yake jin ba Adalci bane ayi saki babu dalili. kuma yana duba dangantaka. yace.
"Baba toh ki mun hak'uri zuwa jibi inna huta sai in sake ta. murmushi tayi tace.
"Aliyu ni nai dakon cikinka wata tara. Kaga wad'annan cinyoyin?. ta bugi cinyarta tana nuna mai. tace.
"toh akai ka yi rayuwarka. Har akwai wani wayo da zaka fini kuwa? Toh ka ji na bari sai jibin. Amman inka yi mu'amalar Aure da Sadiya bazan yafe maka ba. kuma zan iya d'aga maka nono akan hakan."
Khadija ta yi wani tsallen murna tare da toshe baki kar su jiyo ihunta. Lallai yau ta sake gasgatawa cewar Goggo tana sonta. kuma za ta ji dad'i a wajanta in ta Auri Aliyu. ta wani b'angaren na zuchiyarta kuma. Cike take da jin zafi da haushin Aliyu. Domun rashin Sakin Sadiya tamkar ruguje maganar Auransu ne."
Aliyu kuwa. Tamkar k'asa ta tsage ya shiga tsabar kunyar da ya ji dangane da furucin Goggo, ita kuwa ko a jikinta. gabanshi ne ya fad'i sosai, ya kasa cewa komai ma. Kawu ne yace.
"Asabe ya isa haka. Yaji kuma sharad'in da kika gindaya mishi. sai mu jira jibin." su Goggo Safiya duk su ka amince akan tai hak'uri zuwa jibin."
jiki a mace Aliyu ya bud'e jaka ya soma ciro tsaraba. su Goggonninshi duk ya mik'a musu nasu. Cikin washewar baki su ka amsa. Kawu ya mik'ama nashi da na matan shi. sannan ya ware na khadija da na Goggo.
Sallama su Goggo Safiya su kai ma Goggo, Dan har goma ta gota. d'akin ya rage daga Goggo sai Aliyu tace.
"Kai da ka je karatu shine har da tsaraba, sai kace wanda ya tafi aiki. naga kayan masu tsada.
"murmushin dole Aliyu ya k'ak'aro. Dan a halin da yake ciwo kanshi ma yake yi. Goggo ta caza mai kai da kalamanta.
"Da yake suna biyanmu kud'in abinci. kuma Aikin ma in mun samu muna tattab'awa. Karatu zanci gaba dayi inaso in shiga kuma jami'ar boko in had'a digiri a fannin daya dace." Goggo tace.
"Ina karatu kam ka yi na muhammadiyya Amma wallahi indai ni ce uwarka baka isa kayi wani dagiri a boko ba. Allah ya amfana wannan d'inma.
"Ameen" kawai ya ce mata. sannan ya ce.
"Baba ni zan tafi in kwanta duk na gaji. ko jiya da muka sauka a Abuja banyi wani baccin kirkiba. Kaina na ciwo." Khadija Goggo ta shiga kwad'ama kira. Cikin hanzari khadija ta fito falon tana wani sulkui da kai. Goggo ta mik'e ta ce.
"Nizan ta fi in kwanta bacci ya dame ni. khadija kam ya kamata ka bata lokaci kuyi hira sosai. An dad'e ba'a had'uba."
tana kaiwa nan ta shige d'aki. Aliyu kuwa baiji dad'in hakan ba. koba komai ya kamata ya daraja Sadiya tunda dai matar shi ce. kuma 'yar uwarshi."
khadija sai b'are b'aren jiki take yi. Tana jera mishi kwanukan Abinci a gabanshi. ciki harda kular abincin Sadiya.
"Ali na. ga abinci sai wanda ranka yai maka. Amma wannan shine abincin da na dafa maka da hannuna." ta nuna mishi kwanon.
murmushi yai mata ya zuba mata idanunshi, bin jikinta kawai ya ke yi da kallo. yanda ta xama mace har mamaki abun ya ke bashi. yana son khadija a cikin ranshi sosai. domun da sonta ya reni jaririyar zuchiyarshi har ta girma. lumshe idanu yayi yace.
