Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
2 / 11
pampo.Na matsa kusa da ita na ce “Innarmu kuka kike? Ki yi haƙuri don Allah ki bar kuka in kina yi hankalina tashi yake” ban san me ya ja ra'ayin Innarmu a wannan lokacin kawai dai na ji ta jawo ni tare da rungume ni tana mai cewa “Haule ina son nesanta ki daga gidan nan amma banda ƙarfi ko izzar yin haka,na sani ke ce ta gaba” “Ta gaba kamar yaya? Innarmu wai mene ne kike son faɗa min?” na tambaye ta duk da a lokacin ba zan wuce shekara goma sha biyu ba amma na fahimci kamar da akwai wani sirri da Innarmu ke ɓoye min” ina kawowa nan sai na yi shuru ina goge ƙwallar da ke yi min zuba saboda wata irin kewar mahaifiyata da ta tsirga min,na miƙe na ce “zan tafi sai kin iso” “Jira na saka kaya mu koma tare” ta faɗa ita ma duk idonta sun yi ja,bayan ta kimtsa muka yi wa Ummah sallama muka dawo gidan Hajiya sai kuma muka tarar da wani sabon tashin hankali Maheer ne a kwance duk ya sandare kamar gawa ga kuma likita biyu kai gare shi.Ni da Lubna muka kalli juna don kuwa tuni muka san mene ne matsalar,da kuma maganin da zai warkar da shi..... [07/03 17:32] MRS SADAUKI: *BAƘIN RUHI*🧌🐲 ```LoVe aNd HoRrOr story```👽 By Chamsiya Laouali Rabo {MRS SADAUKI💫✍️} *SADAUKARWA :* Ga dukkan iyayenmu MATA da suka tsaya tsayin daka don bamu kariya a kan dukkan wani da ke son cutar da mu. *FCWA*☀️ ________________________ 03 Daga inda nake tsaye muke ƴar kallon-kallon ni da Maheer,kallo ne yake yi min wanda ke nuni da cewa eh ya san komai a kaina.A yadda yake juya idonsa tuni na fahimci abin da ke zuciyarsa,magana yake yi min ta ido wacce kuma sarai nake jin abin da yake cewa tamkar da bakinsa ne yake magana. “Ki zo ki cire min ƙwayar kambun maitarki da kika jefa min ,in kuma mutuwata ce farin cikinki shi kenan sai ki ci gaba da riƙon inuwata da kika damƙe” Ido na lumshe bayan na gama sauraran abin da ke fito wa daga idonsa,maimakon na basa amsa ko yi masa zancen abin da ya shafi maganin cutarsa sai tambaya da na jefo masa ni ma ta ido kamar yadda yayi min ,“wane ne kai ? ” ƙin bani amsa yayi sai ya juyar da kansa gefe. “Kar dai ki ce min zargina gaskiya ne ke ce kika jefa shi cikin wannan halin?” Lubna ta tambaye ni tana mai matso bakinta kusan kunnena.“Ki ɗauko kofin ruwa ki same ni a ɗaki” shi ne abin da na ce mata kafin na yi gaba abina,babu jimawa kuwa ta shigo kofin hannunta na karɓa na yi ta kallon ruwan na ƴan sakanni kafin na tofa yawuna a ciki suka fara tafasa suna canza kala a sannu-sannu,sai kuma na ƙara tofa wasu sannan na miƙa mata kofin ta fita. Na ja wata ajiyar zuciya ina jin duk babu daɗi yadda ya wahala domin ni,duk da cewa ni kaina ban son hakan nake yi ba na cutar da mutanen da suka ɓata min rai. Na saki ɗan murmushi a fili na ce “ko wane ne shi? Ta ya aka yi yake magana da ido?” ban kai ga samo amsa ba Lubna ta shigo tana yi min wani kallo kafin ta ce “sai ki je suna son yin magana da ke” Na ce “su wa?” “Likitocin da