"Sure...." Dakin Khaleesat ta nufa, shi kuma ya tafi ya ci gaba da karatun da yake a parlor, Khaleesat ta mike tana kallon Safiyyah bayan ta shigo dakinta tace "Why are you looking this way Sophie?" Safiyyah tace "Wallahi kwanan nan zaki ji nayi ma matar can duka a kasar nan" Khaleesat tayi murmushi tace "Me kuma tayi maki again?" Gefen gado Safiyyah ta zauna kana ganinta kasan ranta a bace yake tace "Tun fa da kika je gidan mugun halinta ya ninku akan wanda take min a baya Khaleesat, she is trying all possible best to make the house miserable for me, dama yanzu ta dena ajiye min abinci kwata kwata, cornflakes da Golden morn sai ta boye a dakinta da sunan taje hada ma yaronta ne duk don kar in sha...." Khaleesat ta sauke ajiyar zuciya tace "To Allah ya kyauta, ko zaki dawo nan?" Safiyyah tace "In dawo nan for what reason? ashe ma riba ta ci kenan idan na bar mata gidan, ai we die together with her in that house, babu inda zan dawo wallahi, kawai rabon ta ci duka ne ba wani abu ba" Lkci daya expression din Safiyyah ya canza daga bacin rai ta kamo hannun Khaleesat tana washe baki tace "Kee naga Housemate dinki ido da ido yau, dama haka yake gayen? Wallahi he is so well flavoured komai yaji, ina masa magana ma ko kallona bai yi ba amma ya amsa min cikin girmamawa, wallahi ya burgeni" Tana blushing ta karasa maganar nata, Khaleesat dai ta saki baki ta kasa cewa komai, can ta kalli kofar dakinta da sauri don ta tabbatar a kulle yake kar ace yana jiyo Safiyyah, sai kuma tayi kasa da murya fuska daure tace "Meye haka Safiyyah what if yana jin ki?" Safiyyah tace "Wallahi raina a bace yake amma yana bude kofar kawai na mance da abinda er iskar matar can ta min, a very calm gentleman, yace min Hi nace Hello... kuma kuna Hausa da shi ko turanci ku ke? Ni sai nake ga kamar ba bahaushe bane ba fa" Khaleesat ta hade rai sosai tace "Don Allah ki rufa mana asiri Sophie, What's all this?" Safiyyah tayi dariya tace "Ni dai kinyi girki? Don wallahi yunwa nake ji" Khaleesat ta mike ta nufi kofa ta fita daga dakin, a corridor ta gansa zai shiga dakinsa, bai kalli ma wanda ya bude kofa ba yayi shigewarsa daki, Khaleesat ta tafi kitchen ta dibar ma Safiyyah abincin da ta girka, jin alamar har ya fito daga dakin nasa ta dawo parlor ta tsaya sai gashi ya shigo parlon, makullin motarsa taga ya dauka da wani littafi, ya daga kai suka hada ido ta fara kame kame tace "Ain't you eating the food?" Yace "Oh, ok na manta" Kitchen din taga ya nufa ta bi sa da kallo, sai da ya shiga sannan ta bi bayansa zata gaya masa kar ya bar mata plate bai wanke ba, tsaye ta gansa kusa da abincin ya dau spoon ya bude tukunyar sannan ya debi shinkafar kadan ya kai baki, kallonsa kawai take da mamaki, ya juya ya kalleta yace "Bad habit right?" Sake dibar abincin yayi ya kai baki, daga haka ya rufe tukunyar yace "Kinga ni ba yunwa nake ji ba, I am full" Ta dinga kallonsa, bata san sanda tace "Ko in zuba maka ka tafi da shi?" Ya bude fridge ya ciro bottle water yace "Aa in na dawo anjima zan ci" Daga haka ya fita daga kitchen din ya nufi kofar living room ya bude, sai a sannan ya juya, ta dauke idonta, yace "See yah" Fita yayi ya kulle kofar daga waje. Sai wajen karfe shidda na yamma Khaleesat ta raka Safiyyah zata hau Uber da tayi ordering, Safiyyah na kallonta tace "Ya Mustapha dai ya hakura dake, jiya nake gaya masa gaskiya kina da wanda zaki aura a gida, don nima na gaji da damuna da yake yi shi sa kawai na gaya masa, ai ko ina gaya masa yace to shikenan dama tun