mata daxu, ta window din kitchen din ta hangosa zaune a Lawn din dake bayan kitchen din waya ƙare a kunnensa alamar he is making a phone call, komawa baya tayi don kar ya hangota ta window din kitchen din, ta ajiye ledan hannunta a hankali ta juya ta fita daga kitchen din ta dawo parlor, tsaye tayi tana kallon handle na kofar living room din, sai kuma ta tafi gun da ya ajiye takardun karatunsa ta hau bincika Books din da sauri, har ta gama dube dubenta bata ga abinda take nema ba, ta koma kitchen din tana kara lekansa, seeing he is still on call ta dawo da sauri ta tafi corridor din dakunansu, tsaye tayi gabanta na faduwa as if contemplating on whether to do what is on her mind or just forget it, ganin she is just wasting time ta runtse idonta ta bude, sai kuma ta kai hannu handle din kofar dakinsa a hankali ta bude ta shiga ciki zuciyarta na bugawa, bin dakin that was neat and tidy ta fara yi da kallo kafin ta karasa can ciki da sauri, har sannan tana kallon ko ina na dakin, ta ma rasa daga inda zata fara duba abinda ta shigo nema, zagaye dakin ta fara yi tana dube dube with confusion, daya wayarsa dake gefen gado yayi haske alamar shigowar sako, kallon screen din wayar take yi ganin wani matashi kamarsa a shekaru ne a fuskar wayar, ta juya ta kalli Trouser dinsa, gabanta na faduwa ta dauka ta kai hannu aljihun wandon, Dollar ta ciro masu yawa tayi saurin ajiyesu gefen gado, sannan ta duba daya aljihun, zaro ido tayi jin makulli da Counter a ciki, ta ciro da sauri tana kallon makullin taga makullin kofar parlor ne, bata san sanda tayi murmushi ba ta ajiye wandon a inda ta dauka sannan ta juya da sauri, ƙamewa tayi a spot din da take ganinsa tsaye bakin kofar dakin ya rungume hannu yana kallonta daga sama har kasa, kawai ta juya masa baya zuciyarta na bugawa taji kamar ƙasa ya bude ta shige ta huta, after some seconds taji yace "Sannu da aiki" Ita dai ta kasa juyowa, she felt so ashame at that moment, she wish this never happened, sai juya makullin hannunta take with shame, Calmly yace "Give me the key" Ta wani turo baki taki juyowa tace "To ba amfani zan yi da shi ba" Yace "Dama in bana nan bincike kike shigowa ki min a daki?" Bata san sanda ta juyo tana kallonsa babu ko kiftawa ba jin abinda yace, sai kuma ta ajiye makullin a gefen gado ta nufi kofa ta bi gefensa ta fice daga dakin ta shiga nata ta tura kofar, nan da nan taji hawaye ya cika idonta ta zauna gefen gado, sai kuma ta ɗora kanta saman pillow hawaye na sauka idonta har da shessheka. Karfe bakwai da few minutes Khaleesat na zaune kan darduma, tun da ta idar da sallah take zaune wajen, da ta tuna abinda Housemate din nata yace mata sai taji hawaye ya cika idonta, gaba daya taji ta tsani zaman gidan, kuma bata jin zata iya ci gaba da zama as far as he is here, ta yanke shawaran kawai zata gaya ma Abdul ya canza mata gida kamar yanda Safiyyah ta bata shawara tun farko taki dauka, wayarta dake gefen gado ta dauka jin ana kira, tana dubawa taga Mustapha ne ke kiranta, ajiye wayar tayi gefenta taki dauka har ya katse, ya sake kira nan ma taki dagawa, bayan ɗan lokaci aka sake kiranta kallon wayar tayi a bit fed up thinking it's still Mustapha sai taga Abdul ne ke kiranta this time around, ta jawo wayar a hankali tayi picking ta kai kunne, sallama