suka kasa yi masa magani mana,a gabansu na basa ruwan ya sha ya kuma tashi daram ya zauna kan ƙafafunsa shine suke son sanin sunan itaciyar maganin da kika yi amfani da ita” Banda kallonta babu abin da nake yi,kafin ma na ce wani abu Hajiya ta shigo ɗakin tana washe baki tare da kamo hannuna ta ce “zo mu je yarinya kin zama cele ai ,manyan likitoci sun kasa maganin cutar Maheer amma maganinki na gargajiya ya warkar da shi garas.Kar ki so ki ga yadda na fita a guje neman taxi ni na manta ma da akwai mota a gidan,ina dawowa kuma aka ce ke ce kika basa maganin” tana maganar ne tana jan hannuna har muka iso falon. Wani irin faɗuwa gabana yake yi,ga manyan likitocin da duniya ta san da su don har a tv ana nuno su.Duk sun gyara zama suna jiran amsa daga gare ni,shi kuma gogan ya wani haɗe rai kamar ba shi ne ya gama shan yawuna ba yanzu. “Ga ta nan ita ce mai maganin” Hajiya ta faɗa tana wani murmushi kafin ta ɗan bangaje ni ta ce “ki gaishe su” A ɗan rikice na ce “ina wuninku?” kusan duk a tare suka amsa kafin ɗayan ya ce “hajiya dama wannan ce ai kamar na sha ganinta restaurant ” yayi furucin yana wani sanyayyen murmushi yana ɗan ƙare min kallo. “Eh ita ce, tana ɗaya daga cikin masu kula da restaurant ɗin ai” Hajiya ta faɗa . “To likitar gargajiya muna son ganin maganin naki ” ya ƙara faɗa wannan karon cikin raha. Da sauri na kalli Hajiya kafin kuma na maida dubana ga Maheer wanda nake jin idonsa a kaina tun ɗazu. “Eh muna son gani Please ” shi ma ɗayan likitan ya faɗa. Hannuna na ji yana jimƙewa da kansa,yayin da kuma nake jin muryar Maheer tana furta wasu harufa cikin Yaren da ba na Hausa ba,haka ma turanci.Kallonsa na tsaya yi yadda sam bai nuna alamar yana yin wani abu ba,amma tabbas amon muryarsa na fita wanda ina da tabbacin iya ni ɗaya ce kawai nake jinta. Ba a ɗauki lokaci ba na ji wani abu jimƙe cikin tafin hannuna,sai na ɗago hannun tare da buɗe shi nan idona yayi tozali da wata koriyar flowers mai masifar haske. “Waooo! ” likitan ya faɗa yana mai zuwa ya ɗauke flowers ɗin daga tafin hannuna kafin ya ce “wannan ai furen floris,Dr Muhamud ka tuna Dr Maheer ya taɓa nuna mana ita?” “Eh sosai ya ce tana maganin komai amma a lokacin ba mu yarda ba,amma Umar ba ka ganin kamar abin nan camfi ne?” “Ya isa haka don Allah,ku bata furenta ta tafi kun tsaya surutu sai ka ce yau ne kuka fara ganin abin almara” Maheer ya faɗa cikin ɗaga murya,duk suka tuntsire da dariya kafin su fara tsokanarsa can kuma shi Dr Muhamud ɗin ya zo ya miƙo min furen,sai da na saci kallon Maheer kafin na karɓa.Har tuntuɓe nake wurin barin falon,ina shiga ɗaki na ja wata doguwar ajiyar zuciya ban taɓa jin tsoron Maheer ba sai yanzu har wani ƙwarjini na ga ya ƙara min. Ban tarar da Lubna ba, kitchen na wuce don na fi zaton tana can amma kafin nan sai da na ɓoye furen floris ɗin cikin kayana.Ai kuwa can na same ta tana ta aikin tuwon gobe,wuƙa na ɗauka na soma yanka mata albasa ba tare da na ce komai ba.Ita