"Dije na nayi kewarki sosai." fari ta yi da idanu tace.
"amma ai na ji ja in jar da ka gama yi a falonnan akan tsohuwar matarka. ni na zaci ko ka daina so na ne ma. harna soma fargabar ta yanda jaririyar xuchiyata zata rayu ba mai rainonta."
gyara zama yayi ya fuskanceta da kyau.
"Dije na. Babu wani namiji da zai so ki irin rabin son da na ke yi miki. Bazan bari ki subce mun ba. ai bazan iya gudanar da rayuwa mai dad'i ba. ko kin manta da sonki na ke rayuwa.? Nan su ka shagala a soyayya. Suna yi ya na cin abincin da khadija ta kawo mishi. Har sha biyu na dare bai sani ba." Da kyar su ka yi sallama da juna. dan ji ya ke yi kamar ya rungumeta su kwana a waje d'aya. ya kasa d'auke idanunshi akan khadijar. domun ta kara mishi wani kyau ne na musamman.
Da sallama ya shiga cikin b'arayin na shi, wanda khadija ce ta nuna mishi ma wajan.
Babu motsin kowa.
tura k'ofar d'akin yayi gabanshi na dokawa."
mrs Bukhari ce
*GAWURTATTU BIYAR,5🤚TAFIYAR TA MUSAMANCE*
1, *MU GANI A ƘASA..🔥*
_Ummu Affan_
2, *ABIN CIKIN ƘWAI..🥚*
_Ummu Maher_
3, *GUNTUN GORO..*💥
_Mom Islam_
4, *GISHIRIN ZAMAN DUNIYA*🌎
_Mrs Bukhari_
5_ *AUREN WATA TARA👩❤️👨*
_Miss Hajo_
Guda ɗaya N300
Guda biyu N500
Guda uku N600
Guda huɗu N700
Guda biyar 1k
*ZAKU TURA KUƊINKU TA WANNAN HANYAR👇*
Fatima Rabiu Sunusi
0037219728
StanbicIBTC Bank.
Shaidar biya tanan 👇
0810 433 5144
Masu tura katin MTN👇
0814 179 9224
...........🥚👩❤️👨💥🌎....
*ƳAN NIGER GA HANYOYIN BIYAN KUƊINKU👇
Guda biyar 1000f
Guda huɗu 700f
Guda uku 600f
Guda biyu 500f
Guda ɗaya 300f
Kai tsaye ku tura da katin Airtel ta wannan number 08141799224
*MUN GODE DA KASANCEWA DA GAWURTATTU TAKUN FARKO*
*GISHIRIN*
*ZAMAN*
*DUNIYA*
_Daga Al'kalamin_
_Badi'at Ibrahim_
( Mrs Bukhari Ibrahim B4B)
Labari wanda yai duba kan gwagwarmayar mata a duniya. Da irin gudummawar da ilimin mace ya ke bayarwa ga al'umma. Da kuma rawar da ilimin mata ke takawa a cikin gidajen Aure.
Kashi na 1
Babi na 17~18
Falon ya turo ya shiga. k'arema falon kallo yake ta yi. komai tsab ga k'amshin sabunta da falon ya ke yi, ga kuma k'amshin turaren wuta na hulut sai tashi yake yi a d'akin. Mamaki ya ke ji. Yau shine ya Auri Sadiya yayarshi, kuma duk kyan d'akinnan nashi ne. k'ofar d'akin da Sadiya ta ke ciki ya tura, cikin fad'uwar gaba. Yana son shiga Amma yana jin nauyinta sosai.
