.
Fuska a sake muka gaisa kafin ta ce “ke ma dai kin kusa ki faso gari ki huta da yawon raba abinci a restorant”
Na yi murmushi na ce “ai kuwa dai kin ga ban ma shaida wa Hajiyar na samu aiki ba”
“In an gama miki interview ai sai ki je ki sanar da ita”
Haka muka ta yin hira har muka isa wani katafaren kamfani,duk da ina cikin garin amma ni ban taɓa ganinsa ba da idona ina dai jin labarinsa.Tun da muka fito daga cikin mota ake gaishe da Zulaihat,sai na fahimci tana da babban matsayi a wurin .
Jikina ne ya soma yin rawa lokacin da muka shiga ofis ɗin ogan,komai na wurin ja ne tun daga labulaye capet da kuma kujeru.Hatta kalandar da ke ɗauke da jerin sunayen watanni ita ma ja ce,haka ma book ɗin nan da mutane ke ɗauke abu mai muhimmanci shi ma ja ne.
Wuri ta nuna min na zauna kafin ta ce “jira yanzu zai fito” sai na sakar mata murmushi kawai ina mai ci gaba da sauraren bugun zuciyata.Kamar minti biyar haka wani babban mutum ya fito,baƙi ne wulul kuma gajere yana da ƙiba sosai ga kuma ƙaton tumbi kamar mai cikin wata tara .
Cike da girmamawa na sauka na gaishe shi har ƙasa,ya amsa cikin sakewar fuska kafin ya bani umarnin na koma inda nake.Zulaihat ce karɓi takarduna ta miƙa masa,a nutsu ya shiga duba su kafin ya soma yi min tambayoyi ina basa amsa daidai da abin da na sani.
Ya yi wani murmushi da ya ƙara bayyana muninsa kafin ya ce “Zuly ƙawarki nada kaifin basira kam,ina ga ita ya kamata mu baiwa kujerar mai kula da baƙinmu na waje ko ya kika ce?”
Ta yi wani murmushi tana mai cewa “ai kuwa ko a makaranta ita ce ta ɗaya,sannan ta saba jagorantar duk wani abu da ya shafi jagoranci ina ga babu matsala in dai ta yarda za ta yi”
Sai duk suka maido dubansu gare ni,wata irin rikicewar na yi da kuma mamakin ƙarshen furucin Zulaihat wai in na yarda.To me zai hana na yarda ? Abin da na jima ina nema ɗin shekara da shekaru.
“Ba ki ce komai Luby” Zulaihat ta faɗa .
Muryata har rawa take na ce “na yarda mana ina so,in dai maganar turanci ce ai kin san nan na fi ƙwarewa babu wata matsala” ina gama faɗar haka sai ogan ya miƙo min wata takarda haɗi da jar biro ya ce na saka hannu a ƙasa wanda ke bada tabbacin na yarda da dukkan sharuɗan zan yi aiki a kamfanin .
Hum! Haule kin san dayawa mutanenmu ƴan Afirka muna yin babban kuskure shi ne saka hannu a takardar da ba ka karanta jawaban da ta ƙumsa ba,to ni ma a lokacin haka na rabbata hannu na miƙa masa.A tare suka saki wata ajiyar zuciya mai bayyanar da tsantsar farin ciki.
Sai a lokacin kuma ogan ya buɗe ƴar takardar da ke ɗauke da hotunana biyu,ɗaya ya ɗauka sannan ya buɗe wani fayil mai ɗauke da hotunan mutane dayawa sannan ya maƙala nawa tare da yi masa wani rubutu can ƙasa.
Bayan ya gama sai ya dubi Zulaihat ya ce “ki kai ta wurin shopping ki tabbatar kin zaɓa mata kayan da za su fi dacewa da aikinta,sannan inda buƙata har gyaran jiki a yi mata .Kin dai fi ni yadda ya kamata na bar miki komai a hannunki,sannan zuwa gobe za ta soma aikin kuna iya tafiya”
Ba mu ƙara cewa komai ba muka fito,cikin yanayin tsarguwa na ce “Zulaihat mene ne kuma na yin gyaran jiki? Halan datti gare ni irin sosai?”