ma sai ta ƙi tanka ni sai ma waƙe-waƙe da ta tsira wanda kusan duk na habaici ne. Na yi ɗan murmushi na ce “ko ki tambaye ni yadda muka yi” Ba tare da ta dube ni ba ta ce “ai na san ba za ki kasa nemowa kanki mafita ba tun da kamar aljana haka kike ” “A'a aljanar ce ba kama ba” na faɗa ina dariya . Ta ce “to ƙila ɗin ma haka ne tun da babu wanda ya san abin da ke cikin duhu” “Amma kin san da cewa na tsorata sosai?” na tambaye ta ina mai tsayawa da yankar albasar. Ta ce “na san dai ba na Maheer ba sai dai ko abokansa” “Wai ke duk komai kin sani game da shi? Ya aka yi kika san abokansa ne?” ba ta kai ga bani amsa ba Hajiya ta shigo kitchen ɗin,wata ƴar matashiyar budurwa na take mata baya. “Lubna ga sabuwar ƙanwa na samo miki,za ta dinga taya ki aiki ki dinga nuna mata komai yadda ake yinsa,don ina sa ran ƙara sunayen jerin wasu sabbin abinci” Cike da ladabi ta gaishe mu duk da dai ko na girme mata ba irin can ba,Lubna ta ce “me sunanki?” “Aliya” ta bata amsa sai muka ɗan kalli juna,Hajiya ta ce “mene ne kuma?” “Babu komai” muka amsa mata. Har ta kai bakin ƙofar fita ta ce “Haule ki haɗa wa Alhaji tea ki kai masa ɗakinsa ki saka citta dayawa da lemun tsami” “Wane alhajin ?” na tambaya da sauri har ina sakin wuƙar hannuna ban shirya ba,Hajiya ta juyo fuskar nan kicin-cikin kafin ta ce “alhaji nawa ke da kwai gidan nan?” Sai da na haɗiye wasu yawu kafin na ce “ɗaya” sai kuma ta juya ta yi tafiyarta.Jikina na ɗan ɓari na ɗora tukunya kan gas na soma haɗa masa tea ɗin wanda dama can ni nake yi amma ban taɓa kai masa shi ɗakinsa ba ina dai jera su kan dianing. Tsit kitchen ɗin ta yi sai Lubna da ke magana jefi-jefi tana kwatanta ma Aliya yadda ayyukan ke tafiya.Ni kuma ina gama dafuwar tea ɗin na juye shi cikin flask na ɗora kan tray da kuma kofukansa,sai da na dubi Lubna kafin na fita na yi tunanin za ta cece ni ta ce na kawo ta kai. Tun da na fara taka step ɗin da za ta kai ni ɗakinsa jikina ya soma rawa,hakan ya bai wa kofukan yin ƙara suna fitar da wani sauti. Bakin ƙofar na ja na tsaya,na fi minti biyu kafin na danna ƙarar rawar neman izinin shiga.Ƙofar ce ta buɗe da kanta,wani sanyi ya ratsa ni haɗi da wani dadaɗan ƙamshi.Murya can ƙasan maƙoshi na yi sallama,ba tare da kuma na ɗago kaina ba. “In kika zuba min ruwan zafi mugun duka zan yi miki fiye da wanda aka baki labari” na tsinkayo muryarsa.Da sauri na ɗaga kai sai na ga ashe ina kusa da shi,hannuna na rawa na ajiye trayn kan table ɗin madubi da ke tsakiyar lafiyayyun kujerun ɗakin.Ina juyawa ƙofar ta rufe kanta,na juyo da sauri ina kallonsa murya na ɗan rawa na ce “hajiya ta ce na kawo ma tea ga shi nan,ni zan tafi” Wani miskilin murmushi na ga yayi kafin ya ɗauki kofi ɗaya ya soma haɗa tea,bayan ya gama ya ƙara ɗaukar wani kofin shi ma ya zuba a ciki duk ina tsaye ina kallonsa. Ya ɗauki kofin ya soma kurɓa kafin ya ɗago ya dube ni ya ce “ki ɗauka ki sha” ko motsawa ban yi ba,sai da ya ƙara cewa “in ba ki sha shayin