Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
4 / 7
za'a kira sallah. fita Goggo ta yi, ta nufi cikin b'arayin su Goggo Asabe. a bakin k'ofa ta tsaya ta bud'e labulen da sallama tace. "Yaya Asabe kun iso lafiya?" Goggo Asabe tace. "lafiya" Goggo Safiya tace. "dama yanzu mu ke shirin za mu kawo ta da kin k'ara hakuri ba cinye ta za mu yi ba. Goggo Asabe ce ta d'agama Goggo Safiya hannu sannan tace. "dama za'a kawo ta. akwai abunda muke jira ne. tunda kun kasa hak'uri za'a kawota ki je." juyawa Goggo tayi. Tana mayar musu da martanin cewar ai ta zaci cinyenin za su yi. ni ko ina d'aki a takure, ina jiyo su. sai wajajen bayan isha. A lokacin na gama galabaita da zazzab'i da yunwa. Goggo mariya ta shigo d'akin da na ke. "ta so mu je Sadiya in kai ki d'akin mijinki." da sauri na mik'e, ta na gaba. ina biye da ita a baya har zuwa falon Goggo Asabe. wasu mata na gani da gani K'awayen Goggo ne. sune su ka rakani d'akina. a falo su ka zazzauna. nasiha su ka shiga yi mun. sannan su ka yi sallama su ka fice. da sauri na bud'e mayafina. ina hawaye Goggo Hansatu ce ta matso kusa da ni. da sauri na fad'a kirjinta nai lamo. kau ta ji jikina da zafi rau. nan hankalinta ya tashi. "Sadiya kin kuwa sha maganinki kuwa, kin ma ci abinci kuwa? kai kawai na iya girgiza mata dan a mugun galabaice nake. Amina ce ta shiga kitchen ta kunna risho. ruwan zafi ta d'aura mun da zan yi wanka. ina zaune kusa da Goggo. kaina na d'aga na kalli rufin d'akina. lantarki mai yin chaji da hasken rana na gani a manne. kamar kwan wuta ya ke, ya na da haske sosai. kuma ya na rik'e chaji. ajjiyar zuchiya na sauke dan na d'anji sanyi a raina. rufin d'akin na sake kallo inaso in tantance da me aka rufe saman d'akin. naga dai abu bak'i zare zare a jere ras. da kyar na gane igiyar dake cikin video kaset ne wannan bak'in mai d'an fad'i na ciki. Goggo Hansatu ce ta katse mun tunani na da cewar. "Sadiya mu je in nuna miki toilet ki yi wanka. ga shayi ki sha sai in baki magani." mik'ewa na yi. na bita a baya. langa langa ta nuna mun ta ce. "ga toilet d'innan ki shiga ruwan na ciki." to. kawai na iya ce mata. na shige toiket d'innan ya sha plasta ya yi kyau. ga shadda irinta gargajiya mai k'aramin baki. cikin nutsuwa na yo wankan tare da d'auro alwala na fito. bedroom na shiga dukkansu su na ciki. wadrope d'ina wacce ta cika bango guda na bud'e. kaya na su na jere reras. doguwar rigar bacci mai sauk'i na sanya. turare na fesa a jikin rigar. sannan na yi sallah. Hadiza ta mik'amun tea a kofi mai kauri, dan har kayan tea duk sun siyo mun manyan gwangwamaye. ahankali na ke sha har na shanye. sannan na sha magani. ina jin su suna ta tab'a hirarsu da ban dariyar jama'ar k'auyannan, yanda su kaita tururuwar zuwa ganin d'akina. ganin hakanne yasa har na d'an sake. a lokacinne na samu