Ta tuntsire da dariya ta ce “in ba abinki ba ke da za ki tarben turawa in ba ki kama kanki ba kina ganin za su yarda su zuba hannun jari a kamfaninmu?”
Murmushi kawai na yi na basar,daga nan gidan gyaran jiki ta kai ni cikin wata ƙatuwar inji na shiga iya kaina kawai ke waje shi ma bayan an gama wannan ɗin sai da aka saka min relax aka sa ni a tukunyar busar da gashi.Bayan mun gama komai sai ta saya min wata doguwar abaya wajen matar mai gyaran jikin,na saka sai na dawo tamkar wata balarabiya na yi kyau sosai.Daga nan gidan cin abinci muka je bayan mun cika tumbinanmu sai muka wuce mall,yadda na ga Zulaihat na jido riga da wando yasa na yi mata magana don ba zan iya saka su ba amma sai na ta saurare ni.Bayan su kuma ta saya min har da after dress da kuma sari ,wasu kayan ma ban san da irinsu ba.
Na yi tunanin gida za ta kai ni amma sai ta wuce da ni gidanta,a falo muka zube ta sa masu aikinta suka kwaso tulin kayan da ta sayo min kowanne da takalminsa.
Sai da aka kawo mana kayan maƙulashe muka taɓa tare da jus sannan na soma duba kayan,sai dai ban ɗauki lokaci ba bacci yayi awon gaba da ni a nan take kuma na soma yin wani mafarki marar kan gado.....
[02/04 11:31] MRS SADAUKI: *BAƘIN RUHI*🧌🐲
```LoVe aNd HoRrOr story```👽
By
Chamsiya Laouali Rabo
{MRS SADAUKI💫✍️}
*SADAUKARWA :* Ga dukkan iyayenmu MATA da suka tsaya tsayin daka don bamu kariya a kan dukkan wani da ke son cutar da mu.
*FCWA*☀️
________________________
05
Mafarki ne wanda sam rabon da na yi sa ina jin tun lokacin isar min da saƙon balaga.Sai da wannan ya sha banban da wancan,don wannan sarai ina ganin wanda ke tarayya da ni.Ba kowa ba ne ba sai oganmu wanda yanzu ya gama yi min interview,abin mamaki kuma a cikin mafarkin bai fi yadda yake yabona ba yana cewa “ashe Zuly ta yi gaskiya kina da taurari masu kyau masu haske,ke ɗin maƙurar ilimi ce” ban farka ba har sai bayan komai ya kammala.A hankali na buɗe idona da suka yi min nauyi,sam ni na manta ma a inda nake sai bayan na watsake ne na tuna gidan Zuly ne nake.
A hankali na tashi zaune ina jin duk jikina na yi min ciwo kamar wacce aka yi wa shegen duka.Ta zo da murmushinta ta ce “ashe kin tashi? Bari na sa a haɗa miki ruwan wanka in kin gama sai ki ci abinci”
Ɗan murmushin yaƙe na yi na ce “to” sai ta ƙwala kiran ƴar aikinta bayan ta zo ta faɗa mata aikin da za ta yi sai kuma ta dube ni kamar mai son tantance wani abu kafin ta ce “kayanki suna ɗakinki an jera a drower”
Abun mamaki kasa yi mata muso na yi ko kuma na tambaye ta yaya na samu ɗaki a nan gidan.Ita ce ta yi min jagora na isa can ɗakin wanda tuni an haɗa min ruwan wanka a baho,kar ku ji zancen wasa a ranar nan Zuly ce ta yi min wanka tamkar wata ƴarta ni kuma na kasa yin wani kataɓus.Duk da ina tune na yi mafarki amma sam tunanina bai bani na tsarkake jikina ba,saboda controling nasa ake yi.Bayan na fito ita ce ta bani kayan da na saka,sannan aka kawo min abinci kamar yadda ta shaida min tun farko.A cikin abincin nan Allah kaɗai ya san irin kalar maganin da aka saka min amma a haka na ci,kar ku tambaye ni maganar sallah don dama can farko ni ɗin na kasance mai wasa da ita ba kullum nake cika biyar ba sai in Umma ta yi min faɗa wannan yasa ko kaɗan ban samu ƙarfin zuciyar yunƙurin yinta ba.