Sadiya
Da sauri na share hawayena, nai saurin kulle idanuna. Kunya na ke ji in sake ma ganin Aliyu." Da sallama a bakinshi ya shigo. A cikin zuchiyata na amsa mishi sallamar tashi. gabana sai sake tsananta bugu ya ke yi. Tamkar wacce aka kama ta yi k'arya. Ajjiyar zuchiya na ji ya sauke da bansan ta meye ba. shiru ya na tsaye a inda ya ke. Amma ina jin tsinin idanunshi a jikina. Da dukkan alama k'arema surata kallo ya ke yi." k'ut ya had'iye tsinkakken yawunshi da ganin surata ya tsinka shi. tudun kirjina kawai ya ke bi da kallo ba ko k'ibtawa. ina kallonshi ta k'asan idona. sai ajjiyar zuchiya ya ke saukewa a jere a jere.
Aliyu kuwa tunda yai arba da Sadiya a kwance cikin goduwar rigar bacci, a take ta kwance shi. surarta wacce ta tsaru ya ke kallo. bai tab'a ganin cikakkiyar mace mai cikakkiyar sura irin Sadiya ba. kirjinta yafi komai jan hankalinshi. yana hangosu ta cikin riga suna k'ara burgeshi. lumshe idanu yayi.
Sadiya.
Ni kuwa duk halin da ya ke ciki ina gani. kallo na kai kan wandonshi daya cika yai fam. har wani danshi na gani a jiki. Da sauri Aliyu ya juya ya fice a d'akin. akan kujera ya zauna tare da dafe kan shi. mararshi na wani juya mishi.
Ajjiyar xuchiya na sauke. Kwanciyata na gyara tare da juya ma k'ofar shigowa d'akin baya. amma abun takaici da haushin na kasa samun bacci sam. damuwowin da su ke damuna yawa garesu sosai.
Aliyu
kwanciya Aliyu yayi a saman kujera. ya na rik'e da mararshi. Bai tab'a jin wani abu mai zurfi haka game da mace ba sai akan Sadiya. lumshe idanu yayi. hoton kirjinta suna sake haska kansu a cikin duniyar tunaninshi. mararshi ya kuma rik'ewa sosai tare da sakin nishi a hankali. A cikin daren dai daga Sadiya har Aliyu Babu wanda ya runtsa. Hakanne yasa su ka wayi gari da matsanancin ciwon kai mai zafi. Sadiya har bata iya bud'e idanunta da kyau.
Sadiya
kiraye kirayen Sallar Asuba ne ya mik'ar dani daga kan gadona. fitowa na yi falon. Aliyu na gani a kwance a kujera Bacci ya fisgeshi. wandonshi na bi da idanu. sai da gabana ya buga. A take tsoro da fargaba ya kamani. Maganar Amina ce ta fad'omun da tace NAMIJI BAYA KAD'AN naga halama. bud'e idanu Aliyu ya yi fes a kaina. Akan kirjina idanunshi ya sauka. Ni kuma duk na dibibice dan kunya. cikin in ina nace.
Dama dama naji za'a shiga Sallah ne. shi ne ka je masallaci."
" Toh" kawai ya iya ce mun. Da sauri na wuce band'aki na d'auro Alwala na fito. ina shiga Falon Aliyu ya mik'e ya fita."
Sallah na soma yi. Ina jiyo fitar shi daga gidan.
Aliyu
yana tafe ya na tunanin taya zaije d'akin Goggo ya ce ta bashi kaya zai sake da asubar nan? Gashi bazai iya zuwa wajan kamilu ya ce ya bashi kaya ba. Dan hakan tamkar tona asirin auren su ne. Duk da dai Kamilu ya zarce aboki a wajanshi. Amma wannan wani sirrine da yake a b'oye. hakan cikin taraddadin abunda zai faru yai k'undunbalar shiga b'arayin su Goggo. tura k'ofar d'akin Goggo ya yi a hankali tamkar b'arawo. A falo ya samu Goggo idar da sallarta kenan. da sauri ya tsugunna dan karta kama danshin dake jikin wandonshi, wanda ya fito ta cikin jallabiyar jikinshi, ga Jallabiyyar ta kunbura. kai ya sauke kunya ta lullub'eshi ya ce.