damar karema d'akin kallo. iya ha'duwa ya tsaru ko a birni d'aki ne na azo a gani. tabkeken gadone 6 by 7 fararene kayan katakon sai ratsin gold da ke jiki. wadrope dina babbace mai kofa shida, sannan ga dresing mirror na a gefe harda kujerar zaman kwalliya. labulayen d'akin kuma gold colour ne. haka ma kafet din dake malale a cikin uwar d'akin shima kalar gold ne. falona kuma kujerune kirar Royal masu kalar gold da ja. manya manya ne sosai daga gefe kuma show glass ce me biyu da abun 'daura tv a tsakiya. show glass dinnan ta sha roses da kiristal masu kyau sai tv na a tsakiya aka ajjiyeshi da video a k'asan shi. kafet ne ja malala a kasan falon haka labulayen falon jajayene masu kyau. falon ba tarkace sam abun sha'awa. Goggo Hansatu tace. "Sadiya hauro ki kwanta kinji. kuma ya kamata mu bar hirar nan haka nan gobe za'a d'auki hanyar gida kuma. koda na kwanta na kasa bacci sam. sai tunane tunane na ke yi. babu abunda ya fi tsaya mun sai zancan Auran Aliyu bayan dawowarshi da wata guda. idanu na lumshe a raina nace. "yau ni ce a tsakankanin masoya biyu na shigo rayuwarsu ba tare da sun shirya ba. na rusa musu duk abunda su ka jima su na tsarawa. Haka nima duk wani tanadi da tsara yanda zan gudanar da rayuwar aurena, da yanda zan gigita mijina da soyayyar da saina juya mishi k'wak'walwa, yanxu duk ya kau. Na auri d'an k'auye yaro k'arami.Da wanne idanunma zan iya mishi kallon miji. Shin yama rayuwar k'auyan zata kasancemun? haka nai ta tunani. sai jefin asuba bacci yai awon gaba da ni. WASHE GARI tun sassafe na yi wanka. sanye nake da shadda mai ruwan k'asa. dinkin riga da siket yasha surrani da milk colour d'in zare. d'inkin ya zauna a jikina sosai. kwalliya na yi mai tsari, jikina kuma sai tashin kamshi ya ke yi. takalmi ne mai tsini a kafata milk colour, haka ma mayafin jikina ya kasance milk. Goggo Hansatu tace. " su Hadiza su raka ki ku gaisa da ayagin surukarki da matan gida. kafin su d'au haramar tafiya kuma. dubanta na yi nace. Goggo kema yau za ki tafi? "A'a Sadiya. zan zauna sai nan da kwana hud'u ranar da Aliyu zai dawo sai in tafi. a k'alla zan d'ebe miki kewa. da'di naji sosai da jin bayanin Goggo. fita mu ka yi da su Hadiza. mu na tafe ne nace. Hadiza lallai Bashir yayi kok'ari daya barki ki ka zo bikina tun daga katsina. gaki har kauyenmu. dariya Hadiza ta yi tace. "Haba Sadiya ai muna tare. abinda na ke so dake shine. karki sake kallon rayuwar da ki ka gudanar ta baya. Sadiya abu guda mace take buk'ata a rayuwarta shine ta samu kulawa da tausayi a gidan mijinta. in gidan aure ya samu wannan toh magana ta k'are. ni shawarar da zan baki shine. ki kawo walwala da farin ciki gidan auranki. ki gaiyato haske da raha a zamanki da.Aliyu. ke wayayyace kinsan meye makamar d'a namiji. idan ki ka yi hakan zaki samu nutsuwar da