tayi masa sannan ta gaishesa, yace "Ya naji muryarki haka?" Tayi shiru tana tunanin ta inda zata fara sanar masa the situation at hand, muryarsa ya dawo da ita tunanin da take, a ɗan tsawace yace "Ke, baki ji na ne zaki min shiru?" Kasa gaya masa tayi don bata ma san yanda zai fara daukar lamarin ba barin yanda taki gaya masa tun farko, Ta ɗan yi yake tace "Ina jin ka, kawai muna da wani jarabawa ne gobe, kuma ina jin ciwon kai, and I haven't covered up, shi yasa nake damuwa" Yace "Na ce ki dena stressing kanki da karatu, u are not dull to be studying as if ur life depends on it, read a little and get enough rest, nasan za ki yi passing ko ma me za kuyi gobe" Tana murmushin karfin hali a hankali tace "To" Yace "Kin ci abinci ne?" Ta girgiza kai tace "Ban ci ba" yace "Ohk get something to eat, idan kin gama sai ki kirani ina jiran ki" Tace "Toh" Katse wayar yayi, ta bude WhatsApp dinta tana duba ko Neighbor dinsu ta mata reply taga ta hau WhatsApp din amma still bata yi reply ba, yau kwana uku kenan basu yi magana da Ummanta ba, Dialing din Number Sha'awa tayi ta direct call, har ya katse ba a daga ba, sai da ta sake kira aka daga, sallama Khaleesat tayi mata sannan ta gaisheta, Sha'awa ta amsa tace "Lafiya lau Khaleesah, ya karatu?" Khaleesat tace "Alhamdulillah ya gida ya su Kamilu?" Sha'awa tace "Duu lafiyansu lau wallahi" Khaleesat tace "Su Ummanmu suna lafiya..." Sha'awa tace "Kwana biyu kinyi magana ta wassap kinji shiru ko, to Ummanku dai bata da lafiya amma da sauki yanzu" Nan da nan Khaleesat taji hankalinta ya tashi don dama tun da taji shiru for days tasan ba lafiya ba, don ko bata yi ma Ummanta magana ba ita zata mata ta wayar Sha'awa taji ko tana lafiya, Hankalinta a tashe tace "Aunty Sha'awa tun yaushe?" Sha'awa tace "Ina jin yau kwana uku, ai an ma ce kar a gaya maki, shi yasa ko mayar maki da sakon da kika yi ta wassap din ma ban yi ba, yanzun ma kar ki wani ce zaki kira kowa kiyi ta mata addu'a kawai Allah ya bata lafiya" Khaleesat taji hawaye na sakko mata ta kasa cewa komai, Sha'awa tace "Wai daga ta tashi zata fito daki tayi alwalan magariba shi ne fa ta yanke jiki ta fadi a bakin kofar dakin, duk kwanan nan ina rabata da saka ma kanta damuwa tunda tasan matsalarta na hawan jini, to kinga ai irin haka ake gudu gashi kuma ya faru, Farida ma ta taho daga legas tun jiya ta iso, kar ki wani tada hankalinki don jikin da sauki" Cike da karfin hali Khaleesat tace "Suna asibiti ne yanzu?" Sha'awa tace "Wani asibiti? To har sai da Farida ta zo sannan ta kai ta asibiti jiya in gaya maki, amma duk kwanakin nan tana gida gashi ko taɓata kika yi a daya barin jikinta bata ji wai, ko magana ma in tayi sai kin sa kunne sosai zaki ji, ke abun fa ba kyau, har yanzu hankalinmu a tashe yake, an dai ce kar a gaya maki kar hankalinki ya tashi...." Khaleesat in hankalinta yayi dubu ya tashi a lkcn, ta kalli Screen din wayarta jin kiran ya katse alamar katin ta ya kare, ajiye wayar tayi ta fara rera kuka kamar an sanar mata da mutuwa... Har karfe goma na dare Khaleesat ta kasa tashi daga kan darduman da take, sosai ta shiga damuwa ba kadan ba, a inda take zaune Abdul ya kirata sau biyu amma ta kasa picking call din nasa, karfe goma da rabi taji anyi knocking kofar dakinta, ta juya ta kalli kofar tana