farko ai da kin gaya masa he will understand" Khaleesat ta sauke ajiyar zuciya tace "To ai kinga gwara haka" a haka suka rabu Khaleesat ta koma cikin gida, har goma na dare bata ji shigowar housemate din nata ba hakan yasa ta gane bazai dawo gidan ba ranan. Washegari da safe ta shirya ta tafi makaranta, bata dawo gidan ba sai kusan karfe hudu na yamma, tana shiga living room ta gane ya dawo gidan da bata nan, bedroom dinta ta wuce bayan tayi wanka tayi sallah ta canza kaya ta fito kitchen zata yi ɗan wake don shi ne a ranta, bayan ta gama hada duk ingredients din taji an bude kofar parlor, ta dai ci gaba da abinda take, kitchen din ya shigo ya ajiye ledan hannunsa yace "Good evening Halysaah" Tace "Ina yini?" Yace "Lafiya lau, Are you baking?" Ta kalli flour din da take kokarin kwabawa tace "No" Yace "What are u using flour for?" Bata yarda su hada ido ba tace "Dan wake" Da mamaki yace "Meye shi?" Ta wani kallesa ganin da gaske jiran amsarta yake tace "Dan waken ne baka sani ba?" Yace "Ban san shi ba" Tace "Toh zaka gansa" Turning stick ta dauko ta fara kwabin danwaken shi dai yana tsaye yana kallo, yace "Hey, why did it change to that color? Ko dai ba flour bane?" Ta ɗan kallesa amma taki basa amsa, yana ta kallo with astonishment har ta gama kwabin, sannan ta wanke hannu ta fara saka dan waken a ruwan dake tafasa kan gas, shi dai kallonta kawai yake, can yace "To haka ake cin sa?" Tace "Aa da bread ake ci" Sounding amused ya kalli sauran bread din dake a kitchen din yace "Really?" Bata san sanda tayi murmushi ba batare da ta sake ce masa komai ba don taga da gaske ya yarda da Bread za a ci ɗan waken, he couldn't stop looking at her and the food har ta gama, ya ga ta soya man gyada, sannan tayi dishing din abincin a plate, ta saka eggs din da ta bare a gefe, ta dauko roban yaji, yace "Dama wai wannan abincin ne? To ai na san sa when i was a kid, idan munje wajen Grandma dinmu tana mana" Without looking at him tace "Da ka girma ne ka dawo America ka mance sa kenan" Dariya yayi ya karasa cikin kitchen din yace "Ohk, Can i taste some inji yanda yake?" Komawa gefe tayi bayan ta saka cokali a danwaken, ya dau cokalin ita dai kallonsa kawai take har ya ɗan juya ɗan waken ya debi seed biyu ya kai baki, she couldn't stop looking at him yana tauna abincin gently as if trying to figure out the taste, can ya karyar da kai yace "It's nice, i like it, i still remember the taste, it's nice" Murmushi kawai tayi, ya sake diban abincin ya kai baki, tace "To kaje da shi, i will make another one" Yace "Aa bazan iya cinyewa ba ai" Yana fadin haka ya dauko wani plate din ya debi ɗan kadan a ciki yace "Thank you" Ta karasa ta amsa cokalin a hannunsa ta kara masa ɗan waken ta saka masa kwai daya, ya kalleta ya ɗan bude ido yace "Thanks Halysaah, but seriously I can't finish all this" Tace "Eat and remain" Ruwa ya dauka a fridge ya fita daga kitchen din. Khaleesat na idar da sallan Isha'i ta fito parlor zata dafo black tea don tana son tayi karatu har zuwa karfe dayan dare, tunda ta shiga daki daxu da yamma bata sake fitowa ba sai lkcn, bacci ta tarda Housemate dinta yake yi a 3 seater, da mamaki take kallonsa ganin wai bacci yake bayan Isha'i, ita bata ma san yana gidan ba sai yanzu da ta fito, kallon wayarsa dake gefensa tayi ganin yana haske, ta leka screen din taga an rubuta A-jay, kiran na katsewa taga 5 miss calls aka yi masa, kamar ta tashesa sai kuma dai bata yi hakan ba, ta dau wayar kawai tana dubawa taga babu password balle pin a