sai kauyannan ya zame miki tamkar America. kai na kad'a. maganarta gaskiya ne. Hakane Hadiza zanyi kokarin hakan. amma wannan sai mun samu fahimtar juna tare da shi. kinsan yaro ne, dole al'amuran ba za su zo mun da sauk'i ba. ni wallahi kunya ma nake ji. Amina tace "shi namiji ba ya kad'an. ni mijina sai da na shekara d'aya a hannunshi ba mu'amalar Aure. sai dai mu yi wasa da juna kawai. gaban na shi ashe ya na da matsala. sai da ga baya ne ya samu lafiya. amma ba wanda yasan wannan labarin sai ku da na sanar ma yau. shi namiji ba'a shekaru bane. kar ki yi girman kai ki je ki shiga wuta a banza." hirar ta mu ta tsaya ne, a sakamakon isowa b'arayin su Goggo Asabe. da sallama mu ka shiga falon Goggo Asabe. duk yayyan Babana su na ciki, da alama tattaunawa su ke yi. gurfana mu ka yi a gabansu mu ka gaishesu da girmamawa. sun amsa a sake babu laifi. kawu Sulaiman yace. "Sadiya. sai ki sake hakuri nan da kwana hudu mu ke sa ran Aliyu zai dawo. ki kula dan baza mu yadda da fitsara irin taku ta 'yan boko ba ma su ido a tsakar ka. Aliyu kuma dole ki mai biyayya domun duk shekarunki da matsayinki kin dawo karkashin ikon shi ne. kar kuma ki ji wani iri. bayan wata guda da dawowarshi za'a d'aura Auranshi. gyatumarki ma ta san da hakan. akwai dokoki da k'a'idoji akan ko wacce surukar gidannan. dan haka za ki iya samun Bilkisu. matar wan Aliyu ta yi miki bayanan daya dace. A sanyaye na ce. Toh kawu zan yi hakan in sha Allah. Su Goggo Asabe a cikinsu ba wacce ta ce da mu uffan. sai daga baya Goggo Asabe tace. "Toh ki koma d'akin ki. magana mu ke yi. dole na kalato murmushi na d'aura ma fuskata nace. Toh Goggo. jiki a mace mu ka fito. mun d'an zazzaga cikin gidan Bilkisu ce tai mana jagora. tare da gabatar mun da surukan gidan. gaggaisawa mu ka yi da kowa. sai dai da dukkan alama ban samu karb'uwa ba sam a wajansu. Dan sai wani hararata suke yi, su nai mun kallon banza haka. komawa mu ka yi b'angare na. Sallama muka soma jiyowa ta namiji a k'ofar b'arayina. Hadiza ce ta fita. "Sannu baiwar Allah, kune k'awayen Amaryar tamu ko? Hadiza da dariya a fuskarta tace. "Eh mune" Murmushi yayi yace. "Sunana Kamilu, nine aminin Aliyu, tun jiya naso in zo dan mu gana da ku, toh sauran abokan namu suna waje, dama a game da sallamar k'ayawyene, bisa ga al'ada." Hadiza tace. "Hakane, sai ku bayar da duk abunda ya sauwak'a, jiya ma baku kawo mana abinci ba" kai Kamilu ya sosa. "Eh ayi mana afuwa, sai yau na gama harhad'o kan abokan, Amma ga abun kari." Hannu tasa ta amsa, leda ce mai d'auke da gasassun zabi, sai robar fenti cike da tea, wanda sai da Kamilu ya fita zuwa cikin zamfara ya siyo kayan tean. nera dubu biyar ya mik'ama Hadiza" "Ga wannan ayi hak'uri, abun yazo mana babu shiri." "Ah babu komai mun gode" ciki Hadiza ta dawo ta kawo mana kayan kari, tare