Ina cin abinci Zuly na yi min hirar yadda aikina zai kasance a gobe da kuma yadda tsarin yake,sai kuma ta soma nuna min yadda ake yin aiki da wata ƙatuwar waya bayan nan kuma ta kira ƴan aiki biyu suka yi min tausa da wani man da aka tanada don yin tausa sai dai shi sun garwaya shi da gubar tsafinsu.
Har cikin ɓargon jikina nake jin yana ratsa min ,a sannu a hankali kuma bacci ya ɗauke ni nan ɗin ma mafarki na yi gani nan a wani ɗakin taro duk turawa ne ciki ni ɗaya ce baƙar fata.Masayar turanci kawai muke yi kowanne na yaba kamfanin da yake yin aiki,bayan mun gama meeting kuma sai muka je muka yi wanka cikin swimming pool maza da mata haka duk muka shiga ciki babu wata suturar kirki.Ina farkawa wannan karon babu kowa a ɗakin sai ni ɗaya,sannan babu wani haske sosai shuru na yi ina daidaita tafiyar numfashina.Daga nan kwance na ga lokacin da wata baƙar inuwa ta fita amma ban iya tantance ta mace ce ko ta namiji.
Kamar minti biyu sai ga Zuly ta shigo tare da kunna ƙwan lantarki,na lumshe ido tare kuma da buɗe su.
“Ki tashi ki shirya ƙarfe bakwai saura ”shine abin da ta ce min.
Da mamakin jin wai har dare yayi gari ya waye na ce “kina nufin yanzu safiya ce?” wani irin kallo ta yi min kafin kuma ta fita,na sauke ajiyar zuciya na tashi na shiga toilet sai a lokacin kuma na lura da an canza min kayan jikina zuwa na bacci.
Cikin bahon wankan na shige,ina tunanin kaina a can ƙasan zuciyata sai dai fa na kasa tuna wace ce ni daga ina nake abu guda kawai ke cikin ƙwaƙwalwata shi ne aikina da kuma Zuly sai oganmu wanda nake jin mugun tsoronsa ya samu wuri a zuciyata ya zauna daram.
Bayan na gama wankan sai na fito,da taimakon wasu turawan masu aikinta na kimtsa cikin wasu arnan kaya riga da wando waɗanda suka ɗame ni sosai suka fitar da shap ɗina.Tamkar wata ƴar tsanar roba haka na koma na yi kyau sosai,gashin kaina kuwa an dunƙule min shi tsakiya sai aka ƙara min da ribbob na gashin doki ta yadda ya sauka har gadon bayana.
Zuly ta shigo ita ma cikin shiga mai kyau sai dai na fi ta haɗuwa kasancewar na fita kyawun fuska da na jiki.Jaka ta miƙa min da sabuwar waya irin ƙatuwar nan wacce ake aikin ofis,kafin ta ce “mu je” ta kamo hannuna,dakyar nake tafiya saboda yadda ban saba hawan takalmi masu tsini ba.
Da muka fito harabar gidan nan na ga ikon Allah don kuwa ba gidan da muka zo ba ne ni da Zuly,wannan tamkar aljannar duniya haka yake.Hatta motocin da ke wurin sun sha banban da waɗancan,cike da girmamawa aka buɗe mana gidan baya muka shiga abun mamaki har da masu take mana baya.Sai da muka hau babban titi ne sannan na gane nan ɗin fa Turai ce ba Afirka ba,wani kamfani ne muka je tun a bakin ƙofa Zuly ta tsaya kafin ta ce “ki nutsu ki aiwatar da aikinki kar ki wani damu jin cewa ke ce baƙar fata a cikinsu” kai na jinjina mata kafin Bodyguard biyu su take min baya har zuwa ɗakin da za a yi meeting ɗin.
