ce ta iso, a hakanma a cike take fam babu waje, dole Babur dai su ka hau. Sun sha 'dan banzan wahala a hanya. Domun surquqin jeji su kai ta ratsawa. Ga wasu kwazazzabai a hanyar. Ga tafiya bata wasa ba, mill 7 su ka yi a kan Babur d'innan. Wujiga wujiga su ka isa. A barayin surukan gidan aka musu masauki. Wato matan yara mazan gidan. A d'akin matar Anas a ka sauke su. Dan d'akinta ya fi ko wanne d'aki a gidan kyau. Kasancewar daga kauyan Lamba a ka Auro ta, kuma mahaifinta shine mai gari.
Sai bayan sun huta sun sha ruwa, da tuwon dawa miyar bushasshen karkashi, da ake kira da bak'ar miya. Sai wata dawo ( fura) k'azamar damu babu sikari ba nono, a ka kawo musu. Sannan motar kaya kuma ta iso.
Abunka da 'kauye, kafin kace me gidan ya cika da mata da 'kananun yara. Ana tambayar Anas " Amarya aka kawo ne" sai sanar musu ya ke yi. Cewar Aliyu ne ya yi Aure. Mamaki da almara su kai ta yi. Kafin dare ya rufa kowa a cikin RAQUMA ya ji labarin Auran Aliyu da ya Auro 'yar masu ku'di. Wanda akai mata kaya na mamaki. Mata fam gidan suna mamakin ganin irin kayan 'dakin Sadiya. Matan mazan gidanne su ka ta ya su Goggo Hansatu kintsa d'akin amarya. Har bayan isha su na Abu d'aya. Bacci su ka yi a cikin 'dakin na ta suna jiran wayewar gari su 'daura daga in da su ka tsaya. Sun kuwa sha cizon sauro, har hakan ya tilasta musu hak'ura da baccin ma baki 'daya. Ga babu wutar lantarki sam a k'auyan, sai dai aci balbal da shi su ke amfani.Cikin daren su ka mi'ke, su ka ci gaba da jera komai a in da ya dace.
*WAYEWAR GARI*
*Mrs Bukhari ce*
*GISHIRIN*
*ZAMAN*
*DUNIYA*
_Daga Al'kalamin_
_Badi'at Ibrahim_
( Mrs Bukhari Ibrahim B4B)
GAWURTATTU BIYAR π€π»
Labari wanda yai duba kan gwagwarmayar mata a duniya. Da irin gudummawar da ilimin mace ya ke bayarwa ga al'umma. Da kuma rawar da ilimin mata ke takawa a cikin gidajen Aure.
True life story
Kashi na 1
Babi na 7~8
Shiga 'd'akin da su Jamila su ke na yi. Nan fa su ka soma yi mun gu'da tamkar za su tsinke hancinsu. Sister Murja ta ce.
"Sadiya gaskiya za mu yi matu'kar kewar ki a Asibiti. Kafin ki gama cin amarci ki dawo." Dariya na k'wak'wulo cike da far'a na ce.
"Ni kuwa ba kewar da zan yi. Bazan so ma hutun nawa ya k'are in dawo ba, na fi so in ta zama wajan angona. Sister Jamila ta sa ka shewa ta ce.
" lallai Ahmad ya sa mu babban rabo da ya same ki a matsayin umman 'ya'yanshi. Zai yi alfahari da kasancewarki matar shi. Uwa uba ga ki da tsoron Allah, kin kuma kasance mai alkhairi, da son taimako. Sadiya ba ki ci ka duba kan ki ba, hankalinki ya fi ta'allak'a ne akan ganin ko wacce mace ina ma ace ta samu ilimi , da duniya za ta yi alfahari da ita. Ina ji a jikina wata rana za ki zama wata." Kokawa na ke ta yi da hawaye na kar ya zubo, dan gudun kar ya fallasani. Amma sai da ya ci amana ta ya zubo da gudu. Kukan kawai na shiga rerawa a hankali, ina tuno yaya rayuwa za ta kasance mun a kauye, kuma a k'ark'ashin namijin da na ba shi shekara biyar, wai me ya sa ba'a cika bai ma mace dama bane? Bayan addinin musulunci ya fa'di girma da daraja, da ma baiwar da Allah yai ma mace. Rarrashina su ka shiga yi, a na su tunanin kukan rabuwa da gida ne. Dan har Jamila ta na yi mun tsiya da cewa. "Sai kace wata karamar yarinya, har da kukan zuwa gidan miji?" Ni dai ban da kuzarin da zan ci gaba da biye ma cece ku ce d'in su.