"Barka da Asuba Baba Ina kwana?" Harara ta zabga mishi tana bin yanayin da ya zo mata da kallo. cikin zargi tace."
"Ka aikata abunda na haneka da aikatawa ko k'usar yak'i?" Kuka ta fashe mai da shi tace.
"wallahi tsinema zan yi insan na sallamama duniya kai. Da kuma Sadiya. Sai ka koma.Aisha ta zama uwarka." bakinshi na rawa ya ce.
" Babu abunda na aikata. wallahi a falo ma na kwana." Ajjiyar zuchiya ta sauke. dan tasan Aliyu ba ya k'arya. Balle kuma ya rantse ma. Tace.
"Akwatin kayan na ka ya na can an kaima ita Sadiyar."
"Toh" kawai ya ce.
"Aliyu" ta kira sunanshi da manyan bak'i. Harya kai bakin k'ofa ya tsaya.
"Kar ka manta gobe da safe ka tawo mun da takaddar sakin Sadiya. karka shigo sai da takaddar."
Bai ce komai ba ya fita. Da sauri ya wuce b'arayinsu. Hasiya ce ta bishi da harara.
Sadiya
ina zaune ina karatun Qur'ani cikin suratul maryam. ya shigo da Sallamar shi. A hankali na Amsa. Kaina na k'asa na ce.
"Barka da asuba an tashi lafiya?. Jin dad'in shi har ya kasa b'oyuwa a fuskarshi. cikin kulawa ya ce.
"Lafiya lau Anty. Amma bari na yi sallah sai in zo mu gaisa a tsanake." Wajan Akwatinshi da ya gani a gefen sip ya wuce.
Jallabiya ya zaro da wandonta. Sannan ya koma falo ya wuce band'aki yayo wanka. Sallah ya yi. Mik'ewa yayi. ya soma nad'e kayan na shi. Daidai fitowata. Ahankali na ce.
Dama ka barshi." Da murmushi ya ce.
"Babu damuwa Anty. Zo ki zauna mu gaisa." dukkan mu a kunyace muke magana. Amma kasancewar shi namiji ne harya soma sakewa.
Zama na yi a saman kujera. Na yi shiru ina sauraronshi. Shima shirun ya yi. Sallamar da aka doko a bakin k'ofar d'akin ce ta katse shirun.
Anas ne. Da dauri Aliyu ya fita.
"Yaya Anas? Rungume juna su ka yi cikin tsananin murna. Anas ya d'agoshi daga jikinshi ya ce.
"Aliyu kaine ka zama babban mutum haka? kai kawai ya sosa yana dariya.
"Yaya naga kowa amma banda kai da yaya Dauda."
"Kaidai ka bari. masu sayan hatsine daga Zamfara su ka shigo. Shine mu ka tsaya a kansu sai da aka gama komai. Ni da Dauda mu ka lissafi. Kusan buhu talatinne ba mu samu ba. Ana yawan yi mana satar da ba mu da masaniyar ko waye a cikin gidannan. Ni da Dauda ne ke rike da makullin rumbun."
"Aliyu ya ce idanu za'asa sosai Yaya. Tunda dai a cikin gidane. Kai amma ko waye ke yin wannan b'arna bai kyauta ma kanshi ba. mu shiga daga ciki mana Yaya."
"Wanne ciki kuma? tsarabata kawai za ka bani malam." Dariya Aliyu yayi. Tare da zura takalma yace.
"muje tsaraba na d'akin Baba ai. Su murtala suna almajirci har yanzu basu gama ba ko? Ficewa su ka yi a gidan nawa. sai da na dena jin muryarsu sannan na mike.