jiki, cire wayar tayi a silent mode sannan ta mayar inda ta dauka tayi wucewarta kitchen, ta gama dafa shayi ta fito parlon kenan taji wayar ya fara ringing loudly, da kyar ya bude idanuwan sa, ita dai ta koma kusa da kofar kitchen din ta makale a jiki, ya ɗan kalli wayarsa ya jawo yana duba screen din, ɗaga kiran yayi ya kai kunne yayi shiru har sannan yana lullumshe ido, can ya ja tsaki ya ajiye wayar sannan ya mike zaune, har sannan bai ganta ba ita ma bata bar jikin kofar da ta makale ba, mikewa tsaye yayi daga karshe yana lumshe ido, gani tayi kamar baccin yake yi a tsayen, ta wara ido tana kallonsa with shock , sai da yaga ya kusa faduwa sannan ya bude idonsa sosai, ta kai hannu bakinta saboda dariyar da taji ya taho mata, tafiya yayi ya isa jikin pillar dake parlon ya jingina ya rufe ido, kasa daina kallonsa tayi da mamaki, he stood there for almost 3 minutes yana bacci, ringing din wayarsa ne yasa ya bude ido da sauri as if frightened, kitchen ta shige don bata son yin dariyar da ya taho mata a wajen, sai a sannan ya ganta bayan ta shige kitchen da sauri, ya fara bin parlon da kallo as if trying to understand what was happening, lkci daya idonsa yayi clearing gaba daya ya fara sosa kai, at first bai yi niyyar bin ta kitchen din ba, can kuma dai ya nufi kitchen din, ta ajiye kofin shayin hannunta ta dafe cabinet tana dariya ciki ciki, tana ganinsa ta hade rai tana juya shayinta da cokali as if nothing happened, fridge ya bude ya dau ruwan gora yana kallonta yace "You are still awake?" Ta ɗan kallesa tace "To karfe nawa ne yanzu da zan yi bacci, as if i am you" Bai ce komai ba ya fita daga kitchen din, murmushi tayi ta bi sa da kallo, daukan shayin tayi ta bi bayansa, taga ya dau makullin motarsa da waya without looking at her yace "Good night Halysaah" Bata san sanda tace "To kar fa kaje kana driving bacci ya dauke ka a kan steering" Bai kalleta ba sai murmushi da yayi kawai ya nufi kofa, ta bi sa da kallo har ya fita sannan ya kulle kofar ta waje, karasawa kusa da window tayi ta ɗan bude curtain kadan tana kallonsa har ya shiga motarsa a garage yayi reverse, sai da ta daina hangen motarsa sannan ta sake curtain din a hankali, tafi minti uku a tsaye wajen ta jingina da window, daga karshe tana tafiya a hankali ta wuce dakinta bayan ta kashe wutan parlon..... Washegari Khaleesat na sauka daga Lyft bayan ta dawo school taga motar Housemate dinta heading toward the garage, kafin ta karasa apartment din nasu har ya shiga ciki, murda kofar tayi taji a bude ya bar mata alamar ya ganta shi ma, tana shiga parlon yana fitowa daga kitchen rike da Lemon gwangwani me sanyi, ya karaso cikin parlon yace "Are you just coming back from school?" Gaishesa tayi, yace "Good evening Halysaah" Bedroom dinta ta wuce ta bar sa a parlon, it's almost 6pm na yamma kuma Safiyyah ce ta bata masu lkci tana mata bayanin wani course dinsu da tace bata ganewa, wanka Khaleesat tayi ta sauya kayan jikinta zuwa kananun kaya sannan ta saka hijab ta fito parlor, yana parlon har sannan yana operating laptop dinsa, ganin zata shiga kitchen yace "Ki bari ki hutu, zan fita sai na siyo abinci" Khaleesat ta kallesa tace "I am cooking noodles" Yace "Ohk then" Tana fadin haka ta wuce kitchen, Ya mike ya wuce dakinsa da laptop dinsa, cikin mintunan da basu da yawa Khaleesat ta gama dafa noodles din da take, ba da yawa ta dafa ba don bata san ko zai ci ba, zata yi dishing din abincin a plate taji ana knocking kofar parlor, ta ajiye plate din hannunta sannan ta