nan to a nan za ki kwana” ko ida rufe bakinsa bai yi ba na ɗauki kofin na soma sha da sauri duk da kuwa yana da zafi.Ina gama shanye wa kuwa na ji ƙofar ta buɗe da kanta,da wani irin sauri na juya har da ɗan guduna don gani nake in na tsaya wasa ƙofar za ta sake rufewa. Da na fito ji na yi tamkar na baro wuta ne na shigo aljanna, kitchen na koma na taya su aikin sai da aka kira sallah na fita. Ko da na gama sallar ma ban koma ba,ɗaki na yi zamana don gobe ni ma a tsaye zan wuni aikin kai wa mutane abinci.Har sai da aka yi sallar isha'i sannan na fita zuwa ɗayar kitchen wacce ita kuma iya girkin gida kawai ake yi a cikinsa.Kuloilin da ta zuba abinci na soma ɗauka ina kai wa can kan table ɗin cin abinci,bayan na gama sai na ɗauki kwanon abincinmu wanda aka sauya mai girma ƙila saboda zuwan Aliya ne.Ko da na koma ɗaki sai na tarar da su duk sun shigo,Lubna ta fara shiga wanka sannan ita ma ta yi daga nan sai na juye abincin cikin babban faranti muka muka soma ci amma sai na lura Aliya babu abin da take sai satar kallona,tun ban damu ba har na tsargu na ce “Lubna ƙanwarki sai kallona take ki tambaye ta halan na yi mata kyau ne” Lubna ta yi ɗan murmushi kafin ta ce “to ke kin ji Aliya wai kina kallonta” Maimakon ta kawar da dubanta a'a sai ma ta ƙara ƙure ni da ido kafin ta ce “na ga ba ta lafiya ne” Da mamaki na ce “wa ya faɗa miki banda lafiya?” Sai da ta saki wani murmushin kafin ta ce “ga gubar maciji nan tana yawo a jikinki” Kasa ci gaba na yi da cin abincin,ban ce komai ba sai Lubna ce ta yi magana “wace irin magana ce wannan? Ya za ki ce guba na yi mata yawo a jiki? Ke ta ya aka yi kika sani? Ke ki bar ma wannan maganar don in wani ya ji sai ya ce mayya ce ke,Ah to in ba maye ba wane ne zai iya ganin abin da ke cikin ɓargon jikin mutum” Lubna ta ƙarashe cikin faɗa yayin da ita kuma Aliya ta kai hannunta kan goshina ,nan take wani baƙin ruwa suka soma zubo min ta baki da hanci.Kamar zan mutuwa haka na ji yayin fitar abin,can kuma ta janye hannunta wanda yake ta kunno koren haske daga can tsakiya tamkar an kunna lantarki. Lubna ta zabura ta tashi tsaye tare yin baya tana “Ya Rasulullahi! Manzon Allah!” Ni kuwa ido na zuba wa Aliya ko kafin na ce wani abu an turo ƙofa,Maheer ne.Da sauri ta ɓoye hannunta mai hasken a bayanta,shi kuma ni ya kafe da ido kafin ya saki murmushi ya ce “kar ma ki ɓata lokacinki ko kin yi yunƙurin fitar da shi ba zai fito ba”maganar ido ce yayi min ya fice,sai kuma na fahimci cewa ba wai iya ni ɗaya ce wannan karon na ji shi ba har da Aliya wacce jikinta ya ɗauki kyarma tun lokacin da ta ga Maheer ɗin. “Wace ce ke?” na jefo mata tambayar,ba ta bani amsa ba sai tashi da ta yi a guje za ta gudu amma tamkar wata ɓarauniya haka na yi saurin cabko ta na riƙe ta gam ina mai ce mata “wallahi babu inda za ki sai kin faɗa min wace ce ke”........ [16/03 11:36] MRS SADAUKI: *BAƘIN RUHI*🧌🐲 ```LoVe aNd HoRrOr story```👽 By Chamsiya Laouali Rabo {MRS SADAUKI💫✍️} *SADAUKARWA :* Ga dukkan iyayenmu MATA da suka tsaya tsayin daka don bamu kariya a kan dukkan wani da ke son cutar da mu. *FCWA*☀️ ________________________ 04 Jikin Aliya ne ya soma yin rawa kamar mazari kafin ta ce,“don Allah anty Haule ki bar ni na tafi wallahi in ya gano ni ce nan na yi masa kutse zai iya hallaka ni ” Cikin ɗaga murya na ce “ba fa zan bar ki ba ,gwara ma ki bani labarinki kuma muddin ina tare da ke to babu abin da zai iya yi miki.Hatta ita gubar da ya bani na sha ba wai don ya cutar da ni ba ne a'a don ya dinga controling tunanina ne” Lubna da ke can tsaye a raɓe ta ce “wato kenan kin san da gubar ma a jikinki? Innalillahi wa'inna ileyhi raji'un! Allah ka tausaya wa rayuwata kar ka ƙara jefa ni cikin wani cakwalkwalin uƙubar da na tsira a baya” Na dube ta kafin na ce “don Allah Malama ki zo ki zauna kika wani tayar da hankalinki sai ka ce baƙuwar ganin abubuwan nan na siddabaru” Wata muguwar harara ta jefo min kafin ta kalli Aliya wacce har zuwa yanzu hannunta na fitar da wannan hasken. “Wace ce ke Aliya?” na sake jefo mata tambayar a karo na biyu. Kai tsaye ta bani amsa da cewa “ni ɗin almajira ce,na taso cikin Bara na kuma girma cikinta.Ni ɗin ba muguwa ba ce kamar yadda kika yi tunani,duk da kuwa ina ɗauke da BAƘIN RUHI a gangar jikina amma ban taɓa cutar da wani ba sai dai na bai wa kaina kariya ga masu son cutar da ni” Na ja wata ajiyar zuciya kafin na ce “amma me yasa kike jin tsoron Alhaji?” “Saboda shi ne babba a gare ni,powersa ta fi tawa ƙarfi sannan a tsarin zubin halitta protector ɗinsa ya fi nawa tasiri” Ina jin abin da ta ce sai na dubi Lubna wacce goshinta ke tsatsafo da zufa.Na saki ɗan murmushi kafin na ce,“na ga powerki irin wacce ake iya sharing nata ne ,ko za ki taimaka ki gutsurawa Lubna ko da ɗigo biyu ne?” Aliya ta jinjina kai kafin ta dubi Lubna wacce ke shirin artawa a guje amma na harɗe ƙafafunta ta hanyar kallo kawai,don ina juya idona ta kasa motsi na riƙe su gam. Na miƙe tsaye ina riƙe da Aliya har zuwa yanzu,ita ma tashin ta yi da taimakona ta samu ta dafa goshin Lubana koren hasken ya fita shuuu kamar yadda ake zuba man fetur a babur,yana fara shiga kuma ta yi saurin janye hannunta. Na saki murmushi na ce “yanzu dukkan tsoronki zai fice,shi kenan ke ma kin dawo tsagenmu” Da idonta da suka kaɗa suka yi jawur lokaci guda take kallona amma ta kasa magana,ban damu ba don na san ƙarfin ikon sarrafa wani yankin power Aliya ne ke ratsa jininta. An ɗauki kamar minti goma kafin Lubna ta dawo normal,ta ja wata ajiyar zuciya kafin ta ce “Haule kin kyauta kin mayar da ni mai ido uku,sai dai ki sani yau ba zan bari ki rumtsa ba sai kin bani labarinki duka” Na yi ƴar dariya kafin na ce “labarina nada tsayi sosai Lubana amma ke ki fara bamu naki,in kin gama sai Aliya ta ɗora daga ƙarshe ni kuma sai na dinga baku nawa lokaci zuwa lokaci” Da sauri Aliya ta ce “eh hakan yayi gaskiya” sai duk muka samu wuri muka zauna. Yanayin fuskar Lubna ya