Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
1 / 7
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels *GISHIRIN* *ZAMAN* *DUNIYA* _Daga Al'kalamin_ _Badi'at Ibrahim_ ( Mrs Bukhari Ibrahim B4B) GAWURTATTU BIYAR 🤚🏻 TAKUN FARKO Labari wanda yai duba kan gwagwarmayar mata a duniya. Da irin gudummawar da ilimin mace ya ke bayarwa ga al'umma. Da kuma rawar da ilimin mata ke takawa a cikin zamantakewar Aure. Kashi na farko Babi na 1~2 Shinfi'da📖 Kano 7/2/2010 gidan cike ya ke dam da 'yan Uwa da abokan arziki, wanda su ka amsa gayyatar biki na, daga gari gari. 'Yan uwan mahaifina da su ka kasance su ne jigon bikin, kab 'dinsu sun halarci wannan biki nawa. Daga 'bangaren maza a waje 'yan daurin aure kuma, Kawu Sulaiman wan mahaifina shine mad'aurin aure na. An cika ma'kil a k'ofar gidan mu dan gudanar da wannan 'daurin aure. Ni kuwa ina cikin kawayena da su ka kasance manyan mata. Dan kab kawayena babu budurwa, daga matan aure masu yara, sai zawarawa. Kasancewar na samu jinkirin aure. Shekaruna talatin da biyar a duniya. Daga gari gari a ka halarci wannan biki dan na yi gayya sosai. Abokan aikina na asibiti ma duk sun hallara, kasancewata ma'aikaciyar kiwon lafiya, bangaren anguwar zoma. Farin cikin da na ke ciki a wannan ranar bai da abun misali. Sanye na ke cikin riga da siket na atamfar Soso, mai kalar green da wani ganye ganye mai ruwan madara a jikin atamfar, na yi kyau sosai, sai busa kamshin turaren humra na ke yi. Kawayena sai tsokana ta su ke ta faman yi. Aminiyata makociyarmu Amina ce ta shigo d'akin da mu ke ni da kawayena ta na haki. Dubanta nai da mamaki nace. Ke kuma lafiya ki ke ta haki kamar wacce jaki ya ka da ita?" Ba ta ce da ni komai ba, hannuna kawai ta ja, tare da kirawo kawata Hadiza wacce ta zo bikina daga katsina. Fita mu ka yi zuwa bayan gidan mu, in da akwai rangwamen taron mata. Ta ce da ni. "Sadiya akwai fa gagarumar matsala a wannan karon ma." Murmushin ya'ke na yi, domun zuchiyata har ta gama yi mun hasashen abunda amina ta ke so ta ce." An fasa auran wannan karon ma ko Amina?" Murmushi na sa ke sakar ma Amina, amma cikin zuchiyata ci take da wuta babababah. Hadiza ta ce. "Amina dukkan mu ba yara bane. Ina tunanin kwakwalwarmu za ta iya shanye komai. Ki sanar da mu abunda ke faruwa." Yawu Amina ta ha'diye ta mi'komun wata kalanda. Hannu nasa na amsa jikina na rawa. A hankali na warware wannan kalandar. Abunda na gani shi ya tsananta bugun da zuchiyata ta ke ta faman yi, take hawaye su ka gama wanke mun 'yar fuskarta. Kalanda ce mai d'auke da hoton Ahmad mijin da zan aura yau, tare da kawata Fatima. Ko da na duba date sai na ga the same date da nawa daurin auren yau. Amina na duba na ce. Ina ki ka samu wannan kalandar Amina, Ahmad d'in dama soyayya su ke yi da Fatima ban sani ba, tare zai ha'da ya aure mu ko kuwa ita ka'dai zai aura, ni ya fasa aure na?" Dukka Wa'dannan tambayoyin a gigice na jeroma Amina, cikin dimuwa da tashin hankali mafifici. Sau uku ana kawo sadaki na, ana fasa auran, sabida kawai na