Sha d'aya na yi, Goggo Mariya ta shigo har d'akin da na ke ta ja hannuna, zuwa d'akin Mama na. Mun yi kuka ni da Mama tamkar rabuwar da baza mu sa ke ha'duwa ba. Jaka ta Mama ta zuge ta sa ka mun wani abu. Da kyar ala zare ni a jikin Mama a ka yi waje da ni. Kowa ya shiga mota. Ina zaune a bayan mota kusa da maman su Amina, wacce ta kasance aminiya ga mahaifiyata. A kusa da ita Goggo Mariya ta zauna, sannan Goggo Asabe. A gaban mota kuma Kawu Sulaiman ne zaune bangaren me zaman banza. D'ayar motar kuma su kawu Bala ne da sauran matan da aka tawo da su. Mama na hango a k'ofar gida, ta na d'aga mun hannu. Nutsa kai na, na yi a tsakankanin cinya ta. Na fi awa hu'du ina kuka mai ta'ba zuchiya, abubbuwa da yawa ne a kar'kashin wannan kukan nawa. Zazzab'i da wani irin jahilin ciwon kai ne, su ka rabke ni. Awa takwas mu ka yi a titi mu na zirara gudu. Kauyan mafara mu ka tsaya a ka yi sallar azahar da la'asar. Daga nan kuma mu ka sa ke mi'kar hanya. Su Goggo Asabe sai hira da dariya su ke yi abinsu. Ni kuwa ina zaune na yi tsuru tsuru, ko k'wakk'waran motsi ba na iya yi. Maman Amina takan sa musu baki a cikin firar ta su jefi jefi. A. Haka har mu ka iso bus top. Babura aka tarar mana. Hawaye sai sabunta kansu su ke ta yi a kumatu na. Kowa ya hau Babur dinshi, ga kaya ni'ki ni'ki a hannun ko wacce daga cikin mu, kaya har a gaba aka saka masu Baburan su ka ta ya mu rik'ewa. Gudu akeyi cikin ciyayi da kaucina, Hankalina baya tare da ni sam. Gani na ke yi wani nannauyan bacci ne na ke yi, mai cike da muggan mafarkai kawai, tunda uwata ta haife ni ban ta'ba ganin k'ungurmin k'auye irin wannan ba. Domun ban ta'ba zuwa da wayo na ba. Sai lokacin ina k'arama Mama ta na zuwa da ni, a lokacin bansan komai ba."
Gidan Amarya
Goggo Hansatu na hango a tsaye a dan k'aramin tsakar gidan da ke b'arayin Sadiya hannunta ri'ke da k'ugunta ta tusa kayan kitchen d'in Sadiya a gaba, ta na ta tunani. Amina ta ce.
"Goggo me zai hana mu yi ma yayan shi Angon magana, ko da kafinta ne a nemo mana wanda zai buga mata kitchen ko da na langa langa ne, kamar yanda aka yi mata bayan gida da langa langa. In ba hakan mu ka yi ba, sai dai in da kayan za mu koma. Goggo Hansatu ta zare idanu ta ce.
" mu koma da me? 'Yannan ni kai na da taimakon Allah na iso lafiya a Babur. Ni ka'dai ma kenan balle kuma ace da kaya. Shawarar da ki ka bayar ta yi kyau sosai. Bari in je wajan matar Anas d'in, ko Allah zai sa mu dace a samu kafintan." Goggo Hansatu da kanta tayi tattaki har zuwa b'arayin Matar Anas. Bilkisu na tsugunne ta na ta kici kicin hura kara ta na son d'aura d'umame. Shi kuma Anas d'in fitowarshi daga d'aki kenan zai fita waje, Goggo Hansatu ta shigo.
"Ahh Goggo Hansatu, ai da kin aiko ni nazo, da ba ki wahal da kan ki ba." Cewar Anas. Bayan Goggo Hansatu sun gama gaisawa da Bilkisu. Sai ta ce da Anas.