fito daga kitchen din, Housemate dinta ta gani har ya fito shi ma to check on who is at the door, amma ganinta kawai ya juya ya koma dakinsa, karasawa tayi ta bude kofar, lkci daya taji komai ya tsaya mata cak ta dinga kallonsa babu ko kiftawa kamar ranan ta fara ganinsa, Yana kallonta daga sama har kasa yace "Meye kike kallo na haka Malama?" Tayi wani yake zuciyarta na bugawa tana in-ina da kyar tace "Ya Abdul, I.. I.. was surprised, san..nnu da zuwa" Da sauri ta juya ta koma parlon, ya bi bayanta yana duba wayarsa dake vibrate a hannunsa alamar ana kiransa, ita dai ta koma bayan kujera ta tsaya kamar munafuka tana kallonsa zuciyarta na bugawa sosai, kana ganinsa kasan ba a lkcn ya shigo America ba, probably tun daxu ya shigo ya sauka hotel, ya ɗaga kiran da ake masa ya kai kunne, tana ganin haka ta juya ta nufi corridor din dakunan apartment din tana waige waige, ganin attention dinsa na kan wayar da yake ta bude kofar dakin Housemate dinta ta shiga da sauri ta kulle kofar, Housemate dinta ya juya yana kallonta da mamaki, gaba daya a rude take ta nufesa tana yarfe hannu ta duka kusa da shi, ya mike still looking at her with surprise yace "Are you alright Halysaah?"
07087865788✍🏻
[5/7, 6:25 PM] khaleesat Haiydar 📚✍️: ✨✨ HALYSAAH ✨✨
By _Khaleesat Haiydar_✍🏻
10.....
Khaleesat ta gyada masa kai tana rufe bakinta da hannunta murya can kasa tace "Plss i have a visitor, i want u to plss pretend you are not staying here, just pretend u came to drop some books for ur Female friend living here plssss" Kamar zata yi kuka ta kare maganar tana kallonsa, yayi shiru shima yana kallonta at first, sai kuma yace "As in how Halysaah?" Ta marairaice masa tace "Kawai dai kayi kamar ba a gidan nan kake ba don girman Allah ka rufa min asiri, u know my former housemate mace ce, act as though u are her friend, kayi kamar wajenta ka zo pls, don Allah ka taimake ni" Bata jira cewarsa ba ta mike ta juya da sauri ta fice daga dakin kafin Abdul ya biyo ta, ya bi ta da kallon mamaki baya ko kiftawa, can kawai yayi murmushi ya zauna ya ci gaba da abinda yake yi a Laptop dinsa, parlor Khaleesat ta dawo suka kusa cin karo da Abdul da ya nufo corridor yace "Me kika je yi a ciki? You didn't even get me something to drink" Ta ɗan yi murmushi a hankali tace "Why didn't you let me know u are coming? Me yasa baka gaya min zaka zo ba?" Yace "Sai na gaya maki in zan zo? Ko ke zaki biya min ticket din jirgin?" Ta girgiza kai cikin sanyin murya tace "Aa ba haka nake nufi ba, ya hanya?" Yana kallonta daga sama har kasa yace "What is wrong with you, why were you sick?" Ta sauke manyan idanuwanta kasa a hankali tace "I don't know too, but i am much better now, naji sauki Alhamdulillah" Yace "Rashin lafiyar ne yasa kika dena daga kirana all this while?" Ta marairaice masa tace "Don baka san yanda nake ji bane a sannan, let me get you water to drink" Daga haka ta wucesa da sauri, ya bi ta da kallo har ta shiga kitchen, Khaleesat ta jingina jikin cabinet din kitchen din ta dafe kirjinta that was heaving so fast, after few seconds ta sauke numfashi sannan ta dau tray ta bude fridge ta dauko ruwa da lemo da glass cup sannan ta fito daga kitchen, zaune ta gansa a parlon yana danna wayarsa, ta karasa ta duka gabansa ta ajiye masa ba tare da ta bari sun hada ido ba, shi dai tunda ta fito kitchen din yake bin ta da ido, ta zauna kan carpet ta tankwashe kafarta ba tare da ta bari sun hada ido ba tace "Ya su Mumy da Daddy?" Jin yayi shiru ta daga idanuwanta ta kallesa taga