yi ilimin boko mai zurfi har ina d'aukar albashi daga asusun gwamnati. Amina jiki a mace ta ce. "Maman mu ce, ta je bikin jiya. Shine aka rarraba kalandar, yau da na zo sai na soma shiga gida kafin in shigo nan, sai na tarad da mama bata nan, ta na nan gidan. A kan gadon ta na ga wannan kalandar. Sadiya iyakar abunda na sa ni kenan." Lumshe idanuna na yi, ina jin son Ahmad na ninka kanshi a zuchiyata. Na ce. Babu komai nagode. Koma mai Ahmad ya ke nufi ai zan ji zan gani, tunda yau ne daurin auran, kuma ma yanzu. A wajan na barsu na shiga ciki, ina ta gauraye hanya dan ba na jin da'di sam, zazzab'i me mai zafin gaske ya ke shirin kwantar da ni. Kwanciya na yi a d'akin da kawayena su ke. Sai liyafar cin abinci da shan lamon kwalba su ke yi. Ni kuwa na zama kurma sai duba siririn agogon fatan da ke manne a tsintsiyar hannuna na ke yi. Zainab kawata ta ce. "Sadiya ta wajajen ina gidan da Ahmad zai sa ki ya ke?" Duban ta na yi a sanyaye na ce. Ta wajajen D'orayi gidan ya ke, amma bansan layin ba gaskiya." Hadiza ta ce. "Rabu da ita Sadiya, bayan anjima anjimannan tare da ita za mu je jere, ko wannan dinma mai gidan na ki bai barki bane?" Ta jefa ma Zainab tambaya. Dariya Zainab ta yi tace. "Ahh haba dai, shima bazai hana ba, ya fa san yanda mu ke da Sadiya. Shima ya na waje cikin maza 'yan daurin auren ai." Ni dai sai bin su da kallo na ke yi. Kanwar umman mu ce Goggo Hansatu ta le'ko d'akin da mu ke tace. "Kawayen amarya da su wa da su waye za su je jere ? Dan Allah ku fito ga iyaye can a wajan mota ku ake jira." Gabana ne ya sa ke sabon bugawar da sai da na runtse idanuna. Su Amina, da Hadiza, da Zainab, ne su ka mi'ke tare da bin bayan Goggo Hansatu. Ni dai ina kwance ina jiran tsammanin abunda zai je ya zo. Su Goggo su na wajan motar kayan da zata kai kayan amarya. Kawu Sulaiman da kawu Bala ne, su ka iso wajan Motar. Goggo Safiya, da Goggo Mariya 'kannenshi ya ce da su. Su shiga gida ya na da magana. Bin bayan su, su ka yi zuwa cikin gidan 'dakin da ke zauran gidan, in da anan su ka sauka su maza mazan. Sawa ya yi a ka kirawo Yaya Asabe Babbar yayarsu a mata, da kuma mahaifiyar Sadiya, da kanwarta Goggo Hansatu. Bayan duk sun hallarane, Kawu Sulaiman yace. "Toh al'amuran daurin auran yarinyar nan komai ya jagule ya damalmale. Aisha kin cuce mu da ki ka bar mana yarinya a gida harta ri'ka ta ri'ke. Ki ka k'i fur ki ba mu yarinyar nan lokacin da 'dan uwanmu Adamu ya rasu. Amma Aisha ki ka yi fur ki ka hana, wai ke 'yar ki karatu za ta yi, Adamun ya baki wasiccin ki bar yarinyar tai zurfin karatu. Toh yaro dai iyayenshi sun gama bincike sun ce 'dan su bazai auri yar boko ma'aikaciyar gwamnati ba, 'yan bariki masu budadden idanu. Shine ni da Bala wan mahaifin Aliyu 'dan gidan Yaya Asabe, mu ka yanke shawarar a 'daura auran da shi Aliyun kawai 'dan wajan ki Yaya. Kuma Alhamdullah, Malam Bala shi ya amshi Auren har da sadaki nera dubu uku ga su." Yaya Asabe ta soma rabka salati tare da fashewa da kuka tace. "Shikenan ni Asabe na shiga uku. Sai da