Direct kujerar da ke ɗauke da sunana na je na zauna,suna ne wanda ba wanda uba mahaifina ya saka min ba a'a Oga ne ya canza min shi ba tare da na san ta ya aka yi kuma na gane nawa ne ba.Leena shine sunan da ke jikin ɗan ƙaramin allon gabana,sai da na yi gyaran murya sannan na danna wayar hannuna wacce ke ɗauke da dukkan bayanan da za mu tattauna a kai.
“Sunana Leena daga ƙasar Kamaru,wakiliyar kamfanin El Mansoor a yau mun kawo muku wata babbar haja wacce muke fatan za ku ji daɗinta sosai fiye da sauran business namu na baya” ina kawowa nan sai na yi shuru ina yi musu murmushi su kuma duk fuskokinsu sun nuna zaƙuwar jin abin da zan ce ɗin.
Na ci gaba da cewa “a ƙididdiga ta malamanmu na spirituality sun gano cewa dayawan mutane a yayin yin bahaya mutum na zubar da kaso hamsin cikin na abin da ya shafi taurarinsa marar kyawu,yayin da kuma zubar da yawu a lokacin da mutum ke tsugunne kan salanga yake ɗauke ɗigo biyu na sinadarin tauraronsa mai haske.In muka haɗa hamsin da biyu sun tashi ɗari cicif.Na san dayawanku za su tambaya ta ya aka yi aka samu ɗari? To amsar mai sauƙi ce duk tauraro mai haske ɗaya yana daidai da kaso hamsin na baƙin tauraro,da za a saka su a injin markaɗe a garwaya su to tasirin farin tauraro ne zai ƙwace kaso mafi rinjaye.Kun ga shi kenan mun samu tauro ɗari kenan” duk shiru suka yi suna nazari amma babu wanda ya iya cankar ainahin gamsashiyar amsar kawai sai suka fara yi min tambayoyin yadda za su yi su zuba hannun jarin wanda dama ni shi nake jira.Sai na soma yi musu bayani dalla-dalla “iya adadin kuɗin da mutum ya zuba iya adadin taurarin da zai samu,kenan kowa sai ya aiko min da saƙon abin da ya yanke ta adreshing email namu”
Ina kawowa nan sai Zuly ta shigo ita da wasu masu aiki su biyu suna ɗauke da tray,amma ita Zulyn ce ta ajiyewa kowa kofin shayi a gabansa tana ajiye min na ɗauka na soma kurɓa ina kallon yadda suke shawara a tsakaninsu.
Ba a kuma ɗauki lokaci ba kowa ya soma faɗin abin da zai zuba na hannun jari,bayan nan duk sai aka watse aka bar ni daga ni sai Zuly wacce ta danna wa oga video call tana murmushi tare da yi masa congratulations akan aikin da na yi nasara ba tare ni na san muhimmancin meeting ɗin ba ko kuma ina jawaban da na kawo suka dosa ba.
Yadda suke murna yasa ni ma na ji sanyi a raina,ina jin oga na cewa “ku tawo gida mu yi shagalin murnar a nan”
Yanayin fuskar Zuly ya ɗan canza ina ganin lokacin da ta saci kallona ta wutsiyar ido kafin ta ce “oga kana ganin lokaci yayi da Luby za ta ga zahiriya da idonta?”
“Eh mana! Ai ba zama za mu yi muna kashe kuɗi wurin controling memorynta ba kawai ku dawo yanzu,sai ku same ni a can filin hutawana ”
Da ƴar damuwa a fuskarta ta ce “oga ko dai ka tarbe mu a can ɗin,don ina gudun Luby ta yi min tirjiya ko borin hauka”
“Ki yi yadda na ce” yana gama faɗa ya kashe,sai a lokacin ne ni kuma na jefo mata tambayar da ta ɗaure min kai “Zuly wace ƙasa ce nan? Ta ya aka yi muka zo nan?”