"Babu komai 'dannan. Ka ga kafinta na ke so ka ne mo mana. Zai buga mana madafi ne da langa langa, kamar yanda aka buga ban d'akin na Sadiya. Na ga wajan ba madafi. Shiru Anas ya yi, sannan ya ce.
" toh bari zan fita yanzu, in je gidan mai gari, yaron wajan shi shine kafinta, sai mu zo da shi ya ga wajan." Godiya Goggo Hansatu ta yi mishi ta fita, ta koma b'arayin Sadiya. Amina ta ce.
"Andace kuwa Goggo?" Zama Goggo Hansatu ta yi tukunna, sannan ta ce.
"Za dai a dace. Ya ta fi kiran kafintan sai ya zo ma ji ta bakinshi. Ba ma wannan ba Hadiza, ina ganin dole ku zan aika zuwa cikin garin Zamfara. Yarinyar nan a siyo mata tocila irin wanda su ke yin chaji da hasken rana. Wannan duhu ya yi yawa, damuwar za tai mata yawa, a siyo mata kalanzir shima, ta 'danyi amfani da shi, kafin ta ko yi kunna kara kuma, abun tuwo na buhu ma, a k'aro mata kamar buhu hud'u. Da tarkacen da kuka san zata sha wuya kafin ta sameshi a wannan kufan." Bilkisu, da matar Dauda Hasiya ne, su ka shigo hannayensu rike da kwanukan abinci. 'Dakin amarya su ka wuce dan ajjiye kwanukan. Tsurewa su ka yi dan ganin ha'duwar d'akin. Bilkisu tace.
"Hasiya ji d'aki, komai a tsare kuma babu kaloli barkatai. Baki Hasiya ta tab'e tace.
" d'akin 'yar boko ba. Wallahi ni sai na ji na tsane ta tun kafin ta zo. Kishin balbali sai tafarfasamun ruhina yake yi. Goggo ma ta ce babbace Amaryar ta fi k'arfin Aliyun fa. Kuma kwantai ta yi a burnin shine aka k'ak'aba mishi ita." Bilkisu tace.
"Haka na ji a wajan Anas, sai dai Baaba ta ce, auran shi ya na nan daram da khadija, daya dawo da wata guda. Tun yarinyar ta na k'arama aka ba shi ita.Ni ai na fiki jin kishin balbali a kanta, da d'akina yafi na kowa tsaruwa a kab surukan gidannan, yanzu an kawo kishiyar da d'akinta ya fi nawa hmm." Hasiya ta ce.
" mu lek'a k'uryar d'akin mu ga ni. Bilkisu ta ri'ke hannunta tace.
"Alkur'an ba ruwa na. Ki zo mu fita." Fitowa su ka yi.
"Goggo ga karin kumallo mun shigar muku. Goggo Hansatu ta ce.
" An gode" bayan su Goggo Hansatu sun gama tattaunawa. D'akin su ka koma. Dumamen tuwon jiya ne da ruwan kokkon gero wanda babu sikarin arziki, shine kumallon. Kokkon kawai su ka sha, tuwon kuma su ka mayar musu da shi. Hadiza da Amina, Goggo Hansatu ta ba su wadataccen ku'di, su ka tafi dan hawa Babur ya fita da su zuwa bus top. Daga nan kuma sai su hau motar da za ta shiga da su, cikin garin Zamfara. Jama'ar gidan Malam mai Hula kuwa, a na ta hidima da shirye shiryen tarbar Amarya, dan Goggo Safiya ta sanar mu su da cewar yau za'a kawo amarya kuma za su yi bu'dar kai. Duk an shisshiga mak'ota an sanar musu. Dan haka gidan ya kasance a cike fam. Sai tsegumi da gulme gulme ne ya ke ta shi a gidan. Wasu su na ganin ba'a kyauta ma Khadija ba, ita data ta so cikin so da begen Aliyu. Mari mai dawo tace.
"Ance tun jiya Khadija ta ke ta faman kuka ko abinci ta kasa ci. Hasiya matar Dauda ta ce.
" wannan yarinya abun a tausaya mata ne, za'a hadata kishi da 'yar boko, 'yar bariki, ga ta rayayyar maraya, kuma ance Babba ce, dan ta girmi Aliyun." Nan fa tsegumi ya ci gaba, kaya kaya kawai ka ke ji.