share hawayen dake idonta amma bata tashi ba sai ma hade rai da tayi, after a while ya sake knocking still dai bata tanka ba, sai kuma taji yace "Assalamu alaikum" kawai ji tayi ya bude kofar dakin ta juya da sauri daga inda take zaune suka hada ido, daga nan bakin kofar ya tsaya yana kallonta, ita dai taki yarda ta sake hada ido da shi, ya karasa ciki ya tsaya still leaving enough distance between them, calmly yace "Maganar da na maki yasa kike kuka? But i was only pulling ur legs Halysaah, i am sorry about that, was just joking" Wasu hawaye suka cika idonta sai kuma ta fara kuka, bude ido yayi alamar mamaki sosai yana kallonta, can dai ya kwantar da murya yace "Look, do not take my words serious Halysaah ni wasa nake maki wallahi" Ta rufe fuskarta da Hijab din jikinta tana kuka a hankali, dukawa yayi da mamaki sosai yana kallonta ya ma kasa cewa komai, after few seconds da taji shiru ta ɗan bude fuskarta don tunaninta ya fita daga dakin, suna hada ido ta daure fuska tace "Ni saboda kai nace nake kuka?" Yace "Toh why are you crying?" Shiru tayi bata ce komai ba wasu sabbin hawayen na cika idonta, Yace "Tell me Halysaah, what is making you cry?" Kamar bazata ce komai ba sai kuma tace "My mother is sick" Yace "Hasbunallah, what's wrong with her?" bata sake ce masa komai ba tana goge idonta, After few seconds ya sauke ajiyar zuciya yace "Amma ai ba kuka zaki zauna kina yi ba, addu'a zaki mata Allah ya bata lafiya" Nan ma dai bata ce komai ba, ya mike yace "Allah ya bata lafiya" Sai a sannan tace "Ameen" Yace "Are you going back home to check on her?" Ta daga kai ta kallesa amma bata ce masa komai ba, yayi shiru shima, can yace "Are you from kano?" Ta gyada masa kai, Yace "Allah Ubangiji ya bata lafiya, and try getting something to eat for Dinner" Ta sunkuyar da kanta kawai, ya juya ya fita daga dakin ya kullo mata kofar gently. Wajen karfe sha biyu na dare Khaleesat na kwance taji ya sake knocking kofar dakinta, juyawa tayi ta kalli kofar, bayan wasu yan sakwanni ta mike zaune tana kallon kofar, sai da ya sake knocking sannan ta sauka daga saman gadon ta dau hijab dinta ta saka ta nufi kofar ta bude, yace "Are you still crying?" Ta hade rai ta girgiza kai without looking at him, yace "Ok naga baki fito kinyi dinner ba and it's past 12, ki nemi abinda za ki ci kar ki kwanta haka" Ita dai bata ce komai ba, yace "Hello" Daga kai tayi ta kallesa tace "Naji" Yace "Good" Kullo kofar dakin nata tayi ta nufi kitchen tana tafiya a hankali, sai da yaga ta shiga kitchen din sannan ya shiga dakinta yana bin ko ina da kallo, after a while Khaleesat ta fito daga kitchen din with a cup of tea and some cookies, tsaye ta gansa corridor, bayan ta karaso yace "Kin ga nima Ummi na bata da lafiya amma ban zauna ina kuka ba kamar yanda kika yi" Khaleesat bata kallesa ba ta shige dakinta ta kulle kofa, tana gama shan shayin ta koma saman gado ta kwanta, tasan yau da kyar ta iya bacci, she wish she can just see herself in Nigeria, but how?? Wasu hawaye ne suka zubo idonta ta lumshe ido, after a while ta jawo wayarta a hankali tayi dialing number Abdul bayan ta tuna ya kirata har sau biyu daxu bata iya tayi picking ba, har kiran ya katse bai daga ba, ta sake kiransa nan ma bai daga ba, tasan as usual yayi fushi kenan, ko