kallonta kawai yake, a hankali ta sauke idonta kasa, yace "Duk kwana biyun nan kin canza Baby, you don't look critically ill da har zaki kasa daga kirana, menene yasa kika dena kirana kuma idan na kira ki ki dagawa? Common WhatsApp kin dena min magana yanzu" Ta kasa kallonsa, tana wasa da gefen hijab dinta a hankali tace "To kwanan nan sai kayi ta min fada ta waya baka considering dina, ga kuma course dinmu da wahala ka sani" Ita kanta ta rasa dalilin da yasa hawaye ya cika idonta, He let out a sigh har a sannan yana kallonta, sai kuma ya dagota sitting her down by his side, gabanta ne ya fara faduwa, in da akwai abinda ta tsana kuma take fargaba a rayuwarta bai wuce Abdul ya zo America wajenta ba, duk da yawanci zuwan da yake it's either tare da Mom dinsa or his Dad, amma duk da haka a dar dar take da shi saboda wasu abubuwan da ya tsira wanda a baya baya mata haka, duk zuwansa kasar sai ta kirko wani abu da zai maidata unhealthy wani lkcn har sai an kai ta hospital, ita da tasan zai kamo hanya ya taho da bata fara ce ma Safiyyah tace masa bata da lafiya ba, yana caressing fingers dinta yayi kasa da murya yace "But you know i love you Khaleesah, ke ce kike jawowa nake maki fada a ko da yaushe" Ita dai bata ce komai ba hawayen dake makale idonta ya gangaro bisa kuncinta, ya kai hannu yana goge hawayen a hankali yace "Ohk, but you know i love you so much right?" ta gyada masa kai kawai, a hankali yace "Housemate dinki fa? Is she around?" Sosai taji gabanta ya fadi, taki barin su hada ido tace "No ban sani ba, i saw she had a visitor daxu ya zo nemanta, probably her friend...." Yana kallonta yace "Friend? Namiji kenan?" Khaleesat ta gyada masa kai, lkci daya ya hade girar sama da ta kasa yace "Yaushe ta fara kawo namiji gidan? When did that start?" Khaleesat tayi karfin halin cewa "Dama tana kawowa time to time ai but not frequently, sai in kilan sun kawo mata reading materials ko bata da lafiya sun zo dubata" Yace "Kuma mazan na kwana a nan?" Khaleesat ta hadiye wani abu da kyar tace "Ni ban sani ba gaskiya, tunda ina dakina always a kulle ai" Kallonsa tayi to cut short the conversation tace "Na dafa noodles yanzu bari in kawo maka kar ya huce" Tana fadin haka ta mike da sauri zuciyarta na bugawa, dai dai nan Housemate dinta ya fito daga dakinsa, Khaleesat taji zuciyarta ya kusa shigewa cikinta tsabar kidimewa, tayi saurin dauke kai tayi hanyar kitchen, Abdul ya juya jin an bude kofar daki, hada ido suka yi da Housemate din nata da ya shigo parlon yana tafiya slowly waya kare a kunnensa duk da ba magana yake a wayar ba hannunsa daya rike da wani Textbook, idonsa kuma na kan Abdul, hannu ya daga masa calmly yace "Hello" Abdul ya bi sa da kallo babu ko kiftawa without replying to his Hello, shi dai Housemate din nata yana tafiya calmly ya nufi kofa ya fita daga parlon, tuni Khaleesat har ta shige kitchen hankalinta a tashe ta dafe kirjinta tace "Na shiga uku....." A haka dai ta fara zubo noodles din a plate, cike da karfin hali ta dawo parlon, Abdul dake ta kallonta yace "Who is he Baby?" Khaleesat ta ɗan yi fari da ido tace "Ni ban ma taɓa ganinsa ba sai yanxu, Nancy ya kawo ma littafi ina ga" Abdul ya mike yace "Ta yaya zaki dinga rayuwa under same roof da wani gardi Baby? Yaushe Nancy din ta fara shigo da samari gidan nan? All this while dama yana cikin gidan nan?" A hankali Khaleesat tace "Na fa ce maka ban taɓa ganinsa ba, i have never seen him before sai yanzu" Ajiye abincin hannunta tayi cike da karfin hali tace "In