Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
2 / 7
ne?" Zan yi miki biyayya mama, amma mama me yasa za'a tauye mun hakkina, a hana ni ci gaba da aiki na? Aikin ceton rayuka fa na ke yi, mama na d'auki ilimi a matsayin GISHIRIN ZAMAN DUNIYA. asara ne boye ilmi, domun yin hakan bai baka damar ka sha romon ilmi ba. Na sha wuya wajan karatu, babu irin fa'di tashin da ba ki yi ba akan ganin kin cika wasiccin da Baba ya yi miki, sai kin yi kamar za ki fa'di, sai ubangiji ya taro ki. Dangin ki kuma su ka nuna mun soyayyar da su ka tsaya mun kan lammuran karatuna, har na ta ka matsayin da na ke a yau na anguwar zoma. Mama a iya sanina tun mahaifina da ran shi, kawo yanzu, babu wani tallafi ko gudummawar da ta ta'ba fitowa daga bangaren dangin Baba. Asali ma sai tauye hakkinmu da su ka so yi. Sai yanzu da na zama mutum......" Sadiya" mahaifiyata ta kira sunana da murya mai amo. "Za ki yi mun biyayya ki amshi auranki a matsayin k'addarar rayuwarki ko yaya?" Cikin rauni da kuka na ce. Na amince Mama na amshi auran, Allah ya sa hakan shine mafi alkhairi. Amma an dur'kusar mun da rayuwata, ko a addinance ba daidai bane a mai da mutumin daya rayu a maraya kauye, sai dai a fito da na kauye zuwa maraya." Jawo ni ta yi jikinta ta mayar da ni tamkar karamar yarinya shekshekar kukan ta na soma jiyowa, rabon da na ji kuka ko rauni a muryar mama, tun rasuwar Baba. Domun Mama ta kasance mace mai kamar maza jarumar Uwa. Da sauri na dago kaina, na dubeta. Hannu na sa ina share hawayenta, kukan nawa na ha'diye na ce. "Haba Mama kar wannan auran ya d'aga miki Hankalin ki, ki kwantar da Hankalin ki, zan yi muku biyayya, da sannu dangin mahaifina za su yi alfahari da ilimin da ki ka tsaya mun nayi." A maimakon Mama ce za ta lallashe ni, sai ni ce na ke lallashinta. Akwatin sarka da 'dan kunnen azurfata, da kuma da d'an kunnen zinari na ta mi'ka mun. Hannu nasa na amsa ta ce. "Ki rike su da kyau wata rana za su yi miki amfani, bansan ko yau za su ta fi da ke ba, ko sai gobe. Amma zan yi ko'karin zuwa in duba ki Sadiya. Sannan wannan dubu ashirin da biyu ne gudummawar biki da na soma samu daga kawayena. Shi ma ki ri'ke ki ta fi da shi, ki adana shi. Ahmad kuma da zaran an watse taro zan sa Hansatu ta ne mo shi, a ba su kayan lefen su da akwatin su. Sadiya ki na da suttura kar ki matsa sai Aliyu ya yi miki lefe, amma bazan hana ki amsa ba in dai sun yi miki adalci sun ba ki." Cikin murya mai taushi na ce "Amma Mama za'a rake kayan d'aki na ko? Domun za su iya ma in da za'a ajjiye ni yawa." Sunkui da kaina na yi dan wasu sabbin ruwan hawaye ne su ka sulalo mun. Cike da tausayi da kulawa Mama ta ce. "Babu abunda aka rage Sadiya kayan ki ne, kuma abunda bazai sa mu waje ba, bazai wuci kayan kitchen ba domun kitchen a tsakar gida ne na matan gida ba ki d'aya. Hansatu za ta ji da komai." Murmushi na yi ma Mama tare da sauke ajjiyar zuchiya mai k'una, na ce. Toh shikenan Mama. " umarnin sa ke sutura Mama ta ba ni. A ban d'akinta na sa ke yo wanka. Riga da zani na sa ka, na lace d'inkin buba. Lace d'in ya amshe ni sosai. Popul colour ne jikin lace d'in, sai manyan fulawowi da aka zana a jikin lace d'in da bak'in zare. Bak'in mayafi da takalmi mai tsini mama ta ba ni. Bada son rai na na ke yin komai ba. Turare mai k'amshi ta fesa mun a jikina tace. "Ki je ki samu kawayenki Sadiya. Na ji