da yi mana bayanin yanda su ka yi da Kamilu. bayan sun gama karyawa, sun yi wanka. sai kuma su ka fito dan tafiya. ina kuka mu ka rabu da su. tare da mun al'kawarin za su kewayo ni. Goggo ce ta ri'ke hannuna mu ka koma ciki. kan gado na fad'a ina ta kuka amma mara sauti. wai wanne irin matsalolin zan fuskanta ne a wannan zaman Auran? mrs Bukhari ce *INA MAI SANAR DA MASOYA CEWAR, LITTAFIN GISHIRIN ZAMAN DUNIYA, YA K'UNSHI ABUBBUWA DA DAMA WANDA YA SHAFI MATSALOLIN DA MATA KE FUSKANTA A GIDAJEN AURE TA FUSKA DA DAMA. DAN HAKANE ZAN BUGASHI A TAKADDA, DOMUN KO WACCE MACE TA MALLAKESHI. KUMA A WAJENA KAWAI ZA'A IYA SAMU, INA KAN HAD'A LIST NA JAMA'AR DAKE SON LITTAFIN, KAFIN IN BAYAR DA AIKIN BUGAWAR, IN KINASON MALLAKAR NAKI A TAKADDA BA TARE DA KINSHA WUYAR BINSHI SHAFI SHAFI BA, KI YI MUN MAGANA IN SAKA SUNANKI DOMUN A BUGO HARDA NAKI, INA MARABA DA KU MASOYANA. SAI NA JIKU.* *GAWURTATTU BIYAR,5🀚TAFIYAR TA MUSAMANCE* 1, *MU GANI A ƘASA..πŸ”₯* _Ummu Affan_ 2, *ABIN CIKIN ƘWAI..πŸ₯š* _Ummu Maher_ 3, *GUNTUN GORO..*πŸ’₯ _Mom Islam_ 4, *GISHIRIN ZAMAN DUNIYA*🌎 _Mrs Bukhari_ 5_ *AUREN WATA TARAπŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨* _Miss Hajo_ Guda Ι—aya N300 Guda biyu N500 Guda uku N600 Guda huΙ—u N700 Guda biyar 1k *ZAKU TURA KUƊINKU TA WANNAN HANYARπŸ‘‡* Fatima Rabiu Sunusi 0037219728 StanbicIBTC Bank. Shaidar biya tanan πŸ‘‡ 0810 433 5144 Masu tura katin MTNπŸ‘‡ 0814 179 9224 ...........πŸ₯šπŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ’₯🌎.... *Ζ³AN NIGER GA HANYOYIN BIYAN KUƊINKUπŸ‘‡ Guda biyar 1000f Guda huΙ—u 700f Guda uku 600f Guda biyu 500f Guda Ι—aya 300f Kai tsaye ku tura da katin Airtel ta wannan number 08141799224 *MUN GODE DA KASANCEWA DA GAWURTATTU TAKUN FARKO* *INA MATAN MASU AMSA SUNANSU NA MA, INA UWAR GIDA, INA AMARYA, INA 'YAN MATA 'YAN KWALISA?* *HAK'IKA DUK MACEN DATA ISA, SAI DA K'AMSHI DA GYARAN JIKI BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI. 'YAR MUTAN KATSINAWA NAZO MIKI DA SIHIRTACCEN K'AMSHIN DA ZAI JIJJIGA MIKI OGA, TA YANDA OGA ZAI LIK'E MIKI.* *SUNAN WANNAN K'AMSHIN MANNE MATA, MAK'ALE MATA* * *WASU KUMA SUKAN KIRASHI DA D'AYE MANNA* 'YAN MATA AKWAI NAKU HAD'IN NA DABAN. *AKWAI KULACCA TA SUDAN* MAI SIRRIN K'AMSHI DA GYARA FATA, GA UWA UBA SA LAUSHIN JIKI, DA KUMA DAWWAMAR DA K'AMSHI A JIKIN FATA. *AKWAI SIHIRTACCIYAR HUMRA, 'YAR SUDAN* WACCE AKAI MA LAK'ABI DA 'YAR BAIWA MAI ABUN MAMAKI. ITA KUMA TADA SHA'AWAR ME GIDA TAKE YI, TARE DA K'ARA DANK'ON SOYAYYA, DA KUMA DAWO MA DA MATA MARTABARSU. UWA UBA AN HAD'ATA NE DA ITATUWAN GYARAN JIKI, DA KUMA SIRRIN K'AMSHI MAI MOTSO SHA'AWAR DUK WANDA YA SHAK'ETA. πŸ’ƒπŸΌπŸ’ƒπŸΌπŸ’ƒπŸΌπŸ’ƒπŸΌ BAN TSAYA IYA NAN BA. AKWAI TURAREN KWANCIYA, WANDA AKE SHAFAWA A MATSE MATSI, DA SAMAN CIKI. πŸ˜€πŸ˜€πŸ˜€πŸ˜€πŸ˜€ KE DAGA JI KINSAN AKWAI AIKI, DAN MAI GIDANKI SAI K'ARA SONKI DA KUMA MAK'ALE MIKI. 