dubasa Safiyyah" Safiyyah tace "Amma ai kya jira ya shigo mu yi masa sallama ko, dadina dake a ko ina sai kin nuna halin ki, kamar ana koranmu daga shigowa gida kice mu tashi mu tafi" Budewar kofar dakin ya sa duk suka yi shiru, Housemate dinta ya shigo da sallama ya zauna kan kujeran dakin ya jinginar da kansa da kujeran, sai ga wani chef din gidan ya shigo da wasu tsadaddun cookies ya ajiye masu kusa da su, sannan ya juya ya fita, Jay na kallon Khaleesat yace "Naga kina son cookies sosai Housemate, here are some for you and ur frnd" Bata yarda ta kallesa ba tana wasa da gyalenta tace "I am okay, tafiya ma za mu yi" a hankali yace "So soon? Amma sai kun ci cookies tukun" Khaleesat ta ɗan kallesa suka hada ido a karo na farko tun shigowarsu dakin, sosai taji gabanta ya fadi tayi saurin sauke idonta, ya kalli Safiyyah yace "In bazata ci ba ke ki ci abunki... Amma ban san sunanki ba kawar Housemate" Safiyya tayi murmushi tana bude cookies din ta dau guda daya tace "Sunana Safiyyah Adam" Yace "Maa sha Allah, it's nice meeting you Safiyyah, i am Jawwad Ahmad, or you call me Jay" Safiyyah tace "Nice meeting you too Jay" ita dai Khaleesat wasa da gefen veil dinta kawai take kanta a kasa, Safiyyah ta bude handbag dinta saboda kiran wayarta da ake yi, tana dubawa taga Cousin brother dinta ne, ta mike tace "Let me pick a call pls" Jay yace "Alright Safiyyah" Kofa ta nufa ta bude ta fita sannan ta kullo masu kofar, ledan da suka shigo dakin dashi ya ɗan bude yace "You got me all this Halysaah" Khaleesat ta ɗan kallesa tace "Um" Yace "Ohk thank you so much i really appreciate" Tana kallonsa a hankali tace "Ya jikin?" Yace "I am getting better gradually, daxu sai naji ina sha'awar wannan tuwon da kika yi some days back" Tana kallonsa tace "Na vegetable soup?" Yace "No, wannan da na kasa ci, the dark soup, I can't remember the name" Bata san sanda tayi murmushi ba tace "Ok miyan kuka?" Yace "Shi... kawai naji shi nake son ci sincerely" a hankali tace "Ohk zaka je can gida anytime soon ne?" A hankali yace "Idan na samu lafiya in sha Allah" Ita dai Khaleesat kallonsa kawai take, shi kam idonsa na gun different direction, Ajay ne ya bude kofar dakin, kai tsaye ya shigo ya nufi Jay yana mika masa wayar hannunsa yana kallonsa, ita dai Khaleesat ta sunkuyar da kanta bata kalli inda yake ba, Jay ya amshi wayar yana duba screen din, sauke ƙafafuwansa yayi daga kan kujeran da yake zaune ganin wanda ke kan layi, ya kai wayar kunne da ladabi yayi sallama hade da gaisuwa, sai kuma yace "Alhamdulillah Abba da sauki, wayar a silent yake ne shi yasa" Sai kuma ya daga kai ya kalli Ajay jin abinda Abban ke ce masa, a hankali yace "A'a ba haka bane Abba, i do eat... but not much, ba gaskiya ya fada ba" Daga haka yayi shiru bai sake cewa komai ba, after a minute yace "To in sha Allah Abba, Allah ya kara girma" Sai da ya jira Abba ya katse wayar sannan yayi wurgi da wayar saman gadonsa yana kallon Ajay, wani kallo Ajay yayi masa ta gefen ido ya juya ya tafi ya dau wayarsa a kan gadon sannan ya fice daga dakin, Khaleesat ta gama tura ma Safiyyah text din da take na cewa tayi masu ordering Lyft su tafi gida, sai kuma ta daga kai ta kalli Jay, ganin mood dinsa ya canza, a hankali tace "Baka cin abincin ne ko?" Yace "Ki kyalesa mana, i