yarinya ta zama 'yar duniyar da a Birni ma ta kasa auruwa, sau uku wannan ne na hu'du ana fasa aurenta. Shine Bala za ka cuce ni ka Aura ma K'usar Yaki ita? Aisha fa sai da ta tabbatar ta raba Adamu da kab danginsa da asirinsu irinna mutan katsinawa, wacce iriyar azaba ce ba ta bamu ba, amma yanzu k'usar Yaki aka aura ma Sadiya? Wallahi bazan yarda ba." Kawu Sulaiman ya ce. "Yaya ki yi hak'uri, ni kai na na ji abun. Kuma kinga Sadiya ta girmi Aliyu da kusan shekara biyar. Goggo Safiya tace. " Ai juya shi za ta yi, tai ta yi mai wayo. Ni na tabbatar sai abunda Sadiya ta ce da Aliyu. 'Yan boko fitsararru da ba zaman aure su ke yi ba. Sun fi so a barsu sakaka sui ta cu'danya da maza wai abokan aikinsu. Kawu Bala ya ce. "Yanzu dai bakin alk'alami ya bushe, ni ne dai Wan mahaifin Aliyu kuma ni ne madaurin Auran shi, ni kuma na amshi Aurannan domun a rufa ma Adamu asiri, shi da ya mutu ya bar baya da k'ura. Yarinya ta yi kwantai kowa na gudun na shi ya aure ta. Asabe hak'uri za ki yi dan Allah. Goggo Asabe ta ce. " yaronnan fa, da rana a kan shi. Daya dawo da wata d'aya za'ayi auran shi da Khadija 'yar gidan mai gari, yarinya ga mai dambu Aminiyata. Wallahi aure kuma ba fashi." Kawu Sulaiman. Ya ce. "Wannan ba zai gagaraba yaya Asabe, yaro zai yi auran shi duk macen da ya ke son Aure." Goggo Asabe tace. "Shikenan yaya zan yi, cuta ce dai an riga da an cutar da ni. Yaro sai da ya zama mutum tukunna, duk wata kadarata, da gadon da shi kan shi yaron ya samu, duk ya k'are a wajan naiman ilimin addini shine har Madina. Amma zai dawo ya samu mummunan labari, wallahi bazan yi wuyar renon Kusar yak'i, da gina shi, Sadiya ta hanani cin arzikinshi ba. Tunda Adamu ya fa'di ya mutu, Aisha ita da 'diyarta ne ka'dai su ke amshe ku'din pension d'in nashi da garatuti. shikenan na yi Allah ya sanya alkhairi." Cikin kuluwa da takaici Goggo Hansatu tace. "An d'aura auran yarinya, babu wani shawara. Toh ya maganar aikinta da take yi na asibiti, daga can kauyan za ta dinga tawowa ko yaya? Sannan ya yarinya zata rayu a maraya, wayayya, mai ilimi, ma'aikaciya, sannan ita ba yarinya ba. Kawai a d'aura auranta da wani Wai shi Aliyu. Ai ta na da hakki ya kamata aji ta bakinta, koma meye sai a yi daga baya. Sannan Sadiya ba yarinya bace, ta girmi Aliyu nesa ba kusa ba, wanne irin zaman aure za su yi to? Aure ba soyayya, kuma a kaita kauye shikenan a dur'kusar da rayuwarta, ba za'a barta ta amfanar da al 'umma da ilimin data karanta ba? Wai me yasa ake ganin illa ne mace ta yi ilimin boko ta yi aiki, dan ta kare martabarta ta mace, da martabar k'asar ta. Mu gidanmu 'yan boko ne, kuma dole Sadiya za ta ci gaba da aikinta." Kawu Sulaiman yace. "Ke dakata Hansatu, wannan ba huruminki bane, ko Aisha bata isa ta tanka mun ba kan batun Sadiya. Domun ni ne uban Sadiya, duk duniya bata da gatan da ya wuce mu. Yarinyar nan zumunci mu ka yi ma, har aka ba ma shi Aliyun domun naga anan taki auruwa, ga shi sai girma take yi, shakaru takatin fa da biyar ai ta gama tsofewa a gida. Maganar