🀣🀣🀣🀣🀣 INA DA TURARE D'AN GASKE NA TSUGUNNO, MAI FARFAD'O DA MARTABA DA KIMAR GABAN MACE, K'AMSHI YA DAWWAMA A WAJAN, YANA SAUKAR DA NI'IMA, YANA KASHE INFECTION, YANA MACE MACE TA HAD'E TSAM. YANA K'ARA D'AND'ANO. πŸ’ƒπŸΌπŸ’ƒπŸΌπŸ’ƒπŸΌπŸ’ƒπŸΌπŸ’ƒπŸΌ INA HAD'A TURAREN FANT 'YAR UWA, WANNAN MA WANI SIRRINE NA MUSAMMAN πŸ’ƒπŸΌπŸ’ƒπŸΌπŸ’ƒπŸΌπŸ’ƒπŸΌπŸ’ƒπŸΌπŸ’ƒπŸΌπŸ’ƒπŸΌπŸ’ƒπŸΌ TA B'ANGAREN KAYAN MATA KAMA DAGA NA NI'IMA, NA INFECTION,DAMA NA MATSI IRI IRI. DA DUK WANI MAGUNGUNAN MATA A KWAI SU, 'YAN GASKE, MRS BUKHARI 'YAR MUTAN KATSINAWA TA ZO MUKU A SHIRYE TSAB. AKWAI SETI NA MAI JEGO, WANDA YA K'UNSHI KOMAI DA KOMAI A CIKI. πŸ’ƒπŸΌπŸ’ƒπŸΌπŸ’ƒπŸΌ KANA AKWAI SETI NA AMARYA, ITAMA NA MUSAMMAN NE, YANA D'AUKE DA INGANTATTUN MAGUNGUNAN JIJITA ANKO. 'YAN MATA WANDA SUKE SHIRIN SHIGA DAGA CIKI KUMA AKWAI NAKU SETI NA MUSAMMAN. AKWAI MAN DILKAR GYARAN JIKI NA AMARYA, DA SABULUN AMARE NA MUSAMMAN *BANGAREN TURARUKAN WUTA NA INA NAN* *TURARUKAN D'AKI, DANA KAYA, DA TURAREN GASHI, DA TURAREN WANKA, TURAREN MOPPING, TURAREN WADROPE, TURAREN BAYAN GIDA. KUJERAR TSUGUNNO, KABBASA, DUK INA SIYARWA. DOMUN NEMAN K'ARIN BAYANI TU TUNTUB'I MRS BUKHARI 'YAR MUTAN KATSINAWA. 08179523215 saina ji ku *GISHIRIN* *ZAMAN* *DUNIYA* _Daga Al'kalamin_ _Badi'at Ibrahim_ ( Mrs Bukhari Ibrahim B4B) GAWURTATTU BIYAR 🀚🏻 Labari wanda yai duba kan gwagwarmayar mata a duniya. Da irin gudummawar da ilimin mace ya ke bayarwa ga al'umma. Da kuma rawar da ilimin mata ke takawa a cikin gidajen Aure. ina mik'a sak'on gaisuwar ban girma ga masoyan littafinnan, kuma aminaina na arxiki. Maman Yaseer Kina k'arfafamin guiwata Hajiyata. Anty Yabi yunusa Kin bani gudunmawa ta musamman ina jinjinar ban girma. oum shuraim 1 Dear ke tawace har abada oum shuraim 2 Godiya ta musamman gareki ummu safais ina jin dad'in comments Aisha Auwal godiya nake yi Ban mance da 'yan amanata ba kabo dota. khadija Beebee Ta marad'i Atitin mama Anty faty Rayyana Mrs Abdul Anty Baraka Mmn Nour ummi Barwa Soopy ta yanzu πŸ˜€ Da duk masoyan wannan littafin da basu ji sunayensu ba, kuyi hakuri abunne da yawa. Bazan manta da iyayen gidana ba ANTY HADIZA BARA'U GIDAN IKO. FAUZIYYA D SULAIMAN SUMAYYA ABDULK'ADIR TAKORI ina mik'a gaisuwata gareku Kashi na 1 Babi na 11~12 Goggo Hansatu ce ta dafa baya na. ta ce da ni. "Haba Sadiya. kar ki bari shaid'an ya yi miki wasa da zuchiya. ki dena kuka, kar ki ji kinyi dana sani akan kasancewarki a wannan k'auyan. iliminki zai fi amfani a wannan k'auyan. ba mu san mai Allah ya ke nufi da had'a wannan Auran ba. k'ila ta dalilinki Gishirin zaman duniya ya yawaitu a wannan karkarar. Aliyu kuma kisan yanda za ki yi, ki ja hankalinshi gareki. nasan kinyi girman da kin riga da kin san ta kan duniya. ki yi amfani da