dad'in yanda ki ka shanye duk damuwar da ki ka shiga, tare da rungumar k'addarar rayuwar da dama ba kasan in da za ta gara ka ba. Ki je kar na ri'ke ki." Jikina a mace na fito. Kowa na ta kallona ana fadin "amarya" kunsan amarya ko ta buzuzuce farin jini gare ta. Cikin su Jamila kawayena na koma. Amma tunanina sam baya ma tare da su, su kan ji ina sauke ajjiyar zuchiya minti minti. Ni ba auran dolen da akai mun ba ne ya jefa ni cikin damuwa da tashin hankali ba. Bazan ce ban shiga ru'du ba, amma rashin aikina da karatuna da na ke ganin zai ta shi a tutar babu, ya fi komai caza mun kai na. Lumshe idanu na yi kawai, cikin kan'kanin lokacin jikina ya rincabe da zazzab'in da bibbiyu na ke ganin mutane, kuma na kasa magana sam, ga ciwon son Ahmad na nukurkusar zuchiyata, ga auran Dole da akaimun da k'anina, kuma ake shirin raba ni da maraya, aiki na na fi bashi mahimmanci fiye da komai, dan burina shine in yi suna, na zama fitacciyar unguwar zoma wacce tasan makamar aikinta. Ni dai ban sa ke sanin in da kaina ya ke ba, sai bayan isha, na farka na ganni akan gado na. Ga Mama da 'yan tsirarin dangin mahaifina ciki har da sirikata yar mahaifina Goggo Asabe. Baki ta tab'e tare da cewa. "Tabbb ke da aka taimakama, kin kasa auruwa ke ce wai har da sumewa. Ashe shi k'usar yak'i, in labarin auranku ya ruske shi, mutuwa kenan ya kamata ya yi. Ai ni sulaimanu ya cuce ni da ya ha'da wannan auran. Yaro karami an ha'da shi aure da Babbar macen da ta fishi shekaru da wayo. Ba lallai bane ya samu tantanin budurci ma a jikinta ba, an gama cudanya da maza, har jiki ya 'd'auki warin maza. Ko wannan ya na karya jazbiyyar jikin d'iya mace, ku kuma gani ku ke yi waye wa ce. Abunda namiji in ba mijin auranki bane, ko a kujera ya zauna ya tashi, bai kamata mace ta zauna ba, dan kare jazbiyyarta, sai ta bari kujerar ta huce dan gudun lalacewar jiki. Amma 'yar boko ai ba ta san wannan ba. Maza su ne abokanta, tunda har ha'da hannaye suke yi da maza da sunan waye wa, tur da irin wayewar da ba ta addininmu da al'adunmu kyawawa na hausa Fulani ba." Jina yi gabaki d'aya na muzanta a wajan, jina na ke yi tamkar tsirara. Wai surukata ce ta ke ya'ba mun muggan kalamai irin Wa'dannan tun kafin ma in tare a gidan 'danta. Ashe har zargina su ke yi da salwantar da budurcina? Ni tunda na karaci karatuna bana yawan mu'amula da maza, sau d'aya tak namiji ya ta'ba ri'ke mun hannuna. Ahmad ne, shine ya kafa wannan tarihin a rayuwata. Ni babbar mace ce, na kasance mai k'arfin sha'awa da son jin dumin namiji a kusa da ni. Lura da na yi da yanayi na ne, yasa ba na sake ma maza fuska dan gudun samun wata matsalar. Ko da yaushe a cikin azumi nake dan ganin na kare martaba da k'imata ta d'iya mace. Ashe na shiga ban d'auka ba bata fidda barawo. Mama na kalla wacce ta ha'de girar sama da ta k'asa tace. "Yaya Asabe, bai dace kina jifan 'yar d'an uwanki da irin Wa'dannan alkaba'en ba. Ai ni a tunanina ya ci ace an jinjina ma tawakkalin da ta yi. Maganar kauye fa ake yi, da mutuwar aikinta. Uwa uba yaronnan k'aninta ne, ku.......... Dakata Aisha yayar za ki yi ma rashin kunya, ashe za ki iya zagin Adamu ma?" Goggo Mariya ce ta ke wannan Maganar. Hannuna Mama ta ri'ke tace. "Mu je ki kwanta a d'aki na, ki sha magani sai ki yi sallah." Sum sum sum na bita Goggo Asabe kuwa kamar za ta ari baki tsabar fa'da. Sai hak'uri 