aiki ma ajjiyeshi za ta yi, mu abunda muka sani shine 'd'akin mace shine darajarta. Mu daraja mu ka ne ma mata." Yaya Asabe ta cabke cikin daga murya tace. "Zancan kauye kuma da kuke yi, ai Adamu daga wannan kauyan ya fito kuma Aisha ta aureshi ta raba mu dashi, ko san zuwa ganin gida ba yayi. Itama dole ta je ta yi zaman aure." Goggo Hansatu za ta yi magana Aisha ta d'aga mata hannu, dole ta yi Shiru, zuchiyarta na yi mata k'una. Cikin raunin murya tace. "Yaya sulaiman Sadiya 'yar ku ce, kuma kune gatan ta. Ni ba ku da matsala dani, Allah ya sanya albarka a wannan auran, Allah yasa hakan shine mafi alkhairi a gare mu baki d'aya." Ta na kai wa nan ta fice a d'akin. Goggo Hansatu kuwa ba karamin rikici su ka yi da su Goggo Asabe ba. Har sai da 'yan Uwa aka shiga zancan sannan fa aka yi sulhu. Kawu Sulaiman yace. "Safiya ina ga kuje ku tafi kai kayan Sadiyan ko? Kawayen ita Sadiyan suna wajen motar su na jira. Hansatu kuma ki kirawo ta ku tafi tare. Barayin Dauda daya gina zai sa amaryar sa nan da wata biyu shi Za ku yi ma Sadiyan jere in yaso shi Dauda ya gina wani. Kui maza rana na yi." Goggo safiya ba ta ce komai ba ta bi umarnin Kawu Sulaiman. Goggo Hansatu ta dubi kawayen amarya tace. "Toh Su waye 'yan kwana domun in fa mu ka je acan za'a kwana waje ba kusa ba?" Hadiza ta ce. "Ai ina ga ni ka'dai ce zan kwana, sai Amina ko?" Zainab tace. "Gaskiya kam ni kam sai dai gobe ma bi ayarin 'yan budar kai mu zo ganin d'akin amarya." Goggo Hansatu ta yi ma su Hadiza jagora cikin motar da za su ta fi. Da ita sai Goggo Safiya, sai Hadiza, da Amina. A gaban mota kuma daga direba sai Anas wan Aliyu. Motar su Goggo Hansatu na gaba. Motar kaya na biye da su a baya. Mahaifiyar Sadiya na dakinta, hawaye kawai ta ke ta faman sharcewa wa. Hankalinta yai matuk'ar tashi, shin wacce rayuwa Sadiya za ta yi a kauye, gashi an aura mata miji yaro, maganar aikinta kuma fa, shin karatun da su ka da'de suna wahala domun samuwarshi, yanzu gashi ya samu har ta kai matsayin ma'aikaciyar asibiti, shikenan dangin mahaifinta sun dakatar mata da cikar burinta da manufarta kan karatun d'iya mace?. "Ya Allah kai ne ubangijin kowa da komai, ya Allah ka saukar ma da Sadiya nutsuwa da dangana, ya Allah ka sa aurannan na ta ya zame mana alkhairi, ya Allah ka raba Sadiya da makiyanta masu son ganin bayanta, Allah ka kawo mata sauyin alkhairi." Sauke hannayenta da ta 'daga tayi, ta na zubar da hawaye. Ta rasa dalilin da yasa dangin mijinta su ka tsane ta. Dan kawai ta zama 'yar boko kuma ma'aikaciyar gwamnati. Shin shi ilimin Mace laifi ne, ko kuwa kasancewarta ma'aikaciya zunubi ne?" Mi'kewa ta yi, ta share hawayenta. Cikin dakewar zuchiyata ta tura d'akin da Sadiya take a kwance. Sadiya Idanuna na runtse domun har zuwa lokacin a cikin fargaba da taraddadin abunda ka je ka zo na ke. Bansan me ke faruwa ba, kuma bansan a wanne matsayi na ke ba a yanzu, matar auran da igiyoyi uku su ka rataye rayuwarta, ko budurwar da ta gaji da kwanciya a gado ita ka'dai, cike da matsananciyar