iliminki. ki dena duban shi a matsayin k'aninki, tunda k'addarar Aure ta maida ki k'asanshi. dole shine jagoranki, kuma shugaba a gareki, kiyi k'ok'arin k'irk'irarma kanki farin ciki da kwanciyar hankali, Aliyu masanin addinine bazai salwantar da hakkin daya rataya a kanshi ba. ki gode ma Allah mijinki zai dawo a matsayin malamin Addinine. Ba jahili kamar Asabe uwarshi ba." baki Goggo Hansatu ta dinga ba ni. tare da yi mun musalan matan da su ka sha gwagwarmaya kuma daga baya su ka samu nasara. Allah ya d'aukaka su, har tauraruwarsu ta haska duniya ta san da zamansu. da misalan matsalolin da mata su ke fuskanta a gidajen Aure. har da ma gararin da yaran jahilar uwa su ke fa'dawa, da kuma shafarsu da jahilcin uwar ta su ya ke yi. tad'aura da cewa. "Shi rayuwar Aure. Sanyi da taushi ce. Ba zafi da Haushi ba. shi zaman Aure hak'uri da juriya ne. Ba rashin ha'kuri da mita bane. Miji d'an lallashine, ba abun tsokanar fad'a bane. Sadiya in ki ka bi da Aliyu ta hanyar daya dace. sai ya zame mijin alkhairin da ba lallai samarin ki na maraya su zame miki ba. sha'anin zamatakewar Aure ya tab'arb'are ba irin na mu na da bane. amma da yawan tashin hankula da fitintunun da su ke tashi a gidan Aure. kaso mafi tsoka matsalar daga matan mu na hausawa ne. Bance mazan basu da laifi ba, dan sun d'auki kaso mafi rinjaye, tunda sun fimu kaifi hankali da tunani. ke kam kina da ilimin da ni kaina ina alfahari da kasantuwarki d'iyata. Sadiya kar ki yi saken da Aliyu zai soma amsar Budurcin waccan yarinyar da zai Aura. domun shi daren Farko na musamman ne, a rayuwa. duk sanda zai tuno da macen daya soma jin d'uminta a rayuwarshi. toh ke zai tuno. kuma za ki samu Babban matsayi na musamman a matsayinki na uwar gidan Aliyu. Ban sanki da taurin kai da raini ba." wunin ranar kab Goggo Hansatu ta na yi mun jawabai ne na yanda zan gyara rayuwar Aure na. kuma na ji dadin hakan matuk'a. Hakan ya wawuce mun kaso mafi tsoka na damuwar dake addabata. washe gari da safe. bayan na yi wanka. ina sanye cikin atampar soso. jikin atamfar bak'ine, sai manyan fulawa jajaye da aka k'awata atampar da shi. kwalliya na yi me kyau. Goggo Hansatu tace. "Sadiya na ji dad'in yanda jawabai na su ka shige ki. shine gudummawata ta bikin ki da ban bayar ba. kuma na ji dad'in yanda naga annuri a fuskarki, kuma kin saki jikinki sosai, tare da rungume k'addararki hannu bibbiyu, ina fata da rok'on Allah yasa hakan ya zame miki alkhairin duniya da lahira, ki samo tikitin shiga aljannah a hannun Aliyu." murmushi kawai na yi mata. tabbas na d'auki dakon duk shawarwarinta domun babu na yadawa. amma a xuchiyata akwai wani miki da bansan yaushe zai warke ba na soyayyar Ahmad da yai ma rayuwata raunin da bana jin akwai namijin da zai iya warkar mun da wannan raunin. k'addarata kam na amsheta. domun