'yan Uwa da su ka zo biki daga sauran garuruwa su ke ta bata. Wanka na yi dan in samu k'arfin jikina. Sannan na rama sallolina, na jima ina rokon Allah yasa mun albarka a Aure na, ya kare ni daga dukkan wani sharri, yasa in samu rayuwa da sauk'i. Mama ta saka ni a gaba ta ba ni ruwan tea mai kauri na sha, amma daci kawai baki na ya ke yi. Magani na sha, nasa rigar baccina. Mama tace. "Ki yi kwanciyarki anan Sadiya. Bance da Mama komai ba, domun in nace zan yi magana kuka ne zai balle mun. Kwanciya kawai na yi. Mama ta dinga shafar kaina kamar karamar yarinya. A daren ranar tare da Mama mu ka kwana gado d'aya, ba ta bar ni na yi tunanin komai ba. Allah ya yi dare gari ya waye, yau ne budar kai, kuma yau za'a wuce da ni gidan mijina. *Mrs Bukhari Ibrahim* *GISHIRIN* *ZAMAN* *DUNIYA* True life story _Daga Al'kalamin_ _Badi'at Ibrahim_ ( Mrs Bukhari Ibrahim B4B) GAWURTATTU BIYAR 🤚🏻 Labari wanda yai duba kan gwagwarmayar mata a duniya. Da irin gudummawar da ilimin mace ya ke bayarwa ga al'umma. Da kuma rawar da ilimin mata ke takawa a cikin gidajen Aure. Kashi na 1 Babi na 5~6 A zaune na ke a bakin gadon Mama, a cikin ado da kwalliya na ke irinna amare. Material ne a jikina, d'inkin riga da siket, ja ne jikin material d'in, sai fulawowi da a ka yi ma material din milk colour. Dan kunne da sarka na sanya na azurfa harda awarwaro. K'afata sanye da takalmi me tsinin gaske milk colour. Light make up na yi ma kaina. Bak'a ce ni, amma ba can sosai ba, kuma baza a kira ni da wankan tarwad'a ba. Ba doguwa bace ni, gajerace 'yar duma duma, domun ina da k'iba amma ba can ba, amma ba za'a kirani da siririya ba. k'irjina a cike ya ke dam da dukiyar Fulani tamkar za su tsago rigata su fito. Ina da tudun mazaune sosai, sannan ina da fa'di, wato hip's. Idanuna manya ne kuma farare, sai dan hancina wanda bai yawanta tsawo ba, baki na kuwa leben saman bak'i ne, sai leben kasan kuma mai haske ne, amma ba ja bane. Ba ni da gashi sosai, amma ina kama shi da ribbon sai dai babu wata jela mai yawa, amma ina da cikar gashi sosai, gashin kaina ba ba'ki bane sosai ya d'an sirka da ja ta sama saman gashin, kuma ba mai laushi bane sosai, kuma bana amfani da man k'one gashi. Girata ta na ga gashi sosai, gashin idanuna basu da tsayi sosai amma a cike suke. Mata da yawa suna sha'awar irin k'ira da surar da Allah yai mun, musamman inna juya ina muskuta mazaunaina. Ba ni da tsantsar kyau ta fuska amma diri kam sai dai in ce Masha Allah. Ajjiyar zuchiya na sauke nan ta ke na shiga tunani mai zurfi. Hirar da ta wanzu a tsakanina da Ahmad, a shekaran jiya da daddare, bayan masu sanya ni a lalle sun sanya ni, na shiga tunanowa. Zaune muke a cikin motar Ahmad k'irar Hala. Shagwab'a ya ke ta zuba mun cewar lailai sai na raka shi dubiyar mara lafiya abokinshi, a gidansu. Ni kuma na ce da shi. Ahmad ba daidai bane mu fita tare, domun sai zuwa gobe ne za'a d'aura auranmu, ka d'an k'ara hak'uri ka'dan, zuwa jibi ina gidanka sai mu je mu duba shi. Idanu ya zuba mun ya na ma kirjina wani irin mayun kallo, kasancewar doguwar rigar wani yadi mai laushi na saka, kuma yadin yana la'bewa a jiki. K'irjina sun fito sosai ta cikin rigar, har shatin bra d'ina ana gani. Gabaki d'aya sai na lura hakan ya firgitashi sosai, da sigar lallashi ya ce. "Haba Sadiya ashe ma baki yarda da ni ba har kika amince in zama