“Ki taso mu je,yanzu kin samu amsar tambayarki in mun koma Kamaru” ta faɗa tare da nufar ƙofa,sai na take mata baya ina mai ci gaba da yi mata wata tambayar “amma ina ne nan?” ba ta bani amsa ba har muka shiga mota muka isa gida.
Da umarninta kuma na bi bayanta zuwa wani ɗaki wanda babu komai a cikinsa sai wani madubi da aka rufe da jan ƙyalle.A gabana ta buɗe shi tare da ɗaukar wuƙa ta tsaga yatsanta jini ya soma ɗiga sai ta shafi madubin nan take yayi ƙara ƙiiiii tare da buɗewa ya fitar da hoton ƙofa amma fa ba ƙofar ba ce don ba ka ganin komai sai wani farin abu kamar gajimare.
Jikina ya ɗauki rawa na ce “ina ne nan kuma Zulaihat?” na yi tambayar ne jin tamkar tunanina ya dawo normal,iya ni ɗaya kawai ke sarrafa shi.
“Ba mu da saurin lokaci Lubna ki zo mu tafi” ta faɗa tana kamo hannuna da niyyar shigar da mu cikin madubin,a tsorace na ce “mu je ina? Wai cikin madubin? Zulaihat wannan ai tsafi ne.Ina kika kawo ni? ” ba ta bani amsa ba ta wani fizgo ni muka ratsa mirror ɗin sai gamu muna yawo cikin wani iska kafin kuma ƙyaftawar ido na gan ni a cikin ɗakin Zulaihat a cikin falo.Tuni zaren carbin tunanina ya tsinke,dukkan jikina rawa yake yi min ina son yi mata tambayoyi amma ina tsoron jin amsoshinsu don ban so a ce abin da nake zargi gaskiya ne.
Ita kuwa Zulaihat sai ta yi fuska tare da haɗe rai ta ce “ki tashi mu je Malama oga na jiranmu”
Cike da masifa na ce mata “babu inda zan je! Gidanmu zan tafi”
Nan ta yi wata dariya kafin ta ce “au haba? Kenan? To wuce ai ga ƙofa nan sai ki tafi”
Sam ban damu da gyatsen da ta yi min ba sai na fita daga ɗakin na fito harabar gidan,babu kowa a bakin get sai na je na buɗe ƙofa da zumar fita nan na yi arba da wata lukutar masifa don kuwa ruwa ne maƙil a wurin tamkar za su taɓo sararin samaniya,babu shiri na koma can cikin falon sai na tarar da ita tana shan ayaba cike da shaƙiyanci ta ce “har an dawo daga gidan ko kuwa an fasa zuwa?”
Idona ne suka kawo ruwa shaaa,ina kallon Zulaihat wacce da dukkan alamu babu ɗigon imani a ƙirjinta.Miƙewa ta yi tare da ɗaukar key ɗin mota ta ce “mu je” dole dangi na ƙi yasa na take mata baya muka shiga motar .Mai gadi ya buɗe mata gate yana wani murmushin da ya tabbatar min bakinsu ɗaya shi da Zuly duk munafukai ne,gudu sosai ta yi har muka isa gidan Ogan.Muna shiga ana kiran sallar magrib,a zaune muka tarar da shi kan kujeru na alfarma ya saka ɗan madaidaicin table a gaba mai ɗauke da cake wanda aka yi wa kwalliya kamar ba ci za a yi ba.