dafo maka black tea?" Komawa yayi ya zauna yaki cewa komai, kana ganinsa kasan he is boiling inside, ita dai ta juya tana tafiya kamar munafuka ta koma kitchen, mikewa yayi ya bi bayanta har zuwa kitchen din yace "Ta yaya wani banza can zai dinga shigowa yana kalle min ke anyhow Khaleesah?" A hankali Khaleesat tace "Ya Abdul kar ka manta communal living muke a gidan nan, this is America.... this isn't my apartment alone, bazan iya cewa ga wa enda za su shigo gidan ba tunda ba gidana ni kadai bace" Tsawa ya mata yace "And so what??? An gaya maki bazan iya kama maki hayar gidan ke kadai bane? Banda kince kina tsoron zama ke daya a gida do you think u will be sharing an Apartment with anyone in America? Do u think I can't afford a full apartment for you??" Har jikin Khaleesat ya fara rawa ganin how fiercely he was speaking to her yana huci, ga idanuwansa sun fara sauya launi, sosai take jin tsoron Abdul ita kam, hawaye ya fara gangarowa idonta muryarta na rawa tace "Ka fara kuma ko?" Kamo hannunta yayi fuskarsa a murtuke suka fito daga kitchen din, ta fashe masa da kuka a hankali har suka dawo cikin parlon, cike da fada yace "Ya bazan fara ba naga wani katon banza under same roof with you? Me yasa tun tuni baki gaya min Housemate dinki na shigowa da gardawa cikin gidan nan ba in samar maki other alternative? Me yasa baki da hankali baki da tunani ne ke a rayuwarki?" Zaunawa tayi ta fashe da kuka sosai ta hade kanta da kujera, ya zauna yana huci, ita dai kuka kawai take tana shessheka, after few minutes ya koma kusa da ita ya dagota drawing her closer to him kamshin turarensa ya cika mata hanci, nan da nan ta hadiye kukan da take tana zare ido, Gently yake caressing dinta murya can kasa yace "I am sorry Baby, amma da kin gaya min da na samar maki wani apartment din ai...." Ta fara kokarin komawa baya tana son kwace kanta daga hannunsa, kin saketa yayi a fusace yace "Why do u always act like a Bush gal Khaleesah? Har yanzu rayuwar Ghetto bazai fita a kanki ba? What is the meaning of this nonsense?" Ta ki barin su hada ido, da kyar tace "To ai... This is a promise you made, amma kuma sai ka dinga..." Cikin tsawa yace "So f what if i break the promise? Ko ance maki tsoronki nake ne? Ko kuma wani ne zai aure min ke dama?" Ta marairaice masa kamar zata yi kuka tace "Ni dae bari in kawo maka black tea" zata mike ya fixgota har sae da fado kansa, ya fige hijab din jikinta yace "Naga alamar kin ma maida ni wani gara don kinga ina biye ki" Ta takure waje daya wasu hawayen na taruwa idonta taki yarda su hada ido tana kokarin kwatar kanta daga grip dinsa, skirt karami ne sosai jikinta sai half vest shi sa ma take ta yawo da hijab tun daxu da ta dawo schl, ya sake fixgota sosai jikinsa, kuka ta fara yi muryarta na rawa tace "Don Allah ka bari plss, this wasn't our deal, you are not keeping to ur promise" Kallonta ya dinga yi saboda yanda tayi provoking dinsa, duk da shi bai yi niyyar mata komai ba da ya wuce ya lallasheta amma tsabar yanda ta hasala shi sai ya fara kokarin kissing dinta, ƙin yarda tayi tana kiciniyar kwace kanta tana kuka, House mate dinta ne ya shigo parlon a lkcn, ya kalli yanayin da suke da kuma yanda take struggling din kwatar kanta daga jikinsa, direct ya nufi cikin parlorn har inda suke without a second thought ya cakumo Abdul yana kallonsa da kyau "Hey, this is America guy, what sort of molestation is this??" Mikewa Abdul yayi yana kallonsa da
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 8 Chapter of 16