took cereal daxu da safe kuma a gabansa, shi in bai bata min rai ba baya jin dadi a rayuwarsa" Khaleesat tayi shiru kamar bazata ce komai ba, can dai tace "To ai Cereal ba abinci bane, ka dai dinga ci ko kadan ne" Ɗan murmushi kawai yayi bai ce komai ba, tace "Shikenan, za mu koma, Allah Ubangiji ya baka lafiya" Yace "Baza ki bari Salem ya dawo yayi dropping din ku ba?" Tace "Aa, Safiyyah nasan brother dinta ne ke kiranta a waya, kaga tun daxu muka gama lectures bata koma gida ba" Yace "Ohk ni bari in ajiye ku" Khaleesat ta zaro ido tace "Aa kai da baka da lafiya, za mu yi ordering Uber do not worry about us pls" Khaleesat ta mike, yana ganin haka shi ma ya tashi, amma sai da ya dafa kujera for sometime saboda juya masa da kansa ya fara yi, A hankali Khaleesat tace "Pls kar kayi stressing kanka, just lie down and rest" Ya dago kansa yace "No, let me see you downstairs" Juyawa tayi ta nufi kofa, ya bi bayanta, ga mamakinta sai ta ga Safiyyah tsabar samun waje tana zaune parlon dake upstairs tana kallo tana cin cookies ga lemo a gabanta, to a ina ta samo lemun da cookies, Safiyyah ta washe baki ganin Khaleesat sannan ta mike tace "Shikenan mu tafi?" Jay da ta hango ne yasa tayi tsit, Khaleesat ta nufeta suka fara sauka downstairs a tare amma gabanta faduwa yake kar su kara ganin karen daxu, hakan yasa ta bari Safiyyah ta shiga gaba, Jay na biye da su a baya har suka sauko downstairs, ai ko karen na ganinsu ya nufo su da gudu yana haushi, Khaleesat ta juya a tsorace zata koma sama ta ci karo da Housemate dinta dake bayanta, ya rikota da sauri yace "C'mon, are you afraid of dog Halysaah?" Bayansa ta koma zuciyarta na bugawa, Safiyyah kuwa sai kora karen take da jakar hannunta fuska daure, shi dai Ajay na zaune parlor tun da ya kallesu sau daya ya dauke kai ya ci gaba da kallon Football da yake, sai da Jay ya kori karen sannan ya juya da gudu ya koma gun Ajay ya zauna saman kujeran kusa da shi, Jay ya juya ya kalli Khaleesat da ta marairaice ita ma tana kallonsa, ya ɗan yi murmushi yace "Ba abinda zai maku ai, bai san ku bane shi yasa...." ita dai bata ce komai ba, Jay ya jufi Ajay yace "Ajay ina makullin motana?" Ajay yace "Me zaka yi da makullin mota?" Khaleesat dai tuni ta nufi kofar fita parlon da sauri don ko kallon Ajay bata son yi, Safiyyah kam tana kallon Ajay tace "To sai anjima, Nagode sosai" Yace "Allah ya tsare" sallama tayi ma Jay shima sannan ta bi bayan Khaleesat, Jay yasan bazai basa makullin ba, hakan yasa ya duba aljihun Ajayn ya zaro few dollars sannan ya juya ya bi bayan Safiyyah, duk yanda yayi da Safiyyah ta amshi kudin taki amsa, Khaleesat tuni ta kusa fita daga gidan gaba daya, a haka Safiyyah ta bi bayanta. Safiyyah na kallon Khaleesat bayan sun shiga Lyft har sun fara tafiya ta rike haɓa tace "Ke ashe wannan gayen da muka yi misunderstanding da farko da muka shigo gidan yana da kirki sosai, in gaya maki da na zauna parlon nan na sama ni kadai ya zo wucewa ya ganni sai ya tsaya yayi powering min TV, har da kunna min wutan parlon, ya kuma nuna min fridge in dau lemo in sha, wallahi i never expect such kind gesture from him duba da yanda ya amsa mana gaisuwanmu da muka shigo parlon da farko, ashe mun yi misperceiving dinsa ne" Khaleesat tayi kamar ma bata ji abinda Safiyyah ke cewa ba.