Kitchen na nufa. Na yi tsaye ina tunanin shin mai zan girka a matsayin abincin safe?" shiru na yi can sai na tuno bari kawai in dafa kuskus tunda bani da d'anyen kayan miya a hannuna. cikin k'ank'anin lokaci na dafa kuskus dina. Ta yi warawara sosai abun sha'awa. kula na sake farkewa na zuba ma.Aliyu. ruwan wanka na d'aura minti goma yayi akan wuta na juye. Rishon na rage tare da d'aura dumamen miya.
Cikin minti Talatin na gama kintsawa. ina sanye cikin wata jar atamfa hightaget. Dinkin diga da siket. Atampar ta amsheni sosai ta kuma dace da kalar skin dina. Dan jan abu na haska bak'i sosai. Kitchin na koma na kashe miyar. zubawa na yi a cikin kular Aliyu ta miya. Sannan na zubama Goggo Asabe nata. a basket na jera komai. takalmi flat shoe ne ja a k'afata. bak'in mayafi na yafa. Sabida atamfar da bak'in kala akai mata ado.
fitowa na yi babban tsakar gidan. Da Hasiya na ci karo ta na k'arema takuna kallo. Shewa na ji ta yi tace.
"Allah ya wadaran naka ya lalace. An salwantar da budurci dole a fito babu d'ingishin komai. Mu kuwa a ranar da komai ya faru munfi sati muna jinya." Da sauri na dubi Hasiya. Tana rik'e da k'ugunta da ganin fuskarta a cike take da ni. Karasawa nayi har inna take nace.
Wannan jahilcin naki ya soma isata. Ya kamata kisan ni ba sa'arki bane, sannan ni ba kishiyarki bace balle in zama abar tsokanarki. Ya isheki na Fad'a miki kenan.
Tafi Hasiya tayi tace.
"ke ce dai jahila wacce ba ta san me ke yi mata ciwo ba. wacce ta kasa auruwa a maraya kawai. Kuma ki sani duk wani wanda ya ci ciwo da ni miya yasha."
"miyar ma bazai gane ya sha ba. "Wato ke Sadiya rashin kunyar taki har takai ki zagarmun mata a matsayinta na matar.wanki? Dauda ke magana daga bakin k'ofarshi.
"Toh ki sani mu a gidannan baza mu d'auki raini da iskancinnan naki ba. Maras kunyar kawai. Ai dama barewa baza ta yi gudu d'anta yai rarrafe..... Kafin ya idasa na daka mishi tsawa.
"Dakata cin kashin ya tsaya iyakar kaina. Kar ka kuskura iyayena su shigo. Dan zamu yi uwar watsi. iyayena sunfi mun kowa da komai a daniya." Da sauri Dauda ya nufoni Banyi Aune ba na ji saukar hannunshi akan fuskata ya zabgamun marin da saida idona ya makance na wucin gadi. ya sake d'aga hannu zai sake sauke mun . Da sauri na tare fuskata Ina jiran inji a inda hannun nashi zai sauka. sai na ji shiru. Ahankali na bud'e idona. Aliyu ne a tsaye ya had'e ranshi hannun da Dauda ya d'aga zai mare ni Aliyu na rik'e da shi. Rannan nashi a murtuke.
"Ba daidai bane dukan mata. Balle macen da take matar Aure. Danme za dukar mun mata? Bakasan darajarta bane ko me? Ina daraja matata bazan ba da wata k'ofa da za'aci kashi a kanta ba, domun a k'ark'ashin kulawata take, kuma hakkinane kula da mutumcinta. Kai wane girmanka ya dace ka rik'e. Dauda ya fisge hannunshi ya na nuna Aliyu da yatsa jikinshi har rawa ya ke cikin d'aga murya ya ce.