mijinki gobe?" Da muryar soyayya na ce. Haba Ahmad wallahi na yarda da kai. Ina kare martaba da darajar kaina ne, da ma gidanmu. Kamata ya yi ka ta ya ni. Ha'da idanun da na yi da Ahmad yasa gabana ya fa'di sosai. Sha'awata k'arara na ke karantowa a idanun Ahmad, sai dai na kasa fassara ma'anar launin fuskarshi gabaki d'aya da ta canja. A cikin mak'oshi ya ambaci sunana. "Sadiya" shid'ewa na yi, domun duk illahirin tsigogin da su ke jikina sai da su ka tashi. Ban yi aune ba, na ji hannun Ahmad a cikin nawa. Sai da numfashina ya d'auke na wucin gadi. Da kyar na yi kokawar dawo dashi. Cikin sauri na fisge hannuna, na kuma ha'de rai na. Meye hakan kuma Ahmad, sai da aski ya zo gaban goshi za ka shigo da irin wannan lalatar?" Da sauri na b'alle murfin motar. Wuf Ahmad ya sake rike mun hannuna. A fusace na juyo, kallon dana watsa mai ne, ya sanya ba shiri ya saki hannuna. Ban ko yi waiwaye ba na shige gida, ina ji ya na biyo ni ya na ta aikin ba ni hak'uri, ni kuwa nai kunnen uwar shegu da shi. Da sallama mama ta shigo ta katse mun tunanina. Ta ce. "Sadiya zo ga karin kumallo ki yi. K'awayenki na wajan aiki sun iso, su na jiranki a d'akin ki. Kuma yaya sulaiman ya ce da wuri za ku wuce, zuwa sha d'ayan rana. Waje ba kusa ba." Ban ce Mata komai ba, na amshi karin kumallon na ci da yawa, dan mama ta ji sanyi. Magani ta ba ni na ha'diya. Sannan na fice zuwa wajan su Jamila. ******* Asalin tarihin Sadiya da ahalinta. Malam Buhari mai hula shine sunan kakana, wato mahaifin Babana. Sananne ne sosai a k'auyan su. Domun Allah ya hore mai arziki sosai, ya na da tarin shanu da rak'uma a wannan zamanin sama da guda d'ari. Gonakan shi kuwa sun fi na kowa yawa a kauyan. Gidan malam mai Hula babban gida ne mai k'ofa hudu. Ko yaro ka tara a hanya zai kawo ka gidan. Ya na daga cikin manyan dakatan k'auyan. Matar shi d'aya mai suna Safiya. Yaranshi kuma biyar maza biyu mata uku Kawu sulaiman shine babban 'dan shi, sai Goggo Asabe ita ce mai bi mishi, sai Goggo mariya, sannan Goggo Safiya ita ce ta ci sunan mahaifiyarsu, sai Adamu wato Babana, shi kuma sunan mahaifin malam Buhari mai Hula ya ci, shine d'an auta. Ya taso a cikin gata sosai daga wajan iyaye, har wajan yayyu. K'auyan RAQUMA shine sunan k'auyan da aka haifi mahaifina. Kuma shine k'auyan da zan je zaman Aure. A cikin garin Zamfara k'auyan yake.a kar'kashin 'karamar hukumar MAFARA Kauye ne wanda ya kasance mai cike da duhun jahilci. babu ko asibiti a cikin kauyan. . Sai in gagarumin ciwo ya rabke su. sai a kai mutum mafara local government akwai asibitin gwamnati a wajan, asibiti ne wanda ba su da wadatar kayan aiki, haka ma likitocin ba su da yawa. Ko kuma a shiga k'auyan Lamba a sai magani a kemis, wanda wannan kemis ya kasance shi ka'dai ne a wannan yanki, in kuma ba haka ba dai, sai an dangana da k'auyanTuraita, anan ma akwai wani 'dan asibiti gajiyayye mai su na SHA KA TAFI. Ba su da gadajen ajjiye mara lafiya.Amma abunda jama'ar 'kauyan RAQUMA su ka fi ga ne ma shine. in yara da manya ba su da lafiya. Sai a shiga jeji duk bishiyar da aka soma cin karo da ita a hanya, toh fa ta zama magani, ganyenta za'a debo ayi sirace ma mara lafiyar nan. Kuma cikin amincewar ubangiji sai ya tashi. In kuma gudawa ce ta kama babba ko yaro, kashin giwa za'a debo a jik'a sai a sha ruwan. Kuma gudawan zai tsaya. Daidai da ban 'daki na ba haya , basu cika yi a gida ba. Sai dai su je gonakan su, aciki su ke yi, maza da mata. Ban 'dakin wanka kawai su ke yi a cikin gida. Bangaren makarantar muhammadiyya kuwa, babu sam a wannan zamanin. malami sau d'aya yake zuwa a shekara ya ba da karatu, wanda ya ri'ke ya samu na Sallah, wanda ma bai ri'ke ba a hakan zai yi Sallah. Maganar makarantar boko ma ba'a magana. 