Duk wannan surutun bai hana su aikin su ba. Wainar gero su ke toyawa. Bisa al'adar kauyan RAQUMA, wainar gero ana yin ta ne in ana wani sha'ani. Kamar bikin Sallah, bikin Aure, da bikin haihuwa. Sun k'ware sosai wajan iya wainar gero. Wasu kuma suna gaban turmi suna daka dawo ( fura) ma su curata daban, masu sa ta a cikin gari daban. Kowa dai ka ganshi, a cikin aiki ya ke." K'auyan raquma ta gama d'aukar harami, gida a cike yake tab da mata, abokan Ango ma suna waje, suna jira amaryarsu ta iso, su tarbeta."
*Mrs Bukhari Ibrahim*
*GAWURTATTU BIYAR,5π€TAFIYAR TA MUSAMANCE*
1, *MU GANI A ΖASA..π₯*
_Ummu Affan_
2, *ABIN CIKIN ΖWAI..π₯*
_Ummu Maher_
3, *GUNTUN GORO..*π₯
_Mom Islam_
4, *GISHIRIN ZAMAN DUNIYA*π
_Mrs Bukhari_
5_ *AUREN WATA TARAπ©ββ€οΈβπ¨*
_Miss Hajo_
Guda Ιaya N300
Guda biyu N500
Guda uku N600
Guda huΙu N700
Guda biyar 1k
*ZAKU TURA KUΖINKU TA WANNAN HANYARπ*
Fatima Rabiu Sunusi
0037219728
StanbicIBTC Bank.
Shaidar biya tanan π
0810 433 5144
Masu tura katin MTNπ
0814 179 9224
...........π₯π©ββ€οΈβπ¨π₯π....
*Ζ³AN NIGER GA HANYOYIN BIYAN KUΖINKUπ
Guda biyar 1000f
Guda huΙu 700f
Guda uku 600f
Guda biyu 500f
Guda Ιaya 300f
Kai tsaye ku tura da katin Airtel ta wannan number 08141799224
*MUN GODE DA KASANCEWA DA GAWURTATTU TAKUN FARKO*
*INA MATAN MASU AMSA SUNANSU NA MA, INA UWAR GIDA, INA AMARYA, INA 'YAN MATA 'YAN KWALISA?* *HAK'IKA DUK MACEN DATA ISA, SAI DA K'AMSHI DA GYARAN JIKI BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI. 'YAR MUTAN KATSINAWA NAZO MIKI DA SIHIRTACCEN K'AMSHIN DA ZAI JIJJIGA MIKI OGA, TA YANDA OGA ZAI LIK'E MIKI.* *SUNAN WANNAN K'AMSHIN MANNE MATA, MAK'ALE MATA* * *WASU KUMA SUKAN KIRASHI DA D'AYE MANNA* 'YAN MATA AKWAI NAKU HAD'IN NA DABAN.
*AKWAI KULACCA TA SUDAN*
MAI SIRRIN K'AMSHI DA GYARA FATA, GA UWA UBA SA LAUSHIN JIKI, DA KUMA DAWWAMAR DA K'AMSHI A JIKIN FATA.
*AKWAI SIHIRTACCIYAR HUMRA, 'YAR SUDAN*
WACCE AKAI MA LAK'ABI DA 'YAR BAIWA MAI ABUN MAMAKI.
ITA KUMA TADA SHA'AWAR ME GIDA TAKE YI, TARE DA K'ARA DANK'ON SOYAYYA, DA KUMA DAWO MA DA MATA MARTABARSU. UWA UBA AN HAD'ATA NE DA ITATUWAN GYARAN JIKI, DA KUMA SIRRIN K'AMSHI MAI MOTSO SHA'AWAR DUK WANDA YA SHAK'ETA.
ππΌππΌππΌππΌ
BAN TSAYA IYA NAN BA.
AKWAI TURAREN KWANCIYA, WANDA AKE SHAFAWA A MATSE MATSI, DA SAMAN CIKI.
πππππ
KE DAGA JI KINSAN AKWAI AIKI, DAN MAI GIDANKI SAI K'ARA SONKI DA KUMA MAK'ALE MIKI.
π€£π€£π€£π€£π€£
INA DA TURARE D'AN GASKE NA TSUGUNNO, MAI FARFAD'O DA MARTABA DA KIMAR GABAN MACE, K'AMSHI YA DAWWAMA A WAJAN, YANA SAUKAR DA NI'IMA, YANA KASHE INFECTION, YANA MACE MACE TA HAD'E TSAM. YANA K'ARA D'AND'ANO.