"Akan wannan karuwar 'yar bokon ka rik'emun hannu a matsayina na Yayanka. Kuma ba tare da ka yi tambaya akan wanne irin rashin kunya ta yi ba?" Bilkisu ce ta fito dan taji ana hayaniya har da ihu. Ganin abunda ke faruwa ne ta zame jikinta.zuwa b'arayin Goggo Asabe ta sanar mata. Ta wuce wajan kawu ta sanar mishi.
Aliyu ya rintse ido, dan kalmar karuwa ta gigita tunaninshi ya ce.
" Babu buk'atar sai na ji me ta yi maka. Amma ai kasan ba matarka bace. Matata ce kuma inasonta duk karuwancinta. Domun y'ar uwata ce ita, Anty bakiji ciwo ba ko?."
"Ai kuwa wallahi baka isa ka ci gaba da zama da ita ba yau ba sai goben ba Auranka da Sadiya ya k'are." cewar Goggo Asabe wacce ta iso ita da kawu da matanshi. Gabana ya yanke ya fad'i take na soma zubda hawaye. Isowa ta yi gabana tace.
"Makirar 'yar duniyar mace. Harkin juya mishi kai kenan yau k'usar yaki ne ke yin fad'a. Fad'anma da wanshi. yaron da ya samu shaidar jama'a a gari bai tab'a fad'aba. Shine da zuwanki kin soma haddasa husuma ko. Kinaso ki raba shi da danginshi kamar yanda uwarki ta raba mu da d'an uwanmu. wallahi Allah ba ki isa ba." Nidai ina tsaye jikina har rawa ya ke yi. Aliyu yace.
"Baba zuwa na yi na tadda ya mareta fa. me yasa zai d'aura hannu a jikinta matar Aure ce fa."
"Auran wa? kama daina kallonta a matsayin matar Aure dan indai nonona kasha toh sai ka saki Sadiya yau d'innan ta koma wajan muguwar uwarta." Kawu yace.
"Ke Sadiya ba su fad'a miki doka da tsarin gidannan bane akan girmama kowa ba? kuka na ke yi sosai kukan da ba na ma iya ganin kowa. cikin shesshek'a kuka na ce.
An fad'amun. Amm"
"Dakata Sadiya iyakar abunda na tambaya kenan. Dauda ya ce.
"kuma fa fitowa na yi sai na ji ta na zage Hasiya. Har da ma Goggo Asabe. Shine daga magana ta hau zagina. kuma ita ta soma marina." cikin kururuwa Goggo da Fatima su ka rufu a kaina da duka kakaf kakaf. ina tsugunne ina kuka. ko yunk'urin guduwa na kasa yi. Aliyu duk ya bi ya rud'e Goggo ya ke ta ba hak'uri. Amma ta k'i fur. Sai da tai mun lis bakina da hancina duk sai yayyon jini ya ke yi sannan ta na huci tace.
"Shegiya maras kunya fitsararriya. kai kuma ka kawo takaddarta yanzu ina jiranka ko kaga mai zai biyo baya. Shashasha mai fad'a akan macen da bata cancanta ba." Fuuu ta fice a gidan. Kawu kuma ya ce.
"Kai Dauda kar ka sake dukanta. Kome ya faru ka kawo gaban manya. Kai kuma Aliyu ka bi umarnin mahaifiyarka kar tai ma baki."
watsewa kowa ya yi ya barmu. Zuchiyar Hasiya da Bilkisu fes dan murna. Aliyu ya zuba mun idanunshi da suka kad'a su ka zama jawur, tausayina tsantsa na gani a idanun Aliyu, kuma ko ba komai ya daraja auranmu, ya kuma kira ni matarshi. Wani sanyi naji a zuchiyata.
mrs Bukhari ce
*GAWURTATTU BIYAR,5🤚TAFIYAR TA MUSAMANCE*
1, *MU GANI A ƘASA..🔥*
_Ummu Affan_
2, *ABIN CIKIN ƘWAI..🥚*
_Ummu Maher_
3, *GUNTUN GORO..*💥
_Mom Islam_
4, *GISHIRIN ZAMAN DUNIYA*🌎
_Mrs Bukhari_
5_ *AUREN WATA TARA👩❤️👨*
_Miss Hajo_
Guda ɗaya N300
Guda biyu N500
Guda uku N600
Guda huɗu N700
Guda biyar 1k
*ZAKU TURA KUƊINKU TA WANNAN HANYAR👇*
Fatima Rabiu Sunusi
0037219728
StanbicIBTC Bank.