'Yan boko tamkar kafurai mutanen kauyan RAQUMA, su ka d'auke su. Babu arabi babu boko haka su ke rayuwa kara zube. Ba su da hasken wutar lantarki sam. Kuma ba su da injinan ni'ka. A turmi su ke daka hatsi, su sarrafa shi ya zama abinci. Mata da kan su, su ke fita su yo karar da za su d'aura sanwa. Ba sa noman masara. Dawa, gero, su ne abunda su ke nomawa. Da yawansu makiyayane. Kuma har yanzu wannan 'kauyan a haka su ke gudanar da rayuwarsu, babu wani canji, ko tallafi da su ka samu, daga b'angaren gwamnati, ko ma daga fararen hular ne. Kakana mai Hula ya ci alwashin ya na so d'aya daga cikin yaranshi maza su kawo canji a kauyan RAQUMA. Amma ko da kawu sulaiman ya ta so, sai ya k'i sam ya ta fi almajirci, ya fi mai da hankalinshi akan Noma da kiwo. Ga shi shine babba a gidan ragamar gidan ba'ki daya a hannunshi take, ga iyalai ya tara. Matan shi biyu, Ladi da Tabawa sai dai a wannan lokacin bai samu magajiba tukunna. Toh sai Hankalin mai Hula ya dawo kan Baba na. Ya na da shekara biyar aka tura shi almajirci. Ya shafe tsawon shekaru sama da goma sha biyu, ya na almajirci. A K'auyan makoli da ke jihar kanon dabo.Har Allah ya amshi ran Malam Mai Hula, burinshi shine Adamu ya yi karatu mai zurfi. Ragamar gidan kacokam ta sake hawa kan kawu sulaiman duk wani kadara ta na hannunshi, kama daga kan gonaki, shanu da rak'uma, har zuwa kan dukiya tsabarta. Sai malamai su ka je su ka samu a garin Zamfara, su ka raba musu gadonsu. Ananne su Goggo Asabe su ka samu gidajen da su ka dawo ciki tare da mazajensu, da yaransu. Kuma gidajen sun kasance a Jere suke reras har guda shidda da asalin family house d'in su. Goggo Asabe yaranta uku. Anas shine Babba, sai fatima, sannan Aliyu. Goggo safiya kuma Allah bai bata haihuwa ba. Goggo Mariya kuma yaranta maza ne guda hu'du, akwai Adamu, Sulaiman, kabiru, sai Dauda. Kawu Sulaiman kuma yaranshi uku, Sajida, Rukayya, Safiya. Babana daya kammala karatun almajircin shi, Kano ya dawo sai ya shiga makarantar boko abu kamar wasa kawai sai ya soma yin yaron shago a kasuwar kurmi. Shagon Alhaji Nuru doron nera mahaifin Mama na. wasa_wasa Baba ya na ta karatun boko, kuma ya mai da hankalinshi sosai. Shine har matakin jama'a. Kakana daya lura Baba mai amana ne sai ya d'auki diyarshi Aisha wato Mama ya aura mishi. Mama na ita ce babba a gidansu. 'Kannenta uku kuma dukka mata. Goggo Hansatu itace mai bi mata, sai Goggo Sadiya wacce Allah yai ma rasuwa, sai Goggo Harira, sai kuma Goggo Binta. Wacce take garin saudiyya da aure. Gidan su Mama 'yan boko ne sosai. Ana yin karatun boko da na muhammadiyya sosai. Mama tasha tsangwama a wajan dangin Baba sosai ba sa kaunarta sam su a tunaninsu ita ce silar da ya sa Baba ya ki komawa kauye. Kuma gani su ke yi, ta mallakeshi ne, kuma ta na mai wayo sabida 'yar boko ce ita. Baba ya yi aiki ne a kar'kashin gwamnati. Haka ma Mama, ma'aikaciyar gwamnati ce. Ni ka'dai Babana ya haifa. Mahaifiyata ta samu matsala a mahaifarta, wanda hakanne