07087865788 ✍🏻
[5/12, 6:46 PM] khaleesat Haiydar 📚✍️: Read My Book "HALYSAAH" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=681294ff01c6bd900451c8e6
✨✨HALYSAAH✨✨
By _Khaleesat Haiydar_✍🏻
15.....
Wajen karfe takwas na dare Khaleesat na zaune parlor tana duba wani reading material dinta wayarta ya fara vibrate, daukan wayar tayi taga number Salem, ita dai kallon screen din kawai take at first, after some seconds ta daga ta sa Hands-free tayi shiru tana saurare, daga daya bangaren aka mata sallama, muryar Housemate dinta ta ji, ta amsa sallamar tare da gaishesa, yace "Ya kika je gida Halysaah?" Tace "Lafiya lau" Yace "How about Safiyyah?" Tace "Tana can gidansu" Yace "Good, thank you so much for the visit" a hankali tace "Allah ya kara lafiya" Yace "Ameen Housemate" Daga haka yayi mata sallama ya katse wayar, bata kai ga ajiye wayar ba wani kiran ya sake shigowa ta ga Abdul ne, sai a sannan ta tuna damuwar da take ciki for days now, nan da nan mood dinta ya canza, tayi picking call din ta saka hands free sannan ta ajiye a gefenta tana ci gaba da duba reading material dinta a hankali ta gaishesa, yace "Didn't you see the money i sent to you?" Ta girgiza kai tace "Ban kula ba" yace "To ki duba" Katse wayar yayi ta jinginar da kanta jikin kujera with many thought running her mind.... Washegari da yamma bayan Khaleesat ta idar da sallah tana zaune tayi dialing number Salem, yana fara ring ya daga, bayan sun gaisa tace "Dama abinci ne zan ma Housemate dina yace min yana so, ban san ko zaka iya zuwa karfe biyar sai ka tafi masa da shi ba, that's if you are available and u don't mind doing so pls" Yace "Oops naje Pennsylvania daxu da safe, but za ki iya zuwa gidan ki kai masa ai, he is at home" A hankali Khaleesat tace "Ohk" Yace "Yeah, ki kai masa kawai can gidan" Tace "To nagode" a haka suka yi sallama ta ajiye wayar, Allah ya so bata dora girkin ba don ta san babu abinda zai sake maida ta gidan nan dai, tayi zuwan farko tayi na karshe. Khaleesat na zaune tare da Safiyyah bayan sun gama lectures din su na ranan, Safiyyah tace "Are you checking on ur Housemate even if ta waya ne kuwa Khaleesat?" Khaleesat ta kalleta tace "I don't have his number ai" Safiyyah ta dinga kallonta da mamaki, can ta girgiza kai tace "Ni ban san me yasa kike haka ba, why won't u ask that guy Salem ya baki? It's almost 10 days now da muka je gidan dubasa tunda kika ga har yanzu bai zo apartment dinku ba kinsan kilan ko bai ji sauki bane" Khaleesat tace "There was a time da muka yi waya da Salem din yace zai turo min lambarsa kuma bai turo ba shi sa har yau ban sake masa magana ba naga kamar baya son tura lambar ne, sannan kawai i assume kilan wannan arrogant guy din ne na gidan yayi stopping dinsa from coming to the house, i suspect they are kind of related or something like that" Safiyyah ta tabe baki tace "To ko in raka ki mu sake zuwa dubasa ne?" ko rufe baki bata yi ba Khaleesat tace "I am going no where, sai dai in ke zaki je sai in masa tuwo ki kai masa, dama ranan da muka je yace min yana son tuwo da miyar kuka, but for me babu abinda zai sake maidani gidan nan wallahi" Safiyyah ta dinga kallonta, can tace "Gaskiya zuciyarki kamar dutse yake Khaleesat, wato har ce maki yayi yana son cin tuwo amma kika kasa yi ki kai masa saboda wani banzan dalilinki, gaskiya you are not nice at all sorry to say" Khaleesat ta mike tace "Ki kirani ko ma me zaki kirani amma wallahi bazan koma wannan gidan ba as far as that bossy Man is in the house, kawai sai in kama hanya in sake komawa don yaji dadin kara raina min hankali ya walakanta ni, in dai ke