Shaidar biya tanan 👇
0810 433 5144
Masu tura katin MTN👇
0814 179 9224
...........🥚👩❤️👨💥🌎....
*ƳAN NIGER GA HANYOYIN BIYAN KUƊINKU👇
Guda biyar 1000f
Guda huɗu 700f
Guda uku 600f
Guda biyu 500f
Guda ɗaya 300f
Kai tsaye ku tura da katin Airtel ta wannan number 08141799224
*MUN GODE DA KASANCEWA DA GAWURTATTU TAKUN FARKO*
*GISHIRIN*
*ZAMAN*
*DUNIYA*
_Daga Al'kalamin_
_Badi'at Ibrahim_
( Mrs Bukhari Ibrahim B4B)
GAWURTATTU BIYAR 🤚🏻
Labari wanda yai duba kan gwagwarmayar mata a duniya. Da irin gudummawar da ilimin mace ya ke bayarwa ga al'umma. Da kuma rawar da ilimin mata ke takawa a cikin gidajen Aure.
*INA MIK'A SAK'ON GAISUWA GA DUKKAN MASOYAN LITTAFIN GISHIRIN ZAMAN DUNIYA, HAK'IK'A NAJI DAD'IN ADDU'ARKU GARENI. GISHIRIN ZAMAN DUNIYA YA D'AUKAKA FIYE DA TUNANINA, YA TSALLAKA INDA MA BANYI TUNANIBA. TUN JIYA NAKE TA SAMUN SAK'ONNI DA KIRAYE KIRAYEN MASOYANA. INA GODIYA SOSAI, ALLAH YA BAR K'AUNA.*
Kashi na 1
Babi na 19~20
Kallona ya sake yi cikin tausayi da tausayawa. Hannunshi ya saka ya d'agoni tsaye. Tare da jinginani da jikinshi. wani irin shocking mu ka ji a jikin juna. wata wawuyar ajjiyar zuchiya na sauke, tare da haki, ga bakina a fashe sai jini yake zubarwa Hannu yasa rik'e mun k'uguna, ahankali ya soma tafiya. Har d'ingishi nake yi tsabar azaba." Hasiya ta na lab'e ta na cizar yatsa. Domun ko a mafarki Dauda bai tab'a mata hakanba. ko a Zamanin amarcinta Sanda gishiri ya ke kan kaza kenan. Ko yau ta ji mamaki da ya shigar mata fad'a. Dauda ne dake bayanta, inda take a lab'e ya ce.
"malama matsa zan wuce in kin gama gulmar. Da sauri ta saki labulen nata. Tare da sauke kanta.
"Dama nasan ko me ake ciki kece mara gaskiya. munafuka mai ta da husuma. Amma Abokiyar husumarki ta nanan zuwa, 'yar sarkin magulmata." Wucewa ya yi ya barta a wajan tare da ficewa a gidan. Ita kuma ya barta da cizon yatsa.
Sadiya
Ahankali muke ta fe. Aliyu ya jera mun sannu ya fi sau a k'irga. akan doguwar kujerar falona ya sauke ni. Hawaye kuwa bai bar.zuba a idanuna ba. tsugunnawa yayi a gurwarsa ya ce.
"Anty ki yi hak'uri dan Allah da dukkan abubbuwan da suka Faru. Goggo ba ta tsaya ta yi bincike bane, kuma zan d'auki tsattsaran mataki akan Yaya Dauda, bazan bari ya bige ki a banza ba.Amma me ya had'aki da Yaya Dauda?.