Tsoron Ogan ne ya ƙara ratsa ni,amma duk da haka ita ɗaya kawai ta gaishe shi.Ya amsa yana kallona kafin ya fara jawabinsa “Luby na san zuwa yanzu kin fara gane aikinki, sannan kin san cikin me kika shiga,da kuma su wa kike tare da su.Sai dai ki sani a tafiyarmu ba gudu ba ja da baya,kamar yadda kika saka hannu a yarjejeniyar tsarin aikinmu za ki yi komai da family suka buƙata wato ƙungiya,to ya zama dole ki yi shi.Sam family ba mu da matsala,ba kamar sauran ƙungiyoyin da kika sani ba ne,mu sam ba mu da buƙatar jini sai in dai mutum ne ya kawo taurin kai muke ɗaukar mataki mai tsauri a kansa.Abin da muke so ba komai ne ba sai abin da bai da amfani wurin al'umma,kamar dai abin da kika gabatar a yau wato kashi/bahaya sai kuma sperm ko yawu ko kuma audugar mata da suka riga suka yi amfani da ita shi kenan fa.Mene ne matsala a nan?” ya ƙarashe tambayar yana mai kafe ni da idonsa masu mugun dafi.
Wasu sabbin hawaye suka zubo min kafin na zube a gabansa na ce “don Allah ka yi haƙuri ka goge sunana daga ciki, wallahi na yi ma alƙawari babu wanda zan faɗa wa wannan labarin ko da kuwa iyayena ne”
Yayi wani murmushi ya ce “tuni ai iyayenki sun san da aikinki,don yanzu haka mahaifinki na asibiti an yi masa gyaran ƙafa sannan mun aika saƙon cewa yau ke ce za ki yi gadi a babbar pharmacie ɗinmu ta saida magunguna.Ko ba ki yarda ba?” yayi tambayar yana mai jawo wayarsa ya kunna min video duk abin da ya faru tun daga lokacin da aka ɗauko Abbana har izuwa lokacin da suke asibiti an yi masa aiki ga Ummah nan zaune kusa da shi fuskarta cike da farin ciki.
Wani irin tausayin kanmu ne ya kama ni,tabbas sun yi min dabaibayin da ban isa na warware ta sauƙi ba.
“In kuma kika ce za ki bijire minti biyu yayi yawa zan aika mahaifinki barzahu” oga ya faɗa .
Cikin razani na dube shi,sai ya gaskata maganar ta hanyar cewa “ƙwaran gaske ,kamar yadda kai ki ƙasar Turai bai yi min wahala ba haka zan katse igiyar numfashin mahaifinki don haka kar ki kawo min wasa ki zo ki yanka cake ɗin nan kafin ya sha iska”
Yana gama faɗar haka sai Zuly ta miƙa min wuƙa,ba don na so ba na yanka cake ɗin wanda yayi daidai da jin wani mashi ya caki zuciyata tamkar ma zuciyar tawa ce na yanka.
Mu uku muka cinye cake ɗin duka,kafin Zuly ta ja ni mu koma can gidanta.....
Ga masu son fara yin payment 500 via 2670215530
ZULFAU YAHAYA
Ecobank DM +22795045822
[02/04 11:51] MRS SADAUKI: *BAƘIN RUHI*🧌🐲
```LoVe aNd HoRrOr story```👽
By
Chamsiya Laouali Rabo
{MRS SADAUKI💫✍️}
*SADAUKARWA :* Ga dukkan iyayenmu MATA da suka tsaya tsayin daka don bamu kariya a kan dukkan wani da ke son cutar da mu.
*FCWA*☀️
________________________
06
Da muka isa gidanta dakyar na samu na yi sallar isha'i,ita kuwa magrib kamar yadda lokacinta ya wuce to haka ta wuce ni don ba zan ranka ta ba.
Gida nake son tafiya,amma da dukkan alamu ba zan samu wannan alfarmar ba.Haka na yi shuru cikin ɗaki ina tunani iri-iri da kuma mamakin yadda Zulaihat ta koma muguwar sheɗaniyar marar imani.Na goge hawaye masu ɗumi da suka zubo min lokacin da tunanin yadda na ga iyayena suna farin ciki ya faɗo a kwanyata.