sha'awa da shaukin jin dumin mijin halali a tare da ita?" "Sadiya!!! Ki sa me ni a d'aki yanzu." Juyawa ta yi ba tare da ta ji amsar da zan bata ba. Jiki a mace tamkar kazar da ta taka wu'ka haka na mi'ke.kawayena su kuma sai aikin zolayata su ke yi. Wai tun kamun a kaini har na riga da na karaya. Da dariyar ya'ke kawai na bisu. Ahankali na dinga ratsa jama'ar biki ina bin sawun mama. Kallon da jama'ar bikin su ke bi na da shi, sai na lura ya wuce gaban misali. Take zuchiyata ta shiga kokawar fitowa da k'arfin tsiya. *Mrs Bukhari Ibrahim* *GISHIRIN* *ZAMAN* *DUNIYA* _Daga Al'kalamin_ _Badi'at Ibrahim_ ( Mrs Bukhari Ibrahim B4B) GAWURTATTU BIYAR 🤚🏻 TAKUN FARKO: Labari wanda yai duba kan gwagwarmayar mata a duniya. Da irin gudummawar da ilimin mace ya ke bayarwa ga al'umma. Da kuma rawar da ilimin mata ke takawa a cikin gidajen Aure. Wannan Labari true life story ne, duk abunda na rubuta, abune daya faru a zahiri, sai d'an k'alilan dana canja, kamar sunaye, da sauransu. Ku bini a sannu, akwai d'umbun darasi sosai. Kashi na farko Babi na 3~4 Da sanyin murya na yi sallama a k'ofar 'kuryar 'dakin mama. Ban ma jira amsar sallamar da na yi ba, na kutsa kai kawai. Idanu ta zuba mun, ta na ko'karin karantar yanayi na. Kaifin tsinin idanuwanta ne ke mun yawo a jikina. Zuchiyata ta shiga cikin taraddadi. Domun bansan meke wanzuwa ba, jikina ya na ba ni babu lafiya. Gwauron numfashi mahaifiyata ta sauke ta ce da ni. "Sadiya! Ga waje k'araso ki zauna, domun ni da ke inaso mu tattauna sosai." Hantar cikina tana kakkarwa na k'arasa in da ta nuna mun da manuniyarta. Zama na yi, kai na a k'asa, jikina kuwa sai bari ya ke yi. Takowa ta yi, ta zauna ta na fuskantata." "Sadiya" ta kira sunana da babbar murya." "Kinsan irin power d'in da dangin mahaifi su ke da shi, kinsan irin rawar da su ke takawa?" Cikin daurewar kai na dubeta, sam ban yi zaton jin wannan Kalmar da ga bakinta ba. Lumshe idanu na yi, ina tunanin dangin Babana sun ci mutumcin mama ne kamar yanda su ka saba. A sanyaye na ce. "Dangine da su ke jibantar al'aumara, kuma sai da su komai ke iya gudana. Da amincewarsu komai zai iya faruwa, domun da uba ake ado, su guma dangin uba. In ba mahaifi da su zaka yi ado. Amma mama......" Hannu da d'aga mun halamar bata son jin tambaya. Mu'kut na ha'diye tambayata. "Sadiya! Ahmad iyayenshi ba su amince mishi ya auri 'yar boko ba. A sakamakon haka ya fasa auranki." Nunfashi naja tamkar wacce aka zare ma rai haka na kasance na wucin gadi, ji na yi kalmar da mama ta jefomun tamkar bulalace wacce ta zane rayuwata tai mata dukan da baza ta iya boruwa a gaba ba. Iya so ina yi ma Ahmad, Allah shine masanin tsantsar son shi da ke raina. Wasu dun'kulallun hawaye ne su ka fashe a kumatu na. Ta ke zazzab'in da ya ke ta shirin kada ni ya samu nasara, har wani turirin zafi ne ya ke busowa daga jikina." "Amma dangin mahaifinki da su ka fini iko da gadara akan ki, ba tare da sun girmama ni a matsayina na Uwa an shawarce ni ba. Sun d'aura auranki da 'dan uwanki. Biyayya kawai