A cikin kuka na bashi labarin kab habaice habaicen da Hasiya ta sani a gaba da shi. Har zuwa wanda tai mun yau. Shiru yayi ya na kallona k'ur, kallon da duk shekaruna na kasa fassarashi. na ce.
"Yanxu sakin nawa zaka yi ko?"
Bansan sanda bakina ya furta hakanba. Domun duk abunnan da ake ciki maganar sakin ya girgizani. Ban sani ba ko dan ban jima da yin auran bane. Bana son duniya ta kafa hujja a kaina wajan zagin 'yan boko. Na dai tsinci kaina cikin tsoron SAKI. tunda nai wannan maganar ya ke bina da kallo kawai. Ni kuma kunya duk ta kama ni.
"Bari in hura kara in d'aura miki ruwan zafi ki gaza jikinki. zanje Lamba in siyo miki magani a kemis. Da sauri na ce. Akwai kalanzir a risho. Magani kuma i na da shi a box d'ina."
bai ce komai ba ya fita. hawayen fuskata na share. zuchiyata a cikin zugi da tashin hankali ta ke. Haka
Aliyu
Aliyu ma. Tunda ya d'aura ruwan wankan a kan risho. ya ke tsaye a kitchin din. sai tunanin mafita kawai yake yi. shi bai ji cewar zai iya sakin Sadiya ba. baisan alkhairin dake cikin auran shi da ita ba. Kuma a zahiri Sadiya ta kai macen da ko wanne namiji ya sota, ya kuma ji yana son kasancewa da ita. bugu da k'ari gata 'yar uwa ta jini, wacce bai kamata a yasar da'ita ba.Amm ya na auna kalaman da Goggo ta jefe shi da shi. cewar indai nononta ya sha ya rayu toh dole ya saki Sadiya. Ajjiyar zuchiya ya sauke, ya rasa tudun dafawa, balle makamar da zai kama. Ruwan ya juye mata ya sirka. har ban d'akin ya kai ruwan.
Sadiya
ya shigowa yayi ya sameni da box d'ina da mirro ina dressing bakina da Goggo ta fasa mini. Zama ya yi yana kallona k'uri yace."
"Ashe da likita na ke tare ban sani ba. Kai masha Allah. Murmushinshi ya fad'ad'a.
Bance dashi komai ba. sai da na gama tas nace.
" 'yar koyo dai waneni da likita. murmushi yai mun.
"Ki je ki yi wankan. zan je in dawo yanzu, ina mai baki hak'uri a karo na barkatai, kuma ki sani ina tare da ke." fita ya yi. ni kuma na shiga toilet na dinga gasa jikina dan ko ina ciwo ya ke yi mun, juyayin maganganun Goggo kawai nake yi, cike nake da mamaki. Wai dama ashe haka lalurar jahilci take? Wallahi gara mahaukaci sau dubu akan jahili.
Aliyu
Fitarshi ke da wuya ya zarce gidansu kamilu.
Kamilu ya fito k'ofar gida, Sai kawai ya ga abokinshi a cikin yanayin tashin hankali mara musaltuwa. Dafa kafad'arshi yayi dan bai ma san Kamilu ya fito ba.
"Aliyu lafiya kake kuwa na ganka a cikin irin wannan yanayin, Meke faruwa? Aliyu ya juyo ya kalli kamilu, idanunshi sunyi jawur, ga wani ciwon kai dake addabarshi, hatta d'and'anon yawunshi ya gurb'ace tsabar tashin hankali.
"Kamilu Baba ce ke son birkita mun fissafi na. Waifa magana take yi akan sai na saki Sadiya, kuma ni bazan iyaba wallahi." Hannunshi Kamilu ya rik'o zuwa cikin gidan na