ππΌππΌππΌππΌππΌ
INA HAD'A TURAREN FANT 'YAR UWA, WANNAN MA WANI SIRRINE NA MUSAMMAN
ππΌππΌππΌππΌππΌππΌππΌππΌ
TA B'ANGAREN KAYAN MATA KAMA DAGA NA NI'IMA, NA INFECTION,DAMA NA MATSI IRI IRI. DA DUK WANI MAGUNGUNAN MATA A KWAI SU, 'YAN GASKE, MRS BUKHARI 'YAR MUTAN KATSINAWA TA ZO MUKU A SHIRYE TSAB.
AKWAI SETI NA MAI JEGO, WANDA YA K'UNSHI KOMAI DA KOMAI A CIKI.
ππΌππΌππΌ
KANA AKWAI SETI NA AMARYA, ITAMA NA MUSAMMAN NE, YANA D'AUKE DA INGANTATTUN MAGUNGUNAN JIJITA ANKO.
'YAN MATA WANDA SUKE SHIRIN SHIGA DAGA CIKI KUMA AKWAI NAKU SETI NA MUSAMMAN.
AKWAI MAN DILKAR GYARAN JIKI NA AMARYA, DA SABULUN AMARE NA MUSAMMAN
*BANGAREN TURARUKAN WUTA NA INA NAN*
*TURARUKAN D'AKI, DANA KAYA, DA TURAREN GASHI, DA TURAREN WANKA, TURAREN MOPPING, TURAREN WADROPE, TURAREN BAYAN GIDA. KUJERAR TSUGUNNO, KABBASA, DUK INA SIYARWA. DOMUN NEMAN K'ARIN BAYANI TU TUNTUB'I MRS BUKHARI 'YAR MUTAN KATSINAWA.
08179523215
saina ji ku
*GISHIRIN*
*ZAMAN*
*DUNIYA*
_Daga Al'kalamin_
_Badi'at Ibrahim_
( Mrs Bukhari Ibrahim B4B)
GAWURTATTU BIYAR π€π»
Labari wanda yai duba kan gwagwarmayar mata a duniya. Da irin gudummawar da ilimin mace ya ke bayarwa ga al'umma. Da kuma rawar da ilimin mata ke takawa a cikin gidajen Aure.
Kashi na 1
Babi na 9~10
Anas ne ya shigo 'barayin Sadiya shi da Amadi kafinta.
"Goggo wannan shine kafintan kin ganshi, kusan duk kauyan nan shi ke yin aikin kafinta." Goggo tace.
"Kaga madafi na ke so ka buga mun na langa langa ko da ta can bangaren ne." Ta nuna mai dai dai in da ya dace.
"Asa k'ofa da abun kullewa a jiki. Amma yau na ke so, ko in ce ma yanzu." Amadi ya duba ya ce.
"Toh da tsohon langa langa ko da sabo?" Goggo tace.
"Sabon dai zai fi, tunda na Amarya ne." Shiru ya d'an yi sannan ya ce.
"Nera dubu uku da d'ari biyar za'a biya. Zan buga mata me kyau, kuma na sa har da ku'din abun hawa. Jiya na siyo langa langar, zan yi gyara, amma zan yi muku da shi. Ina gamawa sai in shiga Gusau in siyo wasu." Goggo ta ciro ku'din a jaka ta ba shi. A cikin minti talatin ya kammala buga kitchen d'in, har da buga katakai zagayen kitchen d'in. Yanda za'a iya jera wasu kayan. Goggo Hansatu ta na tsaye a kitchen d'in ta na jera kaya. Mamaki da al'ajabin irin muguntar da dangin mijin yarta su kai ma Sadiya ta ke yi. Domun zaman wannan k'auyan k'ayau tashin hankaline ga wanda yai rayuwar maraya. Ta gama jera komai da komai, kuma duk da haka akwai sarari sosai, kitchen ya yi mugun kyau, sai dai k'asan ba siminti k'asa ce kawai. Kayayyaki da dama baza su yi ma Sadiya amfanin komai ba domun kayan wuta ne. Sauran kayan da su ka rage, Goggo ta d'aga kar'kashin gado ta zuba mata shi.