zaki je zan yi girkin in baki, after all kince the arrogant guy is nice to you ai" Safiyyah bata tanka ta ba ta fara danna wayarta kawai, a haka suka rabu ko sallaman kirki basu yi da juna ba, har Khaleesat ta isa gida a lyft bata san sun iso ba, a duk kwanakin nan Allah ya sani Housemate dinta na ranta don babu ranan da zai zo ya wuce bata tunasa a zuciyarta, ba willingly taki zuwa gidan ta dubasa ba kawai wannan mutumin ne bata son ta sake haduwa da, sannan she is afraid of the huge dog in the house, kar ma taje mutumin ya sakar mata karen ta shiga uku, amma a ko da yaushe Housemate dinta yana ranta tana kuma son sanin how he is feeling, a hankali ta bude motar ta sauka duk jikinta a sanyaye ta nufi apartment dinta ta bude kofar ta shiga, turus tayi a living room din ganinsa kwance kan 3 seater yana bacci, juyawa taga yayi with his eyes still close yace "Good evening Halysaah" Sauke idonta tayi daga kallonsa, walking slowly ta karasa cikin living room din ta nufi can kusa da single sitter ta tsaya still looking at him, a hankali ya bude ido ya fara bin parlon da kallo alamar he is looking for her, suna hada ido calmly tace "Good evening" Mikewa zaune yayi trying to recover fully from his sleep yana shafa fuskarsa yace "How are you?" Tace "Alhamdulillah, ya jikin?" Yace "Naji sauki ai" Shiru tayi kamar me tunanin abinda zata ce, can kuma dai tana rike da edge din gyalenta cikin nutsuwa tace "Naga baka zo bane, i thought jikin ne har yanzu...." Ya girgiza kai without looking at her yace "Abbana ne yasa na je Nigeria, we spent 6 days in Nigeria, jiya muka dawo" Yana fadin haka ya daga kai yaga kallonsa take, da sauri ta kauda kanta tana nodding tace "Ohk" Daga haka ta juya ta nufi dakinta kamar munafuka, ya koma yayi kwanciyarsa. After almost an hour Khaleesat ta fito parlor, ta samesa zaune ya gama baccin yana danna laptop dinsa, kanta a kasa ta karasa cikin living room din ta dan kallesa suka hada ido tana kame kame tace "Dama tambayarka zan yi in maka tuwon ne yanzu zaka ci?" Yace "Tuwo kuma? Aa kinga you just came back from school, ki bari next time in sha Allah" Tace "Ohk" Daga haka ta tafi kitchen to make a light dinner, bayan ta gama girkin ta fito parlor, har sannan yana nan zaune, ta ɗan kallesa tace "You care for some?" Ya kalli hanyar kitchen din sai kuma yace "Let me dish it my self" Daga haka ya ajiye laptop dinsa ya mike ya tafi kitchen din, ita dai tana tsaye ta bi sa da kallo, bayan few minutes ya fito da bowl din pasta din ya zuba very little quantity, with another plate of the pasta, ita dai kallonsa take, ya mika mata na plate din ta sauke idonta ta amsa, ya zauna ya ajiye bowl din nasa, a hankali tace "Wannan ne zai isheka?" Yace "Eh" juyawa tayi zata bar wajen, yace "Bedroom za ki je ki ci abincin kenan" Ta gyada masa kai tayi tafiyarta daki. Wajen karfe tara na dare Khaleesat ta saka hijab dinta jin yana knocking kofarta sannan ta tafi ta bude kofar, yace "Sai da safe Halysaah, i am going home" at first shiru tayi, can kuma a hankali tace "Why are u having two home?" Ya ɗan buda ido yayi murmushi yace "One is a home, the other... a comfort zone" Ta langwabar da kai tace "U said two same thing ai, A Home is also known as a comfort zone" Dariya yayi yace "Not in my case Halysaah, they are two different thing to me" Shiru tayi kafin tace "So now, which is home and which is comfort zone?" Yayi murmushi yace "Kema dai kamar er jarida, how is ur frnd?" Tace "She is fine" Yace "And ur Bossy boyfriend, hope ya daina saka ki kuka dai yanzu?" Ta wani kallesa zata kulle kofarta da sauri yace "Wait, it's just