canza kafin ta ce “ban ma san daga ina zan fara ba,farko dai zan iya cewa na yarda da karin maganar nan da Hausawa ke yi ' ba duka ƙyalƙyali ne gwal ba' tabbas na yarda da hakan bayan shekaru biyu da suka gabata na rayuwata.Kamar dai kowacce ƴar talakawa haka na tashi da burin samun aiki mai tsoka , wannan yasa na kashe kaina wurin yin karatu tuƙuru.Na bi duk wani matakin ilimi da kika sani,na yi digiri har da digirgir sai dai fa samun aiki ne ya zama jan aiki.Tun ina ajiye takarduna har na gaji na bari,cikin haka ne Umma ta sama min gurbin aiki nan wurin Hajiya can farko iya zuwa can restaurant ne aikina ina kai wa costumer abinci .Kamar yadda kika sani iya wannan aikin kawai ba wani kuɗi ne masu yawa ba,amma haka nake yi don gujewa zaman banza.Sama da wata biyar ina wannan aikin ,daidai ɗaya rana ban taɓa cire burina na samu babbar kujera akan karatun da na yi ba.Sau tari ina jin haushi in na ga masu kuɗi suna shigowa nan su ci abinci na kuɗaɗe dayawa har su bar ragowa nan.Masu zuwa da ƴan mata kuwa haka zan zauna ina ta kallon yadda maza ke tattalinsu,duk abin da kika duba a jikin ƴan matan kuɗi kawai ke magana.Sai fa rayuwarsu ta soma burge ni ina sha'awar cewa ina ma ni ce,zan iya ce muku ma har hassadarsu ke tsarga min musamman in na ga mace wacce ba ta yi wani dogon karatu ba amma tana da kuɗi sosai nake jin haushi.Sai kuma ƙarfin imanina yayi ƙasa ina ganin Allah ya azurta kowa amma ni ya bar ni cikin ƙuncin talauci ni iyayena waɗanda kusan ma a lokacin ni ce ke kula da su saboda Abbana da ya samu karaya bai aikin komai. Kusan da wannan burin yin kuɗi nake kwana nake kuma tashi da shi har Allah ya jefo min wata ƙawata da muka yi makaranta da ita.Ba zan manta ba wata baƙar rana ce wacce ta shiga lissafin ƙaddarata,ina kwashe plate ɗin da aka ci abinci na ji muryar wata da na sani ta kira suna “oh Lubna ? Ke ce?” ni ma cike irin zumuɗin nan irin ka jima ba ka ga mutum ba na nufe ta zan rungume ta amma don wulaƙanci ta yi saurin ja baya tana yamutsa fuska kamar ta ga kashi kafin ta ce “wai ƴar aiki kika zama bayan duk uban karatun da kika yi? Ki rasa abin da za ki yi sai tarben customer ?” Duk da na ji babu daɗi haka na danne zuciyata na ce “to ya zan yi tun da ban samu aikin gwamnati ba,faɗa min Zulaihat ina kike aiki?” Ba ta bani amsa ba sai wuri da ta samu ta zauna kan ɗaya daga cikin kujerun da ke wurin,“me ke da kwai marar nauyi ? Don yunwa nake ji shi yasa ma na tsaya da motata cikin rana na ci abinci na wuce” ni kuwa gwiwaina ne suka yi sanyi jin Zulaihat ce wai da mota duk da ban yi mamaki ba duba da suturar jikinta iya jakarta ma tana iya ciyar da ƴan gidanmu na tsawon wata biyu,uwa uba kuma wayarta iphone wacce kusan duk masu zuwa restaurant ɗin nan ina ganinsu da ita. Jiki na yi min ɓari na ce “jira na je na kawo miki” sai na koma can ciki na haɗo mata abincin da na san ƴan gayu irinta na so har da lemun kwalba,da na kawo mata sai ta bani damar zama kan kujerar