uxuri bazai mata ba, ajiye wayar tayi ta juya zuwa daya side din gadon. Washegari da safe Khaleesat na zaune daki tana ta kokarin kiran Aunty Farida amma baya shiga, har Sha'awa sai da ta kira ita ma wayarta baya shiga, ta rasa wa kuma zata kira, ta kalli agogon wayarta dake nuna karfe goma sha daya ta ajiye wayar tayi tagumi, tun daga daren jiya har yau bata da sukuni, ko schl din ma yau tasan bazata iya zuwa ba, juyawa tayi jin knocking a kofar dakinta, tana dai zaune har sai da ya kwankwasa kofar sau uku sannan ta sauka daga saman gado, walking slowly ta tafi ta bude kofar, Yace "Good morning Halysaah, how was ur night?" Without looking at him tace "Fine" Yace "Ya jikin Mama? Kun yi communicating da su?" Kai kawai ta gyada masa bata ce komai ba kuma bata kallesa ba, Paper da pen din hannunsa ya mika mata yace "Can i get ur Email Address?" Ta daga kai ta kallesa da mamaki tace "I don't understand" Yace "I mean ur Email Address" wayarsa ne ya fara ring ya mika mata takardan da pen ya daga kiran sannan ya juya ya bar wajen, ita dai ta bi sa da kallon mamaki, can ta juya ta koma daki ta ajiye takardan da pen da ya bata, after some minutes sai gashi ya dawo yayi knocking yace "Can i get the paper" Tasowa tayi ta bude kofar bayan ta dau pen da takardan tace "Why are you asking for my Email Address?" Yace "Ki dae rubuta ki bani" Shiru tayi, sai kuma ta jinginar da paper din jikin kofa ta rubuta sannan ta mika masa ya amsa ya juya ya bar wajen, yana fita da few minutes taji message ya shigo wayarta, ta dau wayar ganin E-mail ne ya shigo ta bude, kallon Image din da ta gani as Email din ta dinga yi babu ko kiftawa, she look shocked and confused at the same time, ta daga kai tana kallon kofar dakinta babu ko kiftawa, dai dai sanda taji sallamarsa, kasa tashi tayi daga inda take zaune, har sai da yayi knocking sau biyu tayi karfin halin mikewa ta isa kofar ta bude tana kallonsa, Yace "I don't know if you find this okay and a good idea" Ita dai bata fasa kallonsa ba looking speechless, Yace "Hope they won't be Mad at this back home Halysaah?" Jin bata basa amsa ba ya gyada kai yace "I guess it's a bad idea, I should have ask for ur opinion first before doing this" Nan da nan hawaye ya cika idonta ta sunkuyar da kanta, yace "Ok it's fine, i will get the ticket cancelled" Daga kai tayi da kyar tana kallonsa hawaye na zuba idonta tace "Thank you so much, i appreciate" Yace "Sure??" Ta gyada masa kai, yace "Ohk, u can order a Lyft that will be taking u to the airport later, ur flight is at 3pm today" Sauke idonta tayi cause she is totally speechless, ya mika mata travelling documents dinta, amsa tayi cike da mamakin how he got them, ya juya ya bar wajen, komawa cikin daki tayi ta kulle kofar tana kallon inda take ajiye travelling doc din nata a dakin, did he come to her room to check ne, to ai throughout babu inda taje, ta karasa gefen gado har sannan jikinta a mugun sanyaye ta zauna, kallon screen din wayarta ta sake yi tana kallon ticket din don ganin abun take kamar a mafarki, tana kara duba taga tun daren jiya ya siya ticket din and kamar yanda yace the flight is by 3pm today, ta ma rasa ko farin ciki zata yi ko kuma wani reaction zata yi, amma da ta tuna she is going back home to see her Mom

Chapter 4 of 16