yasa ban da k'ane bare wa. Na taso cikin soyayya da gata na mahaifa. Burin Baba shine in zama ma'aikaciyar asibiti. Alhamdullah na cika ma Baba burinshi. Ko da Allah yai mai rasuwa karatuna bai tsaya ba. Da ku'din pension da garatutin Baba na samu na ha'de karatun likitanci na. Sai dai na fuskanci kalubale da dama a rayuwa. A sakamakon k'alubalantar karatun 'ya mace da Malam bahaushe ya ke yi. Hakanne ya kawo mun jinkirin aure. Sau uku ana kawo sadaki na. Daga baya a dawo a kar'ba. Sabida kawai na kasance 'yar boko kuma ma'aikaciya a 'kar'kashin asibitin gwamnati.Wannan shine ta'kaitaccen labarina. Dawowa daga labari Tafiya su Goggo Hansatu su ke ta faman ci. Tafiya yankin azaba. Hadiza ta ce. "Goggo wai da ma Sadiya ba a garin Kano za ta zauna bane? Ni na ga wannan kamar hanyar Zamfara ce fa, ina karanta sunayen k'auyukan da ke kafe a allon kan titi. Sai kuma na ga mu na ta kutsawa cikin k'auye." Goggo Hansatu cikin takaici ta ce. "Gidan Sadiya mu ke zuwa. A wannan k'ungurmin k'auyan k'addarar Aure ta kawo ta." Hawaye ta share tace. "Ahmad iyayenshi sun 'ki amincewa ya Auri Sadiya. Hakanne ya sa dangin mahaifinta su ka ha'da ta Aure da 'dan uwanta. Da gyatumar shi yaron da gyatumin Sadiya Uwa d'aya uba d'aya. Ku yi mata fatan alkhairi kawai." Mamaki da tausayin Sadiya ya hana Hadiza da Amina samun zarafin cewa komai. Goggo sadiya, da Anas kuwa. In kun tanka ku da ba kwa wajan, toh sun tanka su ma. Sai kauyen kawai su ke bi da kallo su na zubar hawayen tausayin Sadiya. Motar su ce ta tsaya a wata madakata wanda a iya nan mota ta ke tsayawa. Sai dai kuma a shiga a kori kura, ko a hau mashin ya shiga da mutum cikin k'auyan. Daga nan madakatar tafiyar mill 7 za'ayi kafin a isa cikin k'auyan. Ga hanyar sam babu kyau. Sakkowa su ka yi daga cikin motar. Goggo Hansatu ta ce. "Lafiya Safiya mu ka sauka anan, Kuma banga gida ba kwata kwata? Anas ne ya ce. " Goggo anan za mu tsaya mu jira motar akori kura, sai mu shiga ta k'arasa da mu. A hakan ma sai dai in yanke za mu bi, wannan hanyar ta mu tayar Babur ce ka'dai ta ke iya bi, da jama'ar da ke tafiyar k'afa. ko kuma ku hau Babur ya isa da ku. Zan shiga motar kayan amarya, mu sai mu bi yanke. Amma k'ananun mota basa iya shiga. Hanyar a lalace ta ke." Salati Goggo Hansatu ta shiga yi ta ce. "Amma Safiya bakwa jin tsoron Allah, da ku ka dakko yarinya a maraya aka dawo da ita k'auye irin wannan. Wannan wanne irin bala'i ne? Dole a warware wannan auran domun Sadiya sai wahala ta kasheta anan. Hmmm wallahi na ga illar auran 'dan cirani wanda ya fito daga kauye. Da ace Yaya Aisha bata auri Adamu ba, da duk haka ba za ta soma faruwa ba." Cikin fa'da da rashin ilimin arabi da boko Goggo Safiya tace. "Hansatu kenan. Sai dai in kece ba kya tsoron Allah. Mu sunnar muhammada Rasulullahi ( S A W) mu ka ha'da. Da k'auyan nan ya na kisa, da Adamu bai rayu har Aisha ta aure shi, ta raba mu da shi ba. Ai matar mutum kabarinshi. Bari ki ji, baki isa ki fa'da mun magana in barki ba, yanzu sai mu da ku." Goggo Hansatu tace. "Toh sai me mu daku mana, mai jaki ma ya ce ai tsere ballantana mai doki? Nanfa rikici mai girma ya 'balle a wajannan. Mata matan wajan da su ka fito cin kasuwar kauye za su koma gida. Su ne su ka raba wannan rikici, da kuma Anas. Hadiza da Amina kasa magana su ka yi, sun tsinke da lamarin. A kori kura

Chapter 2 of 7