a harmless question Halysaah" Tace "To da nace maka kuka yake sa ni?" Yace "Ohk, Allah sa kar in zo ina baki hakuri kwanan nan bayan ya saka ki kukan, and before i forget me yasa baki cin cookies dake kitchen?" Tace "Nawa ne da zan ci?" Yayi shiru kamar bazai ce komai ba, can kuma yace "To ki dinga ci daga yau duk abinda kika ga na siya ki dauka idan kina bukata, I didn't buy them all because of my self alone, ko da namiji ne a gidan nan ko wata mace daban in zan siya abu in ajiye zan siya ne in surplus not for only me, kin gane ko? Har bottle water ina siya mana ne mu biyu ba ni kadai ba, after all there is love in sharing" Ita dai idonta na kasa bata ce masa komai ba, Yace "Good night" juyawa yayi ta bi sa da kallo har zuwa parlor, sai kuma ta kulle kofar dakinta a hankali. Washegari Asabar Khaleesat ta gama laundry da take a kitchen, tayi tidying din duk gidan sannan taje tayi wanka ta fito parlor tana tunanin abinda zata girka kafin ta fara karatu cause it's almost 12pm, tun karfe goma Housemate dinta ya shigo gidan ya wuce Bedroom dinsa, ta ma san bacci, ita kam mamakin yanda baya gajiya da bacci take, knocking kofar parlon aka yi, she is expecting Safiyyah dama amma bata yi tunanin da wuri zata zo ba, ta karasa gun kofar ta bude a bit relieve ta samu me taya ta girki, da mamaki ta bi sa da kallo bayan ta koma gefe don da ta ci gaba da tsayuwa wajen taga alamar bangajeta zai yi ya shiga parlon, direct taga ya nufi dakin Jay ya bude ya shiga, kasa rufe baki tayi tsabar mamaki, tana jin sa yana ma Jay bala'i a dakin, ita dai bata ji muryar Jay din ba, Jay ne ya fara fitowa daga dakin, kamar yanda ta zarga kuwa baccin yake, laptop din da ya bari kan kujera da ya shigo daxu ne ya dauka, Ajay na fitowa ya mika masa laptop din, a mugun fusace Ajay yace "What the hell should i do what with it again bayan lokaci ya kure? Kasan implications din da abin nan da kayi zai ja min kuwa?" A karo na farko Jay yace "Kai dalla wayar a silent yake, kuma ni ban san akwai recent aikinka a ciki ba, da bazan taho da shi ba ai" Ajay dai kallonsa kawai yake kamar ya shaƙo sa, Jay ya zauna kan kujera ya jinginar da kansa tare da lumshe ido, banda hararan Ajay babu abinda Khaleesat da ke tsaye parlon take yi, lkci daya Jay ya mike yace "Hey let me see you off, wanka zan yi" a takaice Khaleesat tace "And pls Housemate warn him not to ever barge into someone else's apartment like this again, this isn't a shopping Mall da zai shigo kai tsaye" A tare suka juya suna kallonta gaba dayansu, Ajay yayi facing dinta calmly yace "Ke, da ni kike wannan maganar ko wa?" Ta wani kauda kai fuskarta a daure tace "In baka son ayi da kai kar ka sake shiga gidan mutane babu Excuse, after all ba tare muke renting apartment din ba da zaka shigo min gida without notice, idan wajen abokinka ka zo maturely sai ka jirasa a waje, you don't have to push ur way into people's apartment like it's a shopping complex" Ajay that was speechless ya kalli Jay, Jay ya shafa kansa yace "Why didn't u knock and wait for me outside, after all she is saying the truth" Khaleesat tace "Ni in ya sake shigo min gida haka wallahi 911 zan kira masa..." Ajay ya ciro wayarsa a aljihu yana mika mata yace "Call them immediately" Ta jefa masa wani kallo tayi hanyar dakinta, Yana kallonta da kyau yace "I will definitely deal with you" Ita dai tuni ta shige dakinta ta kulle kofar da makulli, Jay na kallonsa yace "Me yasa zaka shigo mata gida kamar tsohon barawo?" Ajay yace "Za kayi bayanin me kake yi da mace under the same roof in America, macen ma da ka kusa haifa, i promise to report you