******
Khadija ta na tsakar gida sai kuka ta ke ta faman yi. Mahaifinta mai gari ne ya fito tsakar gidan, ganin Khadija na kuka ya sake jagula shi.
"Khadija ke tun jiya wannan kukan bai k'are ba? Na fa'da miki kiyi shiru, dole Aliyu ya za'bi d'aya ko ke, ko 'yar bokon da aka Aura mishi, amma bazan bari a ha'da ki kishi da 'yar duniya masu budadden idanu ba. Ina ganin ki yi hak'uri da Aliyu shi zai fi.Domun anci amanarmu, yarinyar shekara nawa ina mishi rainonta, sai ace kuma yanzu anyi mishi aure. Mai dambu mahaifiya a wajan Khadija, kuma aminiya ga Goggo Asabe. tace.
" Haba malam ba'a gaggauwar yanke k'auna, musamman k'auna irin ta Aliyu da Khadija. Yarinyar nan tun tana yarinya Aliyu ke kula da ita, tun sanda aka ce matar shi ce. A RAQUMA babu wanda bai san son da su ke yi ma juna ba. Kuma ni na tabbatar Aliyu ba zai fifita tsohuwar guxumar da aka ce an aura mishi ba, sama da Khadija. Yana yima khadija wani irin makahon so, kai ka sani malam. Ni gani na ke yi ka bari tukunna Asabe ta dawo in ji meye nufinta, ai yau za su dawo." Girgiza kai yayi yace.
"Mai dambu hoo. Toh Allah ya kaimu ta dawo d'in. Ni zan fita. Tace.
" Adawo lafiya malam. Amma za mu je gidan bikin da Khadija inna gama share d'akin tumakai." Ya ce.
"Gidan watsewa zai yi yau kenan. Hauwa da Hajara ma duk sun tambayi anguwa. Toh su kuma tumakan fa?" Mai dambu tace.
"Hamisu ya na gida, baza shi ko ina ba. Har sai na dawo."
"Sai kun dawo" ya sa kai ya fice. Mai dambu ta kammala duk aikace aikacen da ya dace ta yi na gida. Sannan ta yo wanka. Da k'yar ta lallab'a Khadija sannan ta yo wankan. Mai dambu tace.
"Nace ki saki jikinki Khadija, dolen Aliyu ya aureki, kuma dole ki mallakeshi, kamar yanda na mallake ubanki, kema ke ce zaki yi mulki a gidan Aliyu. Kuma ai ke ya ke so kab k'auyannan babu wanda bai sani ba. Ki share hawayenki, in dai nice uwarki, toh hatta Asabe saikin fita iko da Aliyu.
Sallama mai Dambu tai ma abokan zaman ta akan cewar ta fita. Adawo lafiya su ka yi mata. Ficewa su ka yi a gidan.
Khadija ta na tafe sukuku babu laka a jikinta, hankali da tunaninta sam baya tare da ita. Gani ta ke yi, in dai ta rasa Aliyu, tamkar munfashinta zai iya tsayawa ne. Sai dai kuma maganganun mahaifiyarta na yi mata wani irin yawon da yake shirin farfad'o da kuzaranta. Amma sai gabanta ya tsananta fad'uwa da su ka iso k'ofar gidan su Aliyu. Abokan shi ta gani a k'ofar gidan. Wani kallo ta watsa musu, wanda su kan su sai da su ka sha jinin jikin su.Kuma sun yarda ba'a kyauta mata ba, sai dai suna taya abokinsu murnar samun matar birni. Su Goggo Asabe ne su ka iso a kan Babur.
Sadiya
Tsai Khadija ta yi ta na kallo na, wasu zafafan hawaye ne su ka zubo mata. Ni ko kaina na k'asa ba ma a iya ganin fuskata. Maman Amina ce ta ke ri'ke da ni. Goggo Mariya ce ta nuna ma maman su Amina gidan da za mu shiga. Ina cikin mayafi na ke jiyo muryar wasu maza su na mun sannu da zuwa.
GOGGO
Goggo Asabe da ta ga mai dambu ta ce.
"Ohh mai dambu yanzu fa kina raina, niyya ta shine, daga nan in wuce gidanki." Khadija ce ta karaso ta fa'da jikin Goggo Asabe ta saki kukan da ta ke ta ri'kewa. Goggo Asabe ta ce.