“Luby sai fa in kin so ne za ki damu,kamar yadda oga ya faɗa miki mu family sam ba mu da wata matsala.Kin ga fa babu wani abu da za a nema wurinki in kika cire lokacinki,ni ban ga abin damuwa ba a aikin da babu kashe mutane ciki sannan ko jinin ɗan tsako ba mu buƙata”
A lokacin da ta yi min wannan magana sai kuma na ga fa kusan tana da gaskiya,duk da cewa su ɗin matsafa ne amma dai fa ba su kashe mutane.Amma abin da ya fi bani mamaki bai fi ta yadda suke son abubuwan shirme ba,cikin son sanin dalilin haka na jefo mata tambayar “Amma Zulaihat me za ku yi da kashin mutane?”
“Don Allah ki bar ce min Zulaihat ɗin nan,ki kira ni da Zuly sannan maganar me za mu yi da kashin mutane ke ce a ba ki san amfaninsa ba shi yasa amma da shine ai ake yin takin zamani ana kaiwa gona don yin noma”
Na ja ajiyar zuciya da yake ni sokuwa ce sai na yarda da maganarta,kuma in faɗa muku gaskiya sosai kalamanta suka yi tasiri a raina don sai na ji na kuma yarda zan yi aiki da su.Ban taɓa sanin illa ne ba sai da na haɗu da ke Haule na ga irin abubuwan da kike yi na ban mamaki.
Jin na samu ƴar nutsuwar ruhi sai na je na yi wanka da ruwa masu ɗumi,da na fito na sha salade na fruit sai kuma a lokacin ne Zuly ta bani wayata wacce take sabuwa dal.Wani irin daɗi na ji ganin ta canza min waya amma layina ne a ciki,ta yi wani murmushi tare da zama kusa da ni ta ce “kwaɗayin na gan ki cikin daula yasa na kawo ki cikin family,dubi yadda jikinki yayi kyau cikin ƙanƙanen lokaci ”
Na ɗan yi murmushin farin ciki kafin na ce “ni dai ki koya min yadda ake aiki da ita” ta yi ƴar dariya kafin ta soma nuna min,muna yi muna taɓa hirar makaranta da kuma ƙawayenmu wanda muka yi aji guda.Duk wani wanda nake da labarinsa sai na faɗawa Zuly aikin da ya samu ko kuma halin da yake ciki.Ban taɓa tunanin cewa rahoto ne take haɗawa ba don farmakarsu sai a ranar da ni ma tawa mission ɗin ta zo,zan faɗa muku yadda komai ya wakana sannu-sannu.
A daren nan sosai muka jima muna hira kafin duk mu kwanta, washegari Zuly ce ta tashe ni sai kuma ta hana ni na yi wanka sallah kawai na yi na saka kayana waɗanda na fito da su daga gida sai jakata.
Fita muka yi muka shiga mota ta kai ni asibiti da tambaya muka samu ɗakin da su Ummah suke.
Ina ganinta na je na rungume ta ina tambayar jikin Abba wanda ke bacci.
“Da sauƙi sosai yanzu likita ya shigo ya duba shi tare da yi masa allura,ya aikin Lubna? wannan fa?” Ummah ta faɗa tana nuna min Zuly .
“Ah na manta ban gabatar miki da ita ba,Zulahait abokiyar aikina ce” na bata amsa.
Umma ta ɗan yi murmushi kafin ta ce “ma sha Allah! Allah ya taimaka ya baku sa'a ya kuma baku cimma nasarar aikinku,ki ƙara yi wa oganku godiya don Allah Lubna .Mutum mai kirki jiya bai bar wurin nan ba har sai da ya ga an shiga an kuma fito da Abbanki”
Wani irin sanyi ya ratsa ni jin wani abin farin ciki,na so in zauna da iyayena amma Zuly ta ƙi bani damar yin haka ta hanyar cewa “ki dai tashi mu je gida ki yi wanka ki canza kaya sai ki dawo ko?”
Da wannan tasa ta ci galaba kaina muka fito,“Zuly mene ne haka? Na ga kamar ba ki son na zauna tare