back home, ita kuma i will teach her the lesson of her life" Yana kai wa nan ya fixge laptop dinsa a hannun Jay, Jay dake murmushi yace "Babu abinda ka isa kayi mata don ta gaya maka gaskiya Malam, kai waye da baza a gaya ma gaskiya ba" Tuni Ajay ya fice daga parlon, Jay ya zauna kan kujera ya dafe kansa yana dariya, the incident was just funny to him, kallon kofar dakinta yayi yana mamakin dama wai haka yarinyar nan take amma take ma saurayinta kuka? Mikewa yayi ya nufi dakin nata yayi knocking kofar yace "Halysaah" sai da ya kirata sau uku sannan ta bude kofar a hankali tana leka parlon kana ganinta kasan a tsorace take, dariya yayi yace "Kinsan waye shi da kika masa rashin kunya Halysaah?" Ta wani turo baki tace "To ni ina ruwana da koma wanene shi, saboda me zai shigo min gida kamar wani barawo, where is it done that way? Ni dai wallahi kar ya sake zuwa min gidan nan in ba haka ba in kira 911" Jay dai sai sauraronta yake, can yayi murmushi yace "So dama kina da baki haka amma kike ma saurayin ki kuka?" Khaleesat ta wani kallesa ta hade rai tace "Ni bana son haka" still smiling yace "Ok, sorry" keeping a straight face tace "Ya tafi?" Jay ya juya zai bar wajen yace "Ya tafi mana" Da sauri tace "Plss ni dai kayi masa magana kar ya sake zuwa, if there is anything ai sai ya kira kaje can gidanku ka samesa kawai ba sai ya zo nan ba" Jay dai murmushi kawai yake yace "Ohk" parlor taga ya tafi, ta koma dakinta ta zauna bakin gado, har sannan gabanta faduwa yake, ita kanta bata san inda ta samu courage din gaggaya masa abubuwan da ta gaya masa ba, ko don dama tana jin haushinsa ne yasa ta samu irin wnn courage din oho, bata fito daga dakinta ba sai da tayi sallan zuhur, a hankali take tafiya ta shigo cikin parlorn, gani take kamar zai sake dawowa gidan at anytime, ai ko wallahi yan sanda zata kira masa, Zaune taga Jay a parlon yana danna wayarsa, tana tsaye bayan kujera tace "Did u warn him not to come back plss?" Jay yace "To ke meye damuwarki ba kin masa warning kar ya sake dawowa ba, ai bazai dawo ba" Kamar zata yi kuka tace "Wallahi zai iya dawowa, kuma in ya dawo baka nan ya zan yi?" Dariyar da yake dannewa ne ya taho masa yace "Ina kuwa zan san yanda za ki yi, ke wa ya aike ki yi masa rashin kunya? Da sai ki yi shiru da bakinki har in fitar da shi daga gidan, Laptop dinsa na dauko daga can gida yana bacci ban san akwai aikinsa da zai yi put foward ta email ba, yana ta kiran wayana kuma ina bacci na sa wayar silent, that was what brought him here" Zaunawa tayi kan kujera tace "That doesn't still warrant him ya shigo gidan mutane kai tsaye, ko magana bai min ba ina bude kofa ya kusa bangajeni fa ya shigo parlon, am i a joke to him?" Dariya Jay yayi yana gyada kai yace "This energy u used in attacking him Allah ya baki irin energy din kiyi using ma Boyfriend din ki" Wani kallo Khaleesat tayi masa, shi dai murmushi kawai yake still not looking at her yace "Naga kamar kin damu da abinda kika masa, ko in kirasa ki basa hakuri ta waya komai ya wuce?" mikewa tayi a takaice tace "Allah ya kiyaye" Daga haka tayi wucewarta kitchen, shi dai murmushi kawai yake looking at a different direction, yasan yau da kyar Ajay yayi bacci akan abinda tayi masa. Bayan Khaleesat ta gama girkin da take ta fito parlor tana kallon Jay ganin fita zai yi don har ya shirya yana saka agogon wrist dinsa without looking at her yace "I think sai gobe zan dawo in sha Allah" Ta marairaice amma bata ce masa komai ba, har cikin ranta ta fara jin tsoron kasancewarta ita kadai a gidan, ya
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 12 Chapter of 16