ββki kwantar da hankalinki khadija. Aliyu dai na ki ne. kuma babu mai raba ku. mai dambu mu je mu daga ciki.
hannun khadija na cikin na Goggo Asabe, su ka kutsa zuwa cikin gidan,
Sadiya
ni kuwa mu na shiga jama,ar biki su ka tarbe ni. Mata an yi cincirindon son ganin Amaryar Aliyu. Nayi mamakin irin taron da aka had'a na mata. kai tsaye d'akin Goggo Asabe cikin k'uryar d'akinta aka shige da ni. a tabarma na zauna tare da sauke ajjiyar xuchiya na azabar da mu ka sha a hanya. ga zazzab'i da ke ta damuna.Gabaki d'aya babu abunda ke mun dad'i. Hankalina ya k'ara tashi matuk'a da ganin irin k'auyan da aka kawoni zanyi rayuwar Aure a ciki. Rayuwar da ake mata fatan d'orewa har abada. fatima yayar Aliyu ce ta zauna kusa da ni.
"Barka da isowa Amarya ina miki maraba. murmushin yak'e na yi mata, na ce.
nagode Fatima. Ina yaran su ke?
"suna k'war gida, wasa su ke yi. Sallamar su Goggo Asabe ce ta katse mu ni da Fatima.
"shigo mai dambu ki ji kan labari. zama mai dambu ta yi, khadija ma ta zauna.
"mai dambu Bala ne ki na ji ya cuce ni, ya had'a Aurannan. Allah shine shaida ta bana son wannan Auran. kuma yaronnan nawa ne, daya dawo za'ayi bikin a lokacin da yake a tsaye, ai mijin mata hudu ne k'usar yak'i. Sannan Khadija ce surukar da nake so Aliyu ya kawo mun ita cikin gidannan. Ke mai dambu kinsan irin amincin dake tsakanina dake, babu batun yaudara, asalima dan zumuncinmu ya sake yin dank'one muka had'a yarannan namu. Ko ba gaskiya ba? Kuyi hak'uri bisa k'addarar data kunno kai.
mai dambu tace
"matsalar fa Asabe ita ce. tsakani da Allah ba'ayi mana adalci ba.babu dattaku a cikin wannan lamarin. kuma mahaifin yarinyar nan cewa ya yi dole Aliyu sai dai ya zab'i d'aya. ko 'yar boko, ko khadija. amma bazai ha'da su ba. kuma ni kai na ina bayan hakan Asabe. Yarinya dai kun cutar mun da ita. Tunda labarinnan ya isheta take ta faman kuka, hankalinmu ba a kwance yake ba sam.
Goggo Asabe ta ce.
"tunda mu mu ke neman iri, zanje in sami mai garin zuwa da daddare in na wuta. saura kwana biyar yaronnan ya dawo."
muk'ut na had'iye wani kakkauran yawu mai d'aci, hawaye sirara su ka surnano mun. na zama abun tausayi. Goggo da kanta ta ke fadama bare cewar cutar ta aka yi da aka aura ma Aliyu ni? yar mahaifina uwa d'aya uba d'aya. Wannan wanne irin k'iyayya Goggo take nuna mini haka? Fatima ta mi'ke ta fita. ana ta hidimar biki. ni kuwa babu wanda ya sake bi ta kaina. ga zazzab'i ga yunwa, uwa uba k'ishin ruwa na ke ji. amma na kasa ko da motsi mai kyau. A mugun takure nake, gashi duk wanda ya shigo sai Goggo ta bashi labarin, a birni sau uku ana sa bikina, amma sabida boko na kasa auruwa, shine aka cuceta aka aura ma k'usar yak'i ni.
Su Amina ne a cikin kasuwar kanawa me suna samaru ta cikin garin Gusau. sun sai duk wani abunda Goggo Hansatu ta ba su sallahu. harda ma wanda su ka tabbatar Sadiya za ta buk'ata. hanyar dawowa su ka nufa. sun wahala sosai wujiga wujiga su ka dawo da yamma lis. Goggo Hansatu za ta fito daga b'arayin Sadiya kenan su kuma su na shigowa.
"wayyo yarannan ina ta tunaninku. ga su Sadiya ma sun iso tun tuni. shine zanje in dawo da'ita ta shiga d'akinta. ku shiga ku huta, yanzu ma