bazanyi jayayya da buwayar Allah ba. Goggo hakane. in sha Allah za ku same ni mai biyayya a gareku. kuma zan hau kan tsanin da kika d'aura ni akai har zuwa Aljanna. zanje in.Gaishe da su Goggo ne. sai in shiga wajan Bilkisu za ta sanar da ni dokokin da aka gindayawa surukan gidannan, kamar yanda kawu ya umarceni. " Toh Sadiya. sai kin dawo. fita na yi. tare da bin Goggonnina d'aya bayan d'aya ina gaidasu. gabaki d'aya a tsarge na ke. dan surukan gidan sai wani tab'e baki su ke yi da ganina. wasu ma har barin abinda su ke gudanarwa su ke yi, su shige d'aki. dan karma mu gaisa. ga habaici da Hasiya matar Dauda take yi mun a duk sanda zamu had'u kan cewar na gama tsofewa a birni ba miji, daga k'arshe an kawo ni k'auye. na Auri k'anin bayana, abun kunya. data gama sai ta sa dariya. yauma hakanne ya faru. dana wuce ta, sai na yi murmushi a raina na ce. jahilci ciwo wanda ya fi hauka. da sallama na shiga d'akin Bilkisu, bayan ta ba ni izini. zama na yi a saman kujerarta muka gaisa. d'akinta ba k'azanta sam a gyare yake tsab ta kunna turare d'an tsinke ya na ta 'kamshi. d'iyarta tana zaune a kan po ta na bayan gida. ga kuma wainar gero a hannunta ta na ci abunta kuma da hanun hagu. Bilkisu ki hanata cin abinci da hannun hagu. sannan bai dace mutum na kan bayan gida kuma ya na cin abinci ba. d'an murmushi Bilkisu tayi tace. "lahh ai ni bansan hagu da damar yara ba." da mamaki na bita da kallo. tana k'ok'arin k'arb'e wainar hannun d'iyar tata. murmushi kawai na yi na ce. Dama kawu ne ya turo ni wajanki, ki sanar dani dokokin da ke kan surukan gidannan. dan in san su. tace "Toh doka dai ta farko shine. Kawu matan shi basa d'aura sanwa. duk wata suruka a gidannan za ta zuba mishi abinci a kai mishi amma sau d'aya a rana. toh sai mu ka yi tsarin da mu ka kasafta kan mu gida uku. wasu da safe, wasu da rana, wasu da daddare, mu ke kaiwa. kuma babu fashi. komai ciwo. na biyu kuma shine za ki dinga yin girki da surukarki wato uwar mijinki. safe. rana,dare. shima ba fashi. da abincin gandu ake yi. bayan wani rikici daya afku a tsakaninmu. shine kawu ya saka wannan dokar, cewar kowa ta yi girkinta, shine ko wacce mace ta samu sauk'in rayuwa. Abu na gaba shine. wajibine ki bi matan yayun mijinki, duk safiya ku gaisa. akwai fitowa hira tsakar gida, wanda ya ke wajibi ne. dan sada zumunci. dole yaranmu su kasance a tare. domun akwai d'akin yara mata. da d'akin yara maza da aka ware suna kwana, dan shak'uwa. kuma baki da wani iko a matsayinki na matar k'ane sai abinda matan yayu suka zartar akan kowa ma. wannan su ne dokokin wannan gida. murmushi na yi mai k'unshe da ma'anoni da dama wanda na barsu a raina. godiya na yi mata ta fito, zuwa d'akina. Goggo Asabe ce a gaban mai gari su na k'arashe zancan su. "ni hak'urin da na ke ta nema ka yi mun shine. Abar