da ke kallon tata.A kunyace na zauna, Allah yayi min sa'a ma babu kowa.Cike da yanga take juya cokali cikin plate ɗin kafin ta soma ci tana latsa waya,message ne na WhatsApp ta soma kunna wa ina saurare kusan duk akan manyan kuɗi ne da kuma kayan da mutane suka yi oder ko kuma suka saya suka yaba,can kuma ta soma mayar wa na ji tana zancen za ta tura miliyoyin kuɗaɗe.Ni kuwa ina zaune sake da baki ina kallonta,kuma kar ku ji zancen wasa wallahi burge ni ta yi yadda take abu na ƴan gayu.Hummm! Faɗar mintinan da na share a zaune kafin Zulaihat ta dube ni ƙaramin misali an fi goma sha,can ta ɗago ta dube ni da idanunta da suka sha gashin zamani ta ce “Lubna gaskiya ba zan ɓoye miki ba na ji takaicin ganinki a wulaƙance kina boyi-boyi,da kyawunki da iliminki.Amma dai komai ya wuce tun da Allah yasa mun haɗu zan duba na gani” Ba tare da na san wane aiki ne za ta samo min ba na shiga yi mata godiya,nan ta shiga nuna min hotunanta da ta yi ƙasashen duniya .Ni kuma sokuwa girman burina sai ƙara farashi yake ina jin cewa ni ma nan gaba kaɗan zan koma kamar Zulaihat,da za mu rabu sai ta bani lambata da ke jikin wani ɗan ƙaramin kati mai ɗauke da dukkan address ɗinta da kuma kantinta na business.Ba ta bar ni haka ba,sai da ta ware dubu goma ta bani shi ma wai don ba ta da canji ne kuɗinta duk daloli ne. Da na isa gida kasa bacci na yi,haka na yi ta juyi kan shimfiɗa .Saƙo kuwa na rubuta shi ya fi cikon casbi kuma sai na goge a ganina sam ba ta cancanci in yi mata text ba.Can na daure na kira ta, lokacin ƙarfe goma saura kwata na dare,har zan yanke kiran sai kuma na ji ta ɗauka tana cewa “Lub baby ƴar halak kin ƙi ambato yanzu na gama maganarki wurin oga ” Na washe baki na ce “na zata ma kin yi bacci,na gode sosai da wannan ƙoƙari me ogan ya ce ?” “Ki zo gobe nan babban kamfani yana son ganin ki,sannan ki haɗo da takardun karatunki sai takardar shaidar ɗan ƙasa da kuma hotonki kala biyu ” Tamkar na yi hauka haka na ji lokacin ba tare da na san ƙaddara ce da rabon a yi ke ja na ba.Tun a daren na jawo ambalof na shiga haɗa takarduna don dama kusan ina da komai da ake buƙata in aka fidda hoto.Bacci ɓarawo ne ya ɗauke ni a wannan daren,shi ma rabi da rabi ne.Tun bayan sallar asubah na shaidawa Umma zancen aikin sosai ita ma ta yi murna.Zuwa ƙarfe takwas na je gidan hoto aka yi min guda biyu,a nan take kuma aka bani su.Daga nan na kira Zulaihat sai ta ce na jira za ta zo ta ɗauke ni,ina nan tsaye ina jiran zuwanta sai wata tsohuwa ta tsaya kusa da ni tana mai neman sadaka .Murnar na samu aiki yasa na zuge jaka na bata sadaka,tana karɓar kuɗin sai ta soma juya su haɗi da kallona tsakiyar ido ta ce “ƴata ki koma gida inda za ki je ɗin nan babu alkhairi ” wani irin haushin ta bani kafin ma na kai ga yin magana Zulaihat ta parker motarta tana yi min horne,da sauri na zagaya na buɗe na shige ina jin tsohuwar nan na sake jaddada min maganarta amma na yi kunnen uwar shegu da ita

Chapter 2 of 11