na ke so ki yi musu Sadiya." Tsintar kaina kawai na yi a tsaye cak, cikin rawar jiki da rawar murya na so in jefo mata tambaya. Amma kash harshena bai bama baki na damar hakan ba, domun ya kasa ha'da kalma mai ma'anar da za'a fahimta, sai in ina kawai na ke yi. Nan ta ke duniyata ta yi duhu, tare da yin ta maule da gangar jikina." Zaunar da ni mahaifiyata ta yi. "Sadiya na sani abun za ki ji shi tamkar albamara, toh a zahiri yanzu ke matar aure ce wacce igiyoyi uku su ka rataye rayuwarki, dai dai da k'ofar gida in za ki lek'a a yanzu haka sai da izinin mijinki. Sadiya girma da darajar miji ya wuce zato ko tsammani, biyayyarki a gare ni shi zai ba ni damar tsallake jarabawar da dangin mahaifinki su ka za na mun. Ki amshi k'addarar da su ka 'kadarto miki. Sadiya ina so ki cire wannan abun a zukatan al ummar da su ke kalubalantar ilimin Mace, ki nuna musu 'yar boko diyace mai tarbiya kamar ko wacce 'd'iya. Ki nuna musu cewar 'yar boko na iya zaman aure, 'yar boko ba mara tarbiya bace, kuma ba karuwa bace, ki nuna musu 'yar boko ita mace ce tamkar ko wacce mace, kuma 'yar boko ta na daraja mijinta, kuma tana yi mai tsantsar biyayya, ki cire musu k'ya matar macen da ta yi boko, ki fito da darajar gidan mahaifinki, domun ko wanne tsuntsu kukan gidansu ya ke yi, ki nuna musu kin haifu cikin 'yar boko, kuma ta dauraki bisa tartibiyar tarbiya. Sadiya ki yi ma dangin mijinki biyayya, dangin mahaifinki ne. Aliyu k'usar yak'i wanda ya ke karatu a jami'atul madina kar'kashin scholarship, 'kaninki. shine mijinki. Sadiya kar ki ce komai ki yi musu biyayya, sannan ki ajjiye aikin ki babu komai. Amma zuwanki wannan kauyan inaso ki yi amfani da iliminki ki shiga gaba wajan wayar da kan 'yan uwanki mata kan muhimmancin ilimin Mace, da irin gudummawar da ilimin mace ke bayarwa a duniya ba ki d'aya, ita mace uwar duniya ce. Ki yi k'ok'ari ki zama malamar ilimi a kauyannan, amma komai za ki aiwatar ki tabbatar da yardar mijinki. Ki yi ko'karin fahimtar da shi, tunda shi ba jahili ba ne." Kuka na rushe da shi, wanda ya dauke ni da'ki'ku masu dama. Mama zuba mun idanu ta yi ba ta yi yun'kurin rarrashina ko katsemun kuka na ba. A lokacin zuchiyata da kwakwalwata ba sa amsar ko wanne irin sa'ko, ji na ke yi tamkar na zama wata halitta ce ta daban. Tausayin kai na da kai na ma ka'dai ya isheni. K'ok'ari na yi in tuno da fuskar Aliyun da aka kira shi da mijina. Amma na kasa, domun bai fi sau biyar mu ka ta'ba ha'duwa ba. Abunda kawai na sa ni game da shi, shine. Shine d'an auta a wajan Goggo Asabe, kuma na girme mishi da kusan shekaru biyar. Taya za'a aura mun 'kanina, ina babbar mace mai shekaru talatin da biyar? Wanne irin zaman Aure su ka zab'ar mana mu yi, dama har yanzu a na yin auran dole ne, ko kuwa a kaina abun ya juyo?" Dukkan Wa'dannan maganganun ni da zuchiyata na ke yi. Na shiga rudin da ya fi k'arfin gaban a misalta balle har ya rubutu. Cikin karyayyar muryar da ta ke sa ke jefa ni a damuwa mama ta ce. "Sadiya! Ko ba za ki yi mun biyayya ba

Chapter 1 of 7