yaronnan ya Auri Khadija. kar a tauye musu hakkinsu. Aure kuma, ai ba Aliyu bane ya ga mace ya ce ya na so ba. ni ma kaina fa na fi son Khadija." mai gari ya ce. "maganar gaskiya Asabe. ba na jin zan iya sauka akan wagga baka. Aure ko? na amince ya Aure ta. amma in ya Saki waccan 'yar barikin daya Auro. in kuwa ba haka ba. wallahi sai dai a hak'ura da Auran. dama yarinya ta na da manema. sabida al'kawarin da ke kanmu ne yasa ban ba ma kowa dama ba" Goggo Asabe gabaki d'aya kanta ya chaza sosai. kuma ta san Aliyu zai shiga tashin hankali mai yawa in aka ce yau ya wayi gari ya bar Khadija. cikin sauke murya tace. "Toh ranka shi dad'e, ni zan koma. duk abunda mu ka yanke da 'yan uwa na, da shi kanshi k'usar yak'in in ya dawo, za ka ji a bakin mai dambu. Maganar saki daya dawo, kafinma ya shiga d'akinta ta juya mishi kai, zan sa ya sauwak'e mata. Ka sauraremu." ( hmm maman Yaseer ke fa kinji) "Toh madallah ina saurarenki Asabe, yaro Allah ya dawo dashi lafiya." sallama ta yi mishi ta fito. ta na tafe ta na ta faman tunani akan wannan lamari da komai ya ke son lalace mata. "duk Bala ne ya ja mun wannan tsiyar. ya k'ak'aba ma yaro Auran dole, yaro da wacce ya ke so shi kuma. ni wannan kafiya ta me gari ta ishe ni wallahi" duk maganganun nan ta na yin su ne, ita kad'ai a hanya. har ta iso gida. ( Oum Shuraim tace, "kya ji da shi dai ) Sadiya wunin wannan ranar cikin nasiha Goggo Hansatu ta k'arar mana da yinin. washe gari ma ta d'aura daga inda ta tsaya. na saki jiki na sosai babu laifi. kullum da safe ina zuwa gaishe da Goggonnina da kawu da matan shi. haka duk wacce na had'u da ita a tsakar gida, ni dai zan gaishe su. wasu su amsa, wasu su yi kunnen uwar shegu da ni. Ina jiyo su, suna hirar tsakar gida tare da shewa. Amma ban tab'a ko lek'awa ba. Allah ya kawo mu ranar Dawowar Aliyu. Goggo Hansatu tun safe ta yi ma matan gida sallama ta kama hanyarta. Ni kuwa a ranar na ci kuka har sai da idanuna su ka yi wani mummunan kumburi. ji na ke yi tamkar in sa hannu na a ka, in rintima uban ihu, ko zan ji sanyi a raina. Wani irin suya zuchiyata take yi mun. bayan na share hawayena ne, sai na mik'e na duba agogo na 'karfe biyu da rabi na rana. kitchen na shiga, na kunna ritso na d'aura ruwan tea. ina tsaye ya tafasa. a cup na zuba wanda zan sha. sauran kuma na zuba a tea flase na barshi a kitchen d'in. dai dai zan fito daga kitchen kenan. sai ga Fatima yayar.Aliyu ta shigo da sallamarta. cikin fara'a na tarbeta. amma kuma sai na ga ta turb'une fuskarta. babu yabo babu fallasa ta amsa gaisuwata. na ce da ita. mu shiga daga ciki mana Fatima, naga kin tsaya daga nesa. Bud'ar bakinta tace. "Fatima kuma, hala kin manta ni Yar Mijinki ce? Koda ma, mun yi tunanin ganin rashin d'a'a a wajan 'yar boko. dama d'abi'arku ce rashin kunya

Chapter 4 of 7